Kurkukun Kaddara Takun Karshe Episode 28 Hausa Novel - Novels Elite

Kurkukun Kaddara Takun Karshe Episode 28 Hausa Novel - Novels Elite

Novels Elite English

 ___________________________________✍️

"Yaya shurem wani abu ya faru ne"?

Tun daga farkon abun da ya faru bayan komawar su gida ya fara sanar da ita kafin ya ƙara da cewa"Yanzu haka da nakeyi maki magana muna a asibiti, an kwantar da ita, cos She is completely unconscious, sunan mijinta da ƴarta kadai take fadi, kuma dr ya tabbatar mana da cewa she is suffering from depression and panic attacks, sannan in har bata samu abun da take so ba zamu Iya rasa ta...."



kusan suman tsaye Aneelerh tayi jiki asanyaye ta sulale daga jikin motar ta zuƙunna, idanunta cike tab da ƙwalla take ambaton inna lillahi wa'inna ilaihirraji'un! A kalla ta ambaci hakan yafi sau a kirga, zuciyarta da matsanancin karfi take bugawa kamar zata fasa kirjin ta...


"Aneelerh ku ta yamu da addu'a, benazir taci wahala banaso narasa ƴar uwata.... " cikin rauni na murya yayi maganar


Zuciyarta ce ta raya mata me zai hana ta sanar da shi zancen Yarinyar da suke hasashen unaisah ce ko dan hankalinsu Ya kwanta..


Da sauri tace yaya shurem akwai abunda nakeson sanar dakai, duk da bani da tabbaci...." 


Cikin rauni na murya ya furta menene? a tsanake Aneeelerh ta kwashe komai ta sanar da shi


"Yanzu haka muna abakin estate din ba'a kaiga ba mu izinin shiga ciki ba, kaga idan Ya tabbata unaisah ce shikenan Zamu samu maslahar ciwon benazir...."


Tana Iya jiyo Sautin ajiyar zuciyar dr shureim"Aneeelrh baki Ji yadda naji ba, Ubangiji Allah Yasa adace, Dan Allah Duk Yadda ake ciki Ki sanar dani....."


"In sha Allah Yaya Shureim zaka ji daga gareni, awani asibiti ne aka kwantar da ita"?


Yace"Obie International hospital"


"Ubangiji Allah Ya tashi kafadunta, in sha Allah zamuzo dubata, Allah Ya bata lafiya" bayan sunyi sallama hawayene suka wanke fuskar Aneelerh

"Aunty Aneelerh meya faru? Su zahrane suke tambayarta

Cikin shessheƙar kuka ta kwashe komai ta sanar da su, gaba ɗaya jikinsu yayi sanyi zuciyarsu ta karaya, musamman Aneeleerh wadda tuni ta sulele jikin motar ta zuƙunna tare da kifa kanta tsakanin cinyoyin ta...


_______________________________✍️



Bayan dr shureim Yai sallama da Aneelerh, ɗagowa yayi da idanunsa wadanda suka kaɗa jawur da su shi kadai ne tsaye a corner din da yai wayar, jiya izuwa yau gaba ɗaya ya fita hayyacinsa sam babu nutsuwa a tare da shi, Fatan shi Allah Yasa su Aneelerh suyi nasarar gano yarinyar nan kuma Allah Yasa ƴar benazir din ce da kuwa yafi kowa farin Ciki da hakan.


Wani abu da ya ɗaure masa kai a binciken da likita yai ya bayyana masu cewa akwai wani abu da ya haifar mata da matsanancin tsoro lokaci ɗaya Ya fara tariyo maganar maminsu lokacin daya shiga dakin take fada masa halin da suka samu benazir ta faɗi ƙasa rabin jikin ta a cikin toilet har kanta Ya daku❗


Tuna wannan Ya shi Zare idanunsa, zuciyarsa na harbawa da ƙarfi dama sai da yai fargaban faruwar hakan shiyasa ya kwana abakin ƙofar ɗakin ashe duk da haka sai da aka kai mata hari! Duk da bai da tabbacin abunda Yake zargi Ya yanke shawarar zai jira har zuwa lokacin da benazir zata dawo cikin hayyacinta don Yaji ainihin menene yayi silar faɗuwarta ƙasa❗❓


Cike da rashin kwarin Jiki Ya Nufi Medical room din da aka kwantar da benazir a Emergency depertment tun kafin Ya karasa Ya hango zeenatu abakin door room din tana sharar kwalla, baiwar Allah duk ta fita hayyacinta damuwa ta hanata sukuni

Har ya ƙaraso Bata lura da da shi ba, saboda ta rufe fuskarta ta tafukan hannayenta.


"Zeenat! Ba nace ki daina kuka ba?"? Sanyayyar muryarsa ce ta katse mata kukanta, 

Idanunta jawur ta dube shi"yaya shureim hankalina bazai ta6a kwanciya ba in har aunty benazir bata dawo hayyacin ta ba..." ta faɗa tana jan numfashi

"dan Allah Yaya shureim ku nemo mata babynta da mijin ta, ni bana so na rasa ta, ni kawai zan ma daddy magana yasa a nemo mata su nasan zai iya. ..."

Ruƙo hannayenta yai acikin nashi"kiyi hakuri ki daina kukan Ya isa haka! Idan har dagaske kin damu da halin da take a ciki, to kiyi mata addu'a Allah Ya bata lafiya, hakan ne zai tabbatar da kaunar da kike mata.." la66anta na kerma ta fara karanto addu'o'i 


"Mu shiga daga ciki" ya faɗa tare da ruƙo hannunta suka shiga room din.


Su Hajiya sarah suna zaune kan kujerun dake fuskantar gadon da benazir ke akwance, babu wani mai kwanciyar hankali a cikin, musamman hajiya layla, fuskarta tayi jawur tsufanta Ya fara bayyana duk ta yamutse kamar itama bata da lafiyan.



Duk sun zuba ido suna kallon benazir wadda tun da likita yayi mata allurar bacci take ta yin shi, har wani firgita take yi kamar mai yin mafarki duk da karfin allurar cikin magagin bacci take ambaton sunan mijinta da yarta saboda sune aranta, baiwar Allah ba karamin jiki taji ba, la66anta sun bushe ƙamas tayi haske kamar ba jini a jikinta, kwarin idanunta sunyi ja da su...


Agaban gadon dr shureim da zeenatu suka tsaya suna kallon ta gwanin ban tausayi, da ace suna da halin da zasu Iya cire mata ciwonta ya dawo jikin su da tuni sunyi hakan...


Wayar hajiya sarah dake a cikin purse ce ta fara ruri da sauri ta curo wayar ta duba sunan mai kiranta My boss wato Alhaji musa.


Picking call din tay ta kara wayar a kunne ko sallamarta bai amsa ba, da kakkausar murya ya ce


"Kin manta Yau kina da aiki a office"? Bata bashi amsa ba, da sauri ta miƙe ta fito daga dakin

Kafin tace"ban manta ba, I'll inform my secretary that I won't be going to work today na ɗauki hutu har sai benazir ta samu lafiya, ay nayi zaton ka kirane don kaji halin da ake ciki game da lafiyarta..." kafin ta ƙare maganar Ya katse da cewa"karki kuskura ki ƙara yi min magana kan benazir! Idan har ba so kike ranki Ya 6aci ba..." ranta Ya 6ace a hasale tace"wai meke damunka ne? Yarinyar nan fa yar yayanka ce, ɗiyarka ce, meyasa kake nuna halin ko'in kula akanta? Sai kace ba jinin ka ba..."? Daƙyar ta ƙare maganar jin wata tsawa da ya daka mata muryarsa da 6acin rai Ya furta"zaki dawo gida ki sameni! Har ni kike ma magana kina ɗaga min murya? Kina cikin hankalin ki kuwa"?yawu ta haɗiya Muryarta adabarbarce ta furta"i'm...so sorry" bata ƙare maganar ba Ya furta"ki faɗawa shurem ya dawo da zeenatu gida, ke kuma zaki zo ki same ni" Duff Yai rejecting call din.


Ya Salam! hankalin ta idan yai dubu toh Ya tashi, bata ta6a hasala shi irin na yau ba, duk tabi tasha jinin jikinta, fargabanta kada taja ma kanta.


_____________________________✍️


Prisoner's shield 👊❤



A hankali Ya ware idanunsa masu ɗauke da bacci da wata irin kasala ya yunkura ya miƙe haɗi da jingina bayan shi jikin pillow, wani irin lalaci yake ji tun karfe 12 bai leƙa ko kofar dakin sa ba, bacci kawai yakeyi, kamar baya jin dadi, short ne kaɗai a jikin shi launin ja, sumar kan shi ta rufe gefen fuskarshi kamar baccin bai ishe shi ba...


Da wani irin kewar unaisah Ya farka, har mafarkinta sai da yayi, sai faman lumshe idanunsa yakeyi, kwatsam hasken ɗakinsa Ya ɗauke ɗuff kamar an kashe switch din dakin Sam bai lura ba ko'ina yayi duhu kamar dare


"Garkuwa namu!...."! cikin kunnansa Yaji wata murya mai kama da ta dattijuwa ta ambaci sunan shi, yayi zaton gizau muryar ke yi masa shiyasa bai mayar da hankali akai ba


"Shield! Shield!! Shield!!! Rass Yaji gabanshi Ya faɗi, A hanzarce Ya buɗe reddish eyes dinsa sosai, a matuƙar ruɗe, sam Ya gaza believing da abun da kunnuwansa suke Jiyo mashi


Durowa yayi daga kan gadon Ya soma bin ceilling din dakin da kallo, a kokarinsa naya gano ta inda sautin muryar ke fitowa.


A hankali Yake bin labulayen ɗakin da kallo farat ɗaya zuciyarsa ta raya masa hanya ɗaya ce zai Iya ganin me Yi masa magana...


A hanzarce Ya juya Ya kalli inda madubin dakinsa Yake, wanda tun da jimawa Unaisah Ta rufe masa shi da towel saboda ta gane baison ganin mirror


Walking slowly Ya nufi gaban madubin Yakai Yatsun Hannunsa dake kerma Ya Yakice Towel din Ya jefar da shi


Kyawawan idanunsa Ya ɗaura akan mirror din duhu ne Ya mamaye cikin sa baka Iya ganin komai....


La66ansa na kerma Ya furta"KHALA❗❓..."  sautin dariyarta ne Ya karaɗe ɗakin nashi daga ji tsohuwace tukuf


"Garkuwarmu ko da Yake Yanzu Ka koma Garkuwarsu....' A hankali ta bayyana ta cikin duhun madubin kamar Yana kallon tv tsohuwa ce tukuf ta rufe ko'ina na jikinta da fararen kaya ko fuskarta baka iya gani sai dai idanunta da suka kasance farare ƙyal launin reddish irin nashi


Muryarsa na rawa Ya sake maimaita sunanta Khala


"Bani da isasshen lokaci yin magana!" ta faɗa tana kallon cikin idanunshi


"Inaso nima na bada gudummuwata wurin ganin kunyi nasarar ruguza tarihin kurkukun ƙaddara ...." da tsantsar mamaki yake kallon dattijuwar


Cikin harshensu na matsafa ta soma kora mashi jawabi...." a karshe ta furta"I'm waiting for your attack! Don't take time, the lives of the other prisoners are in danger!" (Ina Jiran farmakin ku! kada ku dauki lokaci, rayuwar sauran fursinonin tana a cikin hatsari)..." har Ya buɗe baki zaiyi magana ɗuff madubin Ya dawo suffarsa ta ainihi, da sauri Ya kawar da idanunsa daga kallon mirror din Ya ɗauko towel din daya jefar Ya lullu6e shi.


Jikin shi har tsuma Yake Yi, numfashin shi da hucin zafi Yake fita, Sam Ya gaza matsawa daga gaban madubin, muryarsa da tsantsar al'ajabi Ya ke maimaita sunan JEREMIAH his childhood friend as the new prison shield gaba ɗaya He was extremely confused, Tashin hankalin da ba'a saka mashi rana har wani tangyal tangyal yayi kamar zai faɗi dakyar ya iya tsayar da kansa bisa kafafunsa abunne Ya daki heart dinsa...❗


A cikin bayanan da dattijtuwar ta sanar da shi hada kwanan watan da za su yi black night ! Shin wacece Khala!?? Baku tunanin tarko ne za'a ɗana masu!? in ba haka ba tayaya matsafiya wadda take rayuwa acikin gidan kurkukun kaddara zata neme sa da sunan bashi gudummuwar tarwatsa kurkukun ƙaddara❓


Knocking kofar room dinsa akai da sauri Ya daidaita nutsuwarsa kamar wani abu bai ta6a faruwa ba...


Yayi zaton unaisah ce sai da yaje gaban kofar ya buɗe karaf idanunsa suka sauka akan chief owais Ya ɗauki wanka cikin shiga ta kakinsa Yayi shirin zuwa Office, from head to toe Ya kalle sa kafin Ya haɗe fuskarsa bakomai Ya tuna ba face unaisah da ya gani adakinsa jiya shiyasa ya ƙarajin haushin mutumin


Chief owais baibi takansa ba Ya nufi cikin dakin hannunsa ruƙe da shopping bag, Ya dire masa ita kan gadon shi


A hankali Ya juyo suka fuskanci Juna


"Ba ka Iya gaisuwa ba ne"? wani ɗan iskan kallo danish Yayi masa


Murmushin gefen fuska chief Yai


"Laifin me na maka kamar baka kaunar gani na"? 


Shiru yayi bai tanka masa ba


Da ace chief yasan unaisah ce Silar dayasa danish Yake haɗe masa rai ay da tuni Yayi masa bayanin da zai kwantar masa da hankalinsa don shi A yanzu mace bata agabansa, burinsa ya gano miyagun gidan kurkukun ƙaddara da kuma kawo karshen su shi ne abunda Yasa agaba


 kallon shoppin bag din yai alamar yana neman ƙarin bayani yaga bakon abu adakin sa


"It's a gift from Uncle Hateem. Please don't break them they're not toys," he said jokingly. tare da buɗe jakar ya soma fiddo da kayan cikin ta


 "suna da amfani, idan ka bani dama zan nuna maka yarda zakai amfani da su" cikin lallami yakeyi mashi magana


Ganin Yayi tsaye Yaki matsowa Ya duba kayan, Yasa chief Tunkararsa Ya ruƙo hannunsa Ya janyo shi har bakin gadon


"Zuwa anjima zan ware mana lokaci in fara koya maka Yadda zakai amfani da su ko baka so"? Yai maganar Yana dubansa sai wani shan mur Yake.


Daurewa kawai cheif yakeyi amma fa ya fara hasala da halin danish kwata kwata baya sakar masa fuska kuma Yaƙi magana da shi, in banda ma Yana neman alfarma awurinsa ay da bai kai matsayin da chief zai kulasa ba


Fucewa yai daga dakin Ya Bar danish a tsaye Ya kasa ta6uka komai, zuciyarsa har yanzu bata daina ambaton sunan jeremiah ba, kalaman tsohuwa Khala sun tsaya masa aransa sai yake ganin kamar amafarki ta bayyana..


zama yayi gefen gadon Ya zubawa kayan ido har cikin rashi Yaji dadin jin cewa Hateem ne Ya bashi kyautarsu, duk da baisan amfaninsu ba amma sunyi mashi kyau, bai ta6a ko ɗaya ba, ya yanke shawarar sai unaisah tazo zasu buɗe su atare


________________________________✍️


*ANEELERH*


"Mu tafi asibitin kawai, bazan Iya jurewa ba...." gani take kamar zata rasa benazir, shiyasa ta hakura da shiga estate din

Su mahoob daman hanyar da zasu tafi suke nema, jiki na 6ari Ya buɗe motar Ya zauna a driver's seat, Aneelerh ta shiga ciki, Zahra na kokarin shiga kwatsam ta hango dankareriyar motar dake tunkaro estate din dakatawa tayi saboda ranta na bata cewar Motar Hajiya saratu ce....


"zahra ke muke jira ki shigo mu tafi" acewar mahboob

"Kaɗan jira, naga kamar motar Hajiya saratu ce ke tunkaro estate din..." jin wannan maganar yasa Aneelerh yin hanzarin fitowa daga motar shima mahboob Ya fito duk suka ƙurawa motar ido cike da sa ran ganin wanene a cikin ta


Lokacin da motar ta kusa ƙarasowa dab da inda suke gudunta ya ragu slowly window glass dinta na back seat Ya zuge hakan Ya basu damar ganin na cikinta

Wata irin nauyayyar ajiyar zuciya zahra ta sauke mai haɗe da annurin farin ciki

Ita kanta Aneelarh ajiyar zuciyar ta sauke haka shima mahboob duk da basu ta6a ganinta ba Yau ne rana ta farko da suka fara ganinta ido da ido

A hakimce take zaune cikin motar, ta ɗauki wankan lafaya, idanunsa na a manne da farin glass ba karamin kyau yayi mata ba


Da alama su take kallo, Umarni ta ba security din dake driving dinta idan sun karasa kusa da motar su zahra yai parking, ya amsa mata da toh 


Daga bayan motarsu zahra yayi parking din motar, jiki na 6ari zahra ta nufe ta, a lokacin ta bude car door din ta zuro kafarta ɗaya waje

Sallama tayi mata cikin girmamawa tace"sannu da zuwa mommy, ya gajiyar aiki...."


Fuskarta da fara'a ta furta"lafiyalou daughter, zuwan bazata akai mana? Amma ya akai naganku a waje..." 

Zahra kamar zatai mata sujjada tsabar yadda take magana cikin ladabi da biyayya


"Masu tsaron gate din ne suka hana mu shiga sunce dole sai an basu izni, har layinki na kira baya shiga nasan kin shiga busy ne..."


"Eyyah! Na sanya wayar a silent lokacin da zan shiga meeting...' tai maganar tare da kai dubanta ga su aneelerh"su wanene? Ina fata dai lafiya? Ta fada cike da son jin karin bayani


"Auntyna ne da ƙanina mahboob, wani abune mai mahimmanci Ya kawo mu .." 

da sauri Aneelerh da mahboob suka karaso bakin motar hajiya saratu cikin girmamawa suka gaishe da ita, fuskarta asake ta amsa masu wato sunci albarkacin zahra shiyasa ta sakar masu fuska


"Pls kuyi hakuri sun shanya ku arana, Yanzu ku shiga motar, mu tafi.  " wani irin dadi Ya lullu6e su, da sauri suka nufi motarsu, bayan sun shiga a jere motocin suka nufi cikin estate din babu wanda yayi gigin dakatar da su cikin securities din sai ma gaisuwar da suke mika ma hajiya saratu wadda ko kallo basu ishe ta ba.


Bayan sunyi parking, kowan nan su Ya fito, Aneelerh sai faman satar kallon katafaren estate din takeyi kamar a dubai, Inaga mahboob wanda Yake ta jinjina kai aranshi Yace"Wai dama haka daular obie estate take? Gari guda, Tabɗijan Daga gani anyi almubazzaranci wurin ginasa, Mutane kamar bazasu mutu subar duniya ba? Yo ni Allahna na tuna ko amafarki ban ta6a ganin katon gini irin wannan ba! Kai jama'a..sai faman santi yakeyi acikin ranshi

Gaba hajiya saratu tayi da sauri suka bi bayanta, zahra hada kar6ar handbag dinta ta ruƙe mata ita, irin fadancin nan

Ashe mahbbob baiga komai ba, suna shiga falon kiris Ya rage ya zabga salati saboda ganin makurar kayan alatun da aka baje ta ko'ina...har wani zazzabi yake ji ajikin shi

Ga masu aiki dake kai komo cikin uniform

"Bismillah ku zauna, Ku ɗan bani mintina kaɗan, Yanzu zan fito..' amsa mata sukai da toh, ta nufi daki zahra tabi bayanta don ta kai mata handbag dinta..

Ya rage saura mahboob da Aneelerh, zama sukai akan tamfatsa tamfatsan royal sofa din falon...

"Karshen duniya yazo aunty aneelerh" ya faɗa yana kishingiɗa bayansa jikin sofa, duk da halin damuwar da Aneelerh take aciki sai da ɗan murmusa jin abunda Mahboob Yace, ita kanta ta girgiza da ganin katafaren ginin

"Alhamdulillah Ya Allah.."ta furta aranta"Ya Allah kamar Yadda ka bamu ikon shiga gidan nan lafiya, Ya Allah ka bamu ikon ganin Yarinyar nan cikin sa'a ba tare da mun sha wahala ba" har cikin ranta wani irin sanyi takeji, fatanta Allah Yasa su dace

Kallon mahbbob tayi wanda ke ta bin ko'ina da kallo baki asake kamar lehen sakarai

"Mahboob! Pls kaja aji mana, kada kai mana kauyanci, duk fa abinda suke da shi mu ma muna shi agida...." tashin Farko Ya ce"muna da lifter..? murmushi aneelerh tayi"a'a amma ai akwai stairs ko"?

Girgiza kai yai"ba irin wannan ba duba fa kiga ni har hawa uku, ga yan aiki ta ko'ina..." murmushi tayi tana kallon shi" nifa aunty aneelerh bawai kyawun gidanne Ya ruɗe ni ba, no kawai almubazzarancin da akai wurin ginasa shiyafi komai 6ata min rai, Allah ba karamin mai imani bane zai zauna agidan nan kuma yaci gaba da yin sallah..." yar dariya Aneelerh tayi 

Kafin wani Ya ƙara magana sofia ta nufo wurinsu hannunta ruƙe da tray na cool drinks tare da snack ta ajiye masu kan table

"Inayi maku barka da zuwa" amsa mata sukai da yawwa 

"Hajiya saratu ce, ta bada umarnin akawo maku drinks, idan akwai abun da kuke bukata ku sanar dani..." har suna haɗa baki furta"a'a mungode,

Bayan ta bar wurin Mahboob Yace"munci darajar Zahra wlh da ko kallo bamu ishi matar can ba, daga ganin ta zatai ji da kai..."


Bayan wasu Ƴan mintuna, Hajiya saratu ta fito har ta canza kayan jikin ta, wata hadaddiyar abayace ta sanya, zahra na abiye da bayanta har suka karaso, zama tayi kan sofa tana fuskantarsu, itama zahra ta zauna.


Ƙara gaisawa sukayi kafin ta ce"Zahra ta faɗa min abune mai mahimmanci Ya kawo ku! ina sauraronku..." cike da dattako tayi maganar.


Gyara zama Aneelerh tayi cikin nutsastsiyar muryarta ta fara kora mata jawabin abun da Ya kawo su...


bayan ta kammala hajiya saratu tayi jimm na ɗan wani lokaci kafin ta dubeta"kun tabbata Yarinyar ce? Shiru sukayi ta kuma cewa" Bana so asamu matsala! Ba ku tunanin ko mai kama da ita ce..."?


Duk da ƙwarjinin da hajiya saratu tay wa aneelerh hakan bai hanata Yin karfin halin furta"muna sa ran itace, saboda ni tamkar uwa nake agareta, Yau shekara shida zuwa bakwai da 6atanta kamar Yadda na fada maki, kuma sunan yarinyar Unasah kamar yadda itama yarinyar da shi owais din yake ruƙo sunanta unaisah, amma muna kiran ta da Angel sunan da daddynta Ya sanya mata..." da kwarin gwiwa Aneelerh tayi maganar don ji take zata iya komai akan yarinyar nan

Numfasawa hajiya saratu tayi abunka ga mace mai izza, bata son abunda zai jawo raini tsakaninta da chief gani take kamar zubda girmane ta nemi alfarma awurinsa shiyasa take jinjinawa lamarin da suka zo mata shi, duk da tana son taimaka masu.


"Ina hoton Yarinyar, Ina son ganin shi" cikin sauri zahra ta buɗe mata hoton awaya ta muƙa mata.


Bayan ta kar6a ta kurawa hoton ido nan take ta gane fuskar yarinyar cikin yaran da owais yazo da su wurin dinner.....


"Ina hoton ita Yarinyar ta wurin ku"? Ta faɗa tana kallon Aneeelerh, yatsun hannunta har kerma sukeyi wurin saurin curo wayarta daga cikin handbag ta buɗe hoton Angel ta yunkura taje gaban hajiya saratu ta miƙe mata wayar


Bayan ta kar6a ta jera wayar zahra da aneelerh akan table din gabanta, a tsanake take nazarta hotonan ita kanta ta gasgata abunda suke hasashe komai iri ɗaya, banbanci ita yarinyar da uwais Yake ruƙe ta fi angel dinsu girma amma duba da tazarar shekarun da yarinyar ta 6ace zai iya yiwuwa itace taƙara girma...


Gaba daya hankulansu Aneelerh akan hajiya saratu duk sun kagara da son jin me zatace masu..


Bakomai take jinjina mawa ba face ta yadda zata zubda girmanta wurin yiwa owais magana, saboda basa jituwa tun time da ta fahimci bai kaunar mijinta, kuma tana jin haushin Yadda ake nuna wariya tsakanin Twins dinta da shi


"Dan Allah ki taimaka mana kamar yadda Allah Ya taimake ki, wallahi baki ga halin da mahaifiyar yarinyar take a ciki ba, yanzu haka tana agadon asibiti kwata kwata bata a cikin hayyacinta, sunan mijin ta da yarta kadai ta ke Iya ambato..."


muryar Aneelerh ce ta katse mata zancen zucin nata


"Meya same ta ne? Ko kina nufin tsawon lokacin da yarinyar ta 6ace bata a cikin hayyacin ta..." ta jefa mata tambayar cike da sonjin karin bayani

Labari aneelerh tafara bata tun guduwar benazir da kuma dawowarta har izuwa kan abun da Ya faru jiya


Jinjina kai hajiya saratu tayi da alama abun Ya tsuma zuciyarta duk da bata nuna ba.


"Allah ya bata lafiya" suka amsa mata da ameen.


"Zan nema maku alfarmar ganinta, amma kafin nan ina bukatar ku bani zuwa gobe, kunsan yanayin aikinsu na jami'an sirri, kuma yaran kamar suna bincike kan case dinsu ne, ganinsu zaiyi wuya, dole sai na fara  yin magana da shi....." 


Aneelerh taso ace ta kira chief din awaya sunyi maganar nan take amma dole ta hakura tunda su ne ke nema awurinta dole su yi biyayya

A tare suka haɗa baki wurin yi mata godiya.


har bakin motarsu hajiya saratu ta rakosu ta ƙara jaddada masu gobe zasuji daga gareta 


Lokacin da motarsu ta haura kan titi, shiru babu mai magana a cikinsu,


"Wani jinkirin Alkhairi ne, muyi hakuri" zahra ce ta fada ganin damuwa na neman rikita auntynta

"Allah Ya tabbatar mana da alkhairinsa" suka amsa mata da ameen

Dai dai motarsu ta kusa shiga tankameman gate din asibitin saiga motar dr shureim tana fitowa daga ciki, kasancewar window glass din abude Yake da sauri aneelerh ta kwala masa kira Ya shureim...

Ya na ganinsu Ya samu wuri Yai parkin din motarsa, fitowa tayi da sauri ta nufi motar ta ɗan zukunna bakin glass din tana kallonsa

Duk sai taji wani iri ba dadi ganin yadda fuskarsa tayi jawur idanunsa sun kumbura

"Yaya shurem Ya jikin benazir din?

"Da sauƙi, amma har Yanzu bata tashi daga bacci ba...

"Allah Ya bata lafiya

"Ameen..." shiru sukai kafin tace"naga ka fito ko gida zaka koma ne..."

"Bani zan koma gida ba, zeenatu zan maida..." sai da yai maganar idonta Ya hango mata zeenatu dake zaune a backseat ta kifa kanta bisa gwiwowinta yatsun hannunta sai kerma suke daga gani babu nutsuwa atare da ita

"Ina fata badai wani abu Ya same ta ba"!


"Daddynta ne Yace amaida ta gida, shi ne take kuka"


"Allah sarki baiwar Allah...." cikin nuna tausayawa tayi magnar, zeenatu duk tana jinsu saidai bata jin zata iya dagowa saboda gaba daya fuskarta ta ca6e da ruwan hawaye..


"Ya ake ciki game da Yarinyar kun samu ganin ta..."? Ya jafe mata tambayar saboda abun na aransa

Nan Aneelerh ta sanar da shi Yadda sukai da hajiya saratu

Jinjina kai yai"in sha Allah gobe idan ta kiraku awaya tare zamuje estate din....ko su mami ban sanar mawa ba saboda bana so su sanya rai har sai mun tabbatar in itace.... 


"Shikenan Yaya shureim Allah Ya kaimu lafiya amma zaka dawo ko"?

"Ay dole na dawo aneelerh, Daga na kaita zan juyo..." Allah Ya dawo dakai lafiya


Sallama sukai ma junansu, ta tsaya tana kallon motarshi har ta 6ace ma ganinsa

Komawa tayi cikin motarsu, Mahboob Ya karasa shiga da su ciki tun kafin yayi parking yake ta faman jinjina kai Yana fadin anyi almubazzaranci wurin gina asibitin sai kace ba wurin jinyar marasa lafiya ba, komeye amfanin ƙawata asibiti ...."

yana karasa yin parking suka fito da sauri suka nufi emergency ward sai da suka fara tsayawa wurin nurse's station bayan sun fada masu sunan marar lafiyar da suka zo dubawa, ɗaya daga ciki tayi masu jagora har dakin da aka kwantar da ita, kafin ma su isa suka hango Hajiya layla tare da Alhaji ubaid abakin kofar asitin suna magana atsakaninsu, fuskokin kowan nan su babu annuri sai tsantsar damuwa

Takun tafiyarsu Aneelerh ne Yaja hankulansu ga dubansu

"Aneelerh......" hajiya layla ta fada cike da mamakin ganin ta, ita kanta baza ta iya tuna rana ta karshe da tai tozali da ita ba.

Aneelerh na karasawa ta rungume hajiya layla batasan sa'adda kuka Ya balle mata ba

Shafa kanta hajiya layla tayi tana ɗan rarrashin ta, hakika tayi mamakin ganin yadda ta kara girma rayuwa kenan andade ba'a hadu ba, tun da zumuncin su Ya watse

Tsawon mintuna hajiya layla tana lallashinta, kafin ta dago idanu jawur ta gaishe da Alhaji ubaid fuskarsa da fara'a ya amsa mata har yana ɗan zolayarta 

Aneelatu kece kika koma haka? Ƴayanki nawa? Cikin shesshekar kuka tace Yarona dayane Yana a school, 

"Allah shi raya shi,

Tace"ameen"

"Ya hakurin abun da ya faru da su Uzair"?

"Mungode Allah" 

"Ubangiji Allah Ya bayyanar da su" ta amsa mashi da ameen

Hajiya layla tace"ki shiga ciki," da sauri ta shiga dakin, 

Su zahra dake atsaye har suna haɗa baki wurin Gaishe da su ita da mahboob suka kuma yi masu ya mai jiki

"Jikin da sauki bacci take, amma ku yan uwanta ne"?

"Ƴaƴan uncle dinta ne mu"

"Allahu akhbar kamar na ta6a ganinku da jimawa lokacin baku kai haka ba.." 

Zahra tace"eh ay muna yawan zuwa joss lokacin baya..."

"Allah sarki ku shiga daga Ciki dan Allah kuyi mata addu'a' amsa mata sukai da toh

Bayan sun shiga, agaban gadon suka iska Aneelerh ta zuƙunna kan gwiwowin ta, kanta akan gadon, hannunta acikin na Benazir, jikinsu duk sai yayi sanyi ganin yadda benazir ta faɗa daga jiya zuwa yau har ta canza...

Har lokacin hajiya sarah na zaune kan kujera sallah kadai ke tada ta..

Gaishe da ita su zahra sukayi tare da yi mata ya mai jiki tace masu da sauki,

"Ubangiji Allah Ya bata lafiya, Allah yasa kaffarane" ta amsa masu da aneen

Gaban gadon suka tsaya kafin suka fara yi mata addu'o'i suna tofe mata jiki da su,.....

Kamar masu zaman makoki haka suka tasa ta agaba suna kallon ta. 

Wureran karfe biyu da rabi ta farka kamar mai ta6in hankali haka ta dinga fusge fusge tana ambaton sunan taj da Angel, ta makance bata ji bata gani bata sauraren kowa hauka kawai takeyi masu, haka suka dinga rurruƙe ta don kokari ma take ta sauko daga kan gado, su Aneelerh sun sha kuka ba kamar da ta furta"kada su bari ta mutu bata sanya yarta a idon ta ba, bata son ta mutu bata ganta ba, su taimaka ma rayuwarta....." 

babu wanda bai zubar mata da kwalla ba, hatta mahboob Yaji tausayinta


Likitan dake kula da ita ne Ya shiga dakin tare da wasu nurses  Ya bukaci su hajiya sarah su fita daga waje

Nan suka fito kowa Ya zauna kan waiting seat suna ta jiran tsammani


Tsawon mintuna ɗuff suka daina jin sautin koke koken benazir, har sun fara fargaban meke faruwane sai ga dr adam Ya fito daga dakin tare da nurses din


Suna ganin shi kowa Ya mike suka nufe shi suna tambayar awani hali take ciki"? 


Fuskarsa babu walwala Yace masu suci gaba da yi mata addu'a sannan su yi kokarin samo yarinyar da zata iya pretending amatsayin yarta daga yau zuwa gobe in ba haka ba sakamakon ba lallai Yayi masu dadi ba, don sunyi iyakar bakin kokarinsu amma abun yaci tura, Yanzu haka allurar bacci suka ƙara Yi mata....."


Hankulansu ba karamin tashi Yayi ba, nan fa suka fara shawarar Yadda za su samo Yarinyar dake kama da Angel ƴar fara mai launin ido ruwan toka..


Aneelerh tayi saurin cewa akwai wata yarinya da ta sani mai kama da unaisah, amma ko za'a same ta sai ya kai zuwa gobe...." ta fadi hakanne saboda tana sa ran gobe hajiya saratu zata kirasu inyaso koda yarinyar ba unaisah bace sai su nemi alfarmar abasu ita aro har zuwa time ɗin da benazir zata ji sauki...


Hankalinsu ba karamin kwanciya yayi ba, hajiya layla tsabar zumudi hada cewa me zai hana yarinyar tazo yanzu? In ma da bukatar suje gidan iyayenta neman alfarma sai suje..tace masu ay yarinyar ba'a kusa take ba, suyi hakuri zuwa gobe sai a sanar da iyayenta amsa mata sukai da toh ..........


Bayan komai ya lafa, Aneelerh ta kira  mami awaya don ta sanar da ita halin da ake ciki, a lokacin tana a falo zaune zuciyarta cike fal da tunanin kome Ya tsayar da su aneelerh har yanzu basu dawo ba? Ko dai sun samu shiga gidanne? Ita kadai take ta tufka da warwara, kiran na shigowa a hanzarce ta dau wayar dake akan sofa hand, ganin sunan aneelerh yasa tay saurin dagawa


"Aneelerh! Ina fata kuna lafiya? Naji shiru baku dawo ba, ba sai da nace maku in baku samu shiga gidan ba kada ku takura kanku?


On the other hand Aneelerh tace"mun samu shiga mami, amma bamu samu damar yarinyar ba...." a tsanake ta sanar da ita komai ta kara da cewa"tace zuwa gobe zata tuntu6e mu,..."


Mami tace"to kuyi hakuri ku dawo gida, wani jinkirin alkhairi ne..."


"Mami, Yanzu haka muna asibiti, benazir ba lafiya..." tunkafin ta kare maganar mami ta doka salati tana fadin wata benazir din? Meya same ta"? Gaba daya hankalin ta ya tashi 

Shigowa ummi tayi falon tana kallon mami dake ta zagba salati tana sauraron Aneelerh dake bata labarin abun da Ya faru bayan komawarsu dr shurem gida, 

"Inna lillahi wa'inna ilaihirraji'i abu baiyi dadi ba, kai jama'a baiwar Allahn nan tana jin jiki, ubangiji Allah Ya tashi kafadunta, Anerlerh gani nan zuwa asibitin, kice wa mahboob kada ya manta da junaid karfe shida Yaje ya daukosa" amsa mata aneelerh tayi da toh

Bayan ta katse kiran, fuska A yamutse ta kalli ummi dake tambayar ta lafiya meya faru taji ta ambaci sunan benzair

Girgiza kai tayi kafin ta kwashe komai ta sanar da ita, hankalin ummi ba karamun tashi yayi ba.


"Yanzu zanje asibitin, ki zauna ke inyaso gobe sai kije kada abar gidan ba kowa, duk da Ana tana nan ba lallai junaid Ya yarda da ita ba kinsan shi da rigima."


Amsa mata ummi tayi da toh, cike da Alhinin abun da Ya faru, da sassarfa mami ta dauko hijabi ta zubla ta fito daga daki, ummi tayi mata adawo lafiy sanna tace agaishe mata da mai jiki, kafin taje goben


 Mami na fitowa daga gidan saiga motar abie ta shigo, hakan ba karamin dadi yayi mata ba, dama abun hawa zata tsayar akaita can, sai gashi Allah ya dawo da shi, Agabanta Yayi parking motar bata jira Ya fito ba, ta bude motar ta shige sai da ta zauna yake tambayarta ina zataje yaga kamar bata acikin nutsuwarta, nan ta sanar da shi abun da ya faru na rashin lafiyar benazir, har faɗa sai da yayi akan fada matan da aneelerh tayi mami tace bafa laifin ta bane, itace ta matsa mata, kuskure daine an riga anyi sai dai ayi fatan Allah Ya tashi kafadunta....

Karya kwana yayi da gudu motarsu ta fuce daga gidan kai tsaye suka nufi asibitin. 


_________________________________✍️


Slowly motar dr shureim ta kunna kai cikin gidan, bayan yai parking ya dago ya kalli zeenatu da ta kifa kai bisa gwiwa tana ta shesshekar kuka


"Bazan gaji da lallashinki ba, dan Allah ki hakuri ki jure ya shurem bayason ganin hawayen babynsa, na fada maki addu'armu take bukata, kuka ba abunda zaiyi mata...." tun da yafara maganar bata dago dakai ba

Fitowa yai daga motar ya zagaya dayan bangaren da take ya buɗe mata"fito mu shiga" still bata tanka mashi ba, dama dakyar ya rabata da asibitin.  Ba karamar badakala suka sha da ita ba. Kuka tadinga yi akan bazata koma gidan ba, dakyar suka lalla6ata.


Ganin zata bata lokaci Yasa shi kai hannayensa ya tuttu6eta kamar yar tsana Yai mata irin daukar da ake ma jariri Ya nufi cikin gidan da ita.


Tana kuka tana fadin yaya shureim bazanje ba ni ka sauke ni, wurin aunty benazir zan koma...bai saurareta ba har ya karasa katafaren falon,  Alhaji musa na azaune kan sofa ya daura kafa ɗaya bisa ɗaya, idanunsa na akan laptop dinsa, hada mug din coffee a gefe yana sha babu alamun damuwa akan fuskarsa hankalinsa kwance


Shigowarsu ne Yasa shi dago da ido Ya kallesu Fuskar shureim a daure Ya dira zeenatu, ransa Ya baci da ganin uncle din nasa kamar baisan halin da suke aciki ba.


"Shureim..." har ya kusa Fita ya dakatar da shi waiwayowa yayi babu walwala Ya ke kallonsa, shi kanshi alhaji musan Ya fahimci fushi Yake da shi

"Ya jikin benazir din? Kamar bazai tanka masa ba ya furta"da sauki"

"Menene sakamakon abunda ke damunta"?

Sai da ya ɗanyi jim kafin yace"It's depression and panic attack...." bai kare maganar ba yai hanzarin fucewa daga falon don baya jin zai iya jurar kallon uncle musa tsaf zai Iya gaya masa magana

Har ya kusa fita daga entry hall din kwatsam sautin muryar zeenatu Ya dakatar da shi Ya kasa kunne Yana sauraronta

Cikin muryar kuka take fadin"Wallahi daddy baka da tausayi, kowa ya damu da halin da aunty benazir take aciki ban da kai! Jiya kana gani haka ta kwana akulle kaki taimakawa ka buɗe mata kofa, har sai da ta kwana, why daddy? Baka sonta ne? Ko tayi maka wani laifi ne da yaja har kake nuna halin ko'in kula akan ta, ni wlh ka 6ata min rai daddy tun da har baka damu da rashin lafiyar aunty benazir ba, hankalinka kwance kana agida sai kace ba ɗiyar yayanka ba,....." kamar daga sama dr shureim yaji saukar mari ji kake tasss 

A matuƙar furgice ya ware dara daran idanunsa, jikinsa na 6ari a sukwane Ya juya cikin takun sauri Ya nufi falon Har zai shiga wata zuciyar ta gargadesa akan kada Yaje Tsayawa yayi yana sauraron su daga inda yake yana iya hangen zeenatu wadda tunda daddynta ya kwasa mata mari gaba daya ta jirkice ta kife kan hannun sofa, jikinta yadinga bari kusan wannan ne karo na farko daya fara ta6a lafiyar jikin ta....baiwar Allah gaba ɗaya ta furgice ta kasa dagowa ta dinga tsala kuka tana fadin na tsane ka daddy, da kanka ka sa hannu ka buge ni? Daddy ka makance ne? Wlh sai dai ka kashe ni daddy..." masifa ta dinga zazzaga mashi 

Zeenatu bata ta6a bashi mamaki ba irin na yau, duk irin shakkarshi da take ji hakan bai hanata fadan ta cikin ta ba, hakan ya tabbatar masa da taji haushin abunda yayi 

Yatsun Hannunsa Ya zubawa idanu cike da jin haushin marin ta da yayi,


Duk da ita taja ma kanta, shi fa ba'ay masa fada ana ɗaga masa murya balle ita da take yar cikinsa...

Walking slowly Ya nufi sofa din da take Ya zube kan gwiwowinsa agabanta.

dr shureim dake la6e Yana kallon shi har saida Ya ɗan ware idanunsa cike da mamakin Yadda Alhaji musa Yai kneel down agaban zeentu mutumin da ko uwarsa baya tunanin Ya ta6a zukunna mata, wannan wani irin sone ya ke yi mata?

Kamar zai mata sujjada haka Ya fara magana"i'm really sorry my daughter, kurkurene ba da son raina ba, kece kika fusata ni zeenatu, banso na mareki ba..." yadda yake yi mata magiya ba karamin ɗaure kan dr shureim yayi ba, har tafin hannu yasa ya shafa fuskarsa don Ya tabbatar in ba mafarki Yake Yi ba


Cikin shesshekar kuka take fadin"Dad ..dy  dama ka daina bani hakuri, don bayi zanyi ba, ni bana son ganin ka, tun da bakason Aunty benazir dina..." bata kare maganar ba, Yai hanzarin furta"waya fada maki bana sonta? benazir kamar ƴa take awurina..."

To amma meyasa jiya kaki bude mata kofa

"Saboda bani na kulleta ba, itace ta kulle kanta .."

"Daddy ni ban yarda kana sonta ba, tun da kaki zuwa asibiti dubata..."

Hannu yakai tare da janyo zeenatu ya kwantar da kanta saman broad chest dinsa Ya daura tafin hannunsa abayanta yana lallashinta..."ki daina kuka bana so, indai akan benazir ne zanje na dubata hope hakan yayi maki"

Tana faman matse kwalla tace"daddy dr yace in har ba'a bemo mata yarta ba, zuciyarta zata buga ta mutu, dan Allah kasa a nemo mata yar babynta, daddy nasan zaka iya..." yamutsa fuskarsa yai kafin yace"naji zanyi kokarin sanyawa a nemo mata ita, Yanzu ki kwantar da hankalinki, Muje daki ki kwanta ki huta, zan sa tani ta kawo maki abinci nasan kina jin yunwa..." yai maganar tare da mikewa ya ruƙo hannun zeenatu acikin nashi, suka nufi bedroom dinsa

gauran numfashi dr shureim Ya sauke aranshi yana mai al'ajabin irin son da Alhaji musa yake ma zeenatu

Sai dai baiji dadin marin da yayi mata ba, yaji zafi aranshi, saboda yaga shatun yatsunsa sun fito ruɗu ruɗu kan kuncinta yasan dakyar in zazza6i bai kamata ba, saboda zafin hannu gare shi, ya ta6a marin zainab mai aikin gidansu lokacin dayaje joss kawai saboda ta haɗa hanya da shi har ta bangaje shi cikin rashin sani, tun da ya kwasa mata mari sai da tay 1 week tana jinyar fuskarta....

 sai dai yasan ba lallai ya bari zeenatu taji jiki ba, tunda yana sonta zai mata maganin abunne

Da wannan tunanin Ya fuce daga gidan Ya shiga mota Yaja Ya nufi asibiti. 


______________________EX-PRISONERS


A tsaye suke su biyu suna fuskantar junansu, tunda batool ta sanar da ita game da wayar da tajiyo aunty ummin su, tana yi a tsakar dare cikin toilet, taji hankalinta Ya tashi zuciyarta harta fara raya mata ko dai aunty umminsu da wata muguwar manufar take atare da su?


"Taya za'ay insan dawa take magana"? Ta jefa wa kanta tambayar


"Wai hada cewa ay bani da wayon da zan iya sanya mata ido..." acewar batool

"Anya batool ba zaki daina kwana dakin ta ba? 

"Saboda me"?

"Indai zaki cigaba dayi mata la6e duk  ranar da ta gano ki,  wlh zata Iya hukunta ki, tun da bamusan me take ƙullawa ba!

Girgiza kai batool tayi"ni dai bana Yi mata mummunan zato, kuma bana so na daina kwana dakinta..." fuskarta ayamutse tayi maganar

"Nima ina kyautata mata zato, amma meyasa take abu kamar mara gaskiya? Waya a toilet kuma a tsakar dare? Sannan har tana fadin baki da wayon da zaki iya sanya mata ido? 

Ruko hannun batool tayi"bazan hanaki kwana dakinta ba, amma kiyi takatsantsan, kada ki ƙara yi mata la6e kibarta kawai, In sha Allah ba abun da zai faru watakil ma bata son ki farka daga bacci ne shiyasa ta shiga toilet tanayin wayar don kada ta takura maki' jinjina kai batool tayi alamar gamsuwa da maganar unaisah

Kafin wani ya ƙara yin magana a cikin su, suka ji an turo door room din, kusan atare suka dago suna kallon mai shigowa har saida gabansu Ya ɗan fadi ganin matar da suke gulmarta

Tayi gayu abunda cikin riga da wando sun kama jikinta, head din data daura ba karamin kyau yayi mata ba, tuni kamshin turarenta Ya buɗe hancinansu

Ganin yadda suka tsareta da ido ne Yasa tace"lafiya naganku atsaye? Ko dai gulma ta kukeyi ne"?

Har suna hada baki wurin fadin"A'a" kashe masu ido tay tare da sakin murmushi tace"ku fadamin gaskiya ba abunda zanyi maku, meyasa da kuka ga nashigo kukayi shiru? Bayan kafin na shigo naji kuna magana cikin raɗa

"Wlh ba gulmarki mukeyi ba..." ta6e baki tayi"shikenan tun da kunki fadamin gaskiya, Ku zo mu tafi dining, it's lunchtime. Yan uwanku suna jira..." 

Amsa mata sukayi da toh, a tare da ita suka fito daga dakin...tunkafin su Isa suka hango su Haris zazzaune kan dining chairs an cika masu table da lafiyyayan abinci

Wuri suka samu kowa Ya zauna har sun fara cin abinci unaisah ta tuna da danish, har ta fara gajiya da halin shi, sam bayason zuwa dining cin abinci sai in taje tay masa magana tukunna Yake fitowa, 

Haka da safe lokacin da zasuyi breakfast sai dai Sajeed ne Ya kai masa adakinsa

"Ina ɗan uwanku ne? Na lura baya son zama acikinmu Yaci abinci.." Ummi ce tayi maganar 

Naufal Yace"Bari naje na kira shi" yai maganar tare da mikewa, ajiyar zuciya unaisah ta sauke dama neman wanda zaije Ya kirasa Takeyi don batajin zata ƙara zuwa dakinsa gudun kada ya kara yi mata abunda yayi jiya

Dawowa Naufal Yai"yace ki kai masa adakinsa" Ya fada idonsa akan unaisah, Yamitsa fuska tayi"batool ki kai masa pls" 

Ummi na murmushi tace"bake Yace kikai masa ba? Ki tashi mana ke Yake son gani"

Maƙe kafaɗa tay alamar bazata je ba, 

Mikewa batool tayi"Bari naje na kai masa.." da sauri ummi tace"koma ki zauna ita zataje, tunda ita Yake son ta kai mashi, Ki kasan ko akwai abunda zai faɗa maki...." turbune fuska tayi ranta ajagule kamar an mata dole ta dauki plate da saving spoon ta zuba mashi  fried rice ta haɗa mashi da juice, tasan bai cika son cin abinci dayawa ba...


A bakin kofar dakin ta tsaya tare da kai hannu tay knocking, shiru ba'a buɗe ba, daga murya tayi"My man ni ce...."  ta fada tana faman haɗe rai


Buɗe kofar yayi, lokacin da ta daura idonta kanshi har saida gabanta Ya faɗi ganin babu riga a jikin shi, zanene kirjinsa Ya ɗan sanya ta jin fargaba

Miƙa masa plate din tay"ga abincin..."

Lumshe idon yai"ki shigo min da shi ciki" make kafaɗa tay"pls ka kar6a kawai ba saina shiga ciki ba,..."

Ya fahimci rigime take ji"wani abu zan nuna maki..."

Harara ta galla masa"salon in shiga ka kara yi min irin abun jiya ko.  " sai da tay maganar Ya fahimci abun da take ma fargaba

"Nayi maki alƙawarin bazan ta6a ki ba, tunda bakiso, pls ki shigo ki gani...." yanayin yadda yayi maganr ba karamin sanyaya mata zuciya yayi ba, cikin lallami  Ya samu ta shigo Ya mai da kofa...

Akan table ta daura masa plate din tare da juice

Ganin Ya nufi gefen gadonsa yasa takai ido wurin har sai da taɗan ji gaban ta ya faɗi ganin acessories din dake zube kan mattaress dinsa masu kyau da tsada

Da mamaki ta furta"My shield Waya baka wannan"? ta fada tana tunkarar kayan kamar mai jin tsoron su

"Wannan mutumin ne Ya kawo min namanta sunanta, Yace min uncle dinsa hateem ne Yace abani su..."

Waro idanu waje tayi tana Yarfa hannu Ta furta"wayyo Allah daɗi, my man yanzu duka wannan naka ne?amma natayaka murna.... Agaban gadon ta zauna yatsun hannunta har kerma suke Yi ta dauki Apple laptop din ta buɗe ta tana kallon ta.


Ta aje laptop din gefe ɗaya takai hannu ta ɗauki iphone din sak kalar wayarta banbanci su colour ne..

bayan ta ajiyeta ta dauki apple ipad din tana jujuyata faskekiyar gaske...

"Amma dai mutumin nan Yana ji da kai, Allah Ya saka masa da mafificin alkhairi, kamar yadda yake kaunarka nima ina kaunarsa...." abun da bata sani na tun da tafara magana danish Ya nutsu yana kallon duk wani motsin ta, gaba daya ta tafi da imaninsa Yanayin yadda take yaba kayan tana murmushi tare da ɗan zare gray eyes din ta ba karamin kashe mashi jiki tayi ba.....idan ta motsa pink lips dinta kuwa har wani haɗiyar yawu Yake Yi


Duk bata lura ba, Headset ta dauka tana dariya tace"amma dai atare zamu dinga amfani da su ko? Kaga ni bani da wannan.." tay maganar tare da kallon shi ta kashe mashi ido ɗaya tare da daura mashi headset din a kansa ta saita mashi a kunnansa.


"Wow!...." wani Irin kyau yayi mata har bata san sa'adda ta manna masa kiss a cheeks din sa ba, mutumin fa gaba ɗaya ya fara zaucewa wani irin yanayi yake jin kanshi

Cire mashi headset din tayi, ta aje kan mattress din ta janyo eye glss box din tana danna akwatin nan take ya bude jerin hadaddun glass ne na maza ta dauko wani mai walwali launin blue sky ta zura mashi a idanun shi

Tabarakallahu ahsanul khaliqin shine abun da ta furta

Da tafukan hannyenta biyu ta tallabo fuskarsa ta zuba mashi ido tana kallon 

Kamar yadda shima yake kallonta ta cikin glass din numfashin su har yana kokarin hadewa dana juna

"Sai naga ka ƙara min kyau my man, bari na canza maka wani" da sauri ta cire na fuskarsa ta dauko wani glass din black colour ta sanya mashi

"Wow kana kashe ni da kyanka...' ta fada tare da cire mashi glass din ta maida shi cikin ɗan akwatin

Ta janyo watchbox  ta buɗe shi jerin tsadaddun agogunane ƴan ubansu 


 ta dauko ɗaya ta kamo hannun shi ta soma kiciniyar sanya mashi a wrist dinshi

"Ka wani kura min ido kana kallona kamar yau ka fara gani na" tayi maganar da zolaya...

Lumshe idonshi yayi ba tare daya furta mata komai ba....

"Wohoho Ina gwanin wani ga nawa..My man wlh kai na musamman ne, komai naka na kece raini ne...Kalli hannunka irin na ƴan gayu wadanda sukaji hutu..." sai faman santin hannunsa take agogon tayi bala'en yi mashi kyau .....

Sam ta manta da abun da ya faru jiya atsakaninsu ta zaƙe sai zuba take yi masa kamar aku

"Kin fara period ne❓Kamar daga sama Taji Ya furta wani bugu zuciyarta tayi mata, a ruɗe ta dago tana kallon shi ido cikin ido suke kallon juna❗❓ 

   



*Daga Alƙalamin Boss Bature💋✊✍️*



 *Littafin kurkukun ƙaddara 500 ne, dukanshi Book One two and 3 Idan kin shirya biya ga Details da zaki tura*


3196407426


First bank 


Bature Hafsat Muhammad,


 *bayan kin tura zaki bada transaction reciept ko screenshot na debit alert a matsayin shaida ta wannan layin 08169856268*

Post a Comment

Idan kuna da tambaya akan abinda Baku game ba ko kuma kuma Neman littafin da babu a nan kawai ku ajiye tambayarku a ta comment ko wani shawara da Zaku bamu.

Previous Post Next Post

Sponsored Link

Sponsored Post