DAGA ALƘALAMIN BOSS BATURE🔥✍️
"Good" ya furta tare da gyara zaman shi, babu wanda ya ƙara furta kalma a cikin su, shiru motar baka jin sautin komai sai sanyin A c dake ratsa fatar su, aranta Allah Allah take su karasa gida don ta nuna ma yan uwanta tsarabar da tayi masu tasan zasu ji dadi.
Gaba ɗaya ƴan aikin gidan suna atsaitsaye gaban door room din marwa, fuskokinsu babu walwala idanunsu sun kumbura saboda rashin isasshen bacci da basu samu ba adaren jiya, sai zullumi da fargaban abunda zai biyo baya sukeyi tun wuraren karfe shida sheikh imam ya karaso gidan, tunkafin karasowarshi bayan kammala sallar asubahi baba obie ya tura su hajjaty tare da security suka dauko marwa daga asibiti yanzu haka tana acikin dakinta tare da sheikh imam malik sautin ruƙiyar da yakeyi mata ya cika kunnuwansu bayin Allah sunyi zuru zuru, hankalinsu atashe tun safe ake abu ɗaya har yanzu ba wani labari mai dadi, a kalla sun shefe awanni abakin kofar dakin suna jiran sheikh imam malik.
"Idan har ya tabbata aljanune suka ɗaura mata ciwon, ni dai inaga zan tattara kayana in koma kauyenmu da zamane, zaifi min kwanciyar hankali don bana jin zan iya cigaba da zama agidan nan...." cikin rawar murya safa tayi maganar.
Abla tace"ni kaina na tsorata wallahi, jiya a zaune na kwana saboda fargaba da zullumin abunda ya faru da marwa, wlh ta bani tausayi baiwar Allah rana daya mutun ya tashi ba baki ga kuturta!"
Sofia tace"nifa saboda tsoro jiya bayan mun dawo gida, dana shiga daki karatun kur'ani na kunna awayata sai da asuba na kashe"
kowa yana tofa albarkacin bakinshi banda hajjaty dake tsaye ta goya hannayenta kan kirjinta, ita dai hankalinta bai kwanta da ciwon marwa ba!
Jin motsin buɗe kofane yasa sukayi shiru suna jiran tsammani, A hankali sheikh Imam Ya fito daga dakin, farar jallabiya ce a jikinsa, ya ɗaure kanshi da rawani, hannun ɗaya ruƙe da cazbaha.
cikin girmamawa suka fara yi mashi sannun da fitowa da fara'a ya amsa masu
tambayoyi suka fara jere mashi kamar yan jarida
"Malam ya ake ciki? Ya jikin marwan? Ta samu lafiya? Dagaske aljanune suka shafe ta? Sheikh zamu iya shiga ciki mu duba ta?
Ɗaya bayan ɗaya sheikh Imam Yake kallonsu, Ya rasa wa zai fara amsa ma tambayar shi sun ƙi bari Yayi magana, ya fahimci sun matsu da su san awani hali take ciki.
har ya buɗe baki zai yi magana Saiga baba obie tare da pravin sun nufo wurinsu.
Miƙa mashi hannu baba Obie yayi suka yi musabaha"sannu da kokari sheikh, Ya mai jikin? An dace kuwa"? Fuskarshi da fara'a yace"mu shiga daga ciki ku gani da idonku.." da sauri suka nufi dakin su hajjaty suna abiye da bayansu, agaban katifar marwa suka tsaya cirko cirko, tana a kudundune cikin bargo jikinta sai makekketa yakeyi, tuni pravin Ya haɗe fuska tamkar bai ta6a dariya ba, ga wani gumi mai ɗumi daya wanke goshin shi, Hanky ya zaro ya fara goge zufar.
An rasa wa zai fara cire bargon murmushi sheikh imam yayi don ya fahimci tsoro suke ji, da zolaya yace ma baba obie"baba kai yakamata ka fara cire bargon mu gani" waro ido baba obie yayi haɗi da girgiza kai yace"ya zakai min haka? dan Allah kadaina wannan maganar, kai dai daka fara aikin kai yakamata ka karasa ladarka.."
yar dariya Sheikh Imam yayi tare dakai hannu ya ruƙo bargon ya fara jan shi ahankali, pravin kamar ya daura hannu akai ya fasa ihu haka yakeji duk ya rasa sukuninshi kamar wani munafiki sai cizon yatsa yakeyi..
Su hajjaty sun baza na mazurai suna jiran ganin marwa, gabansu sai faduwa yakeyi .
Lokaci da sheikh Imam ya ƙarasa cire bargon, gaba ɗaya suka zabura suna kallonta idanunsu azazzare cike da mamakin ganin bakinta Ya buɗe sunyi matukar razana da lamarin, ta ko'ina zufa ce ke tsastsafowa ajikinta kamar wadda aka tsamo daga cikin tafki, kafafunta sun miƙe daga lauyewayar da sukayi, amma yatsun hannayenta basu dawo daidai ba har yanzu da kuturtar sai dai yatsun sun ɗan saki ba kamar farko da suka matse ba har suna fidda ruwa mai yauƙi yanzu babu ruwan.
Kusan Atare su hajjaty suka ambaci sunanta da karfi Marwa.
buɗe baki tayi zatayi magana sai dai ta kasa sautin muryar baya fita dakyau gura gura take magana kamar wadda harshenta ya ƙone kwata kwata ba'a iya gane me take cewa, har sun fara murna taji sauki ashe da sauranta, pravin har zai fita daga dakin jin takasa magana yasa shi dawowa ya tsaya yana kallon marwa afakaice yake sakin murmushin mugunta.
Jikin su hajjaty yayi sanyi lakwas, har sun fara sharar kwalla
Baba obie yace"Ikon Allah! sheikh dagaske dai jinnune suka shafe ta? Ya fada cike da son jin karin bayani, a tsanake sheikh imam ya ce
"Eh, bakaken aljanune a jikin ta, sune suka haddasa mata ciwon..." waro idanu waje su hajjaty sukayi wani irin tsorone Ya kamasu murya na rawa abla tace"dama Aljanu suna iya canza ma mutun halittar shi" jinjina mata kai sheikh imam yayi"fiye da haka ma zasu iyayi.." kallon kallo suka jefawa junansu.
Aruɗe baba obie ya furta"Inna lillahi wa'inna ilaihirraji'un!
Zuƙunnawa sheikh imam yayi daga gaban katifar marwa idanun shi akan fuskarta Ya soma magana"kada ki sanya damuwa aranki, Allah yana atare dakai, duk wani abu da kika ga ya faru dake mukaddarine daga Allah, bana so ki kuntata kanki, ko ki ƙyamaci kanki, balle kiyi tunanin illata kanki saboda wannan lalurar data same ki, kiyi kokarin cinye jarabawarki kada ki gaza, Aljanun da suka haddasa maki ciwon nan suma bayin Allah ne, babu abunda ya fi karfin mahaliccin mu...." tun da ya fara magana idanun marwa suka cicciko tab da kwalla ita kadai tasan me take kitsawa aranta.
"nayi alƙawarin zan taimaka maki amma fa dole sai kema kin taimaki kanki, kiyi kokarin bin abun da Allah da Manzonsa sukace ayi domin samun kariya daga sharrin su, da zuciya ɗaya in sha Allah zaki ji sauƙi, jikinki zai dawo kamar yadda kike ada" jinjina mashi kai tayi alamar ta gamsu da maganar shi.
"Ma.. malam muma ataimaka mana dan Allah, ka faɗa mana hanyoyin da zamu kare kan mu daga sharrin su"
cikin shesshekar kuka abla tayi maganar.
murmushi sheikh imam yayi tare da kallonsu ɗaya bayan daya sai yaji sun bashi tausayi ganin yadda jikinsu ke ta kerma kamar mazari
"Ku samu wuri ku zauna zanyi maku bayani" da sauri suka kewaye sheikh imam suka zauna kan ƙasa suna jiran jin me zaice.
Miƙewa yayi da sauri ya ɗauko kujerar mirror Ya ajiye agaban baba obie don ya zauna.
"Nagode sheikh" ya fada tare da zama kan kujeran.
Tun shugowar pravin dakin sheikh imam bai ɗaga ido Ya kalle shi ba, sarai ya san da zaman shi, dama tunfil azal basa jituwa tsakanin su ko gaisuwa bata ta6a haɗasu ba,
Shiru yayi kamar akwai abunda Ya hana shi fara magana, wayar pravin ce ta fara ringing daga cikin aljihunsa da sauri ya fuce daga dakin don ya amsa kira.
Fitar shi keda wuya sheikh Imam Ya fara magana yana duban marwa cikin tattausa harshe yace mata"kiji tsoron Allah! Rass gabanta Ya fadi, su hajjaty suka kalle shi da alamun rudani akan fuskokin su.
"Idan akwai wani abu da kike aikatawa badai dai ba to ki daina! Sau dayawa mu muke ja ma kanmu shiga cikin masifa, Allah ya gatanta mu ya bamu hanyoyi da dama da zamu iya ba kanmu kariya amma muna wasa damar mu...." ga dukkan alamu Sheikh imam Ya canza maganar daya dauko da farko hannunka mai sanda yayi mata kuma ta fahimce shi hakan yasa ta duƙar da kanta ƙasa hawaye suna cigaba da wanke fuskarta.
"Kina yin azkar? Girgiza mashi kai tayi alamar a'a
"Baki iya ba ne"? Ɗaga mashi kai tay alamar eh.
"Ya salam! Wannan wani irin ganganci ne? Da ranki da lafiyarki? Wallahi da ace kina kokarin kiyayewa babu wani mahalukin daya isa ya cutar dake in ba Allah ne ya kaddara za'ayi galaba a kanki ba, azkar garkuwa ne agare mu, ita kuma addu'a da kike gani takobin mumuni ce kuma ita addu'a tana iya canza kaddarar mutun, daga mummuna zuwa mai kyau.
Nasiha ya fara yi mata jikinta yayi sanyi lakwas, su abla tuni ido ya raina fata don su kansu bakowane keyi ba har kwara hajjaty itada ta musulta daga baya tana kokarin yi akai akai
"Gaba ɗaya inaso ku bani aron hankulanku, ku saurari abunda zan fada maku..." amsa mashi sukayi da toh,
Shiru yayi jim kafin ya fara magana"abunda ya kamata ku sani shine, Zikirin safe da yamma yana da matuƙar mahimmanci sosai, wanda inda Musulmi yasan mahimmancin sa da kuma kariya da yake bashi da bai barshi ba koda na kwana ɗaya ne, don haka ina ƙara jan hankulan ku da Ku yawaita Lazimtar Zikirin safe dana yamma.." atare suka hada baki wurin furta in sha Allah malam zamu kiyaye
Shiekh imam ya ɗaura da cewa"abu na gaba Yin alwala, mutum ya kasance yana yawaita zama cikin tsarƙi domin hakan na bada kariya, bayan haka akwai Qiyamul laili, da kuma Neman tsari yayin shiga bayan gida (toilet) idan zaku yi bacci ku yi alwala, sannan ku karanta ayatul kursiyu bayan ita sai falaki da nasi suna da Muhimmanci sosai..." jinjina kai kowan nan su yayi sheikh imam ya numfasa yana dubansu kafin ya dasa da cewa
"Sannan Faɗin La’ilaha illallahu wahdahu la sharika lahu, lahul mulku wa lahul hamdu wahuwa Ala kulli shai’in kadir sau ɗari safe da yamma
Faɗin Bismillahillazi la ya durru Ma’asmihi shai’un fil ardi wala fissama wahuwa ssami’ul alim” sau uku safe da yamma, Faɗin “A’uzi bikalimatillahit-tammat min sharri ma khalaka” sau uku safe da yamma"
baba obie ya nutsu yana sauraron sheikh imam har cikin ranshi yaji dadin yadda ya zaunar da yan aikin gidan yana koyar dasu yadda zasu kare kansu hakan ba karamin faranta ranshi ranshi yayi ba, shi kanshi ya karu da sheikh imam.
"Malam, wallahi ni yawan mantuwa gare ni, kona yi kokarin yi sai wani abun yaja hankalina..." Sofia ce tay maganar, shiekh imam Yace"akwai islamic apps na waya, da zaki iya sauke wa.." da sauri hajjaty tace"ina da shi zan tura mata nima dashi nake amfani, shi yake tunasar dani lokacin yin ibadata da kuma lokacin yin azkhar" murmushi sheikh imam yayi idon shi akanta yace"kinyi masu wayau, zaman tare baice haka ba, meyasa tuntuni baki sanar da su ba"?
Sunnar da kanta ƙasa tayi
Calmy ta furta"ay ni bansan ba su amfani da shi ba"
Gyaɗa kai yai"haka ya dace, In ka san abu na karuwa ne, to ka yi kokarin sanar da wasu suma su amfana, na tabbata da ace shirin labarina ne aka saki jiki na rawa zaki fada masu koba haka ba"? Gaba daya suka sanya dariya.
Murmushi baba obie yayi, shima sheikh imam din murmushine akan fuskarshi.
Baiwar Allah marwa duk da halin da take aciki saida tayi murmushi fuskarta sharkaf da hawaye...
Nasiha ya cigaba dayi masu akan su daina shagala duk runtsi duk wuya kada su yi sakaci da ibadarsu da kuma neman tsari daga gurin Allah, cike da gamsuwa suke sauraran shi daga bisani yace Idan har ku ka kiyaye zikirorin dana faɗa maku, sannan ku ka kuma ƙaurace wa saɓon Allah toh haƙiƙa Allah zai kare ku daga kowani irin sharri, kuma zaku yi rayuwa cikin kwanciyar hankali domin da Ambaton Allah ne da yimasa biyayya ake samun natsuwa. Allah yasa mudace" atare suka amsa mashi da ameen haɗi dayi mashi godiya
Baba obie yace"sheikh muna godiya sosai, jazakallahu khairan..." da fara'a ya amsa mashi da ameen...
Kafin ya kalli Su abla"ina bukatar mutun ɗaya da zai dinga kula da marwa"
shiru su ka yi kowa tsoron kusantarta ya ke yi, yanzu ma da suke adakin don sunga sheikah imam ne ga baba obie shiyasa suka saki jiki.
"Kada ku bani kunya mana! Kun riga da kunsan lalurar nan ba ita ta daura ma kanta ba! idan har kuka ce zaku juya mata baya ko ku ƙyamace ta zaku sa ta tsani kanta ne harta aikata ma kanta abunda bama fata, ayanzu bata da wasu yan uwa na kusa da ya wuce ku, ku take gani amatsayin yan uwanta wadanda zasu share mata hawaye...."
cikin sanyin murya hajjaty tace"wallahi bani ƙyamar marwa, kawai abune da bamu saba gani ba, muna jin tsoro amma in sha Allah zamuyi kokarin bata kulawa, ni nayi alkawarin zan dinga zuwa dubata...."
Shiekh imam yace"Alhamdulillah, naji dadin jin hakan daga gare ki, zuwa anjima in sha Allah zan aiko maki da magunguna na musulunci, sannan kafin in tafi zan kar6i contact dinki saboda in tura maki addu'o'in da zaki dinga tofa mata aruwan wankanta dana shanta,.."
"Toh malam, muna godiya Allah ya saka da alkhairi..."
miƙewa yayi bayan yayi masu sallama baba obie ya ruko hannun shi suka fita daga dakin....
Kamar jira suke sheikh Ya fita daga dakin da sauri su abla suka gudu zuwa kitchen Ya rage saura Hajjaty adakin.
Bata san sa'adda ta fashe da kuka ba, gashi ba halin Yin magana, da hannu ta dinga bugun katifa tana kuka, da sauri hajjaty ta rukota tana lallashin ta idanunta cike tab da kwallo, wani irin tausayintane Ya kamata.
"Marwa ki daina kuka, In sha Allah zaki ji sauki ki dawo kamar yadda kike ada, nayi alkawarin zan taimaka maki muyi duk abunda sheikh imam yace"
tunda hajjaty ta fara magana marwa tayi shiru tana kallonta wallahi tayi danasani yafi sau a ƙirga, kuma tayi mamakin yadda hajjaty ta amince zata kula da ita sa6anin sauran yan uwansu da suka gudu daga dakin.
Bata ta6a tsammanin hajjaty tana da saukin kai, da tausayi ga mutunci irin na yau ba, sai taji ta tsani kanta, hakanan batai mata laifin komai ba mace mai kyakkyawar zuciya amma saboda abun duniya ta amince zata yi mata leƙen asiri don abata matsayinta akuma koreta daga gidan wa'iyazubullah, bakomai ta tuna ba face hajiya saratu, ita da tayi silar jefata halin da take aciki, amma kwata kwata bata nuna damuwarta akanta ba, ko kalmar sannu ay ya kamata ta furta mata, ayanzu ta gane wasu mutanan sai kana da amfani agurinsu suke kula ka da zarar sunga bazasu amfana dakai ba sai su watsar dakai, tayi danasani taso ace tana da baki da yau saita fallasa asirin wanda yayi silar jefata halin da take a ciki ko da zata rasa ranta ne❗
Amma duk da haka bata makaro ba, ta ɗauki alwashin saita tona asirin wanda ya cutar da ita!
"Marwa"! Muryar hajjaty ce ta dawo da ita daga duniyar tunanin data lula
"Kiyi hakuri Kinji yar uwata, bana son ganin hawayenki, nasan kina jin yunwa bari na kawo maki abinci in kika kammala ci sai in taimaka maki kiyi wanka..." kifa kai marwa tayi jikin pillow ta rushe da kuka mai tsuma zuciya, tamkar ranta zai fita, zuciyarta ta karaya, a halin yanzu ba rayuwarta ta ke jima tausayi ba, rayuwar hajjaty itace abun tausayi....dakyar hajjaty ta shawo kanta har ta samu marwa ta daina kuka, da sauri ta mike taje kitchen donta haɗo mata abunda zata ci.
___________________________________✍️
*Hajiya Saratu*
A zaune take kan mirror chair jikinta sanye da sleeping gown ta manyan mata, fuskarta sam babu walwala ta zabga tagumi da hannunta ɗaya bata jima da farkawa daga bacci ba, ko wanka ta gaza shiga tayi, saboda rashin kwanciyar hankali, duk bayan yan mintuna saita duba wrist watch din hannunta, lumshe idanunta tayi yayin da acan ƙasan zuciyarta take tariyo maganganun da suka tattauna ita da Hajiya laurat a jiya, bayan ta taso daga office tsoro da fargaba suka hana ta dawo gidan, tace ma driver dinta ya wuce da ita aso villa acan suka haɗu da hajiya laura tun daga kan yanayin fuskar Hajiya saratu ta fahimci babu lafiya akwai wani abu da yake damunta, bayan sun zauna a pool yard masu yi masu hidima suka kawo masu coffee da kayan marmari tace mata bismilla su fara sha, girgiza kai tayi alamar bazata sha ba, hajiya laura tace wai meke damunki ne? kiyi magana mana, a shirye nake da in taimaka maki don mu shawo kan matsalar, ajiyar zuciya hajiya saratu ta sauke tana faman yamutsa fuska ta kwashe komai daya faru dangane da ciwon marwa ta sanar da hajiya laura.
"Wallahi ina cikin tashin hankali, zama gidan ma ya gagareni, yanzu haka da kika ganni daga office ko gida ban wuce ba nayo nan don in fada maki halin da nake ciki"
Shiru hajiya laura tayi jim da alamun ruɗani akan fuskarta tace"ni abunda bangane ba, kina nufin dare ɗaya ta farka da lalurar"?
ɗaga mata kai hajiya saratu tayi, al'amarin ya ɗaure mata kai
"Kuma an kaita asibiti?
"Bani da masaniya, amma bari na kira baba naji halin da ake ciki" tay maganar tare da curo waya ta danna ma baba obie bayan ya ɗaga, ta tambaye shi awani hali marwa take a ciki, ya sanar da ita abun da likitoci suka ce, tayi mashi sallama ta ɗago ta kalli hajiya laura da tayi zugudum tana kallonta, ta sanar da ita abun da baba obie ya faɗa mata, ga mamakinta sai taga hajiya laura ta saki murmushin gefen fuska takai hannu ta dauki cup of coffee ta kurba still da murmushi akan fuskarta, hakan ba karamin ɗaure ma hajiya Saratu kai yayi ba fuskarta a ɗaure tace"bana son iya shege meye abin murmushi aciki?
Yar dariya laura tayi"kwantar da hankalinki mutuniyata, kinsan wani abu"? Girgiza kai tay alamar a'a
"Wallahi ko nayi rantsuwa bazanyi kaffara ba yarinyar nan marwa silar ciwonta yana da alaƙa da aikin leƙen asirin da kika sanya ta!! Hankali atashe Hajiya saratu ta zaro ido tana kallon laura aruɗe ta furta"ban..ban gane me kike nufi ba?
"Ke yanzu har sai nayi maki bayani? Yakamata ki gane mana, kiyi amfani da brain dinki, ciwon yarinyar nan aikin asiri ne, wlh ture akayi mata, in ba haka ba taya za'a ce rana ɗaya mutun ya tashi da cutar kuturta sannan ba baki, ai ke daga ji kinsan ɗaura mata ciwon akayi, Ni abun da na fahimta watakil hajjaty ta kama marwa tanayi mata leƙen asiri, shiyasa ta kulle mata baki don kada ta iya furta magana, bayan haka ta ja mata cutar kuturta don kada ta samu damar da zata yi rubutu da hannayen ta balle harta tona mata asiri...."
Dafe kai hajiya saratu tayi yayin da zuciyarta ke bugawa da karfi da karfi gaba ɗaya tabi ta ruɗe.
Hajiya laura taci gaba da cewa"hmmm wallahi ɗan adam ba abun yarda bane! Dama na jima ina zargin hajjaty, indiyawan nan basu tsoro Allah, ko a fina finan su zakiga suna yawan zuwa wurin bokaye don ayi masu asiri, matar nan munafuka ce wlh, tana amfani da rauhanai shiyasa ta mallake mutanan gidanku har ta samu gindin zama take iya shegen data ga dama, yanzu gashi ta kassara rayuwar marwa....."
Runtse idanu Hajiya saratu tayi, hankalinta Ya tashi har wani dishi dishi take gani a idanunta muryarta na rawa ta furta"inna lillahi wa'inna ilaihirraji'un! Na shiga uku"!
hajiya laura tace"ay mun sha ja maki kunne akan ki kori hajjaty daga gidan kika ƙiya, ay ni banma san ya akai kika yi gangancin da pravin ya ɗauko maki bakauya yar kauyan india masu bautar shanu ya ajiye maku agida, to wallahi kwara tun wuni ku dauki mataki akanta in ba haka ba hmmmm nan gaba Allah kadai yasan me zata aiwatar.." maganganun hajiya laurat sun tsaya mata arai sun kuma ɗaga mata hankali, bata ta6a jin faɗuwar gaba da tashin hankali irin na jiya ba, ta jima a vila suna tattaunawa da hajiya laurat har shawarwari ta bata dangane da yadda zata kare kanta daga sharrin hajjaty da kuma hanyar da zata bi don ta gano ainihin wacece ita.
Bayan sunyi sallama da juna, hatta shiga motarta tana zullumi da fargaban hajjaty, ta tsorata da ita ba kadan ba, ko bayan data dawo gida kasa shiga bedroom dinta tayi saboda tsoro, dakin baba obie ta fara shiga ta zauna wurin shi har saida aka fara kiran magrib ya tashi zai tafi masallaci kafin ta dawo dakinta sam ta kasa sukuni wani irin tsorone Ya kamata babban tashin hankalinta kada hajjaty tayi silar kassara rayuwarta kamar yadda ta kassara rayuwar marwa ya ilahi abin ya ɗaga hankalin ta, ba ita ta runtsa ba adaren jiya har saida pravin ya dawo ya fara mata faɗa akan rashin dawowarta da wuri, baiwar Allah saboda tsoro ta kasa mayar mashi da martani saima ta rungumeshi ta ƙanƙame shi hakan ba karamin daure mashi kai yayi ba, yaja hannunta suka zauna gefen gadon ya tambayeta meke damunta cikin sanyin murya tace mashi bata jin dadin zuciyarta tsoro take ji saboda abun da ya faru da marwa shiyasa taki dawowa gidan..
murmushi pravin yasaki har cikin ranshi yaji dadin tsoratar da tayi saboda shi agurinshi damace ya samu da zai dinga juyata son ranshi, tun da ya gano lagwon ta, a daren ranar sai da ya biya bukatar shi da ita, son ranshi ta sakar mashi jiki yayi abunda yakeso dama ya kwana biyu bata bashi hakkin shi ba.
Bayan ta dawo daga duniyar tunanin ta miƙe tana zagaye ɗakin tana tufka da warwara akan yadda zata bullowa lamarin dole ta ɗauki mataki! Ta tsani hajjaty fiye da yadda ta tsani mutuwarta❗
__________________________________✍️
Lokacin da Benazir ta farka daga bacci, da wata irin kasala ta buɗe idanunta wadanda suka kaɗa jawur muryarta na rawa ta fara ambaton sunan Angel mikewa zaune tayi kan gadon, hannunta ɗaya dafe dakanta, ga wata faduwar gaba da take ji
"Babyna! Where are you? Mami Ina Angel dina? Bata nan ne? dakyar ta iya saukowa daga kan gadon tayi miƙa haɗi da yin hamma kafin ta fara baza ido tana neman Unaisah, ita kadai ce adakin, hajiya layla taje office din dr jazz domin amsa kiran da yayi mata.
"Angel! Angel! Can't you hear me calling you? Where are you?" Da karfi tayi maganar tare da nufar kofar toilet ta kwankwasa"pls idan kina ciki, Ki amsa min babyna kinji..." ta fada tare da kanga kunnanta jikin kofar, shiru taji ba a amsa mata ba, da alama babu mutun aciki, hakan yasa tay pushing door din ta shiga ciki tana bin ko'ina da kallo kwata kwata bata ga kowa ba, ji tayi kamar ta daura hannu akai ta fasa ihu, gaba ɗaya tabi ta rude dama saida ranta ya bata cewar ba lallai ta ganta ba
Fitowa tayi daga toilet din, ta nufi bed dinta, ta zukunna tana leƙen karkashin gadon don taga ko anan ta buya
Adai dai lokaci hajiya layla ta shigo dakin hannun ta ruke da takardar sallama kaitsaye idonta suka sauka akan benazir.
rass taji gabanta Ya faɗi ganin yadda tabi ta ruɗe tana ambaton sunan babynta, tuni taji hawaye sun ciko idonta sam takasa karasa shiga ciki saboda fargaban amsar da zata ba benazir idan ta tambayeta Ina babynta, batasan ya zatayi da ita ba, ga tsananin tausayinta da take ji.
"Mommy"! Muryar dr shurieim ce ta katse mata zancen zucin ta, aɗan firgice ta juya baya tana kallonsu, a jere suka nufo ta su uku ne, Shureim da Alhaji ubaid tare da hajiya sarah fuskokinsu dauke da murmushi, dakyar ta haɗiye damuwarta ta nufe su tana fara'a suka rungume juna ita da hajiya sarah bayan sun raba jikinsu, shureim Ya matsa kusa da mommynsu Ya rungumeta tare da manna mata kiss gefen fuskarta.
"Sannun ku da zuwa"
hajiya sarah tace"ay min afwa wlh banji dadi ba, jiya banzo na duba jikin benazir ba, ban kuma kira naji ya kuke ba" murmushi hajiya layla tay"kai haba ba komai wlh, ay kinama kokarin zuwa dubata, wlh kada kiji komai benazir tana cikin koshin lafiya.." tai maganar tare da kallon Alhaji ubaid dake kallonta, harara ta ɗan watsa mashi afakaice saboda taji haushin rashin kiransu da baiyi ba jiya, cikin sanyin murya yace"kiyi hakuri jiya bana jin dadin jikina ne shiyasa ban kira ba, naso ma inzo dubaku" ta6e baki tayi"ay kwara da kukazo gaba ɗayanku, ga Benazir can tana neman yarta, kuma yarinya masu ita sun dauki abunsu, dama likita ne ya bada maganin bacci aka bata tasha kafin aka rabata da yarinyar yanzu gata can ta hargitsa dakin tana neman yarta"
Hankalinsu ba karamin tashi yayi ba, Dr shureim yace"baiwar Allah, na tausaya mata, wlh dama saida naji fargaban zuwan ranar nan, gashi sun shaku da yarinyar"
Alhaji ubaid yace"yanzu ya zamuyi jama'a? ay ni nayi zaton ma zamu taras da su ashe har sun tafi, gaskiya banji dadi ba, ban ta6a haduwa da yarinyar ba balle inmata godiya ita da iyayenta da sukai mana halacci.."
Hajiya layla tace"wannan duk mai saukine tunda aneelah tasan gidan iyayenta, wata rana saimuje muyi masu godiya, yanzu dai muji da maganar benazir! Menene mafita"!
Hajiya sarah tace"ni nama rasa ta cewa wlh, amma ni aganina, abun da yakamata shine mu lalla6ata mu fada mata cewa daddyn yarinyar yazo ya dauke ta sun tafi mall, da anjima zai dawo da ita, saboda mu samu mu bar hospital ɗin da ita, in ba haka ba dakyar zata amince ta bi mu" gaba daya sunyi amanna da maganar hajiya sarah, atare suka nufi dakin, suna shiga suka isketa zaune gefen gado duk ta yamutse gashin kanta kamar na mahaukaci, ga fuskarta sharkaf da ruwan hawaye.
Atare suka hada baki gurin yi mata sallama, da sauri ta miƙe tana kallonsu, muryarta na rawa ta furta"mami! Ya shureim! Daddy! aunty Sarah! Ina babyna? Tana ina? Na duba ko'ina banganta ba! Dan Allah ku fadamin waya daukar min babyna? Wlh in har ba'a dawo min da itaba, zuciyata zata buga in mutu kowa ya huta"!
kusan atare suka haɗiyi yawu kowa yasha jinin jikinshi, dakyar hajiya Sarah tayi karfin halin furta"haba Benazir? Meyasa zaki daga hankalinki akan yarki? Waya isa Ya rabaki da ita? Ki kwantar da hankalinki, Yarinyar nan takice halak malak.."bubbuga kafafunta tayi saika rantse da Allah batasan me take ba, bayan da hankalinta tsabar pretending ne
"Ni kawai ku fadamin tana Ina? Meyasa banganta ba"?
"Benazir, daddynta ne ya dauke ta, sunje mall zasuyi maki siyayya da anjima zai dawo da ita gida..." cike da fargaba hajiya layla tayi maganar, shiru tayi jimm na ɗan wani lokaci kafin ta sauke nannauyar ajiyar zuciya fuskarta ayamutse tace"mami dagaske Taj yazo nan? Shi ya dauki Angel dina"? Murmushi suka sakar mata, dr shureim yace"kwarai kuwa dagaske shiyazo ya dauketa.."
"Amma bai tambayeni ba? Ko ya daina sona? Ta fada tana zare masu eyes dinta
Alhaji ubaid yace"ya tambayeki mana, ay saboda ke sukaje yin siyayyar, yana son ya faranta miki rai.." wani irin tsallan murna ta daka tana dariya.
kallon kallo su hajiya layla suka jefawa junansu hankalinsu atashe, wato akwai gwarama idan suka koma gida taji shiru taj baizo mata da yarta ba.
"Mommy zamu jiraku a mota" dr shureim ya fada tare da kallon daddynsu atare suka fuce,
Badajimawa ba, saiga su sun fito tare da benazir har ta canza kayan jikinta ta maida kayan da aka kawota asibitin da su, a backseat na motar dr shureim ta zauna, yana agaba tare da alhaji ubaid, Hajiya layla kuma a motar hajiya sarah ta zauna, a jere motocin suka fuce daga asibitin.