Kurkukun Kaddara Takun Karshe Page 17 Complete

Kurkukun Kaddara Takun Karshe Page 17 Complete

Novels Elite English

 _ *~✊💋BOSSLADIESWRITERS💋✊~*_




                     سجن القد💋🔥💞    



                  ~Takun Ƙarshe🔥~




            Dedicated to Aunty Kubra💋💞




قصة حب رومانسية غير عادية بين السجناء مع   تطورات معقدة💋💘😘



An extraordinary romantic love story between prisoners with complex twists ❤💋💘




Daga alƙalamin Boss Bature💋✊






__________________________✍️





Shessheƙar kukan su ta cika ɗakin, babu mai lallashin wani a cikin su, tsananin tausayin taj ne ya kamasu jin irin kalubalen da ya fuskanta, A hankali unaisah ta ɗaura tafukan hannayenta dake kerma kan fuskarshi ta share mashi hawayen shi, cikin sanyin murya tace"daddy, ka yi haƙuri, ka daina zubar da hawayenka, bana son ganin su, kallonta yai da rinannun idanunsa muryarsa na ɗan rawa yace"My Angel, ni nawa ƙaluban dana fuskanta bakomai bane akan naku! Ku ne kuka ga rayuwa, ku yakamata a jajanta mawa, a kuma tausayama rayuwarku....." gaba ɗaya hankulansu Sajeed na akanshi, da ruɗani unaisah tace"daddy, kasan abun da ya faru dani bayan na gudu daga rugar su danejo"?

Lumshe idanunsa yai hawaye na sintiri ya ɗan jinjina kanshi kafin ya motsa la66ansa"na san abun da ya faru dangane da rayuwar kullan da ku ka yi a GIDAN KURKUKUN ƘADDARA, da kuma irin baƙar izayar da suke yi maku, ranar da mu ka fara ji daga ni har chief duk irin juriyarmu sai da muka zubar da hawayen mu saboda abun ya ɗaga hankulanmu, ya razanar da mu, bazan iya misalta maku halin da muka shiga a lokacin da muka ji labarin abun da ake aikatawa a GIDAN KURKUKUN ƘADDARA.


Kallon kallo Su Naufal suka soma jifar junansu da shi idanuwan kowannansu sunyi jawur da su, saboda kukan da suka sha, bakomaine yasa su kallon juna ba face mamakin yadda akai daddyn Angel Yasan abun da ake aikatawa agidan kurkukun ƙaddara,  Unaisah ce kadai batai mamaki ba saboda tasan dama sun sani watakil abakin salsabeel suka ji komai.


Murya na rawa Batool Tace"daddy dama kunsani? Meyasa baku kawo mana dauki ba? Kunsan kuwa irin ƙuntatar rayuwar kullan da mukayi a gidan kurkukun ƙaddara? Ta fada hawaye masu ɗumi suna sintiri akan kuncin ta, muryarsa a raunace ya furta"mu kan mu ba mu jima da sani ba, da ace tuntuni mun san da zaman ku da har rayukanmu zamu iya sadaukarwa don mu ceto rayuwarku" 


Ummin dake kallon batool jikin ta har tsuma yakeyi saboda tsabar ƙagara da son jin tarihin rayuwarsu babban burinta taji menene ma'anar gidan kurkukun ƙaddara da taji sunata ambato a bakunansu.


Jan numfashi batool tayi kafin ta ɗaura da cewa"mun rayu tun kafin mu mallaki hankulanmu, bamu ta6a ganin hasken rana ba, babu shige babu fuce, a ɗaki ɗaya muke a kulle, kullum cikin uniform ɗaya, abinci sau ɗaya arana, bamusan dadin rayuwar duniyar nan ba, duk wani hakkinmu na rayuwa  an tauye mana shi, mu bamu san dadin iyaye ba, sannan babu mai jin kukanmu, balle a kawo mana dauki, anjuye mana tunaninmu balle musan cewa muma mutane ne masu ƴan ci kamar kowa.... ..." bata ƙarasa maganarba saboda kukan daya tokare makoshinta, tamkar zatayi kakarin amai.


Cikin karyayyar murya Unaisah tace"tsohuwa tamira ta ta6a fada min cewa na jininmu ne kadai zai Iya sadaukar damu, har yau nagaza yarda da maganar nan, Ina kokwanton tayaya za'ay iyayen da su ka yi silar zuwanka duniya ko wani naka ya sadaukar dakai inda za'a azabtar da rayuwarka? Daddy wanene ya sadaukar dani❓


A matuƙar ruɗe ta jefa mashi tambayar tana kallon shi.


Cikin sanyin murya yace"unaisah ni kaina a rude nake, bansan wa zan zarga ba Allah shine yasan wanene mugun da yayi maki wannan aika aikar"

 Muryar ummi araunace tace"dan Allah ku fahintar dani, tun ɗazu inata magana kunki bani amsa! Inaso naji meya faru da ku? Sannan Ina ne GIDAN KURKUKUN ƘADDARA"!?


Daƙyar Unaisah ta lallashi zuciyarta dake yi mata radadi, kafin ta ɗaura idanunta akan fuskar ummi"zan fada maki komai da kikeson ji aunty ummi" A hankali ummi ke kallon fuskar unaisah 


Lokacin da tafara bata labarin rayuwarsu wata irin zuface ta soma wanke fuskar ummi, jikinta ya hau yin kakarwa saboda razanar da tayi, ko a mafarki bata ta6a jin labari mai matuƙar firgitarwa irin wannan ba tuni hawaye sun soma yar tseral kan kuncinta.   


Abunda yafi tsaya mata arai cikin labarin da Unaisah ta bata shine mutuwar Unaizah yar gidan daddy, ba ita ba harta taj Jikin shi Ya gama mutuwa saboda bakomai suka sani ba dangane da rayuwarsu saida unaisah tafara basu labari, chief dake atsaye bakin door yana sauraron su kasa jurewa yayi, wani irin jiri jiri Yake gani acikin idanunsa, zuciyarsa har wani tafarfasa take yi tamkar zata kone kanta tsabar 6acin rai da fusata, jijiyoyin wuyansa tuni sun fito rudu rudu kan goshinsa, juyawa yai da sauri Yabar kofar dakin, A hanzarce big guy yabi bayansa gudun kada zuciya ta debe shi Ya je yai ma kanshi Illa.

  

Zuciyar ummi dake hauhawa tana harbawa da wani irin mahaukacin bugu na tashin hankali tama rasa ina zata jefa kanta taji dadi gaba ɗaya taji ta tsani rayuwar duniya, Hakika Labarin su Unaiza Ya karya mata zuciya, ya ƙara mata karfin imani sai yanzu ta gane babban kuskuran da tayi nagaza daukar ƙaddarar rayuwarta, cikin shesshekar kuka mai haɗe da gunjin kuka ta furta


"Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un!! Wannan wata irin musibace? Ku fadamin Tayaya akai har kuka Iya jure wannan ukubar da ƙananun shekarun ku batare da zuciyoyinku sun buga ba? La66anta na kerma ta fada tana dubansu kafin taci gaba da cewa "Zuciyata tagaza yarda da abun da kunnuwana suke jiye min! hankalina Ya tashi! Zuciyata ta karaya! Wannan wani irin zaluncine? Su wanene wadannan Fasikan mutanan mugaye azzulamai marasa imani da tausayi, wadanda basu ɗauki ran dan adam abakin komai ba, wai su wanene su dan uban su? Wasu irin dabbobine su jahilai, Masu matattar zuciya, Anya kuwa suna da zuciya a kirjinsu? Anya kuwa mutanene su kamar kowa? Ina kokwanto akansu..." gaba daya ummi ta burkice masu sambatu kawai takeyi kamar sabon kamu ahauka, da alama abun ya razana kwakwalwarta.


Rashin imanin da akai ma yaran ya ɗaga hankalin ta, fashewa ta kuma yi da kuka kafin taci gaba da fadin"sun manta cewa zasu mutu su koma ga Allah? Wai su basa tunanin makomar su ne? Duniya kaɗai suka sa agaba, ko Sun manta cewa duk wani abu da suka mallaka aduniyar nan zasu barshi? Daga su sai halin su za'a binne su!?...."


ɗaya bayan ɗaya take kallon su jemimah dake ta kuka aranta ta ayyana yanzu gaba dayansu nan an lalata rayuwarsu har da yan ƙananan cikin su wani irin yunkurin amai ne yazo mata da gudun gaske ta mike ta fuce daga dakin, Har batool ta yunkura zata bita taj yai saurin ruƙe hannunta,

"ku barta tayi kuka ta hakanne zata samu saukin abunda take ji aranta" jiki asanyaye batool ta zauna.

Shi kanshi bazai Iya misalta irin kunar da zuciyarshi take yi mashi ba

Cikin muryar lallashi Yace da su"Idan na ce kuyi hakuri kamar na cuce ku ne, saidai ba yadda zakuyi hakurin nan dai shine yakamace ku, Allah Baya barin hakkin wani akan wani, wadanda suka azabtar da rayuwarku In sha Allah za su ga mummunar sakayyar da Allah zai masu tun agidan duniya zasu fara ɗanɗana kudarsu kafin su koma ga mahaliccinsu su fuskanci makomarsu......." daƙyar Ya samu ya shawo kansu, kafin ya bi su daya bayan daya yayi huggin dinsu duk don ya kwantar masu da hankalin su, sai da ya tabbatar ya share masu hawayensu tukunna yace


"Dan Allah kada ku sanya damuwa aranku, ku kwantar da hankulanku in sha Allah komai yakusa zuwa karshe, yanzu ku koma dakunanku ku yi wanka ku kwanta ku huta, nasan baza a rasa masu fama da ciwon kai a cikin ku ba, zanyi magana akawo maku breakfast har bedroom dinku"


muryoyin su adisashe suka amsa mashi da toh, 


kafin suka mike kamar wadanda aka zarewa laka haka suka nufi kofar dakin suka fuce.


Bayan fitarsu Ya rage daga Unaisah sai batool sai kuma Taj,

Mikewa batool tayi jikinta tamkar na wadda tayi zazza6i ganin ta nufi kofar dakinne Yasa taj yi mata magana"Ina zaki je ne"?


"Ɗakin Aunty Ummi" amsa mata yai da okey, bayan ta fuce ya maida dubanshi ga unaisah, janyota yai tare da kwantar mata da kanta kan kirjinsa hannunsa akan kafadarta

"Ina fata yanzu babu abunda ke maki ciwo"? muryarta kasa kasa tace"eh daddy,"

Da yar zolaya yace mata"ya rashin ji ko da yake naga kin daina Yanzu"? ƙara shige mashi tayi tana yar dariya, bubbuga bayanta yai da hannunshi, kafin ya janyeta, ya mike kan gwiwowinsa ya fuskanci alkibla yakai goshinsa kasa yai sujjada murmushi tasaki tana kallon shi, da sauri itama tayi sujjadar kamar yadda yayi, tsawon mintuna kafin suka dago da kansu fuskar kowan nan su dauke da annurin farin ciki

"Daddy fada min me ka ce acikin sujjadarka"

Numfasawa yai kafin yace"nayima Allah godiyane da ya bayyanar min da ke da ranki da lafiyarki" 


"Nima haka" murmushi suka kuma saki gaba dayansu,


"Daddy Inaso na tambayeka, tayaya akai ku ka hadu da su salsabeel? Ko ya fada maku yadda akai suma suka ku6uta daga kurkukun ƙaddara"?

Shiru ya ɗanyi kafin yace"ki bari idan yazo sai ki ji daga bakin shi, yanzu nafiso ki kara samun kwanciyar hankali" amsa mashi tayi da toh


"ki tashi mu shiga toilet ki wanke fuskarki kizo mu ci abinci"


Ya fada tare da ruko hannunta suka shiga toilet, bayan sun wanke fuskokin su suka fito atare

A gefen gado suka zauna Ya bude masu abincin tray din da suka ajiye kan table

Cikin kulawa yake bata abinci abaki tana ci, tsabar dadi kamar ta zuba ruwa a kasa tasha, wai yau gata ga daddynta


"Daddy, Ina aunty Aneelerh da babynta"?

Murmushi Yasaki kafin Yace"suna nan cikin koshin lafiya, kwanakin baya nabibiyi layin wayarta amma ba'a ɗaga ba sai wata rana dana ci sa'a aka daga wayar kinsan wanene ya daga" girgiza mashi kai tay alamar a'a yana murmushi yace"ƙaninki baby junaid," waro idanu waje tayi da tsantsar farin ciki tace"daddy sunan shi junaid" daga mata kai yai alamar eh


"baki ga yaron ba kyakkyawa dashi, ga wayau sai ma in yana surutu.." cike da zumudi tace"daddy inason ganin shi tare da aunty aneelerh, dan Allah ka kaini wurin su nayi missing dinta"


"Zan kaiki in sha Allah, amma ba yanzu ba, ki ɗan ƙara hakuri" tur6une mashi fuska tayi, bakinta cunkushe da abincin daya tura mata, yar dariya yai tunawa da kuruciyarta.


"Banji kin tambayeni danejo ba"!

Sakin fuskarta tay, "tana araina daddy, bazan ta6a mantawa da halaccinta agareni ba, ni dai ba abun da zance sai dai inyiwa Allah godiya saboda Ya hadani da mutanan kirki masu sona tsakani da Allah' ta fada fukarta da ɗan murmushi,


"Yaushe zaka kaini Wurinta in ganta"?


"Ko zuwa anjima idan kika kara jin sauki sai muje ko"? Daga mashi kai tay alamar eh.


Shiru suka dan yi kafin ta kuma cewa"daddy mommy adama fa? da uncle abdallah!! Suna nan suma"?

Daga mata kai yai alamar eh, 

"Alhamdulillah Ya Allah" ta furta da matsanancin farin ciki, ashe da rabon in sake ganin yan uwana.


"Ina granny ɗina da sauran mutanan buzaye"


Jiki asanyaye ya ajiye cokalin dake a hannun shi, nan take ta fahimci babu lafiya, muryarta adan rude tace"daddy menene"?


Cikin sanyin murya yace"unaisah sun riga mu gidan gaskiya, mahaifina da mahaifiyata, da kuma kakata kusan duk a lokaci ɗaya suka rasa rayukansu nima sai daga baya naji labari..."


Cikin sanyin murya tace"ubangiji Allah Yajikansu ya gafarta masu, Allah ya jaddada rahama agare su..." amsa mata yayi da ameen

Shiru suka danyi na wani lokaci batare da ya cigaba da bata abincin ba

So take ta tambaye shi dangane da  mahaifiyarta sai dai takasa saboda zuciyarta taki bata hadin kai, Har yanzu bata daina jin ɗacin radadin abun da tayi mata ba, ta tsani mahaifiyarta fiye da komai na duniyar nan, tana son ta haɗu da ita ba don komai ba sai don taji dalilin dayasa ta yi watsi da ita, idan ba ta son ta meyasa ta haife ta❓



*HAJJATY 💋*


A zaune take gaban dressing mirror, fuskarta dauke da murmushi bakomai take tunawa ba face fuskar Naufal, ta kasa mantawa da shi, Yaron ya kwanta mata aranta, daren jiya data kwanta bacci har mafarkinsa tayi, 

da alama bata jima da fitowa daga wanka ba, duba da towel din dake daure a chest dinta

Tun dazu takasa tabuka komai gaba daya ta shagala da tunanin naufal, ta ƙosa pravin ya shigo donta nuna mashi hoton naufal tasan zaiyi mamakin ganin me kama da ita.


Wayar ta dake ajiye kan mirror din ta dauka ta budo hoton shi tana kallo har zooming din fuskarsa take yi

Jin motsin shigowar mutun yasa tayi saurin juyawa don ganin wanene

Pravin ne ya shigo sanye da farar jallabiya, fuskarshi babu annuri ko miskala zarratin kamar wanda aka fada ma sakon mutuwarsa

 Sam bata lura da yanayin shi ba, cike da zumudi ta mike ta nufe shi tana fadin"honey, ina ka shiga tun jiya bansaka a idanuna ba"? Fadawa tayi kan kirkinsa tai huggin nasa kafin ta ɗago da fara'arta tace"ka yi shiru baka ce min komai ba"? Wani kallo ya soma jefa mata mai kama da harara, da alama ta manta abunda tayi mashi jiya shiyasa ta zaƙe tana shige mashi

Ganin baida alamun yi mata maganane yasa tace"fadamin baby, ko dai hajiya saratu ce ta 6ata maka rai"? Banza yai da ita baice uffan ba..

Murmushi tadan saki"nasan itace ta bata maka rai, bari na nuna maka wani abu nasan zakayi farin ciki idan ka ganshi" ta fada da sauri ta nufi mirror

Goya hannayensa yai akan kirjinsa yana jiran karasowarta.


"Baby, duba ka gani, jiya a wurin taro bayan tafiyarka naga wannan yaron mai kama da ɗan mu Naufal kyakkyawan gaske" cikin annushuwa ta mika mashi wayar don ya kar6a ya gani, rai amatuƙar 6ace yakai ma wayar bahagon naushi tayi sama ta ƙundumo kan tiles ta bada wani sauti mai karfi.


idanunta azazzare ta dago tana kallon shi, Huci yake yi tamkar mayunwacin zaki Ya furta"kin manta abunda ki kai min jiya"? Dafe kai tayi da hannu daya idanunta tuni sun cuko tab da kwalla, ranta abace tace"pravin! Meyasa zaka jefar min da wayata? Laifin me nayi maka? Saboda kawai naki bin umarninka? Wai meke damunka ne pravin? Agaban mutane fa ka ruko hannuna kaja ni zaka fitar dani daga hall tayaya bazan ki binka ba? Ko so kake afara zargin mu ?


Kafin ta ƙare maganar Ya daka mata tsawar data firgitar da ita, nuna ta yai da yatsan hannun shi"yi min shiru! Bana son jin komai daga gare ki, ashe harni ban isa in baki umarni ki bi ba! Hankalin ki ya kwanta Kin kunyata ni a idon jama'a..." hawayene suka soma sintiri akan fuskarta, muryarta na rawa tace"pravin ka fahimce ni mana, kasan bazan ta6a kin bin umarnin ka ba, hakanan batare da kwakkwarar hujja ba! Ni nayi hakanne saboda bana so wani ya tuhume mu..." yatsansa ya daura kan la66anta, shiru tayi tana kallon shi

Can kuma ta fashe da kuka tasa hannu ta ture yatsan nasa tana fadin"baka kyauta min ba, Tun jiya nake zumudin in nuna maka hoton sajeed Yaron dake kama da danmu amma shine ka fasa min waya..."?

Ta6e la66ansa yai kafin ya furta"ki yi hakuri rainane ya 6aci, " ya fada tare da zukunnawa ya dauki wayar yana fadin"zan siya maki wata" 


"bana so, ni dai ka gyaramin tawa, saboda bana son na rasa hoton sajeed"

Harara ya watsa mata tareda cewa"meye alakarki da shi ne? Kawai daga ganin yaro yana kama dake? Mutun nawa kika sani suna da masu kama dasu a duniya? Kamar kanki farau"

"Ni wannan bai dameni ba, Ina son shi saboda inajin shi kamar ɗana dana rasa"

 Rai a6ace ta fada kafin ta juya ta koma kan gado ta zauna, tana cigaba da matsar kwalla

Murmushin gefen fuska pravin yasaki Yana dubanta, 

Komawa gefenta yai ya zauna bayan ya ajiye wayar ya ruko hannunta acikin nashi

"Look, bana so ki sanya damuwa aranki,  idan har rashin naufal ne ke damunki, nayi maki alkawarin nan bada jimawa ba zaki haifi wani babyn, sai ki sanya mashi sunan naufal din"

Wani kallo ta jefa mashi batare da tace mashi ƙala ba, lallashinta Yacigaba dayi duk don ya samu yashawo kanta.


HAJIYA SARATU



_safa da marwa take yi a tsakar dakinta, zuciyarta cike fal da tunanin abunda Pravin yayi mata jiya a dakin taro, tun jiya abun ke ci mata tuwo akwarya, abun sai nanuƙarta yakeyi, zuciyarta ta gama hasala, wai har ita pravin zai kunyata gaban yan uwanta da abokananta? A ina ya samu ƙwarin gwiwar yi mata haka? ruƙe qugu tayi da hannu ɗaya fuskarta babu annuri_



*Daga Alƙalamin Boss Bature💋✊✍️*




 *Littafin kurkukun ƙaddara 500 ne, dukanshi Book One two and 3 Idan kin shirya biya ga Details da zaki tura*


3196407426


First bank 


Bature Hafsat Muhammad,


 *bayan kin tura zaki bada transaction reciept ko screenshot na debit alert a matsayin shaida ta wannan layin 08169856268*

1 Comments

Idan kuna da tambaya akan abinda Baku game ba ko kuma kuma Neman littafin da babu a nan kawai ku ajiye tambayarku a ta comment ko wani shawara da Zaku bamu.

  1. Dan Allah inason ciaban littafin nan a Ina zansu

    ReplyDelete
Previous Post Next Post

Sponsored Link

Sponsored Post