An yi kira ga gwamnatin tarayya da kuma jihar Katsina da su sa baki kan bacewar mataimakin shugaban kungiyar Miyetti Allah Cattle Breeders Association of Nigeria (MACBAN), Injiniya Mannir Atiku Lamido.
A wata sanarwa da iyalan Injiniya Lamido suka fitar mai dauke da sa hannun dansa Malam Abdullahi Balarabe, iyalansa sun nuna damuwarsu kan bacewarsa.
Sanarwar wacce ta bayyana cewa Injiniya Mannir ya bata ranar 23 ga Yuni, shekarar 2023 a kan hanyarsa na zuwa jihar Kaduna daga Katsina, an bayyana shi a matsayin mutum mai kima da kishin kasa.
Duba da rashin samun cigaba mai ma’ana a binciken ko da an gano motarsa da wayoyinsa da sauran kayansa, kwanaki 351 bayan bacewarsa, ya zama dole a yi kira ga gwamnati dakuma kungiyar Miyetti Allah ta Najeriya. MACBAN), don gaggauta daukar mataki kan lamarin.
Sanarwar ta bukaci gwamnatin tarayya da na jihar Katsina da jami’an tsaro su gaggauta daukar matakin magance wannan rikici domin ganin ya dawo lafiya da kuma kare afkuwar irin wannan lamarin.