Kwas! kwas !! sautin takalmanta Ya ratsa kunnuwansu, kusan atare su Aneelerh suka ɗago tare da kallon inda sautin ke fitowa...
Ƙura idanu sukayi suna kallon su, kafin Aneelerh tayi wani irin yunkuri ta miƙe jikin ta na 6ari, zuciyarta na dakan uku uku, gaba ɗaya tabi ta rikice gani take kamar a mafarki take kallon su!! Kokwanto ta farayi anya kuwa sune? Tajudeen da Angel? Ko dai idanunta ne suke nuna mata badai dai ba? Tayaya mutanan da suka 6ace almost 16years yau kwatsam ta gansu, da ransu da lafiyar su, kanta ne ya wani irin sara mata da sauri ta dafe goshin ta, ganin hakan yasa Zahra ta miƙe a matuƙar ruɗe take kallon Aneelerh...
Lokacin da unaisah ta ɗaura kwayar idanunta akan fuskar Aneelerh, Ras taji gabanta Ya faɗi, wani irin burki taci ta dakata da yin tafiyar, idanunta azare take kallon ta, wlh ko amafarki taga fuskar Aneelerh sai ta shaida ta balle kuma azahiri, La66anta na kerma ta furta"Aunty Aneelerh? Daddy! Auntyna ne? Ita ne nake gani azahiri ba mafarki ba? Daddy wallahi itace aunty Aneelerh ce...." kalamanta ne suka dira akan kunnan Aneelerh, baiwar Allah jiki na 6ari ta watso da gudu mayafin ta har yana ƙoƙarin zamewa, da gudu unaisah ta nufe ta, takalman kafarta suka kusa kayar da ita kasa, amma ahaka ta jure don bazata iya jira aunty Aneeleeh ta karaso gareta ba, zubewa Aneelerh tayi akan gwiwowinta tare da ware hannayenta biyu ta rungume unaisah, tayi hugging dinta tightly lokaci ɗaya suka fashe da matsanancin kukan farin ciki mai tsuma zuciya 😖
A hankali taj ya ƙaraso Ya tsaya daga bayansu, tare da goya hannayensa bisa kirjinsa.
A sukwane hajiya saratu da chief suka miƙe tsaye suna kallon su, fuskokin kowan nan su ɗauke da murmushi su kansu da suka sake haɗa wannan zumunci ba karamin dadi suka ji ba, farin cikin da suka gani akan fuskar Aneelerh da unaisah ba zai misaltu ba.
Yadda Aneelerh ta rungume unaisah, kamar zata mayar da ita cikin cikinta, a kalla sun shafe mintuna goma manne da juna, kafin Aneelerh ta raba jikin ta daga na Angel, a lokacin itama ta durƙusa kan gwiwowinta, Aneelerh ta sanya tafukan hannayenta biyu ta tallabo fuskar unaisah da su, itama unaisah ta tallabo fuskar Aneelerh da nata tafukan hannun, suka kurawa juna ido yayin da hawaye ke sintiri kan fuskokinsu, cikin shesshekar kuka Aneeleeh take fadin"Angel dina! Kece nake gani? Dan Allah ki fahimtar dani nagaza yarda da abun da idanuna suke gane min! Wayyo Allahana.." ta fada tana jan numfashi.
"inna lillahi Ya Allah Idan Mafarki nake kada ku tada ni, kubarni kawai inci gaba da yin shi, Ya ilahi Angel dina ce..Ina kika shiga? Kika bar auntynki da ciwon rashin ki? Angel wayyo Allah...duk tabi ta susuce
Cikin muryar kuka unaisah tace"Aunty Aneeleeh, ni ce Angel dinki, ƴarki, Aunty Aneeleehna, ba mafarki kike Yi ba, ni ce dagaske, Angel dinki abokiyar firarki, mai sanyaki nishadi..." ƙara rungumeta Aneeleerh tayi.
Gyaran murya taj yayi cikin karayar zuciya ya firta"Aneelerh!.." kamar jira take yayi magana, a zabure ta mike ta tsaya agabanshi idanunta jawur ta furta"taj! kasan irin haukan rashin ku da nayi? Me nayi maka dana tsantsanci haka daga gareka?..." kwalar rigarshi ta damƙa da hannayenta biyu ta jijjiga shi kamar zata rufe shi da bugu taci gaba da fadin"taj meyasa kayi min haka? Meyasa ka gudu da unaisah kuka barni da kewarku? Taj kasan irin kunci da radadin dana naji a lokacin dana farka naga babu ku"?
Kalamanta sun karya zuciyarshi baisan sa'adda hawaye suka wanke fuskar shi ba, Zahra dake kallon su tuni hawaye sun wanke fuskarta ga wani farin ciki da ya lullu6e ta na ganin Unaisah, Jikin chief owais yayi sanyi lakwas tsantsar tausayinsu ne ya kama shi, ba shi ba hatta Hajiya saratu sai da taji tausayinsu duk da bakomai ta sani ba dangane da rayuwar su ba.
"Taj Ina mijina? Ina uzair! nasan Yana atare ku? Ka faɗa min taj meyasa kuka gudu daga gida? Tsawon shekara da shekaru baku ta6a waiwayena ba? Laifin me nayi maku taj? Idan wani abu ne yasa kuka gudu meyasa baku sanar dani ba? Harga Allah bakuyi min adalci ba taj! dai dai da rana ɗaya baku ta6a nema na ba ko da awaya ne...." Daƙyar ta ƙare maganar, Lokaci ɗaya ta yanke jiki zata faɗi da sauri taj ya tarota ta faɗo kan kirjinsa.
Da sauri zahra ta karaso gabansu tana kuka, zuƙunnawa taj yayi a hankali ya kwantar da kanta bisa laps din sa, har lokacin Angel tana a durkushe kan gwiwowinta da karfi take furta"Aunty aneelerh ki tashi! Dan Allah ki tashi wayyo Allahna daddy ka ce mata ta tashi" duk tabi ta rude zahra ma kukan take tana ambaton sunanta, Hajiya saratu ta kasa furta komai, lamarin ne da ta6a zuciya..
robar ruwa mai sanyi chief ya dauko daga kan table, Ya nufo wurinsu Ya buɗe murfin tare da mika ma Taj, Hannunsa na kerma Ya kar6a Ya tarfa ruwan a tafin hannu Ya watsa mata kan fuskarta, nan take taja mumfashi tare da furzar da shi...
Cikin karyayyar murya ya furta"Anila! dan Allah ki saurareni, wallahi bada son ranmu muka gudu ba, mummunar ƙaddara ce ta afka mana wadda tayi silar barinmu gida..., na rasa komai nawa Aneeleeh..." ya faɗa yana kallon cikin idanunta, dakyar take kallon shi, wani irin azababben ciwon kaine Ya far mata, ita kadai tasan halin da take a ciki.
"Nasan zaki fahimce ni Aneeleerh, har abada kinsan bazan Iya gudunki hakanan ba tare da wani ƙwaƙƙwaran dalili ba, dukan mu babu wanda baiyi kewar rashinki ba, kuma ko bayan da muka gudu kina aranmu bamu manta dake ba....."
"Taj ina mijina...."! Gabansa ba karamin faduwa yayi ba, kallon chief yayi da sauri ya girgiza mashi kai alamar kada Ya faɗa mata, saboda a halin da take ciki muddin suka sanar da ita tsaf zata iya zaucewa.
"Aneelerh, bansan Ina uzair Yake ba! Idan ba zaki manta ba, ba atare muka bar gida ba, adaren ranar da abun ya faru kinzo har gida kin same ni kina kuka kika ce uzair bai dawo ba, har na kwantar maki da hankali, tun daga wannan lokacin ban ƙara sanya uzair a idona na, amma muna nan muna bincike akanshi, in sha Allah shima zamu gano shi.
zuciyarta ba karamar karaya tayi ba, tuni ta sake fashewa da wani sabon kukan.
Kafin wani ya sake magana a cikin su, wayar Hajiya saratu ta fara ringing, da sauri ta zaro wayar daga cikin handbag dinta, ta duba mai kiran ta, p.a din tace, picking call din tayi"Okey, Gani nan zuwa yanzu nan.." ta faɗa tare da katse kiran ta dago ta dubi chief.
"My son yakamata na tafi, naso in tsaya amma kirane na gaggawa, duk halin da ake ciki pls ka sanar da ni..." ta fada cikin saurin murya, kafin ta dubi su Zahra.
"Zahra, Ni zan wuce, in sha Allah idan na samu time zanzo asibitin in duba mara lafiyan..." tayi masu fatan Alkhairi, godiya suka dinga yi mata, Har bakin mota chief tare da zahra suka rakata, akan idonsu motar ta fice daga gidan.
Dawowa sukai wurinsu Taj dake a durkushe ƙasa.
"Taj baka fadamin meyasa kuka gudu ba..."? Cikin jin ƙunar rai ta jefa mashi tambayar.
Atakaice ya labarta mata abun da ya faru da su, tun farkon da suka fara yi ma Alhazawan nan leƙen asiri da kuma farmakin da suka kawo mashi atsakar dare harya gudu da Angel....."
sai dai bai sanar da ita wayar da uzair ya kira shi ba ya dai ce shi baisan meya faru da uzair ba, har yau suna neman shi ba su gan shi ba, hankalinta yayi mugun tashi jin wannan musifar data afka masu, hatta zahra tayi matuƙar firgita jikin ta sai tsuma yake abun ya bata tsoro...
"Shiyasa bamu neme ki ba, saboda rayuwarmu tana a cikin hatsari, idan har miyagun suka san muna raye ba za su kyale mu ba, don dole muka killace ce kanmu kafin Allah ya tona asirin su"
"Inna lillahi wa'inna ilaihirraji! taj wannan wani irin tashin hankaline! Ni dama saida raina ya bani ba hakanan kuka gudu ba, Allah Yasa basu kashe uzair ba, nama san mawuyacin abune uzair ya rayu watakil sun kashe min shi...." bai bari ta ƙare maganar ba, Ya fara lallashin ta dakyar Ya shawo kan ta....
Zafafan hawayene suka cigaba da wanke kuncin ta,
"Boss!" chief ne Ya kira sunan shi
"Na'am yalla6ai"
"Ina son magana daku, ban da unaisah"
A hankali Ya ɗago da Aneeleeh, da sauri zahra ta zuƙunna tare da tallabo ta don gaba ɗaya jikin ta ba kwari dakyar ta samu ta miƙe.
Unaisah dake kallon su ta shiga ruɗani tunda chief Yace Yana son ganin su ban da ita...
Ruƙo hannunta taj yayi, suka nufi sofas din wuri ya zaunar da ita
"Daddy meya faru"?
"Kada ki damu, magana ce mai mahimmanci zamuyi, Idan muka gama zamu sanar dake, cike da gamsuwa tace toh
"ɗazu Kin faɗa min kina jin yunwa, ga snacks nan da juice ki sha kafin mu gama magana" yatsun hannunta har kerma suke wurin daukar burger ta fara cin ta.
idanunta akan su Aneelerh dake tafiya suna nufar can nesa da ita, zuciyarta cike fal da farin ciki, kamar wadda akaiwa albishir da gidan Aljanna, bakinta yaki rufuwa sai faman tariyo fuskar aunty aneeleeh takeyi, burinta su gama maganar don ta tambayeta ina ƙanin ta da daddynta ya bata labari ta haifa mata....
Bayan kowan nan su ya zauna kan kujeru suka nutsu suna jiran jin me chief zai sanar da su
"Inaso ku faɗa masa abun da ya kawo ku neman ƴar sa"! Ya faɗa batare da ya ɗago ya kalli waninsu ba, aɗan ruɗe Taj Ya kalli su Aneeelerh.
Baiwar Allah tama rasa ta ina zata fara, saboda tasan ba lallai Ya amince masu ba.
"Aneelerh kinyi shiru! Faɗa min meyasa ku ka zo neman Angel? Tun jiya chief yayi min bayanin zuwan ku amma bansan cewa ku bane, nayi mamakin ganin ku! Tayaya har kuka gano inda mu ke!? Ya fada cike da son jin ƙarin bayani.
Cike da fargaba Aneeleeh ta fara zayyana masa abun da ya faru na bayyanar benazir, bata 6oye mashi komai.
tunkafin ta ƙarasa maganar yanayin fuskar taj ya canza zuwa tsantsar 6acin rai, kwata kwata baiji dadin bayyanar benazir ba, saboda tafi ta aransa baya buƙatarta arayuwar shi, wani irin ɗaci yaji aran shi, Aneeelerh ta fama mashi tsohon raunin dake a zuciyar shi.
ko sunan ta baison ji, aranshi ya arayyana da ranta da lafiyarta tsawon shekara da shekaru bata ta6a neman su ba? Idan har shi bata neme shi ba ay yakamata ko yarta ta nema baisan wata irin zuciya bace a kirjin benazir ya riga da yasan halinta domin kuwa ba zai ta6a manta irin rayuwar auran da sukai da ita ba, macace mara kunya batasan darajar aure ba, ta azabtar da shi da soyayyarta.
gaba ɗaya sun lura da yanayin shi, kamar baya atare da su, Aneeleerh duk tasha jinin jikin ta, dafa kafadarsa chief yayi a hankali ya kallesa idanunshi sun kaɗa jawu"dan Allah kada kace inyi hakuri, saboda bana jin zan iya yafewa benazir, hasalima ban yarda cewa dagaske ta damu da mu har haka ba, Allah kadai kasan manufar da take da ita akan mu, ba zan ta6a yarda da benazir ba, matar da ta tafi tabar yarta a kwamin wanka, taje can tana yawon biɗiɗin ta tsawon shekaru bata ta6a neman mu sai yanzu"? Hawayen dake taruwa a cikin idanunsa tuni sun wanke fuskarshi hakan ba karamin ɗaga hankalin zahra da Aneeerh yayi ba..
Shi kadai yasan ƙunar da zuciyar shi take yi mashi
Shiru chief yayi sam ya kasa furta magana,
Cikin karyayyar murya Aneelerh tace"dan Allah taj kayi hakuri mu manta da abun da ya wuce, Benazir tayi nadama, neman ku take ruwa ajallo don ta nemi yafiyarku, wallahi taj ta riga ta gane kuskurenta" tana magana tana marairaice mashi fuska don ya tausaya masu"ka dubi girman Allah ka kuma duba darajar yarinyar dake atsakaninku ko dan saboda ita yakamata ka sassauta mata, Allah ma muna yi mashi laifi ya yafe mana balle mu da muke ƴan adama, taj ita kanta bada son ranta ta gudu ba kamar yadda na faɗa maka asiri akayi mata, yakamata kayi nazari kada ka yanke hukunci cikin fushi, nasan Benazir bata kyauta maku ba, amma ka duba pls, tana fa sonku shiga akayi tsakaninku saboda babu yadda za'ay uwa ta haifi ɗan sunna tayi watsi da shi......"
babu alamun taj zai fahimci maganar ta, idanunsa sun kaɗa jawur bakomai yake tunano ba face lokacin da ta ɗauki cikin unaisah hauka ne kadai batayi ba saboda ta tsani ciki, har fadi take zai bata mata shape din jikin ta, bayan haka tasha yin yunƙurin zubda shi Allah bai nufa ba.
"Pls, koda bazaka yafe mata ba, dan Allah ka amince Unaisah ta gana da mahaifiyarta..." kafin ta ƙare maganar yace
"Aneelerh kin riga da kinsan ƙiyayyar da unaisah take ma benazir, tunkafin ta mallaki hankalin ta, unaisah bata buƙatar mamanta, Nima kuma bana bukatarta...." hankalinsu ba karamin tashi yayi ba, Ga samu ga rashi, kallon chief Aneelerh tayi ya kasa kunne yana sauraron su.
"Dan Allah ka taimaka mana ka sanya baki a maganar nan!...." ta fada hawaye na bin fuskarta.
Duk yadda taj yaso hana chief magana sai da ya sanya baki
"Taj, I won't come between you and your ex-wife, Unaisah ita ce damuwata! Bana so ta rasa gatan da uwa take ba ɗan ta! duk irin tsanar da tayi mata wlh tana bukatar soyayyar mahaifiyarta fiye da taka!" ya ɗan dakata da maganar yana kallon taj, wanda ya nutsu yana sauraron shi.
"kai kanka ba zaka so unaisah ta rasa albarkar mahaifiyarta ba, shin zaka so unaisah tabar duniya ba tare data gana da mahaifiyarta ba? Ya jefa mashi tambayar cikin tausasa harshe shiru taj yayi
"Zaka so ne ta mutu da bakin cikin mahaifiyarta? Taj Ka riga da kasan mahimmanci uwa a addinance, ko da kuwa ta banza ce, bana so mahaifiyar yarinyar nan ta mutu a sanadin rashin ganin yarta da batai ba, kuma bana so unaisah ta rasa soyayyar mahaifiyarta, ba zakai mata kwaɗayin ta samu ladar dake a cikin kyautatama iyaye ba? Ka gama da iyayen ka lafiya ita bakaso ta gama da nata iyayen lafiya ne"?
cikin kwantar da murya chief ya cigaba dayi mashi nasiha, su Aneelerh duk sun nutsu sun kasa kunne suna sauraron shi, mutumin Ya kara shiga ransu, yadda yake magana cikin hikma da ilmi ba karamin sace mashi zuciya yai ba.
Jikin shi yayi sanyi sosai, kalaman chief sun ratsa zuciyar shi, aranshi yana ji koda bazai yafewa Benazir ba, zai yi kokarin haɗa Unaisah da maman ta, Benazir taci albarkacin chief wlh da ko kallo bata ishe su ba. Koda kuwa zuciyarta zata buga ta mutu ne....."
Gyaɗa kai yayi cikin sanyin murya yace"Na amince, wallahi taci albarkacinku, bazan iya watsa maku ƙasa a ido ba, Ina matuƙar ganin ƙimarku da darajarku, kuma bana fata Allah Ya nuna min ranar da zan bijire ma bukatarku..." ya faɗa yana kallon chief da Aneelerh, har cikin ran su sunji dadin maganar shi.
Hanky chief Ya zaro daga pocket dinsa Ya miƙa ma taj don ya share hawayen shi, da sauri Ya kar6a yai masa godiya kafin ya share fuskarshi
"Yanzu za'a iya bamu aronta muje da ita asibitin"?
"Ban amince a fita da ita daga gidan nan ba, sai dai Idan mara lafiyar za'a kawo nan ta zauna"! Acewar chief, yarfa hannu Aneelerh tayi, tuni murnar da suke ta koma ciki, muryar ta kamar zata fashe da kuka tace"dan Allah ka taimaka mana! Ka dubi girman Allah ku bamu ita, mu kai ma mamanta, Benazir ba zata iya zuwa nan ba..." saukowa tayi daga kan kujerar ta zukunna kan gwiwowin ta, da sauri ta yace tashi ta zauna, jiki asanyaye ta koma ta zauna.
"Aneelerh kina ganin unaisah zata yarda idan taji cewa wurin mahaifiyarta zaku kaita? kin riga da kinsan irin tsanar da tayi mata, tun kafin ta mallaki hankalin ta...." dafe kai Aneelerh tayi, sam ta manta da wannan zancen ita dai burinta kawai Angel taga mamanta
"Ya zamuyi taj? Wallahi nasan mawuyacin abune Unaisah ta bamu hadin kai"
Taj yace"ko nayi rantsuwa ba zanyi kaffara ba, Unaisah ba zata amince da ita ba don ta yanzu..."
"Kana nufin ta san komai game da yadda mahaifiyarta ta gudu bayan ta haife ta?"
"Ta sani yalla6ai"!
"Ya salam, kunyi babban kuskure da kuka sanar da ita, saboda kun dasa mata ƙiyayyar mahaifiyarta, tun da kuruciyarta, kuma yaro yana da ruƙon abu a zuciya....."
Shiru taj yayi shi kanshi yasan yayi kuskuren sanar da Angel, duk da ba a hayyacinsa ya faɗa mata ba, a lokacin da take cikin azabtar da shi da rashin jinta, har ya taushe mata fuska da pillow, aranar ne ya sanar da ita, don ta tausaya mashi tasan cewa shi kadai ne gatan da take da shi......."
Shiru sukayi tsit na wani lokaci, Kowa da abunda Yake saƙawa aran shi
Unaisah dake zaune tana shan lemu sai kallon su take Yi, ta rasa me suke tattaunawa, tsawon lokacin nan basu gama ba, gashi ta ƙosa ta sake huggin din auntyn ta.
"Ko da zan baku unaisah! Zan gindaya maku sharudda, saboda a halin Yanzu bincike mukeyi kan case dinsu, Rayuwarsu tana a cikin hatsari, babu buƙatar kowa yasan suna araye, daga ita har taj din!" hankali atashe zahra da Aneelerh suka kalli fuskar chief da yayi maganar.
"Dalilin dayasa tun farko na kira ku gefe ɗaya, don in gargaɗe ku akan kada ku kuskura kuyi gangancin da wani zaisan suna araye!!...." babu wasa akan fuskarshi yayi maganar.
"Idan har kukai kuskuran da wani Ya sani, ku kuka da kanku! zaifi kuyi takatsantsan yadda mukai maganar anan to mu binne komai anan"!
ya faɗa tare da kwankwasa table din gabansa.
Zahra ba karamin tsorata tayi ba, Jikin ta har ya fara kerma, dama da biyu chief ya tsoratar da su don su dauki maganar serious kada su 6ata masu dokar aikin su.
Murya na rawa Aneelerh tace"in sha Allah ba zamu bari wani ya sani ba,..." la66an zahra na kerma tace"wallahi nima bazan yi kuskuran sanarma wani ba, nayi maku alkawari..." Aneelerh tace"zahra bata da matsala, zata rufa mana asiri, ba zata bari wani ya sani ba, amma ni damuwana tayaya zamuje da unaisah asibitin"?
"Unaisah ba zata bamu matsala ba, Zan ja mata kunne akan kada ta fadama kowa ina araye! Ita ma kuma kada ta bayyana kanta koda wani ya nuna ya santa! abun da yakamata shine zaku je da ita amatsayin yarinyar da kuka ce zaku kawo masu, kada abari kowa yasan itace yarta ta ainihi!"
gaba ɗaya sunyi amanna da maganar Taj,
"Itama unaisah za'a fada mata cewa zataje duba mara lafiyane wadda yarta ta 6ace mai kama da ita, ta hakane kadai zamu samu yardarta, inyaso daga baya idan suka shaƙu da juna ta yadda ba zata iya jurar rashinta ba, sai afaɗa mata gaskiya" sai da taj yakai Aya Aneelerh tace"amma anya ba za'a samu matsala ba? Benazir idan tana sambatu sunanka dana Angel take fadi saboda mun riga mun fada mata sunan yarta, bayan haka Alhaji ubaid yasan unaisah, itama tasan shi! Kana ganin idan ta ganshi bazata nuna ta sanshi ba? Ko ta tambayi meye alakarshi da mara lafiyar....."
Calmly chief yace"wannan ba matsala bane, idan har zamu bada unaisah dole asibitin ya kasance a karkashin kulawar jami'an mu, zamuyi magana da likitocin dake kula da mommyn nata, zamu sa ahana kowa shiga dakinta, daga ita Unaisah din sai grandma dinta, ko itama tasan ta ne"?
Girgiza kai tay yai"a'a hajiya layla bata san angel ba, bana tunanin ko a hoto ta ta6a sanin ta, saboda babu zumunci atsakanin ta da taj...."
Taj yace"abun zaizo mana da sauki saboda kaf dangin Benazir ba wanda yasan Angel sai kakanta, bayan haka bana tunanin sambatun da maman nata takeyi zai tona asirin wacece ita, duk da Angel tana da kaifin basira but zata ruɗe ne saboda tasan ba ita kadai bace mai suna angel after that koda ta furta sunan taj ba lallai tai tunanin ni take nufi ba"! ajiyar zuciya Aneeelerh da zahra suka sauke a lokaci ɗaya.
"Amma da zarar ta dawo hayyacin ta, Aneelerh ki sanar da ita cewa yarta ce, sannan kiyi kokarin jan kunnanta akan kada tace zata furta wata kalma da zaisa unaisah ta gane itace mahaifiyarta...." amsawa sukayi da toh
Chief ya ɗaura da cewa"Ko da zamu baku ita, ba yanzu ba, sai zuwa dare zansa akawo ta asibitin, She will be under the care of our officers because we won't be careless with her life..." cike da gamsuwa suka amsa mashi da toh, sunjima suna tattaunawa, a karshe taj shi Ya ce zai yi magana da unaisah dangane da zancen zuwanta asibitin bayan haka sun yanke shawarar canza mata suna duk dan kada a gane itace.
Godiya su Aneelerh suka dinga yiwa chief kamar zasuyi mashi sujjada, har saida taj yace su daina baison ana yi mashi godiya kafin suka dakata har cikin ransu sunji dadin hadin kan da suka samu a wurin shi........"
Unaisah kamar jira take su kammala maganar, tana ganin sun nufo wurin ta, jiki na 6ari ta miƙe ta nufesu, murmushin farin ciki suka saki, da sauri Aneeelerh ta ɗauketa kamar karamar yarinya ta rungumeta a jikin ta, zahra sai jin dadi take yau gata ga yarinyar data kwallafa rai akai.
Su uku suka zauna kan sofas din, taj da chief suna zaune can inda suka baro.
Aneelerh ta kasa janye idanunta daga kan Angel, tayi mamakin girman ta, ga wata madarar kyau da tayi komai nata ya canza mata, sai faman sakar ma juna murmushi suke yi.
"Aunty aneelerh, daddy Ya faɗa min kin haifa min baby boy, Yana Ina?
"Angel, ƙanin ki junaid Yana a school, bawan Allah, Kullum burinshi yaga Angel, Yana matukar sonki Angel, tun yana jariri nake nuna mashi hotunanki, Yasan komai dangane dake ganinki ne kadai bai ta6a yi ba...." marairaice fuska tay kamar zata fashe da kuka
"Ina son ganin shi..." da sauri zahra ta lalubo hoton junaid awayarta ta mika ma Unaisah, yatsun hannunta har kerma sukeyi wurin karbar wayar, ta kura mashi ido tana kallon ɗan kyakkyawan yaron aunty aneenerh, wani irin farin cikine Ya bayyana akan fuskarta, hada videos dinsa ta kalla.
"Aunty Aneelerh, fuskarshi kamar anyi photo copy din fuskarki, dake yake kama, Wallahi harna ƙosa mu haɗu da ɗan ƙanina, In rungume shi a jikina in ji ɗumin shi, Ya Allah nagode maka da ka nuna min wannan ranar, ga ni ga aunty na, ga ɗan kanina da zan gani wayyo dadi...." zahara dake kallon ta ji take kamar ta rungumeta, Yarinyar tajima da sace zuciyarta, tun ranar da suka hadu awurin dinner din hateem ashe da rabon su sake haduwa matsayin yar uwar mijin auntynta......
"Angel ga zahra, itace ta ɗauko min hotonki awurin dinner, ɗiyar uncle dina ce..." sai lokacin Angel ta dubi zahra dakyau, nan take ta gane fuskarta, da sauri taje ta rungume zahra, fuskar kowan nan su da murmushi....
"Angel ina tayaki murnar ganin auntynki, Nima nayi murnar ganinki, wallah ba zan iya misalta farin cikin da nake a ciki ba, naji dadi dana zama silar haduwarku...." ta ƙare maganr tare da raba jikinta daga na Unaisah, share mata hawaye tayi da tafukan hannayenta"ki daina kuka kinji, Allah yakamata muyiwa godiya daya sake hadaku, naga ma kamar baki da lafiya, fuskarki ta kumbura, Jikinki da zafi..." cikin kulawa da nuna tausayawa tayi mata maganr
Cikin sanyin murya tace"lafiyana lou, babu abunda ke damuna, farin cikin ganin auntyna ne" ta fada tare da kallon Aneelerh dake kallon ta.
Wayar Aneeleerh ce ta fara ringing, ta ɗauko bag din data bari kasan sofa ta zaro wayar
"Tun bayan da chief ya kiraku wayarki take ta ringing, banaso na katse maku tattaunawarku shiyasa ban kawo maki ita ba..." murmushi aneelerh tayi aranta ta ayyana har yanzu tana nan da wayonta, ga hankali
Ko da ta duba screen din wayar missed calls ta gani sunkai ashirin, daga wurin mutun uku hajiya layla da dr shurem dana mami din su..
Unaisah zan amsa kira" amsa wa tay da toh, mikewa aneelerh tayi ta nufi gefe ɗaya, tabar zahra zaune tare da Unaisah kamar wasu kawaye haka suka fara fira
Hajiya layla ta fara danna wa kira, bayan sun gaisa hajiya layla tace"Aneelerh ya ake ciki? Naji shiru baki kirani ba, ko dai iyayen yarinyar basu bamu ita bane? Wallahi jiya ko baccin kirki Benazir batayi ba, tana ta sambatu tana ambaton sunan yarta .."
"Ki cigaba da kwantar mata da hankali, nayi magana da iyayen yarinyar sun bamu ita, amma sai zuwa anjima zata zo asibitin"
Muryar Hajiya layla da alamun farin ciki ta furta"Alhamdulillah!....wallahi naji dadi Aneenerh, dan Allah kuyi mana godiya wurin iyayanta..."
Murmushi Aneelerh tayi"in sha Allah zanyi masu" sallama sukai da juna, ta sauke ajiyar zuciya, idanunta akan su unaisah, wani irin sonta ne ke kara baibaye zuciyarta,
Layin mami ta kira, ko sallama Aneelerh bata kaiga yi ba, mami ta katse ta da cewe"Aneelerh sai yanzu zaki kirani? Baki ga missed call dina bane? Kunsa inata zullumi, na kasa tsaye na kasa zaune..."
"Allah sarki mami, Yanzu na dauko wayar, banga call din ki ba"
"Toh ya ake ciki ne"?
"Mami, mun ga yarinyar, dagaske ba unaisah bace, zahra tayi kuskuren fada mata sunan ta, ashe ita wannan sunanta Azeezaty, suna bala'en kama da unaisah, amma iyayen yarinyar sun bamu aron ta har zuwa time da benazir zataji sauƙi"
"Toh Aneelerh, har naji sanyi wlh, yanzu zakuje asibitin ne"?
"Mu zamu tafi, ita kuma yarinyar sai zuwa anjima da dare za'a kaita"
"Allah yakaimu lafiya" ameen mami, daga haka sukai sallama da juna, komawa tayi wurin su unaisah suka cigaba da yin firar yaushe rabo, chief tuni ya shige gidan saboda yana son ya fita office, zama taj yai a wurinsu suka dinga sanya juna nishadi, ana tuna rayuwar baya, har wuraren ƙarfe 9 na safe kafin su Aneelerh suka mike zasu tafi, Angel kamar tay masu kuka taso su shiga ciki suka ce a'a sai zuwa na gaba suna sauri ne, dakyar taj ya lallashe ta yace ta koma gida, zaije ya rakasu, tana ji tana gani ya tafi da su aneelerh, a motarshi yakaisu cikin estate din inda suka bar motarsu, sai da ya tabbatar sun tafi kafin ya dawo.
________________________________✍️
Fitowa dr shureim yayi daga bedroom dinsa, Ya kimtsa tsaf cikin shigar su ta larabawa, hannun sa ruke da wayarshi, har ya fara tafiya kiran Aneelerh ya katse mashi hanzarin shi, da sauri yai picking tare da kara wayar a kunnansa
"Assalamu alaikum Aneelerh, barka da safiya, fatan kun wayi gari lafiya"
On the other hand Aneelerh tace"lafiyalou Alhamdulillah, Ya shureim.."
"Tun ɗazu nake ta kiran layin ki don inji Ya ake ciki game da yarinyar an dace ko kuwa"?
"Yaya shureim, mu hadu asibitin zanyi maka bayanin komai" amsa mata yayi da toh, kafin sukai sallama, a tsanake Ya nufi falo, tunkafin Ya isa ya hango mutanan gidan a dining sun hallara sunayin breakfast,
"Shureim har ka kammala shiryawa"? alhaji ubaid ne yai masa maganar
"Eh daddy..." ya faɗa tare da gaishe da su, Alhaji musa yace"ba zakayi breakfast din bane"?
"Idan naje can zanyi..."
"Okey,
Hajiya sarah tace"in sha Allah idan na taso daga office zanbiyo asibitin.."
"Allah ya kawo ku lafiya..." satar kallon zeenatu yayi, hannunta ruke da cup tana shan tea, murmushi ta sakar mashi tare da kashe mashi ido ɗaya...lamarinta ya fara bashi tsoro yarinya kamar mai iskokai?
"Zeenatu ba zaki bini mu tafi ba"?
"Ina zamuje"?
"Asibiti wurin auntynki benazir.." maƙe mashi kafada tayi"bana jin dadi, bazan iya zuwa ba, ka tafi kawai..." da mamaki hajiya sarah take kallon ta
"Zeenatu! Kin kuwa saurari abun da yace maki dakyau? Asibitinne ke bazaki je ba? Dallah tashi ki bi shi ku tafi, idan kika zauna gidan me zaki yi ke kadai? Daddynki ma fita zaiyi..." bata kare maganar ba, Alhaji musa ya katse ta da cewa"ba ki ji tace bata da lafiya ba?
Rai a6ace hajiya sarah tace"amma ay lafiyarta qalou, ni banga wani alamun rashin lafiya atare da ita ba..."
Alhaji ubaid yace"shureim ka tafi kawai, Kada ku takura mata, tun da ba koshin lafiya gare ta ba, ni bana so ma taje asibitin taita kuka kamar jiya da mukai ta fama da ita...." jiki asanyaye dr shureim Ya miƙe idanunsa akan fuskar zeenatu, itama kallon nashi take Yi, ji take kamar ta tashi tabi shi sai dai ta kasa kamar ana ruke kafafunta, a hankali Ya juya yana tafiya kamar babu kuzari a jikin shi, bakomai yake tariyowa ba face kalamanta! Meyasa zeenatu ta canza daga jiya zuwa yau? Ya jefawa kansa tambayar da baida amsarta!!
*Ga me bukatar karanta littafin kurkukun kaddara, 500 ne dukanshi za'a tura Via Opay, 8103884440 Hafsat Bature Muhammad, shaidar biya za'a tura ta whatsapp, 08103884440*