Kurkukun Ƙaddara Takun Ƙarshe chapter 33 Complete

Kurkukun Ƙaddara Takun Ƙarshe chapter 33 Complete

Takun Ƙarshe

 ✍️

EPISODE 33

Sai da yayi mai isarshi kafin A hankali chief ya raba jikinsu daga na juna ya tallabo fuskarshi da tafukansa, kwata kwata babu kuzari a jikin shi kamar lagwanin fitila, fuskarshi ta 6ace da blood dinsa, idanunsa sunyi nauyi dakyar ya iya buɗe su ya kalli chief yana faman jan numfashi, wani irin tausayin shi ne ya kama shi ga tsananin ƙaunar yaron da yake ji, duk da baisan meke damun shi ba, a sambatun da yayi, chief ya fahimci sun samu sa6ani ne tsakanin shi da Unaisah! Shiyasa jiya a mota ta dinga yi mashi kuka, har tayi mashi karyar bata jin dadin jikin ta, yanzu kuma ga ɗan uwanta yana sambatu akanta har yana yunkurin halaka kan shi, hakan na nufin akwai wani abu daya shiga tsakaninsu wanda yayi silar jefa su halin da suke ciki?! Abun ya daure mashi kai.!



"Bansan meke damunka ba! banji dadin yadda kake kokarin illata kanka ba! Meyasa ba zaka nemi taimakon mu ba uhyum? 


Cikin kulawa yayi mashi maganar, shiru Danish bai tanka mashi ba saboda wani irin jiri jiri da yake gani a idanun shi


Ruƙo hannun shi chief yayi da niyar su fita daga toilet din don Ya duba lafiyar shi, da sauri Danish Ya fuzge hannun shi, dakyar sautin voice dinsa ke fita


"I don't want to see anyone! Just leave me alone! ka tafi kawai..."


"No bazan iya ƙyale ka ba, Idan kai baka damu dakanka ba, Ni na damu dakai, Please, Danish, let's go treat your nosebleed."


Girgiza kai Danish yayi"bana so, lafiyata qalou, zan kula da kaina, kawai ka tafi ni bana son ganin ka..  "


"Ni kuma ina son ganinka, ba inda zan tafi, in kaga nabar dakin nan to ka samun sauƙin abun da ke damun ka ne" babu wasa a fuskarsa yayi maganar tare da harɗe hannayensa kan kirjin shi, kallon kallon suka fara jefawa junan su, chief ya rasa yanda zaiyi da shi, yaron yafiye taurin kai ga kafiya, da ƙiwuya kamar yaron goye ...


Ƙwara ya lalla6a shi su wanye lafiya, idan ba haka ba zai iya illata kan shi..


Cikin sigar lallashi Yace"pls Danish, ka bani damar da zan baka kulawa, ba cutar dakai zanyi ba, bana jin dadin ganinka a halin da kake a ciki, na damu dakai Danish, ina jinka tamkar ɗan uwana, A shirye nake dana taimaka maka wurin ganin mun shawo kan abunda ke damun ka."


tun da chief ya fara magana cikin sanyin murya, Danish ya nutsu yana sauraron shi kamar yana fahimtar shi.


"Nayi maka alƙawarin ba zaka ta6a dana sanin yarda dani ba...." bai ƙare maganar ba, raunanniyar muryar danish ta katse mashi hanzarin shi"bazan ta6a yarda dakai ba, ƴan uwana kadai na yarda da su, amma ku ba abun yarda bane! duk halin ku ɗaya, kuna da son zuciya, ba ku da tausayi, Tun ina jariri na taso rayuwata a gidan kurkukun ƙaddara, bansan komai dangane da duniyarku ba, saboda an tauyemin hakkin rayuwata, ina da ciwon zuciyar abun da iyayena suka aikata min, bansan wani jin dadi na duniya ba, unaisah itace farin cikina......." wasu zafafan hawaye ne suka wanke fuskarshi, zuciyar chief ta karaya, baisan sa'adda hawaye suka cika idanun shi ba, sambatun Danish sun ta6a zuciyar shi, shi kanshi baisan Yana furta kalaman ba, rashin Angel ya fara zautar da shi, dama kuma abun ya jima yana ci mashi tuwo a kwarya.


Da sauri chief Ya ƙara huggin dinshi tighly a kirjin shi, kamar zasu koma mutun ɗaya, a hankali yake shafa bayanshi da tafukan hannayen shi cikin kwantar da murya ya soma yi mashi raɗa a kunanshi


"Danish ba duka muka taru muka zama ɗaya ba, ina rokon alfarma a wurinka, ka jarabani nayi maka alkawarin zan sanya farin ciki acikin rayuwarka, inaso na samu kusanci dakai, saboda na share maka hawayenka in kuma baka kulawa, bayan haka zanyi kokarin sasanta tsakaninka da ƴar uwarka unaisah duk da bansan meya faru atsakaninku ba"


Cikin sanyin murya ya furta"tayi fushi dani, ta daina sona, nasan ban kyauta mata ba, amma bayin kaina bane, ina so na bata hakuri koda ba zata cigaba da kula ni ba, ni burina ta yafe min kada ta ruke ni a zuciyarta, hukuncin yayi min tsauri bazan iya jure ba...ka taimaka min dan Allah..." a karo na farko da Danish Ya ambaci sunan Allah, ba tare da shi kanshi Ya lura da furucinsa ba, lumshe ido chief yayi, wani irin sanyine ya ratsa zuciyar sa, har lokacin suna a rungume da juna, yaji dadin damar daya samu dama burinshi yaja shi a jikin don su samu abunda suke so, yanzu ya samu mafita, ya riga daya gane lagwonsa wato Unaisah, yayi imanin badan sun samu sa6ani atsakaninsu ba, da bazai ta6a samun damar da har Danish zai kula shi ba, murmushin gefen fuska ya saki aranshi ya furta yanzu wasan zai fara🔥


"Zan taimaka maka in sha Allah, zanyi iyakar bakin kokarina gurin ganin kun sasanta tsakaninku, amma fa sai ka yi hakuri ka cire damuwa aranka, yanzu muje ayi maka treatment na bleeding dinka"


"Bani buƙata, zan iya gyara kaina" ya fada tare da raba jikin su daga na juna, ya sanya hannu ya matse hancin shi, nan take jinin ya daina ɗiga.


"Inason zanyi wanka" fita chief yayi daga ɗakin, ya tsaya a bedroom dinsa Yana jiran shi, tufka da warwara ya fara dangane da yadda zai ja shi a jikin shi , yaso yaji meya faru atsakaninsu sai dai ya fahimci baya son sanar dashi, kamar yadda itama unaisan taki sanar da shi, bai damu da hakan ba, saboda shima baison yaji abun da zai hana shi runtsawa kwara atafi ahaka yana dai kyautata masu zato.


Kafin fitowar Danish Ya kira landline na kitchen Ya isar da sakon Yana bukatar breakfast a kawo mashi a dakin Danish


Within 10 mins chef Ya shigo hannun shi ruƙe da tray na kayan abinci har saida gabanshi ya faɗi ganin jinin dake agaban jallabiyar chief bai dai tanka ba, tun da ya gaishe shi Ya sauke masu akan table kafin Ya fice daga dakin.


Harya fara gajiya da tsayuwa, jin motsin buɗe kofa Yasa shi saurin kai idon gare shi, Ya fito fess dashi kamar wani abu bai ta6a faruwa ba, towel ne ɗaure a waist dinshi, tun da ya fito chief yake kallon shi, bai ji dadi zanan tatttoo din da akai mashi ba, daga bayan shi har gaban kirjin shi da damtsen hannun shi zanan waɗannan halittunne masu zako zakon akaifu, launin ja da baƙi bawai don baiyi mashi kyau ba, hasalima kyau zanan yayi mashi sai dai abun da yake jimawa ranar daya musulunta dole yaji ba dadi saboda haramunne zanan tattoo kuma daga gani permanent ne nashi irin wanda bai gogewa, sauƙin shi ɗaya Idan ya musulunta bashi da zunubin komai.



har saida ya nufi closet kafin chief ya kau da ido daga kallon shi, ƙarnin jinin ne Ya fara takura mashi fucewa yayi daga dakin Ya nufi dakin shi, ya canza kayan jikin shi ya sanya wata jallabiyar kafin ya dawo dakin danish.


A zaune ya same shi akan mirror chair ya sanya short da singlet a jikin shi, ya zabga uban tagumi da hannun shi biyu, har yanzu ba yaji shi daidai.


"Danish bismilla, taso muyi breakfast, nasan baka ci komai ba" cikin kulawa yai mashi maganar

In a cool voice Ya furta"bana iya cin komai, Unaisah nakeson gani..." ya yi maganar tare da mikewa Ya nufi kofar fita daga dakin, da sauri chief yasha gabanshi...

"Unaisah bata nan, ko kaje dakin su ba zaka ganta ba" 

Hankalin shi atashe ya furta"ta gudu saboda tana fushi dani ko"? Ya fada idanunsa cike tab da kwalla"

Girgiza kai chief yayi"ba abunda kake tunani bane, muje mu zauna  I'll explain everything to you.."

Related Books:


 ya ruko hannun shi suka zauna daga gefen gado suna fuskantar junansu..

Calmly chief ya zayyana mashi komai dangane da zuwanta asibiti, bai boye mashi komai ba ...." bawan Allah har cikin ranshi yaji dadi da unaisah ta haɗu da mamanta, sai dai yana jin tsoron ta juya mashi baya tun da ta samu iyayen ta..."


"Angel dina taga mamanta"? Jinjina mashi kai chief yayi, 

"Kaima in sha Allah iyayenka zasu bayyana kuma zasu baka farin cikin daka rasa arayuwarka ..." yanayin fuskarshi ne Ya canza zuwa tsantsar 6acin rai.


"Bana son su, bani bukatarsu, bana son ganin su, na tsane su, ni bani da iyaye, unaisah ce gatana" murmushi chief yayi.

 

"Baka tunanin kaima iyayenka suna kaunarka? Think about it. zai iya yiwuwa wani ne a danginka ya sadaukar dakai ba iyayenka ba, kai da kanka kace tun kana jinjiri aka sadaukar dakai, watakil iyayenka basu san an sace masu kai ba, don ni gaskiya bana tunanin a duniyar nan za'a samu iyayen da zasu haifi kyakkyawan yaro kamar kai su suyi watsi da shi...." shiru Danish yayi baice mashi komai ba, kamar yana nazarin maganar shi, sai dai babu alamun zai fahimce shi.


Cikin dabara chief yacigaba da kwantar mashi da hankali, har ya samu suka ci abinci atare, bayan yayi mashi alkawarin zai kai shi wurin Unaisah amma ya bashi shawarar ya ɗan bata tazara watakil ta sauko daga kan dokin zuciyar da tahau...yace mashi bazai iya ba, baya jin dadi in bata atare da shi, yafi son yaganta akusa dashi ko da bazata kula shi ba.. Akarshe  yace mashi da anjima zai kai shi wurinta suga juna in har hankalin shi zai kwanta....


Lokacin da su Batool suka farka har yar rige rigen zuwa dakin unaisah su kayi don suga kota dawo amma suna shiga suka iske babu kowa, Hankalin su ba ƙaramin tashi yayi ba, wasu har sun fara kuka, saida Ummi ta sauko down ta same su zazzaune kan sofas kowannansu Ya zabga uban tagumi kamar masu zaman makoki.


Suna ganin ummi suka nufe ta"aunty ummi har yanzu yar uwarmu bata dawo ba, dan Allah ina taje ne bata fada mana ba"?

Kwantar masu da hankali tayi kafin ta sanar da su inda taje, har suna hada baki wurin fadin aunty ummi dan Allah zamuje asibitin wurinta, harma muga yar uwar chief din muyi mata ya jiki" 

"Kuyi hakuri, ba za'a bari kuje ba, ku bari ta dawo kawai, in sha bazata jima ba" rigima suka sanya mata musamman jemaimah da azeeza dakyar ta samu ta shawo kansu har suka hakura.


_______________________________✍️


*OIH*


A hankali ta buɗe idanunta, ta ƙurawa ceilling ido na wani lokaci, kafin ta shafa jikinta da hannunta, jin babu mutun yasa ta yunƙura zata miƙe da sauri hajiya layla ta taimaka mata ta zauna, muryarta na rawa ta furta"wayyo Allah na, mami ina babyna? wa ya dauke min ita? Jiya fa na ganta da ido na, har na rungumeta a kirjina! Ko dai mafarki nayi ne..."? gaba ɗaya tabi ta ruɗe ta ɗaga hankalin ta, dafa kadarta hajiya layla tayi fuskarta da murmushi tace"kwantar da hankalin ki, babyn ki tana nan cikin koshin lafiya kuma tana a tare dake" girgiza kai tayi tana faman zare ido tace"to ay banganta ba! Babu ita ko'ina, wani ya dauke min Angel dina..." ta fada tana laluba bedmattress.


tun da asuba aka canza masu room yanzu suna a privet room na asibiti, tamkar bedroom na gida haka Yake, har gado ɗaya aka ƙara masu saboda ya ishe su ita da unaisah.


"Mommy wlh bata nan, ta 6ace, wani ya sace min ita, nama san taj ne Ya gudu da ita saboda yana jin haushina...." saukowa tayi daga kan gadon ta durkusa tana leƙen karkashin gadon sumar kanta duk ta rufe fuskarta da bayanta...

"Benazir me kikeyi anan ki tashi mana, nace maki yarki tana atare dake yanzu zata fito, Ki zo ki sha maganin ki, ga breakfast an kawo mana..."  ta faɗa tare da ruko hannunta, fashewa tayi kuka tana fadin"wayyo Allahna mami, wlh babu ita, na shiga uku na bani na lalace, baby ta 6ace..." duk yadda hajiya layla taso ta shawo kanta abun Ya faskara gaba daya nema take ta zauce...

Motsin buɗe kofar toilet ne Ya katse mata kukan nata, a firgice ta juya tana kallon kofar tana faman zare dara daran idanunta, tundaga kasa ta fara kallon kafafuwanta dake asanye da slippers farare tas da su, da sauri benazir ta wurga idanunta kan fuskarta, harsaida ta lumshe su saboda wani sanyi daya ratsa zuciyarta, fitowarta kenan daga wanka, doguwar riga ce a jikin ta pink colour tayi wani fresh da ita kamar babu damuwa atare da ita.



Ƙurawa juna ido sukayi batare da kyaftawa ba, hajiya layla dake kallon su tsabar murna bakinta yaƙi rufuwa yadda kasan gonar auduga.



Cikin sanyin murya unaisah ta furta"mamana! Kin tashi lafiya! Ya jikin naki? Kin farka baki ganni ba am sorry na shiga toilet yin wanka ne..." wani irin bugu zuciyar Benzar tayi yanayin fuskarta ya nuna kamar tana kokarin dawowa hayyacin ta ne.


Murmushi Angel ta sakar mata har dimple dinta suka lotsa, kamar ta samu tv haka ta ƙura mata ido tana kallon ta.


"Benazir baki gane ta ba? Babyn da kike nema ce, Kije wurin ta..." jikinta na 6ari kamar mazari ta mike ta nufi unaisah, tana karasawa ta zube kan gwiwowinta ta sanya hannu biyu tayi huggin dinta tightly akan kirjinta, wani irin yanayi suka tsinci kansu mara misaltuwa, kusan a tare heart dinsu ke bugu da karfi da karfi, tuni kwalla sun cika idanun kowan nan su.


"Babyna ne"? Ta fada tare da tallabo fuskar unaisah ta ƙura mata ido tana faman zare mata idanunta har saida gaban angel ya fadi tarasa gane meyasa take jin ta kamar mahaifiyarta.


"Kinyi shiru baki amsa min ba! Baby na ne? Ke ce? Ta fada tana ɗage mata eye brows dinta.


Jinjina mata kai unaisah tayi"ni ce mamana" yawu benazir ta haɗiya kafin ta furta"taj ne Ya kawo min ke uhum? Yana ina"? Rass gaban Angel Ya faɗi ta zaro ido tare da kallon hajiya layla wadda ta kura masu ido tana kallon su gwanin ban sha'awa.


 Lamarin ya daure mata kai, meyasa take ambaton sunanta da sunan daddynta? To kodai itama sunan yarta ne da mijinta hakan? Abun da daure kai, tayaya akai sunan su yazo ɗaya"? Ta jefa ma kanta tambayar da bata da amsar ta, ranta ne ya raya mata ay ba ita kadaice me irin nickname dinta ba suna dayawa, shima sunan taj din ba daddynta kadai ke da shi ba, hakan yasa ta saki jikin ta.


Jinjina mata kai tayi"daddyna ne Ya kawo ni, shima yana nan zaizo wurinki amma sai kin kwantar da hankalinki..." cike da zumudi tace toh toh zan kwantar da hankalina..."

Huggin dinta unaisah ta karayi wani irin dadi takeji, ta dade batayi bacci mai dadi irin na jiya ba, bata ta6a zaton zata iya runtsawa ba saboda halin damuwar datake a ciki na abun da ya faru tsakaninta da Danish amma cikin ikon Allah silar baiwar Allahn nan jiya tayi bacci mai nauyi kuma ta samu relief na radadin da zuciyarta keyi mata.


"Mamana, Ki shiga toilet, kiyi wanka zaki ji dadin jikin ki, Idan kika fito dakaina zan baki abinci abaki .." wani irin dadine Ya lullu6e benazir, da sauri ta kalli hajiya layla idanunta cike tab da kwalla tace"mommy tana sona sosai, dama nasan bazata guje ni ba, saboda ita jinina nace, kuma tasan bada san raina na gudu nabarta ba..."


rass gaban angel ya fadi maganar benazir ta jefata arudani, lokaci daya brain dinta tafara tariyo mata labarin mamanta data gudu tabarta a kwamin wanka, tuni yanayin fuskarta ya canza zuwa tsantsar 6acin rai, gani take kamar yawancin iyaye mata basu da tausayin ya'yansu shiyasa suka watsar da su bayan sun haife su.


"Benazir ki shiga kiyi wankan, babynki zata jiraki anan" jikin ta na rawa ta mike ta shiga toilet din, tun zuwansu  hajiya layla ke taimaka mata tayi wanka saboda rashin nutsuwar da bata da ita, amma yau da kanta tayi wanka abun ba karamin dadi yayi ma hajiya layla ba, atare suka zauna da angel ta fara bata abinci abaki tana ci sai dadi take ji, ita ma ta dauki spoon ta debo ta sanya ma angel abaki hajiya layla nata kallon su gwanin ban sha'awa bayan sun kammala cin abinci, dr jazz ya shigo duba lafiyar benazir shi kanshi ya fahimci nasarar da suka fara samu don alamu sun nuna takusa regaining hankalin ta....yau ko allura ba'ayi mata ba, magungunanta kadai suka bata tasha.


Kafin dr jazz yabar dakin saida Ya kira unaisah, suka ke6e a kofar dakin ya tambayeta meke damunta? Chief ya fada mashi bata da lafiya..." murmushi tayi masa kafin tace"ba abunda ke damuna, lafiyata qalou.." lallashinta ya dinga yi yana lalla6ata duk don ta fada mashi amma ta nace akan ita lafiyarta qalou, yace toh shikenan idan akwai wani abu da kike bukata ki sanar dani, chief ya bani amanarki bana son ganin damuwa atare dake, har cikin ranta taji dadin maganarshi, tace in sha Allah zan baka hadin kai dr, nagode da kulawarka agare ki, bayan tafiyar jazz ta juya zata shiga dakin har saida suka bangaji juna ita da benazir, taji shiru bata ganta ba shine tabiyota kada asace mata babynta, murmushi unaisah tayi tare da ruko hannunta suka koma cikin dakin, daga jiya zuwa yau wata irin shakuwace mai karfi ta shiga tsakaninsu, duk wani motsin unaisah akan idon benazir ta hanata sukuni tana a maƙale da ita ko toilet bata son ta shiga, tafi son taji dumin jikin ta anata, haka itama unaisah ko tari Benazir tayi saita nuna damuwarta akanta.


Wuraren karfe 12 dr shureim da Alhaji ubaid suka zo asibitin, a bakin kofar dakin jami'an dake sanye da fararen kaya suka dakatar da su suka ce ba abada iznin shiga ciki ba, hankalin dr shureim ba karamin tashi yayi ba saboda baisan da dokar za'a hanasu shiga room din ba, Alhaji ubaid yace bazai yiwuba babu yadda za'ay su hana shi ganin yar shi, tun da harya tako yazo dole ya shiga ya duba lafiyarta, ganin dagaske ba zasu bari su shiga bane yasa dr shureim kiran layin hajiya layla, bayan ta ɗaga ya sanar mata zuwansu, fitowa tayi daga dakin sanye da hijabi, wani irin annurin farin ciki suka gani akan fuskarta, bayan sun gaisa Alhaji ubaid Yace"ya mai jikin? Ina fata jikin nata da sauki. " murmushi hajiya layla tayi"mai jiki Alhamdulillah, benazir ta fara samun lafiya, shureim bai fada maka abun farin cikin daya faru jiya ba"? Murmushi alhaji ubaid yayi"ya fada min, wlh naji dadi nayi murna naso ace na gana da iyayen yarinyar don inyi masu godiya" 


labari ta fara basu na abunda ya faru da safen nan ta ƙara da cewa"yarinyar tana da wayou, baka ganta ba kamar benazir dince ta haifata sunyi kama, abunda yafi daure mun kai shakuwar su baka ga yadda suke tarairayar junansu ba.  " wani irin dadine Ya lullu6e dr shurem da Alhaji ubaid


"Alhamdulillah, ubangiji Allah Yasa yarinyar ta zama silar warakarta. " suka amsa mashi da ameen

"Yanzu ba zamu samu ganin Benazir din ba"? Alhaji ubaid ne yayi maganar, 

Hajiya layla tace"ba zasu bari ku ganta ba, kuyi hakuri kawai har zuwa lokacin da zasu salleme mu"

Dr shureim Yace"gaskiya ni bazan iya hakura ba, ina son ganin yar uwata..Alhaji ubaid yace ni bansan dalilin kafa dokar ba, in ma za'a hana wani ya shiga ay dai ba a hana ni ba, ni da nake mahaifinta.." kiri kiri jami'an suka hana su shiga ciki gashi sun kwallafa rai akan son ganin su, zuwan dr jazz ne Ya sama masu maslaha, da farko yayi kokarin fahimtar da su dangane da dalilin dayasa suka hana shiga, Yace iyayen yarinyar ne basa son wani abu ya samu yar su, shiyasa suka sanya tsaro a asibitin bayan haka basu san wani abu da zaisa ita benazir din ta gane ba mamanta bace" Alhaji ubaid yace su dai a taimaka abarsu su ganta.."_ ganin ya kafe ne yasa dr jazz ya kira chief a waya ya sanar da shi dangane da zuwansu Alhaji ubaid, shiru yayi jim yana nazari dama don saboda Alhaji ubaid suka kafa dokar amma daya tuna yadda taj ya fada masa ya yi ma unaisah bayani akan ko wani ya nuna ya santa kada ta nuna ta sanshi, ya dai san in suka hadu idan ta ganshi zata iya gane shi tun da yarinyar da wayon ta amma bai kamata su hana family din mara lafiyan ganin ta ba zasu iya zargin wani abu, hakan yasa chief furta"Jazz ku bar su su shiga, amma kada su ɗauki lokaci, sannan ka sanya ido akan su bana son fira mai tsayi ta shiga tsakanin su da yarinyar .." amsa mashi yayi da toh, bayan sun gama wayar ya sanar da su Alhaji ubaid sun samu iznin shiga amma kada su wuce mintuna biyar, lokacin da suka shiga unaisah ta shiga toilet, bata samu ganin su ba, ta dai jiyo muryoyinsu a dakin suna magana, sunyi jiran fitowarta amma har time ya cika ba ta fito ba, sai bayan da suka fita daga ɗakin kafin ta fito daga ciki.



Around karfe 3 na rana su Anila suka zo tare da su mami hada abie, bayan sun gaisa sukayi ma hajiya layla ya mai jiki tace masu,  ay tama fara samun sauƙi sosai, har labari taba anila na irin shakuwar da sukayi, ba karamin dadi taji ba, su kansu sun lura da cigaban da aka samu na lafiyarta, saboda tana gane kowa dayazo wurinta, har sunayensu take kira, Unaisah taji dadin zuwan aunty Anila, har tambayar baby junaid tayi anila tace mata ta yi hakuri school yake zuwa kuma sai marece yake dawowa cikin gida, bata ji dadi ba saboda ta kwallafa rai akan son ganin shi, lallashinta anila tayi tace kada ta damu zatayi kokari koda cikin weekend ne zata kawo mata shi, sun jima a asibitin kafin daga bisani suka tafi


_________________________________✍️




Bayan sallar magrib, Unaisah tana zaune gefen gadon benazir dake akwance tana bacci ta ruƙe hannunta acikin nata don kada a sace mata babynta, 

Hajiya layla tana zaune kan darduma hannunta ruƙe da cazbaha tana ja,..."


Baiwar Allah duk dauriyar da takeyi sai da tagaza jurewa duk bayan ƴan mintuna sai ta shiga toilet ta yi kuka, tayi kokarin cire shi aranta ta kasa, zuciyarta sai azalzalarta takeyi akan shi, bata bari hajiya layla ta gane halin da take a ciki ba ....


A hankali ta cire hannunta daga na benazir, ta mike ta shiga toilet ta tsaya agaban sink, ta fashe da kuka da sauri ta toshe bakinta da tafukan hannayenta don kada su jiyota, fuskarta tayi jawur hatta idanunta sun kankance, damuwarta awani hali yake a ciki? Tasan halin shi yana da wuyar sha'ani ba lallai ya yarda da wani ba, zai cigaba da killace kanshi ne adaki watakil ma har zuciyarshi ta buga Ya rasa ranshi! Wa zai bashi kulawar da take bashi? Mutumin da baisan komai ba sai soyayyarta itama tasan da hakan, Itace jindadin shi na rayuwar duniyar nan...amma meyasa yayi mata hakan? ya rasa akan wa zai gwada rashin imaninshi sai akanta? Abunda yafi 6ata mata rai tana fama da radadin ciwon ciki ya nemi illata rayuwarta, duk in ta tuna yadda ya janyo kafafuwanta cikin rashin imani ya wurgar da ita kanta gado ya hambare kanta, abun Ya 6ata mata rai, sai dai har yanzu wani sashe na zuciyarta yaƙi aminta da zargin da takeyi mashi saboda bai ta6a yunkurin cutar da ita ba wannan ne karo na farko daya farayi mata hakan...." runtse idanunta tayi wani irin kululun bakin cikine Ya tokare makoshin cikin karyayyar murya ta furta"meyasa kayi min haka? Me nayi maka dana cancanci hakan daga gare ka? Ka rasa wa zaka cutar sai ni? Angel dinka? Mai son ganin farin cikinka me share maka hawayenki"?


Ta jima acikin toilet, sai da ta gama sambatunta, kafin ta wanke fuskarta ta fito jiki asanyaye, wayarta ce ta fara ringing, da sauri ta nufi backpack din ta curo wayar tare da duba sunan mai kiranta, tayi mamakin ganin sunan chief Owais ya bayyana, tun time da daddynta ya bata layinsa bata ta6a kira ba ta daiyi saving dinta.



Picking call din tayi tare da kara awayar a kunne cikin sanyin murya ta gaishe da shi ya amsa mata

"Ya mai jikin"?

Tace"alhamdulillah, da sauki sosai, bacci takeyi yanzu"

"Okey, ina fata dr jazz Ya duba lafiyarki"? Ya fada tamkar baisan abun da ke damunta ba..

"Eh, naji sauki ma"

"Okey, nazo asibitinne, amma ban shigo ciki ba, Ina parking a space, Yanzu zan turo ataho mun dake..." waro ido tayi jim kafin ta amsa mashi toh,

Bayan ya katse kiran ta sanar da hajiya layla game da zuwan chief


Ko minti biyar ba ay ba, sai ga agent sanye cikin kaki, da sauri ta dauko hijab ta zura a jikin ta, Allah yaso benazir bacci takeyi da kuwa ta hanata fita.


Tana fitowa daga dakin agent din Ya miƙa mata face mask, ta sa hannu ta kar6a kafin ta sanya a fuskarta, tabi bayan shi suka fito... Tunkafin su karasa harabar ajiye motocin ta hango chief ya dauki wankan suit, yana daga tsaye ya jingina bayan shi jikin motarsa, fuskarsa na asanye da mask, gaba ɗaya hankalinsa na akan wayarsa da yake dannawa. ...


"Assalamu alaikum..." sanyayyar muryarta ce ta ratsa kunnanshi, A hankali ya ɗago suka haɗa da juna da sauri ta sunnar da kanta kasa kamar wata munafuka, kunyar shi taji tunawa da huggin dinta da yayi a jiya.  

Lumshe idanunshi yayi tare da sake buɗe su kan fuskarta, jiya zuwa yau ba karamin jinta yake a cikin zuciyar shi ba.


"Ya kuka ƙare da Sis din nawa"? Murmushi tayi kafin ta fara bashi labarin shakuwarsu.. " kallon ta kawai yakeyi daga yanayin ta ya fahimci taji dadin kasancewarta da mamanta hakan ba karamin faranta ranshi yayi ba

"Kinyi kuka ne"? da sauri ta girgiza kai alamar a'a

"Kada kiyi min ƙarya, naga alamun hakan a idanunki" shiru tayi jikin ta ya fara kerma sam batason kowa yasan abunda ke damunta...

"Ina daddy na da yan uwana"? tayi mashi tambayar ne don ta mantar da shi

"Baki da layin shi"? 

"Ina da shi, amma wayar babu card da zan kira shi" 

"Ina wayar" da sauri ta fiddo da hannunta, ta miƙa mashi ita, bayan ya kar6a yace"ki shiga cikin motar, ki jirani" amsa mashi tayi da toh...


Buɗe mata murfin motar yai, kwata kwata bata lura da mutun a ciki ba, ta kutsa kai ta shuga ta zauna, wani irin ni'imtaccen sanyin A.c ne Ya ratsa fatar jikin ta mai hade da kamshin turare

Wurga idon da zatayi karaf ta sauke su akan fuskarshi, ta cikin mirror ta hango shi, kiris Ya rage ta fasa ƙara saboda ta tsorata batasan da mutun ba

A firgice ta kalle shi, yana a gefenta farar jallabiya ce a jikin shi, fuskarshi sam babu walwala, zuciyarta ta hasala ranta ya 6aci da sauri tafara kokarin bude murfin motar taji shi a garƙame kamar taga wani mugun abu..

Hakan ba karamin karya mashi zuciya yayi ba, wani irin shakkarta Yake ji

"Angel... Pls ki tsaya inyi maki bayani nasan zaki fahimce ni..." banza tayi dashi kamar bata ji me yace ba


"Nayi zaton kece mutun na farko da zaki fara yi min uziri ki fahimce ni idan na aikata badai dai ba sainaga ba haka ba, kamar bakisan wanene ni ba"? Muryarshi ba karamin kashe mata jiki tayi ba, ta haɗe fuskar kamar bata ta6a dariya ba duk don kada yayi tunanin zata raga mashi...

Fashewa tayi da kuka tana fadin"bana son jin muryarka! Bana son ganin ka! Meyasa kazo"? Hawayene suka wanke fuskarshi.

"Pls ka kyaleni in rayuwata, yanzu bana bukataka, na riga na gane ba dan Allah kake tare dani ba akwai wata manufa aranka..."  ta faɗa tana zare mash gray eyes dinta wadanda suka kada jawur da su. 

"Bazan ta6a sauraronka ba, saboda kai makaryaci, kayi min karya danish meyasa baka yarda cewa kaine ka aikata min hakan ba lokacin da nazo dakin ka"? Ta jefa mashi tambayar tana kallon fuskarshi duk yabi ya dabarbace sai lokacin ta lura da yanayin shi har rama yayi ga wata matsananciyar damuwa data gani akan fuskarshi

"Kiyi hakuri ki yafe min Angel, na aikata babban kuskure, amma ki fahimce ni bada son raina na aikata miki hakan ba, nima bana acikin hayyacina, lokacin da kikazo dakina na manta komai daya faru saboda bayin kaina bane sai daga baya nayi mafarkin abunda ya shiga tsakanin mu..." ya faɗa yana haɗiyar yawu mai ɗaci. 


"Angel kinsan bani kadai bane kuma har yanzu elders suna bibiyar rayuwata ko su zasu iya shiga tsakaninmu don su rabani dake saboda sun san cewa ke daice lagona, ta hanyar shiga tsakanina dake ne kadai zasu iya cin galaba akaina.." wani irin faduwar gaba take ji, ita kanta bata son tayi silar da zai koma kurkukun ƙaddara, maganar tashi taso tayi tasiri azuciyarta....


Jin tayi shiru yasa shi tunanin ko ta yafe mashi ne, matsawa yayi kusa da ita, ya ɗan kwantar da kanshi saman kafaɗarta da sauri ta sanya hannu ta ture shi da karfi ta wurga mashi harara da kakkausar murya tace"kada ka ƙara gigin ta6ani! Idan har ba so kake inyi maka abunda baka ta6a tsammani ba! Kabarni inji da abunda ke damuna Danish! Ka nisanta kanka dani zaifi maka kwanciyar hankali"


Kamar karamin yaro haka ya fashe mata da kuka, bawan Allah Ya rasa meke yi mashi dadi a duniyar nan


"Ki tausayama rayuwata angel, ki yafe min koda ba zaki cigaba da kula ni ba, bana so kina fushi dani, na yarda na amsa laifina, ki yanke min kowani irin hukunci ne a shirye nake dana kar6e shi...."


Bata ta6a ganin tashin hankalin akan fuskarsa irin na yau ba, taji tausayin shi amma in ta tuna irin rashin imamin daya yi mata adaren shekaran jiya sai ta ji taƙara jin tsanar shi, akan me zataji tausayin shi bayan shi bai tausaya mata ba? kalaman auntyn ummi ne suka fara dawo mata cikin kanta, idan har tabari namiji yana ta6a ta zata samu ciki, wannan maganar ta ɗaga mata hankali, tabbas in har ta cigaba da bashi fuska zaicigaba da kokarin kusanta kanshi da itane, wannan dalilin ne yasa tace"Zan yafe maka, amma abisa sharaɗi ɗaya"? Jikinsa na kerma yace"wani irin sharaɗi ne"?

"Kayi min alkawarin zaka yi komai nace"? ɗaga mata kai yayi alamar eh

"Daga rana irin ta yau bana so ka kara kusanta kanka dani...." kafin ta kare maganar yace"bazan iyaba angel..." da sauri ta daura yatsanta kan la66ansa da ruwan hawaye suka jiƙa tsit yayi yana sauraronta

"Idan har dagaske kai garkuwa ne agareni mai bani kariya daga dukkan abun cutarwa toh inaso kabani kariya daga sharrinka danish! Ka nisanta kanka dani, in har kana son farin cikina, saboda ganinka da nakeyi a yanzu raina yana 6aci..." wasu zafafan hawayene suka kara wanke fuskarshi

"Baka da mafita data wuce wannan! In har kayi min hakan zan yafe maka.." runtse idanunshi yayi yana jin wani irin kunci da takaici kamar ya binne kanshi haka Yake ji, bakomai ya fado mashi aranshi ba face kalaman chief, dayace mashi ya bata tazara kada ya tursasa mata saboda ayanzu tana akan dokin zuciya! 

Numfashi Yaja kafin a hankali ya buɗe idanunshi a acikin nata, har saida gabanta ya fadi ganin yadda suka kaɗa jawur tamkar an watsa mashi barkono a cikin su, kyakkyawar fuskarshi ta 6aci da ruwan hawayen shi har cikin ranta tana jin kamar bata kyauta mashi ba.  

Cikin rauni na murya yace"na amince in har hakan zaisa ki yafe min, bazan ƙara takura maki ba" dakyar ya kare maganar, kafin ya kifa kanshi saman laps dinshi

"Danish! Ta ambaci sunan shi bai amsa mata ba, 

"Bana so wani yaji abunda ya faru atsakaninmu! Koda chief ne! Duk da bansan ko ka riga da ka faɗa masa ba" muryarshi kasa kasa yace"ban fada masa ba" ajiyar zuciya ta ɗan sauke, da sauri ta share hawayen ta kafin ta kuma cewa"don na yanke alakar dake atsakaninmu hakan ba yana nufin bana sonka ba! Kawai bana son ka akusa dani ne, sannan bana son hukuncin da na yanke ya shafi rayuwarka! kada ka hana idon ka bacci saboda dani, kuma kada ka ƙi cin abinci, idan kayi hakan bazan ji dadi ba..." tana magana hawaye na kara wanke fuskarta, kasan hijab din jikinta ta sanya ta share hawayen kafin ta daidaita nutsuwarta.




Kafin Takai hannu ta zuge window glass ɗin motar, tayi ma chief magana don ya buɗe mata car door ɗin da ta gaza buɗe wa, dagangan Ya datse kofar motar shiyasa ta gaza buɗe, yanzu daya tabbatar sun gama magana, da kanshi ya buɗe mata, ta fito idanunta cike tab da kwalla dakyar ta haɗiye kukan da take ji, haɗa ido sukayi cikin na juna, muryarta ƙasa ƙasa ta furta"mun gama magana inaso zan tafi" bata san hawayen da take 6oyewa sun fara sintiri kan fuskarta ba, hanky ya zaro mika mata"ki share hawayenki"! Kar6a tayi a hankali ta fara share kwallar

Iphone dinta dake a hannun shi ya miƙa mata"na sa maki card, zan kira anjima zamu yi magana, ki koma ciki yanzu" amsa mashi tayi da toh nagode, kamar karta tafi haka take ji tana tafiya tana waiwayon motar zuciyarta cike fal da tunanin shi....


*AFTER SOME DAYS*


(Bayan wasu kwanaki)


tun daga ranar da chief Ya kawo danish asibitn bai ƙara matsa mashi akan ya kawo shi ba, daga shi har ita unaisah din sunji jiki ba kaɗan ba daurewa kawai sukeyi, sauƙin su ɗaya kowannansu Ya samu abunda Yake ɗebe mashi kewa, chief ya zama tamkar abokinshi baya barin shi acikin damuwa, sai da yasan ta yadda yai harya samu kar6uwa a wurin danish, kullum suna atare abinci ma atare suke cin shi, abu uku ke raba su lokacin sallah, lokacin zuwan chief wurin aiki da kuma lokacin bacci, wani lokaci har ƙarfe shabiyu na dare suna kaiwa adakin danish harya fara koya mashi yadda zaiyi rubutu da yadda zaiyi amfani da waya harma da laptop, saboda yana son su fara making phone call da prime minister hateem, su big guy har mamaki sukeyi idan suka ga chief da danish suna magana cos basu ta6a tsammanin yaron zai iya sakar ma wani jiki acikin su har haka ba, bawan Allah Danish dannewa kawai yakeyi ba dan chief yana kokarin lallashinsa da debe mashi kewa ba da tuni ya jima da zaucewa, saboda rashin ganin unaisah ba karamin illa yakeyi mashi ba, duk daren Allah sai ya farka da radadin rashin ta, shi kadai yake haukanshi kafin Allah ya kawo mashi sauƙi, bai ta6a bari chief yaga gazawarshi ba tun da ya fahimci mutumin baya son damuwarshi kuma yana bashi kyakkyawar kulawa...


Idan muka koma 6angaren Benazir jikinta yayi sauƙi sosai, tana samun kulawa a wurin mutane ukun nan da suka tsaya mata, dr jzz, hajiya layla da kuma unaisah, cikin ƴan kwanakin nan ta dawo hayyacin ta sai dai babu wanda Ya lura da hakan kuma bata nunama kowa ba, ita kanta tasan dalilin ta nayin hakan, dagangan take yin pretending, kusan kullum ne sai su anila sunzo dubata, haka zalika Alhaji ubaid da shureim basa gajiya da zarya wurin zuwa asibitin, har ila yau Alhaji ubaid bai haɗu da unaisah ba, ba su ta6a cin karo ba, duk lokacin da zaizo tana a toilet, ko tana bacci, itama Hajiya sarah tana kokarin zuwa asibitin duk da ayyukan office da suke yi mata yawa, sau ɗaya suka ta6a haɗuwa da unaisah har suka gaisa da junan su wani abu daya daurema unaisah kai muryar matar tayi shige data cousin din aunty pretty da ta ta6a kira, aikuwa aranar har jaraba kiran layin aunty pretty tayi saboda ta tuna da ita, sai dai kash ba'a ɗaga kiran ba, saboda wayar ta koma hannun zeenatu dr shureim ne ya bata donsu dinga gaisawa, ita kuma dama bata cika ruke waya a hannunta ba, sai ta wuni bata dauketa ba sai in ta tashi kiran dr shureim tukunna take daukarta..


Alhaji musa tun zuwan da yayi sau ɗaya, bai ƙara zuwa asibitin ba, ko awaya baya kira balle har yasan wani hali suke a ciki, gashi har dr ya fara tunanin sallamar su saboda taji saukin jikin ta sosai..


*DAGA ALƘALAMIN BOSS BATURE✍️*


*Ga me bukatar karanta littafin kurkukun kaddara, 500 ne dukanshi za'a tura Via Opay, 8103884440 Hafsat Bature Muhammad, shaidar biya za'a tura ta whatsapp, 08103884440*

Post a Comment

Idan kuna da tambaya akan abinda Baku game ba ko kuma kuma Neman littafin da babu a nan kawai ku ajiye tambayarku a ta comment ko wani shawara da Zaku bamu.

Previous Post Next Post

Sponsored Link

Sponsored Post