Kurkukun Kaddara Takun Karshe Page 23 Complete


Health College

Kurkukun Kaddara Takun Karshe Page 23 Complete

Novels Elite English

 _*~✊💋BOSSLADIESWRITERS💋*~_




                     سجن القد💋🔥💞    



                  ~Takun Ƙarshe🔥~




            Dedicated to Aunty Kubra💋💞




قصة حب رومانسية غير عادية بين السجناء مع   تطورات معقدة💋💘😘



An extraordinary romantic love story between prisoners with complex twists ❤💋💘





Daga alƙalamin Boss Bature💋✊





_________________________________E23✍️





Baiyanar sa tamkar bainar mutuwa ne, zaiyi wuya mutun ya hada ido da shi ba tare da zuciyarsa tayi yunkurin dakatawa da bugawa saboda firgitarwar dake gare sa, shin wanene Wannan Evil giant din?



   Asalin Sunan sa Jeremiah shi tun fil azal mugun mutunne tunkafin zamantowarsa Giant mugunta da zalunci kaɗai yasa a gaba, inaga yanzu da suka fara ba shi horon zama Garkuwar prison abun ba'a magana babban abun da zai baka mamaki ƙarancin shekarunsa dududu bai fi sa'an garkuwa ba amma a halitta basamude ne saboda girman jikinsa.


A yanzu haka Yana a cikin Rijiyar sirihi, wato mataki na ƙarshe da suke ba mutun na horan zama evil giant, ita wannan rijiyar sihirin bata ruwa bace, mazauni ne na bakaken aljanu da shaiɗanu, kwanan watan da za su gurfanar da shi yayi dai dai da lokacin da suka ɗaga na yin black night, aranar za su fiddo da shi saboda rashin imani da zalunci, nayi imanin ko makiyina bazanyi mashi fatan yakai wannan ranar agidan kurkukun ƙaddara ba saboda musifar da zata afku na bayyanar Jeremiah, rayuka ne za'a salwantar bila adadin ba yara ba ba kanana ba ba tsoffi ba hatta jarirai ba zasu ƙyale ba wa'iyazubillah.....


________________________________✍️


Motsin buɗe ƙofar ɗakin ce ta karaɗe kunnuwansu kamar gumaka babu wanda ya motsa a cikin su sai faman zare idanunsu su ke yi, gaba daya sun sha jinin jikin su saboda sun san ba alkhairi ba ne ya ke tunkaro su.



Dattijuwar macace tsohuwa tukuf, gata doguwa kamar Fatalwa, tun daga kasa har sama ta rufe jikinta da doguwar riga mai hula launin Ja, hannunta ɗaya ruƙe da sanda, kafafuwanta suna asanye cikin jajayen takalma, ta rufe fuskarta da mask launin Ja, tsoffin Idanunta ne kaɗai a buɗe, zuciyar mace da rauni aka santa amma ita wannan baiwar Allahn babu zuciyar imani a kirjinta, batasan menene tausayi ba, muguwar macace shaidaniya mai hali irin na kafuran farko, daga gaban rigarta akwai taurari uku masu kyalli daga gani tana ruke da babban muƙami na gidan kurkukun ƙaddara.


A hankali ta zura kafarta sautin takun tafiyarta kamar na dawakai babu sassauci, daga bayanta akwai wasu gabza gabzan Giants dake take mata baya su biyu, ɗaya daga cikin su yana a ruƙe da madaidaiciyar tukunyar ƙasa an rufe samanta da jan ƙyalle, yayin da ɗayan kuma Yake ruke da faranti mai ɗauke da ganye sai ƙananun kofuna da alama ruwa ne a cikin su.



A tsakar Dakin Ta dakata da yin tafiyar, wani kaskantaccen kallo ta soma jefa masu ɗaya bayan ɗaya kafin ta ba giants din umarnin su fara gudanar da abun da Ya kawo su.


Mai ɗauke da tukunyar ne Ya sauke ta ƙasa yasa hannu ya buɗe jan ƙyallen da suka rufe ta da shi, cikin takun majiya ƙarfi Ya nufi gadajen ƴan matan, ɗaya bayan ɗaya ya ke damƙar su da karfi sannan ya cusa yatsun hannunsa tsakankanin cinyoyinsu, wata auduga ce naɗe cikin panties din su yake zaƙulowa jawur da ita, wani sabon salo suka 6ullo da shi idan yaran suka fara yin jinin al'ada sai su sanya masu audugar da suka tsaface ta a cikin panties dinsu, ita amfanin ta jinin al'adar da suke zubdawa ta ke tsanewa ta ruƙe sa a jikinta ko ɗiga baya yi, suna yin hakan ne saboda a buƙace suke da jinin na su wani mugun sihirine suke yi da shi.



Tuni sautin koke koken su Ya cika dakin, Jikinsu sai kerma Yake yi saboda tashin hankali, duk audugar da ya curo a gabansu cikin tukunyar ya ke zuba su,, bayan Ya gama dattijuwar tai gyaran murya, da sauri ɗayan giant ɗin me ruke da faranti Yabi su ɗaya bayan ɗaya ya mika masu kofunan, wani ruwan sihirine a ciki mai kamar jini, ga ƙarni warinsa babu dadin shaƙa, bayin Allah kamar za su zauce a haka suke shan ruwan wasu har sun fara yunkurin amai amma saboda fargaban kada su zubda a azabtar da su yasa suka daure suna sha.



Wani irin ɗaci ne Ya ratsa maƙogwaronsu tuni idanunsu sun kaɗa jawur tamkar garwashin wuta.


"Zaku Iya ba su ganyen" dattijuwar ce ta furta maganar, watsa masu ganyen su ka yi a ƙasa, bayin Allah jiki ba kwari suka sauko kasa kamar dabbobi haka suka kama cin ganyen da aka watso masu ƙasa.


Shu'umin murmushi dattijuwar ta saki ta cikin mask dinta, Har zata Juya kwatsam idanunta suka sauka akan Gado mai ɗauke da number 100, A hanzarce Ta wurga tsoffin idanunta kan Yaran dake cin ganyen rigunansu tabi da kallo masu dauke da numbers from 80 suka fara har izuwa 99 amma babu 100 nan take ta fahimci bata acikin su lokaci ɗaya yanayin fuskarta ya canza zuwa 6acin rai.


Da kakkausar Murya mai amo Ta furta sunanta


"GABRIELA"! ta faɗa tana zare idanu cikin 6acin rai


"Kada ki kuskura ki bari na sake maimaita kiran sunanki! Ki fito tun kafin ranki Ya 6aci"! Shiru babu alamun wadda aka kira da sunan Gabriela zata fito daga ma6uyarta, ran dattijuwar ya 6aci matuka ta fusata sai faman zazzare idanu takeyi tana bin ko'ina na dakin da kallo, Har yau tana mai mamakin karfin halin Yarinyar da rashin tsoranta, ga kafiyar tsiya abun a jinin ta ya ke..


Kallon sauran yaran tayi"Ina Yar uwarku gabriela take" da tsawa ta furta maganar, muryoyinsu na kerma suka amsa da cewa ba su san inda take ba..


Ɗaga murya ta kuma Yi a karo na biyu ta furta"nasan kina saurarona! Idan har baki fito ba, zakija ma sauran ƴan uwanki! Ina mai baki umarnin ki gurfanar da kanki agabana tunkafin In zaƙulo ki da hannu na" ta fada tana huci kamar zakanya, sarai tasan inda ta 6oya amma saboda karfin izza tafi son ta kawo kanta agabanta.. "


Kallon giant din da ke a gefenta tay, kamar jira yake ta bashi Umarni, azafafe Ya Nufi gadon mai number ɗari, Ya zura hannu Ya damƙo ƙafarta Kamar yar dambe haka tadinga bubbuge shi da kafafunta hada karfin halin naushin sa da hannunta, wurgo da ita yai waje ta gangaro kan floor, yar guntuwar rigarta tuni ta tattare ta haura kan waist dinta da sauri ta sanya hannu ta kamo rigar ta lullu6e mazaunanta, gaba daya nannaɗadɗiyar sumar kanta ta rufe fuskarta.



Yunƙurawa tayi da karfi ta miƙe tare da dunƙule yatsun hannayen ta alamar zatai faɗa sai faman haki take yi tana huci, daga ganin idanunta babu tsoro a cikin su, duk irin azabtarwar da ake yi masu baisa zuciyarta ta raunana ba, duk cikin yaran babu mai irin karfin halin ta.



wani irin gumi ke tsastsafowa ta hancin ta da gefen kanta, Yarinyar ba karamin kyau ne da ita ba, ga dirin jiki tana shape irin na ƙarfafan mata, gaba ɗaya jikinta tabon raunuka ne, gefen goshin ta hada ɗinkin ciwo da aka ta6a yi mata agidan kurkukun sakamakon wani mugun rauni da ta ta6a ji akwanakin baya.


Shu'umar dariya Dattijuwar ta saki tana tafa hannayenta kafin ta jinjina mata da babban yatsa ta ce"sannu da kokari Gabriella, da ace bakiyi min hakan ba da ban shaida ke jinin jatuminki bace, karfin halin ki yana burgeni ina son inga mace haka..." ta fada tana cigaba da sakin dariya mai sautin gaske.


Gabriela dake kallonta tsantsar tsanarta take ji, ta tsani matar fiye da yadda ta tsani kowa a duniyar nan...

Cike da karfin hali Ta furta"muguwa azzaluma.."



kafin ta ƙare maganar dattijuwar ta daka mata tsawa mai razanarwa, a firgice sauran yan uwanta suka koma kan gadonsu jiki na kerma.


Ita kuwa wadda akai ma tsawar babu alamun firgita atare da ita kamar ana tunzurata taci gaba da fadin"kin manta abunda na ta6a fada maki? Ni bana jin tsoronku har bada azabtarwar ku ba zata ta6a sanyani yi maku biyayya ba saboda ku din dabbobine dakikai kuma jahilai sai kun yi mummunan ƙarshe a wulakance zaku mutu...' ta faɗa tana cije la66anta da gumi ya jiƙa su.


 Idanu a matuƙar zazzare dattijuwar ke kallonta da wani irin fusata ta kalli ɗaya daga cikin giant din dake take mata baya da ido tayi masa magana, cikin takun majiya karfi Ya nufi gabriella gadan gadan, lokaci ɗaya ta soma ja da baya hankalinta a matuƙar tashe batasan me zai aikata mata ba, babban abun da take jima tsoro kada ta rasa ranta ba tare da ta cika burinta na ganin ta haɗu da ɗan uwanta gabriel, ba ta son ta mutu batare data gana da shi ba, daba don shi ba da tuni ta jima da kashe kanta.



Watsa wa tayi da gudu ta nufi kofar shiga toilet dinsu ta buɗe kofar ta shige taja ta rufe, tana faman jan numfashi kamar daga sama taji dirar mutun a toilet din kamar aljani haka Ya faɗo mata tuni la66anta sun fara kakarwa muryarta na rawa ta soma faɗin karka kuskura ka ta6ani!! kada ka matso kusa da ni, ka ƙyaleni, Idan ka cutar dani dan uwana bazai kyale ka ba sai ya kashe ka..." 


sambatu tadinga yi cikin rawar murya  mai haɗe da tsantsar tashin hankali da fargaba sam ta manta cewa giant basa ji basa gani, kallonsa take kamar dodo gaba ɗaya inuwarsa ta lullu6eta.


Ƴan uwanta dake zazzaune kan gadajensu tuni zafafan hawaye sun wanke fuskokin su lokacin da suka fara jin sautin kururuwar gabriela ta cika dakinsu da wani irin azababben sautin kuka mai ƙaraji tamkar ana zare ranta nan take suka fahimci abun da giant din yake yi mata, haƙiƙa zuciyar su ta yi matuƙar karaya.



Tsawa dattijuwar ta kwatsa masu babu digon imani aranta


"kar in kuskura in ƙara jin sautin koke koken ku, ko da tari ne bana son ji idan ba haka ba, zansa ay maku abun da akai mata" jin wannan maganar yasa sukai shiru, kukan nasu ya koma na zuci.


Tsawon mintuna goma cuf, Kafin giant din Ya fito daga makewayin sanye cikin kakinsa kamar bai aikata wani abu ba..


Wata irin mahaukaciyar dariya tsohuwar tayi idonta akan giant din ta jinjina masa da yatsan ta.


Kafin ta juya cikin takun izza ta nufi kofar makewayin nasu ta buɗe kofar tasakai ta shiga.


A kwance ta hango ta kamar matacciya babu sutura a jikinta sai faman sakin nishin azaba ta ke yi numfashinta na fita da hucin zafi, ga wani jini dake gangarowa ta tsakankanin cinyoyin ta, baiwar Allah ko ina na jikinta Ya raunata kwata kwata bata acikin hayyacin ta, ita kaɗai tasan tartsatsin azabar da ta sha, cikin fitar hayyaci take ambaton sunan ɗan uwanta gabriel, yayin da hawaye ke tsastsafowa kan kincinta masu ɗumin gaske, idanunta sun juye jawur kamar garwashin wuta, takasa tsaida gangar jikinta sai birgima takeyi saboda zogin azabar da gabanta yakeyi mata.


Zuƙunnawa dattijuwar tayi saitin inda take, muryarta da gadara tace"bakin ki ne Yaja maki! Nayi mamaki da har kika Iya rayuwa, ay nayi zaton zanzo na same ki awargaje babu rai, amma saboda taurin kai har yanzu numfashin ki bai daina fita ba...." ta ƙare maganar tare da tofa mata yawu mai yauƙi kan fuskarta har cikin idanunta Ya shiga.


"Faɗa da aljani ba riba, wannan somun ta6i ne, nan gaba idan kika kuskura kika sake yunkurin yi min rashin ɗa'a farfesun namanki zansa ayi min shashasha kawai' ta faɗa tare da kai hannu ta damƙi sarkar cross din wuyan gabriellah taja ta da karfi ta shaƙe mata wuya, birgima tadingayi cikin fitar hayyaci ta soma kokarin ceton kanta sai dai ta gaza, dattijuwar bata kyale ta ba har saida taga ta daina motsi jikinta Ya saki tukunna ta ƙarasa balle sarkar ta jefar da ita gefe ɗaya, fatar wuyanta tayi jawur saboda shakar da tai mata.....


Mikewa dattijuwar tayi fuskarta babu fara'a ta sanya ƙafa ta naushi cikin gabriela tsabar rashin imani duk da ta sumar da ita hakan bai mata ba...


Fucewa tayi daga toilet din, ta ba giant umarnin ya dauko gabriellah, yan uwanta na kallo ya fito da ita zindir babu kaya ya ratayata kan kafadarsa suka fice daga dakin, kamar jira suke su tafi gaba daya suka rushe da kuka mai cin rai, haƙiƙa sunji zafin abunda Ya faru da gabriela saboda suna sonta, tana taimakon rayuwarsu wurin kwantar masu da hankali idan damuwa ta addabe su sai gashi yau sun gaza taimakonta sunaji suna gani anci zarafinta an wulakanta rayuwarta.


Allah kadai Yasan Ina zasu kaita? Zata rayu ko ta mutu? 


________________________Gabriel💔


A firgice Ya farka daga bacci, hannunsa dafe da saitin zuciyarsa dake harbawa da karfi da karfi, fuskarsa ta jiƙe sharkaf da gumi.


La66ansa na kerma ya soma ambaton inna lillahi wa inna ilaihirraji'un.


zuciyarsa ce batay masa dadi, kuma yana ji aransa wani mugun abunne ya faru da yar uwarsa dake acan gidan kurkukun ƙaddara, saukowa yai daga kan gadon su, yakai hannu ya kunna switch din dakin haske ya gauraya ko'ina, idanunsa sun cika da kwalla, gaba daya ya rasa meke masa daɗi.



A hankali yake yin tafiya kamar wanda aka zarewa laka sam babu karsashi a jikinsa, toilet ya shiga bayan ya fito ya nufi closet dinsu ya canza kayan jikinsa da jallabiya, kafin ya tsaya kan darduma ya fara jera nafilfili saboda yai mata addu'a.


Bayan ya kammala jiki asanyaye ya ɗaga hannayensa sama ya fara addu'o'i hawaye na wanke fuskarsa


Shesshekar kukansa ce ta farkar da naufal, tunkafin ya bude idanunsa kunnansa suka soma jiyo muryar sajeed Yana fadin"Ya Allah kada ka bari acutar min da ita, Ya Allah ka kare min ita daga sharrin duk wani abun cutarwa...


Da wata irin kasala naufal ya sauko daga kan gadon yaje gefen prayer mat din Ya zuƙunna Yana dubansa.


"Sajeed meke damunka ne naga kana kuka"?


Idanunsa jawur ya kalle sa"Naufal bana jin dadin zuciyata, ina ji araina wani abu Yana faru da gabriela, kwata kwata banyi bacci mai dadi ba"


Dafa kafadarsa naufal yai cikin kulawa da nuna tausayawa yace"meyasa baka ta da ni munyi sallar atare ba"?


"Bana so na takura maka" girgiza kai naufal yayi"babu takura, nima yar uwata ce sajeed, zan iya hana idona bacci don muyi mata addu'a"


Kallonsa kawai yai ba tare daya ce masa wani abu ba.


"bro ba ka tunanin Danish zai Iya taimaka mana? Da alamun ruɗu sajeed ya furta"bangane me kake nufi ba"


Naufal yace"ina nufin me zai hana mu nemi taimakonsa akan ya ɗauko mana yar uwarmu, tun da yana da ƙarfin da zai iya yin hakan"


"tayaya zai iya zuwa gidan kurkukun ƙaddara Ya taimake ta? ni bazan Iya tunkararsa da maganar nan ba, saboda bana so ya sake shan wahala, Za su Iya cutar da shi idan Yaje......." Ya faɗa Yana faman matse kwalla, kafin wani Ya kuma furta kalma sautin motsin buɗe kofar dakin su Yaja hankulansu ga duban door room din, kusan a tare suka zabura suka mike tsaye suna kallon shi babu wanda Yayi zaton shi ne, saboda bai ta6a shigowa bedroom din su ba, watakil Yana ɗan zagaye gidanne Ya jiyo sautin muryoyin su shiyasa ya shigo dakin na su


Har suna baki wurin gaishe da shi cikin girmamawa.


Bai amsa masu gaisuwar ta su ba, gaba daya hankalinsa na akan fuskar sajeed, farar jallabiya ce a jikinsa ta kamasa.


"Meke faru ne"? Ya jefa masu tambayar, da sauri naufal Ya nuna sajeed da yatsa"shi ne ke kuka"


takawa yayi a hankali Ya karasa gaban sajeed yakai hannu ya dafa kafadarsa


"I'm sorry nayi maku la6e, ba hali na ba ne, na fito ina zagaye gidanne sai najiyo voices ɗinku kuna magana, bakomaine Yaja hankalina ba, face sautin kukan ka, fadamin meke damun ka" da wata irin sanyayyar murya mai haɗe da kasalar bacci ya furta maganar


Sajeed bai 6oye masa komai ba, dangane da Sister dinsa, ba zato ba tsammani yaji chief Yai huggin dinsa da hannu biyu kamar kaninsa, tuni yaji wani irin sanyi ya ratsa zuciyarsa kamar an yaye mashi damuwar shi, a hankali chief ya daura hannu daya kan bayan sajeed Yana ɗan bubbuga masa bayan cikin sigar lallashi muryarsa kasa kasa kamar tameyin raɗa ya furta"ka cigaba da yi mata addu'a, Allah Yana atare da su, kuma Yana sane da duk wani hali da suke a ciki, in sha Allah komai yazo karshe, In har sister dinka nada tsawaicin kwana zata rayu ne kamar yadda kuma kuka rayu bayan wahalar da kuka fuskanta....." daɗaɗan kalamai chief ya cigaba da furta masa, ko a mafarki ba su ta6a tunanin chief zai shigo bedroom dinsu balle har ya rungumi ɗaya daga cikin su, sun kara ganin darajarsa da kimarsa a idanun su, sunyi mamakin hakan sosai, mutumin ya ƙara siye zuciyoyin su.

Sai da  ya tabbatar Ya kwantar masa da hankali kafin ya raba jikin su daga na juna.


Fuskarsa da damuwa ya furta"time din sallar asuba yayi, ina jiranku a falo ku shirya mu tafi masallaci, ku sanar da sauran yan uwanku maza" amsa masa sukai da toh, gently ya juya har Ya kusa fita daga dakin muryar sajeed ta ratsa kunnansa.


"Nagode chief, kamar yadda ka faranta min rai, kaima Allah Ya faranta maka naka"


Ba tare daya juyo ya kallesa ba Ya furta"Ameen, but ku kira ni da sunana Owais, zanfi jin daɗi"


Murmushi suka saki atare suka hada baki wurin furta"Yaya Owais" jinjina kansa yai kafin Yasakai Ya fuce daga dakin, wayyo Allah dadi kamar jira suke Ya fita, da sauri Sajeed Ya ruko gaban rigarsa ya soma shinshina kamshin turaren chief.


"Naufal shinshina kaji" shinshinawa naufal yayi sai dadi suke ji

"Wallahi baka ji dadi ba daya rungune ni, sai naji kamar an wanke min damuwana, mutumin Yana da mutunci sosai komai nasa yana burgeni....." santin chief suka cigaba dayi.


Kafin daga bisani naufal yace"yana fa jiranmu zamu tafi masallaci, mu yi sauri mu shirya" 


💘UNAISAH ANGEL💋


kiran sallar asubahin farko, wayarta ta fara ringing kamar zata fasa kunnuwan su, cikin duhu ta farka tare da laluba hannu ta damƙo wayar dake ajiye kan nightstand ta ɗago da ita ba tare da ta duba sunan mai kiranta ba tai picking


"Unaisah! Ina kika shiga inata jaraba kiran layinki bana samu" wata irin zabura tayi aɗan ruɗe saboda bata gane wacece ba.


"Nasan baki gane mai magana ba, Aunty pretty ce"


Ajiyar zuciya ta sauke muryarta da kasalar bacci ta ce "Yanzu na gane, Ina kwana kin tashi lafiya"


"Ki yi hakuri na katse maki baccin ki, na damu da son jin awani hali kike a ciki kwana biyu ba ki neme ni ba"


Muryarta adidashe Tace"ba komai, nima kina araina"


"Ban yarda ba, meyasa baki kara kirana ba? Ni ay fushi ma nake dake, kin manta dani" muryar benazir da alamun 6aci rai tay maganar.


"Ba haka bane wallahi ban manta dake ba, nayi rashin lafiya ne amma yanzu naji sauƙi, wayar ma bata a hannu na sai jiya na kar6e ta"


Tana jiyo sautin muryar aunty pretty tana zabga salati gaba daya ta ruɗe jin bata da lafiya


"Inna lillahi! Yanzu ya jikin naki? da sauki?


Murmushi unaisah tayi jin yadda ta ruɗe"ay na fada maki da sauƙi yanzu"


Tana jiyo sautin ajiyar zuciyar ta

"Har naji sanyi araina, Allah ya ƙara maki lafiya, wallahi baki ji yadda naji ba saboda na damu dake, dan Allah Idan nan abuja kuke da zama, ki bani dama inzo gidan ku, dama yau nakeson fita anguwa" 


waro idanu unaisah tayi da sauri tace"a'a ni ban ma ta6a zuwa abuja ba, a kano mu ke" 


"Allah sarki, kinyi min nisa, in sha Allah wata rana zan kawo maku ziyara"


"Nagode da kulawarki a gare ni" sun jima suna waya kafin daga bisani su ka yi sallama, ta ajiye wayar tana faman sauke ajiyar zuciya, ita kanta tana son haɗuwa da matar sai dai tasan ba abune mai yiwuwa ba, na farko batasan wacece ita ba? Idan har dagaske number da take amfani da ita ta sajeed ce me zai biyo baya?


da wannan tunanin ta sauko  daga kan gadon ta kunna hasken dakin nasu


a hankali ta sauke idonta kan Deeja dake bacci tana jan minshari kwatsam taga ta fara mirginawa zata faɗo ƙasa daga kan gado, cikin zafin nama ta yi hanzarin tallabota a hankali ta wurga ta kan mattress din


Murmushi ta dan saki kafin ta juya ta shiga toilet, har yau tana mamakin jinin daya dauke mata tun bayan da ta sha bakar wahala bai dawo ba, har cikin ranta bata ji dadi ba, saboda taji ance alamun girma ne ga mace, kuma idan tanayi boobies ɗin ta zasu kara cukowa sannan hips dinta zai ƙara faɗaɗa komai ma na jikinta zai canza ta zama cikakkiyar budurwa, a gaban sink ta tsaya tana lalubar wurin don taga idan za'a samu ko da alamunsa ne sai dai bata ga komai ba...." fuskarta ayamutse ta kalli mirror kamar zata fasa ihu haka take ji, ita da take son ta zama house wife idan har bata fara wadannan abubuwan ba ina ita ina iya zama matar aure? ta faɗa aranta, kafin ta sa hannu ta zame wuyan rigar baccin ta, ta soma leƙen kirjin ta, murmushi tayi ganin sun ƙara girma ba laifi, wani irin dadi ne Ya lullu6e ta, har yau bata bari danish ya gan su ba, saboda kullum in zata sanya kaya sai ta ɗaure su tamau don karsu fito.


jujjuyawa ta yi agaban mirror din tana kallon qugunta, ni dai na rasa me angel take ma zumudi, da alama batasan meye ake azaman auran ba.


Gaba ɗaya matasan gidan sun tafi masallaci, bayan sun kammala sallah shiekh imam ya zaunar da su don suyi karatun da yake biya masu kullum.



Fitowa yai daga bathroom, waist dinsa daure da towel fari, gaban dressing mirror Ya tsaya zuciyarsa cike fal da tunanin halin da sajeed ke aciki, saboda Ya damu da yaran musamman wadanda ke acan gidan kurkukun ƙaddara sun tsaya masa a zuciyarsa, ayanzu baya da wani buri da ya wuce su kai masu ɗauki, shaf shaf Ya shirya kanshi cikin dark jeans tare da v neck shirt ta ɗame fatarsa.


Hayewa yai kan gadonsa ya daura kansa bisa pillow, hannunsa ruke da wayarsa, layin Boss Ya danna ma kira bayan yai picking suka gaisa da juna


"Inason ganinku, tare da salsabeel a room dina" amsa mashi boss yayi da toh"


Bayan wasu ƴan mintuna, wayarsa tai alert, unclock Ya danna a hankali kofar ta buɗe suka shigo su uku, cikin girmamawa suka gaishe da shi ya amsa masu


"Have a seat" ya fada Yana nuna masu couch, zama sukai suna fuskantar sa... Ya ɗan dauki lokaci kafin ya dan bude idanunsa dake a lumshe ya dubesu daya bayan daya kafin ya tsayar da idanuna akan salsabeel


"me yakamata mu yi? bana son abun yadau lokaci, ko dan saboda sauran yaran dake fuskantar barazana da buƙatar mu kai masu dauki....." babu wasa akan fuskarsa yai maganar



Calmly Salsabeel Ya fara magana"yalla6ai, ni bani da hanyar da zan iya jagorantar mu zuwa gidan kurkukun ƙaddara, saboda garkuwar sihirina ta karye kuma ina da tabbacin daga wajen su ne suka yi min hakan, amma nasan ɗan uwana zai Iya taimaka maku, shi kadai ne yasan hanyar da zai shigar daku Gidan kurkukun ƙaddara amma fa dole mu bi komai asannu kada muyi gaggawa saboda gidane mai hatsarin gaske, wani irin kurman ginine idan har baka da ilmi akansa kai kuskuran shiga kwakwalwarka zata iya ta6uwa"


Jin wannan maganar daga bakin salsabeel Yasa Taj da big guy suka kalli junansu da alamun rudani.


"Amma idan har Garkuwa ne zaiyi maku jagora shi ya san ta yadda zai shigar daku ba tare da kun sha wahala ba, amma fa da wuya danish Ya bamu haɗin kai, mutum ne mai wuyar sha'ani yana da kafiya, kuma har yanzu shi garkuwar su ne zasu iya sarrafa shi daga can kurkukun, ni dai ashawarata tun yanzu ku fara jan shi a jiki kuna koya masa abubuwa masu mahimmanci kamar rubutu da karatu tun da baisan komai ba ta hakanne zai fara sakin jiki da ku har asamu abun da ake so" gaba ɗaya sun gamsu da bayanin salsabeel.


Numfasawa chief yai kafin ya ce"in sha Allah zamu yi ƙoƙarin jan shi a jiki,"


Big guy yace"ni abunda ke ɗaure min kai da yaron kwata kwata baya son mutane su rabe shi in ba yan uwansa ba, kuma baya son wani ya rabi yan uwansa, meyasa"? ya tambaya yana kallon salsabeel


"Rashin sabo ne, idan Ya saba da ku zai daina, amma fa da buƙatar ku guji bata masa rai, in har ya nuna baison abu to kada ayi masa in ba haka ba komai zai iya faruwa, idan ransa ya 6aci evil heart ɗinsa zata iya motsawa abun da bana fata" ta6e baki big guy shi dai har yanzu bai yarda da Danish ba.


Shiru sukayi na wani lokaci


"I understand that dealing with them won't be easy." gaba ɗaya suka maida duban su ga chief da yai maganar


"in sha Allah, zamu yi zaman tattaunawa tare da chief of army, da kuma commender na america, bayan haka za mu tuntubi rassan jami’an ISOD da ke wasu kasashen, saboda taron ya shafi kowa da kowa. Dole ne mu hada kai kafin mu ci nasara a kansu. "


"Haka Yakamata yalla6ai" suka fada atare


Lumshe idanunsa yai gaba daya sun fahimci damuwar abunne ke addabar zuciyarsa


A lokacin da basuyi tsammani ba suka ji ya furta"na rantse da wanda raina ya ke a hannunsa wallahi duk wanda na kama da sanya hannunsa a kungiyar matsafan kurkukun ƙaddara sai ya ɗanɗani kuɗarsa ko da kuwa mahaifina ne bazan raga masa ba, ..., " yayin da yake yin maganar idanunsa sun kaɗa jawur saboda tsantsar 6acin rai


"In sha Allah sir mahaifinka ba zai ta6a zama ɗaya daga cikin su ba..." kafin taj ya ƙare maganar chief yai hanzarin katse sa yana huci yace"nima ina fatan hakan amma nasan mawuyacin abune, boss bana son na zurfafa bincike saboda fargaban kada inga wanda banyi tsammani ba, Ina jin tsoron ace akwai sanya hannun wani a family dina zuciyata zata karaya watakil ma hakan zaiyi silar da zuciyata zata buga...." ba su ta6a ganin tashin hankali tsantsa akan fuskar chief irin na yau ba, kwata kwata babu walwala atare da shi 

Hada baki sukai wurin kwantar masa da hankali suna bashi baki, dakyar suka samu ya lafa yana faman sauke ajiyar zuciya ya kifa kansa jikin pillow... Bai sake dagowa ba, kamar bacci ne yai awon gaba da shi.


Miƙewa sukai atare suka bar dakin, zuciyoyin su cike fal da tashin hankali, su kansu tsoron ranar da asiri zai tonu suke yi saboda sun san dole akwai na jininsa, a kwanakin baya ya ta6a basu labarin kiran sirrin da wani bawan Allah yake yawan yi masa akan Ya binciki danginsa akwai bara gurbi acikin su wadanda suke sadaukar da yaran family ɗinsu har faɗa masa yai yaran da ake haihuwar su a mace ba mutuwa sukai ba suna nan da yaransu, bai ta6a maida hankali akan mutumin ba sai bayan da prisoners suka bayyana tukunna Ya fara gasgata maganar mutumin da har yau baisan wanene shi ba..."


Abakin kofar dakin nasa suka dakata da yin tafiya suna kallon junansu damuwa ce ƙarara akan fuskokin su kowa da abun da yake saƙawa aran shi sam sun kasa magana daga bisani suka fuce.



Chief Har ya fara nutsawa cikin baccinsa Wayarsa dake ajiye kan drawer ta fara ringing kaitsaye sautin ya daki kunnansa


A hankali yadan bude idanunsa wadanda ke lullu6e da yalwar gashi ya kalli ceilling din dakin kafin miƙa hannu ya ɗauki wayar


Motsa la66ansa yai tare da furta sunan Uncle hateem.


Picking call din yai


"Uncle am sorry, jiya na shiga bedroom dinsa na taras yana bacci shiyasa ban kira ka,"


On the other hand prime minister yace"Son ka hanani ganin maganin da zai warkar min da zazzabina....."


"Sorry uncle nayi laifi ay min afwa"


"It is okey, yanzu yana ina ya farka daga bacci"?


"Yanzu zanje bedroom dinsa na duba sa"


"Okey, akwai sako da za'a kawo masa daga company.." tun kafin ya ƙare maganar chief ya furta"uncle wani sako kenan"?


"Idan an kawo zaka gani, nasan idan na fada maka ba zaka bari sakon ya iso ba, zaka hana ne"


"Haba uncle, ni na isa in hanaka yin alkhairi..."


"Hakane, amma bazan fada ba" ya faɗa da zolaya


 murmushi chief yai"andai hanani jin menene bakomai in an kawo zan gani, bari naje na basa ku yi magana"


"Video call zamuyi zanfi jin dadin ganinsa" amsa masa yai da okey, janye wayar yai daga kunnansa Ya nufi desk ya dauko ƙaramar laptop dinsa Ya sauko down babu kowa sai masu aiki dake zaryar kai abinci kan dining,  ta elevator ya hau ta sauke sa second floor........


Abakin ƙofar ya tsaya yai masa knocking, shiru ba abasa iznin shiga ciki ba, yanke shawarar shiga yai a hankali ya tura kofar a zaton sa bacci yake yi, yana shiga ciki yaji alamun motsinsa a toilet, har ya juya zai fita da niyar anjima zai dawo sai kuma yaji an bude ƙofar, fitowa yayi daga ci ki jikinsa asanye da kayan baccin sa


Ganin mutum adakinsa Yasa shi cin burki ya tsaya yana kallon bayansa cike da mamakin wanene ya shigo masa bedroom dinsa...


A hankali chief Ya juyo suka fuskanci juna, nan take danish ya ƙara daure fuskarsa tamau babu annuri.

 

Takawa yai zuwa gabansa Ya miƙa masa hannu don su gaisa, maƙe hannunsa yai alamar bazai bayar ba, 


"Ba ay min haka" ya fada tare da sanya hannu ya janyo danish yayi huggin dinsa kamar zai maida sa cikin sa, kamar wani mugun abu ya rungumesa sai kankame jikinsa yake yi, bayan chief ya raba jikinsa daga nasa ya soma yi masa magana.


"Barka da safiya, Ina fata ka tashi lafiya" shiru yayi bai tanka masa ba, wani kallon ƙasan ido yake jifa masa da ace chief baisan halinsa ba da sai yace ya tsane sa


"Ba magana? Ko da ya ke nima dalili ne Ya kawo ni roon dinka, kar6i nan uncle dina ke son magana dakai" ƙin kar6a yayi,


"Ina nufin uncle dina Hateem, mutumin dana hada ka da shi shekaran jiya, ina fata ka tuna sa" zare masa idanu danish yayi, sarai ya fahimci wa yake nufi abun da bai gane ba ta ina za suyi magana da uncle din nasa?


In a low voice ya furta"yana ina"?


Miƙa masa laptop din yai" anan zakuyi magana da shi ta video call"


wani kallon rainin wayau danish yai masa arude ya furta"tayaya zanyi magana da shi ta wannan abun" ɗan zaro ido chief yayi, can kuma ya saki fuskarsa tunawa da wanene shi


"Oh okey na fahimta lemme show you yadda zaku yi magana" bayan ya kira hateem video call fuskarsa ta cika laptop screen din, juyama danish ita yayi"look at him ku yi magana"


har saida danish Yaso Ya firgita lokacin da ya sauke idonsa kan laptop screen din ganin fuskar hateem mai ɗauke da murmushi, muryarsa cike da nishadi Yace"my baby boy danish, ka tashi lafiya? Ya ka kwana jiya? Ka yi kewana kuwa ko kuwa ka manta dani" yatsun hannun sa na kerma Ya kar6i laptop din daga hannun chief Ya kura ma hateem ido yana kallonsa batare daya furta komai ba, shi mamakinsa tayaya har ya bayyana akan wannan abun?


"Ka zauna ku yi magana" chief ne Ya fada tare da nuna masa gefen gado, jiki na bari yaje ya zauna yaci gaba da kallon hateem dake ta faman sakar masa murmushi


"Ka yi shiru baka tanka min ba, ko dai kamanta dani ne? Fadamin sai in tuna maka" shiru yayi bai masa magana ba, mamakin duniya ya cikasa


Chief dake atsaye ya harɗe hannayensa kan kirjinsa sai kallonsa yake yi zuciyarsa cike fal da tausayin rayuwarsa baiyi tunanin tsayawa ya kammala wayar ba sai ya juya ya fita daga dakin.


"Bazan damu ba, kallon da kake yi min ya tabbatarmin da ka gane wanene ni, shekaran jiyama da muka fara haduwa sai da nasha wahala kafin Ka yi min magana" ya faɗa yana murmushi.


"Nakasa jurewa ka tsareni da wadannan kyawawan idanun naka please ko da zagina ne kayi ni dai burina naji muryar nan taka mai kwantar min da hankali, chief bai fada maka nayi zazzabin rashin ka ba"? Ya fada yana marairaice masa fuska alamar zaiyi kuka...


Yana faman furzar da numfashi Ya dan motsa la66ansa kamar baison furta maganar yace"ina son ganin ka"


"Ba ga ni kana gani na ba" girgiza kai danish yai alamar a'a


"Ka fito kazo nan dakina" 


"No bazai yiwu ba, ay bana kasar yanzu ina canada kai kuma kana nigeria, sai na hau jirgi tukunna zan iya zuwa wurin ka" hankali atashe danish Yace"a'a ni dai kawai kazo ka fito daga wannan abun ina son ganinka" waro idanu hateem yai da alamun ruɗani akan fuskarsa.


"Ba yadda za'ae na fito, laptop ce fa, baka ga ƙarama bace taya ni da nake babban mutun zan fito ta cikin ta" kamar zai sanya masa kuka yace"ni dai kazo ina son ganinka" ya fada yana shafa laptop screen din a kokarinsa naya gano kofar da zai buɗe wa prime minister Ya fito waje.....


Chief owais Na awaje Yajiyo sautin fashewar wani abu daga dakin danish....




*Daga Alƙalamin Boss Bature💋✊✍️*



 *Littafin kurkukun ƙaddara 500 ne, dukanshi Book One two and 3 Idan kin shirya biya ga Details da zaki tura*


3196407426


First bank 


Bature Hafsat Muhammad,


 *bayan kin tura zaki bada transaction reciept ko screenshot na debit alert a matsayin shaida ta wannan layin 08169856268*

Post a Comment

Idan kuna da tambaya akan abinda Baku game ba ko kuma kuma Neman littafin da babu a nan kawai ku ajiye tambayarku a ta comment ko wani shawara da Zaku bamu.

Previous Post Next Post

Sponsored Link

Sponsored Post