Kurkukun Kaddara Takun Karshe Page 9 Complete


Health College

Kurkukun Kaddara Takun Karshe Page 9 Complete

 _ *~✊💋BOSSLADIESWRITERS💋✊~*_




سجن القدر💋✊🔥



~Takun Ƙarshe🔥~




قصة حب رومانسية غير عادية بين السجناء مع تطورات معقدة💋💘😘



An extraordinary romantic love story between prisoners with complex twists ❤💋💘




Daga alƙalamin Boss Bature💋✊




__________________________✍️







Har Ya ruƙo hannunta za su shiga ciki sai kuma Ya dakata yana faɗin "Au namanta, Auntyn ku ummi tana buƙatar abinci ban sani ba, ko akwai abunda chefs suka gama girkawa yanzu"? ya tambaya yana duban ta.


 "Akwai naga sun kammala Rice and chicken stew tare da coleslaw hada zobo ma ... " kafin ta ƙarasa lissafa mashi yace"Okey, Ki jira ni, bari na shiga ciki in kar6o mata" amsa mashi tayi da toh.


 Bayan shigarsa kitchen din ta soma tunanin ko awani hali Garkuwarsu ya ke a ciki? ta yi matuƙar damuwa da shi, ganin shi da take yi a mawuyacin  hali ba karamin karya mata zuciya ya ke yi ba, rabon da ta sanyashi a idanunta tun da asuba da su ka shiga yi mashi addu'a, da tunanin shi ta wuni ta bari sai da anjima ta shiga duba shi.


   "My babe, I'm back" Muryar Boss man ce ta fargar da ita, da sauri takai dubanta gare shi, Hannayen shi ruƙe da handle din wooden tray mai faɗi, daga saman shi haɗaɗdun warmers ne   babba da ƙarama tare da plates da sauran tarkacen kayan abinci"


 Miƙa mata yayi kar6i nan, ta sanya hannu ta kar6a cikin kitchen din Ya koma jim kaɗan Ya dawo hannayen shi ruƙe da wani madaidaicin faranti mai ɗauke da mixed drinks masu sanyi.


 Ganin tana kallon shi yasa shi kashe mata ido ɗaya, murmushi tasakar mashi, a tare suka jera zuwa cikin falon.


Jikin Batool Har Kerma Yake Yi wurin mikewa da wani irin sauri ta nufi Unaisah zata rungumeta, ganin Tray a hannunta yasa ta dakata tana faman ɗaure mata fuska tace"Ina kika shiga inata nemanki"


"Ina a kitchen fa, Girki Na tsaya taya masu aiki" ta faɗa tare da wucewa ta sauke tray din hannunta saman Carpet, Parveen tun da tayi tozali da Abinci takasa samun sukuni, Tafi kowa zalama.


A Plate Batool ta zuba ma Ummi abincin ta hada mata da pineapple juice ta miƙa mata, fuskarta da fara'a ta kar6a tana fadin nagode My babe," a tsanake ta soma Ci.


    Ɗaya bayan ɗaya unaisah ta soma kasa masu abincin tana miƙa masu a plate, bayan ta gama da su itama ta zuba nata tare da Boss man a plate ɗaya, suka zauna suna ci gwanin ban sha'awa, falon Yayi tsit baka jin sautin komai saina taunar abincin da suke ci...


  "Ummi Ina son Yin magana dake  bayan sallar magrib" Boss ne yayi mata maganar, amsa mashi tayi da toh.


"Amma wannan ɗin abincin daren mu ne"? Acewar Parveen, Harararta Naufal Yayi.


 "Kusan ƙarfe shida na marece, A haka Har kike tambaya, toh abincin dare ne, mu da cin wani abincin sai gobe da safe in Allah yakaimu" javed ne Ya bata amsa Yayin da yake kur6ar lemu me sanyi.


 "Ba'a magana idan Ana cin abinci," Boss ne ya faɗa yana duban su.


 "Dariya fa da murmushi suma ba'ayi"?


 Jemimah ce ta jefa mashi tambayar yayin da take cunkusa abinci abaki tana tauna.


 Dariya suka sanya gaba ɗayansu cikin raha.

  

"sajeed Ina wayata" 


Dafe kai Yai da hannu ɗaya"Am sorry sister, Na cinye maki chargy, bansan ko kina da charger ba"


 "Akwai charger bani wayar" da sauri ta miƙe taje gaban sofa din da yake a zaune, Wayar Ya zaro daga trouser pocket nasa ya miƙa mata ita.


  Tasa hannu ta kar6a, kafin ta nufi bedroom dinsu, shigarta keda wuya wayar hannunta ta soma ringing, tana kokarin ɗaga Wayar ta kashe kanta kamar tayi hauka saboda ta gane number da suka kirane ita da sajeed.'

 Cikin takun sauri ta nufi backpack din su, ta buɗe ta dauko cazar wayar ta jona a socket, akan idonta wayar tayi haske alamar ya ɗauka, lumshe idanunta tayi tare da jingina bayanta jikin gadon, zuciyarta a cike fal da tunanin shi.



*💋NAZLI👑*


Sautin daddaɗan kiɗa ne da ke tashi a katafaren gym room (ɗakin motsa jiki) da ke a gidan prime minister, an ƙawata shi da manyan injinan motsa jiki, a tsaye take saman thread mill tana gudu cikin shiga ta kayan motsa jiki, sport bra tare da short launin black colour, sunyi bala'in yi mata kyau, sun bayyana farar fatarta sol ko kwarzane babu, tamkar bata ta6a yin rarrafe ba arayuwarta saboda hasken fatarta harta gwiwar ƙafarta tayi jawur da ita, dirar mace doguwa ga kyan sura, ta ɗaure lallausar baƙar sumar kanta sai salƙi take yi da sheƙi ta sauko har saitin waist din ta, gaba ɗaya ta tattara nutsuwarta akan abun da take yi, sautin music din ba ƙaramin ni'ima yake samar mata ba, kyawawan idanunta na akan tanƙameman madubin dake manne da bango, zufa ce ta soma tsastsafo mata ta ko'ina ta jiƙe sharkaf da ita, babu alamun gajiya atattare da ita, daga gani ta ƙware a 6angaren gym.


    Bakomai ne acikin zuciyarta ba, face zallar begensa, duk yadda taso ta hana kanta tunawa da shi abun yaci tura, tayi tunanin zata iya sarrafa zuciyarta wurin hana ta tunaninsa sai dai abun yaci tura, a kowani daƙiƙa son shi ƙara ninkuwa yake yi a zuciyarta, ga dukkan alamu Nazli batasan menene So ba, ko da yake girman kai da izza sun hana ta gane cutarwar da take yima kanta, shiyasa ta kasa miƙa wuya"


 Tunanin shi ne ya haifar mata da jin Kasala, ba arziƙi ta dakata da motsa jikin, ta kai hannu ta ɗauki short towel fari ƙal ta soma tsane jikin ta da shi, bayan ta kammala fitowa tayi daga gym room din ta nufi bedroom dinta, kai tsaye ta shiga bathroom domin yin wanka.


  Shigowa ɗakin Yazrin tayi cikin shiga ta riga da wando black and white, tayi rolling veil akanta, hannunta ruƙe da wayarta.


     Ganin babu ita a dakin yasa tayi tsammanin ko ta fita ne har zata juya ta juyo motsin ta a toilet da sauri ta la6e a bayan labule.


  Gently ta zuro ƙafafunta dake sanye cikin slippers, bathrobe ce a jikinta fara ƙyal, hannunta ɗaya ruƙe da towel sai faman tsane sumar kanta take yi.


   Yazrin dake a la6e bayan labule, wayarta ta danna ta shiga camera ta ɗage labulen a hankali ta soma ɗaukar Nazli video batare da sanin ta ba.


  Dressing mirror ta nufa cikin takun qasaita, wasu tsadaddun mayukan gyaran jiki ne asaman mirror din, bayan ta zauna ta soma bin ko'ina tana shafe shi a tsanake, kafin ta dauko bakhhoor burner ( turaren wuta) ta soma turara jikinta da sumar kanta, komai nata cikin aji take yin shi, Nazli macece mai tsafta ga son gayu, kuma ma'abociya son ƙamshi. 


 Duk wani motsinta, Yazrin na kallonta ta cikin camera, bayan ta gama gyaran jikin nata, closet ta nufa jim kaɗan ta fito, har ta canza kayan jikin ta zuwa kimono robe, yazrin da ke ta daukar ta video kayataccen murmushi ne kan face dinta, aranta ta ayyana ukhty Nazli badai iya gayu ba, bata gama zancen zucin nata ba, taga Nazli ta haye saman Royal bed dinta hannun ta ruƙe da wayarta, bakomai take kallo ba face hotonsa, har zooming dinshi take yi da zira ziran yatsun hannunta, hoton da take kallo tsohuwar ajiyace a kalla yakai shekara biyar, lokacin yakai masu ziraya a canada, ba tare da sanin shi ba ta dauki hotan,  dama duk in yaje basa jituwa da Nazli, har ya bar ƙasar basa sakarma juna fuska kai kace makiyane, Yazrin ce kadai suke mutunci da juna, kuma a lokacin suna matuƙar ƙaunar junansu, amma izza ta hanasu bama juna kulawa sai dai su yi magana ta text message, tamkar basa a gida ɗaya.


    fita tai daga gallery ta shiga wurin messages dinsu

  Har ta rubuta "I miss u.... ' sai kuma ta goge, zuciyarta na raya mata zubda aji ne ta nuna ta damu dashi, shi ne yakamata yafara yi mata magana

 Jefar da wayar tayi gefenta, tare da kai hannu taja lallausan duvet dinta ta lullu6e fuskanta, ganin hakan yasa Yazrin fitowa daga bayan labulen cikin sanɗa ta nufi gadon, tare da hayewa ta janyo wayar Nazli cike da fargaba cikin sa'a ta ɗauko ta batare da security din wayar ya shiga ba, hakan ba karamin dadi yayi mata ba.


   Whatsapp dinta taso ta shiga sai dai kash password Ya hanata, tunani ta soma yi me Nazli ta rubuta a matsayin password dinta?


 Gudun kada ta tayi mistake ta samu matsal

 Zurfi tunani ta shiga, can zuciyarta ta raya mata cewar ta jaraba rubuta date of birth din Aki Owais saboda ta ta6a ganin ta rubuta shi a diary din ta amatsayin rana mafi mahimmanci agare ta.


  Wani irin tsalle ta daka ganin Ya buɗe, da sauri ta shiga nutsuwarta tana leƙen Nazli, wadda tuni bacci yayi awon gaba da ita 

  Yazrin tayi mamakin ganin tsawon lokacin da suka dauka ba suyi magana wa junansu ba, Ranta ya sosu bata ji daɗi ba, ji take kamar ta dauki pillow ta bubbuga mata akanta tsabar haushin da taji.

  "Ƴar bakin ciki, In sha Allah baki da miji a duniyar nan daya wuce big bro, bazan zauna na zuba maki ido kina cutar kanki ba, Akhi Owais shi ya dace ya mallake ki, nayi maki sha'awar auran shi saboda samun miji nagari irin shi ba abu ne mai sauƙi ba, Ina son kiyi rayuwar farin ciki yar uwata, dole na shirya tsakaninku.... " acikin zuciyarta ta furta maganar tare da cigaba da danna wayar, daga wayarta ta tura video din data dauka, kaitsaye ta yi mashi sending, shaf shaf ta rubuta mashi text message da harshen turanci kamar haka


  _Nayi kewarka bugun zuciyata, ina mai baka haƙurin nuna halin ko'in kula da nayi, ba'asan raina ba, nayi danasanin hakan don ba ƙaramin cutuwa nake yi ba na rashin jin ɗumin jikinka a kusa dani, ka duba whatsapp in ka, na tura maka video dina don ya ɗebe maka kewar rashi na, nasan zaka ji dadin kallon shi_


 fuskar yazrin dauke da murmushin mugunta ta tura mashi message din, bayan ta gama ta ajiye mata wayarta, ta nufi kofar fita daga dakin tana faman sakin dariya, ta riga da tasan me zai biyo baya muddin Nazli taga aika aikan da tayi mata ba ƙaramin husuma zata tada ba, zata ce ta zubda mata aji awurin chief owais.


*A GIDAN UNCLE ƊAN IYA*


Kusan Atare Su ka yi Parking din motocin su, Mahboob ne Ya fara fitowa daga front seat hannun shi ɗaya ruƙe da key din Motarshi, fuskarshi dauke da murmushi yake kallon Motar  zahra.


 "Sannu da dawowa Hajiya Zahra Surukar Kaka Obinna" Ya faɗa tare da buɗe Back Seat din Motar Shi Ya duƙar da kai Yana leƙan Baby Junaid dake zaune Hannayenshi rungume da Food basket dinshi, Ga school bag din shi a gefe, Sai faman ɗaure fuska Yake, Da alama rigimar tashi ce ta motsa.


  "Ranka Shi daɗe, Mun ƙaraso gidan, zaka iya takawa da kafarka ne mu shiga ciki ko kuwa ni kake so In goyaka"? Da zolaya mahboob yayi maganar yana dariya.

 Yamutsa mashi fuska baby junaid yayi   "ni ka goyani" Ya fada A kule.


  Juya mashi baya Mahboob Yayi Ya ɗan zuƙunna Baby Junaid Ya Haye bayan nashi, Bayan Ya miƙe Ya ɗauko mashi Backpack dinsa tare da kwandonsa


 Adai dai Lokacin Zahra Ta fito daga motarta, tayi shiga cikin Lafaya, Hannunta ɗaya ruƙe da Ƴar purse dinta

  Fuskarta da fara'a take duban Baby Junaid Da Mahboob

  "yau wata rana mun dawo gida atare, baby junaid dina zo nan" ta faɗa tare da miƙa mashi hannu, babu musu Ya soma kiciniyar saukowa daga saman bayan mahboob, daukarshi tayi Mahboob yace"Wato ni kake gudu? Zamu hadune ɗan rainin wayau, tun da naje dauko shi Daga school Yake ta jin haushina saboda naje amakare shi kaɗai Ya rage ba'aje daukarsa ba, baisan nima bada son raina ba, Motarce ta samu matasala sai da nakaita gyara tukunna naje daukoshi da ita"

Dariya zahra tayi"Gaskiya baka kyauta ba, taya zaka bar mana Baby Shi kadai Ga yunwa, meyasa baka kirani awaya naje daukosa ba"


"Banyi dabarar yin Hakan ba, Yanzu dai tun da mun dawo gida, gashi nan ki kaima jatumarsa, nagaji da kallon kumburarran fuskarshi" 


 "Mahboob baka da mutunci, zamu rama ne" ta faɗa tana dariya, baby junaid kuwa Ya ɗaure fuska, Kumatunshi sunyi jawur da su, da alama kuka Yake so yayi.


   Atare suka nufi cikin gidan, tana agaba mahboob Yana abayanta 

Bayan shigarsu Falo, Suka taras da mami da Ummi zaune suna kallo a plasma tv din falo, Cikin girmamawa suka gaishe da su.


   "Sannun ku da dawowa, Ya gajiyar aiki"? Cikin Kulawa mami tayi maganar, atare suka hada baki wurin cewa"yawwa mami"

 Ummi dake kallon Baby junaid tace"to fa, Me akayi masa ne naga yana ɗaure fuska"

Mahboob Na dariya Yace"wallahi Ummi Rigimarshi ce ta motsa, Kinsan Halin shi.


Zahra tace"bawani nan, shine Yaƙi zuwa ɗaukarshi da wuri, Yabar shi a school yana ta jira"


 "Gaskiya mahboob Baka kyauta mana ba, saboda Allah, Haka akeyi? Sai kabar mana Yaro  ga Yunwa" Ummi ce ta faɗa tana satar kallon baby junaid duk don ta nuna mashi taji Haushi.


 "Ay mashi uziri mana, hakanan dai Mahboob bazaiƙi zuwa ɗaukar baby junaid ba sai dai idan wani uzirinne Ya ruƙe shi" mami na fadan hakan Mahboob Yace"ay har bayani nayi ma zahran, motana ne Ya samu matsala sai da nakaita gyara, in sha Allah Hakan ma bazata ƙara faruwa ba zan dinga zuwa ina dauko shi akan lokaci"

 Ummi tace"haka Yakamata"

 "Zonan babyn mommynsa" acewar Ummi ta fada tana miƙa mashi hannu, maƙe mata kafaɗa yayi alamar bazaije ba, Saima Ya ƙara ƙanƙame Zahra, mami na dariya tace"In banda abunki sai kace bakisan halinsa ba idan Yana fushi Yafi buƙatar jin ɗumin mommynsa,"

"Ina auntyn tawa take"? 

"Tana a kitchen"

Maimaita kalmar kitchen Zahra tayi, aranta ta furta me kuma Aunty Aneelerh take yi a kicin"? Batayi Ƙasa a gwiwa ba, Ta nufi kitchen din Mahboob Har Ya zauna kan sofa, sai kuma Ya miƙe Yabi bayan zahra.

 Tunkafin su ƙarasa kitchen din suka hango Aneelerh ta haɗa uban gumi a kitchen tana girki, Ita kadai.

  Sam bata Ji alamar shigowarsu ba, ta zage damtse sai motsa miya take Yi 

  "Aunty Aneelerh"? atare suka haɗa baki wurin kiran sunanta,  da sauri Ta rufe soup pot din, Ta juyo tana fuskantarsu, kafin ta ɗaura idanunta akan Baby Junaid,

Murmushi ta sakar masu "Sannunku da dawowa,"

 "Yawww, Auntyna, Yau ke kike Aiki akitchen Ina Ana"? Zahra ce ta jefa mata tambayar, Mahboob Yace"Allah yasa dai lafiya"

Girgiza kai tayi cikin sanyin murya ta soma magana"ba lafiya...." gaba ɗaya ta labarta masu abunda Ya faru zuwansu dakin Ana tare da su mami, Hankalinsu Ba ƙaramin tashi yayi ba, Musamman Mahboob.


 "Bansan Ya zanyi ba, Taƙi faɗa mana abun da ke damunta, Ni tsorona kada wani abu Ya faru da ita" fuskarta da tsantsar damuwa ta furta maganar

  "Nima hankalin bai kwanta da ita ba, dafarko nayi tsammanin Damuwar halin da ƴan uwanta suke aciki ne ke damunta, ashe ba haka bane, daga gareta ne" Acewar Mahboob.

 Kafin Zahra ta furta magana baby Junaid Ya fashe da kuka, Dama ranshi a6ace Yake, da sauri Aneelerh Ta miƙa hannu ta kar6e shi cikin sigar lallashi take jijjiga shi tana fadin"Am sorry My baby boy, kayi hakuri nasan nice na 6ata maka rai,' muryarshi da shessheƙar kuka Yace"wayyo Allah mommy, Kuna ta surutu Kin ƙi kulani, baki missing ɗina ba" dariya zahra da mahboob su ka yi, hakan Ba ƙaramin 6ata mashi rai yai  ba, Hada Jifar Su da harara 


 Shafa sumar kanshi tayi"Na kar6i laifina, ay min afwa... " zumbura mata baki yayi,

 Zahra tace"aunty Aneelerh, Ki tafi dashi ɗaki Ni zan ƙarasa girkin, Inyaso da anjima Sai mu ƙarasa tattaunawa"


 "Keda kika dawo daga aiki a gajiye kuma kike neman in bar maki girki, a'a gaskiya Ki bari na ƙarasa ai ba ni kadai nake yi ba, Tare da Ummi muke Yi, bata jima da komawa falo ba.. "

 Kafin Ta ƙare maganar, Mahboob Yace"tun da tace zatayi kibar mata kawai, Nima saina tayata, baby junaid yana buƙatar kulawarki, Kije Ki lallashe shi"

Murmushi tasaki Tana kallonsu, Har cikin ranta take jin tsantsar kaunar Yan uwanta, Haɗin kansu Na burgeta, fatanta Allah Ya dawwamar da farin ciki arayuwarsu, Hakika suna kyautata mata.

 "Nagode, zahra, Mahboob, Allah Ya barmu mun ku,"

 Amsa mata su ka yi da ameen

 "Zan shiga ciki, pls zahra Ki dafa mashi indomie" amsa mata tayi da toh, Bayan fitar Aneeleeh daga kitchen din, Mahboob Ya ajiye food basket din Junaid, Yabi bayan aneelerh hannun shi ruke da backpack din Baby junaid,

Bayan Ya ajiye mashi adaki, Ya fito Ya nufi nashi room din, shaf shaf Yayi wanka Ya sanya gajeran wando da ƴar singlet, Kafin Ya  nufi kitchen don Ya taya zahra girki kamar wani mace, atare suka cigaba da kula da girkin, suna tattauna fira dangane da matsalar Ana.

"Amma kai a tunaninka meke damunta"?

"Sister Ni kaina nakasa gane wani tunani zanyi dangane da matsalar Ana, sai dai kawai mubita da addu'a, Allah ya yaye mata abunda ke damunta,'

"Ni aganina, Mu kar6i Contact din Ƴan uwanta , mu tuntu6esu may be sunsan meke damunta, tunda sunfi kusa da ita"

"Nima nayi tunanin hakan, Yanzu dai mu jira, zuwa lokacin da su Abie zasu dawo gidan, nasan zasu Kirata su tambayeta,"

 "Hmm kana ganin zata Iya faɗa masu gaskiya? Bayan Aunty Aneeleeh tace tare da su mamie suka je dakin nata amma taƙi fada masu, ai ni aganina idanma akwai wanda Ya dace ta fadamawa baiwuci su mami dinba"


 Jinjina kai Mahboob Yayi"kin fadi gaskiya,"

"Ni abunma Ya fara bani tsoro, da naji aunty aneeleeh tace Ana ta dinga kwala masu ihu tana fadin su fita subar mata dakinta, Anya mahboob bata da matsalar kwalwa?

Mahboob Yace"Bana tunanin hakan, wata'kil Aljanune suka shige ta, mu cigaba da tayata addu'a Allah Ya kawo mata saukin abunda ke damunta"


 "In sha Allah zamuyi mata"

 Daga haka basu ƙara magana ba, sun maida hankali akan Girkin da suke Yi.


Fitowa Aneelerh tayi daga Bathroom, Bayanta goye da baby junaid, tayi mashi wanka, sai faman hade mata fuska Yake Yi, Riga da wando ta Dauko ta zura mashi ajikinshi, ta feshe shi da turare, zama tayi gefen gadonta,ta ɗaura shi saman laps dinta, hannunta ɗaya dafe ta shi,tarasa meke yi mata daɗi, Ita dai Hankalinta bai kwanta da halin da Ana take aciki ba, Ji take aranta kamar wani abunne Zai faru, zuciyarta batayi mata daɗi, sam ta manta da baby junaid Tayi zurfi a tunaninta, Har Ya fara lumshe ido zaiyi bacci, Muryar Zahra ta fargar da su, 

    hannunta biyu ruƙe da plate din indomie, Sai tiriri Take Yi, daga saman indomie din ta shimfiɗa mashi Soyayyan kwai, Mahboob Yana abiye da bayanta, Hannun shi ruƙe da mugs biyu na kakkauran Tea.


 "Sannunku da kokari, nasanya ku aiki ko hutawa ba ku yi ba"


  "Pls ki daina fadin hakan, Mu yakamata mu Yi maki sannu, anbarki da girki a kitchen, Su mami suna a falo fira tai dadi" Mahboob Ne yai maganar

 Asaman Table zahra ta daura plate din, Mahboob Ma ya sauke nashi mugs din, atare suka fuce daga dakin.


 Baby junaid tunda yayi tozali da indomi Ya soma sakin murmushin murna, Har wani lashe le6ensa Yake Yi

 "Mommy da zafi, kuma ni Yunwa nake ji Allah" ashagwa6e Yayi maganar

 "calm down Your Mind my baby boy, Ni zan baka da hannuna, kasan dai mommy bazata bar baby junaid dinta Yaji zafi ba ko"? Ɗaga mata kai yai alamar"

"Yawwa my boy" ta faɗa tare dakai hannu ta dauki fork, ta soma nannaɗo taliyar tana hura mashi da baki idan ta huce saita tura mashi abaki, kusan atare suka cinye indomie din dakwai, Kafin suka sha tea din su.

  "Kada kayi bacci, Yanzu za'a fara kiran sallar magrib," ɗaga mata kai yai alamar toh, Janshi ta soma yi da fira duk dan kada yayi bacci.


Bayan Kammala sallar Magbrib, A lokacin Abie da Uncle ɗan Iya sun shigo gidan, babu wanda Ya tuntu6esu da maganar Ana, sun bari ne sai sun huce gajiyar da suka kwaso ,Har saida suka kammala cin abincinsu, Tukunna Ummi ta sanar da su Halin da ake ciki, babu 6ata lokaci, Abie Yasa suka hallara A falon gidan gaba ɗayansu, Ana ce kaɗai ke babu acikin su.


Aneelerh da zahra da Mahboob suna zazzaune kan Carpet, A lokacin baby junaid Ya jima da yin bacci, Yana can kwance saman gado.

 Abie da Uncle ɗan Iya suna a zaune saman Sofa mai mazaunin mutun uku,  Abie Yana sanye da farar jallabiya ya manna farin glass a idanunsa, Yayin da Uncle ɗan Iya yake asanye da Riga Yar shara ta farin Yadi, daga ciki ya sanya gajeran wando baƙi.

 Su Mamie da Ummi suna zaune saman Sofa mai mazaunin mutun biyu, dukansu Hijabai ne a jikin su. tamkar mutuwa ta gifta babu mai magana acikinsu, Har na tsawon mintuna kafin daga bisani Uncle ɗan Iya yayi masu gyaran murya, suka ɗago suna duban shi, da hannu Ya nuna Mahboob

 "Je ka kira ta" Amsawa mahboob Yayi da toh, ya miƙe ya nufi bedroom din Ana, abakin ƙofar Ya tsaya tare da kai hannu yayi knocking kofar kusan sau uku bata buɗe ba, Har ya fara tunanin ko bacci tayi ne sai kuma Yajiyo mutsu mutsunta ta cikin ɗakin.

A hankali ta turo ƙofar ɗakin, tare da leƙo da kanta,

 Ko da mahboob yai tozali da fuskarta sai da gabanshi ya faɗi ganin yadda ta kumbura suntum, idanuwanta sun kaɗa jawur, daga gani kukan take cikin yi

In a calm voice Ya furta"ina fata ban katse maki baccin ki ba"

Muryarta adisashe tace"ban kaiga Yin baccin ba,"

Jinjina kai yayi"Uncle ne yace in kira ki, su na a falo shi da su mamie da abie"

Shiru tayi jimmm kamar bazata motsa ba, har saida ya maimaita mata maganar tukunna tace Toh, ka jirani mu tafi atare" 

"Okey" 

Maida ƙofa tayi ta rufe ta, badajimawa ba sai gata ta fito sanye da doguwar riga, ta yafa mayafi akanta,

 Jin ta ruƙo hannun shi acikin nata ne yasa shi saurin kallonta, sam hankalinta ba akwance Yake ba, bai yi yunƙurin raba hannun shi daga nata ba, A haka suka nufi falon, sai da suka kusa isa yayi saurin zame hannun shi daga nata, Takun tafiyarsu ne Yaja hankalinsu mami ga dubansu

Cikin girmamawa Ana ta gaishe da su, tare da samun wuri gefen Aneelerh ta zauna tana faman jan numfashi, bayan mahboob Ya zauna.


 Abie dake kallon Ana Ya soma Magana a tsanake


"Inaso ki natsu ki saurare ni," jinjina mashi kai tai alamar toh

"Ki ɗauka tamkar mahaifanki ne suke yi maki magana, kada ki ji shakkun faɗa mana abun da ke damunki, saboda mu kaɗai ne makusantanki a yanzu, Haƙƙinmu ne mu kula da rayuwarki, Idan wani abu ya same ki ba zamu ji daɗi ba" wani irin sanyine ya ratsa zuciyarta, haƙiƙa kalaman abie sun yi tasiri a zuciyarta. 

  Uncle ɗan Iya ya ɗaura da cewa"banji daɗin abun da Ummi ta fada min ba, baki kyauta mana ba, ashe baki ɗauke mu yarda muka ɗauke ki ba, meyasa zaki zauna abu na damunki ki gaza gaya ma kowa? Meye amfanin 6oye mana eye"? Muryarshi da faɗa yake yi mata magana, alamar ranshi ya 6aci.


   Sunnar dakai ƙasa Ana tayi yayin da idanunta ke akan Yatsun hannayenta

  "Meke damun ki ne, inaso ki faɗi mini gaskiya"? Ya jefa mata tambayar, Su Aneelerh da su mami sun natsu suna kallon ta.

Numfashi taja tare da sauke shi A hankali ta furta"Idan na 6ata maku rai, dan Allah ku yafe ni, Aunty Aneelerh, mami, ummi, Zahra, Mahboob, abie, uncle, Allah ne kaɗai zai Iya biyanku, duk da kasancewata yar aiki agidan nan, Sannan ba musulma ba amma kun daukeni tamkar jinin ku, ko dan saboda nuna damuwar da ku ka yi akaina zan fada maku gaskiyar abun da ke damuna...." ta faɗa tana mai ƙanƙan da kanta, gaba ɗaya duk sun ƙagara da suji meke damunta, musamman Mahboob Ya kasa ɗauke idanunsa daga kan fuskarta, wani irin tsantsar sonta da ƙaunarta yake ji, ga matsanancin tausayinta dake addabar zuciyarsa.

 "Cikin kwanakin nan, Ina yawan yin mugayen mafarkai, waɗanda suke neman haukata ni, bansan meyasa hakan yake faruwa dani ba, idanuwana suna gane min abunda yafi ƙarfin gani na wanda silar hakan yasa nafara zaucewa, ni gani nake ma kamar mutuwa zanyi..... " muryarta na rawa ta ƙare maganar nan take ta fashe da kuka mai sautin gaske, Hankalin su ba ƙaramin tashi yayi ba, Jikin kowannansu yayi sanyi

 "Kiyi shiru, Kukan Ya isa haka, Ki faɗa mana me kike gani a cikin mafarkin naki"! Uncle ɗan Iya ne yai maganar

 Cikin shessheƙar kuka tace"wallahi duk yadda zanyi maku bayani ba lallai ku fahimce ni ba, ni kaɗai nasan halin da nake aciki, ni kaɗai nasan bala'en da nake gani, Ba tun yanzu ba, tun ina ƙaramata idan nayi mafarki mummuna yana zama dagaske, hatta rasuwar iyayenmu saida nafara yin mafarkin zasu yi hatsarin mota, sai gashi ya tabbata, uncle ɗina ma ni nayi mafarkin mutuwarsa kuma ya tabbata, da wuya inyi mafarki mummuna bai zamto gaske ba, ni damuwata mutanan da nake a tare da su bana son wani abu ya sami wani daga cikin ku...." tashin hankalin da ba'a saka mashi date, A matuƙar ruɗe Zahra take kallon Aneeleerh, Ummi ta kalli Mamie, Idanuwansu azare, mahboob kuwa kusan suman zaune yayi.


  Shiru tayi Tana faman yin shessheƙar kuka,

 Abie dake kallonta, nazarin maganarta yakeyi, yaso ace musulmace ita, kodan ya bata shawarar ta runƙa yawaita yin azhkar, da sauran addu'o'in neman tsari.

  Tsawon lokaci falon yayi tsit, babu mai magana acikinsu, sai kallon kallo da suke jefawa junansu.

   Muryar Uncle ɗan Iya ce ta katse Shirun nasu

   "Ki daina sanya damuwa aranki, Mafarki ba gaskiya bane, shaidan ne yake assasashi, Ki yawaita yin addu'a, muma kuma zamu tayaki, Allah shi yake tsare bawansa, in sha Allah babu abun da zai same ki, damu kanmu,"

Ajiyar zuciya ta sauke, Cikin sanyin murya tace"in sha Allah uncle, zanyi hakan"

  "Aneelerh, Idan zata kwanta bacci ki rakata dakinta, Ki yi mata addu'a," Ya fada yana duban Aneeleerh, Cikin girmamawa Ta amsa mashi da toh,

     Kwantar mata da hankali suka cigaba dayi, Kowa sai da ya sanya bakin shi wurin Lallashinta da bata baki, Har saida suka tabbatar Ta samu saukin damuwarta tukunna mamie tace"daga yau kada ki sake ware kanki a daki! Kina jina ko"? Daga mata kai  tayi toh

 "Kidaina kuntata kanki adaki, ki dinga fitowa waje wurin su Aneelerh Kuna yin fira, hakan zai ɗebe maki kewa don na fahimci hada kaɗaici ke damun ki" jinjina kai ana tayi alamar toh.

  Gyaran murya abie yai tare da cewa"Idan kina buƙatar wani abu, Ki fadama Aneelerh ko zahra, su sanar dani in sha Allah zamuyi maki shi, kada kiji komai ki dauka tamkar Iyayenki ne" wannan maganar da abie Ya furta mata ba karamin ta6a zuciyarta yayi ba, nan take ta fashe masu da kuka mai tsuma zuciya, sautin muryarta dakyar yake fita wurin yi masu godiya.

  "Ku tashi ku rakata daki ta kwanta ta huta" Ummi ce tayi maganar tana nuna su zahra, ruƙo hannun Ana Aneeleerh tayi atare suka miƙe, Zahra tabi bayansu, Har cikin dakinta suka kaita, Bayan ta kwanta Aneelerh da zahra sukayi mata addu'o'i, Kafin daga bisani suka yi mata sallama, Kamar karsu barota haka suke ji, bayan sun fito daga dakin sun kulle mata kofar, zahra ta kalli Aneelerh

 "Nifa tsoro yakamani aunty na, tun da naji Ana tace mafarkinta yana zama gaskiya, wallahi bana so wani abu ya samu ɗaya daga cikin mu"

  Ita kanta Aneelerh hankalinta ba akwance yake ba, zuciyarta taki Aminta da kalaman ana, sai dai tayi kokarin danne damuwarta wurin kwantar ma zara da hankalin ta


 "Zahra kin riga kin sani, mafarki ba gaskiya bane, Ni ko kadan hankalina bai tashi ba, kema kuma inaso ki kwantar da hankalinki, In sha Allah babu abun zai faru, face alkhairi"


Cikin sanyin murya zahra tace"Allah Yasa" Ta fada a yayin da suke shiga falon, komawa sukayi saman carpet suka zauna kowa zuciyarsa da fargaban maganar Ana.


Idan muka koma 6angaren su Ummin america tun bayan kammala sallar magbrib, tayi wanka ta shirya cikin Baƙar jallabiya, tayi rolling veil akanta, ta bi ko'ina na jikinta ta feshe da turare, bakomai take jira ba face kiran Boss man, tun da ya fada mata yana son magana da ita gaba daya ta rasa sukuni ta kosa taji me ya ke son faɗa mata, tana cikin yin safa da marwa a room dinta, wayarta tayi ringing a hazarce tayi picking call din, muryar boss ce ta isar mata da sakon ta same shi a down, jiki na rawa ta fito daga dakin ta sauko down stairs babu kowa a falon, duk suna a dakunansu


A falo ta same shi tsaye cikin shiga ta jallabiya, ya goya hannayensa akan kirjinsa, fuskarsa a sanye da face mask.


  Da fara'a ta nufe shi batare da 6ata lokaci ba, suka jera a tare suka nufi swimming area din gidan, ko'ina ka kalla hasken fitilun lantarki ne tamkar da rana.


"ina sauraron ka Yalla6ai, tun da muka fito kayi shiru baka ce komai ba" ummi ce ta fada tana kallon Taj dake a gefenta.


 "ga dukkan alamu Kin ƙagara da kiji dalilin kiran da nayi maki"

 Jinjina mashi kai tayi alamar Eh, A yayin da suke zama saman kujerun dake a bakin pool din masu kyan gaske, suna fuskantar Junansu.


"Nasan zakiyi mamaki idan nace maki chief ne Ya bada Sako A fada maki" 

A ruɗe tayi mashi farfari da idanunta cikin kagara ta furta"A message from the chief for me? Does he know about me? So what did he say? 


  Calmly Boss Ya furta"Yeah Yasan da zaman ki fiye da tunaninki, chief da kike gani baya zama wuri ɗaya da mutumin da baisan tarihin rayuwarsa ba," Wani irin bugu kirjinta yayi mata cike da fargaba ta furta.


"I don't understand what you mean! Chief ya san komai dangane da rayuwana! How is that possible?"


  Dariya boss yayi ganin yadda ta shiga ruɗani

  "Ki kwantar da hankalin ki Ummi, Amsarki tana atare dani, ki natsu ki saurari me zan fada maki" fuskarta a yamutse ta amsa mashi da toh.

  Numfasawa yayi kafin Yaci gaba da fadin"sakon da chief Yace A fada maki shi ne, Gobe Idan Allah ya kaimu, zamu fita tare da Yaran nan zuwa cikin estate din su, muna so su halarci Farewell dinner din Uncle ɗinsa Hateem, amma fa bama so kowa yasan da wannan zancen! Zuwan bazata zamuyi tare da su, ke kuma abun da muke so daga gare ki, ki yi kokarin shirya mana su.... " kafin Ya kare Maganar tace"wai kana nufin prime minister Hateem na canada ne za'ayiwa dinner din? ɗaga mata gira yai alamar eh, but amma meyasa naji kace zuwan bazata za'ayi da yaran"? Ta faɗa tana mai neman ƙarin bayani.

   Bai 6oye mata komai ba, dangane da budurin da aka sha lokacin da Danish ya rikiɗa, naƙin amincewa da zaman su a family din"

  Jikinta yai sanyi"Allah sarki, ashe abun da ya faru kenan, ko da yake dama zaiyi wuya su yarda da su, ni kaina lokacin daya rikiɗa ba ƙaramin firgita nayi ba, saboda abu ne da ban ta6a gani ba, toh su kansu abun da zai sa su ƙi yarda da zamansu kenan, bayan haka hukuncin da shi baba obie ya yanke na raba alaƙar prime minister hateem da danish yayi dai dai, a fahimta na yayi hakan saboda gudun kada ɗansa ya cutu.... " jinjina kai taj yai alamar gamsuwa da bayanin ta, kafin wani ya qara magana a cikin su, sai ga jami'in isod Ya fito daga ƙofar falo, hannun shi ruƙe da plate mai ɗauke da mugs biyu na coffee, akan table din dake a tsakatsakiyarsu ya ajiye plate din kafin yabar wurin

  Tura mata mug ɗaya taj yayi"kisha, ni nasa a kawo mana dan muji dadin tattaunawa' murmushi tayi har cikin ranta taji dadin karamcinsa, A hankali ta ɗauki mug din ta soma kur6ar coffee din, shima ya dauki nasa yana sha, bayan ta tsagaita da sha ne taci gaba da magana "kowani bawa da irin tashi jarabtar, Idan kaji na wani kai naka ba komai ba, shiyasa a koda yaushe akeson bawa ya zamanto mai hakuri dakai zuciya nesa, haƙiƙa ina tausayin wadannan bayin Allah, duk da ban kaiga jin tarihin rayuwarsu ba... ' murmushi taj ya ɗanyi tare da cewa"kada ki damu, nan badajimawa ba zaki ji tarihin rayuwarsu, In sha Allah"


Gyaɗa kai tayi "A ina za'ayi dinner din sannan ƙarfe nawa ne zasu je can din"?

  

 "A cikin Estate din nan, Bayan sallar la'asar"


  Shiru tayi alamar tana nazarin wani abu, yayin da yake binta da kallo.


 "Menene dress code din da za'a sanya a wurin dinner din"? ta tambaya tana kallon fuskarsa.


"abaya matan za su sanya, A cikin suturunsu mun sanya masu abaya na larabawa kala kala, A ciki za'a daukar masu masu kyau na mutunci, sannan bama son suyi shigar da zata baiyana sumar kansu, a rufe masu ko'ina na jikin su.


Gyaɗa kai tayi"okey, in sha Allah amma baza'ay masu make up ba"?

 

"Duk kyan da Allah yayi masu"? Ya faɗa da murmushi kan fuskanshi, Itama ummin murmushin takeyi"masu kyaun ma su na yin make up, ko da yake naji ka ce arufe masu ko'ina na jikin su, ba buƙatar yin make up, ɗaga mata gira yai alamar eh.


   "Tare da ni zaku tafi ne"?

"Idan kina ra'ayin zuwa"

 Girgiza kai tayi alamar a'a

 "Meyasa"? 

"Nafi so kubarni a gida, nasan Su Unaisah zasu bani labari, har ma su daukar min video na dinner din in gani nima"


 "Ban yarda ba, yakamata kema ki shirya mu tafi tare dake, zaki ji dadin shiga cikin family ɗin Obinna," jim ta ɗanyi tana wani tunani aranta.


  "Kinyi shiru baki ce komai ba" 

Numfasawa tayi tare da cewa"ka yi hakuri amma zuwana ba lallai ya zama alkhairi agare ni da ku kan ku ba, bana so na 6ata maku shagalin ku, nasan ka fahimce ni"  jim ya ɗanyi yana jujjuya mug din hannunsa, tabbas ya fahimci me take nufi,shi kanshi yasan ba lallai chief Ya amince su tafi da ita ba, yadai ɗan bugi cikinta ne don yaji idan tana son zuwa sai kuma akaci sa'a bata ra'ayi.


  "Alfarmar da nake nema a wurin ku, dan Allah ku barni in fita gobe, Inaso zan ziyarci gidan ƙawata dake aure anan abuja"


  "Bani da wannan hurumin, Amma in sha Allah zanyi kokarin nema maki alfarma wurin chief, but inaso kisan da sani duk inda zaki je jami'in mu ne zai kai ki," har cikin ranta taji dadin maganarsa.


"Idan akwai abun da kike buƙata ki faɗa min" cikin kulawa yayi mata maganar yana dubanta.


  "Dan Allah ka fadamin shin dagaske ne chief Yasan komai dangane da rayuwana"? Ta fada cike da fargaba.


 Jim ya ɗanyi yana dubanta kafin Yace" "I'll give you an assignment. If you can find the answer, then I'll tell you what you want to hear," A ƙagare ta ke kallon shi, A hankali Ya sanya yatsun hannayen shi tare da zame mask din fuskarshi.


 Wani irin kallo ummi ta soma binshi da shi, Yau ne karo na farko da ta fara Yin tozali da fuskar Boss man, bata ta6a tsammanin Yana da kyawun fuska har haka ba.


 "Dama haka kake da kyau"? da alamun mamaki ta furta maganar, Murmushin gefen fuska Ya sakar mata har dimple dinsa ya lotsa, nan take ta soma kokarin tariyo inda tasan fuskarshi sai dai kash takasa tunawa amma tabbas tana ji aranta ta ta6a sanin shi ko kuma wani ne me kama da shi.


 "Ina da aure, Ki daina kallona, matana tana da kishi, zata iya yin komai akaina" da zolaya taj yayi maganar.

 Ummi tace"tasan tana da kishi meyasa ta auri namiji mai kyan sura? Ay kamata yayi ta auri mummuna, ni fa bazan 6oye maka ba, ka jima kana bani mamaki kai da abokin aikin ka big guy da chief din ku, tun da nataso rayuwata da wuya a samu namijin zan gifta awuri batare daya bi ni da kallo ba harma ya neme ni, amma ku sam babu wannan tunanin aranku, zuciyarki a tsarkake take, hakan ba karamin daure min kai yake yi ba, shi chief mace ko kallo ma bata ishe shi ba, wata irin dakakkar zuciya ce da shi.


  Ƙayataccen Murmushi Taj Ya sakar mata batare daya furta mata ƙala ba


 "Wallahi nasan ka, sai dai bazan Iya tuna a ina nasan ka ba, ni hatta muryarka na jima ina son tuna ina na son ta," still face dinsa da murmushi Yake dubanta.


 "Amma meyasa kake yi min kama da Unaisah? Ko dai idanuwana ne suke nuna min badai dai ba"?


    "Ba laifin idanuwanki bane, Unaisah Ƴata ce, Jini na ce, Ni mahaifinta ne, asalin sunana Tajuddeeen,"


  "I can't believe it, Unaisa fara ce zan iya sanyata a jinsin larabawa, kai kuma daga ganin ka hausa fulani ne"

 "A salin sunana Zaheer Tajudeen, Zaheer sunan Mahaifina ne, Tajudden kuma sunana ne, Ki tambayi Unaisah menene full name dinta zata fada maki da bakinta, Ita kanta ayanzu haka batasan cewa Ni mahaifinta bane ƙaddara ce ta rabamu, sai gashi cikin ikon Allah mun sake haɗuwa," murmushi ummi tayi"Allah sarki, Na tayaka Murna, amma mahaifiyarta wani jinsi ce"? 

 "Hausa Arab ce" Dariya Ummi tayi cikin raha ta furta"hausa arab! Bayan hausa fulani har Hausa rab ke da akwai, ban ta6a ji ba sai akanka"

 "Ina nufin Half cast ce, Mahaifinta hausa fulani ne, mahaifiyarta kuma Balarabi ce" gyaɗa kai tayi"masha Allah, shiyasa yarinyar taka takasance fara sol, Ga gashi tubarkalla amma tsakanin kai da mahaifiyarta halin wa ta ɗauko"? murmushi yasaki yana dubanta yace"meyasa kika tambaye ni"?

"Unaisah tana da faɗa, daga ka kalli idanunta zaka shaidan hakan, ga wayau da kaifin basiri Allah Ya bata fiye da sauran ƴan uwanta" haƙiƙa Yaji daɗin Yabon da ummi tayi mata,

  "Haka mutane suke cewa, shiyasa nima nake alfahari da ita, Inason Unaisah, fiye da yadda nakeson kaina, A halin Yanzu bani da tamkarta a duniyarnan, Itace ta rage min wadda nake gani naji sanyi araina, silar unaisah nasamu alheri da dama wadanda idan na fada maki su zakiyi mamaki, ɗaya daga ciki Unaisah itace silar haɗuwana da Chief" da mamaki Ummi ta ɗan zaro mashi sexy idanunta haɗi da buɗe baki, Jinjina mata kai yayi" Murmushin gefen fuska tasaki"Ina ƙara tayaka murna, Yarinyarka Jarinka ce, Allah Ya albarkaci Rayuwarta" amsa mata yayi ameen, daga ita har shi sun ji daɗin zaman firar da su kayi, Haƙiƙa taj ya ɗebe mata kewar kaɗaicin dake damunta, ta ƙara ganin mutuncinsa da ƙimarsa a idanunta, Sai dai tarasa gane meyasa take jin kamar ta ta6a sanin shi? Musamman daya faɗa mata sunan shi sai yawo yake mata akai.


Ni'imtacciyar Iskar dake kaɗawa ta ƙara masu ƙaimin firar ta su, kafin wani lokaci taj yace da ita"kada na cika ki da surutu, ko zaki koma ciki ne"? Fuskarta da fara'a tace"no ko kusa, ni baka takuramin ba, saima ɗebe min kewar da ka yi, naji dadi fiye da tunanin...... " bata ƙarasa maganarba sakamakon sautin dirar motar daya ratsa kunnuwanta, kusan atare suka juyo suna duban motar.


Bayan sojan dake driving din motar yayi parking, Ya fito Ya zagaya ya buɗe mashi murfin back seat dinta, Ƙafarshi kaɗai ya zuro waje Gaban ummi ya faɗi rasss, jikinta ya soma kakarwa, A hankali ya ƙarasa fitowa daga cikin motar, kamar kullum cikin shiga ta malamai magadan annabawa, bai ɗaura idanunsa akan kowa ba sai akan Ummin america, a sukwane ta miƙe tana gyara mayafin da tayi rolling, taj kuwa fuskarshi dauke da murmushi ya nufi sheikh imam yana fadin"Ya sheikh Barka da zuwa tun ɗazu muke ta sa ran ganin ka" Martanin murmushin Shiekh Imam ya mayar masa a yayin da yake kokarin kau da idanunsa daga na ummi ya mayar da su akan fuskar taj, musabaha su ka yi  shikeh imam yace"Ay min afwa, ban samu damar zuwa duba mara lafiya na ba, wallahi yana araina da shi na wuni, wani uziri ne ya ruƙe ni"

  Jiki na rawa Ummi ta juya ta nufi ƙofar shiga falo, Duk don kada su gaisa da sheikh imam, har ta kusa kaiwa ga ƙofar muryar taj ya ratsa kunnanta

   "Ummi, ki zo mana ku gaisa da sheikh imam" tamkar an dasa mata aya ta tsaya cak, tana mai mayar da numfashi, Har cikin ranta bata ji daɗin dakatar da itan da yayi ba, sai dai bata jin zata iya watsa mashi ƙasa a ido, musamman yau daya faranta mata rai.

   Tunkafin ta juya ta soma jin takun tafiyarsu bayanta, jiki asanyaye ta waiwayo tana dubansu, lokacin da suka ƙaraso da sauri ta sunnar da kanta ƙasa, muryarta na rawa ta furta"sannu da zuwa" 

 Cikin sanyin murya ya amsa mata da yawwa

Taj dake dubansu a fakaice yace"sheikh bari na gabatar maka da ummi,"jinjina mashi kai yai alamar toh

  "Ummi Tamkar uwa take a wurin yaran da muke raino, ita ce take kula da su"

Fuskar sheikh babu annuri ya furta"anya kuwa sunyi dacen uwa"? Har sai da gaban ummi ya fadi rass jin abun da yace, hatta shi kanshi taj aruɗe ya kalli fuskar shaikh imam



*Daga alkalamin Boss Bature💋✊✍️*



 *Littafin kurkukun ƙaddara 500 ne, dukanshi Book One two and 3 Idan kin shirya biya ga Details da zaki tura*


3196407426


First bank 


Bature Hafsat Muhammad,


 *bayan kin tura zaki bada transaction reciept ko screenshot na debit alert a matsayin shaida ta wannan layin 08169856268, Ƴan Niger kuma su yi min magana ta layina 08103884440*

Post a Comment

Idan kuna da tambaya akan abinda Baku game ba ko kuma kuma Neman littafin da babu a nan kawai ku ajiye tambayarku a ta comment ko wani shawara da Zaku bamu.

Previous Post Next Post

Sponsored Link

Sponsored Post