Kurkukun Kaddara Takun Karshe Page 19 Complete


Health College

Kurkukun Kaddara Takun Karshe Page 19 Complete

Novels Elite English

 _*~✊💋BOSSLADIESWRITERS💋*~_




                     سجن القد💋🔥💞    



                  ~Takun Ƙarshe🔥~




            Dedicated to Aunty Kubra💋💞




قصة حب رومانسية غير عادية بين السجناء مع   تطورات معقدة💋💘😘



An extraordinary romantic love story between prisoners with complex twists ❤💋💘




Daga alƙalamin Boss Bature💋✊



____________________________________✍️


 ANEELERH


Bakinta ɗauke da sallama ta shiga dakin abie, yana daga zaune gefen gadon shi sanye da farar jallabiya, idanunsa a manne da farin glass, yayin da hannun shi ke a ruƙe da kur'anin da yake karantawa, sai da yakai aya kafin ya ɗan ɗago yana dubanta tare da amsa mata sallamar da ta yi


A tsanake ta shiga ta zauna daga kasan gadon kusa da kafafuwan shi, cikin girmamawa ta gaishe da shi

Fuskar shi dauke da murnushi yace"oum junaid, kin tashi lafiya" sunnar da kanta kasa tayi fuskarta da murmushi tace"lafiyalou abie"


"Ina jikallan nawa? Maimakon ki tafo min da shi? ko dai rowar ɗan za'ay min ne" cike da jin kunyarshi tace"a'a abie, ni na isa in hana ka jikanka" 


Murmushi yayi kafin ya Miƙa hannu ya ɗauko wayarsa dake ajiye kan side drawer ya miƙa mata


"Kar6i nan, Ki duba sakon da aka turo miki" da sauri ta sanya hannu ta kar6a, kafin ta ɗaura idanunta kan screen ta soma karanta sakon 


_Assalamu Alaikum, barka da rana abie an wuni lafiya, ya iyali, ƙawar Aneelerh ce benazir matar tajudeen, Ina son yin magana da ita sai dai bani da contact dinta, dan Allah a hadani da ita, nagode sosai, ku huta lafiya__



Lokacin da ta kai ƙarshen Sakon Idanunta azare, baki a buɗe da tsantsar mamaki take kallon screen din wayar, sam takasa gasgata abun da aka rubuta mata, Muryarta ƙasa ƙasa take maimaita sunan Benazir Benazir!


Abie dake ta kallon ta, ganin tayi kasaƙe babu alamun zata motsa ne yasa shi yin gyran murya, kamar wadda aka zungura da sanda a ɗan firgice ta dube shi tana faman zare idanu

"Lafiya? Ko bakisan ta ba ne"?


Muryarta a harmutse tace"abie, na kasa yarda ne da abun da gani, wannan sakon da aka turo min daga benazir ne aminiyar nan tawa, matar da yau tsawon shekara goma sha wani abu da 6atan ta...." kafin ta ƙare maganar abie yace"kina nufin Benazir yar gidan Alhaji ubaid? Wannan ƙawar taki ta ƙuruciya" jinjina mashi kai tai alamar eh.


"To ki kira layinta mana sai ki ji idan itace da gaske" amsa mashi tayi da toh, da sauri ta miƙe ta fuce daga ɗakin a falo ta tsaya kafin ta danna call, jikin ta har kerma yakeyi tsabar zumudin taji idan banezir ce take neman ta. ......



*DAULAR ALHAJI MUSA*


Gaba ɗayan su sun Hallara a kan dining chairs, Tani da lami ne suke dawainiyar yin serving din su, an shake masu table da lafiyayyan abincin breakfast.


Tun da suka zauna babu mai magana acikin su, zeenatu da benazir abayane a jikin su, sun daure kansu da head scarp,    yayin da Hajiya sarah ta sanya fitted gown ta atampa, kayan sun bi shape din jikinta, sam babu ɗankwali akanta sai zallar gashin kanta da ya sauko har kan kafadarta, mom layla ma atampar ce ta sanya, Alhaji Ubaid da shureim jallabiya ne a jikin su, Alhaji musa ne kadai ya ɗauki wankan tsadaddiyar shadda launin blue sky, kayan sun zauna mashi abunka ga namijin duniya, yayi kyau sai dai babu annuri akan fuskarshi kamar kullum Ya haɗe rai kai kace bai ta6a murmushi ba, tsabar yadda ya ɗaure fuskarshi yana faman shan kamshi kamar wanda iska ke yi ma wari.


Abinci yake ci kamar baisan tauna shi, hajiya layla dake kallon shi ji take kamar ta shaƙe shi saboda haushin shi da take ji.


Dr shureim dake cin abinci a tsanake ranshi ne ya bashi cewar Ana kallon shi a hankali ya dago da idanunsa kai tsaye suka shiga cikin na zeenatu, murmushi ta sakar mashi tare da kashe mashi ido ɗaya, da ɗan mamaki akan fuskarshi Ya zaro mata ido da sauri ta sunnar dakai kasa tana cigaba da sakin murmushi, girgiza kanshi yayi kafin ya maida hankalinsa akan abunda Yake yi.


Gaba ɗaya Hankalin benazir baya atare da su, ta tasa plate din abinci agaba ta kasa ci saboda tunanin Yarinyar da ta kira ta a daren shekaran jira, tun washe garin jiya take ta kiran layin baya shiga hankalin ta yaƙi kwanciya.


"Benazir Lafiyar ki kuwa? ko wani abu na damunki ne? Tun dazu na lura dake kin kasa cin komai" cikin kulawa mom sarah tayi mata magana.


Sauke ajiyar zuciya tayi kafin tace"ba abunda ke damuna mommy, lafiyana qalou"

"Okey, ki fara cin abincin kada ya huce, ba lallai yai maki dadi ba"

Amsa mata tayi da toh 

Spoon ta ɗauka ta soma cin abincin zuciyarta cike fal da tunanin Unaisah


Wayar dr shureim ce ta soma ringing daga cikin aljihunsa, Hannu ya zura ya curo ta yana duban me kiran nasa.


"Ka tsaya ka kammala cin abincin, Inya so daga baya sai ka yi picking call din" 


Muryar Alhaji ubaid ce ta katse masa hanzarinta.


"Daddy, kira ne mai mahimmanci,"

"Shikenan je ka daga" mikewa yai a hanzarce yabar dining din


Tafiyarsa keda wuya Hajiya layla ta dubi Alhaji Ubaida dake a zaune gefenta tace"ya maganar da mukayi dakai jiya"? 

Murmushi yadan saki Yana duban fuskar Alhaji musa Yace"ay na fada maki, Ki ƙara hakuri"


girgiza kai tayi"bazai yiwu ba, ni bazan cigaba da zama acikin gidan nan ba! Wannan ay abun kunyane ace muna zaune gidan kaninka....." maganar na dira kan kunnan Alhaji Musa Ya ajiye spoon din hannunsa, fuskarsa a murtuƙe Ya ke duban Hajiya layla, yasan tayi maganar ne don Yaji ta.

Gaba daya hankulansu mom sarah ya dawo kanta.


"dan Allah ki yi shiru ya isa haka! Muje ɗaki mu yi magana" galla masa harara tayi"wallahi babu inda zanje, ko na bika bai wuci ka bani hakuri ba, Ni nagaji da zama acikin gidan nan, gaba ɗaya a takure nake, Kai ko gudun surutun mutane ba ka yi? tsawon kwanaki kana zaune agidan kaninka tare da Iyalinka"?

Hankali atashe mom sarah tace"dan Allah kiyi hakuri, mu kammala cin abincin sai muyi magana...." kafin ta ƙare maganar Alhaji musa Ya dakatar da ita ta hanyar daga mata hannu tuni taja baki tayi shiru.


Jikin zeenatu harya fara yin kerma saboda batason tashin hankali arayuwarta, abun kaɗan ke rikitata, ita dai benazir ba ta ce komai ba ta zuba ido tana kallom mommyn nasu dake ta faman tada jijiyoyin wuya.


A gadarance Alhaji Musa Yace"Bana son haniya"


Harara ta watsa mashi"ay idan baka fita harkar mijina ba, hayaniya yanzu ka fara jin ta, wallahi bakaso zaman lafiya ba, akan me zaka dinga juya mutane son ranka sai kace wasu bayin ka, komai sai dai ka bada umarni abi, to wlh bazan lamunta ba! Hakuri na Ya ƙare, idan shi ka rufe masa baki to ni baka isa kayi galaba akaina ba!" ta fada tare dakai hannu ta bugi gaban table da karfi, kafin ta yunkura ta mike tare da kallon Alhaji ubaid.


"Ni zan tafi, tun da naga kai baka da niyar barin gidan," mayar da dubanta tayi ga benazir"tashi mu tafi" jiki asanyaye benazir ta miƙe, nan take zeenatu ta fashe da kuka tana fadin"Inna lillahi mom layla dan Allah kada ku tafi, wallahi banso, mommy kada ki bari su tafi, daddy kace masu su su yi haƙuri su zauna, ko kuma su tafi da ni" Hankalin Tani dana lami ba karamin tashi yayi ba, ganin rikicin dake shirin 6allewa.


Wani irin tausayin ta ne ya kama benazir sam batason ta rabu da yarinyar sai dai ba yadda zatai dole tabi umarnin mahaifiyarta.


Da sauri Alhaji Ubaid Ya mike muryarshi da 6acin rai Yace"haba layla menene haka? Yanzu abun ki kai kin kyauta? Mutane suna zaman su lafiya kin tarwatsa masu farin cikin su"


Dakatar da shi Alhaji musa yai, Cike da isa Ya mike tare da kallon fuskar Hajiya layla dake huci.


"Ga hanya nan ki tafi, Allah Ya raka taki gona" bayan ya furta hakan Ya juya azafafe Ya nufi bedroom dinsa Yana shiga ya dauki wayarsa, Call Ya danna tana fara ringing akayi picking

Muryarsa akausashe Yace"kada ku bar kowa ya fita daga gidan nan Idan Har bani na baku umarni ba"!


On the other hand Muryar wani basamuden mutun ta amsa mashi da cewa "Angama Yalla6ai" sauke wayar yayi 



"Haba dear, why ba zaka bari su tafi ba, na fa ji kiran wayar da kayi, meyasa zaka rike su? Tun da matar nan ta nuna bata son tafiya to ka ƙyale su su tafi mana," muryar mom sarah a kule tayi maganar tana duban bayan shi...


Tamkar tayi magana da bango, babu alamun zai juyo ya fuskance ta balle harya amsa mata, Rai a6ace ta dawo ta gaban shi ta tsaya idanunta cike tab da kwalla ta furta"magana fa nake yi maka....." 


da buɗar bakinsa sai cewa yai"Toh Uwata Ina sauraron ki" ya fada yana ruƙe qugunsa, Idanunsa akan fuskarta, bata san ya akai ta tsinci kanta da jin shakkarshi, sam takasa cigaba da yin maganar.


Gefen wuyanta ya shafa da tafin hannun sa"sau nawa zan ja maki kunne akan ki daina shiga abun da ya shafi dangina!" cikin sanyin murya tace"bazan ƙara ba"


Jinjina kanshi yai, kafin ya ƙara furta wata maganar, Muryar zeenatu ta karaɗe kunnan su.


Shigowarta kenan dakin ko sallama babu, Muryarta da shesshekar Kuka take fadin"daddy dan Allah kada ka bari su tafi, ni ban gaji da ganin su ba, ko kuma ka bari na bi su mu tafi a tare"


Juyawa yayi tare da daura idonsa akan ta, fuskarta tayi jawur hawaye na sintiri kan kuncinta.


Miƙa mata hannu yai da sauri ta nufe shi, hugging dinta yai tare da ɗaura hannunsa kan bayanta yana dan bubbuga shi cikin sigar lallashi.


"Ya isa, Ki daina kuka My daughter, ko dan saboda ke bazan bari su tafi ba, dolensu ne su zauna gidan nan ko suna so ko basa so" sauke ajiyar zuciya zeenatu tayi jin abunda yace, Hankalin ta ba karamin kwanciya yai ba, Hajiya Sarah ta kasa furta komai, Jikin ta yai mugun sanyi musamman yadda Taji Alhaji musa Yana magana da gadara babu ɗa'a a kalamansa....


A fusace Layla Ta nufi dakin ta, bayan tace da benazir taje ta haɗo kayanta su tafi, bin bayan ta Alhaji ubaid yayi kamar zai rufeta da bugu sai faɗa yake yi mata, Ko kallo bata isheshi ba, trolley din kayanta ta ɗauko Ta fara kwashe kayanta dake a cikin closet tana jerawa a akwatin.


Dawowa dr shureim yayi aɗan rude yake kallon dining din ganin babu kowa, da sauri Ya nufi dakin Benazir Yana shiga ya sameta, zuƙunne gefen gadon ta tana kuka, ga trolley din kayanta da ta gama haɗawa.


a ruɗe ya furta Benazir? Lafiya? Meya faru naga hawaye akan fuskarki"?


Jiki asanyaye ta mike tare da kallon shi, fuskarta tayi jawur da ita.


 "Yaya shureim bayan kaje amsa kira, mommy ta fara faɗa akan ita bazata cigaba da zama gidan nan ba, shine tace min inzo in hada kayana mu tafi, ni kuma bana son tafiya saboda ban cimma burina ba, na ganin na haɗu da Aneelerh...." 


Share mata hawayen ta ya somayi da hannayensa cikin sigar lallashi Yace"kiyi hakuri ki daina zubar da hawayen ki, bana so kina sanya damuwa aranki, amma ni kaina na goyi bayan ku tafi benazir! Ko dan saboda abunda ke faruwa dake agidan nan, Ina jin tsoron na rasa ki, kwata kwata hankalina bai kwanta da zamanki ba'


"Yaya shureim idan na tafi tayaya zan haɗu da Aneelerh"?


Harya buɗe baki zaiyi magana, kwatsam Wayarsa ta fara ringing, a hanzarce Ya duba sunan mai kiran nashi, wani irin annurin farin cikine Ya bayyana akan fuskarshi, arude benazir tace yaya shureim lafiya naga kana murmushi"


"Alhamdulillah, Kiran da muke ta jira ne sai yau Allah Ya nufa zamu gana da su, kar6i kuyi magana, abban Aneelerh ne Yake Kiranki...." Yatsun hannunta har kerma sukeyi wurin picking call din kamar zata zauce tsabar murna


Muryarta da zumuɗi ta furta"Assalamu alaikum Abie Ina kwana...."


Kafin ta ƙare maganar unexpected Muryar Aneelerh ta ratsa kunnanta da wani sauti mai karfi ta furta"BENAZIR!! Mafarki nake ko gaske"? Fashewa da kuka benazir tayi jin muryar aminiyarta da kunnuwanta sukai maraicin ji na tsawon shekaru.


Cikin shesshekar kuka tace"Wallahi nice Aneelerh, nice benazir din da kika sani..."


Kafin ta ƙare maganar, Itama Aneelerh ta fashe da matsanancin kuka tana fadin"Benazir baki kyauta ma kanki ba! Meyasa? Meyasa? Meyasa kika gudu na tsawon shekaru? Idan wani abu ke damunki ba zaki faɗa mana ba? Kinsan irin kunci da radadin da muka ji bayan tafiyarki? Kin kama hanya kin gudu kin bar jinjira acikin kwamin wanka, Da ranki da lafiyarki baki ta6a kira kinji awani hali Yarki take a ciki ba, wai dan Allah meyasa kikayi haka benazir meyasa.....?" kasa ƙarasa maganar tayi saboda kukan da ya sarƙe makoshin ta.



Tsananin tausayin su ne Ya kama dr shureim, tun dazu yana atsaye yana kallon Banazir kuma yana sauraran komai da suke tattaunawa.



"Dan Allah Aneleerh Ki nutsu inyi maki bayani..." Aneelerh bata bari tayi mata bayanin ba rai a6ace tace"me zaki faɗa min benazir? Ni meyasa ma kika kirani ne? lokacin da yakamata ki kira baki kira ba sai yanzu da lokaci ya kure...." hankali atashe benazir ta ke sauraron ta idanunta sun kaɗa jawur da su la66anta na kerma ta furta"meyasa kikace haka"?


Ɗuff taji Aneelerh ta kashe kiran, hawaye na sintiri ta dago tana kallon shureim wanda tuni jikin shi ya gama yin sanyi.


"Yaya shureim ta kashe kiran, dama nasani ba lallai ta kula ni ba..." tsananin tausayinta ne Ya kama shi, hannu yasa ya kar6i wayar, Ya sake Kiran Aneelerh taƙi ɗagowa. 


Text message Ya tura mata


_Aneelerh ki ɗaga kiran, Ba benazir bace yayanta dr shureim ne Ina son Yin magana dake_


A 6angaren Aneelerh, Jiki amace ta sulale kan carpet ta zauna dirshan sai kuka takeyi, bakomai take tunawa ba face Angel da tajuddeen, Taji takaicin yadda Benazir tayi watsi da rayuwarsu gashi Yanzu ita benazir din ta dawo su kuma sun 6ata babu su a doron duniya

Muryar Angel ta soma tariyowa kalaman da saba fada mata tuntana yar ƙanƙanuwarta 

  

_Aunty aneelerh wai meyasa Mommyna bataso na? gani yar kyakkyawa dani kowa rububina yakeyi amma ita, bata damu dani ba, shine ma ta haifeni ta bar ni acikin kwamin ka,  idan bata sona to meyasa ta haife ni ay da ta sani ta kashe ni acikin ta_


Ƙarar shigowar sakon ne Ya fargar da ita daga zurfin tunanin da ta shiga, zuciyartace ta dinga tunzurata akan kada ta duba wayar ta ƙyale ta kawai, saboda ta bata haushi, Taji zafin abunda tayi.


Wayar sai ringing takeyi taki dubawa, kasa jurewa tayi, saboda ita kanta tayi kewar aminiyartata, bazata taba mantawa da ƙawancensu ba, duk da taci wahalar banezir saboda rashin jin maganarta.


Yatsun hannunta na kerma ta ruƙo wayar ta duba sakon, bayan ta gama karantawa, a kagare ta soma kokarin bin kiran don taji me dr shureim zai faɗa mata, aranta tana mai mamakin bayyanarsu lokaci ɗaya.


Video Call ta kirasu don ta ƙara tabbar da cewa su dinne, bayan sunyi picking call din kallon kallon suka soma jefawa junansu, kowa yasha kuka, hakika sunyi mamakin canzawar da sukayi, duk sun fara manyanta...

Cikin sanyin murya ta furta"ya shureim! Dama kana nan"!

Jinjina mata kai yai alamar eh, kafin Ya soma magana cikin nutsastsiyar muryar shi.


"Aneelerh, inaso ki nutsu ki saurari abun da zan fada maki" amsa mashi tayi da toh, saboda tana ganin girma dr shureim.


"Abun da Ya faru da banezir bayin kanta bane, mu kanmu bamu san da hakan ba sai lokacin da ta dawo, bata a cikin hayyacinta gaba ɗaya alamomin da muka gani ajikinta ya tabbatar mana da cewa Kurciya akayi mata, shiyasa ta gudu tabar yarinyarta batare data tuntu6i kowa nata ba......" atsanake shureim ya fayyace mata komai, Ita kanta benazir din batasan da abun da suke zargin anyi mata ba sai yanzu da taji abakin dr shureim, hankalinta ba karamin tashi yayi ba, aneelerh kuwa jikinta yagama mutuwa, cikin tashin hankali take ambaton inna lillahi wa'inna ilahirraji'un.


Dr shureim Yace"hakuri zamuyi da abunda Ya riga ya faru, bana so muna tuna ba....." nasiha ya cigaba dayi masu har saida Yaga hankalin su Ya kwanta, kafin Ya bar wayar a hannun benazir Ya basu wuri don su gana da junansu

Kamar yau ce rana ta farko da suka fara haɗuwa, sai bin kansu suke yi da kallon kurulla, Allah ne kaɗai Yasan irin kewar  juna da su ka yi.


"Benazir bansan yadda zan misalta maki farin cikin da nake a ciki ba, Allah shine shaidata, Naji dadin ganinki da ranki da lafiyarki"


Cikin sanyin murya tace"nima haka Aneeleerh, ashe da rabon zamu gana bayan tsawon lokaci"? Ta fada tana matse kwallar da ta cike idununta.


"Aneelerh, Ina Yarinyata dana bari? Ina mijina Yake? Mommy ta fada min basa kasar nan amma ni ban yarda da maganarta ba, dan Allah ki fada min gaskiya, saboda nasan ke kadaice zaki fada min"


Fuskar Aneelerhh ɗauke da matsananciyar damuwa take kallon benazir dama sai da tayi fargaban tambayar da zatai mata, tuni taji zafafan hawaye sun cika mata idanunta.


"Aneelerh kinyi shiru baki ce komai ba? Pls ki yi min magana wlh ji nake kamar zan zauce saboda ƙagarar da nayi na son ganin su ..."  ta faɗa tana dubanta


"Kada ki ji komai, Ki faɗamin kawai ko da ace sun mutune zan rungumi ƙaddara..." cikin karfin hali ta faɗa, tun da tafara maganar Aneeleeh ke kallonta gwanin ban tausayi.

 

bata jin zata Iya sanar da ita a yanzu, ko dan gudun kada zuciyarta ta buga, ƙwara ta kwantar mata da hankalin ta.


Ƙaƙaro murmushi tayi akan fuskarta 


"Abun da mami ta faɗa maki gaskiya ne, suna nan cikin koshin lafiya, sun yi tafiya zuwa south korea inda Uncle dinsa abdalla ke zaune, amma ina ji araina sun kusa dawowa"


Tsabar farin ciki yasa banezir sakin dariya har fararen hakoranta suka bayyana, Aneelerh dake kallonta tsantsar tausayintane Ya ƙara kamata.


"Dan Allah Aneelerh idan kina da hotonta ki turomin inason ganinta, Idan ma kina da number taj din ki bani sai muyi magana da shi, wlh naƙagara da son ganin su"


Murmushi Aneelerh tayi"kada ki damu zan tura maki da hotonta har ma dana yaro na, sai dai bani da layin taj bansan da wanne yake amfani acan kasar ba"


Da mamaki tace"Aneeleerh dagaske kin haihu? Ya'yan ki nawa yanzu"?


"Shi kadai Allah Ya bani, baki ganshi ba, kyakkyawa kamar Angel dinki.."


Muryarta na rawa tace"Allah sarki, Aneeleeh, na tayaki murna, Ina mijin ki ko shima hada shi suka tafi korean"?


"Atare suka tafi" murmushi benazir tayi kafin ta kuma cewa"ki bani labarin Yarinyata, inason jin kuruciyarta, Ina fata dai bata dauko halina ba.." dariya aneelerh tayi da zolaya tace"like mother like daughter, Har tafi ki rashin ji magana," waro idanu banazir tayi hada sanye hannu ta dafe kanta ɗaya"indai kuwa hakane nasan ba lallai ta yi min da sauki ba, watakil ma ta tsane ni, bata son ganina" ta fada tamkar zata fashe da kuka 


"Ki ma daina wannan tunanin, taya ɗa zai ƙi jinin uwarsa, ay bata da abu mafi soyuwa da yawuce mahaifiyarta, ni nasan Angel bazata ta6a gudunki ba"

 

kwantar mata da hankali taci gaba dayi, har ta bata labarin unaisah, taci dariya wani wurin kuma ta matse kwalla.


"Allah sarki tajudden na barshi da dawainiyar yarinya, abunda yakamata ace ni nayi bansamu damar yi ba..." in a cool voice tayi maganar," shiru suka danyi na wani lokaci kafin Aneelerh tace"Har yau babu labarin Aisha! Baiwar Allah taga rayuwa, gaba daya ƙaddarace ke bibiyar rayuwarmu lokaci ɗaya ƙawancenmu ya tarwatse nayi takaicin rasa farin cikin amintarmu' hawayen dake taruwa acikin idanunta tuni sun fara wanke fuskarta....


Shiru banezir tayi zuciyarta cike fal da jimamin halin da suka tsinci rayuwarsu.


"Inaso nazo gidanku Aneelerh, ki kirani da layinki, sai inyi saving contact naki" amsa mata tayi da toh, sunjima suna waya kafin sukayi sallama da junansu..


Meya faru bayan Ummi Ta fuce daga dakin su Unaisah?


Da gudu ta nufi dakinta, tana shiga ta bude toilet ta tsaya agaban Sink tana kwarara amai, idanunta sun kada jawur da su, shatun jijiyoyin goshinta sun fito rudu rudu kamar zasu fasa fatarta, tayi kuka tamkar ranta zai bar gangar jikin ta, komai na duniyar nan ya sire mata, taji takaici da tsanar rayuwar da ta daukarwa kanta saboda takasa hakuri ta rungumi ƙaddarar ta, Sai gashi yau taji abunda Ya jefata adanasani, Yan kananun Yara da basu ji ba basu gani ba, wadannan ma tun suna jarirai suke fuskantar jarabawar rayuwa, Ita kuwa da ilminta da hankalin ta da tunaninta ta faɗa harkar karuwanci saboda ta kasa cinye jarabawarta lamarin yayi matukar gigita tunaninta... 


Faucet ta kunna ruwa ya soma shararowa ta tarfa hannu tana watsa shi akan fuskarta, kamar an zare mata karsashin jikinta, da wata irin kasala ta fito jiki babu ƙwari ta faɗa kan gadonta tare da kifa kanta jikin pillow, bakomai take tariyowa ba face rayuwarta ta baya...

Sam ba taji motsin shigowar mutun ba, saboda ta lulu duniyar tunani 

A hankali batool take tafiya tana tunkarar gadonta, hayewa tayi kan gadon ta zauna kusa da ummi tana leƙen fuskarta


"Aunty Ummi," kamar daga sama taji muryar batool, a hankali ta buɗe idanunta da suka kumbura ta daura su kan fuska batool.


"Dan Allah ki daina kuka aunty ummi, bana son ganin hawayen ki, bana jin dadi" ta fada muryarta na rawa alamar zata fashe da kuka.


Janyota ummi tayi tare da kwantar da ita kan kirjinta, sosai ta rungumeta ta daura hannunta akan bayanta batare data furta magana ba.


 Aranta tana mai mamakin tawakkalli irin Na Yaran, abunne da daure kai, da ace wani mai karancin imanin ne hakan ta faru da shi da tuni yajima da hadiyar zuciya ya mutu amma su a haka suka jure da dadi da ba dadi sukai ta rayuwar ƙunci a kulle tun kafin su mallaki hankalin su.


Numfashi taja, wani irin kaunar yarance taji ta ƙara kama zuciyarta, har ta fara tunanin tawace hanya zata taimaka masu don ganin sun inganta rayuwarsu tun da basu san komai ba .

Bakomai ne ya fado mata aranta ba face zagin da ta ta6a yima batool har ta kirata da sunan jahila wadda bata san komai ba sai ci da bacci... Runtse idanunta tayi sosai tana mai jin takaicin kalaman da ta furta mata, gashi yanzu yarinyar tafi kowa kaunarta

Shafa sumar kan batool taci gaba dayi kafin wani lokaci bacci yai awon gaba dasu arungume da juna kamar zasu dawwama ahaka.......💔


___________________________________✍️


*❤Unaisah Angel💋💝*


Fitowa tayi daga part dinsa bayan ta gama gyara masa shi, A hankali take saukowa down daga kan stairs zuciyarta cike fal da tunanin abubuwa da dama wadanda suka faranta mata rai a yau kamar wata zautacciya sai faman sakin murmushi take yi.


"Daughter i'm back" miryar taj ce ta katse mata zancen zucin nata, kallon shi tayi fuskarta da fara'a, da sauri ta karasa sauko down, mayafin kanta har yana kwancewa daga kanta ya zame ya faɗo kan kafadarta, sumar kanta ta rufa mata bayanta.


Tana ƙarasawa ta fada kan kirjinshi kamar wadanda suka dade basu ga juna ba.


Murmushi yasaki yana fadin"sannu da kokari ina fata kin yi abun da Ya dace" 


ɗagowa tayi da kanta ta daura idanunta akan nashi"har gyara masa part din sa nayi, kafin ma na kammala har ya fita ban same shi ba"


"May be ya tafi gidan kakansa ne" acewar chief,


"Kinsan me naje yi agida" girgiza mashi kai tayi alamar a'a.


"Auntynki na faɗa mawa ta hada maki wani abu mai dadin gaske zuwa anjima zatay baƙuwa, amma fa ban gaya mata wacece zata zo ba" 


"Naji dadi daddy, kana ji dani"


Mayafin ta dake akan kafadarta ya ruko yana fadin"bari na gyara maki shi" A hankali Ya soma naɗa mata shi, bayan ya kammala ya manna mata sumbata kan kuncin ta kafin ya ɗago da kansa


kwatsam! Ba zato ba tsammani Yaji saukar dundu akan bayanshi tamkar za'a rusa shi, tsabar zafin da yaji ne yasa shi saurin dafe bayan da hannu, tuni ya fara ganin jiri a cikin idanunsa.


Hankalin ta amatuƙar tashi ta wurga idanunta don ganin wane yayi wannan aika aikar saboda itama taji sautin dundun da akayi mashi.


Har saida gabanta Ya faɗi lokacin da tayi arba da shi atsaye yana huci tamkar mayunwacin zaki, tsabar fusata jikin shi har gumi yake fitarwa, magana yakeso yayi amma saboda zafin da zuciyarshi keyi mashi ya kasa sai la66ansa dake kerma.


Harara ta watsa mashi saboda ya bata haushi, zuciyarta ajagule ta ruƙo hannun taj Tana fadin"Inna lillahi! daddy dan Allah kayi hakuri..."_ bata ƙare maganar ba, danish Ya fusgo ta tare da janyota jikin shi, yasa hannu biyu ya rungumeta kamar zai maida ta cikinsa


Lamarin yayi matuƙar ɗaurewa taj kai, idanunsa jawur yake kallon danish Yama rasa me zaiyi, amma tabbas dundun da yayi masa ya kusa yi mashi illa saboda zogin da bayansa keyi mashi kamar an ɗoɗana masa wuta yadda kasan ba hannun mutun bane yayi dundun, yaji zafinsa sosai.


Kiciniyar kwace kanta tafara yi hawaye tuni sun wanke fuskarta ganin baida alamun sakinta ne yasa ta daddage ta gartsa mashi cizo kan kirjinsa, ko gizau baiyi ba, saima ya kara hadeta da jikin shi, zuciyarta har tafarfasa take yi mata saboda 6acin rai.


 Kallon kallon suke jefawa junansu tsakanin shi da tajuddeen, kwata kwata bai yi yunƙurin Janye angel daga jikin danish ba, saboda ya fahinci Yaron ba shi kadai bane tun daga kan dundun da yayi mashi ya shaida hakan.


Shigowo Falon big guy da ɗan saurinsa Yana ganinsu Ya nufe su da mamaki Yake kallon Danish daya rungume unaisah

"Lafiya? Meke farune"?

Taj ne yai karfin halin fada masa abun da danish yayi masa 


Zuciyarshi ta sosu Harara Ya watsa masa kafin Yace"Sakar ta, tun kafin na 6ata maka rai, kaida bawani koshin lafiya ba har ka fara neman rigima? Ko kunya baka ji ba ka rungume Yarinya gaban ubanta! Idan ma baka sani ba to bari na fada maka wannan da kake gani mahaifinta ne wanda Yai silar zuwanta duniya...." ko ajikinsa bai ma fahimci me Big guy yake nufi ba, sai ma haushin shi da yake ji, Jira yake big guy yakai hannu zai raba shi da ita anan ne zaiga ainihin true colour dinsa...


 Atsawace big guy yace"baka ji me nace ba, ka sake mana"!


"Ka daina yi mashi tsawa, Ka kyale shi kawai, nayi mashi uziri saboda baisan komai ba, kuma Yaro ne sai muna lalla6a shi"


Big guy bai tsaya sauraron Taj ba Ya kai hannu zai ja rigar unaisah, wata irin kururuwar tsawa danish Ya daka mashi tamkar saukar aradu, Gaba ɗaya saida suka firgita saboda Yadda sautinta Ya cika masu kunnuwan su, Unaisah dake manne ajikinshi tsabar kiɗima kiris Ya rage ta saki fitsari a wando, saboda firgitar da tayi.


idanunsa sun kaɗa jawur Yana huci Ya furta"kada ka kuskura ka ta6aba, Ranka zai 6aci, zanyi maka abun da baka ta6a tsammani ba, Idan har kayi gigin shiga tsakanina da ita...." ya faɗa yana faman cije red lips dinsa, yadda kasan ba daga bakinsa kalaman suka fito ba saboda girman su.



da gudun gaske Naufal da Sajeed suka fito daga dakunansu, kamar wadanda aka koro tun wannan tsawar da danish ya kwatsa kowan nan su Ya firgita har wadanda ke adaki, kai hatta Ummi da batool sai da suka farka daga bacci jiki na 6ari suka sauko down stairs, ɗaya bayan ɗaya suke fitowa ƙwansu da kwarkwatarsu, hankalinsu gaba daya yana akan Daninsh dake a rungume da unaisah, jikinta sai kerma yakeyi duk tabi ta ruɗe, numfashinta kanshi dakyar take fidda shi.


Kusan atare suka hada baki suna tambayar meya faru? danish dan Allah kayi mana bayani meyasa ka ruke Unaisah ka sake mana ka matseta.. Sajeed ne yai maganar, 

Big guy daya gama harzuƙa Har Ya yunkura zai Ƙara kamo rigarta Taj yai saurin damƙar damtsen hannun shi, suka hada ido da juna girgiza mashi kai yai alamar a'a saboda shi yasan mai yaji dakyar in ba sai yayi jinyar bayansa ba.


"Haka zamu zuba mashi ido muna kallon shi? Baka ga yadda Ya matse ta bane? Ko magana takasayi"!


 Cikin muryar lallashi Taj Ya dubi Danish dake ta faman zare idanunsa tsabar masifa har ƙanƙance su yakeyi


"Dan Allah kayi hakuri ka sake ta, indai saboda ni ne bazan ƙara taba maka ita ba"  Mamaki da al'ajabine Ya kama su Ummi dake kallon Ikon Allah

 

"Meyasa zaka bashi hakuri? Kaida ƴarka? Tsoron shi kake ji ne"? A harzuke Big guy yai maganar


Taj yace'ba tsoron shi nake ba, fitina ke bana so, idan mukace zamu bi ta karfi da yaji donmu kar6e ta wlh ba zamu iya ba sai dai muja yai mata wata illar kwara mu lalla6a shi' guntun tsoki Big guy yaja, gaba daya haushin danish Ya cika shi, duk da yana tausayin prisoners sai dai ayanzu lamarin danish Ya fara sanya shi kokwanto akansa, gani yake kamar yaron yana da wata muguwar manufa.


Haduwa su Naufal sukayi suna ta yi mashi magiya don Ya sake ta, Amma Ya ƙi sakinta


Suna acikin wannan Halin, a lokacin da basu yi tsammani ba, Sallamar Salsabeel Ta katse su, gaba ɗaya suka dago suna Kallon shi 


Ganin shi yasa danish sakin Unaisah tai taga taga zata faɗi da sauri batool ta ruƙota, sai faman haki takeyi tana sauke ajiyar zuciya kamar wadda tasha gudu....


Sunyi tunanin shi kadaine Yazo, kusan atare muryoyinsu khadeeja Ya daki kunnuwansu, tunkafin su karasa shigowa suka fara kokarin tunano su wanene? Saboda sun haddace muryarsu ko tari sukayi za su iya sheda su.


Ɗaya bayan ɗaya suka fara Shigowa bakunansu dauke da sallama, Lokaci ɗaya suka Ci burki suna Kallon su Unaisah dake kallon su, kusan atare zuciyoyinsu ke harbawa da matsanancin karfi, Tsabar rudani da al'ajabi Ya hana su gasgata abunda idanuwansu suke nuna masu, har abada ba zasu ta6a mantawa da muryoyin yan uwansu ba, balle kuma kamannin su da basu ta6a gogewa a idanunsu ba, Kokwanto sukeyi anya kuwa yan uwan sune da suka baro prison ba rai? Ko dai mafarki sukeyi ne? Ko kuwa idanunsu ne suke nuna masu badai dai ba? Tayaya ma haka zata yiwu? 


Murza idanunsu suka farayi don su kara tabbatarwa da kansu abun da suke gani dagaske ne ko akasin hakan!


Kamar yadda suke al'jabin ganin su haka suma su Rubina suke kallon su da matuƙar ruɗani akan fuskokin su, babu mai magana acikinsu falon yayi tsit kamar mutuwa ta gifta, har na tsawon mintuna kafin salsabeel Ya fara magana 


"Abun da kuke tunani dagaske ne, Ku daina kokwanto, wadannan da ku ke gani ƴan uwanku ne, da kuka baro agidan kurkukun ƙaddara, ni kuma sunana salsabeel ɗan tsohuwa tamira, nasan ba lallai ku shaida kamanni na ba, amma ita Unaisah ta gane ni...." fuskar shi dauke da murmushi ya yi maganar, har lokacin babu wanda ya motsa daga cikin su kamar gumaka, tsantsar tsabar rudani da mamaki ne Ya daure su har suka kasa magana, Hatta khadeeja da take da tabin hankali tayi kasaƙe tana bin su da kallo kamar tana so ta tuna su wanene su ...... .


"Tayaya ma haka zata yiwu? Ni fa nagaza gasgata abun da idanuna suke nuna min, Kaina Ya ƙulle dan Allah ku fahimtar dani, ni dai a iya sanina kafin mu baro gidan kurkukun ƙaddarar amace muka barsu yanzu kuma sai mu gan su da ransu da lafiyar su? dama wanda Ya mutu Yana dawowa ne"? Sajeed ne Ya faɗa fuskarshi da alamun ruɗani

  Salsabeel Ya fahimci halin da kowan nan su Ya shiga, In har ba faɗa masu ainihin abunda ya faru yayi ba, toh zaiyi wuya su yarda da bunda suke gani, cikin sanyin murya ya fara ba su labarin abun da ya faru bayan barin su gidan kurkukun ƙaddara......


Waiwaye adon tafiya


Tayaya akai Salsabeel tare da su khadeeja suka ku6uta daga gidan kurkukun ƙaddara!? Bayan a iya sanin mu su deeja sun mutu sakamakon zuciyarsu da ta buga❓❓❓


Bari mu koma baya don jin meya faru?


Suna shiga Cikin Toilet ɗin, Danish Ya datse ƙofar da sihirin shi, ya Janye tukunyar fulawar daga kan ƙofar, nan ta ke ta bayyana duk irin wahalar da suka sha ta ƙi buɗewa shi Bugu ɗaya yayi mata gaba ɗaya ta 6alle murfin ƙarfen ya dare biyu, Sun yi mamaki da al’ajabi yace da su”Ba zai bi su ba, zai tafi da Akwatin kayan su tare da back pack ɗin su, za su tarar dashi a bakin ƙofar da zasu 6ula idan sun ƙarasa” hankalin su bai kwanta da maganar shi ba, gani su ke yi kamar wani mummunan abun zai faru da su idan baya atare da su, ganin sun toge sunƙi tafiya yasa shi  Kwantar masu da hankali, daƙyar ya samu su ka Zuƙunna ƙasa tare da kutsa kai ɗaya bayan ɗaya su ke shiga cikin ƙofar da rarrafe, Bayin Allah ga yunwa ga ƙishin ruwa, ga raɗaɗin da zuciyarsu ke yi masu, Ita kanta hanyar da suka biyo Wata uwar ƙura ga yanar girgizo da ƙwari sai hawan masu jiki su ke yi, Amma saboda rashin kwanciyar hankali yasa basu damu da su ba. Babu mai magana acikinsu saboda ƙunar da ran su ke yi masu, Angel ce tai ƙoƙarin tunasar dasu akan suci gaba da ambaton addu’o’in data koya masu ko sun samu sassaucin a wurin Allah, sun ɗau ki shawararta ahaka suka Dinga tafiya da rarrafe babu ƙaƙƙautawa, idan suka gaji su kan ɗan zauna su huta kafin su dasa da wata tafiyar, A ƙalla sun shafe tsawon awanni Takwas suna rarrafawa ba tare da sun kawo ƙarshen Ƙofar ba, a takure su ke Bayin Allah sun ga rayuwa gwiwowin ƙaffuwan su duk sun gurje sun sage, maƙoshinsu ya bushe ƙamas, tun suna ambaton ƙishir ruwa suke ji har sun gaji sun yi shiru.........”😭


A tsugunne yake gaban gawar tsohuwa tamira, yayin da hawaye ke sintiri kan fuskarsa, idanunsa sun kaɗa jawur da su, zuciyarshi ta gama karaya, tamkar baya a cikin hayyacin shi, gaba ɗaya rayuwar duniyar ta sire mashi, duk sai yaji ya tsani kanshi, bai da wani buri daya wuce shima Ya mutu, sai dai baya son ya mutu batare daya gyara rayuwarsa ba, yana da burin wata rana yayi rayuwar yanci, kamar ko wani ɗan adam, yana son yayi sallah ya gana da ubangijinsa, Tun kafin Ya mallakin hankalinsa Rayuwarsa take a cikin gidan kurkukun ƙaddara cikin kunci da takaici, idanunsa sun jima suna gane masa bakin zaluncin da ake aikawata agidan kurkukun ƙaddara, babban takaicinsa mutuwar mahaifinsa tamira batare da ta cimma burinta ba na ganin ta kawo karshen zaluncin shuwagaban nin gidan kurkukun ƙaddara, bai ta6a tsammanin zata riga shi mutuwa ba, yaso ace yacika mata burinta sai dai kash ƙaddara ta riga fata......


Babban burinshi Su Unaisah su tsira da ransu ko dan su kai labarin gidan kurkukun ƙaddara saboda al'umma su san da zaman shi, ko an samu wadanda zasu yi shahada su kawo karahen zaluncin da ake aikatawa.....


Hawayen dake sauka kan kuncinsa a hankali suke ɗiɗɗiga saman gawar tsohuwa tamira....


Gaba ɗaya ya manta da lokacin shi da ke tafiya, sam ya shafa'a ya manta da zancen binne gawarsu da yace zaiyi saboda hankalinsa ya gushe.


Kwatsam yayi zurfi acikin tunaninsa, ba zato ba tsammani kamar daga sama Yajiyo sautin dirar wani abu mai matuƙar razanarwa, harta ginin dakin sai da ya girgiza, lokaci ɗaya ya zabura ya miƙe zuciyarshi na harbawa da karfi da karfi, tunkafin ma yaga menene ranshi ya bashi cewar Giants ne na gidan kurkukun ƙaddara, mutanan da babu ɗigon imani aransu, zuciyarsu tamkar dutse take, kurame ne kuma makafi ne basa ji basa gani umarnin Elders din su kadai suke bi.


Wani irin wahalallan Yawu salsabeel Ya hadiya mai ɗacin gaske, tuni zufa ta soma wanko mashi, gaba daya yabi ya zauce saboda bai da karfin da zai Iya ja da su, sunfi karfin shi nesa ba kusa ba.


Tsabar kidimar da yayi ce ta shi yin zarya a dakin tsohuwa a kokarinsa naya nemo hanyar da zai kubutar da gawawwakinsu gudun kada su wulakantasu .. 


Kafin yayi wani yunkuri Ya soma jiyo takun tafiyarsu, A matuƙar firgice Yake kallon fadadan kafafuwansu.


Kusan su uku ne, Wasu irin gabza gabzan samudawa masu kirar Zakuna, kamar fatalwu haka suka fado dakin, from head to toe sun rufe jikinsu da bakaken kaya baka Iya ganin komai nasu.


_Yawu salsabeel Ya haɗiya, ta ko'ina zufa ce ke tsastsafo mashi ta cikin hudojin gashin fatarsa, muryarsa da tsantsar tashin hankali Ya furta"zanyi maku bayani...." bai ƙarasa maganar ba, Muryar wani basamude daga cikin su mai amon gaske Ya furta"Salsabeel ka yi kuskuren ƙetare iyakarka, ka riga da kasan hukuncin wanda Yaci amanar Elders! Sakamakon ka mutuwa ce, zakayi mummunar mutuwa salsabeel zamu kashe ka sannan mu watsa ma karnukan mu naman ka su cinye shi, bayan haka waɗannan ƙasƙantattun gawarwakin da ke a kwance zamu kwanta da su, idan muka gama biyan buƙatarmu da su, zamu cire sassan jikinsu muyi farfesu da su, Kasusuwan jikin su kuma zamu rataye su ne......_ 😳😳😳



*Daga Alƙalamin Boss Bature💋✊✍️*



 *Littafin kurkukun ƙaddara 500 ne, dukanshi Book One two and 3 Idan kin shirya biya ga Details da zaki tura*


3196407426


First bank 


Bature Hafsat Muhammad,


 *bayan kin tura zaki bada transaction reciept ko screenshot na debit alert a matsayin shaida ta wannan layin 08169856268*

Post a Comment

Idan kuna da tambaya akan abinda Baku game ba ko kuma kuma Neman littafin da babu a nan kawai ku ajiye tambayarku a ta comment ko wani shawara da Zaku bamu.

Previous Post Next Post

Sponsored Link

Sponsored Post