Kurkukun Kaddara Takun Karshe Page 22 Complete


Health College

Kurkukun Kaddara Takun Karshe Page 22 Complete

Novels Elite English

 _*~✊💋BOSSLADIESWRITERS💋*~_

                     سجن القد💋🔥💞    

                  ~Takun Ƙarshe🔥~

            Dedicated to Aunty Kubra💋💞

قصة حب رومانسية غير عادية بين السجناء مع   تطورات معقدة💋💘😘

An extraordinary romantic love story between prisoners with complex twists ❤💋💘

Daga alƙalamin Boss Bature💋✊


_________________________________E22✍️

Ta jima tana kallon hotunan kafin Ta miƙe ɗauke da su a hannunta, da sauri ta juya ta nufi mirror drawer ta buɗe gida na uku ta saka su a ciki.


Tana ƙoƙarin mikewa sallamar Taj Ta katse mata hanzarin ta daga wajen dakin ta jiyo muryarsa.


"Daddy gani nan zuwa na gama shiryawa, waya ta nake nema banganta ba"


"Ina kika ajiyeta ne"?


Watsa hannu tai kamar tana agabansa na manta daddy


"Jiya naso na ganta a hannun ɗan uwan ku sajeed, bari na tambaye shi" amsa mashi tayi da toh aranta tana  mai mamakin yadda sajeed yake da nacin son waya, sam baya gajiya da ita."


Badajimawa ba, taj Ya turo kofar dakin Ya shigo hannunshi ruke da wayar.


Face dinsa da murmushi Ya mika mata"Na lura baki son wayar nan taki, saboda ba ki damu da ita ba, me zai hana ki bar ma sajeed din tun da yafi ki sonta"



Muryarta da yar shagwaba tace"wallahi inason abuna, sai dai asiya masa wata tunda Yana so, dr laura fa ta bani ita taya ma zan bada ita" ta yi maganar tare da kar6ar wayar daga hannun sa


"Kin ta6a kiranta ne kunyi magana"?


"Mantawa nakeyi wlh, amma in sha Allah zan kirata in na samu nutsuwa"


"Baki kyautaba yakamata kiyi kokari ki kirata" amsa mashi tayi da toh


"Daddy dani kadai zamu tafi"? 


"Eh, next time suma zan kai su gidan"  


Ruƙo hannunta yai acikin nashi, suka fito daga dakin, babu wanda Ya lura da su fira taja hankulan su, tana kallon su Deeja dake ta faman sakin murmushi wani irin sanyi taji aranta, yanzu damuwarta akan sauran prisoners ne wadanda ke AGIDAN KURKUKUN ƘADDARA! 


Har sun kusa fita daga falon, Kamar ance ta wurga eye balls dinta kan second floor, kwatsam Ta hango Danish dake kallon ta, cikin shiga ta pajama launin blue sky, tayi tunanin ba ita Yake kallo ba, sai tai saurin kau da idon ta, gudun kada ya ga za su fita,  tasan halin mutumin nata.


Suna fita daga falon ta sauke ajiyar zuciya, kasancewar baida nisa part din nashi, A ƙafa suke tafiya suna fira hanyar da suka biyo ko'ina hasken electric bulbs ne tamkar ba dare ba ga wata iska mai ni'ima dake kaɗawa


"Daugher, kina jin sautin da nake Jiyowa kuwa"?  da mamaki Tace A'a daddy menene"?

"Akwai mutun abayan mu, baki ji sautin tafiya ba" aɗan ruɗe ta furta mutum kuma? Wanene? bata jira ya bata amsa ba tayi saurin juyawa don ganin waye.


Har saida gaban ta ya faɗi idanunta adan zare take kallon shi, Hannayensa harɗe akan kirjinsa, fuskarsa babu fara'a, kayan baccin da ta gan shi da su sune a jikinsa fararen ƙafafuwansa ko takalma babu.



Juyowa taj yai tare da kallon shi, ashe tunda suka fito Yake biye da su, shi taj yasan da zaman shi itace bata lura ba.


Muryarta kamar zata fashe da kuka tace"daddy, mu tafi da shi kawai"


ƴar dariya taj yai tare da cewa"ya zama dole ay, wa ya isa ya hana shi zuwa"?


"mu tafi My man, nayi zaton kayi bacci, shiyasa ban neme ka ba, dama zamu je part din daddyna ne don in gaisa da Auntyna" 


kamar jira yake ta bashi damar yabi su, da sauri ya nufe su, a maimakon ya tsaya gefen ta sai ya shiga tsakaninta da taj, yasa hannu ya raba hannayensu dake ruke cikin na juna lamarin ya daurewa taj kai aranshi ya ayyana wannan wani irin namijin kishine? Uban nata ma bai ƙyale ba inaga idan wani ne daban ba? Tun yanzu ya fara jin fargaban yadda zata kaya tsakanin chief da danish tabbas akwai ƙura.


A haka suka jera har suka ƙaraso ƙofar shiga Part din, Komai nasa shigen kalar na sashen da suke ne banbancin kaɗan ne amma fa Ya haɗu, Ita kanta Angel tayi mamakin katafaren Ginin gidan Chief gari guda An ƙawatashi kamar A dubai.


Dafe kofar taj yai da hannunsa a hankali ta zuge masu, katafaren falo ne an kawatasa da furniture, ga wani sanyin A.c na mai sanyaya zukata


Sai ƙara kallon ko'ina take tana ɗan jinjina kanta, har cikin ranta ta ƙara jin ƙaunar chief saboda kyautatawarsa ga daddyn ta.


"Bismillah, Ku zauna bari naje nayi mata magana" ya fada tare da wuce ya nufi upstairs.


A hankali suka zauna kan sofa, kallon sa tai suka hada ido cikin na juna.


"Baki kewata ba? kin manta da dani jiya ko ki neme ni" yana magana tamkar baisan motsa lips dinsa


"Ni da kai waye mai laifi? Jiya ko kallo ban ishe ka ba, ka kama hanya ka bi uncle din chief inata kallon ka ko waiwaye na bakai ba" ta faɗa tana kwa6e masa fuska 


Lumshe idanunsa yai batare daya furta mata komai ba


"Har ciwon ciki nayi jiya kamar zan mutu, ni kadai a restroom na kasa bude kofa har na fadi kasa na suma duk kana ina"? 


"Ina atare dashi," atakaice Ya bata amsa


Ruƙo hannunsa tai tana kalllon dogon yatsan hannunsa dake asanye da silver ring, yayi matukar yi mata kyau 


"Shi ne Ya baka wannan"? Ɗaga mata kai yai alamar eh,


Da fara'a akan fuskarta tace"Bani labarin abun da ya faru tsakanin ku jiya"?


Sai da ya fara kai soft lips dinsa saitin kunnanta kafin ya fara bata labari saboda bai iya ɗaga muryar shi.


Sai faman sakin murmushi takeyi hakika taji dadin kyautatawar da prime minister yayi masa, kuma ta fahimce shima yaji dadi tun da gashi nan da bakinsa yake bata labari mutumin da be cika surutu irin haka ba.


"My man, Ni dai fatana Allah yasa mutumin nan ya zama alkhairi agare ka, wlh tunda nagansa naji ya kwanta min araina saboda kamannin dake a tsakaninku..."


 kafin ta ƙare maganar Sautin takalman daddynta ne Yaja hankalin su ga dubansa, saukowa yai down a hanzarce Ya nufe su Yana fadin"daugher, bacci takeyi auntyn naki, ko zaki je ki same ta adaki, Inaso ki bata mamaki" murmushi tayi tare da mikewa da sauri Danish Ya miƙe zai bita, kallon shi tayi cikin sanyin murya tace"ka zauna ka jira ni, Yanzu zan fito ba daɗewa zanyi ba" 


Taj dake kallon su murmushi yai tare da ƙarasawa gefen Danish yace"Idan saboda ni ne, To mu zauna gani ka gaka ita sai ta shiga watakli hankalinka zaifi kwanciya,' 


Kamar kuwa yasan sbd shi Ya miƙe zai bita, komawa yayi ya zauna hankalinsa akan Angel dinsa Harta haura kan stairs.


A hankali Ta zura kafarta cikin dakin, tana shiga ta soma bin ko'ina da kallo masha Allah, a hankali ta sauke idanunta kan Danejo dake a nannaɗe cikin bargo sai sharar baccin ta take yi.


watsa wa tayi da gudu ta daddage ta haye kan gadon gaba ɗaya ta ƙanƙameta tana dariya, wata irin firgita danejo tayi cikin magagin bacci take fadin"daddyn Angel, wayyo Allahna kana ina wai wanene ke takura min! Nashiga ukuna"


Yaye mata bargon Angel tayi, tana faman haki ta buɗe idanunta waɗanda suka kada jawur saboda bacci, A hankali ta sauke su kan fuskar Unaisah ta ƙura mata ido tana kallon ta, da tsantsar ruɗani take binta da kallo, Itama unaisah kallonta takeyi cike da kewarta, ba zata ta6a mantawa da fuskar denejo ba, ta ƙara haske fara jawur da ita kamar ba'indiya saboda kyau, ga gashin kan nan nata mai tsayi baki wulik har gadon bayanta..


Muryarta aɗan tsorace ta furta"wacece ke"? Mutun ko aljan"!


Dariya unaisah tayi cike da nishadi tace mata"Baki gane ni na"? 


Waro idanu waje danejo tayi da ƙarfi ta furta"ANGEL" 


tuntsirewa unaisah tai da dariya tare da faɗa mata ta sake rungumeta, daura hannayenta biyu tayi akan bayanta tana fadin"Ni ce, Angel dinki, ashe da rabon zamu sake haduwa danejo na" mamaki Ya hana danejo magana, da sauri ta tallabo fuskar unaisah da tafukan hannayenta, ta kura mata ido tana kallon ta batare da ta kyafta idanunta ba, ko amafarki taga fuskar Angel sai ta shaida ta, duk da ta ƙara girma a yanzu ta zama yar matashiyar budurwa, tuni taji hawaye sun wanke fuskarta, da sauri ta kwantar da unaisah kan kirjinta,  itama kukanne Ya kubce mata, sautin shesshekar kukansu duk Ya cika dakin, a hankali take shafa sumar kanta tana faman sauke ajiyar zuciya, Allah ne kadai Yasan irin kaunar da take Yi mata, taso unaisah, tayi kukan rashinta kamar zata zauce, muryarta kasa kasa ta furta"Alhamdulillah Ya Allah, nagode maka wallahi bazan Iya misalta farin ciki da nake aciki ba, Ya Allah nagode maka daka bayyana min Angel ɗina, Ya Allah nagode maka...." cikin shessheƙar kuka ta faɗa, tama rasa inda zata tsoma ranta saboda murnar ganin Angel.


ɗagowa unaisah tayi tasanya tafin hannu ta goge mata hawayen cikin sanyin murya tace"Aunty Danejo, naji dadi da Allah Ya sake haɗa ni dake a matsayin matar daddyna, I can't thank you enough saboda halaccin da kikai min arayuwa Allah ne kadai zai Iya biyan ki, kin so ni kin kuma kaunace ni tsakani da Allah, duk da bakisan koni wacece ba a lokacin amma kin taimaki rayuwa, kiyi hakuri ki yafe min laifin da nayi maki....' tana faɗa tana matsar kwalla.


 "Angel laifin me kikai min? Ni ay baki min laifin komai ba...."

Girgiza kai tai hawaye nabin kuncin ta tace"nayi maki laifi, bayan mun shaƙu da juna, na gudu daga rugarku kina ji kina gani har biyo ni ki ka yi kina kiran sunana don in tsaya amma naki sauraronki, ashe da rabon in sha wahala" idanunta acikin na danejo takeyin maganar 


"duk da bana danasanin ƙaddarar rayuwar da ta riske ni saima farin ciki da nakeyi saboda a kowani rashi da nayi toh akwai nasara acikin sa" tun da tafara magana danejo ta nutsu tana sauraronta, har cikin ranta tana mai mamakin girman yarinyar da kaifin basirarta, komai nata na dabanne shiyasa take da saurin siye zuciyar mutune.


"Aunty danejo, Kinga ikon Allah ko? Bayan na tafi sai gashi Allah Ya hada ki da daddy na har kun yi aure, amma baki takura kanki ba babu danginki a kusa, ki bani labari ya kikaji da kika fara shigowa cikin burni" yar dariya danejo tayi kafin ta fara bata labarin irin yadda ta tsinci kanta farkon shigowarta birni, ta tabka ƙauyanci taj ba karamin hakuri yayi da ita ba, saboda tsoro da rashin sabo da irin rayuwar birni.


Gaba daya suka kama yin dariya kamar wasu zautattu, Yadda kasan wasu aminnan juna.


"Amma dangin ki fa? Shikenan ba zaki sake haduwa da su ba"? 


"Ay Yayi min alƙawarin zai kaini rugarmu nan badajimawa ba" murmushi Angel tayi"amma naji dadi watakil nima in bi ki muje, in gano su hasiya da bawuro" 


"Baki manta da sunan su ba" jinjina mata kai unaisah tayi"ban manta ba, na haddace su akaina"


"Dama kece bakuwar da zanyi"? ɗaga mata gira tai alamar eh.


"Daddynki Ya faranta min raina, naji dadin ganin abun da banyi zato ba, amma lokacin da kika gudu ina kika je ne , tayaya akai aka gano ki? Ta fada cike da son jin karin bayani.


"Ki manta kawai, nadai ci wahala amma komai Ya wuce, bana son tuna baya" jinjina kai tay alamar ta fahince ta.


"Ina daddyn naki yake"? 


"Nabar shi a falo su biyu ne tare da ɗan uwana Danish"


 Ruƙo hannunta tayi"muje falon" saukowa sukayi daga kan gadon atare suka fito


A lokacin Taj Yana zaune kan sofa tare da Danish, tun bayan tafiyar Unaisah hankalinsa Yaƙi kwanciya, musamman da yaji ta daɗe bata fito ba, taj Yaso Yaja shi da fira sai dai Yaƙi bashi hadin kai, Jin motsin saukowar su down, yasa shi saurin kai idonsa ga dubansu, lokaci daya ya sauke ajiyar zuciya ganin Angel dinsa.


Fuskar taj ɗauke da murmushi yake kallon su, danejo kuwa tun da ta daura idonta kan fuskar danish gaban ta Ya fadi rass har sai da ta ɗan dakata da tafiya saboda taji fargaban ganin masifaffan kyan dake gare shi, ganin ta dakata da yin tafiyar ne yasa unaisah yi mata gyaran murya tare da cewa"Shi ne dan uwana danish, kada kiji komai atare da shi muka zo"


 jinjina kai tay kafin ta bi ta suka karasa saukowa down asaman sofa dake fuskantar su taj suka zauna, kowan nan su murmushine akan fuskarshi banda danish wanda hankalinsa ke akan unaisah.


"daddyn Angel, inatayamu murna cikin ikon Allah sai gashi Allah ya bayyana mana ita, amma meyasa baka fada min anganta ba"?


"Saboda inaso na baki mamaki" yar dariya tayi"wallahi ka bani mamaki kuma ka faranta min raina, ubangiji Allah Ya ƙara tsare mana ita daga sharrin makiya da mahassada dama duk wani abun cutarwa" har cikin ranshi yaji dadin kalamanta"ameen ameen, ga dan uwanta nan ku gaisa da shi" tun da tafara magana taki yarda ta kalli danish saboda tsoranshi da take ji, kallo ɗaya da ta masa kafin su sauko down ta gane ba shi kaɗai ba ne.



Muryarta na dan rawa ta furta"eh ta fada min sunan sa danish, ya kake dan uwan angel, Ina fata kana lafiya" muryarsa kasa kasa Ya amsa mata da lafiya, ba tare da ya dube ta ba


"Amma daddy Angel ya kuke da shi"?

Taj yace"yanzu ba lokacin tambaya bane idan na samu time zan maki bayani, tashi muje kitchen mu dauko masu abunda kika shirya masu"


 mikewa tayi taj yabi bayanta suka nufi kitchen



A hankali unaisah ta sanya idonta a cikin nashi, Murmushi tasakar mashi har dimple dinta Ya lotsa, sai yai tamkar baisan tana yi ba.


"Ba dai fushi kake da ni ba? Fadamin ko na bata maka rai na"? Ta fada tana ɗage mashi gira wani kallon kasan ido mai kama da harara ya wurga mata  


"Na fahimce ka, nasan bai wuci saboda na tafi na barka bane, ni narasa gane kishin da kakeyi akaina, sau biyu kana dukan daddyna, na farko ka jefa masa pillow daga upstair saboda yayi hugging dina, na biyu kuma ka Naushe shi da wannan kafcecen hannun naka saboda ya gyara min mayafina, next time inaga hannayensa zaka karya idan Ya ƙara ta6ani..." ta faɗa tare da ɗaura kafa daya bisa ɗaya tana jifar shi da harara kallon kawai yakeyi bai tanka mata ba.


"Ƙwara tun yanzu ka fara yi masa biyayya kana kyautata masa, saboda daddyna shi yake da ikon mallaka maka ni, Idan ba haka ba wallahi  kana ji kana gani zai aura min...."


kasa ƙarasa maganar tayi ganin yana nannaɗe hannun rigarshi, ay tuni tasha jinin jikinta, damtsen hannunsa Ya fito fari sol ga zanan tattoo na tambarin kurkukun kaddara, adan tsorace tace"my man yanzu saika buge ni akan wannan maganar" banza yayi da ita babu alamun zai tanka mata.


Murmushi tayi tare da kai hannu ta ɗauki wayarta dake a jiye kan sofa inda tabar ta, a fakaice ta soma daukar shi video ba tare da sanin shi ba, saboda yayi mata kyau he looks so sexy cikin sleeping dress expecially da ya naɗe hannun rigarsa zanan tattoo dinsa ya bayyana.


A tare Taj da danejo suka shigo falon hannayen su ruke da trays na kayan abinci, kafin su karaso tayi saurin ajiye wayar, ta yi ma danish alamar ya gyara hannun rigar sa, hannu yasa yaja hannun ya rufe damtsen nasa, bayan sun ƙaraso saman lallausan carpet din falon suka sauke masu farantan.


"Bismillah My daugher, inaso ki ba auntynki mamaki, Ki zauna Ki cinye abincin nan ke da dan uwanki Danish" murmushi unaisah tayi kafin ta sauko ta zauna.


"Malam Danish bismillah" ya faɗa Yana nuna masa carpet din, sam baiyi niyar ci ba, amma saboda unaisah Ya sauko Ya zauna, shima taj din da danejo suka  zauna suna fuskantar su, tuni kamshin abincin Ya karaɗe hancin su, wani haɗaɗɗen dambun Shinkafa ne ta zuba masu a plate, Yaji kayan kamshi ga nama manyan yanka da ta jera masu asaman dambun, ta tsiyaya ma su juice mai sanyi a cups, tun da suka fara cin abincin, Ta lura da yadda danish yake ci kamar zai fasa ƙaramin bakinsa, da alama dambun yayi masa daɗi, hatta taj da danejo satar kallon sa suke yi su kansu ba suyi tsammanin zai iya cin abincin har haka ba, bayan sun kammala cin dambun ta sake zuba masu farfesun ƴan ciki, kamar masu fama da yunwa haka suka tasa shi gaba suka lamushe, ta kuma ƙara zuba masu gurasa haɗi na musamman taji kuli kuli da kayan lambu da aka yayyanka ga mai dake kyalli asamanta tare da tsiren nama, danish bai ta6a cin gurasa ba sai Yau, kai harta dambun shinkafar yaune karo na farko daya fara cinshi, yaji dadin abincin har ƙwarar cikinsa yayi, Angel dake kallonsa sai faman sakin murmushi takeyi ba tare da ya lura da ita ba, bayan sun kammala cin abincin kowa yayi kulu wash rabu hani'an danejo ta kwashe kayan abincin ta nufi kitchen da su

"Daughter, dare yayi muje na raka ku  gida, Kada chief Ya tuhume ni, kinsan yanzu bani da hurumin daukarki tun da a karkashin kulawarshi ku ke har zuwa time da zamu kammala bincike"


"Bakomai daddy, na fahince ka," shafa gefen fuskarta yai, danish dake kallon su tuni ya hade ransa, shi fa har yanzu bai daina kishi da taj ba, saboda baisan alaƙar dake a tsakanin iyaye da dansu ba.


Fitowa danejo tayi daga kitchen, ganin su tsaye yasa tace"ya akai nagan ku a tsaye ku zauna mana muyi firar yaushe rabo"


Taj ya ce"Zasu tafi ne" ɗaure fuska tay"bangane me kake nufi ba, nayi zaton ta dawo gida kenan," girgiza kai yai"ay tana a gidan amma a part din chief suke da zama, zata dinga zuwa kuna gaisawa da juna...." dakyar ya samu ya fahimtar da ita, atare suka raka su unaisah har gida kafin sukayi masu sallama.


Lokacin da suka shiga falon babu kowa har sun koma bedrooms dinsu alamar time din bacci yayi, kamar kar su rabu da danish har saida ta raka shi bedroom dinsa kafin ta dawo ta nufi nasu dakin, tana shiga ta samu deeja kwance kan gadon su sai jan minshari takeyi, murmushi tasaki tana kallon ta, har yanzu kwalliyar dazu ce akan fuskarta duk ta ca6e kamar ƴar mahaukaciya, ta jima tana kallon ta, kafin ta fara cire kayan jikin ta, ta musanya dana bacci, fuskarta dauke da annurin farin ciki, ta hayekan gadon, bata damu da rashin ganin batool ba, tasan bazata wuce dakin aunty ummin su ba, huggin pillow tai, Allah ne kadai yasan dadin da take ji sam ta manta da zancen kiran aunty pretty gaba daya tunaninta akan abun farin cikin daya faru yau ne


______________________________________✍️



Zaune ya ke kan sofa ya ɗaura ƙafarsa ɗaya bisa ɗaya, yayin da idanunsa ke akan laptop din gabansa da yake operating lokaci ɗaya ya ɗan dakata Ya jingina bayansa jikin Sofa haɗi da lumshe idanunsa zuciyarsa a cike take fal da tunanin prettynsa har yau jiran hajiya laurat yake yi don jin amsarta, tun jiya bayan kammaluwar dinner din hateem ziyad ya nemi alfarmar yin magana da ita bayan sun ke6e cikin girmamawa ya gaishe ta, ta amsa masa daga bisani ya fara kora mata jawabi game da bukatarsu, lokaci ɗaya yanayin fuskarta ya canza zuwa 6acin rai kamar bata son zancen Benazir da yake yi mata, acikin ranta tayi mamakin jin cewa a hannun Zaki ta faɗa ita sam ta manta da rayuwar benazir tamkar ma ba'a halicce ta adoron duniya ba, saboda tun fil azal hajiya laura basa ga maciji da hajiya layla wata irin gaba ce atsakaninsu shiyasa bata shiga shirgin abun da ya shafi layla, a lokaci shi kanshi ziyad ya lura da 6acin ran da take a ciki amma sai ta waske ta ƙaƙaro murmushi tana fadin Allah sarki benazir ashe dama zaki ne ya taimake ta? Alhamdulillah wlh nayi murna ziyad, sai dai abun da ya daure min kaina babu wanda Ya kirani daga gidan Ya fadamin cewa anganta amma in sha Allah zan fidda lokaci inje can gidan da kaina don in tabbatar ta dawo in yaso daga bisani zan tuntu6i shi zaki din...." akan haka suka ƙare magana ziyad yai mata godiya kafin suka rabu.


A hankali Zaki ya buɗe idanunsa Yana kallon ceilling din falon, duk don saboda son haɗuwa da ita, ya ɗaga tafiyarsa canada.


Yayi zurfi a zancen zucin nasa muryar turai ta ratsa kunnansa


"First born barka da hutawa" ta faɗa tare da daura masa mug din coffee kan table, murmushi ya sakar mata, yana ɗaya daga cikin abun da yake burge shi da mommyn nasu in har zata ganshi zaune yana aiki akan laptop sai ta kawo mashi coffee .


"Mom har yanzu baki yi bacci ba"? ya faɗa yana kallon ta.


"Tayaya zan iya runtsawa Jazz bai dawo ba, daddynku bai dawo ba shima, su nake jira su dawo sai in kwanta" tayi maganar tare da ɗaura gwiwowin hannunta bisa ga hand sofa din da zaki yake zaune idanunta akan fuskarsa


"Ko akwai wani abu dake damun ka ne"? Ta fada cikin kulawa


"Babu komai" ya bata amsa atakaice tare da kai hannu ya dauki mug din Ya soma kurbar coffee


"My son, tayaya zaka 6oye min damuwarka, bayan ni mahaifiyarka ce, ta ido kadai ina gane damuwarka, tun lokacin da ka shigo ƙasar nan na lura da damuwa aranka"


Sauke mug din yai kan table kafin ya dubi hajiya turai"nagode da kulawarki agare ni, amma ki kwantar da hankalin ki ba abun da ke damuna" 


Gyaɗa kai tay"haka nakeson ji" ta faɗa ne ba dan ta yadda da maganarsa ba tasan baya son taji ne


"Bari na shiga ciki, ka kula min da kanka" amsa mata yai da toh


Bayan tafiyarta ajiyar zuciya ya sauke, bawai baya son fada mata bane yafi son ya fara jin halin da take a ciki in har ta isa gida lafiya, kuma iyayen ta sun kar6eta ba abun da zai hana shi sanar da nashi iyayen labarin ta.


Ƙarfe goma da rabi, jazz da sir mubarak suka dawo gidan lokacin da suka shigo falon tuni Zaki Ya koma room dinsa ba su taras da shi ba, 


Hajiya turai na kwance kan gado tajiyo sautin sallamar sa, jikinta har rawa yakeyin wurin saukowa daga kan gadon da sauri ta nufe shi yana atsaye cikin shiga ta kakinsa


"Sannu da dawowa, tun dazu nake ta jiranka nayi kewarka yau kayi dare " cikin nuna kulawa tayi maganar tare da ruko hannunsa suka shiga dakin


"I'm sorry bansanar da ke zan kai dare ba, wani aiki ne mai muhimman ci Ya ruƙe ni" ya faɗa Yana kallon cikin idonta,

"Ba nace ki daina jirana ba? daga kinga nayi dare to ki kwanta kiyi bacci"

Maƙe masa kafaɗa tayi"kai ma kasan bazan iya jurewa ba...." murmushi ya ɗan saki"kinsan me na tuna"? Girgiza mashi kai tay alamar a'a"


"Waɗannan twins din na wurin Owais, ko da yake yace min ba twins bane, ɗaya ta girmi ɗaya" da mamaki hajiya turai tace"ikon Allah, amma nayi mamakin jin hakan komai nasu fa iri ɗaya kamanninsu sun 6ace"


"Zai iya yiwuwa yan gida ɗayane" jinjina kai tay alamar eh


"Yaran sun kwanta min araina, kinsan ni da son ƴa'ƴa mata, duk family dinmu ni kadai ne nake da ya'ya maza ina alfahari da hakan amma inason ya'ya mata, ga hateem nan shi mazan yake so Allah bai bashi ba"

 


shiru mom turai tayi kamar ta dan shiga damuwa, sam bai lura da halin da ta shiga ba, ya nufi toilet Ya shige jin ƙarar rufe kofar shi Yasa jiki asanyaye ta koma gefen gadonsu ta zauna idanunta sun ciko tab da kwalla..


Ceilling ta ƙurawa ido tana tunano wani abu da ya ta6a faruwa acan lokacin baya shakeru da suka gabata, ta ta6a haihuwa ya'yan suna mutuwa wanda silar hakan Yaja har sir mubarak Ya hanata haihuwar gaba ɗaya gudun kada itama tarasa ranta kamar yadda ya'yan da take haihuwa suke rasa ransu da zarar sun dira a duniya, Allah kadai yasan halin da ta shiga awannan lokacin saboda ta kwallafa rai akan son taga ta haihu da sir mubarak sai dai Allah bai bata ba shiyasa har su hajiya saratu suke yimata gorin sai dai taci ta kasayar


Yunkurawa tayi jiki ba kwari ta mike ta futo daga ɗakin nasu ta nufi bedroom din jazz sai da ta matse kwallar da ta taru a idanunta kafin tayi mashi sallama shiru ba'a amsa mata ba, har ta fara tunanin ko yayi bacci ne, shigarta ke da wuya kwatsam taci karo da wayarsa dake yashe kan floor ga dukkan alamu wurgo da ita yayi, hatta lap coat dinsa  anan ya jefar da ita, hankalin ta ba karamin tashi yayi ba, a razane ta kalli gadonsa a zaune ta same shi tsakiyar mattress, Ya kifa kansa bisa gwiwowin sa, lokaci ɗaya ta rasa sukuninta da sauri ta nufi kayan nashi ta kwashe su ta je ta ajiye masa kafin ta dauko wayar ta nufin gadon nashi ta hau sama ta zauna tana fuskantar shi


"Jazz meke faruwa dakai ne"? ta fada fuskanta dauke da matsananciyar damuwa


Shiru babu alamun zai tanka mata


"Nasan kana ji na jazz, ka ɗago ka kalle ni sannan ka fadamin meke damunka" A hankali Ya ɗago da fuskarsa wadda ta jiƙe sharkaf da hawaye idanunsa sun kaɗa jawur, wani irin bugu taji zuciyarta tai muryarta na rawa ta furta"jazz kuka kake? Meke damunka ne? Ko bakada lafiya ne? Aruɗe ta fada tana shafa fuskarsa


"Jazz dan Allah ka fadamin ko hankalina Ya kwanta" daƙyar Ya iya motsa la66ansa Ya furta sunan faryat, lokacin ɗaya annurin fuskar hajiya turai Ya ɗauke ɗuff, saboda ta fahimci silar shigarshi halin da yake aciki, batasan ya zatai da jazz ba, tayi fama da shi akan ya rabu da faryat amma yaƙiya saboda tasan bazata ta6a auran shi ba, hasalima ma yarinyar bata kwanta mata aranta ba, saboda fitsararta da rashin kunyarta..


"Jazz yaushe ne zaka daina yaudarar kanka akan yarinyar nan? sau nawa ina maka gargadi akan ka fita sabgarta? Na fada maka ba sonka takeyi ba yakamata ka hakura ka nemi wata ay ba ita kadai bace mace a duniya....." kafin ta ƙare maganar ya tarin numfashin ta da cewa"bazan iyaba mommy, Allah ne ya jarabce ni da sonta, wallahi nayi kokarin cireta araina amma na kasa ki tayani da addu'a Allah ya yaye min sonta in ba haka ba zatai silar da zan rasa raina..."


har saida gaban turai Ya fadi jin abun da yace, ta fahimci mahaukacin son da yakema faryat ba lallai Ya fahimce ta ba


"Me tayi maka ne"? labari Ya fara bata na abun da Ya faru tsakaninsu lokacin da ya je wurinta bai 6oye mata komai ba, har nemansa da tayi don ya bata hadin kai, 


"Mom kullum na kirata sai ta ci mutuncina, tace wai ni ba namiji bane tunda bazan iya biya mata bukatarta ba, sannan bazata ta6a auran mara asali dan tsohuwar mai aikin gidan su ba...." ya faɗa idanunsa cike tab da kwalla


Ita kanta hajiya turai hawayen ne ke sintiri kan kuncinta, ta tsani taji ana yi mashi gorin asali kamar kanshi farau, ta rasa gane meke damun wasu mutanan sun manta cewa bawa bashi ke daurawa kansa ba? Allah ne Yake kaddara masa rayuwarsa?


"Jazz ta yi kuskure A kalamanta, wallahi sai tayi danasani, saboda ka fi karfinta nesa ba kusa ba, kuma kaine cikakken mai asali tunda kana jin tsoron Allah kuma ka tsare mutuncinka, ni in banda kaddarar so ina kai ina Faryat"? ta faɗa ranta amatuƙar 6ace


"Tafi ni komai tun da tana da asali"


"Kaima kana da asali jazz" da sauri Ya kalle ta


"Mom bangane me kike nufi ba, ke da kanki kika fada min baki da kowa a danginki mahaifina Ya rasu" girgiza kai tayi"na fada maka hakanne saboda ka fidda rai da kowa nawa, bana son maganar jazz ka cigaba da hakuri in sha Allah komai ya kusa zuwa karshe" tun da tafara magana jazz Yake kallonta har yau ya rasa gane dalilin dayasa bata son tayi maganar abun da Ya shafi danginsa, shi dama yasan dole tana da family dinta akwai dai wani abin da take 6oye masa, duk da yana neman ƙarin bayani daga gareta sai dai ya hakura yabarwa zuciyarsa zai cigaba da hakuri kamar yadda ta ce har zuwa lokacin da zata sanar da shi komai....


Shiru sukayi na wani lokaci babu mai magana a cikin su, 


"Ina ibad"? ya tambaya yana kallon ta


"Tun bayan sallar Isha' Yai bacci, ya yi jiran dawowarka har fadamin yai ya kira layinka bakai picking ba"


murmushi yayi"Allah sarki ɗan uwana, dama nasan dole ya neme ni, na sanya wayar a silent ne saboda aiki da nakeyi"



"Bari na kawo maka dinner dinka nasan kana jin yunwa, but pls ka shiga toilet ka wanke fuskarka bana son ganin hawayen nan" ta fada tana nuna face dinsa da yatsa amsa mata yai da toh da sauri ya sauko daga kan gadon Ya nufi toilet.


Tana ta bin bayansa da kallo har ya shige kafin Ta mike ta fito daga dakin


Kitchen ta shiga ta shirya masu abinci ta fara kaima jazz a room dinsa kafin ta dauki na sir mubarak ta nufi dakin su


Lokacin da ta shiga a tsaye ta same shi hannun shi ruƙe da wayarshi Yana daddanata har ya sanya kayan baccinsa


"Ina kika je ne" ya fada ba tare daya kalle ta ba


"Na shiga kitchen shirya maku abinci ne," ta fada tare da ajiye masa tray din bisa table, murmushin gefen fuska ya dan saki batare data ankara ba, abun da bata sani ba tun time da ta shiga dakin jazz Ya fito Yabi bayanta gaba daya ya ji maganganun da su ka tattauna har recording voices dinsu yayi a wayarsa, yayi mamaki abun da yaji suna tattaunawa, maganganun sun tsaya masa aransa, wani lokaci turai tana da zurfin ciki, in har ba la6e yayi mata ba ita da jazz bayajin damuwarsu sai in tura takai bango  tukunna take sanar da shi.


_______________________________✍️


Aneelerh har tayi shirin kwanciya bacci, sautin ringing din wayarta ya dakatar da ita, A hankali ta kai hannu ta dauki wayar ganin sunan surukar arziƙi yasa tayi saurin picking call din idanunta na akan baby junaid dake kwance kan mattress Yana sharar baccin sa


Cikin girmama suka gaisa da junansu


"Aneelerh kwana biyu? Ya ki ke Ya su mamin"?


"Alhamdulillah, muna nan lafiya lou"


"Ina jikan nawa ko har anyi bacci"


"Yayi bacci tun ɗazu"


"Allah sarki nayi missing nashi, Ya maganar zuwan naku?


"In sha Allah, cikin week din nan zamu zo"


"Allah yakaimu lafiya" ta amsa mata da ameen daga bisani sukayi sallama taso ta fada ma hajiya adama zancen dawowar benazir amma ta bari sai benazir ɗin tazo gidansu sai ta kira ta awaya suyi magana don ta bata mamaki, murmushi tayi tare da ajiye wayar kan nightstand, ta janyo junaid on her chest ta rungume abun ta.


_________________________________✍️



_Dare Mahutar bawa, sai dai bakowa ne ke samun kwanciyar hankalin runtsawa a cikin sa ba, saboda akwai wanda ya manta yaushe rabon da idanunsa su runtsa saboda rashin kwanciyar hankali_


*👹GIDAN KURKUKUN ƘADDARA👹*



Daki ne madaidaici mai fadi da tsayin gaske, irin ginin dutsen nan ne dayai shekara aru aru, daga saman dakin fitilun kwai ne guda uku masu haske idan ka kalli bangon dakin ta ko'ina jirwayen jinine da ya daskare, kai harta iskar dakin ta gauraya da karnin jini da warin jikin mutanan dake rayuwa a cikin sa. 


Matasan Ƴan matane zazzaune kan gadajen ƙarfe, kowaccen su tana asanye da guntuwar riga launin ja wadda bata rufe gwiwar ƙafarsu ba sun rame sun ƙanjame fatar jikinsu duk sahun yakushi da kurajen fata kai gaba dayansu sun koɗe baka gane fari acikin su saboda duhun da fatarsu tayi wanda bakomai ne yajawo hakan ba face uƙubar da suke fuskanta, wadannan bayin Allahn babu irin tashin hankalin da ba su gani ba sunga bala'e da masifa tsirararsa, gaba daya an salwantar da rayuwarsu, tun lokacin da aka kaddara masu rayuwa agidan kurkukun ƙaddara amfani ake da su kamar injina, babu wani sassauci.


 gaba ɗayansu babu wacce ta haura shekara sha bakwai dukansu matasan Ƴan matane gwanin ban tausayi, dukkan gabban jikinsu sun raunata, ko tafiya ba su iyayi sai dai adauke su akai su inda za'a yi amfani da su in angama a dawo da su😭 zuciyarsu da fargaba take bugawa, numfashin su da tashin hankali suke buso shi, idanunsu sun kumbura suntum sun ƙafe saboda tsabar kukan da suke sha wanda tun sunayi hawaye na zuba har takaiga ruwan hawayen sun daina fitowa sai dai kukan zuciya mai ɗacin gaske, basu da wani burin dayawuce Allah Ya dauki ransu su huta.



Biyo bayan da Garkuwa Ya gudu tare da wasu daga cikin prison haƙiƙa ran Elders yayi mugun 6aci matuƙa sun harzuƙa evil heart dinsu ta hasala, wanda silar hakan Yaja suka fara azabtar da sauran prisoners dake agidan kurkukun ƙaddara, babu imani ko miskala zarratin yanzu ko abinci mai dadi babu a gidan kurkukun ƙaddara babu wani jin dadi ko na daƙiƙa sai baƙar izayar rayuwa, Allah ne kadai Yasan adadin jinin da suka zubda na yaran da suke raino, da kuma Yaran da suka gur6ata ma rayuwa, wani shiri suka fara yiwa kansu saboda suna hasashen akowani lokaci za'a iya kawo masu farmakin bazata, kuma suna da tabbacin asirin su yana dab da tonuwa, basu ta6a fuskantar barazana da tashin hankali irin na wannan lokacin ba!!


_Zaman tattaunawa sukayi a karo na biyu a dakin sirrinsu wanda a lokacin suka yanke shawarar za su ba ɗaya daga cikin  Evil giant ɗin da suke da su horon zama prison shield saboda asamu wanda zai maye masu gurbin Garkuwar su da suka rasa saboda sun fahimci yayi masu nisan kiwon da ba zasu iya tanƙwara shi ba, da buƙatar su samu wanda zai zamanto abokin karawar Garkuwa, saboda a halin Yanzu Idan aka kawo masu farmaki tare da shi to kuwa tabbas za'a ci galaba a kansu tun da babu wani giant da zai Iya karawa da shi idan ba su elders din ba, amma Idan suka gurfanar da sabon Giant din su mai ruƙe da mukamin prison shield zai yi wuya a iya rusa su in ba wani iko na Allah ba, sannan shi wannan giant din zai iya aikata duk wani rashin imani da suke so, ba a halicci zuciyarsa da imani acikin ta ba, baƙin mugune kuma azzalumin mutun ne shu'umi mai hadarin gaske, baisan menene tausayi ba, kurma ne sannan makahone bayaji baya gani in ba umarnin ubayen gidansa ba wato Elders, Shi fa wannan giant din baida mararraba da bakin shaidanin Aljani saboda sune suka rinjayi halittarsa ta ɗan adam_ 

    



*Daga Alƙalamin Boss Bature💋✊✍️*



 *Littafin kurkukun ƙaddara 500 ne, dukanshi Book One two and 3 Idan kin shirya biya ga Details da zaki tura*


3196407426


First bank 


Bature Hafsat Muhammad,


 *bayan kin tura zaki bada transaction reciept ko screenshot na debit alert a matsayin shaida ta wannan layin 08169856268*

Post a Comment

Idan kuna da tambaya akan abinda Baku game ba ko kuma kuma Neman littafin da babu a nan kawai ku ajiye tambayarku a ta comment ko wani shawara da Zaku bamu.

Previous Post Next Post

Sponsored Link

Sponsored Post