Kurkukun Ƙaddara Takun Ƙarshe chapter 42 Complete by Boss Bature

Kurkukun Ƙaddara Takun Ƙarshe chapter 42 Complete by Boss Bature

Takun Ƙarshe

Boss Bature

A kishingiɗe yake saman lallausan rug din dakin baba obie ya ɗaura head dinsa kan pillow, jikinshi na sanye da jallabiya fara kyal, fragrance dinsa ya haɗe da sanyin A.c din dakin, ba su jima da dawowa daga sallar asuba ba yabiyo baba obie dakin shi...A hankali yake danna phone dinsa Kira ne ya shigo ganin sunan commender james yasa shi picking call din tare da kara wayar a kunne, cikin girmamawa suka gaishe da junansu kafin daga bisani commender james ya sanar da shi sun samu izni daga manyan su, za su shigo Nigeria da shi da sauran sojojin da suka tsinci su Angel a dajin evil forest

Chief yace"I'm very happy to hear that, I can't wait to see you"

Commender james yace"I'm also very happy, this is the first time I'll be coming to Nigeria because of the children we found in the forest, naji dadi saboda abun alfahari ni agare ni" 


sun ɗan jima suna tattaunawa kafin daga bisani su ka yi sallama da juna.


Fitowa baba obie yayi daga toilet, jikinshi sanye da jallabiya fara, ya dago da ido ya dubi owais fuskarshi da fara'a yace"jikallena, nabarka  zaune kana jira na, uziri ne ya ruƙe ni a ciki" dagowa chief yai tare da kallon shi suka haɗa ido da juna"barka da fitowa,"


"Yawwa owaisu na, fadamin me kakeson ci insa akawo mana, yau atare zamu yi breakfast.."


ya faɗa yayin da yake nufar bedside drawer chief yace"duk abunda kakeson ci nima shi zan ci "


Landline din kitchen baba obie ya kira, bayan an daga kiran ya isar da sakon abunda za'a kawo masu na breakfast bayan ya ajiye wayar


Ya samu guri kan lallausar rug din ya zauna haɗi da daura kan shi saman laps din chief yadda kasan uba da ɗansa.


ya ɗago ya kalli fuskar Owais dake kokarin saita shi da phone camera"me zaka min haka"?


"Hoto zan ɗauke ka, naga ka yi min kyau" 


murmushi baba obie ya sakar mashi"duk kyau na nakai ka"? 


"Eh mana, mu da mukai gado agurin ka, gaba ɗaya kamanninka muka ɗauko" 


Saurari Littafin >>>>Kurkukun Ƙaddara Takun farko  Kada a manta ayi mana subscribe like da kuma comment sannan a yi share. Domin samun sabbin littafi idan Mun ɗora.

"Na tsufa owais, yanzu babu wannan kyan da kake faɗin ina da shi" 

"Kai kake ganin haka, ni tun da na taso rayuwata ban ta6a ganin mutumin daya tsufa da kyan shi irinka ba" ƙayataccen murmushi baba obie ya saki yana kallon fuskar chief, yaji dadin kalaman shi sun faranta ran shi.


"Baba, ɗazu kace zamuyi magana, ya fada bayan ya kammala daukar shi hoton.


shigowar hajjaty dakin ne ya katse firar su, ta ɗauki wankan material, hannunta ruƙe da tray na kayan breakfast dinsu agabansu ta ajiye tray din cikin girmamawa ta gaishe da su suka amsa mata har ta juya zata fuce daga dakin muryar baba obie ta dakatar da ita.

"Ya jikin marwa"?

"Da sauƙi baba,"

"Okey, ubangiji Allah ya bata lafiya" ta amsa mashi da ameen bayan ta fuce daga dakin chief ya dubi baba obie"wacece marwa"? 


Ba halinsa bane tambayar abunda bai shafe shi ba, just saboda yaji ya ambaci ya jikin ta.



"Ɗaya daga cikin masu aikin gidan nan ce, bata da lafiya" iya abunda ya fada masa kenan saboda baison ya ɗaga mashi hankali, kamar yadda su twins sukai hijra saboda kyamar marwa.



"Allah ya bata lafiya" ya amsa mashi da ameen


Tea pot baba obie ya dauka ya tsiyaya masu shayi a kananun kofuna suka dauka suna sha 



"Ka tambaye ni dangane da maganar da nace maka inaso muyi ko" ɗaga mashi kai yai alamar eh


"Nasan bazaka ji dadi ba, amma kada ka hanani tafiya" janye cup din hannunsa yai daga kan lips dinsa"tafiya zakayi"! Jinjina mashi kai yayi"lagos nakeson zuwa gurin aminina, kasan na daɗe ban ziyarce shi ba, kuma shi yana kokarin zuwa akai akai ya dubani har gida" jinjina kai chief yai"yaushe ne zaka tafi"? 



"Karshen watan nan, 3 weeks zanyi in dawo" ɗaure fuska chief yayi"har sati uku baba, ina laifin one week" murmushi yayi"dama sai da nayi fargaban fada maka nasan da wuya ka kyale ni, indai bazaka barni ba to saidai muje atare" girgiza kai chief yayi"ba zan iya binka ba, naso muje atare amma ayyuka sunyi min yawa, amma fa bazan bari ka tafi kai kadai ba,"! Yamutsa fuska baba obie yai"to ni da wa zan tafi owais? Kowa yana da aikin yi, bana son in takura masu"


 Shiru yayi jim kafin yace"zanyi magana da pravin, ya ɗauki hutun aiki Ya bika ku tafi, don gaskiya ni bazan bari ka tafi kai kadai ba" 



"Haba owais kamar wani karamin yaro, sai kace bakasan wanene kakan naka ba, waɗannan kafafuwan nawa ba inda basu taka ba, har birnin sin sunje, nafa yi yawan duniya fiye da tunaninka, tun ina matashina nake fita kasashen waje ni kadai abuna."


 Murmushi chief yayi"da da yanzu ba ɗaya ba, ka manyanta sosai ga tsufa, shiyasa nake tattalinka bana son wani abu ya same ka, duk da nasan Allah ke tsare bawansa." 


kalaman chief sun kara faranta ranshi murmushi yayi yana kallon fuskar shi"anya akwai wanda yakaini dacen jika a duniyar nan"? chief yace"ni yakamata nayi wannan tunanin, cos bana tunanin akwai wanda yayi dacen kaka irina, ina alfahari dakai," dariyar farin ciki baba obie yasaki idan owais na yabon shi dadi yake ji kamar ya zuba ruwa kasa ya sha.


"Owais Mu fara cin abincin nan kada ya huce.." Chief ne yayi serving dinsu atsanake suke cin abinci ya lura duk dagowar da zaiyi sai sun haɗa ido da baba obie wani kallon so da kauna yakeyi mashi.


"Naga kana kallona, ba zan canza maganata ba, zanyi magana da pravin din atare zaku je nasan zai baka kulawa ta musamman kuma zai dinga sanar dani duk wani motsinka" dariya baba obie yayi"oh ɗan leken asiri zaka hada ni da shi kenan" ɗaga mashi gira chief yayi"bakomai nasan saboda kaunar da kake yi min ne, naji na amince muje atare da shi din" ya fada yayin da yake tura abinci abakin shi.


Knocking room door din akay daga waje, baba obie yace shigo ciki"


muryar hajiya saratu ce ta katse masu cin abincin nasu, atare suka dago suna kallonta, shugowa tayi jikinta sanye da swiss code lace, idanunta sanye da farin glass, ta aza veil a kafadarta, ta kashe daurin ture kaga tsiya, hannunta na aruke da handbag dinta.



Kwata kwata babu annuri akan fuskarta saida taga chief ta ɗan saki fuskarta.


"Shalelena barka da safiya, har anyi shirin xuwa office.. " murmushi ta sakar mashi"barka da safiya babana, ina fata ka tashi lafiya" tay maganar tare da samun guri ta zauna tana fuskantar su..

"Lafiyalou auta,"


"Barka da safiya auntyna, kin tashi lafiya? murmushi tasakar ma chief da fara'a tace"lafiyalou my son, ina fata kaima haka ya aiki"?

Yace"Alhamdulillah"


"I'm sorry na shiga busy, kwanaki nace zan shiga asibiti in duba patient din nan banje ba, Ya jikin nata? Ya kuma babynta Unaisah ina fata suna lafiya"? cikin kulawa tayi maganar tana duban shi.


"She's feeling better, almost 3 days da sallamarta, unaisah tana lafiya" 


"Masha Allah, naji dadin jin hakan"


 tun da suka fara magana baba obie ke kallonsu cike da mamakin taya akai suka sasanta tsakaninsu, shi dai yasan tsakanin jikallan nasa da autarsa ba sa jituwa.


gaba ɗaya sun fahimci kallon da yakeyi masu, murmushin gefen fuska ya saki har cikin ranshi yaji dadin shiryawarsu"tun yaushe kuka sulhunta tsakaninku bansani ba"? Ya faɗa yana kallon su

Murmushin dattako hajiya saratu tayi batare data furta kalma ba, chief ne ya bashi amsa da cewa"me ka gani baba?

Nuna su yayi da yatsan shi"ga abunan azahiri, ku fadamin wani ɗan arzikin ne ya hadamin kanku? Ni dai nasan baku jituwa"


tattausan murmushi sukayi

Hajiya saratu tace"Allah ne ya hada kanmu, dama can shaidan ne ya shiga tsakaninmu amma muna kaunar juna, ko ba haka ba my son" ta faɗa tana kallon shi


"Hakane baba, kuma in sha Allah ba za'a kara jin kanmu ba" har cikin ranshi yaji dadin maganarsu, dama baya son sabanin da suke samu atsakaninsu.


"Alhamdulillah, naji dadi ubangiji Allah ya cigaba da hada mun kanku, Allah ya kara dankon zumunci atsakaninku, shi kuma shaidanin daya shiga tsakaninku Allah Ya kare mu daga sharrinsa"


 A tare suka amsa mashi da ameen, kwata kwata baiyi masu maganar mara lafiyan dayaji sun ambata ba, hankalin shi ya karkata akan jituwar da suka samu.


Miƙewa chief yayi da sauri baba obie yace"Grandson ina zuwa bamu gama yin breakfast ba"? 



"I'm sorry, Grandpa. I'll come back later"


ya faɗa tare da russinawa ya sumbaci forehead dinshi hajiya saratu dake kallonsu ba karamin burgeta sukayi ba, sabanin da da take jin haushi intaga baba obie da owais suna bama junansu kulawa kamar uba da da, abun yana 6ata mata rai saboda ita aganinta baya son twins saboda ubansu ba jinsinsu bane shiyasa yake nuna wariya tsakaninsu, abun da ta fahimta ayanzu owais yana matukar girmama baba obie biyayya yakeyi mashi sau da kafa  dama ita zuciya tana son mai kyautata mata.



Tayi zurfi a tunaninta, muryar baba obie ta katseta, firgigit tayi tare da kallon shi, har chief ya fita daga dakin bata lura ba.


"Fada min meke damunki? Tun shigowarki na lura da yanayinki kamar bakya jindadi ko"? Gyara zama tayi, kafin ta fara kora mashi jawabi.


"Baba akan marwa ne! Naga ciwon nata yayi tsauri shine nace me zai hana amaida ita garinsu gaban iyayenta? Ita kanta zataso ta kasance a karkashin kulawarsu hankalinta sai yafi kwanciya, ba kamar nan ba, ba dangi iya bana baba, kuma kaga ciwon nan nata bana lafiya bane, zata iya goga ma wani...." fuskarta ayamutse tayi maganar, kamar irin ta damu da ita din nan.


 Shiru baba obie yayi jim kafin yace"Auta, kin taba zuwa duba lafiyarta ne"? ɗaure fuska tayi

Murmushi yai"nayi mamakin jin maganarki, inace tin ranar farkon da ta fara lalurar baki kara leƙawa ba, aranar ma guduwa kikayi daga dakin ko"? Ya faɗa da zolaya, sunnar da kanta kasa tayi batare da tace komai ba.


"Meyasa zaki ce amaida marwa garinsu? Ko dan saboda lalurarta?  Da can da take mana hidima bamu guje ta ba sai yanzu da Allah ya jarabce ta? Munyi mata adalci kuwa? Yamutsa fuska tayi"baba ka fahimce ni, nasani ba ita ta daura ma kanta ba, babu wanda yafi karfin Allah ya jarabce shi, amma ni dai aduba mana, saboda lalurarta su twins suka daina kwana gida, kasan su da kyankyami kuma abune da basu saba gani ba, shiyasa duk suka firgice, ni kaina hankalina ba akwance yake ba, wlh dakyar nake iya bacci agidan nan gani nake kamar nima abun zai shafe ni..." da mamaki baba obie ke kallonta, ta haɗe rai ba annuri akan fuskarta, duk zaman nan da ake baisan cewa su twins sun bar gidan ba sai yanzu da yaji a bakinta ay da tuni yasa an dawo da su.



"Indai akansu twins ne zansa su dawo gida, amma marwa bazata koma gurin iyayenta ba, har sai ta samu lafiya, saboda anan ta samu lalurar, kuma anan zata samu warakarta in sha Allah, Ni ba zan bari mutuncina ya zube a idon jama'a ba, yarinya da lafiyarta ta fara aiki agidan nan sai kuma in maida ma iyayenta don amfaninta ya kare uhyum? Kiyi tunani mana, su kansu iyayenta ba za su ji dadi ba, su ga mun maida masu yarinyar su da nakasa a jikin ta.. "



Ran hajiya saratu ya 6aci muryarta tamkar zata fashe da kuka tace"baba ban taba neman abu agurinka kaki yi min ba, sai yau saboda kawai na nuna bana son zaman marwa agidan nan! Yakamta ka duba lamarin nan baba fisabilillahi saboda ita su twins sun kasa zama gidan nan, nima na rasa kwanciyar hankali, baba kafison farin cikin marwa akan namu kenan..." yunkurawa tayi zata miƙe da sauri ya dakatar ta ita"saratu koma ki zauna" zama tayi fuskarta ba fara'a...

Bottle water ya dauka me sanyi ya tsiyaya mata ruwa a cup ya mika mata, tana faman haɗe rai ta kar6a ta kurbi ruwan sau uku kafin ta ajiye tana kallon shi.



Yayi shiru yana nazarin maganar ta, arayuwarshi baya son bacin ran ya'yan shi, sannan baya son duk wani abu da zai haifar da rashin kwanciyar hankali atsakaninsu, sai dai bayajin zai iya mayar da marwa garinsu ahaka batare da taji sauki ba, yanajin tausayin ta, bayan haka bazaiso mutuncin shi ya zube agurin iyayenta ba.


"Baba nasan me kake tunani, indai akan iyayenta ne, wlh daga mun basu kudi zasu ja baki suyi shiru, kaga sai suci gaba da yin jinyarta, ni nayi alkwarin zan dauki nauyin duk wani abu da za'a kashe gurin nema mata lafiya, ni kawai gidan ke banaso ta zauna" gauran numfashi yaja kafin ya dubeta"auta" tace"naam baba"

"Kada ki makara, ki tashi ki tafi aiki, zanyi tunani, in sha Allah idan na yanke shawara zan sanar dake" amsa mashi tayi da toh, kafin ta mike tayi mashi sallama ta fuce daga dakin.


__________________________________✍️


Lokaci ɗaya Zuciyarta ta fara bugawa da matsanancin ƙarfi tamkar ana buga ganga, numfashinta ya fara fita cikin sauri, yayin da kirjinta ke harbawa yana sama da ƙasa da kokarin jawo iska a cikin hunhunta, wani irin gumine ya fara tsasstsafowa ta cikin hudojin gashin jikin ta, zufa ta soma gangarowa ta cikin nannaɗaɗdiyar sumar kanta tamkar yayyafin ruwan sama jikinta ne ya fara kakkarwa, Yatsun kafafunta dana hannunta suka kama kerma, idanunta suna arufe gam ta matsesu, fatar kwarin idanunta sai kerma take sakamakon kwayar idanunta dake jujjuyawa, kokari take ta buɗe idanunta takasa saboda raunin da sukayi, jikinta tamkar babu jini saboda rashin kuzari, ga wata matsiyaciyar kasala data daskarar da ita daga yunkurin da take yi na son farkawa, Allah kadai Yasan tsawon makonnin da ta dauka bata acikin hayyacin ta sakamakon duguwar sumar da tayi.


 A kalla ta shafe awa cikin mayuwacin hali tana kokarin ƙarfafa kanta donta samu damar buɗe idanunta, ta ko'ina ba sauƙi, jikinta tamkar an daddaure shi da igiyar kaca, sai faman jijjiga jikin takeyi donta samu kwarin gwiwar tada kanta.


La66anta dake a bushe ƙamas fatarsu ta faffashe hada busasshan ɗigon jini, da ƙyar ta iya moving dinsu ta furta"GABRIEL" kwata kwata sautin muryarta baya fita, cigaba da ambaton sunan tayi duk da radadin da makoshinta keyi mata mai azabar zafi, meyasa ta ambaci sunanshi? A karo na farko data dawo hayyacinta? Saboda shi ne aranta.



Lokaci ɗaya ba zato ba tsammani kwatsam tayi wani yunkuri da iya karfin ta na karshe ta daddage ta banbare kanta daga jikin abunda take a kwance tayi wata irin zabura ta miƙe zaune tana faman jan numfashi, sannu A hankali ta buɗe idanunta wani irin duhune bakikkirin ya mamaye ganinta, bata ganin komai tamkar ta makance, batasan a ina take ba? Meya faruwa da ita? ta manta komai, kamar tayi loosing memory din ta, tayi matuƙar rudewa ta rikirkice tunaninta ya gushe, daddafe kanta tayi da tafukan hannayenta cikin rawar murya ta furta"A ina nake? wa ya kawo ni nan? Meya faru dani? Babu mai jina ne? Kuyi min magana bana ganin komai, ko dai na makance ne...." sautin muryarta baya fita dakyau.

Kamar ta fasa ihu haka take ji, saboda takasa gane meke faru da ita? A ina take.



A lokacin da batay tsammani ba, kwatsam ba zato ba tsammani, wani siririn haske ya kurdado ta saman gurin da take, Waro idanu waje tayi cikin tashin hankali da tsantsar rudani take kallon hasken, A hankali hasken ya fara mamaye ɗakin har saida ya karaɗe cikin sa tamkar da rana.


Idanunta suka washe, amatuƙar ruɗe take kallon inda hasken ya fito ashe fitilune na saman ceilling din dakin, da sauri ta dubi inda take a zaune, Metal bed ne (gadon ƙarfe) irin kirar zamanin da na kaka da kakanni, Gadon Yana da girma da tsayi, ga wata lumbutsetsiyar katifa tattausar gaske mai dadin zama hada matassan kai guda biyu, daga saman gadon Yana da rumfa hada labulaye a kewaye da shi, kamar irin gadon sarakuna 


Gaba ɗaya ta ruɗe ta rasa gane waya kawo ta dakin? Da sauri ta kalli kayan jikinta, farar riga ce shara shara kamar matacin kwakko, komai na jikinta ana gani, rigar tana da dogon hannu, tsayin ta bai wuci Iya gwiwar ta ba.


Sumar kanta kamar an kifa mata yayi, ta bushe ba gyara duk gashin ya yamutse, ƙoƙarin saukowa tayi daga kan gadon sai dai ta kasa saboda tsayinsa bata san ya zatay ba, matsawa tayi daga bakin gadon ta leƙa ƙasa cikin sa'a ta ga matakala irin ta bene mai hawa shida, numfashi ta ɗan ja tare da sauke ajiyar zuciya, a hankali ta ɗaura  ramammun kafafuwanta kan matalar farko ta yunwa zata miƙe aikuwa wani irin jiri ya kwashe ta saboda rashin kwarin jikinta gaba ɗaya ta kundumo ƙasa timmm! ba karamin dakuwa tayi ba, amma saboda karfin hali da kwarin gwiwa irin nata ta daddage ta miƙe tana faman fitar da numfashi mai haki kamar wadda tasha uban gudu


miƙewa tay tsaye tana kallon katafaren ɗakin mai girman gaske, gado ɗaya ne aciki sai book shelve ma'ajiyar littattafai, da tsoffin akwatinan karfe daga gani tsohuwar ajiya ce, ga wardrobe mai girma ta jikin bango, wurga idanu tayi kan tukwanan kasa da ta gani girke a kasa, ɗaya saman ɗaya an jera su daurin ɗaurin sunyi sauro a jikin bangon da suke, hada kwaryaye rufe da faifan su, hada tukwanan furanni masu ban sha'awa daga gani koma wanene mamallakin ɗakin ma'abocin son kayan laka ne ko kuma makerin su ne.


A hankali ta ɗauke idanunta daga kan tukwanan ta bi bangon dakin da kallo, zanunnuka ta gani masu ban sha'awa, a hankali take tafiya tana nufar tsakar dakin tana cigaba da kallon abun mamaki da al'ajabi gami da rudani ita dai batasan waya kawota cikin shi ba! Ta manta komai.



tana cikin jujjuya idanu karaf ta hango Madubi zagayayye yana da mariƙi dake ajiye kasa...takawa tayi cike da fargaba ta nufi madubin yayin da zuciyarta ke cigaba da harbawa da karfi da karfi..tsayawa tayi agaban madubin tana kallon fuskarta, ta tsorata da ganin ramar da tayi, kashin wuyanta ya kwambare kamar zai fasa fatarta, ziraran yatsun hannunta ta daura akan wuyan tana shafa kashin kafin ta motsa yatsun a hankali ta shafa fuskarta, manyan idanunta dara dara launin brown ta zare su tana bin kanta da kallo, tana iya hangen dukiyar fulaninta sun rame sun kanjame bayan ada ba haka take ba, tana da kira irin ta karfafan mata masu jini ajika amma yanzu ta rame ta bushe ta faɗa kamar ba ita ba.


da zata iya tuna mummunan abunda ya faru da ita har zuciya zata iya hadiya ta mutu saboda tana da fusatacciyar zuciya, idan ta rikice babu mai iya sarrafa ta.


ta jima tana kallon kanta a cikin madubin, jiri jiri ta fara gani a idanunta da sauri ta dafe cikinta dake yi mata kukan yunwa ga wani kishin ruwa na fitar shari'a, makoshinta ya bushe ƙamas ko yawun da zata hadiya ta samu relief din kishin babu shi abakinta.


juwa ce ta kwashe ta gaba ɗaya jikinta ya rinjayeta ta yanke jiki ta faɗi ƙasa a sume..


Saurari Littafin Kurkukun Ƙaddara Takun farko  Kada a manta ayi mana subscribe like da kuma comment sannan a yi share. Domin samun sabbin littafi idan Mun ɗora.

 

Cikin abunda baifi minti ashirin ba kacal, taji safkar ruwa mai sanyi kan fuskarta, dogon numfashi taja haɗi da sauke ajiyar zuciya sam takasa ta6uka komai, ko yatsan hannunta bata iya motsawa saboda rashin kwarin jiki.


cikin mawuyacin hali ta ɗan yi karfin halin buɗe idanunta biji biji take kallon mutumin dake tsaye akanta batasan wanene ba.


Cikin disasshiyar murya ta furta"ruwa!ruwa!ruwan, zan sha! Kishi nake ji..." dakyar sautin muryarta ke fita tana tsaka da sambatu taji an kanga mata wani abu kamar bakin gorar ruwa saitin bakin ta, wani irin sanyine ya ratsa zuciyarta, lokacin da ruwan ya jiƙe makoshinta nan da nan ta fara kwankwaɗarshi makoshinta har wani sauti yake badawa kwat kwat...!!


"Ki sha A hankali kada ki shaƙe" cikin kunnanta ta tsinkayi muryar dattijuwar dake mata magana.


 Sai dai kwata kwata bata fahimtarta, tafi buƙatar ruwan fiye da komai ayanzu kamar rayuwarta ta dogara akan shi.


saida tasha mai isarta kafin ta fara numfarfasawa tana haki, wata irin nutsuwace ta shige ta, hatta bugun zuciyarta da fitar numfashinta sun daidaita, ganinta dawo daidai sannu a hankali take kallon fuskar tsohuwar da ta tallabe kanta akan kirjinta, hannunta yana ruƙe da gorar ruwa, tana asanye da alkyabba fara sol mai hula, tsohuwace tukuf fuskarta duk  tamoji tamoji, gashin kanta fari fat hurhura ta mamaye ko'ina na gashin, hatta gashin jagirarta fari ne fat, daga ganin tsohuwar tayi gwagwarmaya a duniya, tsufanta bai boye kyawunta ba, bakowa bace wannan face Tsohuwa


 *KHALA* dattijuwar arziƙi, fara mai farar aniya, tsohuwa mai zuciyar imani, macace mai tausayi da jinkan mutane, abun da zai baka mamaki tana ɗaya daga cikin Elders na kurkukun ƙaddara sune masu fada aji, tana da ƙarfin iko, amma meyasa ta fita daban acikin su⁉️


Gabriella ta tsareta da idanu tana binta da kallon kurulla, fuskarta da alamun ruɗani


kamar yadda take kallonta haka itama tsohuwa khala take kallon ta.


la66anta na kerma ta furta"wacece ke? Wa ya kawo ni nan? Meya faru da ni? Ki fadamin ina son sani" shiru tsohuwar tayi nata ce mata komai ba.



"Kinyi shiru baki ce mun komai ba, meyasa kike kallona? Wacece ke?....." ta faɗa arude tana tararraba idanu.


Tattausan murmushi ne ya bayyana akan fuskar dattijuwar, cikin sanyin murya ta furta"Sunana Khala, nasan baki sanni ba, kuma baki ta6a jin labari na ba, yau ne karo na farko da kika fara ganin fuska ta..." cike da dattako tayi maganar.


Ta ɗan dakata tana kallon gabriella.


"Yau tsawon makonni Ina jinyarki, Due to the traumatic brain injury that put you in a coma, I know you can't remember what happened to you because you've lost your memory..." tun da ta fara magana Gabriella ta nutsu tana kallonta.


"naji dadin samun lafiyarki, inatayaki murna"


Saurari Littafin Kurkukun Ƙaddara Takun farko  Kada a manta ayi mana subscribe like da kuma comment sannan a yi share. Domin samun sabbin littafi idan Mun ɗora.

ta fad'a fuskarta ɗauke da annurin farin ciki, ita dai gabriella takasa gane komai, gaba daya arude take da tsohuwar, bata fahimtarta



"Naji kin ambaci nayi jinya tsawon makonni bana acikin hayyacina, meya faru dani"? Girgiza kai khala tayi"I won't tell you because I don't want you to remember what happened to you, ko dan saboda lafiyarki, a yanzu nafi bukatar kwanciyar hankalinki, saboda ina da buri akanki"! Aruɗe Gabriel take kallonta, harta buɗe baki zata tambayeta wata irin yunwa ta murɗa cikin ta, da sauri ta dafe cikin da hannu tana faman yamitsa fuska ta kalli khala"ki taimaka min da abinci, yunwa nake ji..."



Ajiye gorar ruwan hannunta tayi, tare da taimaka mata ta zauna dakyar, Sandar ta dake ajiye kasa ta ɗauka, ta mike tare da juyawa ta nufi wani teburi dake a dakin hada kujeru biyu a kewaye da shi, daga saman teburin kwanukan abinci ne.



Ta ɗauko bowl ɗaya ta juyo tare da kallon Gabriella



"Bansani ba ko kin iya cin zogale da kuli..." tunkan ta ƙare maganar gabriella tace"Ina ci, koma menene zanci.." murmushi khala tasaki ta nufo gurinta ta miƙa mata kwanon, Hannunta na kerma ta cire murfin ta fara dibar zogalen tana ci, duk da babu ɗanɗano abakinta, kunnuwanta har motsi sukeyi tsabar dadi, hannu baka hannu kwarya take duma loma tana turawa a karamun bakin ta kamar zata shake, kamar kyaftawar ido ta lamushe shi tass hada sanya harshe tana lasar kwanan..dariya khala tayi"kin koshi ko kina bukatar kari" da sauri ta ɗaga mata kai, juyawa khala tayi cikin takun dattako ta koma gaban table din ta buɗe wani kwano mai ɗauke da tsokokin nama taje ta mika mata kwanon"kalacina ne na safe, da naci na rage, bansan yau zaki farfadowa ba, shiyasa ban tanadar maki abinci ba, amma kiyi hakuri da wannan, idan aka kawo min lunch dina zan baki kici ki koshi" kar6e kwanon gabriel tayi hannunta na kerma ta fara daukar tsokar tana ci, sai da tacinye tass khala ta ɗauki gorar ruwan ta miƙa mata, ta kar6a ta sha.


Nannauyar ajiyar zuciya ta sauke wani irin relief taji a jikin ta, duk da bata koshi ba, taji ɗan dama dama a cikinta.


Kokarin mikewa tayi da sauri khala ta taimaka mata ta mike tsaye kan kafafunta, cikin sanyi murya tace"har yanzu baki bani amsar tambayoyin da nayi maki ba, na ruɗe na kasa tuna komai, wanene ya kawo ni nan? Ko kece? Sannan meya faru dani? A ina nake?


"Ki manta da komai, sai ki zauna lafiya, tunawar baida amfani, idan kika bani hadin kai, kuma kika bi sharuddan da zan fada maki zaki tsira da rayuwarki, idan kuma kikayi min gaddama zaki dawwama awahala..." kalamanta sun rikita gabriela cikin rawar murya tace"meyasa zaki hanani tambayarki? Ina son nasan wacece ni! Meya faru dani, ina ji araina kamar na manta wani abu arayuwata, dan Allah ki tuna min..." dafa kafadarta tsohuwa khala tayi"nayi maki alƙawarin zan baki amsar tambayoyinki amma ba yanzu ba, har sai zuwa lokacin da tunaninki ya dawo dai dai..." shiru gabriella tayi gaba daya jin kanta take kamar ba ita ba, kamar ma ba aduniyar mutane take ba.


Tafiya khala ta soma yi tana nufar cikin dakin calmly ta cigaba da magana tana kallon fuskar gabriel


"Sharuddan da zan gindaya maki, na farko koda gigin wasa kada ki ƙetare iyakarki! Ma'ana kada kiyi yunkurin nema ma kanki hanyar da zaki fita daga dakin nan! Babu ruwanki da komai da zaki gani adakin nan! Ki zama tamkar makauniya, bana son mutum mai karanbani da kafiya..." ta faɗa tana jinjina mata kai, ita dai gabriela tayi zuru tana binta dana mujiya saboda batasan komai ba sai yadda akai da ita.



"Idan kika bani hadin kai, zaki tsira da ranki, kuma zan gatantaki, babu abunda zaki nema ki rasa adakin nan.." fuskarta da murmushi tayi maganar, kafin ta juya ta ɗaga sandar hannunta tayi mata nuni da wata ƙofa


Sannan tace"wannan kofar, makewayina ne, idan uziri ya kamaki zaki iya shiga, harma wanka zaki iyayi don kiji dadin jikin ki, arana zaki ci abinci sau uku, idan kadaici ya dame ki, zan baki story books da zaki dinga karantawa, suna da dadi zasu debe maki kewa, ga kuma furanni abun sha'awa zasu faranta maki rai" ta faɗa still da murmushi akan fuskarta.


Gabriella tayi sototo tana kallonta kamar sakarya, wuce wa tsohuwa khala tayi agaban bookshelve ɗin ta tsaya tare da kai hannu cikin shelve tana neman storybooks din da zata bata guda uku ta curo ta juyo ta nufi Gabriel ta nuna mata su.


"su kadai na baki iznin ki karanta, bayansu ban laminta ki ta6a sauran littattafan dake a cikin shelve din ba" jinjina mata kai tay alamar toh, bayan ta kar6i books din khala tace"ki samu guri ki zauna, har yanzu jikinki ba kwari," cike da ladabi ta amsa mata da toh, don yanzu ganinta take kamar mamanta saboda itace mutun na farko data fara gani a idanunta bayan tsawon lokaci data ɗauka a coma..


Ruƙe hannunta khala tayi, taja ta har zuwa gaban table din ta zaunar da ita kan kujera"idan kika gaji da karatun, ki koma kan gado ki kwanta kiyi bacci ki huta" cikin sanyin murya ta amsa mata da toh.


"Akwai inda ke yi maki ciwo a jikin ki"? Girgiza kai tay alamar a'a


"Okey, ko bayan na fita daga dakin, kika ji wani guri nayi maki ciwo a jikin ki, ki kira sunana sau uku, zan ji ki" 


"Toh,"


"Good girl" ta faɗa tare da shafa fuskar Gabriella da yatsun hannunta.


"Ki kula min da kanki" lumshe ido gabriela tayi kafin ta buɗe su tuni tsohuwa khala ta bace ma ganinta, har saida taji gabanta ya fadi ganin babu ita, akan table din ta ajiye books din data bata.


ta mike tsaye jikinta na kerma take bin ko'ina da kallo a kokarinta nata gano ina ta shiga, ganin babu ita adakin, yasa ta hakura da nemanta, ta juya ta nufi kofar makewayin da ta nuna mata, ta buɗe ta shiga, makewayine irin na zamani ya hadu komai cikinsa fari kyal, a tsaftace ba kazanta, a hankali take kallon cikinsa, bathtub ta gani ga shower, ga toilet seat, da cabinet, bata tsaya bata lokaci ba, ta cire rigar jikinta ta rataya a hanger, ta zukunna zatay fitsari taji gabanta amatse dakyar fitsarin ke fita nishi ta dinga yi a wahalce ta samu ta kammala.


ta miƙe tana faman sauke ajiyar zuciya, Takura kanta tayi da tunani har saida kwakwalwarta ta fara neman rikicewa tukunna ta hakura tana faman jan numfashi, ta nufi kwamin wankan ta shiga ta kwanta tare da kai hannu ta kunna bathtub faucet  ta cika kwamun da ruwa mai ɗumi wata irin ni'ima taji mai dadin gaske.


Ta daɗe acikin ruwan tana ɗumama jikinta kafin tayi wanka ta maida rigarta, ta fito ta zauna kan kujerar, ta dauki storybook ta fara karantawa.



Murmushine ya bayyana akan fuskarta, da alama labarin da take karantawa ya faranta ranta, babi huɗu ta karanta, ta fara jin kasalar bacci, miƙewa tayi tare da kwashe books din ta nufi book shelves din dakin inda taga khala ta dauko mata su, tana kokarin ajiyesu ta hankaɗe wasu jerin littattafai  dake a shelves tana kokarin tallabe su biyu suka rikito ƙasa, wani irin faduwar gaba ta ji, tsoro ya kamata tunawa da gargadin da tsohuwar tayi mata akan kada ta ta6a komai na dakin, jikinta na kerma ta zuƙunna tana kokarin tattara books din kamar diary suka an kulle su da makulli tayadda baza'a iya buɗe su ba. 


 Akan laps dinta ta daura books din kamar ance ta kalli covers dinsu karaf tayi tozali da hoton abunda ke akan diary na farko, zanan kananun yara ne su uku sanye da jajaye kaya, mata biyu sun sanya namiji a tsakiyar su, kayan matan rigace dai dai gwiwa launin ja, shi kuma namijin riga da wandone jajaye, abun da ya ɗaure mata kai da hoton cover din, duka yaran an daure masu hannayensu da igiya, an toshe bakinsu da jan kyalle, ga hawayen jini kwance kan fuskokinsu, da rubutun larabci aka rubuta sunan books din kokarin karantawa tayi A hankali ta furta sunan shi *sijill al-sujnā* bata san menene ma'anar sunan shi ba, janye na farkon tayi ta dubi sunan ɗayan diary din *tārīkh sijnil qadar* miƙewa tayi da sauri ta maida su gidan da suka fadowa, ta gyara su dakyau ta yadda ba azagane dun faɗo ba, da sauri ta nufi matakalar gadon ta haye ta kwanta tare da lumshe idanunta.


___________________________✍️


*HAJJATY*


Safa da marwa takeyi atsakar dakinta, Hannun ta ruƙe da wayarta, kwata kwata babu nutsuwa atare da ita, saboda fargaba da tashin hankalin ciwon marwa jiya taga abunda ya rikitar da ita, kusan kwana tayi adakin marwa tana kokarin shawo kanta saboda kukan da takeyi abun yayi yawa kamar zata kashe kanta, hajjaty ga tsoronta da take ji amma ahaka ta daure ta zauna adakinta har saida ta shawo kanta ta hanyar kunna mata karatun kur'ani kafin ta samu jikin marwa yayi sauƙi har bacci ya ɗauke sannan ta dawo daki, yau tun da safe ta buga ma sheikah imam kira awaya ta sanar da shi halin da marwa take aciki, tace mashi ta kasa gane meke damunta, sheikh imam ɗin yace zai shigo in sha Allah.


A yanzu haka shi take jira, ta kasa shiga dakin marwa saboda bata jin dadin ganin ta a mawucin hali, yarinyar ba karamun tausayi take bata ba.



Kira ne ya shigo wayar da sauri ta duba screen din wayar ganin sunan sheikh imam ne yasa ta daga da hanzari ta daidata nutsuwarta gurin yi mashi sallama bayan ya amsa mata yace"na iso gidan" amsa mashi tayi da toh, da sauri ta dauki mayafi ta rufawa kanta, ta zura flat shoes a kafarta, ta fito ta nufi main falo din gidan tasan anan yake tsayawa idan ya shigo.


Tunkafin ta karasa ta hango shi zaune kan sofa as usual cikin shiga ta magadan annabawa.. masu aikin gidan dake ta kai komo cikin girmamawa suke gaishe da shi, har abunsha sun kawo mashi da snack, har ya fara shan lemun ya hango hajjaty, mikewa yayi tare da tunkararta, da fara'a tace"barka da safiya malam, ya gida ya iyali" murmushi yayi jin ta tambaye shi ya iyali.


bayan sun kammala gaisawa tayi gaba yabi bayanta har zuwa dakin Marwa saida ta fara shiga kafin tayi mashi iso ya shiga daga ciki, a lokacin marwa tana kwance kan katifarta, bacci mai nauyine ya dauke ta sai faman jan numfashi take yi, daga gani awahalce takeyin baccin.



"Malam, ni dai narasa gane kanta cikin kwanakin nan, in ta fara kuka kamar ranta zai fita, kuma wlh ina kiyayewa gurin bata maganin kamar yadda ka ce.." tay maganar tana kallon shi.



Matsawa yayi daga gaban mattress din Ya zuƙunna Yana kallon yatsun hannayen marwa da fatar fuskarta, farat ɗaya ya gane babu lafiya, ciwon nata ma ƙara ha66aka yakeyi babu alamun sauƙi, lamarin ya ɗaure mashi kai, a kalla ya shafe mintuna yana kallonta yana nazari akan yanayin ta.


Hajjaty dake kallon fuskarshi sheikh imam tuni tasha jinin jikinta ganin yanayin shi ba walwala.


mikewa yayi tare da kallon hajjaty"anya kuwa kinbi sharuddan bata maganin dana fada maki dai dai? Ko dai kinyi kuskure ne" arude ta girgiza kai"wallahi ban ta6a kuskureba, ina kokarin kiyayewa kamar yadda na fada maka..." bayani tayi mashi yadda take bata maganin, dalla dalla kamar yanda ya fada mata, tabbas ya yarda da maganarta, abunda bai gane ba ta ina matsalar take! Shiru yayi jim yana kara bin marwa da kallo

Muryar hajjaty na rawa tace"malam akwai matsala ne"?



Ya fahimci hajjaty bata lura da habbakuwar ciwon marwa ba ..

Numsafawa yayi kafin ya furta"ina maganin nata yake"?


Jikinta na 6ari tace"ga su can akan mirror, bari in dauko maka" dakatar da ita yayi da hannu tsayawa tayi, tana faman zare idanunta, juyar da kai sheikah imam yayi tare da kallon gaban mirror din marwa A hankali Ya nufi gaban madubin Ya tsaya tare da kallon robobin maganin, ɗaya ya ɗauko ya buɗe ya kalli ruwan dake a ciki, yakai hancin shi ya shinshina da sauri ya kawar da kanshi gefe saboda zaurin daya buso hancin nashi.


Hankalin hajjaty ba karamin tashi yayi ba ganin yadda ya haɗe rai sosai, ɗaya bayan ɗaya ya buɗe murfin robobin cikin matsanancin tashin hankali ya juyo a sukwane ya kalli hajjaty dake ta zare idanunta


"Ya akai haka"? Ya faɗa yana dubanta


Muryarta na rawa tace"meya faru shiekh? Ban gane me kake nufi ba" haɗe rai yai tamkar ba sheikh imam ba, da kakkausar murya yace"wanene ya canza ruwan maganun dana baki"! Rass taji gabanta Ya faɗi ta fara zare na mujiya, jikinta ya hau yin kerma abunka ga matsoraciya kamar wata mara gaskiya sam takasa bashi amsar tambayar da yayi mata.


 Hakan ba karamin bata mashi rai yai ba"baki ji ina magana bane! Wanene Ya canza ruwan maganin? Saboda ni ba haka na baki shi ba, gaba ɗaya an canza ruwan cikin shi, bayan ni a iya sanina launin ruwan maganin baya canzawa..." A fusace ya fada yana binta da kallon tuhuma

Hankalin ta idan yai dubu toh ya tashi, Gabanta ya dinga faduwa gaba daya tabi ta rude, ta rasa amsar da zata bashi, wlh kwata kwata bata lura da hakan ba, sai da yayi maganar ta tuna da lokacin da ɗan aiken shi ya kawo mata maganin tabbas da ta buɗe tana dubawa taga launin ruwan ya banbanta.


Wahalallan yawu ta haɗiya cikin rawar murya ta furta"wallahi na rantse da wanda raina yake a hannunsa bani na canza ruwan maganin ba! Wlh bani bace, bansan wanene ba, Inna lillahi wa'inna ilaihirraji"un..." gaba ɗaya tabi ta ruɗe wata irin zufar tashin hankali ce ta wanke fuskarta, gani take kamar shiekh imam yana zargin ta.


Girgiza kai shiekh imam yayi"kin bani mamaki! Meyasa zakiyi mata haka? Ko dan kin gaji da jinyarta ne? Ni fa ban tursasa maki ba, aikin lada ne tun lokacin dana bukaci wanda zai kula da ita da kin fadamin bakiso ay da ba haka ba"


Runtse idanunta tayi, wasu zafafan hawaye suka wanke fuskarta, kalaman sheikh imam sunyi mata tsauri, taji ɗacin su azuciyarta.


"ka yarda dani, wlh ni ba muguwa bace, bazan iya cutar da marwa ba, ina da zuciyar imani, ko kiyashi bazan iya cutarwa ba, balle ɗan adam, wlh bani na canza ruwan maganin ba, na shiga ukuna" 


 ta fada tare da dafe goshinta da hannu daya.


tunda sheikh imam yaga yadda ta rikice nan take ya fahimci ba ita bace, dama da biyu ya furta



"Ya Isa haka, Na yarda bake bace, amma wanene toh? Dole akwai yarda akai aka canza ruwan, kuma koma wanene mutunne, lokacin da dan aikena ya kawo maki maganin a ina kika ajiye shi"? Waro ido waje tayi  murya na rawa tace"a dakina"



Sheikh imam yace"hakan na nufin anan aka canza ruwan maganin kenan? To wanene? Akwai wanda ke shiga dakin ki ne"? Shiru tayi jim gabanta na faduwa da matsanancin karfi, hankalinta ya tashi, kwata kwata bata kawo ma ranta pravin ba, tasan bazai ta6a yi mata hakan ba, me ma zai kaishi canza maganin marwa? Har abada ba za ta bari wani yasan akwai alaka tsakaninta da pravin ba.



Tayi zurfi cikin tunaninta muryar sheikh imam ta katse ta"kinyi shiru baki bani amsa ba? Wakike tunanin ya canza ruwan maganin? In har baki fadamin gaskiya ba, zanje in fada ma baba obie abunda ke faruwa"


 a firgice ta zare mashi dara daran idanunta, wani irin faduwar gaba ta ji daram kamar ana mata lugude a kirjin ta, arude ta girgiza mashi kai"kayi hakuri sheikh, wlh bani da masaniya, amma nayi maka alkawarin zan binciko koma wanene" jinjina kanshi yayi"kinyi alkawari? Ɗaga mashi kai tay"in har kika sa6a hmm kinsan sauran, keda baba obie ne" matse kwalla tayi, cikin sanyin murya tace"in sha Allah ba zan saba ba, amma sheikh meyasa kake tunanin wani ne ya canza ruwan? Baka tunanin bakaken aljanun jikinta ne sukayi mata hakan don kada ta samu sauki? In ba haka ba taya za'ay wani ya canza ruwan? Akan wani dalili"?   Ta faɗa tana kallon fuskar shi.


Murmushi shiekh imam yayi tare da dan girgiza kanshi kafin yace"ba al'janu bane suka canza ruwan, mutunne, dole akwai yadda akayi, ki zauna kiyi tunani dakyau..."


Cikin sanyin murya ta amsa mashi da toh,


"Sannan sheikh, akwai wani abu da marwa takeyi min, ni dai nagaza fahimta, duk in na shugo dakin zan bata magani, sai ta dinga goga hannunta a kasa, taita yunkurin yi min magana idan taga na kasa gane me take nufi saita kifa kanta jikin pillow...." bata ƙare maganar ba sautin tarin marwa ya katse hanzarin su, sam sun manta da ita dakin, maganganunsu su ne suka farkar da ita


Atare suka kalle ta, tana a zaune kan mattress din, ta jingina kanta jikin bango, idanunta suna rufe ga siraran hawaye dake zarya kan kuncinta, gwanin ban tausayi



"Marwa"! Jin muryar sheikh iman yasa tay saurin bude idanunta.


tana ganin shi ta fara kokarin yin magana donta gaishe da shi sai dai takasa.



"Basai kinyi min magana ba, na fahimce ki," ajiyar zuciya ta sauke, idanunta sun kaɗa jawur da su

Zukunnawa yai agaban katifar yana dubanta yace"Hajjaty ta faɗa min da akwai wani abu da kike yi mata nuni da hannu ta kasa gane menene ko zaki nuna min in gani"?



da sauri ta ɗaga mashi kai, jikinta na kerma ta matso bakin kafitar, ta daura hannunta akan floor ta dinga goga su tana kallon sheikh imam cike da sa ran zai fahimce ta, ita dai hajjaty sai faman zare ido takeyi fatanta Allah yasa shikeh imam ya gane menene marwa ke son fada mata abun yana damunta.


  A kalla marwa ta kwatanta mashi yafi sau biyar ganin kamar baigane ba yasa ta fara matsar kwalla.


zurfin tunani ya shiga can yace"wani yana zuwa dakin nan? Girgiza mashi kai tay alamar a'a"


"Ko ana tsoratar dake ne"? Still ta girgiza mashi kai, shiru yayi yana kara hasasowa can yakuma cewa"kodai kina son kiyi rubutu ne.. "Ga mamakin sa sai yaga ta daga mashi kai alamar eh hada ɗan murmushin ta.


Hajjaty tayi mamakin jin hakan sosai, da sauri ta nufi drawer din marwa ta fara neman littafi dakyar ta zakulo wata jotter tare da pen, ta dawo bakin katifar ta buɗe mata jotter din ta ajiye agabanta, ta zira mata pen din dakyar ta matse biron da hannayenta, ta soma kokarin gogawa paper din, lamarin ya daure masu kai, daga hajjaty har sheikh imam din, sun kagara da suga me ta ke son rubutawa.


Duk yadda taso ta rubuta sunan wanda yayi mata aika aikar takasa, biron yaki zama a hannunta duk ta cakalkala paper din akarshe ma ta yayyage, jefar da pen din tayi kasa ta fashe da kuka tare da kifa kanta jikin pillow, gaba daya jikinsu yayi sanyi, zuciyarsu ta raunata da tausayinta.


Cikin sanyin murya shiekh imam ya ce"kiyi hakuri, na fahimce ki, akwai wani abu da kike son fada mana, amma kin kasa, abunda nakeso dake ki kwantar da hankalinki, in sha Allah nan badajimawa ba ciwonki zai zama labari, zamu tayaki da addu'a sannan zan canza maki wasu magungunan.



tun tana shesshekar kuka hartayi shiru ta hakura musamman da taji maganar sheikh imam hankalinta ya ɗan kwanta, har taji zata iya hakura har zuwa time da zataji sauki tunda bata da mafita.


Mikewa yayi tare da kallon hajjaty, 


"ki zubda ruwan maganin dake a cikin robobin, zan kawo maki wani amma fa dole kiyi takatsantsan, kada ki kuskura ki bari wani yasan inda kika boye su ko kuma wani yasan na canza mata maganin nan daga ni sake wannan maganar, In kuwa kikai gangancin da wani ya sani har aka sake samun matsala to ki kuka da kanki domun kuwa bazan kyale ki ba...." a kausashe yayi mata maganar saboda ta ɗauki maganar shi serious, baiwar Allah duk tabi ta rude jikinta har kerma yakeyi sai taji dama bata kar6i aikin ba saboda bata son abunda zai hana ta kwanciyar hankali.


Sallama shiekh imam yayi mata, ya fuce yabarta da jimami


 ________________________✍️


Zaune yake a gefen gadon shi, jikinshi sanye da voile fari, tafukan hannayenshi tallabe da qur'ni, Ya tattara dukkan nutsuwarsa akan kira'ar da yake yi, acan kasan zuciyar shi damuwa ce cunkushe baya jin dadin zuciyarshi saboda halin da Benazir take a ciki ya damu ita, yana matukar jin tausayin ta.



Yana tsaka da yin kira'ar, sautin knocking Ya katse shi



Ɗaga murya yayi"wanene"? 



"Ya shureim ni ce, Ina son yin magana dakai" jin muryar Benazir yasa shi saurin miƙewa ya ajiye kur'anin Ya nufi kofar ya buɗe mata, A hankali ta shigo ciki, jikinta sanye da abaya, tayi rolling veil akanta, hannun ta ruƙe da yar purse dinta, ga wasu highhill da ta saka a kafarta, aruɗe yake kallon ta ganin hada make up akan fuskarta. 


"Ina kwana ya shureim ka tashi lafiya..." 


"Lafiyalou sister, Ya jikin naki"?

"Naji sauki sosai" shiru sukayi fargaban shi kada tace yakaita gurin azeezaty ya san halinta in rigimarta ta motsa.



"Lafiya? Naga kamar kinyi shirin zuwa anguwa,"?


Murmushi ta sakar mashi

"Eh, gidan su anila nake son zuwa, jiya munyi waya da ita, ta fadamun yaronta baida lafiya, ashe shiyasa bata kira ta yi min ya jiki ba.." tun da tafara magana shureim ke kallonta gani yake kamar karya ta shirga mashi don ta samu yakaita gidan.



Ganin irin kallon da ya ke yi mata ne yasa tai saurin furta"wallahi dagaske nakeyi maka, bari in kira maka anilan ku yi magana" tay maganar tare da kai hannu ta buɗe purse dinta, ta curo wayar ta kira layin anila tana fara ringing, ta miƙa mashi fuskarta dauke da murmushi.


"Assalamu alaikum, Anila barka da safiya"!


On the other hand tace"ya shureim ina kwana ka tashi lafiya? Ya jikin benazir din? Wlh junaid ba lafiya shiyasa ban samu na kira naji ya ku ke ba ashe ma har an sallame ta" ajiyar zuciya ya dan sauke.


"Lafiyalou anila, Benazir taji sauki, itace ma ta kira min ke, tace tana so tazo duba junaid, ubangiji Allah ya bashi lafiya, in sha Allah yanzu zamu zo"


"Allah Ya kawo ku lafiya, ngde" sallama sukayi ya mika ma Benazir wayar


"Ki bari sai anjima muje, yayi wuri yanzu" girgiza kai tay haɗi da ɗaure fuskarta"ya shureim itafa ta nuna tana son inje yanzu"


"Naji, amma dan Allah idan mu ka je gidan, kada ki yi mata maganar yarinyar nan Azeezaty, nasan hada hakan yasa kike zumudin zuwa gidansu, kiyi hakuri Benazir yarinyar nan ba yarki bace idan kika sa hakuri in sha Allah kema zaki ga taki yar.." 


dukar dakai kasa tay, idanunta suka ciko da kwalla.


"Kiyi hakuri idan maganata batayi maki dadi ba" girgiza kai tay'na fahimce ka, in sha Allah bazanyi mata maganarta ba, ay na hakura tuntuni" ajiyar zuciya ya sauke "haka nakeson ji, Kin fada masu mommy zaki fita" girgiza kai tay"a'a yanzu in zamu tafi sai mu gaya masu" amsa mata yai da toh


Kafin ya juya ya shiga ciki ya ɗauko carkey dinsa Ya fito suka jera atare suka nufi dining room, mutanan gidan duk suna azaune suna yin breakfast, mutumin ya haɗe fuska sai shan kamshi yake kamar iska tana mashi wari, abincin ma da aji da izza yake cin shi tamkar baya son tauna shi..


A fakaice hajiya layla take aika mashi harara kamar zata rufe shi da bugu, shi dai Alhaji ubaid ya nutsu Yana cin abin cin shi, yayin da zeenatu take fuskantar mommyn ta, sam takasa cin abincin ruwan lemu kawai take ta aikin durawa cikin ta, hankalinta da tunaninta suna akan Azeezaty, jiya har mafarkinta tayi, bata da burin daya wuce su haɗu da ita, don ta tambayeta wacece Unaizah mai kama da ita❓


Takun tafiyar su shureim ne yaja hankulansu ga duban su,


Bayan sun karaso cikin girmamawa suka gaishe da su kowa ya amsa masu banda Alhaji musa hakan bai dame su ba, sun riga sun dan halinshi


mami ta dube su"ina zuwa haka shureim"?

"Zamuje gidansu anila ne, yaronta baya jin dadi" hajiya sarah tace"Allah sarki, itace kawar benazir wadda suke zuwa asibiti dubata ko"? Benazir ta amsa mata da eh"Allah ya bashi lafiya" mami tace"ay da kun fada min tun dazu dana shirya mun tafi atare, amma idan kun isa gidan ku kirani dan Allah" suka amsa mata da toh, Alhaji ubaid yace"ku gaishe min da mutanan gidan, ace ma anila inayi mata yamai jiki, Allah ya bashi lafiya, idan na samu lokaci zan shigo gidan" ya amsa mashi toh.


"Ya shureim zan biku dan Allah" zeenatu ce tayi maganar, har zata miƙe Alhaji musa ya jefa ta da wani kallo tuni tasha jinin jikin ta, muryarta na rawa ta furta"dan Allah daddy ka bari su tafi dani, mommy kice ya shureim ya tafi dani inaso in bi su" atsawace Alhaji musa ya furta"karki kuskura ki ƙara magana! " a tsorace taja baki tayi shiru, idanunta akan fuskar shureim dake kallon ta, wani irin tausayinta ne ya kama shi, yana so su tafi da ita sai dai yasan daddynta bazai barta ba.



"Musa ka barsu su tafi da ita tunda tana son zuwa..." Alhaji ubaid ne yai maganar, 

Banza yayi da shi tamkar baiji abunda yace ba, hakan ya sosa zuciyar Alhaji ubaid musamman layla ranta ya 6aci, harara ta galla mashi akan idonshi, ita day hajiya sarah tayi shiru batace komai ba.



"Shureim ku tafi, Allah ya tsare hanya.." ta fada tare da yi masu alamar su je, ruko hannun Benazir yayi suka kama hanyar fita daga falon yana jiyo sautin shesshekar kukan zeenatu, har waiwayowa yayi sai kallon shi takeyi duk sai yaji ba dadi amma idan ya tuna abunda alhaji musa ya fada mashi sai yaji kwara zamanta agidan duk da shi baiga amfanin hakan ba saboda yayi imanin cewa Allah shi yake tsare bawansa aduk inda yake.


Har suka shiga mota, bai daina tunanin zeenatu ba, ta tsaya mashi aranshi yana jin tausayin rayuwarta


Tsawon mintina kafin suka karaso anguwarsu anila, motarsu ta na shigowa layin gidan suka hango anila atsaye cikin shiga ta abaya fara ta goya baby junaid abayanta, hannunta ruƙe da wayarta..


Tunkafin su karaso ta ɗaga masu hannu alamar su tsayar da motar, agabanta yayi parking, ta nufi backseat ta buɗe ta shiga ta zauna kafin ta warware goyan junaid ta kwantar da shi kan kirjin ta.


Dr shureum yayi zaton gidan zasu shiga har zai tada mota benazir ta ruƙe hannun shi ya dubeta da mamaki"ba ciki zamu shiga ba, Anila ki faɗa masa inda zamuje"


Cikin sanyin murya tace"ya shureim obie estate zaka kaimu" aruɗe yake kallonsu da mamaki yace

"Bangane ba, me zakuyi acan? Anila fada mun ina fata dai ba gidan iyayen yarinyar nan zakuje ba"?


"Ya shureim muje kawai, zamuyi maka bayani daga baya, wani abune mai mahimmanci zai kai mu can" bai musa masu ba, yayi reverse  ya miƙi hanyar  fita daga unguwar

"Anila ya jikin junaid din! Ko dai shima duk plan dinku ne"? Murmushi suka saki, Anila tace"a'a ba plan bane, dagaske baida lafiya, amma jikin nashi da sauƙi.."

"Meke damun shi ne"? Kafin ta bashi amsa junaid ya fara mutsu mutsu kamar zai farka hakan yasa tay shiru tana kokarin lalla6a shi don ya koma baccin.

Cikin kulawa dr shureim yace"Allah ya bashi lafiya" ta amsa mashi da ameen.

Post a Comment

Idan kuna da tambaya akan abinda Baku game ba ko kuma kuma Neman littafin da babu a nan kawai ku ajiye tambayarku a ta comment ko wani shawara da Zaku bamu.

Previous Post Next Post

Sponsored Link

Sponsored Post