Kurkukun Kaddara Takun Karshe Page 21 Complete


Health College

Kurkukun Kaddara Takun Karshe Page 21 Complete

Novels Elite English

 _*~✊💋BOSSLADIESWRITERS💋*~_

                     سجن القد💋🔥💞    

                  ~Takun Ƙarshe🔥~

            Dedicated to Aunty Kubra💋💞

قصة حب رومانسية غير عادية بين السجناء مع   تطورات معقدة💋💘😘

An extraordinary romantic love story between prisoners with complex twists ❤💋💘



Daga alƙalamin Boss Bature💋✊





_________________________________E21✍️




A tsanake salsabeel ya ƙarasa ba su labarin yana duban fuskokin su, waɗanda suka jiƙe sharkaf da ruwan hawaye, sautin koke koken su ya cika falon, ta ko'ina shessheƙar kukan su ce, Ni kaina bazan Iya misalta zunzurutun farin cikin da ya mamaye zukatansu ba, saboda baya faɗuwa abun sai wanda ya gani da idanunsa, kamar an ruke kafafuwansu sun kasa motsawa su ƙarasa ga junansu, sai kallon ƴan uwansu suke yi kamar yarda suma suke kallon su, ashe rai kan rai? Ashe da rabon zasu gana da junansu? Muryar na rawa suka soma ambaton sunayensu Deeja Eve Yasmin, Rubina, Hibba, Sarah Mubeen, la66ansa na kerma suke ambaton sunayensu, gaba ɗaya rayuwar su ta prison ta dawo masu sabuwa fal acikin zukatansu wani irin tsantsar tausayin ƴan uwansu ne ya kama su jin irin azabtuwar da su ka yi a daji.



"Ba kuka yakamata kuyi ba, Allah Ya kamata ku gode mawa, da ya sake haɗa ku da yan uwanku da ransu da lafiyarsu..." tun kafin Taj Ya ƙarasa maganar, cikin sagewar gwiwa gaba ɗaya suka zube kan gwiwowin su atare su ka yi  Sujudash shukr, khadeeja ce ka ɗai ba tai sujjadar ba, hannayenta ruƙe da takalmanta da ta rungume a ƙirjinta sai faman zare idanunta ta ke yi tana ƙyafƙyafta su, hatta yanayin fuskanta ya canza ga dukkan alamu ƙwaƙwalwarta ce ke ƙoƙarin tariyo mata wani abu da ta yi loosing din shi sai dai kash ta ƙasa tunawa sai ma kanta da ya fara juya mata.


Lokacin da suka ɗago daga sujjadar suna yiwa Allah kirari haɗi da yi mashi godiya, fuskokinsu sunyi jawur da su saboda kuka, da sauri suka fara rungumarsu a jikinsu kamar zasu mayar da su cikin su, ɗaya bayan ɗaya suke hugging dinsu hadi da sumbatar kuncinsu, sautin muryoyinsu masu dauke da tsantsar annurin farin ciki sun cika ko'ina na dakin, Haris sai faman tambayar deeja yakeyi wai fa bai gane ta ba, ba shi ba hatta Unaisah tambayar deeja takeyi suna ta fadin Ina deeja take bamu ganta ba .... salsabeel da ke sauraronsu dariya ce kumshe a bakinshi, 

Da hannu ya nuna masu ita tare da cewa"Gatanan tana kallon ku, sai kunyi hakuri da yar uwar taku, ba lallai ta gane ku ba..." tunkafin Salsabeel Ya karasa yi masu bayani haris ya nufe ta da gudu aikuwa ta watsa aguje kamar wadda taga wani mugun abu, bawan Allah kamar zai fashe da kuka saboda ƙagarar da yayi na son ganinta, 

Muryar shi da shesshekar kuka yace 


"Deeja na kin manta ni? Ni ne fa haris dinki na gidan kurkukun ƙaddara!..."


 fashewa tayi da kuka, hankali ya dawo kanta murya na rawa take fadin"wallahi ba kai bane Haris dina ba, ƙarya kake yi min ni bansan ka ba, Haris dina baƙi ne ba fari ba, kuma shi ba siriri bane' gaba ɗaya suka sanya dariya ga hawaye akan faces dinsu


"Deeja ni fa baki gane ni ba"? Unaisah ce tai maganar, tana nuna mata kanta da yatsa, maƙe mata kafaɗa khadeeja tayi"wayyo Allah ni wallahi ban san su wa ne ne ku ba, Wai ya salsabeel ba cewa kai wurin gasar kyau zaka kaimu ba to su wadanda su wanene ni sun wani tsareni da idanunsu" tana kuka ta faɗa.


"Khadeeja baki gane su ba? Ƴan uwanki ne fa" salsabeel ne ya fada yana kokarin  fahimtar da ita watakil silar hakan ta dawo hayyacin ta.


"Deeja haris dinki ne fa, abokin kukan ki me share maki hawayen ki, dan Allah ki tuna ni deeja, wallahi bakisan haukan rashinki da nayi ba, nayi kewarki deeja kamar zan zauce, har jinya nayi saboda ke" ta6e mashi baki tayi.


"Wallahi bakai bane haris dina ba, ay shi ba haka yake ba"


Dafe kan shi yai da hannu ɗaya zuciyar shi ajagule yace "Na fahimce ki, nasan na canza kema kin canza khadeeja, Ki kalle ni da kyau ni ne dai wannan haris din naki"  harara ta watsa mashi tana faman zumbura bakin ta.


magiya suka dinga yi mata a karshe da sukaga bata da niyar bari su ta6a ba, aiko da gudu suka nufeta gaba daya suka ɗauke ta suka ɗaga ta sama suna jujjuyata, tuntana kuka tana fadin su sauke ta ƙasa, Har dai ta fara tiƙar dariya ba don ta gane su ba, sai don jin dadin abun da sukeyi mata, sauke ta kasa sukai da sauri Haris ya rungumeta ajikinshi suka ƙanƙame juna, ta yi lamo tana faman sauke ajiyar zuciya kamar tana son ta tuna shi sai dai takasa.


Ruƙo hannun Mubeen Angel tayi acikin nata, idanunsu cike tab da ƙwalla suke kallon juna, ta ji tausayin shi, ba zata ta6a manta abun da ya faru lokacin da zasu bar kurkuku ƙaddara ya yanke jiki ya faɗi haka suka haura kafa suka barshi, bawan Allah ashe har ciwo yayi,

Huggin dinsa tayi a kirjin ta, hannayenta daddafe da bayan shi, shima ya dafe ta cike da kaunar junansu,

Hankalin danish bai kai kansu ba, ya basu ya baya, hannayen sa suna acikin na salsabeel sai faman sakar ma juna murmushi sukeyi, wani irin dadi ne Ya lullu6e kowannan su

"Kaine silar komai danish" salsabeel ne ya fada yana dan bubbuga shoulder din sa alamar jinjina


Duk wannan abun dake faruwa akan idon sheikh imam babu wanda Ya lura da shi, Shigowar sa kenan falon Ya taras da abun farin cikin dake faruwa hakan yasa shi tsayawa abakin kofar yana  kallon abunda yai matuƙar faranta ransa.


Hatta Taj da big guy murmushi ne ɗauke akan fuskokinsu, kamar waɗanda akai wa albishir da gidan Aljanna babu wanda basu burge ba acikin su, sun tausayawa rayuwar su, ga wani irin son yaran da kaunar su da ya mamaye zuciyoyin su.



Ummin america dake ta kallon su, idanunta sun yi jawur saboda kukan da tasha, dama ba ta jima da gama yin shi ba, gaba ɗaya idanunsu na akan prisoners dake ta tsalle tsallen farin ciki a tsakar falon suka rurruƙe hannayen junansu tare da kewaye kawunansu suka haɗasu guri guda gwanin ban sha'awa yadda kasan fararen furanni a garden tsabar kyan da sukayi.....


Cikin Harshen Larabci sheikm Imam Ya fara karanto masu addu'o'i yayin da yake ƙarasa shiga cikin falon gaba ɗaya hankali ya dawo kan shi, da sauri suka raba kawunansu tare da ɗaga hannayensu sama suna amsa mashi da ameen ameen, mutun ɗayane baya amsa addu'ar sheikh imam  wato Danish, har Yanzu bai matsa daga gefen Salsabeel ba.



Bayan ya gama jera masu addu'o'in kowan nan su Ya shafa akan fuskarsa.


Kafin su sauke hannayen su, sautin takalman mutanan da ke shigowa falon taja hankalin su ga duban su


Chefs din dake girka abincin gidan ne suka shigo hannayen su ruƙe da ƙaton Cake stand mai hawa bakwai an ƙawata shi yayi matuƙar jan hankulan su.


Bayan sun sauke masu cake din akan glass table, ba su tafi ba, tsayawa sukai don ayi shagalin da su.


Cikin harshen turanci ɗaya daga cikin chef din yace"muna tayaku murnar haɗuwa da ƴan uwanku, kuma muna tayaku murnar samun ƴan ci arayuwar ku, sannan muna yi maku fatan Allah ya dawwamar da farin ciki arayuwarku"  gaba ɗaya suka haɗa baki wurin yi masu godiya.



"Bismillah, wannan na ku ne, chief ne Ya bada Umarnin A haɗa maku Cake, saboda ku ji daɗin yin shagalin murnar ganin yan uwanku" ɗaya daga cikin chefs dinne Ya faɗa, bayin Allah saboda farin ciki hawaye ne suka cicciko idanunsu waɗanda suka kumbura saboda kukan da suka sha.


Hannayen su ruƙe cikin na juna suka kewaye Cake din, Lokaci ɗaya wani abu ya faɗo masu aransu wanda ba komai bane face farkon zuwan Sabbin prisoners gidan kurkukun ƙaddara, ba zasu ta6a mantawa da lokacin ba har abada, ranar da giants suka kawo masu cake sunata murnar yanka shi  akarshe majnoon yayi ajalin shi.


 cikin shessheƙar kuka jemimah tace"Genie Ina majnoon ɗina? shi bai dawo ba? Yakamata shima Yazo tun da su deeja ma da suka mutu sun tashi"


 kumatunta jawur tayi maganar, gaba ɗaya ta karya masu zuciyoyin su.


"Jemimah wanda ya mutu ba ya dawowa sai dai idan dama kwanansa ne ba su ƙare ba, Majnoob Ya mutu ba zai ta6a dawowa awannan duniyar ba, amma in sha Allah zamu haɗu da shi agidan aljanna" yayin da Unaisah take yin maganar bakomai take tunawa ba face fuskar majnoon da unaizah, hakika ba zasu ta6a mantawa da farkon zuwanta gidan kurkukun ƙaddara ba, lokacin da ta sauko kan stairs cikin shiga ta school uniform red colour, ƴar gayu da ita wayayya ta goya back dinta abayanta.


muryarta ce ta soma yi ma unaisah gizo a kunnanta.


_Hi, Am unaizah ƴar gidan daddy, can i know u_


_that's Impossible, ae ni bana sharing soson wanka, Kuma bana wanka in ba a cikin bathtub ba, I can't stay here i wanna go home, cos daddy ba haka Ya kwatanta min school ɗin ba, Yace min fa komai irin na Gidan mu ne, but why naga banbanci_


Runtse ido unaisah tayi yayin da take jin wani irin kewarta a zuciyarta, tayi fatan ace gaba ɗayansu ne suka rayu sai dai kash Allah baya barin wani dan wani yaji dadi.


Siraran hawaye ne suka wanke fuskar Sajeed tunawa da yar uwarsa Gabriella wadda a halin Yanzu ba shi da tabbacin tana araye kota mutu, lokaci ɗaya sautin muryarta ya soma cika kunnuwansa farkon kasancewarsu agidan kurkukun ƙaddara lokacin da za'a raba su da junansu tana kuka tace


_ My twin bro, Ka kula min da kan ka, Duk inda za'a kai ni zan dawo wurin ka_


Kowa da abun da yake tunawa aran shi, ganin jimamin nasu bame ƙarewa bane yasa sheikh Imam Yi masu nasiha mai ratsa zuciya, ya dinga jawo masu ayoyin kur'ani Yana fassara masu har saida yaga sun samun nutsuwa tukunna Ya dakata...


"Waye zai fara Yanka mana cake din"? boss ne ya faɗa yana kallon su don jin za6in su, Har suna hada baki wurin furta"Unaisah" 

 

Idanunta amarairaice ta kalli faces din yan uwanta kafin ta sanya yatsun hannunta dake kerma ta dauki ƙaramar wuƙa, har taj ya yunkura zai ruƙo hannunta don ya taimaka mata ganin hannun ta na kerma, tunawa da danish yasa shi fasawa don har yanzu bayanshi bai daina yi mashi zogi ba.


A hankali ta yanko cake din tare da ɗagowa tana kallon su idanunsu duk suna akanta, tama rasa wa zata fara bama cake din duk da akwai wanda zuciyarta ta aminta da cancantarsa, satar kallonsa tai nan take idanunsu suka shiga cikin na juna,


"Angel ki ba danish, shi Ya cancanta ki bamawa," muryoyinsu sajeed ne suka cika kunnuwanta.


kau da ido tayi daga kan danish ta kalli daddynta, Lumshe mata idanunsa yai alamar ya amince mata.

Murmushi ta ɗan saki har dimples dinta suka lotsa, matsawa tayi kusa da danish, ta miƙa masa cake din ya buɗe ƙaramin bakinsa ta sanya masa, gaba daya suka soma tafa masu, Bayan ta ƙara cirar wani cake din ta miƙa ma daddyn ta Yaci.


daga bisa ni ta miƙa ma Haris Wuƙar, Ya kar6a Ya datsi cake din ya sanya wa deeja abaki, wani irin farin cikine Ya lullu6e su


Bayan ta gama taune na bakinta, ya bata wukar don ta bashi, abunka game tabin hankali, maimakon ta kar6i wuƙar sai ta sanya hannu ta 6allo ƙato ta duma masa abaki har cikin hancinsa ya shiga, gaba ɗaya suka sanya dariya, cike da nishadi.


Kar6ar wukar batool tai, ta ballo cake din ta ba mubeen Abaki Yaci, Kafin Ta sake gutsuro wani ta miƙa ma Rubina itama taci, ɗaya bayan ɗaya duk sai da suka ciyar da junan su cake din.


Tunawa da aunty umminsu dake ta kallon su, yasa batool ta sake kar6ar wukar daga hannun Sarah, ta yanko cake din taje gaban ummi ta miƙa mata, murmushi tasaki tare da ruƙo hannun batool ta tura shi abaki tana taunarsa ɗagowar da zatayi kwatsam suka haɗa ido da sheikh iman dake ta satar kallon ta, duk sai taji jikinta yayi mugun yin sanyi, tuni taji wasu hawayen sun cika idanunta, muryarta na rawa tace da batool"ba ki ba sheikh imam cake din ba" tana fadin hakan tai saurin juyawa ta nufi hanyar komawa bedroom dinta, sam yakasa janye idanunsa daga kallon ta hatta su taj sai da suka lura da kallon ummi da yakeyi sai dai basu kawo komai aran su ba.


Jiki asanyaye Batool ta ƙara yanka wani cake din taje gaban sheikh Imam Ta miƙa mashi, sai da Ya fara ɗaura tafin hannunsa akanta ya ɗan shafa shi ya furta"Allah yayi maki albarka" kafin Ya buɗe baki ta saka mashi cake din'


Murmushi kowan nan su Yasaki gwanin ban sha'awa.


Da zolaya big guy yace"yau an nuna min wariyar launin fata, Ni babu mai bani cake din"?


da sauri sajeed yace zan baka, girgiza kai yayi"I'm sorry Ni mace nakeso ta bani ba jin sina ba" dariya suka sanya gaba dayan su.


Harara boss yadan jefa masa cikin muryar raɗa Yace"kai bana son iya shege fa, halan tazurancin naka ne Ya motsa" ƴar dariya yai har hakoransa suka bayyana.


"Ni zan baka cake din" jemimah ce tayi maganar, da karfin hali fuskarta sharkaf da hawaye, gaba ɗaya suka sanya dariya, 

matsawa big guy yai tare da kai hannu ya dauki Jemimah, kafin Ya bata wukar Ta yanka ta bashi abaki, shima ya karbi wukar ya 6allo cake din Ya sanya mata abaki.

Sautin tafin su Ya cika falon, wunin ranar shagali sukayi babu kakkautawa yadda kasan gidan biki.



_______________________________✍️



Safa da marwa takeyi a tsakar dakin ta, fuskarta dauke da tsantsar farin ciki, gaba daya ta shagala da tunanin Yar ta Angel sam ta manta da zancen tafiyar su, zumuɗi Ya hana ta zauna jira take Aneelerh ta tura mata da hotunansu duk tabi ta kosa da son ganin fuskarta


Jin ƙarar shigowar sakonni ta whatsapp din da ta buɗe ne, yasa tai saurin duba screen din wayar dake ruke a hannunta, wayyo Allah dadi, tsabar zumudin ta buɗe sakon Aneelerh yatsun hannunta har kerma sukeyi, lokacin da ta ɗaura idanunta akan hoton Unaisah ƙafafuwanta kasa ɗaukarta sukai, awani slow ta koma gefen gado ta zauna hannunta ɗaya dafe da bakinta take kallon hotunan Unaisah, yayin da zuciyarta ke harbawa da karfi da karfi tun da take a duniyar nan bata ta6a jin son wani ɗan adam  fiye da yadda takeson ƴarta, duk da basu taba haduwa ba amma taji wani irin mahaukacin son yarinyar na ƙara shigar zuciyarta.


Hotunan da Aneeleeh ta turo mata na unaisah tun tana jaririyarta nannaɗe cikin farin towel, hada hotunan Birthday dinta lokacin ta cika shekara goma aduniya, sunyi kyau hotunan kamar lu'u lu'u


Wani irin sanyine Ya ratsa zuciyar benazir, a kalla ta shafe mintuna tana kallon hotunanta, kafin ta buɗe na baby junaid din Aneeleeh, Murmushi tasaki tana kallon kyakkyawan yaron kamar sabon fure ya kwanta mata aranta, Bakomaine Ya faɗo mata aranta ba face Fatimar yaya shureim ita kadaice babu acikin su


A hankali ta furta"Allah sarki Aisha ke kadai ce babu jinin ki araye, mun yi babban rashi, Allah yajiƙan fatima Allah Yasa mai ceto ce....." idanunta cike tab da kwalla tayi maganar.



"Benazir zaman me kike yi"? Rass taji gabanta ya fadi jin muryar hajiya layla, a hanzarce ta dago tana duban kofar shigowa dakin, Hannunta ruke da trolley din kayanta, fuskarta babu fara'a sai faman huci take yi, Shigowa dr shureim yayi da sauri yana kokarin shawo kanta"mommy dan Allah ki yi hakuri ki fasa tafiyar nan, kinga daddy bai amince maki ba, Yakamata kibi umarninsa ko dan gujewa fushin ubangiji...." harara ta watsa mashi tana fadin"shureim zan 6ata maka rai wallahi, Idan kai bazaka bi ni ba to ka ƙyale ni in kama gabana, har yaushe ne zan cigaba da zama ana raina min wayau agidan nan? nafa san me nake yi, ni ba shashasha bace..." mai da dubanta tayi ga benazir wadda tuni ta miƙe tsaye damuwa ce tsantsa akan fuskarta.


"Wuce mu tafi, Idan kema ba zaki bi ni ba, to ki zauna tare da su" ta fada rai a6ace.


Cikin sanyin murya Benazir tace"mommy ki yi hakuri dan Allah, kinsan bazan ƙi bi umarninki ba amma bazan iya tafiya ba...." baki asake Layla ke kallon ta.


"Nima ba son zama gidan nakeyi ba, Aneeelerh ce ta kira ni awaya, kiran da muke ta jira, sai yau Allah Ya nufa, dan Allah mami kibarni in hadu da ita inyaso daga baya sai mu tafi"


Girgiza kai hajiya layla tayi"kawai kizo mu tafi, in mun fita zamu fara biyawa gidan su Aneelerhn kafin mu tafi" da ƙarfin hali tai maganar, ita kanta tana jin fargaban zuwa gidansu aneelerh saboda bata so Benazir ta gane karyar da tayi mata nacewa su taj sun bar kasar amma a halin yanzu idanunta sun makance burinta su bar gidan duk abun da zai faru ya faru.


Gyada kai Dr shureim yayi"ki bita ku tafi, Allah Ya kiyaye hanya, Ni zan jira daddy"


Tsoki layla taja, tare da juyawa ta nufi kofar fita daga dakin, da sauri benazir ta dauko mayafi, dr shureim ne ya janyo mata trolley din kayanta, lokacin da suka fito falon gidan, yayi dai dai da fitowar su Hajiya sarah da gudu zeenatu ta nufi benazir tana kuka ta ruƙe mayafinta.


"Aunty benazir kada ki tafi kibarni, dan Allah kada ki tafi, Mami Dan Allah ku yi hakuri ku zauna, Idan wani abu mukai muku badaidai ba zamu gyara, Ni dai banso ku tafi"


 "zeenatu zonan"! Muryar Alhaji musace ta katse mata koke koken nata, jiki ba kwari ta saki mayafin benazir ta koma wurin shi ta tsaya, ruƙe hannunta yai acikin nashi, Hajiya sarah kamar an rufe mata baki takasa ta6uka komai sai kallon su da take yi, dakatawa sukai da yin tafiya jin muryar Alhaji ubaid


"Wallahi idan kika sa kafa kika bar gidan nan batare da yawuna ba, to ki sani abakin auran ki"!! hankulansu Dr shureim atashe suke kallon shi har suna hada baki wurin furta daddy meyasa?


Dariyar takaici layla tasaki tana tafa hannu tace"sai me donka sake ni? Ni dama ay najima da gajiya dakai tun lokacin da na gane kai bakomai bane face rakumi da akala, Ina amfanin zama da namiji solo6iyo irin ka"? 


Rai a6ace ta faɗa tana kallon cikin idon shi, Kalamanta sun ƙona masa rai, daƙyar Ya iya hadiye yawu mai ɗaci ba tare da ya iya furta komai ba.


Dauke idonta tayi daga kanshi ta kalli Alhaji musa, dake atsaye ya harɗe hannuwansa kan kirjinsa fuskarsa babu fara'a


Harara ta watsa mashi kafin tace 


"Hankalinka Ya kwanta Ka shiga tsakanina da mijina, In sha Allah zaka ga sakayyar hakan" wani kallon ƙasan ido Ya watsa mata mai wuyar fassaruwa.


"Shureim Benazir, kada ku bi ta idan har na isa daku, Kubarta ta tafi ita kadai tun da bata jin maganata" acewar Alhaji ubaid.


Murmushin takaici layla tasaki, ba tare da ta ƙara furta kalma ba ta juya a fusace tabar falon


"Ka bar su su tafi" Alhaji musa ne ya fada agadarance.


Da sauri benazir taja trolley dinta tabi mommynta, shima shureim yabi bayanta


A bakin motar shureim ta tsaya zuciyarta a kuntace, batai tsammanin zasu biyo bayanta ba


Dr shureim na ƙarasowa Ya buɗe mata back seat din motar ta shiga ciki, sannan ya sanya masu trolley din kayan su a boot, daga bisani itama benazir ta shiga ciki.


Bayan ya shiga ya zauna a driver's seat, yai ma motar key, zuciyarsa cike fal da damuwar abunda Ya faru, yaji takaicin yadda Alhaji musa ya nuna halin ko'in kula akan tafiyar mamin su, abun da Yafi bata masa rai furucin mahaifinsu yansu shikenan yana ji yana gani auran iyayensu zai rabu"? 


"Shureim! Ya akai naga ka dakata da yin driving din"? Cikin rauni na murya yace"mommy  Kiyi hakuri mu koma, idan kika tafi ya kike so muyi da rayuwarmu? Ke kanki bazaki so abun da zai tarwatsa farin cikin mu ba...."


Shiru tayi tana nazarin maganarshi, ga dukkan alamu jikinta yayi sanyi lakwas


"Mommy, kina atare damu Ya muka ƙare inaga idan baki nan? Duk wani mai nufin mu da sharri zaiji dadin cutar da rayuwarmu, bayan haka mommy tsawon shekara nawa kuna atare da daddy, auren soyayya kukayi kun tara zuri"a da dadi da ba da daɗi kunyi hakuri kun jure zama da juna sai akan wannan dalilin zaki kashe auranki? Mu kanmu bazamu ji dadi ba dan Allah ki tausaya mana mommy ku dubi girman Allah ki fasa tafiyar nan ko dan saboda mu"


benazir ce tayi maganar tana duban fuskar mami kamar zata sanya mata kuka.


Zancen zuci ta soma yi 


_wannan hanyar dana ɗaukarwa kaina ba me 6ullewa ba ce, ƙwara in tsaya in ƙwatar mana ƴancin mu, dole Inyi faɗa ko da kuwa zan rasa raina ne saina shiga tsakanin mu da shi_


Ba zato ba tsammani suka ga ta buɗe  motar, wani irin farin ciki ne Ya lullu6e su, da sauri benazir ta fito shima shureim Ya fito suka dauko trolley dinsu dake a boot suka bi bayanta.


Kamar yadda suka bar su hajiya sarah tsaye a falon haka suka taras da su, sunyi mamakin dawowar Hajiya layla, ko kallo ba su isheta ba, Kai tsaye ta wuce room dinta


Da gudu zeenatu ta  nufi benazir suka rungume juna suna dariyar farin ciki,


Fuskar hajiya sarah dauke da murmushi  ta dubi dr shureim"ta fasa tafiyar ne"?


"Eh mommy," ya bata amsa, Har cikin ranta taji dadin dawowarsu.


Mutumin kuwa murmushin gefen fuska Ya ɗan saki, yayi tunanin security officers din gidanne suka hanata tafiya baisan cewa itace tai ra'ayin kanta ba, fucewa yai daga falon cikin takun isa.


Alhaji ubaid dake kallonsu ajiyar zuciya ya sauke.


"Daddy, dan Allah kuyi hakuri da abunda Ya faru atsakaninka da mommy, ku yi kokari ku sasanta junanku" 


Jinjina kanshi yai fuskarshi dauke da murmushi yace"kada ka damu shureim, ni dama ban dauka da zafi ba, itace ke da matsalar, in sha Allah zanje na lallashe ta" ya fada tare dakai hannu yadan bubbuga kafadarsa kafin Ya juya ya nufi dakin layla don su sasanta junan su. 


Koda ya shiga ɗakin, ya taras da ita zaune  agefen gado, kamar mai jin shakkarta Ya raba ya zauna yana duban ta


kafin yai magana tai saurin katse shi da cewa"basai ka bani hakuri ba, ni yakamata na nemi yafiyarka, ka yi haƙuri idan na 6ata maka rai, in sha Allah bazan ƙara ba, zan bi umarninka in zauna har zuwa lokacin da ka so mubar gidan" da wani irin mamaki yake duban fuskarta, kamar amafarki yake jin kalamanta, Wai yau layla ce da kanta take bashi hakuri har take fadin  zata bi umarnin shi?



"Allah yasa ba mafarki nakeyi ba" murmushi tayi tare da dubanshi tace"ba mafarki bane mijina, dagaske ne, abun nayi ban kyauta ba, su shureim sun yi min nasiha nima naga rashin kyautuwar hakan shiyasa na dawo.


Ruko hannayenta yai acikin nashi hawaye tuni sun cika idanunsa


Cikin sanyin murya yace"layla bazan iya misalta dadin da naji ba, kin faranta raina ayau, duk da nasan nine mai laifi amma kiyi hakuri ki yafe min, sannan inaso ki sanyani a addu'arki,  Ni kaina bansan meyasa bana iya bijirema umarninsa ba, bana son bacin ran musa, saboda ya kyautatamin arayuwa shine silar duk wata nasara da na samu..." bai kare maganar ba tai saurin rufe bakinsa da tafin hannunta, saboda ta tsani taji Yana yabon musa, saboda ita tasan ba hakanan Ya kyale shi ba shiyasa baya iya ganin laifinsa, amma taci alwashin zata gano ainihin wanene Alhaji musa da duk wani abu dayake takama da shi.


Abun da bai ta6a tsammani ba, Yaji layla ta kwanto da kanshi saman kafadarta, bawan Allah sai Ya kara lafe mata kamar wani karamin yaro.


"Kada ka damu, ni bakai min laifin komai ba, In sha Allah zantayaka da addu'a kamar yadda ka bukata, kaima kuma inaso ka dage dayiwa kanka addu'a" amsa mata yai da toh, cigaba da kwantar masa da hankali tayi, har saida ta cika shi da farin ciki ta dinga zolayarsa tana tuna masa farkon haduwarsu kafin su yi aure.



"Yanzu tun da komai Ya daidaita mu koma dining mu ƙarasa yin breakfast din" cikin kulawa mom sarah tayi maganar tana dubansu.


"Aunty ki tayani murna" acewer benazir


"Fada min meya faru"?


"Aneelerh ta kirani awaya har mun yi magana da ita"


Murmushi hajiya sarah tasaki"masha Allah, ina tayaki murna my daughter, wlh naji dadi yanzu yaushe zaki je can gidan na su"?


Kallon dr shureim tayi wanda gaba daya hankalinsa na akan zeenatu dake a gefensa sai dadi take ji sun fasa tafiya.


"Yaya shureim yaushe zamuje? Ni ko yanzu ma kace a shirye nake Allah" ta fada a kagare.


"Gobe in sha Allah zan kai ki" da sauri zeenatu tace"yaya shureim nima zan bi ku, dan Allah ku tafi dani" ta faɗa a shagwa6e tana kallon shi.


"Kada ki damu ƙafa ta kafarki, duk in da zani je a tare zamu tafi" cikin muryar raɗa yayi mata maganar, dariya murna tasaki.


Benazar tace"kwantar da hankalinki rabin raina, gobe atare zamu je"

"Nagode auntyna"


"Ki daina murna, kin manta da daddyn ki halan, ba lallai ya amince ki fita ba" tur6une fuska tai.


"Mommy pls ki roƙan mun shi yabar ni inje" ta fada tana bubbuga kafafuwanta


"Zanyi mashi magana zuwa anjima nasan zai bari mu tafi da ita" acewar dr shureim

Hajiya sarah na murmushi tace"kunfi kusa ay, nasan kana masa magana zai amince, tun da yana ji dakai na gaban goshinsa" dariya sukai gaba dayan su.


______________________Twins❣



A kwance yake kan katafaren gadonsu idanunsa na fuskantar ceilling, yanayin fuskarsa sam babu walwala ya haɗe rai kamar wanda aka aiko ma sakon mutuwarsa, bakomai ne yake damunsa ba face haɗin da mommynsa tayi masa, ya riga da ya san halinta ba lallai ta canza ra'ayin ta ba, shi fa arayuwarshi sam baida ra'ayin yin auren wuri, yafi sha'awar yai sharholiyarsa son ransa, a yadda ya tsara ma kansa sai yakai 45 years zaiyi aure, bugu da ƙari baya jin zai iya auran yarinyar saboda ba'ajinsa ba ce, jiya kafin ya kwanta bacci sai da yayi bincike akanta ta hanyar amfani da wayarsa har ya gano wanene mahaifinta wato karen ƴan siyasa, aransa ya ayyana tayaya shi da ya fito daga babban gida shahararren family da duniya tasan da zamansa, zai auri wannan yarinyar, Bayan haka mommyn sa minister ce daddynsa Ceo ne na babban companynsu Obi Tech, tayaya zai auri interior designer? Companyn ma da take aiki ba nata ba....


Abu ɗaya daya hana shi sukuni, kyawun fuskarta da surar jikin ta, daren jiya dakyar ya runtsa, ba halin Ya rufe idanunsa sai ya tuna lokacin da ta fashe mashi kuka la66anta na kerma, kissing ɗinta da yayi har cikin zuciyarsa yaji wani irin shauƙi da bai ta6a jin sa a wajen wata mace ba, kawai yayi ƙarfin halin tofar da yawu ne don Ya muzanta ta.


Motsin buɗe toilet ne Ya katse masa zancen zucin nasa, A hankali yakai idanunsa ga duban mai fitowa


Zaid ne ya fito waist dinsa daure da towel, suna haɗa ido da juna Ya sakar masa murmushi


"Bro me kake tunani ne? kamar wani abu na damunka? Banza yayi dashi bai tanka mashi ba


"Faɗamin meya faru jiya bayan mommy ta kira ka awaya"


Yamutsa fuska yayi, tamkar baisan maganar ya furta"zaka iya tuna yarinyar nan da mommy ta kawo wurin mu"? 


Shiru zaid yayi yana kokarin tuna ta can yai murmushi tare da cewa"kana nufin Zahra"? Ta6e baki zayn yai kafin yace"oho na manta sunanta"


"Itace zahra, yarinyar ta kwanta min araina saboda ina son mace mai kamun kai daga gani iyayen ta sun bata tarbiya" ya faɗa tare da samun wuri gefen gadon su Ya zauna yana kallon zayn


"Mommy ce ta haɗa ni da ita...." bai 6oye masa komai daga abun da ya faru tsakaninsa da zahra.


Har Ya ƙare maganarsa zaid bai ankara ba saboda zuciyarsa da ta karaya, har ga Allah bai ji dadin hukuncin da mommynsu ta yanke ba na hada zayn da zahra, saboda yasan halin ɗan uwan nasa bai jin magana fiye da shi, yarinya mai kamin kai an haɗa ta da ɗan iska, ina ma ace shi mommynsu ta hada da zahra da ba abun da zai hana ya gyara rayuwarsa saboda samun mace ta gari wadda zuciyarsa ke muradin mallaka...


"Zaid? Naji kayi shiru bakace komai ba? Nasan kana tayani jimami ne"


Jinjina kai zaid yai kafin yace"zayn banji dadin abun da kayi mata ba, saboda ba laifinta bane, mommy ce ta hada ta dakai,  ni nasan ba itace ta shirya faruwar hakan ba..." ya fada cikin sanyin murya yana kallon zayn dake faman ya mutsa masa fuska


"Me zai hana ka jaraba amincewa da buƙatar mommy, ni nayi imanin ba zaka ta6a danasanin auran zahra ba, watakil ta zama silar shiriyarka...." kafin ya ƙare maganar zayn ya wurga masa harara tare da katse sa da cewa"kana son ta ne? 


"Meya kawo maganar so? Kawai daga na baka shawara amatsayinka na dan uwana" guntun tsoki zayn yaja"bani buƙatar shawarar ka, nayi zaton  zaka tayani jimamin abun takaicin daya same ni ashe ba haka bane dakai da mommy kanku ɗaya..." ya fada yana cije la66ansa"har abada bazan ta6a sonta ba, zan amince da ita ne saboda mommy, sannan zan aureta badan ina sonta ba sai don in mayar da ita abun biyan buƙata na amma babu maganar mutunci atsakaninmu muddin ta aure ni taga ma jin dadin zaman duniyar nan"  muryarsa a kausashe ya furta maganar


Runtse ido zaid yai har cikin ranshi baiji dadin kalaman zayn ba, baisan ya zaiyi ya shawo kan mommynsu akan ta janye maganar haɗa shi da zahra saboda zayn ba mutumin kirki bane, muddin ya auri zahra bakin cikinsa zaiyi silar mutuwarta, dole ya nema mata mafita tunkafin afkuwar lamarin, Indai daddyn su baisan da maganar ba zaiyi kokarin tunzurasa akan kada ya amince da maganar mommynsa....Saukowa zayn yai daga kan gado daga shi sai yar singlet da short Ya nufi toilet Yana huci Ya shige ciki, zaid dake zaune gaba daya kamar an zare lakarsa shi dai ya damu da zahra baya son mommynsu tayi silar jefa ta cikin wani hali 


wayar dake a kan side drawer din su, Yakai hannu ya dauka Ya danna wa landline din kitchen tana fara ringing maid ta ɗauka, ya bada umarnin akawo masu breakfast dinsu, Kafin Yai cutting kiran ya ajiye wayar kan drawer


Badajimawa ba, Abla ta shigo dakin da tray mai dauke da kayan abinci, ta ajiye masu kan drawer bayan ta gaishe da zaid ta juya ta fuce..


________________________Dattijon Arziƙi🤍


A zaune yake kan lallausar darduma, hannunsa ruƙe da cazbaha, a hankali Yake motsa la66ansa, kusan rabi da kwata na hankalinsa na akan chief owais dake kwance saman dardumar ya ɗaura head ɗinsa akan laps din baba obie, kyawawan idanunsa suna a lumshe tamkar na mai jin bacci, su duka biyun daga ka kalle su zaka shaida tsantsar nishadin da suke aciki, musamman baba obie, ransa fari fat tunda owais ya kawo mashi ziraya yau kusan wuni yayi awurinsa duk inda zasuje atare suke tafiya, ba su jima da dawo daga masallaci ba suka shigo garden don su sha iska, sai faman satar kallonsa yakeyi kamar ya haɗiyesa haka yake ji tsabar kaunarsa da ya ke ji.


"Grandpa, wannan kallon na menene"? Idanunsa a lumshe Ya jefa mashi tambayar.


Fuskar baba obie da fara'a Yace"Kallon so da kauna ne rabin raina, wallahi yau ka faranta min rai, gaba daya ka debe min kewar hateem dake damuna...." A hankali chief Ya ɗan bude idanunsa Ya saci kallon fuskar baba obie karaf suka hada ido cikin na juna

"Baba...." Ya fada ba tare da ya ƙarasa maganar ba

"Na'am sanyin idaniyata, Naji ka kira sunana kuma ka yi shiru" gyara kwanciyarsa yayi batare daya bashi amsar tambayar sa ba.


"Duk cikin jikokina babu wanda Ya more ni kamar ka, kaga cinyar nan tawa tun kana ƙarami kake tumurmusarta, gashi har yanzu baka daina taushe min ita ba' murmushin gefen fuska Chief yai masa har chin dimple dinsa Ya dan lotsa.


"Meya fi raina"? Ya fada Yana kallon fuskarsa.


"Ni fa idan ina atare dakai, sai naii kamar an mallaka min komai na duniyar nan, ni dai Allah Ya jarabce ni da sonka kakana ina fata Allah ya dawwamar da farin ciki atsakanin mu zan cigaba da tayamu addu'a Allah Ya  Ya ƙara mana tsawaicin kwana ko dan na cika maka burinka akaina......."


 tun da yafara magana baba obie ke kallon shi da wani irin matsanancin farin ciki akan fuskarsa, dakatawa yayi da jan cazbahar Ya ɗaura tafin hannunsa kan sumar Owais a tsanake Ya soma shafata kamar yana yi masa susa.


"Kalamanka sun sanyaya min zuciyata, Owais kai na dabbanne, wallahi yadda nake jinka bana jin ko iyayanka, kai tamkar bugun zuciyana ne, wallahi bansan Yadda zan misalta maka kaunarka da nake yi ba....." kafin Ya ƙare maganar, ruwan hawayen da suka taru cikin idanunsa suka gangaro kan fuskar chief, lokacin da yaji saukar su a ruɗe Ya zabura ya mike daga kwancen da Yake, Idanunsa akan fuskar baba obie

da alamun ruɗani Ya furta"baba meyasa ka zubar da hawayen ka? shiru yayi batare daya iya furta masa wani abu 


"Fadamin mana, ko dai maganar da muke yi ce ko kuma akwai wani abu dake damunka"? Girgiza kai yai"a'a owais kada ka damu babu abun da ke damuna, kawai bana son duk wani abu da zai shiga tsakanina dakai, Ina jin fargaban duk wani abu da zaisa ka juya min baya, ni dai bana son 6acin ranka......' ruƙo hannayen baba obie yai acikin nasa yatsun hannunsa har kerma sukeyi"baba bazaka iya boye min komai ba, idan har kana da damuwa kallo ɗaya nake yi maka na fahimta, Ina ji araina da akwai wani abu dake damunka dan Allah ka fadamin habibi na, nayi alkawarin zanyi iyakar bakin kokarina wurin kawar maka da damuwarka...." da ƙwarin gwiwa ya furta maganar Yana kallon idanun baba obie da suka kada jawur gray eyes dinsa sunyi ja tsufansa duk Ya ƙara fitowa.


Wani murmushi yayi mai ta6a zuciya kafin yace"Idan na faɗa maka abun da ke damuna zaka 6oye min sirri na ba zaka fada ma kowa ba sannan zaka rufa min asiri" jinjina kai owais yai da alamun rudani akan fuskarsa

kamar baison furta maganar Yace"najima inason sanar dakai, sai dai inajin fargaban yadda zaka dauki abun aranka, ka yi min alkawarin ba zaka fusata ba" ya fada la66ansa na kerma, ba karamin rikita tunanin chief owais Yayi ba, gwiwarsa harta sage In a low voice Ya furta"ni mai rufa maka asiri ne babana, bazan bari kowa Ya sani ba, tona maka asiri tamkar tonawa kaina asirine da zuri'armu" jinjina kai baba obie yai sai da yafara kallon garden Din Ya tabbatar babu mai kallon su kafin Ya matsa gab da chief owais Yayi masa raɗa a kunnansa.


Lokaci ɗaya chief ya ɗan janye kunnansa da tsantsar mamaki Yake kallon baba obie wanda tuni yasha jinin jikinsa, ba zato ba tsammani a lokaci ɗaya suka tuntsire da dariya kamar wasu zautattu,  Yaushe rabon da inga chief yayi dariya irin wannan ni kaina namanta, komai nasa mai jan hankali ne.


dariyar tayi matuƙar tafiya da imanina, saboda gaba ɗaya ta bayyana zunzurutun kyan fuskarsa, dimpla dinsa duk sun lotsa, fararen hakoransa kamar auduga tsabar hasken su, sun ɗau lokaci suna tiƙar dariya kafin daga bisani chief ya kifa kansa bisa kafadar baba obie, hankalinsa ba karamin kwanciya yayi ba, da farkon yai tsammanin wani mugun abunne  zai faɗa masa ashe ba haka bane

Muryarsa tamkar tame jin bacci Ya furta"Grandpa are you kidding me"?


Baba obie na murmushi yace"Wasa nake maka owais, Ni ina ni inayin aure, tsofe tsofe dani, ga tarin ya'ya da jikoki"


"Wannan ba hujja bace, Indai Kana son Yin auren ka fadamin, in sha Allah  I will try to find a righteous life partner for you."


Da zolaya baba obie yai masa dundu akan bayansa tare da cewa"Owais wlh wasa nake maka, kawai don inga reaction dinka ne, kuma nagani tunda gayanan na sanya ka yin dariyar da ka dade baka yi taba"



Sauke ajiyar zuciya chief yai kafin ya sake furta"please ko da nan gaba kaji kana bukatar abokiyar rayuwa ka sanar dani, zan goyi bayanka kuma zan nema maka dattijuwa dai dai da kai" dariya baba obie yayi "Allah ya kiyaye In auri tsohuwa, Haba owais Ina laifin Yar sha takwas mai jini a jika, wadda zata sangarta ni, kasan mu tsoffi munfison adinga tarairayarmu kamar irin new born baby, Yanzu ni owais idan na auri dattijuwa kamana me zata min"? da mamaki chief  ya ɗago yana kallonsa kai kace ba daga bakinsa kalaman suke fitowa ba.


Kafin Ya bashi amsar maganarsa, Wayar baba obie Ta fara ringing, da sauri ya zarota daga aljihu tare da picking call in ya kara a kunnansa.


Chief owais sai kallonsa Yake yi har yau yana mamakin tsufan kakan nasa, kwata kwata babu rudin tsufa atare da shi, yana da karfi ga kaifin basira, idanunsa kuwa kona matashi albarka saboda yadda yake gani da su ko bai sanya glass ba, harta sandar da yake rukewa ta gayu ce ba dan ya gaza taka kafarsa ba.


"Alhamdulillah Alhamdulillah, almost 3 time baba Obie Ya furta hakan, Hannunsa ɗaya dafe da saitin zuciyarsa alamar Yaji sanyi aransa.


"Ina fata kun sauka lafiya, Ubangiji Allah Ya huta gajiya, Ina ƴan jikokin nawa da surukar arzikin Ina fata duk suna lafiya"?  Ya tambaya yana sauraron muryar wanda suke magana da shi.


"Madallah, naji dadin jin hakan, Hateem ka kula min da kanka, tun da ka haura kabar kasar nan nake ta zullumi duk bayan yan mintina saina duba Onn news inga ko kun sauka lafiya don nasan sune nafarkon da zasu fara buga labarin yadda jirginku yayi landing sai gashi cikin ikon Allah Ka kirani...' yai maganar fuskarsa dauke da murmushi


"Muna atare da owais, watakil Ya manta wayarsa agidane, wuni yayi awurina yanzu haka muna a garden..."


 miƙa ma owais wayar yayi"uncle dinka ne ke son magana dakai, kar6i kuyi magana kai masa bangajia jirginsu Ya sauka lafiya...." 


da sauri chief Ya kar6i wayar tare da karata a kunnansa

"My uncle, Ykk Ina fata kun sauka lafiya"?

On the other hand muryar prime minister ta amsa da cewa Alhamdulillah Myson, tafiya tayi kyau yanzu haka Ina a bedroom dina dakyar na samu jama'a suka ƙyale ni"

"Sunyi kewarka ne, Kai dinne badai farin jini ba,

Yar dariya hateem yai kafin ya numfasa Yace"Ina yarona? tun ina a cikin jirgi nake ta tunaninsa, owais Yanzu haka da nake maka magana zazzabi nake ji a jikina saboda kewar sa, ina ta  kiran layi ka donka bani shi mu gaisa bana samu" dagowa yai ya saci kallon baba obie Ganin sun haɗa iso yasa shi saurin canza yare zuwa larabci saboda baison Yaji me zai furta.


"Uncle, zazza6i saboda shi"?


"Hmm ba zaka gane ba, dan Allah Ka hadani da shi"


Hankalinsa adan tashe Yace"pls uncle, ka daina sanya damuwa aranka, bana jin dadi, na manta wayana agida ne shiyasa baka same ni ba, amma in sha Allah idan na koma zan yi kokarin hada ka da shi ko hankalinka Ya kwanta amma kafin nan pls ka sha magani kada zaza6in yai yawa"


"Owais babu wani magani da zai warkar da zazza6in nan kawai ka hadani da shi, saboda shi kadaine warakana" baba obie dake kallon owais ya kura masa ido ba tare da ya fahimci me suke cewa ba.


"Okey uncle, zanyi abun da kake so"

"Nagode owais, and pls abashi kulawa ta musamman, bana so ya nemi wani abu ya rasa, na yarda dakai kuma nasan zaka Iya min abun da nake so" cikin girmamawa ya amsa masa da toh uncle.


Sun ɗan jima suna waya kafin sukai sallama Ya mika ma baba obie wayar, harara Ya galla masa"fadamin me kuke tattaunawa ne naji ka canza yare don kada naji ko"


Girgiza kai owais yayi"ba haka bane....." bai ƙare maganar ba, sallamar Hajjaty ta katse su, ba karamin dadi owais yaji ba saboda bay da amsar da zai ba baba obie akan tuhumarsa da Yakeyi


Tuni kamshin turarenta Ya gauraye hancinansu, Hannayenta ruke da tray ta shigo garden din, Tea set ne akan tray din tare da fresh fruit, bayan ta ajiye masu fuskarta da fara'a ta gaishe sa su,a mutunce suka amsa mata

"Idan kin shiga ciki, Ki sanar da mutanan gidan su prime minister sun sauka lafiya yanzu ya kirani awaya ya fadamin nasan ba lallai suji ba"

Murmushi tayi"in sha Allah zan sanar da su" ta fada tare da mikewa ta fuce daga garden


"Kana sonta ne? Naga kana kallon ta" muryar chief ce Ta ratsa kunnansa da sauri ya kau da idonsa daga kallon bayan hajjaty ya wurga masa hararar zolaya"dan Allah ka daina wannan maganar, kawai daga na kalle ta? Ta6e baki owais yayi batare dayace komai ba, Ya dauki Tea pot Ya tsiyaya masu  a cups, atare suka zauna suna sha gwanin ban sha'awa


___________________________________BossBature✍️



A6angaren Aneelerh wunin ranar da farin ciki tayi shi, babu wanda baisan da zancen bayyanar benazir ba, Harta su mami da abie sai da ta sanar da su, sunji dadi har addu'a sukai mata akan Allah ya ƙara tsareta daga sharrin wadanda sukai mata kurciya da kuma fatan Allah Yasa suma su Taj su bayyana kamar yadda benazir ta dawo.


Tun bayan da ta kammala sallar la'asar ta duƙufa tana kallon hotunan benazir da ta tura mata awaya, kamar yau tafara ganin ta, gaba daya zumudin son ganinta takeyi, akwai abubuwa da dama da take son taji daga gare ta, tana son tasan meya faru da ita bayan guduwarta? Sannan A wani hannu ta faɗa? Murmushi tasaki yayin da take yin zooming fuskar benazir tayi haske jawur ta ƙara jiki ta zama big mama..


"Ya Allah kamar Yadda Ka nuna min benazir da ranta da lafiyarta Ya Allah ka nuna min su Uzair haka, har Yanzu ban fidda rai da su ba, saboda Inaji araina suna araye, Ya Allah ka tsare min mijina da dan uwansa da angel dina aduk inda suke, Ya Allah Idan sun riga mu gidan gaskiya kajiƙansu ka gafarta masu alfarmar annabi muhammd SAW......"


 muryarta na rawa ta ƙare maganar saboda kukan daya ciyota.....


"Aunty Aneelerh" muryar zahrace ta katse mata kukan nata, da sauri ta sanya tafin hannu ta share hawayen don batason zahra taga kukan ta, hakan zai iya sanyata damuwa, murmushi ta kakaro akan fuskarta ta dago ta kalli zahra dake shigowa.


"Na'am Sisterna"


"Auntyna Ina ƙara tayaki Murna, Aunty benazir ta bayyana saura Angel dinmu in sha Allah itama zamu ganta, Ni nasan yau dakyar zaki iya runtsawa saboda zumudin haduwa da Aunty benazir" cike da nishadi zahra tayi maganar, tare da samun wuri gefen Aneelerh ta zauna tana dubanta.


"Nagode zahra, ki cigaba da tayani addu'a Allah Ya bayyana su uzair, bana jin zan ma Iya bacci adaren yau, in sha Allah zanyi nafilfili akan su..." ta fada tana ɗan yamutsa fuskarta dake a kunshe da damuwa.


"Lokacin da yayan benazir Ya fada min cewa kurciya akai mata har ta gudu tabar gida, wallahi bakomai ya fado min araina ba face 6acewar su taj, farat ɗaya aka neme su aka rasa, a tsakar dare, zahra baki tunanin suma kurciyar akayi ma su"? Idanunta Jawur ta jefa mata tambayar, shiru zahra tayi jimm alamar tana nazari kafin taɗan jinjina kai tace"nima nayi tunanin hakan, zai iya yiwuwa, amma kada mu dogara akan hakan tunda bamu da tabbaci"

"Kin fadi gaskiya zahra"

Shiru suka danyi na wani lokaci..


"Zahra, dazu muna cikin yin magana bamu ƙarasa ba abie Ya kira ni..." murmushi zahra tayi


"Ni ma sham na shafa'a...." labari ta fara bata na dinner din hateem tun daga farko har karshe ta dire mata.


Bakomai ne Ya tsaya ma Aneelerh arai ba face yarinyar da zahra ta bata labarin sun haɗu har sunyi hotuna.


"Ki nuna min hoton in gani" zumbur zahra ta mike tana fadin inna lillahi na manta wayar a hannun baby junaid tun ɗazu tana a wurinsa, Allah Yasa bai yi min barna ba" da sauri ta fuce daga dakin ta shiga neman baby junaid itace har dakin ummi da mamie duk baya a ciki, har falo bata gan shi ba, da sauri ta nufi dakin abie nan ma babu shi ta dawo ta shiga dakin uncle still ba junaid


Sai da ta gama shan wahalar nemansa har zata juya ta koma daki ta jiyo sautin muryarsa a kitchen shi da Ana suna magana.


"Kinga wannan itace Angel dina aunty zahra ce ta dauko min hotonta"


Adai dai lokacin zahra ta shiga kitchen din kafin Ana Ta kar6i wayar don taga hoton Angel din motsin shigowar zahra ya firgitar da junaid aruɗe Ya saki wayar ta kife kan floor, wani irin bugu zuciyar zahra tayi ba ita ba hatta Ana hankalin ta, sai da Ya tashi idanunsa azare suke kallon junaid wanda tuni yasha jinin jikin shi.


Muryarsa na rawa ya furta"aunty zahra bani bane, Ana ne ta kada miki waya...' yana magana yana girgiza kansa duk yabi ya rude, Jikinta na tsuma Ta nufi wayar ta dauko ta tare da juyo da ita, gaba ɗaya screen dinta ya tsastsage fatsa fatsa baka Iya ganin komai.....


Kamar ta fasa ihu haka Taji tsabar bacin rai, a fadace tace"junaid hankalinka Ya kwanta ko? Ka fasa min waya! daga abun arziki na baka ita don ka kalli hotuna"  ta fada tana zare masa ido fuskarta adaure tuni Ya ƙara firgita.


"Sister zahra kiyi hakuri shima bada son ransa hakan ta faru ba, kada ki tsorata shi" Ana ce ta fada cikin kwantar da murya.


Bata tsaya sauraronta ba, Ta ruko wuyan rigar junaid"don kaga ina maka wasa da dariya ko? Shiyasa har ka samu kwarin gwiwar fasa min phone, muje daki yau saika yaba ma aya zakinta ɗan rainin wayau, dallah jibarka ko kunya babu" la66ansa ya fara ta6ewa alamar zaiyi kuka"kar na kuskura naga hawaye a idonka, wayar wuta zan sa maka" shiru yayi can kuma ya fara mata magiya"bazan ƙara ba aunty zahra, dan Allah kada ki buge ni, na tufa Allah" kiris Ya rage ta fashe da dariya ganin yadda Ya tsorata kamar ta ta6a bugunsa Alhalin tun da ya taso babu wanda Ya ta6a bugunsa



Janshi tayi har zuwa bedroom dinta, Ta zaro wayar charger a jikin socket, kafin ta dawo gare shi da gudu ya fuce waje yana kuka, biyo shi tayi aguje tana kwala masa kira.


Bai nufi ko'ina ba sai dakin mommynsa Yana shiga Ya faɗa kan laps dinta Ya ƙanƙameta yana fadin"mommy kice ma aunty zahra kada ta bugeni, bana so..." duk yabi ya dabarbace, a rude Aneelerh ke kallon bayansa Jikinsa sai kerma yakeyi"fadamin kaida wanene"?


"Aunty kibarni da babyn nan, Allah Yau sai yaji ajikinsa, Har ni zai fasa ma screen din waya? daga abun arziki na bashi aronta don ya kalli hoton Unaisah shine zai fasa min phone"


"Amma banji dadi ba junaid, meyasa zakai mata haka? Ka kyauta abun da kaima aunty zahra"? Ba tare daya dago dakansa ba yace"tayi hakuri bajan ƙara ba, mommy ki siya mata wata wayar cikin kudina da nake tarawa a wurin ki" dariya sukayi gaba dayansu jin abun da Yace. 


"Aunty aneelerh yanzu ya zanyi? Ni takaicina hotunan da baki gani ba"

Mika mata hannu Aneelerh tayi muga wayar da sauri ta bata, duddubawa tayi kafin tace"zanyi magana da mahboob yakai maki ita wurin gyara, kada ki damu idan an dawo da ita sai ki nuna min hotunan" ajiyar zuciya zahra tadan sauke"shikenan amma duk da haka saina tsala masa wayar nan" ta fada tare da yunkurawa zata zane bayansa fashewa yayi da kuka yana fadin"aunty zahra kada ki bugeni, Allah Yana sama Yana kallon ki..."  dariya zahra tayi"kasan da hakan shine ka fasa min wayar"? Muryarsa da shesshekar kuka Yace"ay mommy zata canza maki wata cikin kudina" tuntsirewa tayi da dariya cike da zolaya tace"ban ta6a sanin kai matsoraci bane sai yau, ay ko daga yanzu tun da na gano lagwonka, da zarar kamin rashin ji zan zane maka baya da wayar cazana" maƙe mata kafaɗa yai, ba tare daya tanka mata



*HAJIYA ADAMA🤍*


A hankali tai parking motarta, fitowa tai cikin shiga ta lace, ta yafa mayafi kan kafadarta, fuskarta manne da farin glass, Shopping bags ta ɗauko a back seat na motar, kafin ta Nufi cikin gidan tana gab da zata shiga bedroom din su ta tsinkayi Muryar Uncle abdallah yana waya


"Kayi hakuri nasan ba haka mukai dakai ba, na saba alkawari amma ka dubi halin da nake aciki, lokaci ɗaya na rasa ɗana bayan haka na rasa ɗan yayana tare da yarsa, na rasa yayana da kakata kai kadaine zaka Iya taimakona a halin da nake a ciki, wlh ni zan iya maida maka adadin kudin dana kar6a a wurin ka saboda ka dawo mun da su indai suna araye na ƙwammace na ƙare rayuwata a talauci akan inci gaba da ganin damuwarta akan rashin haihuwa..." 


Muryarsa amarairaice yayi maganar kamar zaiyiwa mutun da suke yin wayar sujjada tsabar yadda yake lalla6a shi yana yi masa magiya 



Cak Ya tsaya da yin maganar ba tare daya ƙarasa ta ba, sakamakon kamshin turaren hajiya adama da hancinsa ya shaƙo masa, a hankali Yai rejecting call din yana kokarin dai daita nutsuwar shi


"Ba halin ki bane Yi min la6e,"! Taji Ya faɗi fuskarshi ba fara'a


Bata tanka mashi ba, har sai da ta ƙarasa gaban gado ta daura shopping bags din kafin ta juyo ta dube shi da alamun rudani akan fuskarta


"Gaskiya ka faɗa ba halina bane, amma wannan wayar da kayi yanzu ta ɗan ɗaure min kaina, dear wani kudi ne naji kana fadin zaka mayar adawo maka dasu idan suna araye!? Har kake fadin ka ƙwammace ka ƙare rayuwarka a talauci akan ganin damuwana na rashin haihuwa? Su wanene kake yin magana akan su?


da wani irin kallon tuhuma take duban shi.


Hannu Yasa yaɗan shafa keyar shi, daga ganin fuskarsa babu kwanciyar Hankali, tsufansa Ya ƙara bayyana musamman fuskarsa duk tayi tamoji tamoji.


Maimakon Ya bata amsar tambayarta sai cewa yai"Har Kin kammala siyayyar? 

Dame dame kika siyo mana ne" A waske Ya faɗa tare da nufar Shopping bags din da ta ajiye kan gado, Ya buɗe Yana dudduba kayan ciki.


Kamar sakarya Haka Ya barta a tsaye Tana kallon Ikon Allah.


"Hajiyata, Yunwa nake ji, pls Ki dafa min abunda zan dan ci"


gyaɗa kai tay aranta ta ayyana koma menene zan bincika duk da ba halina bane amma da buƙatar nasan dawa kake waya akan su wa kake magana


Cire mayafin tayi, ta daura sa kan gadon, Kafin Ta juya tana fadin"Sorry dear, nabarka da Yunwa, bansan lokaci Yaja har haka ba, bari naje kitchen na shirya mana abun da zamu ci"


Bayan fitarta daga dakin ajiyar zuciya ya sauke, kamar wanda Ya ku6uta daga hannun dogarawan sarki, kwantar da kansa yai kan pillow idanunsa sun kaɗa jawur bakomai Yake tariyowa ba face nasihar yayansa Malam Zaheer haƙiƙa yayi babban rashin da har abada bazai ta6a samun makancinsa ba


Agogon ɗakin Ya kalla kusan ƙarfe Biyar Na marece, lumshe idanunsa yayi zuciyarsa nayi masa wani irin radadi daga gani yana acikin matsananciyar damuwa, Muryoyin su Uzair ne suka fara yi masa gezau acikin kan shi bazai ta6a manta ranar da suka shigo ɗakinsa da zumuɗin sanar dashi sun samu matayen da zasu aura.


 "Kunyi shiru bakuce min komai ba"

"Taj ka fara fada masa" harara Taj Yai ma uzair ay kai yakamata ka faɗa masa ni kunyar shi nake ji Allah, acikin kunne sukeyin raɗar 


Murmushi Uncle abdallah yai sai yake ganin kamar komai A yanzu Yake faruwa.


"Mijin mace ɗaya, abincin Ka Yana jiran ka" kamar daga sama ya tsinkayi muryar Hajiya adama, da sauri Ya mike  Ya shiga toilet jim kadan Ya fito Ya nufi dinning din, A tsaye Ya same ta tana karasa jera masu abincin


Murmushi suka sakarma Juna"Bismillah, babyn Hajiya adama" atare suka zauna suna fuskantar Juna.


 "Sannu da kokari matar mutun ɗaya, nagode da kulawarki agare ni, Naji dadin girkin nan" ya fada Yana kokarin tura jallop rice din daya debo a spoon"Shiyasa nake alfahari dake saboda kin Iya girki"

Murmushi tasaki Jin Yabon da yai mata"nima ina alfahari dakai," shiru suka danyi kowa yana cin abincinsa can ya ƙara dagowa ya saci kallon fuskarta karaf suka hada ido duk saiya rasa sukuninsa

"Wai lafiya naga kamar wani abu na damunka"? 

Girgiza kai yai"ba wani abu, kawai ina tunanin ranar da zamu rabu" ras taji gabanta Ya fadi arude tace"Abdallah? Meya kawo maganar rabuwa? Anya kuwa kasan me Harshen Ka ya furta"?


Ya ɗan tsorata da ganin Yadda Ta ɗaga hankalin ta.


"Kaga In baka lafiya muje nakaika asibiti bawai ka kama Yi min sambatu ba"

 babu wasa akan fuskarta tayi maganar.

Cikin sanyin murya yace"kiyi hakuri hajiyata, Nima zolayarki nakeyi, maganar rabuwa da nayi kinsan akwai mutuwa ko kuma wata kaddarar ta rayuwa da zata iya sanyawa mu juyawa juna baya!


Harara ta galla masa, tuni idanunta sun ciko tab da ƙwalla mikewa tai da sauri tana fadin"banji dadin maganar nan ba, eh nasan mutuwa dole ce amma meye na kawo maganar rabuwa muna tsaka da cin abincin mu"? Ta jefa mashi tambayar hawaye nabin fuskarta shiru yayi sam ya rasa amsar da zai bata


"Na rasa uzair da taj, na rasa unaisah, haba kabarni inji da wannan radadin mana, akan me zaka tada min maganar rabuwa...." rai a6ace Ta bar dining din ta  nufi bedroom dinta


Da sauri Ya miƙe yabi bayanta jiki na rawa saboda baisan bacin ranta, lallashin ta Ya dinga yi kamar zai mata sujjada dakyar Ya samu ya shawo kanta har ta daina fushin da shi



*💘EX-PRISONERS❤*


Wuraren ƙarfe takwas na dare Gaba ɗayansu sun hallara A main falo din gidan yadda kasan gidan biki ko suna, sai surutu sukeyi suna yin firar yaushe rabo abu Yaƙi ƙarewa kamar Yauce rana ta farko da suka fara sanin junan su, da alama dai gidan Chief Ya zama Gidan marayu kowa ka kalli fuskarsa annurin farin ciki ne, ummi tana azaune kan sofa tare da batool hannun ta ruke da waya video take daukar su ba tare da sun sani ba.


Mutun ɗayace babu acikin su, Unaisah dake a daki Tana shiryawa, kamar yadda sukai da daddynta zai kaita Part dinsa dake agidan, wata hadaddiyar abaya ta sanya launin black and white ta ɗauko mayafi tayi rolling nasa akanta, tabi ko'ina na jikinta ta feshe shi da turare yarinya fa ta zama budurwa wani irin gayu take ji, 


Bayan ta sanya takalma, ta soma tunanin Ina ta jefa wayarta, sai yanzu ta fado mata aranta, farat daya tafara tunanin aunty pretty matar da sukai waya shekaran jira da dare gaba daya ta manta saboda lalurar da ta same ta ga kuma baiyanar daddynta da yan uwanta da suka ƙara mantar da ita zancen matar.


_Neman wayar ta soma yi, tun daga kan mirror har cikin closet din su, tsabar ruɗu itace har karkashin gadon su neman wayar, zukunnawar da zatai keda wuya taci karo da kananun hotunan nan, tura hannu tayi tare da janyo su zuciyarta cike fal da tunanin hotunan wanene._



_Kamar a mafarki take kallon fuskokin mutanan dake akan hoton, wani babban mutun ne mai kyan sura ya ɗauki wankan tailored suit a jikinsa, ɗayan hoton baturiya ce fara sol itama suit ne a jikin ta._


_Ƙurawa hotunan ido tayi tana kallonsu ba tare data Iya gane daga ina suka fadowa ba, ko wanene Ya jefa su karkashin gado, to ko dai Aljanune suka ajiye su? ta fada acikin ranta, can kuma ta sake kallon hoton Alhaji sai taga kamar an daura mashi fuskar Sajeed banbancin su sajen dake a fuskar alhajin da kuma manyantakar sa shi kuma sajeed bai da saje a fuskarshi_



*Mu haɗu gobe idan Allah yakaimu da rai da lafiya, Daga Alƙalamin Boss Bature💋✊✍️*



 *Littafin kurkukun ƙaddara 500 ne, dukanshi Book One two and 3 Idan kin shirya biya ga Details da zaki tura*


3196407426


First bank 


Bature Hafsat Muhammad,


 *bayan kin tura zaki bada transaction reciept ko screenshot na debit alert a matsayin shaida ta wannan layin 08169856268*

1 Comments

Idan kuna da tambaya akan abinda Baku game ba ko kuma kuma Neman littafin da babu a nan kawai ku ajiye tambayarku a ta comment ko wani shawara da Zaku bamu.

  1. Dan Allah kurkukun kaddara takun karshe 22

    ReplyDelete
Previous Post Next Post

Sponsored Link

Sponsored Post