Kurkukun Kaddara Takun Karshe Page 20 Complete


Health College

Kurkukun Kaddara Takun Karshe Page 20 Complete

Novels Elite English

 _*~✊💋BOSSLADIESWRITERS💋*~_




                     سجن القد💋🔥💞    



                  ~Takun Ƙarshe🔥~




            Dedicated to Aunty Kubra💋💞




قصة حب رومانسية غير عادية بين السجناء مع   تطورات معقدة💋💘😘



An extraordinary romantic love story between prisoners with complex twists ❤💋💘




Daga alƙalamin Boss Bature💋✊



_AUNTY XEE Thank you for being there for me. Your support has been a lifeline.💋💞_ 



__________________________E20✍️




Tashin hankalin da ba'a saka masa rana!, Idanunshi azazzare Yake duban su,  jikinshi ya soma kakarwa, tsabar kiɗima zuciyarshi tamkar zata fasa ƙirjinshi saboda bugun da takeyi masa, bakomai ne yafi ɗaga masa hankali ya zautar dashi ba face kalmar zasu kwanta da gawawwakinsu, Inna lillahi wa'inna ilahirraji'un wannan wace irin musiba ce? Cikin karyayyar murya yace"Ni yakamata ku hukunta saboda ni nayi maku laifi, na roƙe ku ko dan sanayyar dake a tsakanina daku....."


Wata irin mahaukaciyar dariya suka tuntsire da ita jikinsu har jijjiga yakeyi kamar ana bugun ganguna, wani daga cikinsu ne ya kuma cewa"Ba sani, ba sabo a tsakanin mu, saboda ka tabka babban kuskure salsabeel ka yi ha'inci, don haka dole ka fuskanci hukunci mai tsanani daga gare mu"


Sunan Allah Ya ci gaba da ambato acikin zuciyarshi, duk addu'ar da tazo mashi yinta yakeyi ba ƙaƙƙautawa, har jaraba Yin amfani da sihirin shi yayi don ya ku6utar da kanshi da kuma Gawawwakin amma abun yaci tura, ƙarfin sihirin shi bai kai na su ba, sun riga da sun yi mashi mugun ɗauri na sihiri ba zai iya ta6uka komai ba.


Ja da baya ya soma yi ganin suna tunkaro shi, cikin matsanancin tashin hankali, kafin ya ƙurema bangon ɗakin tuni ɗaya daga cikinsu yai zazzafan taku ya damƙi wuyan salsabeel da kafcecen hannun shi, nan take numfashinsa ya soma ƙoƙarin ɗaukewa, ɗaga shi yai sama tun Yana kiciniyar ƙwace kanshi harya fara gazawa idanunsa sun kaɗa jawur sun fiffito waje, nan take ya soma bleeding ta baki ta hanci, wani irin raɗaɗin azaba ne Ya ziyarci salsabeel tamkar ana yi mashi ɗaskanan wuta a jikin shi, fuskarsa tayi jawur jini ya kwanta a fatarsa, hawaye da gudu suke kwararowa ta cikin idanunsa bakomai zuciyarshi ke tariyo mashi ba A lokacin face kalaman mahaifiyarsa Tamira, Idanunsa na akan gawarta.... Numfashinsa na kiciniyar ɗaukewa gaba ɗaya ya gama jigata har ya fidda rai da rayuwa, a lokacin da basuyi tsammani ba  suka jiyo sautin dirar wani abu a bayansu, da sauri giant ɗin daya shaƙe wuyan salsabeel ya sake shi jiki ba ƙwari ya kife ƙasa kan shi Ya daki ƙasa daƙyar numfashin sa ke fita da hucin zafi, kusan atare Giants ɗin  suka juya baya don ganin menene Ya faɗo cikin ɗakin da har Ya bada sautin mai kuwar gaske.


Da wani irin tsantsar Al'ajabi suke kallon shi, yadda kasan saukar aradu Haka Ya faɗo masu Yana huci kamar Mayunwacin Zaki, kwata kwata babu riga a jikin shi sai dogon wandon kakin Giant, jikin shi sai tsuma ya ke yi tsabar fusata, ta ko'ina zufar 6acin rai ce ta ke tsastsafo masa, harta tsokokin jikinsa motsi su ke yi, da wani irin hucin zafi numfashin sa ke fita.



Shin Wanene Wannan? To bakowa bane face GARKUWA, dalilin dayasa shi dawowa kurkukun saboda hankalin shi yaƙi kwanciya yasan mawuyacin abu ne Salsabeel ya samu fita daga cikin kurkukun tare da gawawwakin salin alin, ranshi na bashi cewar wani mugun abun zai iya faruwa da Salsabeel ɗin, shiyasa lokacin da su ka shiga cikin makewayin bayan ya buɗe ma su Angel kofa yaƙi bin su yace su fara yin gaba shi zai taho da Akwatin kayan su tare da back pack ɗin su, za su tarar dashi a bakin ƙofar da zasu 6ulla idan sun ƙarasa, yayi hakanne don ya samu damar dawowa ya taimaki rayuwar salsabeel saboda baya son ya rasa shi ko dan saboda halaccin da ya yi mashi a rayuwa bazai ta6a mantawa ba, yaji mutuwar tsohuwa Tamira don haka bazai bari rayuwar salsabeel ta salwanta ba❗



Kallon kallo su ka soma jefawa junan su tsakanin Giants da Garkuwa, wato gaba da gabanta, Aljani Ya taka wuta, banbancin Danish da sauran Giants shi ƙarfin sa Na Evil giants ne masu Star Uku kai ko a cikin su Ya zarce su Power, babban kuskuran da Elders sukayi shine damƙa amanarsu gare shi saboda ya zama garkuwarsu a duk lokacin da za'a kawo masu hari, ba su ta6a tsammanin garkuwarsu zai Iya cin amanarsu ba, shiyasa suka bashi sihirin da ya fi na kowani giant na gidan kurkukun ƙaddara, a halin yanzu babu mai iya karawa da shi sai Elders wato Leaders ɗin su, Danish Yana da kwatankwacin ƙarfin giants ɗari a jikin shi, baƙaƙen shaiɗanun dake a jikin shi wani irin ƙarfi ne da su na fitar shari'a, kuma basa ji basa gani umarnin shi kaɗai suke bi, hatta su kansu elders ba su isa su hana shaiɗanun bin umarninsa ba, kuma su sukayi kuskuren ɗaurashi akan turbar da yake ashe da rabon su yi danasani mai girman gaske,


Duk da Salsabeel baya acikin hayyacinshi Hankalin shi ba ƙaramin tashi yai ba, ganin Danish Ya dawo! Muryarshi na rawa ya furta "meyasa! Meyasa Danish? Meyasa ka dawo? Ina ka baro su Angel? Sautin muryarshi ko fita batayi shi kaɗai yake sambatun shi ba tare daya iya ɗagowa da kan shi ba, saboda raunatar da yayi.



Ɗaya daga cikin giant dinne Ya ambaci sunan shi"Garkuwarmu"! Yana huci Yace"Ni ba garkuwarku bane! Garkuwar su ne! idan har kuna son zama lafiya to ku ƙyale salsabeel da gawawwakin nan, Idan ba haka ba, zanyi maku abun da baku ta6a tsammani ba"! da kakkausar murya ta majiyi ƙarfi ya faɗa yana nunasu da yatsan hannun shi.


A lokacin kusan suman tsaye sukayi saboda mamakin kalaman shi! haƙiƙa yayi matuƙar ɗaure ma su kai sun firgita da jin furucin sa.


"Amma dai wasa kake mana ko"? Girgiza kai yayi "na ta6a yi maku wasa makamancin wannan!?


"Idan kuwa har dagaske ne, Elders sunyi kuskuren yarda dakai maci amana! Ka bamu mamaki! Ina ka samu ƙwarin gwiwar da har ka Iya gaya mana magana a gaban idon mu ba tare da jin shakkarmu ba?" Shiru yayi baice masu komai ba.


"Tun wuri ka yi gaggawar Janye ƙudurinka, Saboda kai namune baka isa ka juya mana baya ba, har abada kai mallakin gidan kurkukun ƙaddara ne, kuma garkuwarmu, Idanma mafarki ka ke yi to ka farka tunkafin lokaci Ya ƙure maka, duk wani abu da zakai taƙama dashi anan ka same shi, kuma da zarar elders sunji maganar nan, kasan me zai biyo baya......" wanda yayi maganar Ya faɗa yana mai yi mashi kashedi.



"Har abada ba zanyi danasanin bijiremaku ba, Shawarar da zan baku shine kuyi gaggawar barin wurin nan idan kunaso ku tsira da rayukanku saboda ni banzo da niyyar na cutar da wani ba, ɗan uwana kawai nakeso na ku6utar daga sharrin ku."



Babu yadda Danish bai yi da su ba akan subar salsabeel amma suka sanya kafiya, dama su giants basu da tsoro kuma basa karaya sai dai komai zai faru ya faru, Kafin kace me faɗa ya kaure tsakaninsu tamkar a filin Yaƙi, tuni ƙura da kururuwa sun karaɗe cikin daƙin, bakajin komai sai gurnaninsu mai matuƙar firgitarwa, gaba ɗaya sun rikiɗa sun koma dodanni masu ban tsoro sai kaima juna farmaki su ke yi kamar abokan gaba, Kakin Giant ɗin dake jikinsu Ya faffasa  saboda garkuwa ne agare su, idan har ba ciresu yayi ba to bazai iya yin galaba akan su ba balle har Ya yi nasarar kashe su, wani irin bahagon naushi ya soma sakar masu akan idanuwansu duk wanda ya nausa nan take ƙwayar idanuwansa ke zazzagowa cikin Jini Ta faɗo ƙasa, gaba ɗaya Ya zautar dasu Ya nakaɗa masu lugudan wahala, Har saida numfashinsu Yabar gangar jikinsu tukunna Ya zuƙunna Yana huci batare daya canza halittarsa ta mutane ba Yabi su ɗaya bayan ɗaya ya farke ƙirjin kowannan su ya 6an6aro zuciyoyin su Ya tura abaki Yana ci saboda Ya ƙara ƙarfin sihirin shi.


Ɗakyar Salsabeel Ya samu ƙwarin gwiwar miƙewa numfashinshi na fita sama sama, muryarsa da rauni Yace "Danish meyasa ka baro su Unaisah Ka dawo don ka taimaki rayuwata, Idan wani abu ya same su fa"?


Danish bai tanka mashi ba, har Sai da Ya gama abunda Yakeyi tukunna Ya girgiza jikinshi ya rikiɗa ya dawo ainihin suffarshi ta mutane.


Ruko hannun salsabeel yayi acikin nashi yana faman fitar da huci Yace"Saboda rayuwarka tana da mahimmanci, bazan bari na rasa ka ba, nasan cewa zasu iya farmakar ka shiyasa na dawo don na ceci rayuwarka, Inaso na cika maka burinka na ganin ka binne gawarwakin su tsohuwa tamira sannan in ku6utar da kai.


Girgiza kai Salsabeel yayi hawaye cike fal da idanunsa yace"Danish ka tafi kawai, Zasu Iya riskarka, wallahi ba zasu ƙyale ka ba, ni kuma bazanso ka ƙara shan wahala arayuwarka ba, Yanzu lokaci ne da yakamata kayi rayuwar yanci Danish, inaso kayi farin ciki kafin kabar duniya, Hakkin ka da aka tauye maka na rayuwa shi nakeso ka samu Danish dan Allah ka tafi, kabarni kawai, ka koma wurin su Unaisah ni basai na rayu ba, rayuwarku tafi mahimmanci agareni nasan zaku haɗa gwiwa don ganin kun kawo ƙarshen elders...." magiya ya dinga yi masa akan ya tafi ya ƙyale shi amma yaƙiya har saida ta kaiga Ya daka mashi tsawa a faɗace Yace"Ka tafi ka ƙyaleni!! nace maka ka tafi! ka tafi !kabarni kawai..." 



Cikin sanyin murya Danish yake faɗin "bazan tafi ba salsabeel, Idan kaga na bar wurin nan to na kubutar da kai ne..."


Gaba ɗaya sun Harzuƙa, faɗa ne ya kaure atsakanin su kamar zasu bugi juna, kwatsam a lokacin da basuyi tsammani ba, sautin tarin Deeja Ya cika kunnuwansu, kamar an dasa masu aya suka dakata dayin sa'in sar da suke yi,  kusan atare suka kai idanunsu ga duban inda take a kwance da tsantsar al'ajabi, babu wanda yayi zaton  akwai me rai acikinsu, da sauri Danish Ya nufe ta Yana dubanta, idanunta a runtse take sambatu cikin fitar hayyaci take ambaton sunan haris da Angel tana faɗin "ku taimaki rayuwata kuna ganin za'a cutar dani........" kallon juna sukayi shida salsabeel, kafin Ya mayar da dubansa ga sauran gawawwakin dake baje ƙasa da sauri yakai hannu ya ɗan ta6a ƙafar Rubina wani iko na Allah nan take Taja Numfashi da ƙarfi ta fesoshi batare da ta bude idanunta ba, sai la66anta dake kerma, ɗaya bayan ɗaya yake farkar da su babu wanda yake a cikin hayyacin sa duk sun jigata sun galabaita, sai sambatu su ke yi suna ambaton ruwa ruwa za su sha, ƙi shi suke ji.



Maimakon salsabeel yayi farin cikin farfaɗowar su, sai ya fashe da kuka yana faɗin "wallahi banso suka rayu ba, saboda bani da yadda zanyi da su, mutuwar ita ce hutunsu, ga shi babu yan uwansu sun riga sun tafi...." 


Cikin tashin hankali ya ruƙo hannun Danish yaci gaba da faɗin"ka taimakamin Mu binne su kawai, su ƙarasa mutuwa acikin ƙabarinsu, ni banga amfanin suci gaba da rayuwa a wannan duniyar  ba, wahala zasu sha idan mutanan nan suka riske mu zasu kashe su ne bayan sun gama wulaƙanta rayuwarsu....", kafin Ya ƙare maganar Danish Yace"bazai yiwu ba, kamar yadda yan uwansu suka rayu suma haka zasu rayu, bazan ta6a bari su rasa ransu acikin gidan kurkukun kaddara ba, ko da kuwa zan jefa kaina cikin hatsari ne sai nayi musu hanyar da za su gudu" da ƙwarin gwiwa ya furta kalaman tare da fucewa daga dakin tsohuwa yaje ƙasan gadon Batool inda suke ajiye robobin ruwa ya dauko su ya wuce toilets din dakin su ya samo masu ruwan da zasu sha, bayan ya dawo yabi su daya bayan daya ya basu ruwan suka soma sha.

 

Salsabeel dake kallon shi tsabar ƙululun bakin ciki baisan sa'adda ya fashe da kuka yana fadin "Danish ka tafi kawai, idan har bazaka taimaka min mu binnesu ba, dan Allah ka tafi zaifi min kwaciyar hankali, Ka rigada kasan bamu da wata hanya da zamu iya ceton su...." Cak Ya tsaya da yin maganar ganin babu danish Kamar walkiya Ya 6ace ma ganin shi, Shiru yayi yana faman haɗiyar yawu cike da zullumin ina Danish Yaje? Ko dai Ya tafin ne ...? Tuni ido Ya raina fata sai kace ba shi bane yake korarsa akan Ya tafi ba, wani irin tsoro ne Ya ziyarci zuciyarshi, hankali atashe yake kallon su Dija dake zazzaune a ƙasa cikin fitar hayyaci suke ambaton sunan ƴan uwan su musamman sunan Unaisah da na Danish, gaba ɗaya sun zauce,  gawar mahaifiyarsa ya kalla tuni wani kukan ya kuma zuwa mashi cikin matsanancin tashin hankali Ya soma ƙwalawa Danish Kira don Ya dawo ya taimake shi ko ya samu ya binne su.



Jin shiru babu alamun zai dawo ne ya sa shi zubewa kan gwiwowinsa Yana ta faman yin shesshekar kuka kamar ransa zai fita.


Kamar daga sama Yaji motsi a ɗakin, A firgice Ya ɗago da idanunsa azazzare ya kai duban sa ga Bookshelve ɗin ɗakin tsohuwa tamira dake Ta motsi, Kafin yai wani yunkuri gaba ɗaya Ya rikito Ya rubza ƙasa, Jikinsa na 6ari Ya miƙe yana kallon ƙofar da ta 6ullo, da matuƙar mamaki akan fuskar shi.


Ta cikin ƙofar Danish ya fito, fuskarshi sharkaf da gumi Ya dubi Salsabeel.


  "Zamu Iya tafiya" wani irin farin Cikine Ya lullu6e Salsabeel.


A ruɗe ya furta"Danish tayaya akai ka gano ƙofar nan? Ban ta6a sanin akwai ta ba, kuma bana tsammanin ko ita tsohuwa tamira tasan da zaman ta" ya faɗa cike da son jin ƙarin bayani.


Yana faman huci yace"Kada ka manta, ka riga ni tsintar kanka acikin kurkukun ƙaddara ni kuma nafi ka sanin komai na cikin sa, duk wata ƙofar sirri dake a kurkukun nan nasan da zamanta, tabbas tsohuwa bata san da wannan kofar ba, tsohuwar hanyace da aka jima da toshe ta, ni da kaina na sake haƙa ta da sihiri na, Idan muka bi ta cikin ta, zata 6ular da mu cikin wani kogon dutse dake wajen kurkukun nan, dalilin dayasa na za6i ku raba hanya da su Unaisah saboda nasan zasu iya farmakar mu idan har suka gano abunda ke wakana, inaso na raba masu hankali ne watakil in mukayi hakan wasu su rayu daga cikin mu" 


Bazai iya jure kallon Danish ba, Yaron Ya burge shi, Ya yi mashi abunda bazai ta6a mantawa ba, ya taimake sa a lokacin da rayuwarsa take akan ga6ar salwanta, da sauri ya janyo shi ya rungume shi yana kuka, kafin ya raba jikin su cikin sanyin murya yace


"Amma danish su Angel fa? Yakamata ka koma wurinsu suna buƙatar ka, bana so wani abu ya same su"


Girgiza kai Danish yayi "kada ka damu, babu abunda zai cutar da su, saboda na rigada na ɗaure hanyar da suka bi da sihiri babu wani mahalukin da ya isa ya iya tsaga kofar ya shiga balle har ya cutar da su, kafin nazo nan sai da na kiyasta awannin da za su yi kafin su ƙarasa kofar da zata 6ular da su waje ni kuma zan riga su komawa bayan na taimake ku"


Murmushin farin ciki salsabeel ya saki,

Basu tsaya bata lokaci ba suka yi kokarin taimaka ma su Hibba don su miƙar da su tsaye, saidai mutun biyu daga ciki kafafunsu sun kasa ɗaukar su sakamakon abunda tsohuwa Zafreen ta yi ma su, bayin Allah sai ihun azaba suke saki, da sauri Danish Ya sungumi deeja ya goyata a bayan shi, ya sanya mayafin daya ɗauko a ƙasa ya ɗaureta tamau, kafin ya ɗauki Rubina ya ɗaurata a kafaɗar shi dama su biyune basu iya tafiya.


shi kuma Salsabeel ya yi amfani da bargon tsohuwa tamira ya nannaɗe gawarta aciki ya ɗaurata a kafadarsa.


A haka suka bi hanyar mai duhun gaske ga zafi tamkar ana rura garwashin wuta, sunci baƙar wahala su sarah kamar numfashinsu zai ɗauke. Cikin awanni takwas da su Angel sukayi suna rarrafawa akan hanyar su duk wannan abun Ya faru, baifi awa biyar ba su salsabeel sukayi nasarar fita daga cikin gidan kurkukun ƙaddara hakan na nufin sun riga su Angel ku6uta saboda tasu hanyar batai nisan wadda su Angel suka bi ba.


Bayan su Salsabeel sun 6ula cikin kogon dutsen, Danish Ya sauke deeja da Rubina daya ɗauko, shima Salsabeel ya sauke gawar tsohuwa tamira, su hibba duk suka zube agajiye har lokacin bakunansu basu gushe da ambaton sunayen ƴan uwansu.


Kallon juna sukayi kowan nan su na haki, da sauri salsabeel ya ruƙo hannun Danish, cikin sanyin murya yace "Danish, bazan ta6a mantawa da halaccin da ka yi min ba, kayi min abunda har abada bazan ta6a mantawa dakai ba, kaine silar ku6uta na daga Gidan kurkukun kaddara kuma kaine silar cikar burina na ganin na cika alƙawarin mahaifiyata dana ɗaukar mata akan in rufe gawarta kada in bari ta wulaƙan ta, Danish ko a mafarki ban ta6a tunanin akwai ranar da zan bar gidan kurkukun kaddara ba, nasha jaraba guduwa nida mahaifiyata amma mun kasa saboda karfin sihirin mu bai kai ba, sai gashi a sanadiyar ka nayi nasarar fita...." tuni hawaye sun wanke fuskarshi.


"Danish, Koda ace ban rayu ba, ni ka gama min komai wallahi, koba komai na shaƙi iskar duniya bayan tsawon lokaci da na kasance a kulle" ya faɗa yana duban cikin idanunsa "ni dai burina ka yi rayuwar farin ciki tare da yan uwanka, ubangiji Allah Ya kare min ku ya tsareku a duk inda zaku kasance, bani da tabbacin zamu sake haduwa wataƙil ma ba lallai mu rayu ba....." bai ƙarasa maganarba ya fashe da kuka mai cin rai, da sauri Danish ya janyoshi suka rungume juna sosai suka kankame jikinsu.


Bubbuga bayanshi Salsabeel yai da hannunshi "ɗan uwana, ka kula min da kanka, wallahi ina mutuwar sonka tun farkon ranar da aka kawo ka gidan kurkukun ƙaddara a cikin tsumman ka, naso ka Danish, zan tafi da kewarka, Allah ya rayamin kai Danish, Ina fata wata rana kaima ka zama cikakken musulmi, ka yi rayuwa kamar kowa kayi Aure ka hayayyafa....."


Lumshe idanu Danish yayi cikin sanyin murya yace"ina sonka ɗan uwana, nima zanyi kewarka, ka kula min da kanka, ina fata mu sake haɗuwa" Yana faɗa Ya raba Jikin shi daga na Salsabeel, A hankali ya soma tafiya yana ja da baya yana duban Salsabeel da ƴan uwan shi waɗanda kwata kwata basa a hayyacin su, wasu irin zafafen hawaye ne suka cika idanuwan Danish bai daina kallon su ba har saida yayi nisa kafin Ya 6ace ma ganin su.



Bai dira a ko'ina ba sai a bakin kogon bishiyar da su Angel zasu 6ula, adai dai lokacin su kuma har sun ƙaraso bakin kogon bishiyar suna ta faman ambaton sunan shi.


Bayan tafiyar Danish A cikin Dajin salsabeel Ya samu wuri a gefen wata bishiya ya binne gawar tsohuwa tamira, ya zuƙunna gaban ƙabarinta yai mata addu'o'i yasha kuka kamar ba gobe, har shaida sai da yayi ma kabarin nata saboda yana da burin wata rana ya kawo masa ziyara tare da ƴan uwansa prisoners don su yi mata addu'a.


(Masu karatu kunji yadda akai salsabeel da su Deeja suka ku6uta daga Gidan kurkukun ƙaddara, nasan wasu zasu ce tayaya har suka dau lokacin nan batare da an ritsa da su ba? To idan ba zaku manta ba, shuwagabannin kurkukun ƙaddara basa a ciki, bayan haka an samu tawayar tsaro, sannan babu wanda yasan meke faruwa a sashen su Angel saboda an rikita lissafin Allon tsafin su, su kan su waɗannan giants din da suka shigo sashen har suka ga salsabeel, bawai sun san me suke shiryawa bane, sun zo ne domin tafiya da su Deeja zuwa wani sashe na daban da suke tarasu don su basu ruwan sihiri wanda zai dawo masu da jinin al'adar su saboda su samu damar gudanar da black night ɗin da za'ayi a ƙarshen watan, amma saboda 6arnar da Danish yayi masu yasa duk wani shirinsu ya wargaje, haƙiƙa sunji zafin tafiyar garkuwa da kuma yaran daya tseratar daga tarkon su, wannan ne yasa lokacin da suka yi taron zaman tattaunawa ɗaya daga cikin Elders Yace


_“Wannan ne Karo na farko da muka yi babban kuskure arayuwar mu, wanda idan bamu miƙe tsaye mun nema ma kanmu mafita ba, to tabbas za’ayi nasara akan mu, Ko a tarihi ba’a ta6a samun prisoners ɗin da suka tsira daga kurkukun ƙaddara ba, su ne na farko kuma sune na ƙarshe, da farko sunyi nasarar ƙetare kurkuku da taimakon Garkuwarmu, Na biyu sun ku6uta daga dajin evil forest da taimakon shi, Babu wani mahaluƙin da ya isa ya iya ƙetare kurkuku da dajin evil forest salin alin ba tare da ya Rasa ranshi ba, amma saboda suna atare da garkuwar prison mun rasa cin galaba akansu saboda mu kanmu bamu isa mu Iya ja da shi ba, babu wata muguwar halittar data Isa ta tunkaresu muddin Yana atare da su, rashin baccin da baiyi ba shine Yaja har muka gaza tunkarar su, lokacin da baccin Ya ɗauke shi munyi nasarar yi mashi abunda zai dawo gare mu sai dai wani abun al’ajabi ya ku6uta daga hannunmu Ya koma ma gangar jikin shi_


Kamar yadda suka ce tun tarihin kafuwar kurkukun ƙaddara ba'a ta6a samun prisoners da suka tsira ba sai akan su, kuma ba kowa bace sila face ƙaddarar kurkuku, da ace unaisah ba ta kasance a gidan kurkukun ba, wallahi Danish bazai ta6a yunƙurin taimaka ma wani don ya gudu daga cikin sa ba shiyasa bai ta6a taimakon su Deeja ba bayan yana da hanyar da zai iya fitar da su.


Salsabeel Ya ci baƙar wahala wurin ɗawainiya da su Hibba, babu wanda bai ji jiki ba a cikin su, saboda yankin da su ka faɗo a dajin babu ko kayan marmari da mutun zai sha, yasha jaraba yin amfani da sihirinsa don ya sawwaƙa masu wahalar amma abun ya faska, Saida ta kai ga ciyawa su ke ci ko su ci ganye don suyi maganin yunwar cikinsu, ga Deeja ba hankali tun da tafarfaɗo sambatu takeyi shi kuma Mubeen wasu irin marurai ne masu masifar zafi suka mamaye fatar jikin shi, kullum sai yayi hauka kamar zai rasa ransa saboda raɗadin azaba, ga uwar rana dake ƙwalo masu ta ko'ina ba sauki, ga damuwar rashin yan uwansu sunyi kuka tamkar zasu kashe kawunansu, baƙin cikin da suka ƙunsa baya misaltuwa, hakika salsabeel yayi namijin kokari wurin ganin Ya basu kulawa duk da wani lokacin abun nema yake yafi ƙarfinsa, gaba ɗaya sun jigata sun sha wahala, babban tashin hankalinsu miyagun halittun daji dake kawo masu farmaki, kusan kullum ne sai Salsabeel Ya zubda jinin shi wurin faɗa da su.


Satin su ɗaya acikin dajin suna shan baƙar azabar rayuwa, acikin rana ta takwas suna cikin tafiya agalabaice sunata yi ma Salsabeel kukan yunwa suke ji maƙoshinsu zafi yake yi masu ruwa zasu sha bawan Allah Ya rasa ya zaiyi da su, da gudu Ya nufi Cikin dajin yana neman inda zai samo musu ruwa tun yana tafiya da kuzarinsa har ƙafafuwan sa suka fara sagewa sai da yagama shan wahala bai samu ruwan ba yana kan hanyar komawa wurinsu kwatsam ya faɗa wani yanki na dajin ba zato ba tsammani ya hango gungun Sojojin ƙasar Ghana da suke yin atisayen horaswa a dajin, da gudu ya tunkare su kamar mahaukaci haka suka ganshi Ya faɗo masu, har sun saita shi da bindigu ya zube kan gwiwowinshi ya fara rokon su akan su taimaka mashi da ruwan sha, gaba ɗaya sojojin suka kewaye shi hannunsu ruƙe da bindigu saboda basu yarda da shi ba, sunyi tunanin wani mugunne shiyasa basu bashi taimakon daya buƙataba, tsawa suka fara daka mashi suna tambayar shi wanene shi? Meyake yi a cikin dajin, sam ya kasa ba su amsa, kwatsam ana haka sai ga su mubeen sun watso da gudu iya ƙarfinsu suna neman shi wata dabbar daji ce ta biyo su aguje, a gaggauce sojojin suka harbeta da bindiga tun kafin su ƙaraso nan take suka tarwatsa kan dabbar ta faɗi ƙasa tana birgima, ai koda sojojin suka ga prisoners sanye da jajayen kaya masu numbers a jikinsu sai suka fara zargin salsabeel ne Yayi garkuwa da su tun da shi ne babba acikin su kuma jikin shi akwai zanan tattoo, wanda alama ce ta tambarin wata ƙungiya, ba su tsaya bata lokaci ba suka ɗaure Salsabeel da igiya tamau, su Mubeen sunata kuka suna rokonsu su ƙyale masu ɗan uwansu amman ko ta kansu sojojin ba su bi ba, gaba ɗaya suka sanya su a bayan motarsu ta sojoji, ba su nufi ko'ina da su ba sai cikin ƙasar Ghana.


Bayan isar su, A headquarter suka ruƙe salsabeel wurinsu, su kuma su Hibba Asibiti suka miƙa su ganin muggan raunin dake a jikin su, babu irin bugun da sojojin nan basuyi ma Salsabeel ba don ya faɗa masu me yakai shi daji tare da ƙananun yara amma yaƙi faɗa masu, sai ce masu yai bazai iya tuna komai daya faruwa da shi ba, ya faɗi hakanne saboda bai yarda da sojojin ba yasan ma koya faɗa masu gaskiya ba lallai su yarda ba, A ƙalla ya shafe kwana uku a hannun sojojin kafin ya faɗa masu cewa su ƴan nigeria ne, iya abunda zai iya tunawa kenan a rayuwarsa, ba su sake shi ba har sai da su rubina dake a Asibiti suka samu lafiya sunata tambayar ina ɗan uwansu Salsabeel tukunna sojojin suka gane cewa ba mugu ba ne, ba su tsaya 6ata lokaci ba don sun  fahimci al'amarin su babba ne ba kamar rahoton da Asibiti suka bayar, hakan yasa suka tuntu6i hukumar sojin Nigeria don su sanar da su dangane da yaran inyaso sai su miƙa case ɗin wurin su.


Lokacin da saƙon Ya riski su Sir Mubarak, bayan ya duba duka bayanan yaran, nan take ya yanke shawarar kiran chief owais don ya sanar da shi zancen case ɗin saboda yafi dace wa da hukumar Isod, su yakamata case din yaran ya kasance a hannun su saboda abune da ya shafi 6angaren bincike. 


Chief Owais yayi farin ciki lokacin da Sir Mubarak ya sanar da shi, dama a lokacin sunata faman bincike kan yadda zasu gano Unaisah, daga shi har taj sunyi tsammanin cikin yaran zasu ga Angel, sai dai ko da sukaje Ghana suka dubasu babu ita aciki,  aranar da sukaje basu kwana ba, sai da suka haɗa yaran gaba ɗaya tare da Salsabeel suka tafi da su a privet jet din chief suka shigo Nigeria....


Bayan komai Ya lafa, Sun sama masu gidan da zasu zauna, basu fara bincikar su ba don sun lura da ba'a hayyacinsu suke ba, sai dai suna lura da duk wani motsin yaran sunyi matuƙar yin al'ajabi da irin rayuwarsu, ba su san komai ba, kamar ranar aka haifo su duniya, daga sunci abinci sai bacci, ba zancen yin sallah, ranar da boss ya kunna masu kallo a tv sunga tashin hankali, kuka suka dinga yi ganin baƙon abu da ba su ta6a gani ba, a ƙarshe deeja ce tayi silar mutuwar tv ɗin.


Chief ne ya ɗaukar ma su Jazz a matsayin likitan da zai dinga duba lafiyar su, kafin ya bashi aikin sai da ya gargaɗe shi akan kada ya kuskura ya sanarma kowa ko da kuwa mommynsa ce, shiyasa dr jazz yaƙi sanar ma kowa nashi wanda silar hakan yaja har sir mubarak ya fara zargin shi akan wayar da yake yawan kama shi yanayi ta maganar gidan kaji, matsalar da aka samu shi Sir Mubarak baisan da zancen Aikin da Jazz ya ke yi ma chief owais ba, sannan baisan a gidan da chief owais ya killa ce su ba, amma Yana bibiyar case din yaran don jin wani hali ake ciki game da binciken su.


Bayan wasu yan kwanaki, Su chief suka tuntu6i Salsabeel suka tsare shi da tambayoyi dangane da rayuwarsu, bai 6oye masu komai ba gaba ɗaya ya sanar da su, wa'iyazubillah kusan zaucewa sukayi saboda tsananin tashin da hankulansu suka yi, ba su ta6a jin labarin daya gigita su ba irin wanda Salsabeel ya ba su, abu kamar ashirin wasan kwaikwayo amman wai a zahiri yake faruwa zuciyoyin su sun karaya ainun.


to a cikin labarinsa ne suka ji ya ambaci sunan Angel, sunyi matuƙar girgiza da jin cewa tana a cikin su, kuma sun raba hanya da su, hankalin su ba ƙaramin tashi yayi ba, musamman taj kamar zai zauce jin cewa Angel dinsa tana a cikin su, ba dan zuciyar imani ba da tuni ya haɗiyi zuciya ya mutu, ganin yadda yake kuka kamar ƙaramin yaro yasa Salsabeel tambayar shi meya faru, Chief ne ya bashi amsa da cewa yarsa ce Angel ɗin da ya ke magana akai, wani irin farin cikine ya lullu6e Salsabeel ganin Mahaifin unaisah, jiki na rawa ya ruƙo hannun shi tamau ya fara jinjina mashi yana faɗin ya gode ma Allah saboda yarinyarsa tana da kaifin basira Allah yayi mata baiwar da zaiyi wuya asamu mai irin ta, bayan haka yace da shi ya kwantar da hankalin shi, in sha Allah babu abun da zai faru da su saboda suna atare da garkuwa yayi imanin in har ba lokacin mutuwarsu ne yayi ba to kuwa zasu ku6uta batare da sun cutu ba, abun da ya dace shine su tayasu da addu'a kuma a bibiyi dajin evil forest inda rabon agansu toh, shi kanshi Salsabeel ɗin yayi mamakin daɗewarsu a dajin, amma da yayi zurfin tunani sai ya tuna cewa Danish baisan inda zai kai su Unaisah ba, shi iya rayuwarshi daga gidan kurkukun ƙaddara sai cikin dajin evil forest, bai ma ta6a sanin akwai wasu mutane dake rayuwa a wajen dajin ba, kuma hada ƙarin ba su da taswirar dajin da komai zaifi zuwa masu da sauƙi, saboda dajin evil forest kurman dajine yana da wuyar sha'ani.


Jami'an isod sun yi matuƙar ƙoƙari wurin ganin sun gano su a dajin, kusan kullum ne sai jiragensu sun kewaye shi suna shawagi Allah ne dai bai nufa za su haɗu da su ba.


Babban abun da yaja ma su Angel daɗewa a dajin, Lokacin da Danish ya ke yin amfani da sihirinsa wurin jigilar ɗaukarsu idan dare yayi lokacin sun yi bacci yana yin tafiya mai nisa da su duk don su nisanta da gidan kurkukun ƙaddara silar hakan yaja har suka 6ace hanya suka bar yankin da ya kamata su faɗa, sukai can wani yankin daban. 


_Alhamdulillah, Kunji yadda akai Su salsabeel suka ku6uta daga gidan kurkukun ƙaddara, da kuma yadda akai suka haɗu da Chief Owais, kuma cikin ikon Allah daga baya sai gashi suma su unaisah an ceto rayuwarsu, a ranar da sojin america suka tuntu6i chief da case din samun yara yan Nigeria a daji, wani irin farin cikine ya lullu6e su, anci sa'a a lokacin yaje babban burnin america kuma sai ga labarin tsintar su unaisah, tunkafin suga su wanene ransu ya basu cewar sauran yaran ne kuma zaiyi wuya in babu ita acikin su, cikin ikon Allah sai ga hotunansu sun gani wayyo Allah tsabar murna lokacin da chief ya turama taj hotunansu da yake shi yana a Nigeria, ko runtsawa baiyi ba adaren ranar da suka shaida baiyanarta_


_A tsanake salsabeel ya ƙarasa ba su labarin yana duban fuskokin su_




*Mu haɗu Jibi Idan Allah yakaimu da rai da lafiya, don jin yadda zata kaya*



Daga Alƙalamin Boss Bature💋✊✍️*



 *Littafin kurkukun ƙaddara 500 ne, dukanshi Book One two and 3 Idan kin shirya biya ga Details da zaki tura*

3196407426

First bank 

Bature Hafsat Muhammad,

 *bayan kin tura zaki bada transaction reciept ko screenshot na debit alert a matsayin shaida ta wannan layin 08169856268*

Post a Comment

Idan kuna da tambaya akan abinda Baku game ba ko kuma kuma Neman littafin da babu a nan kawai ku ajiye tambayarku a ta comment ko wani shawara da Zaku bamu.

Previous Post Next Post

Sponsored Link

Sponsored Post