Ganyen gwanda na kumshe da sinadiran lipid, calcium, iron, bit C, bit B6, folate, Thiamine, magnesium, phosphorus, potassium, sodium, zinc, Bit A, bitamin E, Bitamin D, D2, D3, Niacin da sauransu. Ganyen gwanda na habaka garkuwar jikin dan’adam.
Su dai garkuwar jiki su ne, ke zama a matsayin sojojin da ke yaki da abokan gaba waton suna yaki da kwayoyin cuta a jiki, dan haka idan suka karamta ko su ka yi rauni to a hakika jikin dan’adam zai raggwanta kuma zai iya fuskantar barazanar kamuwa da cututtuka daban-daban.
Related Story:
MAGANIN GYARAN NONO MAI SAUKIN HADAWA
A dalili da haka akwai bukatar jikin dan’adam ya samu garkuwar jiki masu karfin gaske dan su iya baiwa jiki kariya daga abokan gaba. Domin samun wannan damar to sai a lazimci amfani da tsirran itatuwan da kimiyya ta bada tabbacin cewa suna taimaka wa garkuwan jiki ciki harda gwanda.
Ganyen gwanda na kashe cututtukan fata sanadin samun sinadirin karapain a cikinsa wanda wannan ke da tasirin kawar da fungal infections. Ga