Sautin ringing ɗin wayarta ne ya farkar da ita daga dogon baccin daya ɗauke ta, tana a kudundune cikin lallausan duvet dinta.
da wata irin malalaciyar kasala ta fara ƙoƙarin buɗe idanunta da su kai mata nauyi saboda baccin da tasha ga wani irin tsami da jikin ta yayi mata, lalube ta fara yi tana shasshafa bedmattress din don taji idan yana nan har ta ƙare lalubawa bata ji mutum akan gadon ba, hakan na nufin ya jima da tafiya.
Tunawa da yanayin da take a ciki yasa tay saurin ware idanunta cike da fargaba ta dubi jikin ta zir take ba sutura, lumshe idanunta tayi cike da jin shaukin shi take ɗan jan numfashi, yayin da ƙwaƙwalwarta ke tariyo mata abun da ya faru tsakanin ta da shi a lokacin da suke tsaka da jin daɗin su.
A hankali ta miƙe zaune ta ja duvet din ta lullu6a kirjin ta da shi, kafin ta jingina bayan ta jikin headboard, sumar kanta ta yamutse saboda damƙar da tasha a hannun big boss, ko ina na jikin ta zafi ya ke mata.
idanunta sun kumbura sun kaɗa jajawur, haka la66anta ma sun kumbura don ba karamin tsotsa suka sha ba, ta galabaita sosai har wani jirin kasala take ji a jikin ta.
Kifa kanta tayi kan gwiwowinta tunawa da nasihar da mahaifinta ke yawan yi mata.
"Ke kadai Allah Ya bani mamana, tun kina ƙaramarki bani da burin daya wuce in inganta rayuwarki ki zama hafizar alkur'ani mai ilimin addini da zamani saboda inyi alfahari dake sannan ki zama abun kwatantace, Alhamdulillah cikin ikon Allah sai gashi kin cika min burina ko'ina zancenki ake duk in na shiga cikin jama'a sun dinga yabonki suna fadin ƴata malama ce hafiza mai cikar kamala da kamun kai ga kyautatama al'umma da son taimako, kowa yabon ki yakeyi, burin kowace mace tayi koyi da Aishatu bintu imam malik mace ɗaya tamkar da dubu, Ummi nasihar da zan maki ko bayan ba raina kiji tsoron Allah, kada ki canza daga yadda nasanki, abun da zaki min wanda zaki biyani shi ne Ki karemun martabana da kimata a idon duniya, kada kiyi abun da zai zubda min mutuncina Aishana"
Rushewa tayi da matsanancin kuka tamkar ranta zai fita, a duk lokacin da ta tuna nasihar mahaifinta zuciyarta ba ƙaramar karaya ta ke yi ba, tana jin tsanar rayuwar data ɗaukarwa kanta, tana mai danasanin abun da yayi silar rabuwarta da mahaifinta, saboda bata da abu mafi soyuwa da ya wuce shi a duniyar nan, kai duk wani gata da ya zata samu agurin ubanta ta samu ninkin baninkin sa.
tana jin raɗaɗin karya alƙawarin mahaifinta da ta yi na kare mashi martabarsa.
kifa kanta tayi jikin pillow, ita kadai baiwar Allah babu mai lallashin ta.
Ba halin ta bane, ba laifin ta ba ne, tana da ilmi tasan zina ba kyau ta kuma san hukuncin wanda ke aikatata amma meyasa takasa dainawa ko da tayi nufin ta tuba ta koma ga Allah? Tasha yunƙurin yin hakan amma aduk lokacin da big boss ya buƙace ta bata iya bijire ma shi.
Ta yi kuka tamkar ranta zai fita kamar ƴar dambe ta dunƙule hannayenta ta dinga bugun mattress kamar zatai hauka ta tsani abunda take aikatawa bata so ta mutu batare da yafiyar mahaifinta ba, kuma batason ta mutu tana aikata sabon Allah tana matukar jin tsoron makomarta.
Ringing ɗin wayarta ne ya dawo da ita hayyacin ta, fuskarta sharkaf da hawaye ta janyo wayar daga kan drawer ta duba sunan me kiranta.
Maji daɗina shine sunan daya bayyana akan screen din, kasa picking call din tayi saboda fushin da zuciyarta ke yi.
Text message ne ya shigo on the top of the screen din wayar, cikin zuciya ta soma karanta abunda ya rubuta mata
_"ummi, na tafi ba tare da nayi maki sallama ba, ki yi hakuri da hakan nasan zaki tashi da kewana, anyi min kiran gaggawane, ba dan nagaji da jin ɗumin jikin ki ba, bazan iya misalta daɗin da kika jiyar dani ba, kin bani cikakkiyar gamsuwa da zan iya ɗaukar kwanaki ban nemi matana ba, bazan iya biyanki ba Ummi, ki fadamin me zanyi maki don in faranta maki"_
Runtse idanunta tayi gam, siraran hawaye suka dinga shararowa kan kuncin ta..
"Ya Allah Ka cire min jarabar son bawan nan naka, Ina neman tsari da shi...."
bata kare maganar ba kwatsam taji dirar motoci acikin gidan, a firgice ta jefar da wayar ta faɗa kan mattress ta duro daga kan gadon, tafin hannunta a tallabe da bargon ta faɗa toilet taja ƙofa ta datse, tana faman zare idanunta, sam ta manta da su Batool tasan bai wuci sune suka dawo gidan ba, abunda take jima fargaba kada wani ya shigo ɗakinta tasan in har suka ga gadonta sai sun zargi wani abu saboda ya 6aci ba kaɗan ba.
Cikin Takun sauri Chief Ya faɗo Falon Ya nufi upstairs, agurguje taj da big guy suka biyo bayan shi, kwata kwata babu kwanciyar hankali akan fuskokin su damuwace ƙarara saboda jami'an da suka tura su nemo Danish kusan awanni har yanzu ba wani labari, har tracking layin sa sukai a karshe suka gano location din da wayar take agida yabar ta baije da ita head quarter din ba, wannan dalilin ne yasa suka yanke shawarar su dawo gidan, watakil su gan shi.
bai nufi ko'ina ba sai bedroom din Danish Yana isa bakin kofar yayi knocking ɗin ta cike da fargaban kada su ki ganin shi.
Jin shiru ba'a buɗe kofar bane yasa shi tureta da hannun shi ya faɗa ciki Yana haki saboda gudun daya sha, bazai iya tuna when last yayi irin shi ba.
da matsanancin faduwar gaba yake bin dakin da kallo wayam babu kowa adakin dafe kan shi yayi da hannu ɗaya idanunshi sun kaɗa jawur babban tashin hankalin shi Ina Danish yaje? ya zai yi da yan uwan shi? Me zai fada ma Uncle hateem idan ya kira yana son yin magana da shi"?
"baya aciki ko"? muryar boss ce ta katse mashi zancen zucin shi
Big guy duk ya rasa kuzarin shi Ya daura ma kanshi alhakin 6atan Danish saboda shi ne silar daya ja har ya yi zuciya Ya tafi, sai yanzu ya ke danasanin bata mashi rai da yayi ganin yadda ya ɗaga hankalin chief Owais.
"Taj bansan ya zanyi ba, baya nan, ya tafi, ya zanyi da raina, bana so na rasa yaron nan wallahi danasan abun da zai faru zuwan mu headquarter da ban tursasa mashi akan yabi mu ba..."
dakyar yake magana saboda damuwar data cika zuciyar shi.
jikinsu yayi mugun yin sanyi.
Cikin raunin jiki ya dubi big guy"Omar, kaga abunda kaja min ko? Idan har yaron nan bai dawo gida nan ba, bazan yafe maka ba..." gaba ɗaya ya rikice masu.
"Sir kayi hakuri, na kar6i laifina, kuma nayi danasanin 6ata mashi rai da nayi, bada son raina ba ya 6ata min rai ne amma nayi maka alkawarin zanje in nemo shi duk in da ya shiga agarin nan..."
yana faɗan hakan ya juya azafafe ya haura kan stairs ranshi ya 6aci da furucin Chief, kalmar daya furta mashi ɗazu daya ce Son danish na kara ninkuwa azuciyar shi yaji haushinta bayan irin cin mutuncin da yaron yayi mashi amma ko kadan ransa bai 6aci ba, shi arayuwarshi bayason wanda zai shiga tsakaninsa da chief, yana matuƙar jin kishin yaga chief yana nunama wani so fiye da shi hakan na kona masa rai yafi so koda yaushe ya zamana na hannun daman shi.
Dafa kafadar chief yai da hannun shi"dan Allah ka kwantar da hankalin ka, bana so kana sanya damuwa aranka, in sha Allah Danish zai dawo ..." lallashin shi ya cigaba da yi, bawan Allah gaba ɗaya ya rasa ƙwarin gwiwar shi.
"Nima Zan bi Omar, Zamuje mu binciko shi"
Numsafawa yai kafin ya dubi Taj da rinannun idanun shi
"Ina sauran Yaran? Sun shigo?"
bai ƙare maganar ba, suka jiyo sautin tafiyar su da sauri taj ya dubi kofar shigowa falon, ɗaya bayan ɗaya suke shigowa kamar yan gudun hijra saboda jigatar da su ka yi, fuskokin su sharkaf da hawaye sun sha kuka bayin Allah har sun gaji sun gode ma Allah, Unaisah tafi su jin jiki har wani jiri take gani acikin idanunta, sun ruke hannun Juna ita da Batool suma sauran sun rurruka hannayen junan su.
"Sun shigo,"
"Pls, Calm them down, I don't want them to worry about losing their brother, ka cigaba da lallashin su, Sannan ashirya masu lunch dinsu"
"Sir kaima kana bukatar hutu, ka koma daki ka kwanta ka huta zanyi magana akawo maka lunch din ka" girgiza kai yai"wallahi bazan iya cin komai ba in har Danish bai dawo gidan nan ba"
Taj yayi mamakin kalaman shi, bai ta6a zaton son da chief yake ma Danish yakai har haka ba, aranshi ya ayyana watakil ko dan saboda sabon da sukai da junan su cikin kwanakin nan.
"Da ka daure.."bai kare maganar ba ya katse shi"Boss ka tafi kawai, Ka kula da sauran yaran, Ka kira auntynsu ka fada mata halin da suke a ciki"
Cike da jin tausayin shi ya amsa mashi da toh.
Lokacin da ya sauko down, A kan sofas Ya hango su zazzaune sun yi shiru kamar masu zaman makoki, tsayar da idanun shi yayi akan Unaisah da ta kwantar da kanta saman kafadar Batool, tayi matukar bashi tausayi, bakomai yake tunawa ba face lokacin data bi bayan Danish ta haura kan titi mota takusa hankadeta ba dan Allah yasa Jami'an su sun yi gaggawar Kai mata agaji ba da tuni rai yai halinsa saboda ta furgice idanunta sun makance bata ji bata gani danish kawai take nema ido rufe, har wani zazza6i take ji ajikin ta mai azabar zafi, ga ciwon kai daya fara takura mata, ta rasa meke mata dadi duniyar nan, ita damuwarta ina Danish ya shiga? Baisan kowa ba agarin abuja, abun da take jima fargaba kada yace zai koma Gidan kurkukun kaddara duk in zuciyarta ta raya mata hakan sai taji matsanancin faduwar gaba ga tashin hankali da firgici.
kwata kwata babu wanda Ya lura da Taj a cikin su saboda damuwar data rufe idanun su.
Har saida yayi masu gyaran murya tukunna suka kalle shi in ka cire Unaisah wadda ta rufe idanunta hawaye sai suntiri suke yi kan kuncin ta.
Jiki asanyaye ya zauna yana dubansu
"Unaisah! " dakyar ta buɗe idanunta da suka rune zuwa ja ta kalle shi
"Meyasa baki jin maganata? Bana hanaki yin kukan nan ba? Ko shi zaisa ya dawo ne"? Yawu mai ɗaci ta hadiya tamkar bata son yin maganar tace"daddy, bana jin dadin jikina ne"
"Ba dole jikinki yaki dadi ba, duk kinbi kin daga hankalinki uhyum! Sai kace ba kisan tawakkali ba Unaisah! Ce maki akai Ya bace ba zaki kara ganin shi ba ne? ya fada yana kallon fuskarta, shiru tayi tana sauraron shi tasan ba lallai ya fahimce ta ba tun da shi a zaton shi sabo ne kadai atsakanin su.
Sassauta muryar shi yayi cikin sigar lallashi yace"kuyi hakuri nima na damu da rashin shi, amma bai kamata ku zauna kuyita kuka ba, ba zai yi maku maganin komai ba saima ya kara jaza maku wani ciwon, ku tayashi da addu'a in sha Allah zai dawo ko dan saboda ku..." sun yi shiru suna sauraron shi.
"Allah Ya kare mana shi aduk inda yake, Allah Ya karkato mana da tunanin shi ya dawo gida .." cikin sanyin murya suka amsa mashi da Ameen
Miƙewa Parveen Tayi boss yace"ina zuwa"?
hannunta dafe da cikinta tace"fitsari ne Ya matse ni" ta fada tare da kama hanyar ta nufi dakin su,
"Nima fitsarin nake ji, tun ɗazu ya matse ni" murya na rawa jamimah tayi maganar tare da mikewa daga kan sofa ta watsa da gudu ta nufi dakin su.
"Time din sallah azhar har ya wuce, Ku tashi ku tafi ɗaki, ku yi wanka ku yi sallah kafin ku fito zanyi magana a shirya maku lunch din ku nasan kuna jin yunwa" cikin kulawa ya faɗa yana duban su.
Bata jin zata iya cin abinci in har Danish bai dawo ba, cike da rashin kuzari ta miƙe idanun ta akan daddynta dake kallon ta bakomai ne ke daure mashi kai da ita ba face haukan da tayi ɗazu ya rasa gane meke a tsakaninta da Danish!.
Ta ɗan tsargu da kallon da yake yi mata, in a weak voice tace"Zan shiga daki, bansan ko zan dawo na iske ka ba, ka gaida min aunty Danejo" bata tsaya taji amsar shi ba, ta juya ta nufi dakin su tana tafiya a harharɗe kamar zata kife ƙasa har sai da ta shige dakin tukunna ya ɗauke ido daga kallon ta.
Knocking door room dinta da akayi ne yasa tayi sauri fitowa waist ɗinta daure da towel, hannun ta ruƙe da wani short towel da take tsane sumar kanta da shi.
Cikin kunnanta ta tsinkayi muryar Batool daga waje tana fadin
"Aunty Ummi ni ce, Mun dawo, ki buɗe min ƙofa..." wani irin sanyi ne taji ya ratsa zuciyarta, taji dadin jin muryar Batool saboda a halin da take a ciki tana bukatar wanda zai kwantar mata da hankalin ta.
"Batool, ki jira ni, Ina shiryawa ne"
"Toh"
Cikin kankanin lokaci ta kammawa shiryaw cikin abaya baƙa mai kyan gaske, ta yi rolling headscarf, ta nufi door room din tana buɗewa Batool tayi sauri faɗawa kan kirjinta, tayi mata wata irin runguma kamar zata koma cikin ta wani irin faduwar gaba taji saboda kunnnata sun jiyo mata shesshekar kukan batool, dama tun da ta rungume ta taji aranta ba lafiya ba.
Aruɗe ta furta"My Babe, meya faru? Baki da lafiya ne"? Ta faɗa tare da tallabo fuskar Batool da hannunta, hankalinta ya ƙara tashi da ganin yadda fuskarta ta yi jawur ta jike da ruwan hawaye
Jijjiga kafaɗarta tayi"meke damunki ne? Wani abu ya faru ne? Fadamin mana waya ta6a min ke"? Ta fada akagare da son jin amsarta.
La66anta na rawa ta labarta mata abunda ya faru a head quarter dangane da batan Danish.
Hankalinta Ya tashi matuƙa muryarta na rawa ta furta"inna lillahi wa inna ilaihirraji"un Amma banji dadin abun da big guy yayi mashi ba, bai kyauta ba Allah, da hankalinshi da komai sai kace baisan wanene Danish din ba..." rai a6ace tay maganar.
"Yanzu Ina su Unaisah din"?
"Duk suna adakin su, gaba ɗaya basa jin dadin jikin su saboda abunda ya faru, munyi kuka har mun gaji"
tsantsar tausayinsu ne Ya kamata ga damuwar bacewar Danish tana jin shi kamar kaninta saboda kaunar da takeyi ma su
Da tafukan hannayenta ta share ma batool hawayen dake sintiri kan fuskarta.
"Ki daina zubda hawayenki, bana so pls, ni nasan zai dawo ne in sha Allah, mu tayashi da addu"a" ta fadi hakanne saboda tasan bazai iya jure rashin Unaisah ba, tun shekaran jiya data ga abunda ke tsakaninsu tasan ba karamin abu ne zai iya raba su ba.
"Aunty Ummi ko sallah banyi ba.."
"Okay, ki shiga ciki ki yi, bari naje gurin yan uwan naki, nasan zasu neme ni" a hanzarce ta fuce daga dakin, sam ta manta bata gyara gadon ba, saukin ma ta bar bargon a toilet.
_________________________________✍️
*ANEELERH💓*
a Zaune take kan gadonta jikinta sanye da riga bubu, ta yi shiru tana kallon baby junaid dake zaune gefen ta hannun shi ruƙe da plate din wainar fulawa wanda zahra ta soya mashi ita, sai tsantsani yake saboda dadin da tayi mashi dama ya iya kwaɗayi, kadan yake balla ya ɗan dangwala yaji saiya tura a cikin karamin bakin shi
Shekaran jiya izuwa yau ya ƙara samun lafiya walwalar shi ta dawo tun da yaga Angel dinsa ta cika shi da farin ciki, ko bacci yake yana ambaton sunanta, tun da suka dawo gida ya addabeta akan ta kira Angel awaya tace mata tazo yana son ganin ta, dakyar take samu ta shawo kan shi, sai dai har yanzu bakowa yake yarda ya ɗauke shi ba, daga momynsa sai zahra da mami amma su abie kam ƙiwuya yake yi masu abun yana daure mata kai, har mahboob bai cika yarda ya dauke shi ba.
Tayi zurfi acikin tunaninta Muryar shi ta katse ta
"Mommy, wannan sauran wainar dana rage na Angel ne, wa zai kai mata? ko ni zakisa mahboob yakaini a mota in kai mata..."ya faɗa yana nuna mata rabin wainar da ya rage a plate din
Murmushi tasakar mashi"na fada maka ba Angel bace, bana so wani yaji kana kiran sunan Angel, ita yarinyar da ka gani sunan ta Azeezaty suna kama ne da Angel din mu"
yamutsa fuska yai tare da maƙe mata kafada"wallahi wayo zaki min, Angel dina ne ita ay har tambayarta nayi tace mun eh itane ko" ya faɗa da shagwa6a yana hade fuska.
Ƙura ma juna ido sukayi batasan ya zatay da shi ba tana son ta tambaye shi meya faru amma tana jin fargaban kada akoma yar gidan jiya, zai iya birkice mata tun da ta fahimci baison maganar kwata kwata.
"Mommy kina kallona ko zaki ci wainar ne in ɗan maki" ya fada yana kokarin 6allo mata da sauri ta furta"a koshe nake my baby boy, na fiso ka ci ka koshi..." farfari yayi mata da idanun shi
"Yaushe zaka koma school"?
Maƙe mata kafaɗa yai"shaina ƙara samun lafiya" yar dariya tayi "junaid na ganoka gudun school kake, Allah next week zan maida ka, ay naga kaji sauki jikin ka ya murmure" yamutsa mata fuska yai tare da zumbura mata baki
"Allah in kinasho in koma ki sani makarantar su Azeezaty, sai mu runka yin wasa da ita"
ya faɗa tare da 6allo wainar da ya rage ma Angel ya tura abaki yana ci, murmushi tayi tare yin kasa da muryar ta"babyna" ya amsa mata naam
Takai hannu ta shafa sumar kan shi.
"Zaka iya tuna abun da ya faru ranar da muka je gidan Hajiya adama"? Dakyar ta kare maganar ganin yadda ya ware idanun shi da karfi, Jikin shi ya fara kerma kamar mazari.
da sauri ta janya plate din wainar ta daura kan table, ta saukowa daga kan gadon ta zukunna agaban kafafuwan shi kamar mai neman gafara.
"Dan Allah junaid ka fada min, kaga ni mommynka ne, duk duniya baka da tamkar ni, idan ma kana jin tsoron ka fadi ne wasu suji nayi maka alkawarin bazan bari kowa yaji ba daga ni sai kai...."
tatta6e fuskarshi yayi ruwan hawaye suka taru acikin idanun shi labbanshi suka kama kerma taji faduwar gaba da ganin yanayin shi sai dai bata jin zata iya hakura a wannan karan, saboda tayi matukar ƙagara da son jin meya faru da su aranar!.
Ruko hannun shi tayi cikin sigar lallashi da wayau da dabara ta karya murya tare da marairaice mashi fuska duk don ya tausaya mata ya fada mata, magiya ta dinga yi mashi yayi shiru yana kallonta da tsantsar tashin hankali akan fuskarshi.
can dai ta ɗan bugu cikin shi da wayau tace"Ni dama na sani Ana guduwa tayi junaid, sai da nace mata kada ta tafi tabarmu amma shine ta tafi, ni bansan laifin da nayi mata...."
bata ƙare maganar ba, sakamakon abinda kunnuwanta suka jiyo mata daga bakin junaid
Cikin shesshekar kuka yace"mommy bafa guduwa tayi ba, Allah dodone Ya kashe ta a cikin gidan nan, ni na ganshi da idona kuma itane tace in gudu in 6oye"
kamar an dasa mata aya ta tsaya cak tana kokarin tariyo maganar shi acikin zuciyarta lokaci ɗaya ta saki dariya tana fadin"haba junaid, abun naka hada zolaya, karya fa babu kyau, In ba zaka fadamin gaskiya ba ay basai ka shirga min karya ba..."
girgiza mata kai yai babu alamun wasa akan fuskarshi ya furta"wallahi mommy dagaske nake faɗe maki, dodone Ya cinye ana adakinta, tana ta kuka hada jini a jikin ta..."
yadda kasan kanzon kurege haka take sauraron shi sai tikar dariya takeyi irin ya raina mata wayon nan shi kuwa ya haƙiƙance yana faɗa mata iya gaskiyar shi sai ma ta maida maganar tashi abun nishadi.
"Mommy ki daina dariya, ba abun dariya bane wlh dagaske nake maki" wani kallon rainin wayau ta wurga mashi kafin tace"junaid bana hanaka yin rantsuwa akan karya ba..."
kuka ne Ya ci karfin shi wannan karan ta ɗan ji faduwar gaba duk da bata yarda da maganar ba ta dauki abun shiririta arude ta ke lallashin shi cikin shesshekar kuka yace"mom.. my ba karya bane, ki daina min dariya, ni banaso dodon daya kashe ana ya kashe mu mommy, dan Allah mu gudu mubar gidan nan ni wlh tsoro nake ji..."
bata san sa'adda ta rungume shi a kirjinta ba, hankalinta yayi mugun tashi saboda kukan da junaid yake yi mata tasan halin kayanta ba karamin abune zaisa junaid yin kuka ba irin haka, tabbas wani mummunan abu ya faru da ya yi silar zaucewarshi sai dai zuciyarta taki yarda da maganar shi, gani take bame yiyuwa bane.
_______________________________✍️
A ƙalla ta fi karfin mintuna a tsaye tana kallon Unaisah dake a kwance kan darduma ta nannaɗe kafafunta cikin hijab, idanunta suna a rufe gam sai yan siraran hawayen da ke sintiri kan fuskarta tayi kukan tayi addu'ar amma har yanzu zuciyarta taki sarara mata daga radadin da take mata, gani take kamar ta rasa Danish.
aranta tana ji in har kurkukun ya koma tabbas zata bishi ne ko da hakan zaiyi silar rasa ranta don ji take bazata iya rayuwa batare da shi ba.
"Unaisah!" ummi ce ta kira sunan ta, tayi shiru tamkar bata ji ta ba
"Nasan kina ji na, ni bansan ya zanyi dake ba, duk irin kokarin da nayi gurin kwantar maki da hankali kinki daina kukan nan, ga abincin ki dana sa akawo maki shima kinki ci, to wai kukan da kike shi zaisa ya dawo ne? Tun da kinyi addu'ar sai kibar ma Allah komai In sha Allah zai dawo...." cikin sigar lallashi ta faɗa tare da zukunnawa gaban prayer mat din
"Dan Allah ki tashi ki ci abincin ki..." da wata irin karyayyar murya ta furta"aunty Ummi, ba zaki gane ba, ni kadai nasan halin da nake a ciki, zuciyata bata min dadi ji nake kamar zan rasa raina ne, yaya Omar ya 6ata min rai, shine silar komai, wallahi Aunty ummi naji zafin kalaman daya gaya ma Danish, duk da baida ilmi ko jahili akayi ma gori sai yaji ba dadi"
jikin Ummi ba karamin sanyi yayi ba, ga wani irin tsantsar tausayin Unaisah daya kamata, tasan bai wuci hada soyayyarshi ke azabtar da ita ba.
"Kiyi hakuri Unaisah, In sha Allah Danish zai dawo, Allah shi zai tsare sa aduk inda yake, mu taya shi da addu'a ni inaji araina ko dan saboda kaunar da yake yi maki zai dawo"
dakyar ta buɗe idanunta wadanda suka kada jajawur ta dubi ummi duk da halin da take a ciki tayi mamakin kalmar kaunar data furta.
fahimtar hakan yasa ummi tay saurin furta"naga kamar yafi kaunarki a cikin yan uwanki, kema haka shiyasa nace haka, kada ki ɗauka ko ina sanya maku ido ne"
shiru tayi bata tanka mata ba.
"ni abun da nake tunani watakil ya ke6e kanshine awani guri don ya gusar da bacin ranshi in ba haka ba Danish ay ba za ace ya 6ace ba, mutumin da ba shi kadai bane tsaf zai iya kawo kan shi gidan nan..."
bata kare maganar ba ta dakata tana kallon Unaisah ganin yadda ta zabura ta miƙe tsaya kamar zata fadi saboda rashin kwarin jikin ta
"Ina zuwa"?
"Yanzu zan dawo aunty ummi, wani abu zan duba" tana fadan hakan tasa kai ta fuce daga dakin cike da sa ran hasashen ta zai zama gaskiya, maganar da ummi tayi ta tuna mata da wani abu daya ta6a faruwa.
________________💋Chief Owais💪
Kwance yake akan gadon shi, yar singlet da short ne ajikin shi, damuwa ta hana shi ta6uka komai, ya dade bai shiga tashin hankalin daya shiga a yau ba, wayarsa dake akan bedside drawers sai ringing ta ke yi daga kiran ya katse wani ke shigowa sautin ya cika kunnuwan shi, amma baya jin zai iya picking din su yasan bai wuci Na hannun damansa bane suke kira don suji ko an ga Danish.
Shaf ya manta da bakin da za su yi, saida tunanin Ya faɗo mashi aran shi kafin ya mike ya janyo wayar shi tare da duba screen din My dad shine sunan daya gani saida ya fara daidaita nutsuwarsa kafin yai picking call din
"My Son, Ya kake Ya aiki, ka manta da daddyn ka ko"?
Duk da halin da yake aciki sai da yaji nutsuwa ta shige shi jin muryar daddynsa
lumshe idanun shi yayi cikin sanyin murya ya furta"lafiyalou daddyna, ni na isa in manta da bugun zuciyata? Mutumin da nake kwana in wuni da tunanin shi araina saboda kaunar da nake masa"
Sautin dariyar mai girma sharafuddeen ce ta ratsa kunnan shi cike da nishadi yace"My Son kasan duk wata hanya da zaka kare kanka agurina, ka faranta raina, but meke damunka ne? Naji muryarka kamar baka jin dadi..."
Shiru yayi jim dama yasan zai yi wuya in daddyn nasa bai gane wani abu ba, dayawan lokutta ta muryar shi kadai yake gane halin da yake a ciki.
"Babu komai, yanzu na tashi daga bacci ne, shiyasa kaji voice dina wani iri"
"Hmm owais kenan, har ni zaka boye ma damuwarka"?
"Daddy, ka yi hakuri zan iya kiranka anjima mu yi magana"?
"Okay, in ba baka kira ba, Ni zan kiraka, ko inzo gidan naka da kaina kasan bana wasa da lafiyarka" yar dariya chief yayi saboda yaji dadin maganar shi ba wani jimawa sukayi ba sukai sallama
layin Omar ya danna ma kira kusan sau uku tana ringin bai ɗaga ba sai a kira na hudu yayi picking.
Kara wayar yayi a kunnan shi"Omar, kana Ina"?
On the other hand big guy yace"na tafi neman bugun zuciyarka saboda bana so in rasa ka" shiru yayi jimm yana maimaita maganar big guy harya fahimci ranshi ya 6aci saboda yayi mashi karya, location dinshi ya nuna yana agidan kamar ko ya sani yana akwance kan gadon bai jima da tashi daga bacci ba.
"Omar zamuyi magana, nasan meke damunka, pls don't forget to get the soldiers ready and go to the airport, jirgin su commender yakusa yin landing nan da minti talatin "
"Consider it done, sir, amma ya yakamata kaima ka shirya mu tafi airport din atare, zasu fi jin dadin tarbar da zamuyi ma su"
"Just do what I say" ya umarta, bai bari big guy ya kara magana ba yayi rejecting call din don baya jin zai iya fita daga gidan a halin da yake a ciki.
*Unaisah Angel*
Bayan fitowarta daga dakinsu bata nufi ko'ina ba sai upstairs tana tafiya jiki duk ba kwari ta tura kofar ɗakin ta shiga daga ciki bata ga kowa ba.
Gadon shi tabi da kallo sai ta dinga ganin kamar zata gan shi kwance yana bacci, kau da idanunta tayi ta juya ta nufi toilet dinsa.
A hankali ta daura tafukan hannayen ta, ta tura ƙofar ta buɗe ta, dira ƙafarta ke da wuya taci karo da abunda yayi silar razanar da ita ta daddage ta fasa kara tana ambaton sunan Allah ta dafe kanta da tafukan hannayenta, hadi da runtse idanunta jikinta ya fara kakarwa, wani irin faduwar gaba taji tamkar ana dakan sakwara a kirjin ta.
dukkan ilahirin jikinta rawa yake kamar mazari tayi matuƙar firgita da abunda idanunta suka gane mata, tayi matukar razana, yatsun hannunta na kerma ta bude kofar ɗakin garin saurin ta fita cikin rashin sa'a tayi tuntu6e da ƙasan hijab dinta dake ja da kasa gaba ɗaya ta wuntsila ta yi kundunbale ta kife ƙasa hankalinta yayi mugin tashi jikinta yadau zafi rau wata irin zufar tashin hankali ce ta fara tsastsafo mata.
Tana ta kokarin mikewa donta gudu taji motsin buɗe ƙofar tuni tasha jinin jikin ta, ta ƙame a durkushe ta kasa ɗagowa yayin da ƙwaƙwalwarta ke tariyo mata Halittar da tagani a cikin toilet dinsa kamar Wolf (kerkeci) jibgegen gaske.
Ƙamshin turaren Chief ne Ya ziyar ci kofofin hancin ta, Kafin Daddaɗar muryarsa ta katse zancen zucin ta
"Unaisah? Are you Okay"? Ay tana jin muryarshi ta yi wani irin yunkuri da iya karfinta na karshe ta zabura ta miƙe, gaba ɗaya ta faɗa kan broad chest dinsa ta ƙanƙame shi, cikin shesshekar murya take faɗa mashi abunda ta gani a cikin toilet din tare da yi mashi nuni da yatsan ta.
Sam ya kasa fahimtar me take nufi, sai kallonta yake yadda ta kankame jikinshi ta hanashi motsawa daga gani ta tsorata ba kadan ba.
"Unaisah, what's wrong? Who's in the toilet?"
Batare data ɗago ba ta furta"dodo ne a toilet din sa,"
"Okay, zanje na duba, ki jira anan" ya fada tare da ruko hannayenta a hankali ya banbare su daga kan waist dinsa.
yayi mamakin uwar zufar daya gani akan fuskarta kamar an yayyafa mata ruwa ga zafin da jikinta ya ɗauka yaji shi har jikin shi da ta rungume shi sai faman jan numfashi take tafin hannunta ɗaya dafe da saitin zuciyarta.
"Ki kwantar da hankalin ki, Ina atare dake, ba abun zai faru..."
yawu ta haɗiya tana faman zare idanunta acikin nashi ta amsa mashi da toh.
har ya ɗaga ƙafa zai nufi toilet din Yaji ta damƙo upper arm dinsa, slowly yakai duban shi gare ta.
Girgiza mashi kai tay a tsorace tace"Don't go alone, I don't want anything to harm you"
murmushin gefen fuska ya sakar mata har cikin ranshi yaji dadin nuna damuwa da ta yi akan shi hakan ba karamin faranta ranshi yayi ba.
"Kada ki damu, ba abun da zai faru dani in sha Allah" ya fada yana kallon Heart shaped lips dinta da suka jiƙu da ruwan hawayen ta.
Taƙi sakin rigar shi saboda ta tsorata da abunda tagani tana jin fargaban wani abu ya same shi, shi da bai saba da wahala ba.
Maƙe mashi kafada tay kamar ƙaramar yarinya cikin sanyi murya tace"hankalina bai kwanta daka shiga ba, pls kada kaje, ka kira salsabeel awaya yazo ya gani ko ka kira sheikh imam malik"
A hankali ya cire hannun ta daga kan arm dinsa
Kamar ta sanya mashi kuka, bai jira ya kara jin me zatace ba, Ya nufi toilet din sai da ya fara karanta addu'ar shiga kafin ya sa tafin hannunsa ya ture ƙofar A hankali ta buɗe.
Without feeling nervous ya fada cikin toilet din, Yana shiga idanunshi sukayi mashi kyakkyawan gani yayi matuƙar mamakin ganin shi kwance cikin kwamin wanka Ya cika shi da ruwa, ko kayan jikin sa bai cire ba ahaka ya kwanta a ruwan Kamar ma bacci yake yi.
_Tsantsar mamaki da al'ajabi ne suka bayyana karara akan fuskar shi, Ikon Allah mutumin da suke ta wahalar nema kamar zasu tada garin abuja, ba irin neman da jami'an su basuyi mashi ba sako da lungu na garin saida suka bincika basu gan shi ba ashe yana acikin toilet dinsa kamar al'jani, ko taya akai ya shigo gidan? Bayan har gate officers ɗin gidan sai da ya tambaye su koya dawo gidan suka ce mashi bai dawo ba, gani yake kamar amafarki yake kallon shi saboda zuciyarsa taki aminta da abun da idanunsa ke nuna mashi_
Da tsantsar ruɗani ya furta"Danish! Is that you?"
*DAGA ALKALAMIN BOSS BATURE✍️*__________________________________✍️