Kwararre a bangaren hadahadar kudi na Kiripto yayi bayani akan asalin abin da zai Faru a ranar 30 ga watan Mayu Wanda hakan ya karyawa wasu mutane gwiwa.
Masani akan Kiripto, Omobare Daniel ya sanya mutane cikin wani yanayi akan bayanansa kan abin da zai Faru a ranar 30 ga watan Mayu inda ya ce ba shine Ranar da zata gashe ba.
A wani Bayani daya wallafa a shfinsa na Facebook, Daniel ya ce masu Minning zasu samu taping dinsu da kuma iya sharing ne ba wai samun tokens dinku ba hasalima ranar 30 ga watan Mayu Rana ce da za a kaddamar da shi wato Launch Pool.
yayin da ya ci gaba da cewa masu Minning za su iya Canza Taping din su ne kawai bayan an kaddamar da shi, inda Daniel ya ci gaba da cewa Babu wata sanarwa Data shafi fashewar sa a ranar 30 ga watan Mayu.
Related Story: Rashin yin linking Tapswap dinku da Wallet zai iya jawo muku asarar mining din da kukayi
Wani lokaci ne mutun zaj iya cire kudinshi daga Tapswap? Daniel ya bayyana cewa mutun zai iya anfana da Tapswap ne idan aka yi listing dinshi, kuma ya bukaci mutane su shirya domin kaucewa samun rashin Jin dadi inda ya yi bayani akan banbancin tsakanin Fashewar da kuma kaddamarwa wato Listing da launch pool.
Akwai Banbancin tsakanin kaddamar wa da Fashewar, Misali kamar NOTCOIN an kaddamar da shi ne a ranar 1 ga watan Janairun wanna shekarar kuma akayi Listing dinshi wato ta fashe a ranar 16 ga watan Mayun 2024 Wanda aka samu Tazarar watanni Hudu tsakanin kaddamar wa da kuma Fashewarta, A don haka ya kamata ku game Banbancin da Fatan Kun gane saboda haka kada ku dauka za a Yaudareku ne ko kuma a saba muku alkawari idan kukaga An samu Tsaiko.
Shima Wani kwararre a bangaren hadahadar Kiripto, yayi bayani akan kaddamar da Tapswap wato Launch Pool da kuma abin da zai Faru a ranar 30 ga watan Mayu, kwararren Obani Ebenezer Nwokoma ya ce kaddamar wa za a yi .
Batu ne na ranar Lunching ba kuma zan sa Rai cewa ranar da zata gashe bane.