Kurkukun Ƙaddara Takun Ƙarshe page 44 Complete by Boss Bature

Kurkukun Ƙaddara Takun Ƙarshe page 44 Complete by Boss Bature

Takun Ƙarshe

BOSS BATURE✊

Jin maganar dr shureim yasa ta saki Batool da ke ta faman yin haki, tana ta ƙoƙarin Gyara veil ɗinta daya rufe fuskarta Unaisah taja hannun ta suka nufi Ciki, Gaba ɗaya idanun su Benazir na akan su, Yadda suke tafiya a tsanake cikin nutsuwa yayi matuƙar burge su, Tamkar tagwaye komai na jikinsu kala ɗaya, gwanin ban sha'awa suke kallon su, Batool sai kiciniyar gyara mayafin takeyi takasa ga ɗan kunnanta da ya maƙale gashinta kwata kwata Unaisah bata lura da halin da take a ciki ba, sai janta ta ke yi.


"Babyna" Benazir ce ta kira ta da sauri ta dubi inda take atsaye lokaci ɗaya ta saki murmushin farin ciki, ta saki hannun Batool cike da zumudi ta nu fe ta Benazir ta rugumota a kirjinta kamar zasu koma mutun ɗaya, wani irin sanyi ne Ya ratsa zukatan su, kamar sun yi shekara ba su haɗu ba sunyi kewar juna.


Fuskar Aneelerh ɗauke da murmushi take kallon su har cikin ranta taji dadin faranta ransu da ta yi...


"Babyna, nayi kewarki, shi ne kika tafi kika barni, fushi nake dake baki damu dani ba" ta fada tare da ɗago kanta ta haɗe fuska alamar bata ji dadi ba' rufe fuska unaisah tay da tafukan hannayenta cike da jin nauyinta ta furta"i'm really sorry mommy na, wallahi na damu dake, ban manta dake ba kina araina"


Murmushi Benazir tay, tare da manna mata peck a forehead ɗinta, ta tallabo fuskarta da tafukan hannayenta, wani irin kallon so da kauna take bin ta da shi kamar zata maida ita cikin cikinta, tuni Unaisah tasha jinin jikin ta da ganin irin kallon ƙurullan da take yi mata.


 Bakomai take tunawa ba face lokacin data barta a kwamin wanka yar jinjira da ita cikin jini, sai gashi Allah ya raya abun shi, ta girma ta zama ƴar budurwa da ita, tsakaninta da taj sai godiya yayi namijin ƙoƙari gurin rainon Angel, har abada bazata ta6a rabuwa da shi ba, ko da bazai kula ta ba sai ta san yadda tay ta maida auran su ko dan saboda Unaisah, ganin bata da alamun daina kallonta ne yasa ta ƙara rudewa muryarta adabarbace ta furta"Ya jikin naki? Kin ji sauƙi"? Yar dariya Benazir tay don ta fahimce unaisah ta gano ta

Ɗaga mata gira tay"Alhamdulillah my baby, naji sauƙi sosai..."


"Yanzu kin gane ni wacece" dariya suka yi gaba ɗayan su, Hakan Yasa ta fahimci taji sauƙi yanzu tasan ita ba ƴarta bace.

.

"Ki ɗauka har yanzu ban dawo cikin hayyacina ba, saboda bana so ki daina kira na da sunan mamanki, kuma bana so na rasa kulawar da kike bani" tattausan murmushi unaisah tay"in dai wannan ne baki da matsala dani, zan cigaba da kiranki mamana, babu abunda zai canza"


Gaba ɗaya Sun maida Hankali akan Unaisah, In ka cire dr shureim wanda gaba ɗaya ya tattara Hankalin shi akan Batool dake ta ƙoƙarin gyara mayafinta ga raɗaɗin da kunnanta ke yi mata duk tabi ta burkice, ajiye cup din hannun shi ya yi kan table tare da miƙewa ya je gabanta ya tsaya ya ruƙo Veil ɗin Zai gyara mata jin hannun mutun yasa muryarta na rawa ta furta"Earring ɗina Ya maƙale gashina za fi nake ji" 


'Okay, calm down, I'll help you."


 jinjina mashi kai tay, ruƙo mayafin yai tare da zame shi Ya sauko kan kafaɗarta bai kalli fuskarta ba sai da Ya Cire mata earring ɗin da ya sarƙe gashin, kafin ya ɗago da idanunshi slowly ya dubi fuskarta adai dai lokacin ta buɗe idanunta kaitsaye suka shiga cikin nashi bai san ya akai ya tsinci kan shi da jin matsanancin faduwar gaba hatta yanayin bugun zuciyarshi saida ya canza tamkar ana buga ganga.


wani irin yanayi mara misaltuwa ne ya ziyarce shi, kamar yadda yake kallon ta haka itama ta ƙura mashi kyawawan idanunta sai faman kyafkyafta su takeyi kamar Yaji ya shiga cikin su, gaba daya ta razana da kallon da ya ke yi mata ga wani yanayi da ta tsinci kanta mai wuyar fassaruwa,  hankalin ta ya ɗan tashi, duk tasha jinin jikin ta aranta ta ayyana wanene wannan? Meyasa ya ke kallona? Ko dai jira yake in yi mashi godiya ne"? Muryarta adabarbarce ta furta"Um... thank you.'  


sam Ya kasa tanka mata sai kallon ta ya ke yi, yau ne karo na farko da suka fara ganin juna,  amma dukansu sun ji wani baƙon al'amari a zukatansu



Hankalin su Unaisah kwata kwata baya akan su..


Abunda yaɗan ɗaure mashi kai kaman nin shi da yarinyar, tun da Allah ya halicce shi bai ta6a ganin ɗan adam din da yake bala'en kama da shi irin Yarinyar nan ba! Ko Benazir da take kama da shi kamannin su bai kai haka ba, ita wannan kamar anyi photocopy din fuskar sa ne don ma ya ɗan manyanta.


"Baby na Who is she? Is she your sister?'  muryar Benazir ce ta katse Kallon kallon da suke jefa ma juna su, ajiyar zuciya dr shureim ya sauke tare da juyawa ya koma kan Sofa Ya zauna yana mai mamakin kaman nin shi da yarinyar yau yaga abun al'ajabin daya rikita shi.


"Sunan ta Batool Sister dina ce" da alamun rudani Benazir take kallon fuskar Batool Ta ɗan razana da ganin kaman nin su, aruɗe ta dubi Dr Shureim ta kuma juya ta kalli Aneelerh hankalinsu gaba ɗaya ya koma kan fuskar Batool, itama Aneelerh tayi mamakin ganin fuskar yarinyar kamanninta sun 6aci dana dr shureim.


Sun yi matuƙar ruɗewa da ganinta, Hankalinta ba karamin tashi yayi ba ganin irin kallon da su ke yi mata Jikinta har Ya fara kakarwa, Unaisah ta ɗan rude da ganin kallon da su ke yi ma Batool amma sai tay tunanin ko dan sunga kamanninta da dr shureim ne hakan yasa ta ɗan yi murmushi tare da ruƙo hannun Batool dake kerma tace"Sister, kinga aunty Benazir, ga yayanta Dr Shureim da nake baki labarin kamannin ki da shi, dama nasan za ku yi mamaki idan kuka haɗu" dakyar Batool ta ƙaƙaro murmushi akan fuskarta hankalinta sam ba'a kwance yake ba.



Saurari Littafin >>>>Kurkukun Ƙaddara Takun farko  Kada a manta ayi mana subscribe like da kuma comment sannan a yi share. Domin samun sabbin littafi idan Mun ɗora.
'

Miƙa mata hannu Benazir tay jiki asanyaye ta matsa kusa da ita, ta yi hugging dinta tightly a kirjinta lokaci ɗaya ta fara jin bugun zuciyarta na ƙarfafa haɗe da faduwar gaba, nan take fatimar dr shureim ta faɗo mata aranta Ƴar jinjirar da ta rasu bayan haihuwar ta da watanni ita kanta batasan ya akai ta tsinci kanta da tunanin yarinyar ba, sam ta kasa raba Batool daga jikinta kamar zata maida ita cikin ta a hankali take shafa bayanta da  tafukan hannayen ta, Batool ta yi shiru tana jin wani irin sanyi da kwanciyar hankali Yana ratsa zuciyarta.


Gyaran murya dr shureim yayi masu, A hankali Benazir ta raba jikinta daga na Batool


"Kun barsu a tsaye ku zauna mana" ya fada tare da nuna masu Sofa, ruƙe hannun Batool Benazir tay acikin nata suka zauna suna fuskantar dr shureim.


Unaisah ta nufi Aneelerh tun shigowarsu take ta ɗaukin son taga baby junaid, ta ɗanyi jinkiri ne don kada ta 6ata plan din su..


"Aunty Anila ina wuni? Ya su Mami da zahra" Magana takeyi ma anila amma hankalinta na akan baby junaid da anila ta rungume a kirjin ta, wani irin kaunar shi take ji kamar ta ƙwace shi daga hannun Aneelerh, ta yi kokari kame kanta ne kada ta cika zaƙewa agane sun san juna da jimawa


 fuskar Aneelarh da fara'a tace"lafiyalou, Zahra tana gaishe dake, ina fata mun same ki lafiya.." 


"Lafiyalou Aunty Aneelerh"

Dr shureim Yace"Babyn Benazir, Ni baki ganni bane, tun da kika ga mamanki kin manta da mu ko" ɗan murmushi tay"ba haka bane ya shureim, kana araina, ina wuni, ya su mami? ina zeenatu"?


"lafiyalou Azeezaty, su mami suna gaishe dake, ina fata mun same ki lafiya.."


"Lafiya lou, naga jikin mamana yayi sauƙi, ubangiji Allah ya ƙara mata lafiya" 


"Ameen babyn mamanta" yar dariya sukai, kafin wani ya kara magana wayar hannun shi tay ringing daga cikin aljihunsa, a hanzarce Ya curota Ya duba sunan me kiransa, mikewa yai tare da kallon Benazir dake kallon shi"Mami ce"?


"A'a bakuwar number ce, bari na ɗaga naji" cikin sauri Ya nufi hanyar fita daga sitting room din, zuciyar shi cike fal da tunanin yarinyar daya tsaya ma shi aran shi, baiso kiran ya katse mashi kallonta da yake yi ba, bai kula ba tun da ya miƙe Batool tabi bayan shi da kallo kamar wuyanta zai 6alle, harya kusa fucewa ya ɗan juya don ya saci kallonta karaf suka haɗa ido da juna, sanyayyar murmushi ya sakar mata tare da ɗaga mata hannu, kunyar shi ce ta kama ta da sauri ta juyar da kan ta gefe ɗaya, mutumin ya kwanta mata aranta tun da Unaisah ta bata labarin kamannin su, yau da ta gan shi face to face sai taji ta kamu da ƙaunar shi.


Da ido Unaisah tay ma Batool nuni da data gaida su Aunty Aneelerh muryarta na dan rawa ta furta"Aunty Anila Ina wuni" da fara'a Anila ta ce"lafiyalou sister fatan mun same ku lafiya" 


"Muna lafiya" 


Bata kau da ido daga kallon fuskar Batool ba, tana so tasan wacece ita? Ko itama ɗaya ce daga cikin yaran da zahra ta bata labarin badakalar da aka sha akan su ranar dinner din prime minister, ko kuwa dai yar uwar chief ce? Ta ayyana acikin zuciyarta, Ta dai bar abun aranta har zuwa time da za su yi magana da unaisah, tayi zurfin acikin tunanin ta taji hannun unaisah akan nata a hankali ta kau da ido daga kallon batool ta dubi unaisah, kar6ar junaid tay daga hannunta ta kwantar da shi kan laps ɗinta, ta ƙura ma shi ido tana kallon shi kamar zata lashe shi..


"Yau dai na kawo maki babynki, da kike ta zumudin son ganin shi, Ina fata na wanke laifi na" ta faɗa tana leƙen fuskarta, jinjina kai Unaisah tay"da har nayi fushi, da ace baki kawo min shi ba, zansa daddyna ne ya kawo ni har gida don inga ɗan ƙanina, amma yanzu kin wanke kanki agurina" ta faɗa da murmushi akan fuskarta


Anila tace"Tun acikin mota yake ta sharar bacci, Kamar wanda Yasha ƙwaya"


"ay ko dai yanzu zan tada shi, saboda ba karamin missing din shi nayi ba...." kafin ta ƙare maganar Baby junaid Ya fara mutsu mutsu alamar zai farka lura da hakan ya ɗaga hankalin Aneelerh, fargabanta kada junaid ya kwafsa masu, tasan muddin ya farka zai yi wuya in bai gane Angel  ba kamar yadda kwanaki ya shaidata a hoto sauƙin ta ma dr shureim ya fita daga ɗakin dama shine damuwarta bata da matsala Benazir tasan komai already sunyi plan.


burinta Ya farka su haɗa ido da juna matsawa tay da fuskarta saitin ta shi ta kurama shi idanunta, miƙewa batool tayi ta dawo gefen Unaisah ta zauna tana kallon junaid ba ta son ta nuna zumudinta akan shi saboda unaisah ta kwa6eta, shiyasa taƙi sakin jiki kada tay wani abu ba dai dai ba.


Saurari Littafin >>>>Kurkukun Ƙaddara Takun farko  Kada a manta ayi mana subscribe like da kuma comment sannan a yi share. Domin samun sabbin littafi idan Mun ɗora.

Da wata irin kasala Ya karasa buɗe idanunshi, sun kaɗa jawur da su, biji biji yake ganin fuskar mutun a saitin tashi, red lips dinsa na kerma ya furta"mommy," shiru yaji ba'a tanka mashi ba, a hankali ya ɗaura yatsun hannayen shi akan fuskar Angel ya shafata har zuwa saitin la66anta ya ɗan matsa su kamar ya samu abun wasa, sam bai gane wacece ba saboda idanunsa sun disashe


"Mommy" ya sake ambaton sunan yana faman yamutsa fuskar shi.


Jin shiru taki amsa mashi ne yasa shi murza idanunshi da yatsunsa suka washe ya sake duban fuskar Unaisah dake yi mashi murmushi, shiru yayi yana kallonta yanayin fuskarshi ya nuna kamar ya ruɗe da ganin ta, tsawon mintuna bai tanka mata ba, kowa yayi shiru suna jiran ganin me zai yi 


Tsinin hancinta Yaja da hannun shi, ta lumshe ido tana dariya, shima sai ya kama dariya kamar sun san juna, lamarin ya daure ma su anila kai, da alama junaid yayi azan mafarki yakeyi

Cikin sanyin murya ta furta"My little bro"


Lokaci ɗaya yanayin fuskarshi Ya canza Ya kura mata ido Yana kallonta ba tare da ƙyaftawa ba, 

Unexpectedly taji ya furta"ANGEL"? Waro idanu waje tay tare da buɗe baki ta dubi Batool itama mamakinne Ya kamata saboda ta faɗa mata basu ta6a haɗuwa da juna ba wannan ne karo na farko


Sam Ta ƙasa furta kalma har sai da taji Ya ce"Angel uhm? Angel ɗina ne? Yayata" Sautin muryarshi baya fita dakyau ta fahimci kamar baya jin dadi, ruwan hawaye ne suka taru akan fuskarta, cike da jin dadi ta jinjina mashi kai  la66anta na kerma ta furta"ni ce"


Aneelerh sai faman sakin murmushi ta ke yi dama tasan zai yi wuya in bai gane ta ba.


Still da ruɗu akan fuskar shi, kokwanto yake, kamar bai yarda ba, Lumshe idanun shi yai tare da buɗe su.


ɗago da kan shi tay tare da kwantar da shi saman kirjinta, ta tallabe shi tare da manna mashi sumbata har sau uku kan cheeks dinsa


Gyaran muryar da Aneelerh tay mata ne yasa ta ɗago adabarbarce ta dube su sam ta manta da Benazir duk saita kama kanta tana faman rarraba idanu  akan su, Basarwa Benazir tayi tamkar bata ji me Junaid yace ba sarai ta fahimci ruɗewar da Angel tayi tasan don saboda ita ne kada ta gane wani abu.



Tun da Aneelerh tay gyaran murya junaid ya kalle ta tayi azan zai sanya rigima akan ta ɗauke shi kamar yadda ya sa6a yi ma kowa ƙiwuya amma wani iko na Allah sai ta ga bai yi ba, aranta ta ayyana watakil ya ga ne Angel dince shiyasa ya yarda da ita, miƙa hannu Batool tay da niyar ta dauke shi Ya maƙe kafaɗa alamar ba zai je ba.


Anila tace"sai kunyi hakuri da shi, baya da koshin lafiya" atare suka haɗa baki gurin furta"Allah ya bashi lafiya" ta amsa masu da ameen



"Kana buƙatar wani abu"? Cikin kulawa unaisah tay maganar tana kalon fuskar shi Ya nutsu Yana ta kallonta


"Batool zubo mashi juice a cup" unaisah ta fada tare da kallon ta da sauri batool ta ɗauko juice din da dr shureim Ya aje a cup bai sha ba ta miƙa wa Angel ta kar6a ta kanga mashi abaki A hankali ya fara sha.


"Naji shiru yaya shureim bai dawo ba" ta faɗa tare da kallon Anila

"May be bai kammala Yin wayar ba" acewar Anila

Sauke ajiyar zuciya ta ɗanyi har yanzu da sauran damuwa akan fuskarta.


Wrist watch din hannunta ta duba karfe ɗaya da rabi


"Bansan lokaci yaja har haka ba," Anila tace"nasan mami zata neme ni"

"Batasan kin fito bane"?

Ta sani amma ce mata nayi gidan ku zanje"


Da zolaya Benazir tace"Mai karya dan wuta dai," dariya Anila tay..


"Naji shirun yayi yawa, bari naje na duba Ya shureim" ta faɗa tare da miƙewa ta fuce daga dakin


Ajiyar zuciya Aneelarh ta sauke tare da kallon su Unaisah, Hankalinta Ya kwanta da ganin yadda junaid Ya saki jiki da ita.


"Aunty Anila ki bani wayarki mu dauki hoto, Na bar nawa a daki.' 


Saurari Littafin >>>>Kurkukun Ƙaddara Takun farko  Kada a manta ayi mana subscribe like da kuma comment sannan a yi share. Domin samun sabbin littafi idan Mun ɗora.

"Okay" ta faɗa tare da zaro wayar tace"bari nayi maku pics din da kaina, ku gyara" hotuna ta fara ɗaukar su kala kala wani daga zaune wani daga tsaye wani kuma sukayi atare su uku junaid dai yana a maƙale da Unaisah Batool tay kwakwar ta ɗauke shi Yaƙi yarda da ita, bayan sun gama ɗaukar hotunan Anila ta ɗibi snacks a dan plate ta ba unaisah" ki bashi yaci, da safe baici abincin kirki ba" kar6ar plate din tay ta fara bashi abaki Yana ci.


Lokacin da Benazir ta fito waje neman Dr shureim A tsaye ta hango shi jikin Motar shi yana yin waya, da sauri ta nufe shi adai dai time din ya kammala yin wayar"ya shureim lafiya naga ka dade baka dawo ba" fuskar shi babu walwala Ya ce"Zeenatu ce ta kira ni da layin tani, tana kuka bata jin dadin jikin ta tace inzo gida tana son gani na"


"Baiwar Allah, dole taji ba daɗi ya shureim, Banji dadin yadda Uncle yake takura rayuwarta, ni nasan hada damuwar hakan"


ta fada cikin sanyin murya tana kallon shi


"Ka tafi ya shureim, Inyaso sai mu tsaida me abun hawa Ya kai mu gida" girgiza kai yai"a'a bazan iya tafiya nabarku ba, zan bata hakuri ta jira zuwa lokacin da zamu koma gida" ya fada yana kokarin danna mata kira da sauri Benazir ta ruƙe hannun shi amarairaice ta furta"a'a ya shureim kada ay haka, tunda kaga ta kira ka da akwai wani abu dake damunta, tana son ganinka, kuma kaima nasan hankalin ka bazai kwanta ba in har ba zuwa kai gurin ta ba..."


 shiru ya yi jimm yana nazarin maganarta, aranta Allah Allah take Ya tafi duk don saboda ta samu taj yace zai kaisu a motar shi


ɗagowa yai da ido Ya dube ta"zan tafi amma zan dawo zuwa anjima in ɗauke ku" Amsa mashi tay da toh ka kula min da kanka" murmushi ya ɗanyi mata harga Allah baiso tafiyar shi ba, saboda yarinyar nan mai kama da shi ta tsaya mashi aranshi.


Akan idon Benazir motar dr shureim ta fuce daga gidan, nannauyar ajiyar zuciya ta sauke tare da duƙar da kanta ƙasa, damuwa ce cunkushe a cikin zuciyarta, ga dai yarta Allah ya nuna mata da ranta da lafiyarta kuma tayi farin ciki mara misaltuwa sai dai bata jin zata samun sukuni da kwanciyar hankali in har taj bai yafe mata ba,  har yanzu tana son mijinta kuma bata jin zata iya rayuwa da wani ɗa namiji a duniyar nan in ba shi ba, zurfin tunani ta shiga da ace tun farko da ya aureta sunyi zaman lafiya zai iya yi mata uziri amma Yanzu koda yaji cewa Asiri akai mata ta gudu tasan bazai ta6a yarda ba saboda yasan wacece ita

Cikin karyayyar murya ta furta"Halina ne Yaja min, Ni na ja ma kaina..."


batai aune ba taji safkar hawaye kan kuncin ta, da sauri ta sanya tafin hannu ta share ƙwallar, kafin ta juya ta nufi hanyar koma wa sitting room din tana ta ƴan waige waige cike da sa ran zata ga 6ullowar taj sai dai har ta shiga babu shi babu alamar shi...


__________Ummin America


Futowa tay daga bedroom din ta jikinta sanye da bubu gown ta material, tay rolling akanta, flat shoes ne a kafarta, matsawa tay gaban handrail ta dafa tana kallon downstairs, A falo ta hango su gaba ɗayan su banda mutun uku, kowan nan su yana azaune kan rug sun haɗa kai suna rubutu a cikin notebooks din su, Sajeed ne kadai ya zauna kan sofa da alama shi ke koya masu rubutun.


Zura hannayenta tay acikin aljihun rigarta, ta nufi stairs cikin nutsuwa take taka matakalar ta sauko down ta nufe su babu wanda Ya lura da ita a cikin su har sai da tay masu gyaran murya tukunna suka dago da kai suka kalle ta har suna haɗa baki gurin furta"Aunty Ummi zo ki ga Rubutun mu, Ki za6i nawa yafi kyau" kusan atare suke mike tare da kewayeta kowa Ya miƙa mata notebook din shi.


ƙin kar6a tay gudun kada ta haɗa rigima kallo ɗaya da tai ma rubutun su sai da taji gaban ta ya faɗi ganin wani jagwalgwalo, a fakaice ta kalli sajeed karaf suka haɗa ido da juna da sauri Ya kumshe dariya yai mata alamar ta duba mana.


"Aunty ummi nawa zaki fara dubawa, nafi su abun kirki"


Jemimah ce ke rokon ta, kar6ar book din tay tare da duba rubutunta itace ke yin rubutu shigen na thailand ka rasa ta yadda take jagwalgwala shi


"Aunty ummi in kin gama duba nata saura nawa" acewar Azeeza, Deeja tace"wlh na riga ki nawa zata duba" kamar zasu sanya mata rigima.


Jinjina kai ta yi"Jemimah Kinyi ƙoƙari ki dage kin ji, idan kika maida hankali har kyauta zanyi maki" uban tsalle ta daka na murna hada yi ma Azeeza gwalo ta kar6i notebook dinta tana ta murna


"Muga naki azeeza' mika mata tay aranta ta ayyana tab lallai wlh da a school suka rubuta Iya shegen nan, jakkin duka zasu ci' amma a fili sai ta ɗan murmusa tace"kema kinyi kokari, Ki ƙara himma" dadine Ya lullu6e azeeza ta kar6i book dinta ta juya ta nufi jemimah.



Saurari Littafin >>>>Kurkukun Ƙaddara Takun farko  Kada a manta ayi mana subscribe like da kuma comment sannan a yi share. Domin samun sabbin littafi idan Mun ɗora.

Ɗaya bayan ɗaya saida ummi ta duba notebooks din Har ƙwara Naufal Ya iya rubuta ba laifi tayi mamaki har saida ta tambaye shi ya akai yafi su iyawa, Da hannu ya nuna mata Sajeed"kullum A ɗaki kafin mu kwanta bacci, Shi yake koya min rubutu da karatu..." jinjina kai tay"Sajeed sannu da kokari, amma yakamata suma sauran ka dage da koya masu kamar yadda kake koya ma naufal" amsa mata yai da toh.



Deeja sai haɗe rai take don ba'a yabi nata ba, muryarta tamkar zata fashe da kuka tace"rubutun ma bazan ƙara yi ba" ta faɗa tana kokarin keta littafin da sauri Haris Ya ruƙe hannunta"wayace maki rubutun baiyi kyau ba, ay naki yafi na kowa" kwa6e fuska tay tare da kallon Aunty Ummi tana faman zum6ura baki tace"amma ayni baki yabi nawa ba ko" yar dariya ummi tay"oh wai saboda ni zaki keta littafin, toh kiyi hakuri mantawa nayi amma naki yafi na kowa" washe baki tay har taji dadi..


"Ni rubutun ma yai kyau ko kar yayi ba damuwa ta bace, indai ba za'a hanani cin abinci ba" ta faɗa tana hura hanci, gaba ɗaya suka sanya dariya, girgiza kai Ummi tay"Allah ya shiryeki foodie, ke dai indai zaki samu abinci baki da sauran damuwa" ɗaga mata gira tay.


Sarah da ta gama haɗe rai wurga notebook dinta tay kan sofa ta juya zata tafi 


"Hey! Where are you going?' muryar ummi ce ta katse mata hanzarin ta, yamutsa fuska tay"nagaji da rubutunne zanje na kwanta" murmushi ummi tay"nasan me kike ma fushi don ban yabi rubutunki ba ko" girgiza kai tay"a'a kawai nagaji ne" daga yanayinta ummi ta fahimci zatai rawar kawai dama tana lura da ita, ta iya raina abu in baiyi mata ba.


"Okey, kije ki kwanta ki huta, da anjima, da kaina zan koya maku rubutun"


"Okay, thanks" ta faɗa tare da juyawa  ta nufi dakin su tana tafiya kamar zata balle tsabar tsawon ta har yanzu bata da ƙiba.


"Kuma idan kun gaji ku aje karatun, kwakwalwa tana buƙatar hutu, amma fa dole ku dage ilmi yana da matuƙar amfani, you have to endure and persist before you succeed." ta6e baki parvin tay"Allah aunty ummi da kin daina wahalar da kanki gurin yi mana bayani, bamu gane komai.." sakin baki tay sototo tana kallon parvin abun ban haushi abun dariya


Rubina tace"nima Allah bani ganewa, Nifa nafison in kwanta inyi bacci ko inci abinci" kallon ta ummi tay


Hibba tace"dama girki kika koya mana, da yafi, kin ga sai mu dinga girka abun da ran mu yake so"


Harara ta ɗan watsa mata"hauka nake in kai ku kitchen da sunan zan koya maku girki? A haka? Ku fara samun ilmin kafin in yi tunanin koya maku girkin"


Hannah tace"wai komai saida ilmi, to a jika abamu musha sai mu haddace" tuntsirewa ummi tay da dariya, Sajeed dake sauraron su baisan sa'adda ya fashe da dariya ba


"Aunty ummi dama kin daina wahalar da kanki gurin yi masu bayani, ba zasu fahince ki ba, har yanzu da sauran su" acewar Sajeed, tsagaitawa tay da yin dariya cike da nishadi tace"wani lokacin kamar masu hankali, wani lokacin kuma wlh kamar in hada ku da tsumagiya inta jibga" dariya sukayi gaba dayan su


"Ina Unaisah da Batool? Banga gifcinsu ba, ko suna adaki ne"? 


Hawwa tace"basa nan tun dazu muka je neman Unaisah don ta bamu notebooks dinmu mu yi karatu bamu ganta ba kuma bata a toilet sai dai muka ɗauko books din" 


"Kun duba ko'ina baku gan su ba? Ko dai sun je dakin Danish ne"? Haris Yace danish Yana atare da chief suna karatu bana tunanin sun je dakinsa"


"To Ina suka je ne"? Ta fada tana kallon su


Yasmin tace"kila sun fita waje ko dai muje mu nemo su"!


Shiru ummi tay bata amsa ba tunani tay ko dai sun shiga bangaren daddyn unaisah ne"?


Da sauri ta zaro wayarta daga aljihu ta lalubo contact din unaisah ta kira layinta tana ta kira ba'a picking har ta katse almost 3 times


Yanke shawarar kiran taj tay har wayar ta ƙare ringing ba'a ɗaga ba


"Nafi tunanin suna acikin gidan nan, ku tayani neman su" amsa mata su kai toh, da gudu wasu suka nufi bangaren hagu wasu dama Suka fara bin sako da lungu suna neman su.


 _________________________✍️



Bayan dr shureim ya isa gidan, a hanzarce Ya fito daga motar Ya nufi Cikin main falo Yana ta sauri saboda Hankalinsa Ya tashi Da halin da Zeenatu take a ciki Ya kosa Ya ganta ko hankalinsa ya kwanta har ya kusa fita daga falon muryar Tani  ta katse mashi hanzarin shi.


"Shureim har an dawo" dakatawa yai tare da kallonta"Tani na same ku lafiya" da fara'a tace"lafiyalou, "


"Ina mutanan gidan"?


"Hajiya layla tana aɗaki, zeenatu kuma bata jin dadi amma na kira daddynta awaya na faɗa mashi, Yanzu haka ya turo family doc din su Yana aɗakin Yana duba lafiyarta..."


tun kafin Ta ƙare maganar dr shureim Ya furta"Ya Salam! Mami tasan bata da lafiya"? Girgiza kai Tani tay"dana je faɗa mata na iske tana bacci shiyasa ban tadata ba"



Hankalin shi atashe Yayi saurin nufar upstairs, azafafe Yake taka stairs din harya haura second floor, Yana isa gaban ƙofar ɗakin yajiyo wata Murya irin ta giggan tantira daga cikin ɗakin


"Don't waste My time, idan baki bani haɗin kai ba, zan kira daddyn naki awaya in fada mashi,"


 shesshekar kukan zeenatu yajiyo tana fadin"ni wlh banso, ka kyaleni, ka kyaleni nace banaso" zuciya da sake sake ta raya mashi wani mugun abunne ke shirin faruwa, gabanshi na faduwa Ya ture ƙofar ɗakin da hannu kai tsaye idanun shi suka sauka akan jibgegen katon nan Ya haye kan gadonta yayi mata rumfa da gabjejen kirjin shi ta maƙure kanta jikin headboard, jikinta sai kakarwa yake yatsun hannunta dana kafafuwanta sai kerma suke, ta rufe kirjinta da tafukanta, Yar rigar wanka ce a jikinta da bata wuci gwiwar kafarta ba, sumar kanta duk ta rufe fukarta....wani irin kishi ne Ya rufe dr shureim baisan sa'adda yai kukan kura daga inda yake yai wani ƙwaƙƙwaran taku Ya damƙi kafar dr mark A firgice Zeenatu ta ware idanunta akan fuskarshi la66anta sai kerma suke.


Dr mark ko ajikin shi, Fuskarshi a murtuke ba annuri Ya dubi Dr shureim da ya ruke kafar shi.


A gadarance yace"malam Lafiya ka ruƙe min ƙafa" ya faɗa yana bin shi da wani kaskantaccen kallo


Rai a6ace dr shureim yace"uban me kake yi akan gadon ta"? ta6e baki dr mark yai tare da nuna mashi Syringe ɗin hannun shi"Ubanta ne Ya kira ni don in duba lafiyar yar sa, ko kana da Ja ne" ya faɗa tare da ɗage mashi gira, ƙarfin halin mutum ya ɗaure mashi kai ko kunya bai ji ba Ya kure karamar yarinya kan gadon ta.


"Amma dai baka da hankali, Don ubanta Ya kiraka ka duba kafiyarta sai yace maka ka shigo har dakinta saman gadon ta? meyasa ba zaka tura me aiki ta kira maka ita ka dubata a falo ba? Hakan da kai ka kyauta? 


Saurari Littafin >>>>Kurkukun Ƙaddara Takun farko  Kada a manta ayi mana subscribe like da kuma comment sannan a yi share. Domin samun sabbin littafi idan Mun ɗora.

Ganin dr shureim zai raina mashi wayau yasa shi saukowa daga kan gadon Yana wani buɗe kafadunshi Ya tsaya agaban shi"meye naka aciki huh? Yakamata kasan irin kalaman da zaka furta min, Ni ba sa'an yin ka bane, kada kace zaka shiga hurumin aikina, ba yau na fara ba!  kuma umarnin mahaifinta nake bi"



A harzuke dr Shureim yace"oh shi uban natane Yace ka shigo dakinta har kan gadon ta don kayi mata allura kuma haka ake allura abi a danne mutum"? Ya jefa mashi tambayar yana binsa da kallon tuhuma.


"Malam ka tsaya a iya matsayinka, nima in tsaya a nawa, tun wuri ka fuce daga dakin nan tun kafin na 6ata maka rai"! A kausashe Ya faɗa Yana Huci saboda baya ɗaukar raini, daga gani yana ji da karfi, juyawa yai da niyar ya koma kan gado saboda kunya bata ishe shi ba, a zafafe dr shureim Ya damƙi Strong Arm dinsa, a sukwane dr mark yai mashi wani kallo mai nuni da kashedi



"Sakar min hannuna! Karka kuskura ka bari na maimaita abunda nace"! Girgiza kai dr shureim yai duk da ya ɗan sha jinin jikin shi amma baya jin zai iya bari dr mark Ya koma kan gadon zeenatu da sunan zai mata Allura, ko ba dan kishinta da yake ba hakan bai dace ba kwata kwata


Hankalin Zeenatu ba karamin tashi yayi ba jikinta sai kerma ya ke yi kamar wadda sanyi ya kama cikin shesshekar kuka tace"yaya shureim ka ƙyale shi dan Allah, wlh idan daddy ya ji ka hana ya dubani ranshi zai 6aci, ni allurar ce bana so tun da akwai magani ya kyale ni in sha" idanunta sun kaɗa jawur



Wata irin zufar 6acin rai ce ta wanke fuskar dr shureim 

Ido cikin ido suke kallon kallo tsakanin su, Taurin kan dr shureim da kafiyarsa sunyi matuƙar daure mashi kay,  mutane da dama suna jin shakkar shi sai gashi yau Allah Ya hada shi da shureim 


"Yaya shureim na roƙe ka, ka sake shi, bana son tashin hankali" 


"Wallahi ba zaka dubata ba! Muddin ina numfashi, wannan wani irin yahudanci ne? Daga kai sai yarinya adaki saboda rashin ta ido har kan gadonta"?


 Dr mark ya gama hasala Har yayi wani yunkuri Zai kai mashi naushi Zeenatu tay saurin saukowa daga kan gadonta, ta faɗa tsakanin ta riqe dr shureim tana kuka.  


Da ace Zeenatu bata yi gaggawar raba tsakanin su ba, da Allah kadai yasan me dr mark zai yi mashi saboda ya fusata shi.



Sassauta fushin fuskarshi yayi, tare da kallon zeenatu da ta kankame shi, hankalin shi ya ɗan tashi da jin zafin jikin ta


Ganin mayen kallon da mark ke binta da shine yasa shi juyawa da zeenatu suka bashi baya.


Shu'umin murmushin gefen fuska ya saki tare da zaro wayar shi ya danna ma Alhaji musa Kira bugu uku Ya ɗaga.


"Sir, Wannan balaraben na gidan ka ya hana in duba lafiyarta saboda kawai Ya iske ni akan gadon ta ina kokarin yi mata allura shine ya rufe ni da faɗa yana gaya min magana mara daɗi" ya faɗa yana kallon bayan dr shureim, sarai yasan sunan shi amma saboda girman kai Ya kira shi da sunan balarabe


on the other hand Alhaji musa yace"Dr shureim Ya dawo gidan ne"?


"Yeah, shi nake magana akai, Yanzu haka muna adakinta"


"Okay, mark ka tafi kawai, i will call you later" ba don yaso ba ya amsa mashi da Okay"


duk suna sauraron shi abun da ya ƙara bata ma dr shureim rai jin ya fada ma alhaji musa yadda ya iske shi adakin batare da jin nauyin hakan ba, hakan na nufin dama ya saba zuwa dakin zeenatun ya hau gadon kuma da sanin Alhaji Musan.


Harara dr Mark Ya watsa ma bayan shi, tare da jan Tsoki ya fuce daga ɗakin.


Kusan atare suka sauke ajiyar zuciya, tallabo fuskarta yai da tafukan hannayen shi, idanunta amarairai ce ta kalle shi wani irin tausayinta ne ya kama shi, kumatunta sunyi ja, pink lips dinta sun kumbura daga gani ta jigata taji jiki ba kaɗan ba


"Me ke damunki"?


Muryarta da shagwa6a tace"ciwon ciki, daga fitowana daga wanka, na fara jin ciwon ciki yaya shureim nasha wahala kamar zan mutu har fadowa nayi daga kan gado, sai da Tani ta shigo ta iske ni kwance kasa ina murza cikina.. Shine ta kira daddyna awaya ta fada mashi shi kuma ya kira mark don ya dubani ni, ni kuma bana son allura"


Saurari Littafin >>>>Kurkukun Ƙaddara Takun farko  Kada a manta ayi mana subscribe like da kuma comment sannan a yi share. Domin samun sabbin littafi idan Mun ɗora.

Calmy yace"amma zeenatu why baki ce ya jira ki fito falo ba? Hakan ya dace ya shigo har dakin ki kan gado zai duba ki"? La66anta na kerma tace"yaya shureim ni banma san lokacin daya shigoba, ina kwance kawai na gan shi akaina, dama haka yake yi min in dai zaizo dubani baya tsayawa falo ɗaki yake shugowa, kuma daddy da mommy sun sani..."


 Girgiza kai yai sha'anin rayuwar gidan uncle nasa sai du'a i, yafi jin haushin Tani da ta kira Alhaji musa, sai kace mami bata agidan ay da ta sani ta tada ta daga baccin da duk hakan bata faru ba.


Ganin kamar damuwa akan fuskarshi yasa tace"ya shureim ranka ya 6aci ko"? Dakyar take magana saboda cikinta dake mata radadi, Girgixa mata kai yai"bakomai, ina maganin naki" da hannu ta nuna mashi kan mirror

Juyawa yai ya nufi closet dinta ya dauko mata abaya ya miƙa mata, hannunta na kerma ta kar6a tasaka a jikin ta.


"Kin ci abinci" 


"Bana jin yunwa ɗazu da safe na cika kina" 


"Okey, ki zauna ki jira ni"


make mashi kafada tay"dan Allah kada ka tafi kabarni ni kadai"


"Ba tafiya zanyi ba, ruwa zan dauko" amsa mashi tay da toh ta zauna gefen gadon tana jiran shi, badajimawa ba ya dawo hannun shi ruke da Cup din ruwa ya zauna ya taimaka mata tasha maganin ganin yadda hannunta ke kerma bayan ta kammala sha, yasa Yace ta kwanta ta huta, marairaice mashi fuska tay da shawaga6a tace"so kake inyi bacci donka tafi kabarni ko" 

Yanayin yadda takeyi mashi magana ba karamin kashe mashi jiki ya ke yi ba, ba zai juri kallon ta ba.


"Ba tafiya zanyi ba, zan koma falo," miƙewa tay"nima zanje falon"

"Pls ki kwanta ki huta, babu lafiya a jikinki"


Kuka ta saka mashi"haba ya shureim nagaji da zama ni kadai, ya kake so nayi da raina? nasan tafiya zakai kabarni..." lallashinta ya farayi"ya isa haka ki daina zubda hawayenki bana so, Idan saboda ni ne muje falon tare saiki kwanta kan sofa, in har hakan zai kwantar maki da hankali" ajiyar zuciya ta sauke ya zaro hanky daga aljihu ya share mata tears din fuskarta, ya ruƙo hannunta suka fito daga dakin


________________________________✍️


 A bangren su Aneeleerh har wuraren biyu na rana suna agidan, Sun Mori lokacin su tare da su Unaisah sallah kadai ta tadasu, sun sha fira da su kamar ƙawayansu, sun ɗebe masu kewa ba kadan ba, musamman Aneelerh taji dadi tayi farin cikin ganin yadda Junaid Ya saki Jiki da Unaisah in a short time su ka shaku da junan su, wasan doki suka dinga yi mashi ita da Batool, akan bayanta ta ɗaura shi ta dinga rarrafe tana zagaye sitting room din batare da gajiyawa ba, Sai murna yake yana fadin doki sukuta sukuta.


Aneelerh tasha ruwan mamaki Ganin Yadda Yake tiƙar dariyar, yaushe rabon da ta ga dariyar Junaid tun ranar da Ana ta 6ace ko murmushi bayayi ga ƙiwuya amma yau ya sake kamar bashi ba, har ta fara tunanin in suka koma gida zata lalla6a shi cikin lallami ta tambaye shi meya faru da ana  aranar watakil ya fada mata tun da taga bakin shi ya buɗe.

Saurari Littafin >>>>Kurkukun Ƙaddara Takun farko  Kada a manta ayi mana subscribe like da kuma comment sannan a yi share. Domin samun sabbin littafi idan Mun ɗora.


har video Benazir ta ɗauke su da wayarta saboda sun burgeta taji daɗin walwalwar da su ke yi cikin nishaɗi bayan sun gama yi mashi wasan dokin, Unaisah ta daure idanunta da mayafinta ta dinga zagaye dakin tana neman su, Batool taja hannun junaid suka dinga garata sai da suka wahalar da ita dakyar ta cafko baby junaid ya dinga ihu Yana tsalle yace mata shima ta ɗaure mashi ido yayi wasan, ta cire mayafin ta ɗaure mashi idanunshi yadda bazai ji zafi ba, kamar makaho haka ya rinƙa miƙa hannu ya na laluban su da gangan Unaisah ta je gaban shi ta tsaya don kada su wahalar da shi, cafko rigarta yai da hannayen shi ya ƙankameta yana fadin ya kama ya kama.


Duba agoga Aneelerh tayi kafin ta kalli Benazir"yakamata mu tafi, kada mami taji na dade" sai lokacin Benazir tace"yanzu abun hawa zamu hau mu koma? nasan ko na kira dr shureim ba lallai yazo ba saboda rashin lafiyar zeenatu..." ta fada tare da ta6e baki


Murmushi Aneelerh tay saboda ta gano me take mawa


"Pls ki kira mijina ya maida mu gidajen mu" cike da zolaya tace"ki dai iya bakinki, Kada babyn naki taji kina kiran sunan ubanta da sunan mijinki, Yanzu ki tada mana 6alli" murmushi Benazir tay tare da kallon su Unaisah dake a zaune kan rug sun gaji da wasan hutawa suke.


Waya ta curo ta danna ma Taj kira tana fara ringing yai picking, 

Tunkafin tay magana Yace"Aneelerh ykk ya su Unaisah, Ina fata kunji dadin kasancewa da su" 

"Alhamdulillah, gasu nan zaune sun gama shan wasa da baby junaid, shima yau yaji dadin ganin yar uwarsa" 

ta fada tana kallon su 


"Masha Allah, Naji dadin jin hakan, Yanzu nake kokarin, kiranki,yakamata su koma yan uwansu sun fara neman su"


"Allah sarki, Nima abun da yasa na kiraka kenan, mun shirya tafiya kuma dr shureim bayanan Ya tafi ɗasu aka kira shi daga gida har yanzu bai dawo ba, mun kira layin shi baya shiga" ta faɗa tana kallon Benazir data tsare ta da ido fatanta Allah yasa ya amince yazo ya dauke su.


Shiru yayi jimm na ɗan wani lokacin kafin yace"Okay, Naso na maida ku gida amma bana a kusa, zansa jami'en mu ya kai ku" haɗe fuska Benazir tay tuni idanunta suka ciko tab da kwalla, gani take kamar ya ɗago su ne shiyasa yace zai turo jami'en su ya kaisu amaimakon shi


"Shikenan, Mun gode ssai," tay mashi sallama, 


Kallon juna su ka yi ita da Benazir


"Nasan saboda ni ne yace bazai maida mu ba" ruko hannun ta Aneelerh tay"pls ki yi hakuri kamar yadda na fada maki, bana so yaran nan su fahimci wani abu kwara mu rabu lafiya, ki daure idan muka shiga mota zamuyi magana, nayi maki alkawarin zan taimaka maki mu shawo kan shi"


 A hankali Benazir ta share hawayen ta, har ga Allah bata son tafiya tabar gidan ji take kamar su kwana anan sai dai tasan ba abune mai yiwuwa ba.


Suna azaune jami'en da taj ya turo yayi masu sallama Yace su fito Yana jiran su.


Hankalin Unaisah ba karamin tashi yayi ba ganin za'a rabata da baby junaid, bawan Allah sai ƙara kankameta ya ke yi duk don kada su raba shi da ita,  bayan sun fito abakin motar suka tsaya, Aneeleeh ta kar6i junaid yana kukan rabuwa da Angel tace mashi yai hakuri za ta zo har gida ta same shi, dakyar tayi mashi wayau ya hakura.


"Toh Mu zamu wuce, zamu tafi mu bar ku da kewar mu" Anila ta fada tana kallon su, duk sun ɗaure fuska saboda basu son su tafi


Saurari Littafin >>>>Kurkukun Ƙaddara Takun farko  Kada a manta ayi mana subscribe like da kuma comment sannan a yi share. Domin samun sabbin littafi idan Mun ɗora.


"Dan Allah yaushe zaku dawo"? Cikin sanyin murya batool ta yi maganar, Benazir tace"in dai mune kusha kuruminku, har sai kun gaji da ganinmu" dadine ya lullu6e su, miƙa masu hannu tay da sauri suka matsa kusa da ita ta haɗa su duka ta rungume su, Cikin kunne ta yi ma Unaisah raɗa"zan kar6i contact dinki a gurin Aneelerh, Ki kula min da kanki, Ina kaunarki sosai" murmushi unaisah tasaki"nima zanyi kewarki mommyna"


Bayan sun raba jikin su daga na juna ta dubi Batool ta shafa gefen fuskarta da tafin hannun ta


"zanyi kewarki, Yau na fara ganinki amma kin kwanta min araina, kamar yadda Babyna ta sace zuciyata, Ina kaunarki, Ki kula min da kanki" dariyar farin ciki batool tayi"in sha Allah, nagode sosai aunty Benazir, nima ina sonki, " taso ta tambaye su dr shureim amma saita kasa saboda kunyarta da take ji.


Miƙa masu hannu Aneelerh tay, itama tay hugging dinsu baby junaid ya haɗe rai Idanunshi sun ciko tab da kwalla.


Sumbatar kumatun shi Unaisah tay, cikin sigar lallashi tace"I'm sorry my little bro,  Zanzo har gidan ku, Aunty aneelerh pls ki kwantar masa da hankali bana so yayi kukan rashi na" ta fada tana kallon fuskar junaid


"Kada ki damu bazan bari yai kuka ba, ku gaida mana mutanan gidan" atare suka amsa masu da toh


Akan idonsu Motar su ta fuce daga gidan, fitar su keda wuya Ummi ta fito daga kofar falon har bayan motar saida ta gani yayin da take karasa fucewa daga gate din

Sun yi tsaye cike da jimamin tafiyar su, baby junaid Ya tsaya masu aransu.


Kwata kwata basu lura da ummi ba har saida ta ambaci sunayen su da sauri suka dube ta 


"Daga ina kuke? Motar waye naga ta fita yanzu? Kallon ta su ka yi ba tare da sun furta kalma ba


"Ba ku ji Ina magana bane"?


Ajiyar zuciya suka sauke atare Unaisah tace"bamu san motar wanane ba,  muma yanzu muka fito"


"Daga ina"? Kallon juna su ka yi

"Kamar baku da gaskiya, ku fada min mana daga ina kuke" ta fada tana jifansu da kallon tuhuma.


"Mun je part din daddyna ne, daga can muke" ba dan ta yarda da su ba tace"shine ko ku fadamin ay dana shirya mun je tare, gaskiya baku kyauta min ba" ta fada tana jifar su da harara dariya sukai atare.. 


"Ku wuce mu shiga ciki," gaba tay suka bi bayan ta hannun su ruke cikin na juna 




*💋BOSS BATURE✊*





Da marece tana a zaune gaban mirror chair tana yin wani makeup ɗin akan fuskarta, saboda kwalliyar da ta yi ɗazu ta goge.


 gown ɗin ɗazu ce a jikinta da alama bata gama gayun ba, ko kuma wanda akayi dominsa bai gani ba, ita kaɗai ce a ɗakin, sai ƴan shafe shafe take ma fuskarta, cikin ƙanƙanin lokaci ta gama tayi matuƙar yin kyau, ta nutsu tana kallon fuskarta ta cikin mirror, pink lips dinta sun jiƙu da lip gloss sai shinning su ke.


Knocking ɗin kofar da akai ne Yasa ta ɗan juya ta kalli room door ɗin su.


Jemimah ce ta shigo jikinta sanye da Overall, ta ɗaure  blonde hair ɗinta da ribbon ta fito ɗass Farar fatar ta gwanin sha'awa.


"Little Sis halan dalili ne Ya shigo dake dakin mu"?


Ta faɗi hakanne don tasan bai wuci chocolate tazo roƙo a gurin ta ba.


murmushi tayi"Aunty ummi ce tace In kiraki, kizo mu yi dinner, in ba zaki ci ba sai mu cinye naki" dariya Unaisah tay"su acici mala'ikun tauna, Ku da baku gajiya da Cin abinci, Har wani fadi kike zaku cinye abinci na ai ko dana karanta maku Charman dudu cikin kowa ya kumbure"


waro idanu Jemaimah tay"Wlh wasa nake maki fa" miƙewa Unaisha tay daga kan chair din"oho in ma dagaske ne bismillah, ku ci ku ga abun da zai biyo baya"


Saurari Littafin >>>>Kurkukun Ƙaddara Takun farko  Kada a manta ayi mana subscribe like da kuma comment sannan a yi share. Domin samun sabbin littafi idan Mun ɗora.

Veil ɗinta dake ajiye kan bed ta dauka ta yafa akan kafadarta, ta koma gaban mirror  ta dauki turare ta fashe jikin ta da shi.


"Sis Unaisah Kin yi kyau wallahi" 


"Thank you, ki tafi ki ce masu su jirani Yanzu zan fito"


Maƙe kafada Jemimah tay"wlh ba inda zanje, so kike muje muyi ta jiran ki kiqi fitowa yawun mu yai ta tsinkewa ko"?


Girgiza kai Unaisah ta yi ba tare da ta tanka mata ba


"Kamar dole saida ni zaku ci, kullum sai anzo kirana"



Kafin ta ankare Jemimah ta buɗe drawer chest, Ta Saci Chocotes biyu ta tura a aljihun rigarta.


"Sis Unaisah mu tafi pls, suna jiran mu" 


"Kada ki takura min pls" ta faɗa tare da juyawa ta nufi shoe rack ta ɗauko wasu hadaddun cone heel ta zura a ƙafafunta.


"Aunty Ummi tace Ki ɗauko mata wannan abun jin kiɗan zata kunna  mana music"


Girgiza kay tay"Aunty ummi ta iya Taya beraye 6anna" ta faɗa tare da nufar inda ta ajiye bluetooth speaker din ta ɗaukota a hannu tace ma jemaimah mu tafi 


Adaidai lokacin da suka fito daga dakin Danish yana atsaye gaban handrail din bene jikinshi sanye da kaftan maroon colour, muryar jemimah ce taja hankalin shi ga kallon su bai sauke idanunshi akan kowa ba sai kan Unaisah, wankan data ɗauka yayi matuƙar ƙayatar da shi, musamman data ju ya baya tana ta fi ya, kwata kwata basu lura da mutun ba, kuma ba su ji ajikin su ana kallon su ba.


Tun kafin su karasa Dining din, Ta hango Su gaba ɗayan su sun hallara A zazzaune kan dining chairs, an cika masu table din da lafiyayyan abinci.


Tana shigowa sautin takalmanta Ya karaɗe kunnuwansu, kusan atare suka ɗago suna kallonta kamar sun samu tv, kwalliyarta tayi masu kyau Nan fa suka fara Santi suna yaba kyan da tayi.


 Ummi tace"lallai yau ƴan matanci ake ji, faɗa min wa kikayi ma kwalliyar nan" farfari tay mata da idanu"Someone special" ta fada da zolaya


sajeed yace"Zan Iya cankan wanene"? Ɗaga mashi gira tay murmushi yayi kafin Ya firta


 "Chief" waro idanu waje su ka yi gaba dayan su, Praveen tace"baka da hankali Sajeed, chief dinne zata ma kwalliya, Mutumin da ko kallon mutane ma bayayi.


Ummi tace"ba abun mamaki bane, Ni dama na fara tunanin akwai wani abu tsakanin su, shiyasa ran nan yaje dake shopping mall ya yi maki siyayya..." ɗaure fuska Unaisah tay"kai aunty ummi, saboda inyi tsaraba yayi min siyayyan ba dan wani abu ba" ta faɗa tare da miƙa mata speaker ɗin hannunta, kar6a ummi tayi ta kunna ta kafin ta ajiye ta under chair ɗin da take a zaune, ta zaro wayarta daga aljuhun rigarta, tayi connecting ɗinta da speaker din.


sai daɗi suke ji za'a kunna masu music, kallon su Unaisah tay sun cika dogon table din ba space, Shima ɗayan mai mazaunin mutun shida babu space, sai ɗayan dining table ɗin daya rage mai mazaunin mutun Uku Javed yana zaune kan ɗaya daga cikin kujerun dake a kewaye da shi, anan ta samu guri ta zauna.


"Ku fara Cin abincin mana" ummi ce tay maganar.


Sajeed yace'wai da jira muke ki fara kunna mana music ɗin, zaifi armashi muna ci muna sauraro" ummi tace"na lura dakai mayen kiɗa da rawa ne, wa ya koya maka ne, cos ka fita daban ko acikin yan uwanka"



 Murmushi yayi batare daya ce mata komai ba, don bazai Iya tuna komai ba dangane da yadda Ya iya rawa ya dai san abun a jinin shi yake.



"Wata waƙa zan sanya mana"? Ta tambaya tana kallon su, 


Har suna haɗa baki gurin faɗin baby calm down, dama itace wakar da suka fi sani.


bayan Ta kunna masu wakar suka fara cin abincin suna gyaɗa kawunansu, wasu daga cikin su har wakar suke bi kamar su suka rairata saboda yadda suka Iya bin baitikan tiryan tiryan ba kuskure.


Saurari Littafin >>>>Kurkukun Ƙaddara Takun farko  Kada a manta ayi mana subscribe like da kuma comment sannan a yi share. Domin samun sabbin littafi idan Mun ɗora.

babu wanda Ya lura da shigowar shi, abakin kofar dining room ɗin ya tsaya yana kallon su ɗaya bayan ɗaya, ba zai iya tuna rana ta karshe daya shigo dining ɗin da sunan zaici abinci ba, Sai yau da dalili ya kawo shi.


"Danish"! da ƙarfi Haris Ya ambaci sunan shi, bai tsammaci wani zai gan shi ba, adaidai lokacin da wakar da suke sauraro ta ƙare hakan Yasan duk suka ji Kiran da Haris yayi mashi, da sauri suka kalli Inda yake atsaye da alamun mamaki akan fuskokin su.



Kusan kowan nan su saida Ya ambaci sunan shi, In ka cire Unaisah da tay shiru tana kallon shi


Ummi tace"Sannu da shigowa, ina fata kazo kaci abinci tare da mu ne" shiru yai bai tanka mata ba, 


"Pls danish kazo muci dinner atare, Munyi missing ɗinka" Batool ce tay maganar,

Naufal Yace"Yau kawai dan Allah, baka ga dadin da muka ji ba na ganinka"! 


gaba daya suka haɗa baki suna yi mashi magiya don ya shigo su ci abincin atare. 


"Dama kun daina wahalar da bakunan ku, Idan so kuke Yaci cikin sauƙi, Unaisah zaku roƙa ba shi ba"  


Sajeed ne yai maganar fuskar shi da murmushi, gaba ɗaya suka maida dubansu Ga Unaisah"pls Kiyi mashi magana, ya shigo muci atare" kau da ido tay gefe ɗaya tay shiru bata tanka ma su ba tayi mamakin maganar sajeed ko taya akai ya gane baya  jin maganar kowa in ba nata ba.



"Aunty Ummi ki sa baki, Ta yi mashi magana" duƙar dakai ƙasa Unaisah ta yi, girman kanta Ya hana ta yi masu abunda suke so, ita kanta so take ya shigo ya zauna suci abincin atare amma bata jin zata iya yi mashi magana.


Calmly ummi tace"Unaisah, pls ki masa magana mana, Ƴan uwansa suna son suci abinci da shi.." 


 sai da ta mula ta sha iska, kafin ta wurga eye balls dinta kan Danish kamar me jin shakkarta, tasan saboda ita ne yaki shigowa gudun kada ya sabama sharuddan ta, ba ta yi niyar yi masa magana ba amma saboda batasan su fahimci sun samu sabani atsakaninsu yasa ta canza ra'ayin ta.


Har Ya juya zai fuce, sanyayyar muryarta ta dakatar da shi


"Big bro, ka zo mu ci abinci atare" a wayance ta faɗa tana kallon shi


har saida ya maimaita sunan data kira shi acikin zuciyarsa


"Ga wuri Na tanadar maka" ta faɗa tana nuna Kujerar dake facing ɗin ta.


baiyi niyar zama ba, amma saboda muradin ransa tayi mashi magana, Ya fasa tafiya Ya jiyo ya shiga cikin dining room ɗin, yan uwansu sai murmushi su ke yi saboda sunji dadin shigowar shi.


Ummi dai ta yi mamakin shakuwar dake atsakanin shi da Unaisah, aranta ta ayyana ko meyasa yake jin maganarta fiye da kowa! Yafi fifita ta akan yan uwansa tana lura da shi, abun da ta fahimta itama Unaisah din tafi ji da shi akan yan uwan shi, don tana lura da ita lokacin da ta ke ji da shi, duk in zasu ci abinci sai tace ma Haris ya kaima Danish nashi aɗaki bayan haka wasu lokuttan tana ganin Unaisah tana satar hanya ta shiga dakin shi, tabbas tana son tasan meke atsakanin su amma tasan ko da ta tambayi Unaisah zaiyi wuya ta faɗa mata gaskiya, aranta ta ayyana yanzun nan zan gano da kaina.


Saurari Littafin >>>>Kurkukun Ƙaddara Takun farko  Kada a manta ayi mana subscribe like da kuma comment sannan a yi share. Domin samun sabbin littafi idan Mun ɗora.

Zama yai kan chair din dake fuskantar Unaisah, ya jingina bayan shi jikin kujerar, ya ɗan lumshe idanunshi ba tare daya kalle ta ba, don baya son abin da zai ja ya karya alkawarin daya ɗaukar mata.


Sun yi shiru babu mai magana a cikin su.


Har saida ummi tace"me kuke Jira Unaisah? Ku fara cin abincin mana" A hankali ta ɗan saci kallon fuskar shi Har saida ta ɗanji faɗuwar gaba saboda kyan da yayi mata, tayi missing din ganin shi a kusa da ita.


a hankali take cigaba da kallon shi ganin ya lumshe idanun shi tasan ba lallai ya buɗe su ba, aranta ta ayyana wani irin kyau ne wannan kullum kamar ana ƙara mashi..."


gudun kada wani ya zargi wani abu tsakanin su yasa ta ɗauki glass of milkshake ta tura mashi agaban shi, ta haɗa mashi da plate of grilled steak with roasted vegetables ta aje agaban shi.


Cikin sanyin murya tamkar tame yin raɗa ta firta sunan shi, A tsanake ya buɗe reddish eyes dinsa dake lumshewa tamkar na mai jin bacci ya kalle ta da su, gaba ɗaya suka tsinci kansu da kallon juna ba tare da kyaftawa ba ya rasa a ina zai tsayar da eye balls dinsa, lip gloss din data shafa ma soft lips ɗinta ba karamin rikitan shi yake ba.


makeup din fuskarta ya tafi da imaninsa, kamar yadda yake kallonta haka itama take bin shi da kallo, tun daga kan dogan wuyansa ta fara har iya zuwa soft lips din sa a hankali tay moving eye balls dinta zuwa ga dogon han cin shi wani irin yanayi take ji ajikin ta mara misaltuwa, sam takasa ta6uka komai, Javed dake akusa da su baisan wainar da suke toya ba hankalin shi na akan abincin da yake ci.


Babu wanda Ya lura da su sai ummi da ta sanya masu ido duk wani motsinsu akan idanunta 


 Yawu ta haɗiya tana ƙoƙarin kau da ido daga kallon shi, ba zato ba tsammani sautin daddadan kiɗa Ya karaɗe kunnuwan su taken waƙar Ko wuya ko dadi adai dai inda baifin Ya fara da 


Ko wuya ko dadi

Ni dake ba zamu rabe ba

Ka zamo ni na zama kai

Ba ranar rabuwa

Ko wuya ko dadi

Ni dake ba zamu rabe ba

Saurari Littafin >>>>Kurkukun Ƙaddara Takun farko  Kada a manta ayi mana subscribe like da kuma comment sannan a yi share. Domin samun sabbin littafi idan Mun ɗora.

Ka zamo ni na zama kai

Ba ranar rabuwa..


gaba ɗaya jikinsu Ya mutu, wata irin kasalace ta mamaye sassan jikinsu, hatta yanayin bugun zuciyar su saida Ya canza.


Kasa ƙarasa cin abincin ta yi A hankali Ta jingina bayanta jikin kujerar batare da ta daina kallon shi ba, waƙar ba karamin shagalar da su tayi ba, sun shagala da kallon juna, sun kasa ta6uka komai, kowa na cin abinci ban da su..."


Cigaba waka tay sun nutsu suna sauraran baitin


Dani dake soyayya ta ginu

A zuciya ta ke na saka kin sanu

Kice dani kin barni na banu

Shine kadai zai sanya ayi mini duren kunu

Kiji ni dai zama dake daram dam-dam

Na rike ki ta kam kam-kam

Makiyan mu suje chan

Banda son ki bansan komai ba...


Lumshe idanunta ta yi a hankali ta dan numfasa ba tare da buɗe idanun ba, wani irin bakon abu take ji a jikin ta, mara misaltuwa, sai taji tamkar saboda su aka yi waƙar saboda yadda wakar take shigarta.


yatsun hannunta sai kerma suke, gaba ɗaya ta shiga yanayi ba zata iya jurar cigaba da kallon shi ba.


Danish dake kallonta wata irin nutsuwa ce ke shigar shi, musamman data rufe idanunta hakan ya bashi damar kallon ta son ran shi, farar fatar dogon wuyanta yabi da kallo Silver necklace ɗin data sanya tayi matuƙar ƙawata wuyanta, moving eyes dinsa yai slowly izuwa kan kirjin ta sam ta manta bata ɗaure boobs ɗinta ta ciki ba kamar yadda ta sa6a, yau yaga abun da take boye mashi, duk da ƙarantar su nipples dinta ba karamin girma ne da su ba.

hannun shi na dan kerma ya dauki milkshake din data ajiye mashi ya fara shan shi ba dan yana jin dadin shi ba, saboda kallonta da ya ke yi yafi mashi komai.



Saurari Littafin >>>>Kurkukun Ƙaddara Takun farko  Kada a manta ayi mana subscribe like da kuma comment sannan a yi share. Domin samun sabbin littafi idan Mun ɗora.

baitin Wakar ne Ya ƙara rikirkita tunanin shi ya ɗan runtse idanun shi yana sauraron daddadar muryar da kunnuwan shi ke jiyo mashi sai yaji kamar Angel dinsa ce ke raira mashi ita.


Na rike ka hannu biyu baby na

Kai kazam fitila annuri na

Ko ana fizgemin nama na

Zan yabe ka da karfin harshe na

Sai da kai

Ba ya kai

Ka sarkafe mini a zuciya ta

Ba ya kai


Ummi tasan takan tsiya, dagangan take maimaita wakar saboda ta ƙara rikitar da su, yau taga abun da Ya ɗaure mata kai, tun daga kan yanayinsu ta fahimci irin tsantsar kaunar da suke ma junan su, don ita abun da tagani ma ya wuce A kira shi da so hada shaukin junansu da suke ji, yar wakar da ta kunna masu kadai ta jefa su awani hali dama da biyu ta kunna ta



Kasa jurewa yayi da wata irin kasala Ya miƙe zai bar dining din gudun kada yayi wani abu ba dai dai ba da zaisa su sake samun sabani da ita, da sauri ummi ta dakatar da wakar ta dube shi.


"Danish Ina zakaje? Naga ko abincin baka fara ci ba" tamkar baisan furta magana yace"bana jin yunwa" marairaice mashi fuska su Haris sukayi"pls danish, kada ka tafi ka zauna ka ci abinci" girgiza kai yai, Shi kadai yasan me yake ji ajikin shi, In har ya cigaba da zama Yana kallon Unaisah komai zai iya faruwa a yanzu haka jikin shi sharkaf Yake Ga gumi da ya wanke shi duk da sanyin a.c din dake a dining room din, su basu lura ba amma ita Ummi tasan me yake ji a wayance tace"ko dai kana da uziri ne"? ya ɗaga mata kai alamar eh.



Shu'umun murmushi Tasaki Okay, Muna jiranka idan ka gama uzirin naka, ka dawo kaci abincin" bai kula ta ba Ya fuce daga dinning din ba don ya gaji da zaman shi ba, sai don bayason yaja ma kan shi bala'e.   



Fitarshi keda wuya Unaisah ta buɗe idanunta da suka kaɗa jawur da su, ga wani zafi da temperature din jikinta ya dauka kamar mai fama da zazzabi.


ta rasa gane meke mata dadi, fitar Danish daga ɗakin yasa taji batasan cin komai, mineral water kadai ta sha ta miƙe jikinta na tsuma ta nufi hanyar fita daga dakin muryar aunty Ummi ta katse ta"Wai lafiya? Shi ya fita baici komai ba, kema kin miƙe zaki fita? Meke damunku ne"? Ta tambaya kamar batasan meke wakana ba.


Yamutsa fuska Unaisah tay tare da kallon Ummi datay maganar

"Wayata zan dauko adaki, yanzu zan dawo" ta fadi hakanne don kada su zargi wani abu.


kumshe dariya ummi ta yi abakinta, tana lura da yadda jikinta ke tsuma.


"Okay, muna jiranki" fucewa tayi daga dining din tana tafiya da nawa kamar wadda kwai ya fashe mawa, tana shiga dakin su ta faɗa toilet taja ƙofa ta datse, zama tay akan toilet seat tayi shiru tana tariyo abunda ya faru a dining room.


Ta rasa gane dalilin dayasa take tsintar kanta awani yanayi duk idan tagan shi ko taji muryarshi! Batasan menene ba, ta kasa ganewa.


bata gama zancen zucin ba, zatayi tsarkin fitsarin da tayi taga wannan farin ruwan mai yauƙi wani irin kyankyami da kyamane suka kamata, da sauri tayi tsarkin ta fito ta tsaya abakin kofar toilet tana faman sauke ajiyar zuciya, bayanin aunty Umminsu ta fara tariyowa a lokacin da take faɗa mata dalilin dake kawo shi, abun da ya daure mata kai kallon juna kawai sukayi ba wani abu ba amma sai gashi ta gan shi, dole ta nemi ƙarin bayani agurin Aunty ummin su.


Saurari Littafin >>>>Kurkukun Ƙaddara Takun farko  Kada a manta ayi mana subscribe like da kuma comment sannan a yi share. Domin samun sabbin littafi idan Mun ɗora.

ga yunwa tana ji sai dai bata jin zata iya komawa dining room din, faɗawa tayi kan bedmattress ta janyo pillow ta rungume shi a kirjinta, wani sanyine ke ratsa zuciyarta, ga wani dadi da take ji a jikin ta.


ta shafe tsawon mintuna shabiyar a kwance ba tare data motsa ba.



"Sister, Aunty Ummi tace kizo wai" muryar hawwa ce ta katse mata zancen zucin ta, ba tare da ta bude idanunta ba tace"okay, gani nan zuwa" bayan fitar hawwa daga dakin ta sauko daga kan gadon ta, ta gyara mayafinta, tana ƙokarin fitowa daga dakin kamar daga sama taji Sallamar Salsabeel da sauri ta juya ta dubi kofar falon, a tsaye yake ya ɗauki wankan shadda kamar ba shi ba, hannun shi ruƙe da trolley, kwata kwata bai lura da ita ba.



"Yaya salsabeel," muryar ta ce ta fargar da shi, murmushi yayi tare da nufarta yana jan trolley ɗin.



"Unaisah ykk"



da fara'a tace"lafiyalou, ya salsabeel kwana biyu baka leko mu ba, munyi fushi" 


ta fada tana haɗe fuska yar dariya yayi"i'm really sorry, wlh kuna araina, yanzu hakama da kika ganni saboda ku nazo"



 Miƙa mashi hannu tayi"kawo na ruƙe maka trolly din" miƙa mata yai tasa hannu ta ruƙe handle din"Menene aciki? Ko kayanka ne"? Girgiza kai yai" mu karasa ciki, zan nuna maki abunda ke a cikin shi" amsa mashi tayi da toh suka nufi cikin falon akan sofa Ya zauna, Ta aje trolley din agaban shi Yace mata ta kira sauran yan uwanta ya faɗa yana hangen su a dining room suna cin abinci sam basu lura da shi ba, da sauri ta juya ta nufi dining room din ta shiga ta kira su, tun da suka ji ta ambaci ya salsabeel ya zo kowa ya ajiye spoon din hannun shi, Cike da zumudin son ganin shi suka fito daga dakin su dukan su hada Ummi.


Kafin su karaso ya mike fuskanshi dauke da fara'a ya gaishe da ummi ta amsa mashi da fara'arta,  kallon su Haris yayi daya bayan ɗaya aranshi yana tariyo lokacin da suke a prison, rayuwa ta canza sun wadatu da kwanciyar hankali



Hannu ya miƙa ma mazan sukayi musaba, Ya dubi Yan matan dake ta faman hade rai

Dariya yayi"fushi kuke dani"? Khadeeja tace"eh mana, tun yaushe rabon da kazo gurin mu, ka manta damu.."

Mubeen Yace"kullum sai munsa ran zuwanka amma saika ki zuwa"

gaba daya suka rufe shi da korafe korafen su dakyar Ya samu ya shawo kan su, har suka hakura da fushin da sukeyi da shi bayan sun gama gaisawa da junansu yace su zauna zasuyi magana mai muhimman ci.


Bayan Kowan nan su Ya samu guri Ya zauna kan Sofas suka nutsu suna jiran jin me zaice masu.


"Ya salsabeel, Wannan akwatin fa? Ko tsaraba ne ka kawo mana" parveen ce tay maganar tare da nuna akwatin da hannu


"Eh tsaraba ce amma bata abun ci ba, Kayan sawa ne" kallon juna su kayi da mamaki akan fuskokin su.


"Ina Danish"? Ya tambaya yana kallon su


"Yana a daki" suka haɗa baki gurin bashi amsa"


Yace"okay, wani ya kira min shi" Haris ne Ya mike da sauri Ya je kiran shi.


falon yayi tsit baka jin hayaniyar komai, duk sun ƙagara da son ganin menene acikin trolly din me kuma ya Salsabeel zai fada masu mai mahimman ci'? 


Jim kaɗan saiga Haris Ya dawo tare da Danish, Har ya canza kayan jikin shi yanzu silk pyjama ne a jikin shi na bacci.


Tun shigowarsu Falon, Unaisah take satar kallon shi, bayan sun rungume juna da salsabeel a amutunce suka gaisa da junan su kafin daga bisani kowan nan su Ya zauna suka nutsu suna kallon salsabeel


Saurari Littafin >>>>Kurkukun Ƙaddara Takun farko  Kada a manta ayi mana subscribe like da kuma comment sannan a yi share. Domin samun sabbin littafi idan Mun ɗora.

"Mu farayiwa Annabi salati" suka amsa mashi da toh, bayan sun gama yayi shiru yana binsu da kallo ɗaya bayan ɗaya kamar mai nazarin wani abu, Azeeza da Jemimah sai faman kumshe dariya su ke yi kamar wasu zautattu.



Ɗaya bayan ɗaya ya fara kiran sunayen su, duk wanda ya kira sunan shi sai ya amsa mashi da Na'am, ummi dai tayi shiru tana jiran jin me zaice ma su


Numfasawa yayi kafin ya fara magana cikin nutsuwa


"Gobe Idan Allah Ya kaimu da rai da lafiya, za'a tafi daku Isod headquarter...." 


Kallon juna su ka yi arude suka maimaita sunan Headquarter, Sajeed Yace"me za mu yi acan ɗin"? Da alama sun ruɗe, murmushi Salsabeel yayi kafin yace"zaku gana da manyan jami'an Isod" Hankali tashe Unaisah tace"mu ɗin"? Jinjina mata kai yayi"kwarai kuwa, Lokaci yayi da zasu gana da ku, don suji daga bakin ku, Suna bukatar bayani game da rayuwarku a gidan kurkukun ƙaddara, zasuyi maku tambayoyi da suka shafi rayuwar da kukai agidan kurkukun ƙaddara da kuma shi kanshi gidan kurkukun"


 Ya fada yana duban fuskokin su sunyi shiru suna sauraronshi kowa da abunda yaƙe sakawa aranshi.



"Nazo ne don in ƙarfafa maku gwiwa, nasan akwai masu jin tsoro har yanzu acikin ku, to inaso ku aje tsoron nan gefe ɗaya da duk wani shakku da zakuji, yanzu lokaci ne da zaku bada gudummuwa ku taimaka masu gurin kawo karshen kurkukun kaddara, bayanan da zaku basu da su zasuyi amfani wurin yin binciken waɗanda suka azabtar da rayuwar ku, kada ku 6oye masu komai, duk mun ƙanƙantar abu da kuka sani ku faɗa masu zai iya zama mai amfani agare su" 



tun da salsabeel ya fara magana Danish Ya rufe idanunshi gam kamar baya atare da su, sarai salsabeel Ya lura da yanayin shi.



"Ku faɗa masu irin kuncin rayuwar da kukayi, Ku faɗamasu azabtarwar da sukayi maku da kuma wulakanta rayuwarku da su ka yi, ku kaɗai kuka san meya faru arayuwarku, tunkafin ku mallaki hankalinku kuke a kulle ba shige ba fuce, idan har kuka 6oye wani abu baku fada ma su ba, kanku zaku cuta, kwara ku tona masu asiri don uban su kowa yasan me suke aikatawa" ya faɗa tare da bugun sofa din da yake zaune akai da hannun shi.


"ku daina ganin ayanzu kun tsira kun samu rayuwar ƴanci wallahi har yanzu rayuwar ku tana acikin haɗari saboda ba zasu ƙyale ku ba, suna nan suna bibiyar rayuwarku don su salwantar daku saboda kune prisoners na farko da suka fara karya dokar kurkukun kaddara, tayaya ku ke tunanin zasu ƙyale ku? Ay ko dan kada ku tona masu asiri dole su nemi hanyar da zasu shafe babin ku"



 Maganar salsabeel ta ɗaga hankulansu, Tuni ido ya raina fata, wasu daga cikinsu har sun fara sharar kwalla,


ya faɗa masu hakanne don Ya tsoratar da su ya kuma tunzura su don su fusata su samu kwarin giwar tona masu asiri idan jami'an sirrin suka tambaye su.


"Ko ba don saboda ku ba, Ku tuna ƴan uwanku da kuka bari agidan kurkukun ƙaddara! Waɗanda basu ji ba basu gani ba kamar ku dai, suna can ana azabtar da rayuwarsu, Sun maida su kamar dabbobi sai azabtar da su sukeyi, meye ribarku idan ku kun samu jin dadin rayuwa su kuma suna awahala? Baku da burin ku dauki fansar abunda akayi maku? Sannan ku cecei rayuwar yan uwanku? Za ku ja baki ne kuyi shiru acigaba da salwantar da rayuwar kananun yara da basu ji ba basu gani ba"? Ranshi a6ace yayi maganar yana kallon su, Jiki asanyaye sajeed Ya sauko daga kan sofa, Ya dawo ƙasa ya zauna hannayen shi biyu tallabe da kan shi, Idanunshi sun ciko tab da kwalla.


Saurari Littafin >>>>Kurkukun Ƙaddara Takun farko  Kada a manta ayi mana subscribe like da kuma comment sannan a yi share. Domin samun sabbin littafi idan Mun ɗora.

Shesshekar kukan su ne Ya cika falon, kalaman salsabeel sun fama raunin dake acikin zuciyar su..." 


Salsabeel bai dakata ba saida ya tabbatar sun fusata sun harzuka kafin ya tsagaita da yin maganar Yana jiran jin me zasu ce.


Cikin shesshekar kuka sajeed yace"wallahi ko ba ka fada mana ba, ba zamu raga masu ba, ni ashirya nake da duk wata tambaya da za'ayi min, nayi alkawarin zan fadi iya abunda nasani saboda nima twin sister dina tana can, bana so su kashe min yar uwata duk da bani da tabbacin tana araye kota mutu...." kuka ne Yaci karfinshi, Ya kifa kanshi saman  sofa.


Wani irin tausayin su ne Ya kama Ummi, Tuni taji hawaye sun cika idanunta, lamarin rayuwar yaran tana matuƙar tada mata hankali, har yau tana jin labarin su tamkar a mafarki saboda abun yafi karfin tunaninta.



Fashewa jemimah tayi da kuka tana fadin


"nima wlh saina tona masu asiri, mugaye azzalumai kawai, hadama wannan tsohuwar data kusa kashe mu nida su Azeeza, Inaji ina gani majnoon dina ya mutu, wlh saina daukar mashi fansa, koda zan rasa raina ne..." rai a6ace tay maganar, idanunta sunyi jawur ga ruwan hawaye dake zarya kan kuncin ta,


dafe kai Deeja tayi da hannunta tamkar zata fasa masu ihu, idanunta sun rune zuwa ja, kwata kwata bata son jin maganganun da su ke yi,


miƙewa tayi da sauri ta fuce daga falon, duk suka bi bayanta da kallo babu wanda yayi yunkurin dakatar da ita.


"Bazan ta6a manta irin azabtarwar da sukayi mana ba, wallahi rantsuwar ɗan musulmi ba gudu ba ja da baya sai mun fallasa su kwara duniya tasan me suke aikatawa, ay yaya Salsabeel ba sai ka sha wahalar yi mana bayani ba, dama mu lokaci kawai muke jira in ma takama har prison din aje damu ayi faɗan da mu, wallahi zamu bada goyan baya ɗari bisa ɗari ko da silar hakan zai ja mu rasa ran mu wlh sai inda karfin mu Ya ƙare, Kome suke son ji zamu faɗa masu...." 



tun da Unaisah ta fara zazzaga masifa, suke kallonta jikinta har jijjiga ya ke yi tsabar fusata da 6acin rai, an ta6o inda keyi mata ƙaiƙayi.." bata ƙare maganar ba, Danish Ya miƙe daga zaunan da yake kan Sofa, gaba ɗaya suka bi shi da kallo Salsabeel Yace"Danish Ina zakaje ban gama magana ba"? Ko kallo bai ishe shi ba,  Ya fuce daga falon, sam unaisah takasa karasa maganar,


Da tsantsar mamaki suka bi bayan shi da kallo har ya 6ace ma ganin su.


Saurari Littafin >>>>Kurkukun Ƙaddara Takun farko  Kada a manta ayi mana subscribe like da kuma comment sannan a yi share. Domin samun sabbin littafi idan Mun ɗora.


Haris Yace"ka gani ko ya salsabeel? Danish Ya canza kamar bashi ba, Yanzu ji muna magana mai mahimmanci Ya tashi Ya tafi kamar abun bai shafe shi ba, haka muke fama da shi baya son shiga cikin mu kuma baya son muje gurin shi..." cikin jin kunar rai Haris yayi maganar yana kallon Salsabeel.

Korafe korafe suka dinga fada mashi akan danish,

Unaisah tace"nasan ma zai yi wuya ya bamu hadin kai, kuma yafi mu sanin komai dangane da gidan kurkukun ƙaddara"


 a marairaice tay maganar,

Shiru salsabeel yayi jim yana ɗan jinjina kan shi kafin cikin sanyin murya yace"sai kun yi hakuri da shi, saboda ba yin kan shi bane,  sau dayawa wasu abubuwan da za ku ga yanayi wallahi ba shi bane"! A matuƙar ruɗe suka kalli Salsabeel, Musamman Unaisah Maganarsa Ta jefata a ruɗani, Har dai tagaza jure tace"Ya salsabeel ban fahimci me kake nufi ba! Naji kace wani lokaci ba shi bane"! Kallon ta salsabeel yayi"ina nufin wani abun da ya ke yi bayin kan shi bane, shaidanun  dake a jikin shi ne, su ne suke Controlling din shi, zai iya wuni ba acikin hayyacin shi ba, nasan baku taba lura da hakan ba, shiyasa baya son shiga cikin ku, kuma baya son wani yaje gurin shi, idan ba wanda yake son gani ba, amma abun da yakamata ku cigaba da taya shi addu'a, In sha Allah idan mukayi nasarar raba shi da evils din jikin shi, zaku sha mamaki, zai dawo ainihin wanene shi...."


 

"Yaya salsabeel amma dai bazai manta damu ba ko"? Batool ce tay mashi maganar,


"Taya zai manta daku? Abokan kuruciyar shi, sai dai wasu abubuwan da yake yi zai daina su, zai canza sosai fiye da yadda baku ta6a zata ba.."


 Hankalin Unaisah Ya tashi ba kaɗan ba, Aranta ta ayyana idan har maganar Salsabeel ta tabbata tabbas akwai damuwa ba kadan ba, sai dai ta hana zuciyarta gasgata maganar shi.



Buɗe trolley din gaban shi yayi duk suka kura ido suna jiran ganin me zai fiddo daga aciki.



Ga mamakin su Uniform dinsu ne na gidan kurkukun kaddara, a ninke sun sha guga tare da cotton scarfs dinsu, wanda tsohuwa tamira ta basu kyautar su


Saurari Littafin >>>>Kurkukun Ƙaddara Takun farko  Kada a manta ayi mana subscribe like da kuma comment sannan a yi share. Domin samun sabbin littafi idan Mun ɗora.

daga gefen shi ya ɗaura su, kafin ya dube su sun saki baki suna kallon kayan bakomai suke tunawa ba face rayuwarsu ta gidan kurkukun ƙaddara har tsohuwa tamira sai da ta faɗo masu aran su, jikinsu yayi sanyi lakwas kamar wadanda aka zarema lakarsu.



"Ga uniform dinku nan, Gobe su zaku sanya, Da wuri za'a tafi da ku in sha Allah"


 kaɗan daga cikin ne suka amsa mashi da toh.

Wrist watch din hannun shi ya duba karfe 9 na dare.


Kafin ya maida duban shi Ga sajeed daya kifa kan shi saman sofa.


"Pls, yanzu ba lokacin damuwa bane, lokacine na ɗaukar fansa, yin kuka ko sanya damu arai bazai ta6a zama mafita agareku ba, hakan zai sage maku gwiwa, shiyasa nakeso ku sanya jarumtaka da rashin tsoro a cikin zuciyarku, ku dage da addu'a, Wallahi komai ya kusa zuwa karshe, Idan kun ba su hadin kai, za mu yi nasara bi'iznillahi" 


"In sha Allah ya Salsabeel zamuyi abunda kace, mun gode da ƙarfafa mana gwiwa da kayi, kuma mun yi maka alƙawarin ba zamu ba ka kunya ba,"  Unaisah ce tay maganar har cikin ranshi yaji dadin jin hakan daga gare ta.


"bayan na tafi, ki ba kowa na shi" ya faɗa yana nuna mata uniform ɗin ta amsa mashi da toh.


ya jima agurin su kafin daga bisani ya yi masu sallama ya ta fi...


Bayan tafiyar shi, ta bubbuɗe Uniform ɗin bata sha wahalar gane na kowa ba, saboda numbers din da ke a jikin su, kwata kwata basu san ganin kayan saboda bakiin tarihin dake atare da su, ba dan sun so ba, kowa ya dauki na shi, itama Unaisan ta ɗaukar ma su nasu ita da Batool su ke da black uniform..


A daren ranar cike da zullumin tambayoyin da za'ayi masu suka kwana, in ka cire mutun ɗaya wadda gaba daya tunaninta akan maganar Salsabeel ne, ta tsaya mata aranta, tana matuƙar jin tsoron abunda ya faɗa masu dangane da Danish.


Awashe gari, tun da sassafe suka farka daga bacci, batare da 6ata lokaci ba, suka shirya cikin uniform din su sunyi kyau kamar ɗaliban high school na ƙasar korea, yan matan sunyi rolling cotton scarfs dinsu akansu, mazan kuma a wuyansu suka laga shi kamar yadda Mazan pakistan suke rolling scarf a wuyan su, bayan sun yi breakfast su ka hallara a falo suna jiran aba su umarnin su fito, Unaisah sai ƙara tunasar da su takeyi akan in sunje su saki jikin su, kada suji shakkun tona asirin abunda ya faru arayuwar su, da yake suna jin maganarta duk suka amsa mata da toh.


Suna atsaye suka soma jiyo takun takalman mutane, at same time suka dubi in da sautin ke fitowa daga can Upstairs, Chief Owais ne Ya fito daga Bedroom din Danish jikin shi sanye da kakin sa, Danish yana abiye da bayan shi, White shirt ce a jikin shi tare da dark jeans, Kwata kwata fuskarshi babu annuri ko miskala zarratin ya haɗe rai, ruƙo hannun shi chief ya yi a cikin nashi, a tsanake suke taka stairs cases, gaba daya Su Haris Sun zuba masu ido suna kallon su, da alama sun burgesu kamar wa da ƙani, kullum suna ƙara mamakin kamannin su.

Saurari Littafin >>>>Kurkukun Ƙaddara Takun farko  Kada a manta ayi mana subscribe like da kuma comment sannan a yi share. Domin samun sabbin littafi idan Mun ɗora.


kafin su karasa saukowa down, Sallamar taj da big guy ta karaɗe kunnuwan su, atare suka shigo falon cikin shiga ta kakin su, tsayawa sukayi suna jiran saukowar chief, Cikin girmamawa su Unaisah suka gaishe da su. fuskokinsu da fara'a suka amsa masu

Sajeed yace"kwana biyu big buy, mun daina ganinka, ka 6oye mana" murmushi ya sakar mashi"i'm busy with work and don't have any free time amma kuna araina, Ina fata na same ku lafiya! " atare suka amsa mashi da lafiyalou.


Bayan chief ya sauko su Big big guy suka sara mashi shima ya maida masu martani bayan sun gaisa da junansu, cikin girmamawa su Unaisah suka gaishe da chief fuskar shi asake ya amsa masu 



Tun saukowarsu Danish bai ɗago Ya kalli kowa ba, Idanunshi ƙasa suke kallo, duk sun lura da mood din shi....unaisah dake ta satar kallon shi maganar Salsabeel take ta tariyowa aranta ta kwana da tunanin shi, ga yanayin da ta shiga ajiyan nan dakyar ta runtsa.


"Zamu Iya tafiya" muryar big guy ce ta katsa masu zancen zucin su.


Ɗaya bayan ɗaya suka fara tafiya har lokacin chief yana ruƙe da hannun Danish, bayan sun fito compound din gidan, suka yi arba da zungura zunguran motocin da za'a dauke su, masu black tunted har guda uku, Cikon ta huɗun su hadaddiyar Motar da chief zai hau ce, basu tsaya bata lokaci ba, big guy da taj suka buɗe masu car doors din suka shisshiga kowa ya zauna, daga bisani Chief yaja hannun Danish suka shiga Motar shi, a Hanzarce Jami'an da zasuyi driving dinsu suka tada motocin a wani slow suka nufi hanyar fucewa daga gidan.



*UMMIN AMERICA💋*



Fitar motocin keda wuya, sai ga Ummi ta fito da sauri kamar zatai tuntu6e, jikinta sanye da kimono robe ashe colour, tayi rolling veil akanta, tsayawa tayi bakin ƙofar falon ganin babu su, ta dafe kai da hannu ɗaya, bataso suka tafi batare da tayi masu fatan Alkhairi ba, taji haushin uzirin daya ruƙe ta a toilet, har cikin ranta bata ji dadin ganin babu su ba, yamutsa fuska tayi sam takasa motsawa, taso su tafi da ita Saboda bazata ji dadin zama agidan ita kadai batare da su ba, ba karamin takura zatayi ba


"Ma'am, Kina bukatar wani abu ne"? Muryar wani jami'e ce ta fargar da ita, da sauri ta dube shi tare da girgiza kai"ba abun da nake bukata" ta faɗa tare da juyawa ta koma falon ta rasa meke mata dadi, Ita kadai kwallin kwal, Har ta zauna kan sofa, sai kuma ta miƙe ta nufi bedroom dinta da niyar ta kira Natasha donta ɗebe mata kewar su unaisah kafin su dawo

Saurari Littafin >>>>Kurkukun Ƙaddara Takun farko  Kada a manta ayi mana subscribe like da kuma comment sannan a yi share. Domin samun sabbin littafi idan Mun ɗora.

A hankali ta tura ƙofar dakin, kwatsam taji wani zazzafan shu'umun ƙamshin turare Ya daki hancin ta, har saida ta lumshe idanunta saboda yadda kamshin Ya shigeta, rass tadanji gabanta ya fadi lokacin da zuciyarta ta raya mata kamshin turaren wanene

A hankali ta furta"Big Boss...." kamar daga sama taji ƙasaitacciyar muryarshi acikin kunnanta"yeah..." wani irin tsoro ne Ya kamata, ta soma yan waige waige tana neman shi gaba ɗaya ta ruɗe gani take kamar ba gaskiya bane kamshin turarensa da kuma muryarshi da tajiyo...."

Ƙara ambaton sunan shi tayi"big boss..." don ta tabbatar ma kanta abun da take ji, kafin ta rufe bakin ta, taji motsin buɗe toilet door, wani irin faduwar gaba taji, tashin hankalin da ba'a saka mashi rana, tayi matuƙar razana da ganin shi, daga ƙasa tafara kallon ƙafafunshi dake asanye da slippers, jikinshi sanye da jallabiya ta kama shi ta bayyana ƙaƙƙarfar surar jikinshi mai matuƙar Jan hankali


Kusan suman tsaye tayi, saboda ta gama ruɗewa tama kasa buɗe baki tay mashi magana, ita mamakinta taya akai ya shugo gidan batare da jami'an dake tsaron gidan sun gan shi ba, kuma taya akai harya shigo bedroom ɗinta ya shiga toilet batare da ta gan shi ba, bayan kafin ta fito daga dakin babu kowa ita kadaice, kuma dole duk wanda zai wuce sai ta gan shi.


Zama yayi daga gefen gadon tare da kallonta Ya kashe mata ido ɗaya ya ɗage gira cike da izza yace"me kike tunani ne? Kinyi mamakin ganina ne"? Shiru tayi bata tanka mashi ba, saboda ita har yanzu bata yarda cewa dagaske shine take gani ba, kokwanto take anya bata samu ta6in hankali ba

Sarai ya fahinci Halin da take aciki, Ko ajikin shi, saima kwantar da kanshi da yai saman pillow 

*Ga me bukatar karanta littafin kurkukun kaddara, 500 ne za'a tura Via Opay, 8103884440 Hafsat Bature Muhammad, shaidar biya za'a tura ta whatsapp, 08103884440**UMMIN AMERICA💋*


Post a Comment

Idan kuna da tambaya akan abinda Baku game ba ko kuma kuma Neman littafin da babu a nan kawai ku ajiye tambayarku a ta comment ko wani shawara da Zaku bamu.

Previous Post Next Post

Sponsored Link

Sponsored Post