Kurkukun Ƙaddara Takun Ƙarshe chapter 32 by Boss Bature


Health College

Kurkukun Ƙaddara Takun Ƙarshe chapter 32 by Boss Bature

Takun Ƙarshe

lumshe ido tayi ya nutsu yana kallon eye lashes dinta da suka jiƙe da ruwan hawaye ita kaɗai ta san me take ji, zaro hanky yai daga pocket dinsa a hankali ya  soma share mata tears ɗinta, jin saukar hannunsa akan fuskarta yasa ta yi saurin buɗe idanunta ƙiris ya rage karan hancinsu ya gogi na juna, hatta numfashin su kokawar haɗewa yake. 

Kasancewar chief na bala'en kama da Danish sai ta dinga ganin kamar shi ne a tare da ita, shima haka yake nuna damuwa akanta ya bata kulawa amma sai gashi rana ɗaya ya karya mata zuciya, duk irin burin da taci akan shi na son ganin sun mallaki juna.  


Tuna wannan yasa ta fashe da kuka duk yadda taso ta haɗiye kukan ta kasa, da sauri chief ya kwanto da ita kan kirjin shi, hankalinshi ba ƙaramin tashi yayi ba, hatta agent din dake driving ɗinsu saida yaji sautin kukanta...."


"Sir meke faruwa ne?" Ya faɗa tare da satar kallon su ta mirror, wani  shock yaji cos bai ta6a ganin chief yayi hugging ɗin macen da ba muharramarsa ba.


Bakomai ya jawo hakan ba face tausayinta daya rufe shi gani yake kamar kanwarsa ce Hindu take kuka...

A hankali ya zagayo da hannayansa ta bayanta, cikin sigar lallashi yake ɗan shafa shi, wani irin relief taji tuni ta nemi kukan da ta ke yi ta rasa, nutsuwa tayi akan chest dinsa ta lumshe idanunta, tana jin wani irin yanayi da bata ta6a jinsa ba, at same time heart dinsu take beating rapidly, tsit kake ji babu mai magana a cikinsu, Cheif bai ta6a tsintar kanshi a irin wannan yanayin ba yana jin wani irin feelings a tare da shi,

daƙyar ya samu ƙwarin gwiwar, raba jikin shi daga nata

ya tallabo gefen fuskarta da hannun shi, sam ta kasa buɗe idanunta wani irin nauyin shi da kunyarshi take ji.

Sexy voice dinsa ce ta ratsa kunnanta"Tell me, meke damun ki? Me yasa kike kuka" la66anta na kerma ta ce"ba abunda ke damuna, lafiyana lou" ta rasa ya akai take jin muryarshi kamar ta Danish hakan ba ƙaramin karya mata zuciya yake yi ba,


"Ban yarda ba, kuka baya zuwa saida dalili! Faɗa min ko dai baki son zuwa asibitin ne? Daddynki ne Ya tursasa maki"? da sauri ta ce "ina son zuwa, ba shi ya tursasa min ba, kawai bana jin dadin jikina ne, bansan meke damuna ba...." gaba ɗaya idanunsa na akan pinkish lips ɗinta sun jiƙa da hawaye sunyi taushi...

Ya fahimci akwai abunda ke damunta, bata son faɗa masa ne, kuma bai son ya takura mata hakan yasa shi furta "Okey, ki daina kuka, Idan muka isa asibitin, zanyi magana da likita ya duba min lafiyarki..." wani irin sanyi taji ya ratsa zuciyarta, still bata buɗe idanunta ba ta amsa mashi da toh, gyara zamanshi ya yi zuciyarshi cike fal da tausayinta ya maida hankalinsa akan laptop ɗinsa, yayin da Unaisah ta ƙurawa glass din motar ido tana kallon motocin dake zarya kan titi, ƙoƙari take ta kauda tunanin Danish a ranta amma abun ya faskara.....💔



_________________________✍️


Su Aneleerh suna zaune a hospital courtyard kan kujeru su uku ita da Zahra tare da Dr. Shureim sun ƙi tafiya gida kowan nansu ya ƙwallafa rai da son ganin haɗuwar Unaisah da mamanta, duk bayan ɗan lokaci sai a

Anila ta duba agogon hannunta, 


Zahra harta fara gyangyaɗin bacci.. 


"Anila anya zasu zo? Naji shiru har yanzu.." Dr. Shureim ne ya yi maganar, fuskar shi ayamutse daga gani ya gaji ba kaɗan ba,

"In sha Allah zasu so, mu ɗan ƙara hakuri, ina ji araina sun kusa ƙarasowa..." ta faɗa tare da kallon zahra dake gyangyaɗi

Da zolaya ta ce, "Zahra kada fa kiyi mana bacci anan, kinsan dai ba iya ɗaukarki zanyi ba, sai dai ko Dr. Shureim ya taimaka mini"  murmushi ya yi tare da kallon ta, idanunta sunyi ja muryarta da kasala tace "na gaji ne, ga yunwa ina ji, ga bacci..."

"Ki zo na sauke ki a gida." girgiza kai tayi, "a'a Ya Shureim kaima nasan ka gaji, bana son ma na tafi, hankalina bazai kwanta ba, in har banga haɗuwar Aunty Benazir da Azeezaty ba.." har cikin ranshi yaji dadin yadda suke nuna damuwarsu akan yar uwarsa....


Kafin wani ya ƙara furta kalma a cikin su, sautin horn Ya karaɗe kunnuwansu, kusan atare suka kai dubansu ga enterance gate din asibitin, a jere motocin suka kunno kai da matsakaicin gudu suka nufi parking space....

 

"Ina tunanin sune suka ƙaraso" a cewar Anila, miƙewa sukayi tsaye suna kallon su cike da sa ran ganin sune.   


Tun kafin motocin su ƙarasa yin parking, Md Dr.Jidenna ya fito daga cikin asitin babban mutunne ya fara manyanta, gashin kanshi duk hurhura, Dr. Jazz na abiye da shi, already sun san da zuwan Chief, shiyasa suka fito don su tarbe shi....


Da sauri Jami'an Isod suka fara durowo daga kan motarsu sanye cikin kakinsu, qugunansu na a soke da kananun bindigu,


Cikin zafin nama suka buɗe masu murfin motar, A hankali chief ya fito kafin Unaisah ta fito idanunta akan katafaren asibitin, a ranta ta jinjina ma haɗuwar shi, su Aneleerh na ganinta farin ciki ya lullu6e su kasancewar akwai bulbs light daya mamaye ko'ina tamkar da rana..


"Yaya Shureim sune muje mu tarbo su"  Anila ce ta faɗa da sauri suka nufi gurinsu, tunkan su ƙaraso Unaisah ta hango su wani irin farin ciki ne ya lullu6eta da sauri ta nufo su, kafin ta ƙaraso Anila ta buɗe mata hannu suka rungume juna, Dr Shureim tun da ya kafe ta da ido ya kasa ƙyaftawa wani irin faɗuwar gaba ne ya dirarsa masa, ya ƙura mata ido kamar zai lashe ta, ita ko ta ƙanƙame Aunty Anila kamar karta saketa, 


"Sannu da zuwa my Azeezaty, tun ɗazu muke sa ran ganin ku..." Anila ta faɗa tare da ɗago da fuskar unaisah, "Ga Yaya Shureim ku gaisa, ɗan uwan mara lafiyan ne" sai lokacin ta lura da shi ita kanta da ta kalle shi saida taji gabanta ya ɗan faɗi, cikin sanyin murya ta ce "ina wuni? Ya mai jiki?"

Murmushi ya sakar mata, "Mai jiki Alhamdulillah, Malama Azeezaty, ina fata bamu takura maki ba, zamu ɗaura maki ɗawainiyar jinya," murmushi tayi "Babu takura, ni naji zan iya, kuma ni abun farin ciki na ne, fatana Allah ya bata lafiya" ba ƙaramin burge shi tayi ba, yarinyar ta shiga ran shi lokaci guda sai yaji inama ace yarinyar Benazir ɗinsu ce da sai yafi kowa farin ciki.


"Aunty Zahra" miƙa mata hannu Unaisah tayi suka gaisa da juna, Zahra na murmushi ta ce "Na ji dadin sake ganinki, Azeezaty tamu, mai mutunci" murmushi kowan nans u yayi.


Taj dake a zaune cikin motarsu Ya nutsu Yana kallonsu Aneelerh, fuskar shi kwata kwata babu walwala.


"Pls ka tashi mu fita mana" girgiza kai ya yi ba tare da ya kalli Big guy ba yace "ba inda zanje, tunda na bada Unaisah babu buƙatar in shiga ciki, ka tafi zan jira ku anan",


"Wai duk akan me kake fushin nan? Saboda baka son ganin  ex-wife ɗin ka?" Banza yayi dashi bai tanka mashi ba,


"Meye na damuwa? Matar da bata acikin hayyacinta, kuma in banda abunka wazai san kaine? Mu da zamu 6adda kama da face mask"? 


A takure ya ce"Don Allah ka kyale ni! Nace ba zan je ba, ka tafi mana..."


gyaɗa kai Big guy ya yi, yasa hannu ya gyara mask din fuskarsa ya fito daga cikin motar, ya nufi wurin su Chief dake atsaitsaye suna gaisawa da su Dr Jidenna.


Ɗaya bayan ɗaya ya miƙa masu hannu sukayi musabaha kafin ya ɗan russina saitin kunnan Chief cikin muryar raɗa yace"Sir taj yace bazai shiga ciki ba!" juyawa Chief yayi har zuwa bakin window glass din motar yayi kncoking din ta, 


"Taj, ka sauke glass" zuge shi yayi,

Duƙowa chief yayi suka haɗa ido da shi "Haba mutumina, mun riga da munzo asibitin shiga ciki ne zai gagare ka uhuym?"


Fuskarshi a yamutse ya ce "Sir pls, bana son shiga ne, nafiso kubarni anan..."


"No taj, ban amince ba," ba don ya so ba, ya ɗauko backpack din Unaisah da ya kar6a a wurinta, ya sargafo hannun jakar a kafaɗarshi, kafin ya fito daga motar,


Ruƙo hannun shi Chief ya yi suka nufi su Dr Jazz atare suka haɗu suka dunguma zuwa cikin asibitin, su Anila suna a biye da bayansu ta ruƙe hannun Unaisah a cikin nata, kamar wani yace zai ƙwace mata ita.


Corridor din da zai sada su da emergency ward suka nufa, cikin girmamawa Nurses da Docs suke gaishe da Chief...


Sau ɗaya Taj ya saci kallon Dr. shureim, ba su ta6a haɗuwa da juna ba, lokacin daya auri Benazir Dr shureim ɗin ba ya a ƙasar ya koma Egypt da zama, sau ɗaya suka ta6a gaisawa a waya lokacin da ya kira ya damƙa mashi amanar ƴar uwarshi..."


Lokacin da suka ƙaraso gaban Medical room ɗin da Benazir take sai kowannansu Ya dakata da yin tafiya.  


Kasancewar kofar ta glass ce suna Iya hangen Benazir dake a kwance tana bacci, Dr Adam Yana a tsaye bakin gadon Yana ƙara duba ta,


Knocking kofar Dr. Jazz ya yi, da sauri Dr Adam Ya juyo ya dube su, aiko da ganin su Chief jiki na 6ari ya fito cikin girmamawa ya miƙa masu hannu suka gaisa..


Fitowa hajiya Layla tayi daga dakin jikinta a sanye da hijabi bakinta washe ta fara gaishe da su, suka yi mata ya mai jiki ta amsa masu.


tunda Taj Ya kalleta sau ɗaya ya kau da idon shi gefe, ba zai ta6a mantawa da irin wulaƙancin da Hajiya Layla tayi mashi ba, hakanan ta ɗaura mashi karan tsana saboda yana son yarta, har faɗi take in banda haɗama irin na ɗan talaka ina shi ina Benazir? waye ubansa a kasar? Da aikin Jarida zai ciyar da ita? "Wama ya sani ko asiri kayi mata shiyasa ta nace saita aureka .." murmushin takaici ya saki ta cikin face mask ɗinsa...,


Dr Adam Ya ce, "ina yarinyar ne?" da yake basu lura da ita ba duk ta takure bayan Anila kamar tana jin tsoron wani abu,


"Azeezaty, zo nan mana" Biy guy ne ya kira sunanta, fitowa tayi idanunta na kallon ƙasa ta tsaya a tsakiyar su, gaba ɗaya ta tsargu da kallon da su ke yi mata, Hajiya Layla ta kasa rufe bakin ta saboda mamakin ganin yarinyar, sai taga kamar sunyi kama da Benazir ɗinta, sai lokacin Dr Jazz ya lura da ita sun ɗan ruɗe da kyawunta,  musamman Dr. Adam har dai ya gaza jurewa ya ce "Tabarakallahu ahsanul khalikin..." bai ƙare maganar ba, Dr jazz ya yi saurin yi mashi raɗa a kunne"kallon ya isa haka! Future wife ɗin babban yayanmu ce, wlh ka shiga taitayinka" da sauri Dr Adam ya rufe bakin shi da tafin hannu.


"Azeezaty, ina fata anyi maki bayanin abunda ya kawo ki nan?" ɗaga mashi kai tayi alamar eh,

"Okey, abunda muke so kaitsaye ki shiga ɗakin wurin patient ɗin, ki yi hugging ɗin ta sannan ki kirata da sunan Mommynki" amsa mashi tayi da toh, kafin slowly ta juya ta nufi ɗakin zuciyarta na dakan uku uku wani irin faɗuwar gaba take ji, gaba ɗaya sun nutsu suna kallon ta...

Duk taku ɗaya idan tayi sai gaban ta ya faɗi rass, ta rasa gane dalilin shigarta yanayin da take a ciki.

Tunda ta zura ƙafarta a ɗakin idanunta suka sauka akan mara lafiyan dake a kwance tana bacci, walking slowly ta ƙarasa ta tsaya daga bakin gadon tana kallon ta, tun daga kan fararen kafafuwanta har zuwa kan fuskarta, sumar kanta ta lullu6e gefen fuskarta daga gani ba ƙaramin hauka tayi ba kafin a samu ta runtsa.

Wata irin kasala ce ta baibaye Unaisah gaba ɗaya ta kasa ta6uka komai sai kallonta takeyi kamar zata haɗiyeta.....


"Ki rungumeta mana, ke muke jira" ƙasa ƙasa da murya Dr Adam ya furta maganar,

Numfashi ta ja kafin ta daidaita nutsuwarta, a hankali ta zauna daga gefen gadon kafin ta faɗa kan ƙirjinta tare da lumshe idanunta lokaci ɗaya ta fashe da matsanancin kuka me sautin gaske ita kanta batasan kukan Ya kubce mata ba, hankalinsu ba ƙaramin tashi ya yi ba amma sai suka yi zaton tayi ne don abun ya tafi dai dai..

Sautin kukanta ne Ya daki kunnan Benazir, cikin magagin bacci ta fara sambatu tana faɗin "Babyna, wayyo Allah mami! ina babyna naji sautin kukan ta, don Allah ku kawo mini ita..." yatsun hannunta na kerma ta ɗaura su kan bayan Unaisah, da dukan hannayenta biyu ta fara shafa bayanta taji mutun akan cikin ta, hakan yasa ta fara kokarin buɗe idanunta, daƙyar ta buɗe su sun kaɗa jawur saboda bacci,


Daga can waje Dr Adam ya ce "Nayi mamakin farkawarta, because bana tunanin allurar da nayi mata ta isa ta saketa..." 

Su Anila duk sun ƙagara Benazir ta karasa farkawa, gaba ɗaya jikinsu sai tsuma yake yi ga wani irin annurin farin ciki da ya wanke zukatansu,

Mayafin kan Unaisah tuni ya jima da zamewa, hakan yaba Benazir damar cusa hannayenta acikin sumar kanta ta cigaba da sambatu tana faɗin "Babyna ne? Mami daddy kuna ina? Wanene Ya kawo min babyna? meyasa take kuka?" Sosai Unaisah ta ƙanƙameta, ta ƙara cusa kanta a kirjin Benazir babu alamun zata saketa, Allah sarki jini ɗaya ba wasa ba, wannan unconditional love ɗin dake atsakanin uwa da ɗanta shine yayi tasiri a zukatansu, a karo na farko da ta fara jin ɗumin mahaifiyarta ba tare da sanin itace ba, aruɗe Benazir ta zabura ta ɗago da fuskarta ta ƙura mata ido tana kallonta, baiwar Allah Angel fuskarta tayi jawur da ita ruwan hawaye ya wanketa tass, da ƙyar take buɗe idanu tana kallon cikin idon Benazir, kallon kallo suka fara jefawa junansu duk hawayen Unaisah sun wanke fuskar Benazir, la66anta na kerma ƙirjinta na bugawa ta furta "Mamana! Ni ce babyn ki, meyasa kika tafi kika barni? kin manta dani a rayuwarki? Nayi kukan rashin ki atare dani mamana!"


Shigowa ɗakin Hajiya Layla tayi daga bakin gadon ta tsaya tana kallonsu, ƙwalla sun taru acikin idanunta,


"Mommy ki faɗamin? Da gaske babyna ne nake gani ba mafarki nake ba? Angel ɗina ne?" Kwata-kwata Angel bata fahimci sambatun Benazir ba saboda ita kanta ta ɗan shiga ruɗanin halin da ta tsinci kanta game da matar,


"Benazir, yarinyar ki ce Angel, ki rungume ta a jikin ki, " Hajiya layla ta faɗa da murmushi akan fuskarta, fashewa da kuka Benazir tayi, da sauri ta kwantar da Unaisah kan kirjinta ta rungumeta sosai kamar zata mayar da ita cikin cikin ta. 

Cikin shesshekar kuka take lallashin ta"kiyi shiru ki daina kuka, bana son ji, nasan nice na 6ata maki rai, kiyi hakuri ki yafe min bazan ƙara tafiya in barki ba, nayi maki alkawarin zan baki kulawa babyna, kinji my Angel"? Sambatu taci gaba da yi taƙi bari Unaisah ta ɗago da kanta ta ƙanƙame abun ta kamar wani yace zai kwace mata ita.....


Jikin Taj ba ƙaramin sanyi yayi ba, da sauri ya duƙar da kan shi hawaye sun cika idanunshi, sai yaji inama ace zai iya zuwa ya haɗa su duka a kirjinshi ya rungumesu,


Zahra sarkin tausayi tuni ta fara matse ƙwalla, ita kanta Aneleerh kukan ne ya kusa kubce mata, da hannu biyu ta toshe bakin ta don bata son ayi zargin ko yarta ce ta gaske,

Lumshe ido Chief ya yi a yayin da yake kallon su, ya jima baiga abun farin cikin da ya sanyaya zuciyarshi ba irin na yau! abun ya ta6a zuciyar shi....


Hatta Docs ɗin dake a tare da su saida suka ji tsananin tausayinsu, A hankali Dr shureim Ya zaro hanky daga aljihu Ya share kwallar da suka tarar masa, yana ji aransa da wuya yarinyar in ba jinin su bace!!


Dr Adam ne ya sauke yar ajiyar zuciya ya ce "in sha Allah zata samu sauƙi, naga alamun nasara tun kan aje ko'ina, Yarinyar ba ƙaramin wayau ne da ita ba, ta iya acting,..." kallon shi kawai Anila tayi su da suka san meke atsakanin su..

Dr jazz ma ya ce "Ubangiji Allah Ya bata lafiya, Allah yasa yarinyar nan ta zama silar warakarta" gaba ɗaya suka amsa mashi da ameen....


"Yalla6ai, muje office mu ƙarasa magana" Dr. Jidenna ne Yayi maganar, atare da Chief suka nufi katafaren office dinsa.Tattaunawa suka yi dangane da Unaisah, Chief ya ce masa baya son kowa ya sake shiga ɗakin mara lafiyan daga grandma ɗinta sai Unaisah, bayan haka Yana so a canza mata ɗaki su maida ta private room saboda Unaisah ta samu damar sakewa wurin yin jinyarta, ya ɗaura da faɗin "Bana buƙatar wani likita ya shiga dakin ta in ba Dr Jazz ba, shi nake so ya cigaba da kula da mara lafiyan"  Dr Jidenna ya ce "Consider it done sir, in sha Allah a cikin daren nan zamu aiwatar da komai" sun jima suna tattaunawa a office din kafin daga bisani suka fito a tare, har lokacin su Shureim suna a tsaye bakin kofar dakin suna kallon su Benazir,

Bayan sun dawo wurinsu chief Yaja hannun Dr Jazz suka ke6e wuri ɗaya dama shi mutuminsa ne, Yana jin dadin aiki da jazz yaron yana da hankali,

"Jazz, nayi magana da Md, kaine zaka cigaba da kula da mara lafiyan! Pls bana so asamu matsala!" murmushi jazz yayi "In sha Allah babban yaya zanyi kokari sosai gurin basu kulawa,"

"Good, sannan inaso ka duba jikin yarinyar, ta faɗamun bata jin dadi, pls inaso ka bata kulawa ta musamman, bana so ta nemi wani abu ta rasa! Kayi kokarin kwantar mata da hankalinta kamar akwai abunda ke damunta"

Jinjina kai jazz ya yi "In sha Allah My Boss, kasan bana wasa da duk wani abu da ya shafe ka" harara Chief ya ɗan watsa mashi, ya sunnar dakai ƙasa yana murmushi... 

Ruƙo hannunsa chief yayi suka koma wurinsu Taj,

Duba agogo big guy ya yi "Yakamata mu tafi dare yayi, almost 12,"

Da sauri Anila ta ce "pls muna son muyi mata bankwana kafin mu tafi"

Dr Adam ya furta "Okey, bari na kira maku ita" shiga dakin yayi,

"Azeezaty yan uwanki suna son ganinki zasu tafi, ki fito kuyi sallama" shiru yaji bata amsa mashi ba, leƙa fuskokinsu yayi abun mamaki bacci ne ya ɗaukesu rungume da juna bayan sun gama shan kukan, gaba daya Unaisah tana kwance kan jikin Benazir shiyasa gadon ya dauke su....

Fitowa Dr Adam ya yi fuskarsa ɗauke da murmushi ya ce "sai dai kuyi hakuri bacci suke yi, ba zamu iya tada su ba"

"Dr ga backpack ɗin kayanta, ka shigar mata da ita ciki" sauke jakar Taj ya yi tare da miƙa ma Dr Adam ya shiga da ita ciki ya ɗaurata kan kujerar gaban gadon.

Kamar kar su tafi haka suka dinga kallon su ta cikin door glass ɗin, kafin daga bisani suka kama hanyar barin asibitin, har bakin parking space Hajiya Layla ta rakasu tana ta faman yi masu godiya kamar zata duƙa ƙasa, shima Dr. Shureim godiya sosai ya yi masu tare da fatan alkhairi, sallama sukayi wa junansu Zahra da Anila suka shiga motarsu, Taj  da Big guy suka shiga tasu motar, kafin Chief ya shiga motarshi, saida Hajiya Layla ta ƙara yi masu Anila godiya saboda halaccin da su ka yi masu kafin motocin suka fuce a jere da matsakaicin gudu, ya rage saura Hajiya layla da Dr Shureim, su jazz tuni sun koma cikin asibitin..

"Shureim ka ga wani ikon Allah? Yarinyar nan tana kama da Benazir, bansani ba ko idanuna ne suke nuna min hakan"

Murmushi shureim ya yi "ba idanunki bane, nima naga kamanceceniyarsu, wlh Mommy naji dadin ganin yadda Benazir ta rungumi yarinyar ajikinta, sai naji inama ace yarta ce, saboda ta kwanta mun araina..." 

Hajiya layla ta ce "ba kai kadai ba shureim, nima yarinyar ta burgeni, ga wayau daga gani tana da kaifin basira, iyayenta sunyi mana hallaci kuma basu nemi komai daga gurin mu ba, ko da yake naga yarinyar ma ƴar masu arziki ce...."

Dr shureim ya ce "Mommy zan wuce gida dare yana ƙara yi, pls ki kula da yarinyar nan, kinga dai yadda yan'uwanta suka damƙa mana amanarta, bana so asamu matsala..."

"In sha Allah Shureim, ay bazan yi sakaci da rayuwarta ba, dole inyi takatsantsan tun da naga ɗiyar manya ce, hada fa jami'ai cikin waɗanda suka kawo ta" 

Ƙara tattaunawa suka yi kafin ya yi mata sallama ya buɗe motar shi ya shiga ciki, akan idon ta motar ta fuce daga asibitin, ajiyar zuciya ta sauke kafin ta juya ta nufi ciki cike da zumudin son ganin yarinyar..

______________________________✍️

Bayan su taj sun rako chief part dinsa, saida suka ga shigarshi cikin bedroom dinsa kafin suka sauko  falo, har sun kusa fita suka tsinkayi muryar ummi daga bayan su

"Boss sannun ku da zuwa"! Atare suka juyo tare da kallonta, sleeping gown ce a jikinta, ta yafa mayafi akanta, da alama ta fara bacci ta farka

"Yawwa Ummi, me kike yi har yanzu bakiyi bacci ba"?

Fuskarta ayamutsa tace"na kasa bacci saboda damuwar rashin unaisah, tun wuraren karfe takwas da rabi muke ta nemanta saboda muyi dinner shiru babu ita, ko'ina mun duba, ƴan uwanta ma dakyar na kwantar masu da hankali har su ka yi bacci, nayi zaton ko taje part din ka ne" Tay maganr tare da nuna taj


Big guy dake kallon ta from head toe gaba daya ta jefa shi ayanayi, saboda kayan baccin jikinta sun bayyana surarta,


"Ummi, unaisah ba agida zata kwana ba, taje asibiti" bai ƙare maganr ba, ummi ta zaro ido tare da dafe kirjin cike da tashin hankali tace"inna lillahi meke damunta? Bata da lafiya ne"? abun da yasa ta ruɗe saboda halin data ganta dazu a daki, abun ya tsaya mata arai, har jiran zuwanta tayi kamar yadda tace mata zata zo amma shiru bata neme ta ba...

Kwantar mata da hankali taj yai"lafiyarta ƙalou ba ita ce ke bata da lafiya ba, yar uwar chief ce...." bayani yayi mata dalla dalla, lokaci daya ta sauke ajiyar zuciya,

"Hankalina har ya kwanta, amma banji dadin tafiya da tayi batare data yi mana sallama ba, yanzu sai yaushe zata dawo gida"? 

"Bani da masaniya, amma bana tunanin zata dauki lokaci, pls ki kwantar ma yan uwanta da hankalli banaso su sanya damuwa aransu"

"In sha Allah, mu kwana lafiya boss, agaida min da madam" ya amsa mata da toh, satar kallon big guy tay ya wani tsareta da ido, harara ta dan watsa mashi haɗi da yin murmushi ta juya ta nufi ciki, harta bace ma ganinsa bai kauda idonsa ba, sai da taj ya bugi kafadarsa kafin ya juya suka fuce kowa ya nufi part dinsa..

______________________________✍️

Prisoners Shield💔

Bawan Allah, kwata kwata baya acikin hayyacinshi, Yasha bakar wahalar radadin da zuciyarshi keyi mashi, tun safe har kawo iyanzu da dare ya ratsa  ko ruwa bai gifta makoshin shi ba, saboda tashin hankalin da yake a ciki, yayi haukan yayi kukan amma babu abunda Ya canza nadaga kuncin da yake ji, babu wanda yayi tunanin ya leko dakinsa yaga awani hali yake ciki, saboda su kansu yan uwan nashi yanzu mantawa su ke yi da shi tun da suka fahimci bayason shiga cikin su kuma baya son kowa ya ra6e shi, a fahimtarsu, unaisah ita kadaice ta damu da shi, bata iya wuni batare da ta leko dakinsa ba, ta damu da shi fiye da yadda ta damu da kanta, itace farin cikinsa kuma gatansa, baya jin zai iya rayuwa batare da ita ba, Unaisah kaddararsa ce! Bugun zuciyarsa ce.

Cikin ikon Allah bacci mai nauyi ya ɗauke shi, hakan ba karamin relief ya sama mashi ba, yayi bacci sosai har na tsawon awanni, gab da za'a fara kiran sallar asuba, ya fara mutsu mutsu, yatsun hannayensa dana kafarsa suka fara kerma....."

Farat ɗaya ya buɗe idanunsa waɗanda suka kaɗa jawur tamkar garwashin wuta, Gaba ɗaya rasa ƙwarin gwiwarshi, kamar matacce Sam ya kasa motsawa daga kan floor, ko yatsansa Ya gaza ɗagawa, wani irin gumi ne Ya wanke jikinshi kamar wanda aka tsamo daga cikin teku, ta ko'ina zufa ke tsatsafo mashi, ga wani azababben zafi da jikin shi ya ɗauka.


shatun jijiyoyin goshinsa sun fito rudu rudu kan fatarsa,a kalla ya shafe mintuna yana kokarin sarrafa zuciyarsa gudun kada evil heart dinsa ta motsa, bakomai idanunse ka hango mashi ba face fuskar Unaisah.


Dakyar ya samu kwarin gwiwar motsa gabban jikinsa, Ya lalla6a Ya miƙe tsaye kan ƙafafunsa, jansu ya dinga yi saboda wani nauyi da sukai mashi dakyar yakai kan shi toilet ya faɗa ciki yana jan numfashi, agaban sink ya tsaya yana faman sauke ajiyar zuciya.


Sannu a hankali brain dinsa ta fara tariyo mashi abunda Ya faru daren jiya atsakaninsu, yaga komai a mafarkinsa.


ɗago da hannayensa yayi tare da saita su saitin fuskarshi Ya ƙura ma tafukansa ido Yana kallon su ....da sauri ya girgiza la66ansa na kerma ya furta"bani bane! Bada son raina ba, bansan na akaita ba, bana a cikin hayyacina!...." dafe kansa yai da hannu ɗaya ya cusa yatsunsa acikin sumar kanshi, ya cigaba da cakuɗata gaba daya ya haukata gashin kanshi, duk ya rikice saboda ya gane shine da kafafuwansa Yaje dakinta adaren jiya har yayi mata aika aikar nan sai dai yayi imanin bayin kanshi bane❗ cije la66ansa yayi har saida suka fashe jini ya fara ɗiɗɗigowa, wani irin tsanar kanshi ne Ya kama shi, kamar ya kashe kanshi haka Yake ji, da karfi ya buga forehead dinsa jikin sink nan take fatar wurin tayi jawur kamar zata fashe, buga kanshi yacigaba dayi yana sambatu yana fadin Ni ne da kaina na cutar da Angel dina? tana kuka tana rokona dan in taimaka mata amma nagaza share mata hawayenta, bani da tausayi, ni mugune, na tsani kaina..." jinine ya fara gangarowa ta kofofin hancin shi, wani irin jiri ya fara kokarin kwasarshi,  ya fara tangal tangal zai kife kasa kwatsam ba zato ba tsammani Yaji hannu mutun akan damtsensa, gaba daya ya janyo shi tare da rungume shi akan broad chest dinsa, ya zagayo da hannayensa akan bayan shi, bawan Allah baya gane komai, idanunsa sun makance, ji yake tamkar angel dinsa ce ta rungume shi, hakan ya shi ƙara ƙanƙame mutumin da ya rungumeshi duk ya 6ata mashi gaban Rigarshi da jininsa, hakan baidame shi ba, babban tashin hankalin shi halin da yaron yake aciki! Ya tsorata da ganin yadda yake kokarin kashe kan shi ❗lamarin yayi matukar gigita shi..

"Ki yafe min Angel, ba yin kaina bane, bazan iya cutar dake ba, sharri akaimin, ba halina bane, ki tausayama rayuwata, ke kadai ce farin cikin da nake da shi a duniyar nan, bani da gata daya wuce ke...." gaba ɗaya sambatunsa acikin kunnan sa, Ya nutsu Yana sauraron shi, har lokacin bai ɗago da kan shi ba, balle har yasan wanene Ya rungume shi.

___________________________________✍️

*Ga me bukatar karanta littafin kurkukun kaddara, 500 ne dukanshi za'a tura Via Opay, 8103884440 Hafsat Bature Muhammad, shaidar biya za'a tura ta whatsapp, 08103884440*

Post a Comment

Idan kuna da tambaya akan abinda Baku game ba ko kuma kuma Neman littafin da babu a nan kawai ku ajiye tambayarku a ta comment ko wani shawara da Zaku bamu.

Previous Post Next Post

Sponsored Link

Sponsored Post