RASHIN ZUWAN AL'ADA (AMENORRHEA)


Health College

RASHIN ZUWAN AL'ADA (AMENORRHEA)

Menstrual Health

Idan al’ada tana dadewa bata zo ba sai bayan watanni 3 zuwa 6, wannan shi likitoci suke kira “amenorrhea”. A gaskiya wannan yanayin bai kamata ace mace tana fama dashi ba. Idan kuma ya auku, to, yana nufin cewa mace tana da matsala kenan.


Amenorrhea ya kasu gida biyu kamar haka:

1. Primary amenorrhea: Wannan yana nufin dadewa na farko ko kuma dadewa na asali wanda al’ada takeyi bata zo ma mace ba. Abinda yasa ake kiransa dadewa na farko ko na asali shine yana faruwa ne ga mace budurwa wacce bata taba yin al’ada ba a rayuwarta, sai ya kasance ta kai munzalin da ya kamata ace ta fara al’adar, to, amma sai bata zo mata ba. Mafi yawanci budurwa tana fara al’ada ne tsakanin shekaru 9 zuwa 13. Don haka idan budurwa ta kai shekaru 16 zuwa 18 bata fara al’ada ba, to, wannan shine primary amenorrhea.


2. Secondary amenorrhea: Shi kuma wannan yana nufin dadewar da al’ada take yi bata zo ba har na tsawon watanni 3 zuwa 6 ga babbar mace, watau ba budurwa ba. 

Dukkan su primary amenorrhea da secondary amenorrhea suma faruwa ne saboda dalilai masu yawa, wadanda suka hada da:

1. Yanayin da Allah ya halicci tsarin jiki akansu kamar daukar ciki, shayarwa, nisan shekaru (menopause) da sauransu. Idan mace tana cikin daya daga cikin wadannan yanayin, to, zata fuskanci daukewar al'ada 

2. Shayeshayen magunguna kamar na family planning ko kuma domin warkar da wata cuta da take damun mace

3. Lahani wanda ya sami tsarin jikin mace na haihuwa (reproductive system defects) kamar jakar da take dauke da kwaya-kwayan haihuwa (ovary) ko mahaifa (uterus) idan suka sami matsala

4. Rashin daidaiton zubar sinadarai a cikin jiki (hormonal imbalance)

5. Yin ayyuka na wahala

6. Damuwa (stress)

7. Kasancewar mace ta zamo mai tsananin kiba ko tsananin sirantaka


Hanyar kadai da za’a iya magance amenorrhea it ace idan aka tuntubi likita yayi bincike mai zurfi domin gano wasu daga cikin dalilan da suke haifar da shi, daga nan sai a bayar da maganin da ya dace.

    SHAWARA GA MATA MASU DAUKEWAR JININ!!

Akwai abubuwa kamar haka da kan taimaka wajan samun fitowar jinin ga wadanda ya dauke musu alhalin kuma ba juna biyu ne dasu ba kuma ba akan tsarin family planning suke ba Ko medical problem;

1. Tabs- Vitamin C II tds x 10/7.

Saboda shan vitamin c yana matukar habbaka sinadarin estrogen ajika Wanda hakan ka iya sa fitowar jinin.

2. Idan ta fahimci lokacin yin period din yayi kuma harta fara jin alamun data saba amma jinin yaki fitowa ko kuwa digo ne dis yake fita ba sosai ba to saita:-

Sai Ki samu garin citta (Ginger powder) ko normal cittar sai ki kwankwatsata Kike danka kina tafasawa kamar tea kike sha ko ki zubawa a cikin tea din mai Dan zafi sosai kina sha musamman da sassafe kafin kici komi.

3. Shan lemon bawo, kankana da gwanda na taimakawa, lemon bawon ki cinye har soson.

4. Sai kuma ana bukatar kisami ruwan dumi mai zafin da bazai de konaki ba, ki zuba a kwalba ko robar lemo kota ruwa ki daure bakin ki kwanta Kike gogata kina garata a mararki xuwa gefe-gefen cikinki ma'ana kamar kina gashin wajan hakan zai taimaka ya yunkuroshi insha Allah.

5. Sai kuma hormonal therapy da akan bayar a asibiti in anje daidai da yanayin ki da zasu taimaka ya  in abun yaci tira.

       WalLahu A’lam.

Dr. Reslan Health Talk

Post a Comment

Idan kuna da tambaya akan abinda Baku game ba ko kuma kuma Neman littafin da babu a nan kawai ku ajiye tambayarku a ta comment ko wani shawara da Zaku bamu.

Previous Post Next Post

Sponsored Link

Sponsored Post