Kurkukun Ƙaddara Takun Ƙarshe page 49 Complete

Kurkukun Ƙaddara Takun Ƙarshe page 49 Complete

Takun Ƙarshe

A ruɗe ta kalli fuskar shi, ya haɗe rai kamar ba daddynta ba, ta rasa gane meke faruwa da shi ne.

Babu wanda Ya lura da abunda Ya faru tsakaninsu, Hankalin yan uwanta baya akan su

Duk da haka bata kawo komai a ranta ba, ta kuma cewa, "Daddy, Chief ya fada maka an ga Danish a cikin toilet ɗinsa...." banza yayi da ita tamkar bai ji maganar ba, hakan ba karamin ɗaga mata hankali ya yi ba.

komawa tayi cikin yan uwanta jiki a mace ta tsaya zuciyarta cike fal da tunanin sauyawar daddyn nata, fatanta Allah yasa ba wani abu ke damun shi ba.


Walking slowly yake taka stairs, da karfi Jemimah ta furta sunan  Danish hakan yaja hankulansu gaba daya suka kalli stairs din bakunansu a buɗe saboda tsantsar kyan da yayi, wata hadaddiyar light grey thobe ce a jikinsa ta bi surar jikin shi, ya ɗaure sumar kan shi with hair ties, gaba daya sun shagala da kallon shi, ƙasa-ƙasa da murya ummi ta furta Tabarakallahu ahsanil khalikin, Allah yayi halitta..."


 A second to the last step na stairs ɗin ya ɗan dakata da yin tafiyar jin alamun kamar ana kallon shi kafin ya ɗago da ido ya dube su, motsin buɗe kofar falo yaja hankulan su.


Gaba ɗaya hankalinsu ya koma kan masu shigowa, Big guy ne ya shigo da sallama a bakin shi, kafin U.s armies din suka shigo kowannansu suit ne a jikin shi...zuba masu idanu su ka yi kamar ba su gane su ba, sun yi shiru suna kokwanton  anya su ne? Saboda basu tsammaci zasu gan su ba.


Dakatawa su ka yi da yin tafiyar suna kallon su kusan su shida suna jira suga reaction din su, Wani irin ihun farin Ciki Gabriel Ya saki, da gudu Ya nufi Lieutenant thompson Sojan daya taimake shi a dajin evil forest saboda sarkar cross din shi, kafin Ya ƙaraso thompson Ya bude mashi hannayen shi ya fada jikin shi yayi hugging din shi gaba daya suka fashe da dariya.


 Wayyo Allah daɗi da wani irin farin ciki sauran ex-prisoners suka nufe su kafin su ƙaraso suka miƙa masu hannuwansu don su yi hugging din su, aiko suna  ƙarasawa ƴan matan suka ƙi bari su yi hugging ɗinsu sai dai suka yi shaking hands, in ka cire jemimah da ta maƙalƙale Commender har saida ya ɗauke ta, mazan cikin su suka yi hugging dinsu ɗaya bayan ɗaya, fuskokinsu dauke da annurin farin ciki, sunyi mamakin zuwan bazatan da suka yi ma su.


 Da tsantsar mamaki Unaisah ta furta"Commander James! Captain Lewis! Major Smith! Jackson Lee! Canal Harry! Lieutenant Thompson! What an astonishing reunion! Is this really a chance encounter?"


Dariya suka saki gaba dayan su, da fara'a commender james ya ce, "Indeed, it's us! We hope you're overjoyed to see us. We've come specifically because of you, and we hope you'll welcome us with open arms." (Yeah mu ne, muna fata kunyi farin cikin ganin mu, munzo ne saboda ku, fatan zaku kar6e mu hannu biyu..." )


bai ƙare maganar ba suka haɗa baki gurin furta, "We welcome you, most warmly! We're truly elated to see you!" 


 Daɗi ne Ya lullu6e sojojin, sai kallonsu sukeyi gwanin ban sha'awa sunji dadin sauyin da sauka samu sun kuma jinjina ma Chief, su Hibba da basu san su wanene ba sai faman baza masu na mujiya su ke yi cike da son sanin su wanene su ɗin.


Captain lewis ne ya nuna su da hannunshi cikin harshen turanci ya ce, "waɗannan sune sauran yan uwan naku"? A tare suka haɗa baki gurin furta Eh, Tambayar sunayen su yayi Sajeed ne ya gabatar masu da su..


Yana zuwa daidai kan Deeja Commender Ya dubi Haris, "Is she your sister cos you look alike"


 Yana murmushi yace Eh sister ɗinsa ce.


 "She's the cause of his heartbreak" Unaisah ta faɗa da zolaya, dariya sojojin su ka yi.


Major smith Ya ce,"Dear Angel, where is that handsome young man, mai nauyin bacci ban gan shi ba ko baya nan .." bai ƙare maganar ba Thampson Ya ce, "nima abunda nake so na tambaya kenan, Ina Danish"? da yatsa Unaisah ta nuna ma su shi, yayi tsaye kan stairs, idanunsa na akan su, gaba ɗaya suka kai duban su gare shi Commender ya ce, "Har yanzu yana nan da ƙyuiyarsa?"


ganin kamar baida alamun zuwa gurinsu ne yasa Unaisah yin saurin cewa,"may be bai gane ku ba ne," major ya sake cewa, "Mun riga da munsan halin shi ai, Ya bacci har yanzu yana yi ko ya daina?


Dariya suka saka gaba ɗayan su, da ido Unaisah tayi mashi alamar ya zo gurinsu ganin kamar sun damu da son ganin shi.


Saukowa down ya yi ya nufe su, commender ya miƙa mashi hannu, "Danish, come here, I'm thrilled to see you! I hope you're safe and sound,"  ya faɗa tare da yin hugging ɗin shi, In low voice ya furta, "I'm fine, ina yi maku barka da zuwa" ya faɗa tare da raba jikinshi daga na commender ya bi sauran yayi hugging ɗinsu tare da yi masu barka da zuwa hakan ba ƙaramin daɗi ya yi ma su ba.


Big guy ne yace da su, "Mu shiga ciki, ku zauna ku huta." Hannayen su ruƙe dana prisoners suka nufi falon, kafin su ƙarasa Taj dake tsaye yana kallon su, Ya matso kusa da su suka gaisa da junansu, big guy ya gabatar masu da Taj a matsayin mahaifin Unaisah sun yi murnar jin hakan sosai, duk budurin da ake Ummi tana can gefe ɗaya tana yin waya har sai da commender ya hangota yana ganin bayanta ya gane itace, nufar ta yayi yana isa ya rungume bayanta, a ɗan firgice ta juya don ta ga wanene ta haɗe rai amma koda ganin commender James sai ta waro idanu cike da mamaki ta ambaci sunan shi, "Sir James, is that you? I'm surprised," ta faɗa tana yar dariya


 Sir james ya ce, "It's me, dear. Yesterday when we called, I hid the point of my coming because I wanted you to be surprised." 



Murmushi ta sakar mashi, "I welcome you wholeheartedly I'm at a loss for words to express my happiness and how much I've missed you."


 "I've missed you too, dear one. I'm overjoyed to see you." Ya bata amsa.


Ya yi zaton za ta yi hugging na shi amma sai ya ga akasin hakan, Taj da Big guy kuwa tun rungumar farko da commender yayi mata suka kalli juna, dama sun san za'a rina tun da su dabi'ar su ce yin hakan, a kan sofas suka zauna gaba dayan su, nan fa ex-prisoners suka fara cika su da surutu suna basu labarin abubuwan da suka faru bayan dawowar su Nigeria, suna tsaka da yin fira Chief Ya sauko down shima ya kimtsa tsaf cikin suit nasa, suna ganin shi suka miƙe da sauri commender ya nufe shi suka rungume juna a mutunce suka gaisa ya yi mashi barka da zuwa, kafin ya nufi sauran sojojin ya miƙa masu hannu suka gaggaisa.


Kowa na gidan tun daga kan Gate security Officers har Chefs na kitchen saida suka shigo falon domin yi ma baƙin Chief barka da zuwa, hakan ba ƙaramin faranta ransu yayi ba ganin yadda kowa ke ɗokinsu sai girmama su ake.


Batare da bata lokaci ba, Chefs suka shirya masu dinner a dining, duk girman table ɗin saida suka cika shi da kayan abinci kala kala.


Yau gaba ɗayansu su ka yi dinner a tare da baƙin su, gwanin ban sha'awa su commender sun ji daɗin karramawar da akai ma su, abun da yafi burge su yadda prisonsers suka saki jiki da su kamar irin sun haɗa alaƙa ta jini da su, hakan yasa suma suka samu walwala kamar suna a gidajen su na America, ga jemimah da ta yi ta basu nishaɗi da surutunta, ta maida commender kamar kakanta, har abinci take bashi a baki, ta yi kane-kane akan laps din shi, Danish kuwa hankalinshi na akan Unaisah ya lura kamar akwai wani abu dake damunta saboda yadda take cin abinci kaɗan kaɗan kuma hankalin ta yafi karkata akan daddynta saboda shine damuwarta.


Bayan sun kammala cin dinner ɗin, wata sabuwar firar ce ta 6arke a tsakanin sojojin da su Chief har kusan ƙarfe goma kafin Big guy ya raka su masaukin da za su zauna, duk yadda Unaisah taso ta gana da daddynta a daren ranar abun yaci tura tana ta jiran zuwan shi tasan ya saba duk in yana gidan dare yayi sai ya zo dakinsu yayi mata sallama kafin ya tafi amma yau taji shiru, koda ta fito bata iske kowa a falon ba, shima yayi tafiyar shi, da damuwa ta kwana a ranta.



Gidan Kurkukun Ƙaddara🔥

_____________________________✍️



Meke faruwa a gidan kurkukun ƙaddara? Saboda gabatowar gagarumin shagalin da zasuyi na black Night, sun fara shirye-shiryen tarbar wannan dare mai daraja a gurin su, Yanzu sun dakata da yin duk wani mugun abu da suke yi a gidan kurkukun, hatta fursinonin su sun yi mamakin sauyin da suka gani, lafiyayyan abinci suke basu mai rai da lafiya har sau uku a rana, bayan haka sun tsaftace ɗakunan prisoners din da makewayin su sun kuma canza masu sabbin Uniform.



Duk da sauyin da suka samu, hakan bai saka su yin murna ba, saboda sun san da wata manufa a ƙasa, wata wutar bala'en ce zata kunno kai, kamar ko sun sani dalilin dayasa suka sauya masu cimarsu daga ganye zuwa lafiyayyan abinci mai gina jiki, saboda albarkatun jikinsu su cicciko suyi ƙiba fatarsu tayi kyau don su ji daɗin aikata fasiƙanci da su, a cikin abincin da ake kawo masu hada wata kwayar sihirin da suke saka masu a cikin dafaffen kwai, kamar sha ka fashe take aiki a jikin ɗan adam walau mace ko namiji, cikin kankanin lokaci Yake ciko da duk wata ramar jikin su ya ha66aka jinin jikin su.


Lallai Elders Sun shirya ma Black Night..💔



Yau gaba ɗaya Sun fiddo da Prisoners din dake a kurkukun zuwa tsakar prison din, ko ina ka kalla sune birjik, sun jera layi, as usual jajayen uniform ne a jikin su, a yanzu babu masu black Uniform na ƴan baiwa tun daga kan su Unaisah.


A ƙalla fursinonin da suka rage agidan kurkukun ƙaddara zasu kai kimanin ɗari uku da hamsin, daga ciki harda jariran da suke raino.


Yan matan suna asanye da short gown wadda bata wuci gwuiwarsu ba, mazan kuma riga da wando ne ajikin su, babu mai magana a cikinsu kamar gumaka sun ƙame a tsaye ko motsi basa yi, Iya ƙwayar idanun su ce kadai take kyakkyaftawa sai numfashinsu dake fita.


Bakomai ne yasa suka nutsu ba, fa ce Giants ɗin dake a kewaye da su, Wasu irin gabza-gabza masu jini a jika.


sun kasa sun tsare sai suntiri suke umarni kawai suke Jira su aiwatar.


Cikin takun Izza Tsohuwa Inno ta nufo gurinsu hannun ta ruƙe da sanda, kamar kullum a cikin shiga ta red gown take, daga bayanta Giants ɗin dake take mata baya ne, kan matakalar benan dake fuskantar prisoners ɗin suka dakata da yin tafiya, ta tsaya tana bin su da ƙasƙantaccen kallo.


har na tsawon mintuna batare data furta kalma ba, sai da ta mula ta sha iska kafin ta fara magana a a gadaran ce


"Duk wanda na kira lamba ɗin shi a cikin ku, Ya koma gefe ɗaya" ta faɗa tare da nuna masu inda zasu tsaya da sandar hannun ta..


"Prisoner no twelve, Thirteen, Fourteen...' duk wanda ta kira sunansa, Jikinsa na kerma yake fitowa daga cikin layi ya tsaya gefe ɗaya, daga gani masu kyawun surar cikin su take zaƙulowa waɗanda suka zama matured.


Kusan fursinoni arba'in da takwas ta kira, mata sunfi yawa acikin su, saida ta kammala kiran lambobin waɗanda ta zaba kafin ta furta prisoner no 100 shiru ba'a amsa mata ba, da alama ta manta aika aikar dasa giant yayi mata, tsawa ta daka masu, "baku ji ina magana bane? Where is she?"


Murya na rawa wata young adult daga cikin su ta yi ƙarfin halin furta, "tun lokacin da kika sa Giant Ya tafi da ita, bamu ƙara ganin ta ba"!


Shiru tayi jim sai da yarinyar tayi magana kana ta tuna abun da tasa aka yi mata.


Giant ɗin dake a gefenta ta kalla, "Tana raye ko ta mutu?" Cikin girmamawa da wata irin buɗaɗɗiyar murya ya ce, "Bani da masaniya, bayan na kaita ɗakin fiɗa kamar yadda kika bani umarni, ban ƙara bi ta kanta ba"


Murmushin gefen fuska ta saki, "If she dies, I will be sad because I want her to witness the black night,

Even though I know even if she is alive, she will not be useful anymore." 



Cike da shaƙiyanci ta faɗa kafin ta sake ce ma giant ɗin,


"Ina ji a raina bata mutu ba, amma bayan da ka kaita ɗakin fiɗa ka tabbatar sun feɗe sassan jikin ta? Ta jefa mashi tambayar.


"Bayan na kaita ɗakin fiɗar, ban ƙara komawa ba, saboda ba hurumina bane"


Bata tsaya taji ƙarshen zancen nashi ba, ta juya cikin takun sauri giants din suka rufa mata baya.


bata nufi ko'ina ba sai dakin fiɗa, koda ta shiga ta tambayi Gigantes Medici ɗin dake a gurin game da Gabriella, basu iya tuna meya faru bayan an kawo ta ba, ta nemi su bata records na fursinonin  da su ka cire sassan jikin su, kwata kwata babu sunan ta.


Babu inda bata duba ba, kamar zata yi hauka, har records ta kar6a na dead prisoners nan ma bata ga sunan Gabriella ba, nan take zuciyarta ta raya mata cewa wani ya ceci rayuwarta.


Wani irin ƙululun baƙin ciki da takaici ne suka mamaye zuciyar tsohuwa Inno, tsabar fusata har wani hayaƙin huci take fitarwa ta kofofin hancin ta, rai a 6ace  ta furta, "duk inda kika shiga zan gano ki ne, koma wanene ya ceci rayuwarki yayi babban kuskuren da bazai iya kubcema azabata ba! " da karfi ta buga sandar hannunta tare da furta sunan Gabriellah da wani irin amon murya mai amsakuwa..



A matuƙar firgice Gabriella ta farka daga dogon baccin da ya ɗauke ta, kanta ne ya fara sara mata da ciwo.


da tafukan hannayenta ta daddafe kan, wani irin gumin zufa ne ya fara tsattsafo mata, Kakkausar muryar dattijuwarne ya fara dawo mata a cikin kanta.


_"Faɗa da aljani ba riba, wannan somun ta6i ne, nan gaba idan kika kuskura kika sake yunƙurin yi min rashin ɗa'a farfesun namanki zansa ayi min shashasha kawai_ 


waro idanunta waje tayi, bugun zuciyarta ya ƙarfafa, ta fara jan numfashi da karfi da karfi


_bakin ki ne ya ja maki! Nayi mamaki da har kika iya rayuwa, ai nayi zaton zan zo na same ki awargaje babu rai, amma saboda taurin kai har yanzu numfashin ki bai daina fita ba_ 


Fashewa tayi da matsanancin kuka tamkar ranta zai fita, cos she recovered her memory, ta tuna komai, abun ka game zuciya ta dinga buga kanta jigin karfen gadon har saida goshinta ya fara barazanar fashewa, wani tafarfasa zuciyarta ke yi mata saboda bakin cikin abunda dattijuwa inno tasa aka yi mata.


Ba dan Allah yasa tsohuwa khala ta faɗo dakin ba, da tuni Gabriella ta jima da kashe kanta, tana shigowa sautin kukan da take saki ya tari hanzarinta, ta waro ido waje tana kallon yadda Gabriella ke buga kanta, Cike da tashin hankali ta yi kukan kura tayi dirar mikiya kan gadon ta damƙi wuyan rigarta, ta jijjigata da hannayenta ta fara kokarin rarrashinta amma saboda bad temper dinta ta makance bata iya fahimtar komai da khala ke faɗa mata, sai kuka take tana fadin, "Let go of me! Let go of me! Why am I still alive? why didn't you kill me? You wicked oppressors, Jesus will never forgive you, you will all go to hell!


cikin fitar hayyaci take zazzaga masifa tana kokarin kwace kanta daga hannun tsohuwa khala don ta ƙarasa kashe kanta, tausayinta ne ya kama tsohuwa Khala duk da tayi mamakin zuciyar dake gare ta, in wani ne ya ga ya tsira zai zauna cikin salama ne amma ita so take ta kashe kanta ta karfi da yaji, da tasan zata dawo cikin hayyacinta da bata bar dakin ba, yanzu gashi tana neman ta dawo da hannun agogo baya, don bazata manta lokacin da ta ɗauka gurin yin jinyarta ba, har ɗinki sai da tayi mata a gabanta saboda raunin da taji.


Allah ne ma ya nufa zata rayu don da wuya giant su kwanta da mace ta tashi da lafiya batare da ta haukace ba ko ta mutu.


Kamar zasu yi dambe ita da Khala,  saboda ta sanya karfi dama Allah yayi ta da ƙarfi kamar doki, da ƙyar khala tayi nasarar buga kanta jikin pillow ta tamurshe ta, ta yadda numfashinta bazai rasa hanyar fita ba, kasa ɗagowa ta yi da kanta saboda khala ta tokare kanta da tafin hannunta, zafafan hawayene suka fara yar tseral kan kuncin ta, cikin disasshiyar murya ta furta, "Bana so na mutu, kada ki kashe ni, Ina son ganin ɗan uwana Gabriel," Wata irin mahaukaciyar dariya tsohuwa khala ta kwashe da ita tuni jikin Gabriella yayi sanyi lakwas.


Da kakkausar Murya khala ta ce, "Kinsan baki son ki mutu me yasa kike kokarin kashe kanki? Yar ƙarama dake sai baƙar zuciya kamar ta kafuran farko! Dame kike taƙama ne? Ina karfin naki yake uhm!"? Nishi ta dinga yi tana huci kamar zata iya ta6uka wani abu.


Sassauta murya Khala tayi, "Ba duka muka taru muka zama ɗaya ba, kasancewata a gidan kurkukun ƙaddara, ba hakan yana nufin nima muguwa bace, kamar yadda kika zata, kinyi min mummunar fahimta, amma nayi maki uziri saboda bakisan komai dangane dani ba..."


 ta faɗa tana kallon idanun Gabriella da suka kaɗa jawur.


Numfasawa tayi kafin ta ɗaura da cewa, "Da ace ni muguwa ce da ban taimaki rayuwarki ba, nasan yanzu tunaninki ya dawo, dama abunda na ke gudu kenan saboda nasan za'a rina, yanzu da ban zo ɗakin nan ba da tuni kin jima da kashe kanki saboda ɗamsil basira, idan kina tunanin mutuwa mafita ce a gareki toh ki daina, shi jarumi ba'a san shi da karaya ba, kada ki zama raguwa ki zama jaruma mai iya tankwara zuciyarta me kuma burin ɗaukar fansar zaluncin da aka yi mata.


Tana jan nishi da ƙyar ta furta, "Who are you? Where did you find me? and Why did you help me?"



"Sanin wacece ni baida amfani, iya abunda zan iya sanar dake shi ne ba a haife ni a gidan kurkukun ƙaddara ba, bada son raina na kasance a cikin shi ba, ta karfi da yaji aka kawo ni nan, bazan iya misalta maki ƙunci da raɗaɗin da na ji a lokacin dana buɗe idanuna na tsinci kaina a gidan kurkukun nan ba, na ga musiba da bala'e da idanuna, abunda ban ta6a zaton ko a mafarki zanga makamancin shi ba, zuciyata a karye take saboda anci amanata an yaudare ni, bayan haka an nuna min fin karfi ba yadda na iya,...." idanunta ne suka ciko tab da kwalla.


"Kamar yadda kika so kashe kan ki, nima nasha yin yunkurin yin hakan amma idan na tuna menene makomata? Sai inji na gaza! Mutuwa bazata hana su cigaba da aikata fasadi ba, saboda su ɗin 6atattu ne in har bamu haɗa hannu mun kawo ƙarshen su ba, babu abunda zai canza na daga zaluncin da suke  aiwatarwa, bayan haka babban abunda yasa nake so na rayu shi ne ya'yana inason na sake ganin su ko da da numfashina na ƙarshe ne".


muryarta na rawa ta ƙare maganar, hawaye suka cigaba da sintiri kan fuskarta, Gabriella dake sauraran khala, itama hawayene kan fuskarta, tana da wuyar sha'ani a rayuwarta bata yarda da mutane amma karo na farko ta yarda da tsohuwa Khala, maganarta ta karya mata zuciya.


A hankali ta zame tafinta daga kan Gabriella, hakan ya bata damar miƙewa ta zauna da ƙyar tana duban fuskar khala da tausayawa


"Ke ɗan uwan ki ɗaya ne, ni kuma jikokina da suka salwanta agidan kurkukun ƙaddara yawa ne da su, inaji ina gani ban iya tsinana masu komai ba saboda an nuna min fin ƙarfi...." fashewa ta yi da kuka kamar ƙaramar yarinya.


Itama Gabriella din kukan ta fashe da shi saboda tausayin khala da ya mamaye zuciyarta ashe ita bata ga komai ba tayi mamakin haƙuri da juriyar tsohuwar da har ta iya kai tsawon lokacin nan bata haɗiyi zuciya ta mutu ba.


"Yau kimanin shekara ashirin cuf, rabon da in shaƙi iskar duniya saita gidan kurkukun ƙaddara, bani da burin da ya wace in tona masu asiri, kullum ne sai na roƙi Allah dare da rana ba fashi, duk da har yanzu ba wani sauyi, ban ta6a gajiyawa ba, saboda nasan Allah ne kadai zai iya cika min burina kuma yana sane dani, wani jinkirin Alkhairi ne kuma ina ji araina ƙarshen kurkukun nan ya zo" ta faɗa tana jan magina.


"Kin tambayeni Ina na tsinto ki?" A ranar bayan na fito daga fadar Elder naji ina sha'awar in kewaya kurkukun duk da bana so nayi tozali da abunda zai hanani kwanciyar hankali, har zan gifta na hango tsohuwa inno tare da giant din da ya ɗauko ki babu sutura a jikin ki raina ya 6aci ba kaɗan ba, nayi zaton ma kin mutu ne, kwatsam idanuna suka hango min yatsun ƙafarki na motsi, wani iko na Allah ni da bana shiga huruminsu bansan ya akai zuciyata ta azalzala min akan in taimaka maki ba, cikin sanɗa na bi bayan su, har suka aje ki a ɗakin fiɗa, tafiyar su ke da wuya, nayi 6adda kama ta hanyar amfani da sihiri na, na shiga cikin Gigantes Medici din batare da sanin su ba saboda hankalinsu ya karkata akan aikin fidar da sukeyi, kafin su zo kanki cikin abunda bai fi daƙiƙa talatin ba, na sace ki na kawoki ɗakina, na fara kokarin tsayar da bleeding din da kike yi kafin na dinke raunukan jikin ki...." tiryan tiryan khala ta zayyana mata komai, wani irin son tsohuwar ne ya kamata har batasan sa'ar da ta faɗa kan kirjinta ba, ta rungumeta cikin shesshekar ta furta, "Ki yi haƙuri nayi maki mummunar fahimta, ki yafe min"


Ɗan murmushi khala tayi kafin ta daura da cewa, "Tun kafin ki dawo hayyacinki na ji kina ambaton sunan ɗan uwanki Gabriel, na kwallafa rai a kan son sanin wanene shi? a cikin bookshelve ɗina ina da littafin register na fursinoni (Sijil al-sujna) a cikin littafin na buɗo ina bincikawa don inga wanene me suna Gabriel, ban sha wahala ba, saboda nayi nazari na gane cewa ku ɗin ba tsoffin prisoners bane cikin waɗanda aka kawo ne a ƙarshen shekara ta dubu biyu da ashirin da uku, cikin sa'a na ga sunayen ku, a fahimtana ɗan uwanki ne ko?..." cikin sanyin murya tace, "twin brother ɗina ne."


"Zaki iya tuna tayaya akai kuka tsinci kanku a gidan kurkukun ƙaddara?" Girgiza kai ta yi har lokacin bata raba jikinta daga na khala ba.


"Bazan iya tuna komai ba, ɗan uwana kadai na sani, pls ki taimaka min in gan shi..."  Shiru tsohuwa khala ta yi saboda tasan me zai biyo baya in har ta faɗa mata cewa baya a cikin kurkukun, cos ta ga sunan shi cikin list na escaped prisoners, ta lura da yadda take mugun son shi in har ta faɗa mata, zuciyarta zata karaya ne kuma zata ga kamar ya manta da ita ne shiyasa ya tafi ya barta batare da ya taimaki rayuwarta ba"


Ɗagowa tayi da kanta, "kinyi shiru baki bani amsa ba, bana so na rasa ɗan uwana, nasan yana cikin wahala kuma yana nemana, pls ki ɗauko shi ya dawo nan mu rayu atare"


Dafa kafadarta khala tayi, "Zan iya jefa rayuwarmu da tashi cikin haɗari, abunda yasa nake 6oyenki saboda a yanzu haka dattijuwar da ta kusa kashe ki, nemanki take ruwa ajallo, amma in har Allah yayi mana tsawancin kwana gaba na yi maki alƙawarin zan hadaki da ɗan uwanki..."


cikin karyayyar murya ta ce, "ya mutu ko"? Girgiza kai tsohuwa khala ta yi, "A'a yana raye, "


"Ta ya kika san yana a raye"?


"Zan nuna maki"


Ɗaga mata kai ta yi alamar toh, saukowa suka yi daga kan gadon, ta ɗauki sandar ta, ta nufi gurin furannin dake a ɗakin, Gabriella tana a biye da bayanta, da sandar ta nuna mata fure kore shar da shi a cikin wata tukunyar shi mai kyan gaske. 

 

"Ɗan uwanki yana a cikin ƙoshin lafiya, kin gan shi nan" aruɗe ta dubi khala, "tayaya hakan zai yiwu! Mutun ya zama fure??"


Dariya khala tayi, "It's a magic trick kema idan naso sai in mayar dake fure, Ko kina da ja ne?" Ta faɗa da zolaya, da sauri ta girgiza kai, 


Zuƙunnawa tayi a gaban furen ta ƙura ido tana kallon shi, cikin sanyin murya ta furta sunan shi abun mamaki sai ta ga furen ya motsa ganyayyakinsa kamar iska ta kaɗa shi.


Murmushi ta saki,"Da gaske kaine?" again ya ƙara motsa ganyen shi, wani daɗine ya lullu6eta har ta buɗe baki zata ƙara magana kwatsam ba zato ba tsammani taji kamar an jeho mata wuƙa a kirjin ta,


dafe shi ta yi da hannun ta, radadi ya hana ta motsa, nan take ta fara yin aman jini,


Hankalin Khala kwata kwata baya akanta batasan meke faruwa da ita ba, saboda tayi zurfi acikin tunanin ta, sai kokari Gabriella take ta ruƙo rigarta amman ta kasa saboda kermar da yatsunta ke yi....🥺


__________________________________✍️


*BENAZIR💔*


Suna a zaune kan darduma su biyu ita da Zeenatu, sun haɗa baki suna karatun kur'ani da suka buɗe akan qur'an stand


Wayar tace ta fara ringing, bayan takai aya ta dakata da yin karatun ta miƙe da sauri ta nufi wayar dake ajiye saman gadonta


"Aunty Benazir, Azeezaty ne?" Zeenat ta tambaya tana kallon ta


Bata ba ta amsa ba, har saida ta dauki wayar, ta dubi sunan me kiranta, tayi mamakin ganin sunan Uncle ya bayyana yau wata rana Alhaji musa ya kira ta, a ranta ta furta Allah yasa alkhairi ne.


Ɗaga kiran ta yi ta kara wayar a kunnanta, tana kokarin yi mashi sallama ya katse ta da cewa, "Ki same ni a garden yanzu" amsa mashi ta yi da toh. 


Aje wayar tayi gaban mirror, ta juya suka haɗa ido da Zeenatu ta ƙura mata ido tana kallon ta. 


"Daddynki ne ya kira ni, ki cigaba da yin karatun yanzu zan dawo" tace toh"


Bayan fitar Benazir, cike da zumuɗi ta miƙe, ta ɗauko wayar Benazir ta fara laluban layin Azeezaty, sam ta kasa ganowa saboda batasan sunan da Benazir tay mata serving ba, amma da ta tuna Benazir ta fada mata jiya ta kira layinta bata samu ba, hakan yasa ta shiga call logs, lambar farko da akai ma saving da God Gift ta danna Call almost 3 times tana kira baya shiga, ba dan ta so ba ta hakura.


Lokacin da Benazir ta ƙaraso Garden ɗin tunkan ta ƙarasa idanunta suka hango mata mutun uku zaune kan lallausar darduma kowannan su shadda ce a jikin shi.


bata iya tantance su wanene ba, saida ta isa wani irin burki ta ci ta dafe ƙirjinta da hannu ɗaya da tsantsar mamaki ta furta, "ZAKI!" 


Yana Jin muryarta da sauri ya ɗago ya kalle ta, zumbur ya miƙe tare da ambaton sunan ta "Benazir!"


Hawaye ne suka ciko idanunta, tayi mamakin ganin shi, kuma tayi farin cikin ganin bawan Allahn nan ba zata ta6a manta halaccin da yayi mata ba..


Gaba ɗaya hankalin Sir mubarak, da na Alhaji musa ya dawo kan su, Sir mubarak na ganin Benazir a ranshi ya ayyana yanzu ya gane dalilin da yasa Zaki ya ruɗe akanta, da alama dai Sir Mubarak ya yaba da kyanta.


Jinjina mashi kai tayi, "Yayana ni ce,"


Cikin sanyin murya ya ce, "Benazir baki kyauta min ba, kinsan irin tashin hankalin dana fuskanta saboda rashinki a kusa da ni.. " bai kare maganar ba, Sir Mubarak ya yi mashi gyaran murya atare suka kalle shi.

Cikin sauri Zaki Ya gabatar mata da Daddynsa, Cike da jin kunyarshi ta gaishe da shi, fuskarshi a sake ya amsa mata, tare da yi mata fatan alkhairi.


"Benazir, ki shiga da shi ciki." Alhaji Musa ne ya faɗa fuskarsa a sake kamar ba shi ba, amsa mashi ta yi da toh, bata yi aune ba ta ji ya ruƙo hannunta a cikin nashi kamar yadda ya saba yi lokacin da suna tare.


Fita su ka yi daga garden din, yace mata ba zai shiga gidan ba, yafi so suyi magana a cikin motarsa, ya buɗe back seat na motar shi yace ta shiga, ji ta yi bazata iya yi mashi musu ba hakan yasa ta shiga ta zauna bayan shima ya shiga ya datse car door din, suka Ƙurama juna ido kamar yau suka fara haɗuwa, sunyi kewar junan su sosai.


"Da ranki da lafiyarki Benazir, baki neme ni ba, kamar kin manta dani a rayuwarki, baki yi tunanin damuwar da zan shiga ba, kin tafi kin barni da kewarki kullum zullumina kina ina? Kin isa gidan iyayenki lafiya ko kuwa?" 


Siraran hawaye ne suka wanke fuskarta, bata ji dadin halin da ta jefa shi ba, tasan shaƙuwar dake tsakaninsu dole ya damu da ita.. 


"Ka yi hakuri Yayana na kaina, wlh kana a raina, ban manta da kai ba, kamar yadda ka damu da ni nima haka na damu da kai..." katse ta ya yi, "Amma meyasa ba ki neme ni ba?


"Ka manta wayata tana a hannunka?"


"Ba hujja bace Benazir, kin riga da kinsan wanene mahaifina a ƙasar nan, kinsan family estate dinmu, why baki je can kin neme ni ba in har dagaske kin damu dani?"


Fuskarshi a yamutse ya yi maganar, kwarjini ya yi mata ta sunnar da kanta ƙasa, tasan bata kyauta mashi ba..


"Me nayi maki dana cancanci hakan daga gare ki? Ko kin daina ƙaunar yayan naki ne?" Yanayin yadda yake magana ba ƙaramin karya mata zuciya yake yi ba, ga kamshin turarenshi da ya kanainaye hancin ta.


Da ƙyar ta furta, "Na kar6i laifina, ban kyauta maka ba, amma ka yafe min, bazan ƙara maimaita kuskuren da nayi ba." Lumshe idanunshi yayi tare da sake buɗe su kan fuskarta, matsawa yayi dab da ita da sauri ta ja da baya, har saida ya ƙureta jikin murfin motar .


Shafa fuskarta ya yi da tafin hannun shi, yana kokarin haɗe bakinsu ta yi saurin kauce mashi, hakan ba ƙaramin ɗaga hankalin shi yayi ba, saboda ta sauya mashi.


"Kin canza min, meyasa?" Muryarta na kerma ta ce, "Yayana ka yi haƙuri, ba halina bane, ko a lokacin da nake amince ma hakan bada son raina bane, sai don bani da mafita ne, kewar mijina ne yasa nake biye maka saboda in samu relief..." wani irin kishi ne ya ziyarci zuciyar shi, idanunshi suka kaɗa nan da nan suka fara yin ja...


"Kin haɗu da mijin naki?"


Ɗaga mashi kai ta yi alamar eh,


Hankalin shi idan yayi dubu toh ya tashi, damuwa ce ƙarara kan fuskarshi, ita kanta ta sha jinin jikinta da ganin yadda numfashin shi ke fita.. 


"Tayaya akai ka gano inda nake?"


Da ƙyar ya furta, "Uncle ɗinki, abokin Daddyna ne,..." ta yi mamakin jin hakan.


A takaice ya bata labarin tun farkon dawowarshi abunda Ya faru har zuwa lokacin da Sir Mubarak ya kira Alhaji musa ya fada mashi lokacin da zasu zo ganin ta ..." 


ƙiris Ya rage ta fashe da kuka saboda tausayinshi da ya kamata, bata ta6a sanin yana sonta ba sai yanzu da ya ke faɗi mata, tayi mamakin zurfin cikin shi...


Ruƙo hannayenta ya yi acikin nashi.


"Ki taimaki rayuwana, ban saba da wahala ba, bansan menene so ba, sai akan ki, ke shaida ce, mata basa a gabana, aikina kawai nasa a gaba, wlh bazan 6oye maki ba tun rana ta farko da na fara ganin ki naji na kamu da ƙaunarki, shiyasa koda kika faɗamin kina so ki yi nesa da kowa naki ban yi maki faɗa ba, saima nayi maki hanyar da zamu bar ƙasar atare saboda idanuna sun makance akan sonki, a ranar da kika faɗamin kina da aure, ban runtsa ba saboda hankalina ya tashi kuma duk da sanin hakan ban ji son ki ya ragu ba saima ƙaruwa...." 


dafe kanta ta yi da tafukan hannayenta, ta rasa ina zata tsoma ranta taji daɗi, kalaman Zaki sun tsuma zuciyarta da tausayin shi, ba dan Taj ba da ba abunda zai hana ta amince mashi saboda gayen ya haɗa komai da mace zata buƙata a gurin namiji, sai dai kash bata jin zata iya rabuwa da Uban ƴarta.


Muryarta na rawa ta ce,"kai ne ka tura ma mijina saƙon ya sake ni?"


Girgiza kai ya yi, "Ba ni bane, bazan iya aikata hakan ba." numfashi ta ɗan ja, kafin ta runtse idanun ta, ya zuba mata ido yana kallonta kamar zai hadiyeta saboda tsantsar son da yake yi mata...


"Daddyna ya bani goyon bayan in nemi soyayyarki, In har kika amince min zai yi magana da iyayenki, on friday za'a ɗaura mana aure, Next week zan koma dake Canada, na yi maki alƙawarin ba zaki ta6a danasanin aure na ba, kin riga da kinsan wanene ni kin san halina, kuma ko bayan auren bazan hana yarinyarki ta zo inda kike ba, har shi kanshi ex-husband din naki bazan raba zumuncin dake tsakanin ku ba..." 


Kuka ne ya kubce mata, hakan ba ƙaramin ɗaga hankalinshi ya yi ba, bazai juri kallon hawayen ta ba, da sauri yayi hugging dinta, halin da take a ciki ya hana ta kwace kanta daga gare shi.


Cikin shesshekar kuka ta ce,"In har da gaske kana so na kuma kana son farin cikina, to ka barni in rayu da mijina, wallahi bazan iya rayuwa da wani ɗa namiji in ba shi ba, ba dan ƙaddara ta raba ni da shi ba, babu abunda zaisa na juya mashi baya, ko dan darajar ƴar dake tsakaninmu bazan Iya rabuwa da shi ba..." 


kusan suman zaune yayi jin maganar ta, raba jikinta ta yi daga nashi, fuskarta ta jiƙe sharkaf da hawaye taci gaba da cewa, "Ka taimaki rayuwana, ka rufa min asiri, in har taimakon da kayi min kayi ne don Allah, toh ka haƙura da ni, mu cigaba da zumunci har ƙarshen rayuwarmu, amma maganar aure babu ita tsakanin mu..."


Maganganunta sun karya mashi zuciya, wani irin zafi ne ya mamaye jikinshi, duk da sanyin A.c din motar hakan bai hana shi fitar da gumi ba.


kifa kanshi ya yi kan kafaɗarta yana ambaton Inna lillahi wa'inna ilahirraji'un, Allahumma ajirni fi musibati wa akhlifni khairan min ha..." sambatu ya ci gaba da yi kamar ya fara zaucewa..


Tasan irin radadin karya zuciya ba kowa ke iya jurar shi ba, fargabanta kada tayi silar da Zaki zai rasa rayuwarsa amma ya zata yi? Bata da mafita da ya wuce ta lallashe shi taci gaba da bashi hakuri...


"Yayana nakaina, matsayinka bazai ta6a canzawa agurina ba, bazan ta6a juya maka baya ba, ina jinka tamkar ɗan uwana na jini, ina mai takaici ƙin amsa bukatarka, bawai don baka kai in aureka ba, wlh kowace mace zata yi burin ta auri namiji jajirtacce nagari irinka, saboda ka haɗa duk wasu kyawawan dabi'u da halaye wanda zaisa mace ta so ka, sai dai kash Allah bai kaddara kaine mijina ba, muyi haƙuri mu rungumi kaddara, zan tayaka da addu'a Allah ya baka mace tagari, wadda zata maye maka gurbina...." cikin karyayyar murya ya furta, "Benazir bazan Iya rayuwa batare dake ba, zan roƙi Allah ya dauki raina in huta da radadin rasa ki da nayi" da sauri ta ce,"In sha Allah bazan zama silar da zaka mutu ba, sai dai in zama silar farin cikin ka na har abada, zan tayaka da addu'a Allah ya baka ikon cinye jarabawar soyayyata, Allah ya cire maka sona acikin zuciyarka..." cikin rawar murya ta ƙarashe maganar.


shiru yayi bai ƙara magana ba, sai bugun zuciyarsa da take ji a jikinta.


"Alfarmar da zan roƙa a gurinka, don darajar manzon Allah SAW, ka rufa min asiri yayana nakaina, kada ka faɗama Daddynka komai da ya faru tsakanin mu, saboda zai iya sanar da Uncle ɗina shi kuma zaiyi min dole ne, nasan bazaka so abunda zai 6ata raina ba..." wani irin zazza6i ne ya lullu6e jikin shi, kamar ya fasa ihu haka yake ji, So bala'ene, duk maganganunta akan kunnanshi sai dai ya kasa furta kalma.


Shafa sumar kanshi tayi da tafin hannunta cikin sigar lallashi ta ci gaba da kwantar mashi da hankali maimakon yaji sauƙi a ranshi saima yaji kamar tana ƙara rura wutar sonta a zuciyar shi..


Tayi fatan ace zata iya share mashi hawayenshi ta aminta da auren shi sai dai kash bazata Iya ba, kamar yadda yake jin azabar sonta itama haka take jin azababbiyar soyayyar Taj, duk namijin da zai aure ta sai dai ya auri gangar jikinta amma ruhinta yana agurin Taj.


Bayan wani lokaci, ta fito daga cikin Motar, da gudu ta nufi cikin gidan tana shiga daki bata iske Zeenatu ba, saman gado ta faɗa ta rushe da matsanancin kuka tamkar ranta zai ita.


Hanky ya zaro daga front pocket dinsa ya share fuskar shi,  saboda baisan daddynsa ya gano abinda ya faru da shi, saboda yayi mata alkawarin zai rufa mata asiri, ka ji masoyi na gari samun irinsu zaiyi wuya aduniyar nan.


Zaki mutum ne mai haƙuri ga tawakkali.


Bayan ya goge fuskar shi, Ya rufe murfin motar, ya zaro shades ya sanya ma idanunsa.



Bayan tafiyar Benazir da yan mintuna Sai ga Sir Mubarak da Alhaji Musa sun fito daga garden din gidan, fuskokinsu ɗauke da fara'a da alama sun ji daɗin firar da suka yi.


"Naji daɗin karramawar da aka yi mana, yanzu sai yaushe mahaifin nata zaizo Abujan ko mu zamu je can Jos dinne? cos ina son ganawa da shi game da zancen auransu"


Alhaji Musa ya ce, "kada ka damu, basai kunje can ɗin ba, tun da har ni na amince da aurensu, shima zai amince ne." murmushi Sir Mubarak yayi, "Mutumina ka faranta raina, Allah ya ƙara dankon zumunci a tsakaninmu," Ya amsa mashi da ameen.


"Ba zaka shiga ciki ka gaisa da madam ɗina ba"


"Ban shirya haɗuwa da surukata ba, sai zuwa na gaba in sha Allah." Ya faɗa yana bin compound din da kallo yana ci gaba da yin murmushi.


Fitowa Zaki ya yi daga motar, fuskar shi da fara'a ya ce, "Daddy, mun riga da mun gama magana da ita, harma ta koma ciki."


Farin ciki ne ya lullu6e Sir Mubarak, 


"Uncle, ina godiya da damar da ka bani, Allah ya ƙara girma da ɗaukaka" ya faɗa yana kallon Alhaji musa, 


Murmushin gefen fuska ya sakar ma shi, "Kada ka damu, na dauke ka kamar ɗana, komai zan iya yi saboda farin cikin ka." 


Bayan sunyi sallama da juna, Alhaji Musa Ya koma gidan, su kuma suka shiga motar su.


Kwata kwata Sir Mubarak bai lura da yanayin fusakarshi ba saboda shades din da ya sanya ya rufe idanun shi ya hana yaga eye balls dinsa waɗanda suka kada jawur tamkar garwashin wuta.


"Bani labari mana my son, ya kuka yi da ita?"


Shiru yayi jim kafin ya cije ya ce, "ta amince Daddy, "


"Alhamdulillah, yanzu da yaushe zamu zo nema maka auren ta?"


Tamkar baison furta maganar ya ce, "Ba yanzu ba daddy, mun yi da ita sai bayan na sake samun hutun aiki zan zo Nigeria sai a ɗaura mana auren" farin cikine ya cika Sir Mubarak.


"Ina tayaka murna my son, ni dama nasan da wuya a samu macen da zata yi rejecting dinka, saboda kai din na musamman ne." Murmushin takaici ya ƙaƙalo kan fuskar shi ba tare da ya iya furta kalma ba, a ranshi ya riga da ya yanke shawarar barin ƙasar gobe, kwara ya nisanta kanshi da ita in ba haka ba zai iya zaucewa.



*MEETING ROOM*



Around ƙarfe 11 na safe hamshaƙan motoci suka fara kurɗaɗowa ta entrance gate din Isod headquarter, jigunannun gaske da matsakaicin gudu suke tururuwar shigowa a jere har kusan guda shida, kowace mota tana da tinted.


A parking space motocin su ka yi parking, a hanzarce Jami'an dake sintiri su ka yi saurin ƙarasawa bakin car doors ɗin suka bubbuɗe masu kofar....



Chief Owais ne ya fito tare da Big guy, motar bayan tasu Senior agents ɗin su ne.


Bayan su sai Commender james  Ya fito shima tare da sauran sojojin da suka zo, kowannansu yana asanye da kakinsa.. 


Motar ƙarshe General ɗin sojoji ne.


A gaggauce Jami'an dake kewaye da su sukayi hanzarin buga kafa tare da sara ma su cikin girmamawa suka gaishe da su kamar zasu zuƙunna masu tsabar ladabi.


Basu tsaya 6ata lokaci ba, Cikin takun dattako suka nufi Secure operation center duk inda suka gifta sai ƙamshin turarensu ya gauraye da iskar gurin daddaɗan gaske, kuma duk hanyar da suka bi jiki na 6ari jami'an dake a gurin ke sara masu, sai dai kawai su ɗaga masu hannu alamar sun kar6i gaisuwar tasu.


Bayan sun hau lift ta sauke su a third floor, A bakin awani Katafaren Meeting room (ɗakin taro na sirri) wanda gaba ɗayan shi a kewaye yake da zallar glass launin blue sky, wanda ke a waje bazai iya ganin na ciki ba, bayan haka bangon gilashin ɗakin soundproof ne irin wanda ke hana sauti fitowa waje, duk wani abu da za'a tattauna iya cikin ɗakin sautin ke tsayawa na waje bazai ta6a iya ji ba..


Gaba ɗaya sun nutsu suna jiran kofar ta buɗe ma su, biometric authentication ce sai ta tantance mutun kafin ta bashi iznin shiga..


Tafin hannu Chief ya ɗaura kan saitin na'urar ta yi screening din shi ta haska kwayar idanun shi kafin ƙofar ta fara sliding slowly har ta ƙarasa zuge kanta..


Walking majestically suka fara shiga ɗaya bayan ɗaya cikin katafaren Meeting room din, U.s armies din dake a tare da su sai faman jinjina kai suke saboda ƙawatuwar dakin taron yayi matuƙar burge su, cos ba su tsammaci zai kai haɗuwar meeting room ɗin su na America ba, wata irin ni'imtacciyar iskar A.c ce mai fita da ɗumi ta fara ratsa hudojin gashin jikin su irin mai sanyaya zuciyar mutun ta kwantar masa da hankali yaji shi a wata duniyar daban.


Wani katafaren zunguraren table ne a tsakiyar ɗakin shape ɗinsa kamar rectangle ya ke iya jikinshi abun burgewa ne sai salƙi da daukar ido yake, ga wasu high-end Chairs kewaye da shi  ga wasu haɗaɗɗun Microphones da Laptops a gaban kowace kujera, bangon dake fuskantar table ɗin wani tafkeken large screen ne.



Komai na yin meeting an tanade shi a ɗakin.


A tsanake kowannan su ya ja kujera ya zauna, suka fuskanci junan su, bayan sun daidaita nutsuwarsu ɗakin yayi tsit na ɗan wani lokaci, kowa da abunda yake saƙawa acikin zuciyar shi...


Abu na farko da suka tsara yi ma junansu barka da zuwa da kuma gabatarwa..


Dakin taron ya yi tsit a daidai lokacin da Chief Owais ya miƙe daga kan kujerarsa tare da tawagarsa, domin fara gabatar da kan shi cikin dattako ya fara magana yana duban kowannansu....


"Good morning everyone, i'm director Owais Sharafudeen Obinna, the Chief of Isod, With me are my team members," ya faɗa tare da yin nuni da su,


"Deputy Director General Omar Musa Wadata, Chief of Operations Ahmad Hassan, Chief of Intelligence Commander Haroon, and Senior Agents Dr. Zarah Saeed, Agents Ethan Kim and Jabeer Osman."  


yanayin yadda yake gabatar da su ba ƙaramin burge su yayi ba komai nashi cikin aji yake yin shi, duk wanda ya ambaci sunanshi zakaga ya saki ƙayataccen murmushi kan fuskar shi..


"Muna yiwa kowa barka da zuwa" ya fada tare da komawa kan kujerarsa ya zauna suma duk suka zauna.



The next person General Noah ne wani bayerabe baƙi mai jiki ya miƙe yana gyara necktie ɗinsa,


"Hello everyone, nice to meet you all, I am General Noah the General Officer Commanding the Nigerian Army, It's an honor to be here today." ya faɗa fuskar shi da murmushi kafin ya koma ya zauna.


Cike da kwarin gwuiwa Commender James Ya miƙe tare da tawagarsa su shidda,



"Hello everyone, I am Colonel James, the U.S. Commander of the Joint Task Force. I am joined by my team.." ya faɗa tare da nuna U.s armies din dake gefen shi,


Ya fara zayyana sunayen su,


"Major Smith, Captain Lewis, Canal herry and Lieutenant Thompson tare da Jackson lee, munayi ma kowa barka da zuwa, mun ji daɗin gayyatar mu da ku ka yi" gaba daya sunji dadin gabatarwar da yayi bayan sun zauna ɗakin yayi shiru na ɗan wani lokaci.



Kafin Chief ya numfasa calmly ya cigaba da kora jawabi, "Thank you, everyone, Let us proceed with the agenda, we are gathered here today to discuss a grave and urgent matter, already mun riga da mun san abun da ya tara mu, dangane da yaran da sojojin America suka tsinta a dajin Evil forest suka damƙa case dinsu a hannun hukumar mu ta Isode..."


 gaba ɗaya sun nutsu suna sauraron shi hadi da kallon fuskar shi,


Ɗan dakatawa yayi kafin ya daura da cewa, "...bayan bincike da hukumarmu tayi mun samu bayanai daga gurin yaran, wato wasu miyagun matsafa ne suka ƙirƙiri wani gini a karkashin ƙasa wanda suke kira da Gidan Kurkukun kaddara! Inda suke kulle mutanan da basu ji ba basu gani ba ta ƙarfi da yaji suke killace su, anan suke aikata duk wani fasadin su.." gaba ɗaya hankalin Jami'an ya karkata akan shi cos ba komai suka sani dangane da yaran.


"But that's not all, bayan ƙuntata rayuwar yaran, suna azabtar da su azaba mai raɗaɗi, ta hanyar yin amfani da karfin sihirin su gurin sarrafa su, su yi amfani da su ta ƙarfi da yaji..."


"But that's still not the worst of it. They use these innocent children as sacrifices for their dark magic rituals, draining their blood and exploiting their suffering for their own gain. And, tragically, they have been known to target young girls during their period, subjecting them to... unspeakable atrocities..."


kasa ƙarasa maganar yayi saboda takaici da baƙin ciki da ya mamaye zuciyar shi, tuni gumi ya fara tsartsafo mashi akan fuskar shi,


haɗa ido su ka yi da commender kasancewar suna fuskantar juna, tun daga kan yanayin yadda ya ƙura mashi ido ya fahimci maganar da yayi tayi matuƙar girgiza shi, a ƙagare yake da son jin karin bayani, hatta sojojin sun yi matuƙar girgiza da jin maganar kurkukun ƙaddara.


Mamakinsu wai har za'a samu yan adam da zasu iya shirya mugunta da zalunci a ƙarƙashin ƙasa na tsawon lokaci batare da asirin su ya tonu ba? 


"Owais, kai muke sauraro, Muna bukatar ƙarin bayani daga gurin ka." General Noah ne ya yi maganar...


Cikin sanyin murya ya amsa mashi da Okay, kafin ya kunna laptop din gabanshi ya fara operating ɗinta nan take large screen ɗin dake a jikin bangon dake fuskantar su ya kawo haske kamar tv nan take ya yi displying video ɗin su Unaisah a  Questioning room wato ɗakin tambayoyi, lokacin da suke bada bayani dangane da rayuwarsu agidan kurkukun ƙaddara komai da suka tattauna camera ta naɗe shi.


Yayin da suka nutsu suna sauraron tattaunawar su, wata irin zufar bacin rai da tashin hankali ce ta wanke goshin su kamar ba A .c a dakin, wlh sun yi matuƙar kiɗima da jin labarin kurkukun ƙaddara da kuma irin mugunyar azabar da ake yi ma matasan yaran da basu ji ba basu gani ba... tsabar fusata da baƙin ciki da takaici yasa jikin commender ya fara tsuma yana zubda gumi.


Bakomai yafi Karya masu zuciya ba face Labarin Unaizah da Majnoon duk irin dauriyar Soja saida ruwan hawaye suka cika idanuwansu kamar zasu fashe da kuka, 


Dunƙule hannu General Noah yayi ya dinga bugun gaban table din yana cizon lower lips dinshi, saboda tsabar fusata.


Commender James kuwa da shi da tawagar shi tsantsar mamaki da al'ajabi Ya hana su ko motsa, sai faman jinjina kawunansu suke yi al'amarin ya girmi tunaninsu, su mamakinsu yadda har matsafan suka share tsawon lokaci suna aikata 6arna a ƙasa batare da an iya kama su ba, a ganinsu sakacin shuwagabannin ƙasarne da kuma waɗanda keda alhakin kula da tsaron ƙasar" 


Jikin kowannansu yayi mugun yin sanyi lakwas, ɗakin taron yayi tsit baka jin sautin komai saina muryoyin su Unaisah.


Murya na rawa General Noah Ya furta"Owais, I can't believe what I'm hearing. Am I not dreaming? What cruelty and evil? I have never heard of such a thing before! a kasar nan wannan tashin hankalin ke faruwa batare da saninmu ba? Toh meye amfaninmu? Nayi danasanin mukamin da nake dashi tun da har ban iya kawo karshen ta'addanci a kasar nan ba, bamu ba al'umma tsaron da ya dace ba..."bai ƙare maganar ba saboda ƙululun baƙin cikin da ya tokare maƙoshin shi. da sauri Canal dake gefen shi ya dafa kafaɗarshi cikin sigar lallashi ya fara ƙoƙarin kwantar mashi da hankali.


Cikin sanyin jiki chief Owais Ya zaro hanky daga front pocket ɗinsa Ya miƙa ma general Noah ganin yadda yake zubda gumi yatsun hannunsa na kerma Ya kar6a ya fara share hawayen dake sintiri kan kuncin sa..."


"Owais lamarin Ya ɗaga hankali na! Wai dagaske ne Yana faruwa?"


Commender James ne ya yi maganar tsabar ruɗin tashin hankali yasa shi jin al'amarin kamar almara.


Jinjina mashi kai ya yi alamar eh ba tare da ya iya furta kalma ba.."


Gaba ɗaya saida ya kunna masu videos ɗin prisoners lokacin da aka zo kan nasu Jemimah kifa kai general Noah yayi kan table ɗin kamar zai fasa ihu saboda tsananin tausayin yaran, kukan zuci yake mai azabar radadi.


Babban abun takaicin da ya haddasa matsananciyar damuwa a zuciyarsu yadda matsafan suke lalata rayuwar ƙananun yaran saboda rashin imani a lokacin da suke tsaka da raɗaɗin ciwon cikin jinin al'ada.


Bayan haka sun karaya da jin irin kullan da suke yi masu tun suna jarirai babu shige babu fuce, abinci sau ɗaya a rana, kaya kala ɗaya, sun ƙasƙantar da rayuwarsu sun tauye masu hakkinsu na rayuwar duniya sun maida su kamar dabbobi.


"Wlh, na rantse da wanda raina yake a hannun shi, mutanan da suka ƙirƙiri gidan kurkukun ƙaddara ba zasu ƙara shaƙar numfashi cikin kwanciyar hankali ba, ɗaya daga cikin su bazai sha ba, idan har suka kuskura suka zo hannu wlh sai sunyi danasanin haihuwarsu da uwayensu suka yi a duniyar nan, sai sun ɗanɗani kuɗarsu sai sun manta da duk wani jin daɗi da suka ta6a ji a duniyar nan..." a harzuƙe Noah ya faɗa kamar ana tunzarashi da ƙyar suka lalla6a shi ya koma ya zauna yana faman yin haki kamar wanda yasha gudu...


Shiru suka yi na ɗan wani lokaci, batare da wani ya ƙara furta uffan ba, ƙoƙari suke su kwantar da hankalunsu don su samu nutsuwar faɗin ta cikin su, tashin hankali ya hana ko ruwan sanyi su kora ma maƙoshin su.


Muryar Big guy ce ta katse shirun nasu


"Abunda muka gano dangane da kungiyar matsafan, sadaukarwa da su ke yi, dole sai danginka, mutun ba zai iya sadaukar da wanda bai haɗa alaƙar jini da shi ba".


Girgiza kai Dr. zahra ya yi, "Banma san me zance ba, mutanan nan sun san me suka taka, kuma daga ji manyan mutane ne a ƙasar nan, shiyasa suka daɗe suna aikata ta'addanci batare da asirin su ya tonu ba..." Maganar Dr. Zahra ta ɗaga hankalin Chief Owais da Big guy saboda sunsan su wanene ke ruƙe da ƙasar wato family ɗin su.


"Mutane ne masu hatsarin gaske, tunkarar su ba abune mai sauƙi ba, ta ya za'ae ma mu san su wanene su balle har mu iya kawo ƙarshen su? Babban abun da ya ɗaure mana kai yaran gaba ɗaya ba su ta6a ganin fuskokinsu ba, hatta shi babban cikin su Salsabeel da ya fi su daɗewa a gidan kurkukun, kai hatta yaron da ke ruƙe da muƙamin garkuwarsu, ya rayu tsawon shekaru baisan fuskokinsu ba amma yasan Nicknames ɗin su, saidai yaƙi faɗa mana komai dangane da su, yana da taurin kai, mutunne mai wuyar sha'ani, ɗan uwansa Salsabeel ya faɗa mana cewa yafi shi sanin su wanene elders..." Big guy ya ƙare maganar yana dubansu.


Ci ya ɗaura da cewa, "Har yanzu suna sarrafa shi, mawuyacin abune ya bamu haɗin kai, ɗan uwansa yace in har muka tursasa mashi zai iya ja mana gagarumar matsalar da bazamu iya magance ta ba..."


Agent Jabeer Osman ya ɗaura da nashi bayanin, "Matsafan suna da kaifin basira da wayau, sun san cewa wata rana asirin su zai iya tonuwa shiyasa basu ta6a yin kuskuran da wani zai san fuskarsu a cikin yaran da suke raino ba, sun iya takun su..." ya faɗa yana jinjina kan shi.


"Garkuwar nasu Yaro ne mai kafiyar tsiya, bai yarda da bare ba, yan uwansa kaɗai ya sani, amma abun ɗaure kai shine silar ɗaukar yarinyar da suka ruƙa matsayin ƙaddararsu suka kaita gidan kurkukun wanda silar kasantuwarta a gidan ya ja har suka samu shaƙuwa mai ƙarfi tsakaninta da shi garkuwar nasu ta yadda su kan su suka gaza raba shi da ita, silar hakan yaja har ya ku6utar da su daga kurkukun.


Big guy ne ya kora jawabin, bayan ya kai karshe Commender James Ya ce"That means Unaisah is his weak point, she can be used to control him, right?"


 Jinjina mashi kai chief yayi murmushin gefen fuska James ya saki, "Everything will be easy for us if we can use her to control him"


"Da buƙatar mu san ya ƙarfin ikon su Yake? Menene rauninsu? da kuma Location ɗin da gidan kurkukun kaddarar Yake kafin mu fara shirye-shiryen kai masu farmaki" A cewar Captain lewis...


Chief Owais yace, "Karfin ikon su, suna iya 6acewa, bayan haka harsashin bindiga baya iya fasa fatarsu, makami ko wuta basa tasiri akan su, In har ba an ta6a lafiyar idanunsu ba, wanda kuma yin hakan ba abu ne mai sauƙi ba, saboda kakin Gaints ɗin dake a jikin su garkuwa ne, makami irin namu bazai iya yi masu illa ba..." gaba ɗaya hankalinsu ya tashi da jin bayanin Chief! Tunaninsu ta ya za'ai su farmaki mutanan da basa jin bullet, ko wuta balle wani makamin irin nasu.


 

Big guy ya ɗaura da cewa, "Bayan haka, su basa faɗa da makami sannan da bugu ɗaya suke kashe mutun." Waro idanu waje su commender suka yi gaba ɗaya sun kiɗima da jin zancen nan,


"Sanin inda gidan kurkukun ƙaddara yake mutun ɗaya ne zai iya yi mana jagora kuma shi kaɗaine zai iya taimaka mana gurin sanin ta yadda zamu iya kashe su cikin sauƙi"

*Daga Alƙalamin Boss Bature🔥✍️*

*Ga me bukatar karanta littafin kurkukun kaddara, 500 ne za'a tura Via Opay, 8103884440 Hafsat Bature Muhammad, shaidar biya za'a tura ta whatsapp, 08169856268 & 08103884440*

Post a Comment

Idan kuna da tambaya akan abinda Baku game ba ko kuma kuma Neman littafin da babu a nan kawai ku ajiye tambayarku a ta comment ko wani shawara da Zaku bamu.

Previous Post Next Post

Sponsored Link

Sponsored Post