" Bai kare maganar ba General Noah Ya katse shi da cewa"Dole saida shi zamu iya farmakarsu? Shi ɗan uwan nashi salsabeel bazai iya yi ma sojojinmu jagora ba" girgiza kai big guy yai"saboda laifin daya aikata masu, sun ɗauke garkuwar sihirin shi, Salsabeel bai da karfin ikon da zai iya jagorantarmu, dole sai dai shi Danish din"!
A kalla sun shafe tsawon awa da rabi suna tattaunawa a karshe dai ba su tsayar da ranar kai farmakin ba, har sai zuwa lokacin da Danish zai basu haɗin kai....
A yammacin ranar Su uku ne zaune saman kujerun backyard din gidan, sunyi shiru babu mai magana acikin su, yanayin fuskokinsu kadai zai tabbatar maka da akwai wani abu dake damunsu, kowan nan su da abunda yake sakawa cikin ran shi..
Muryar chief ce ta katse shirun nasu"Ina salsabeel din? Ka kira shi? Naji shiru baizo ba"
Cikin nutsuwa big guy yace"yace min yanzu zai shigo, mu kara hakuri nasan yana akan hanya"
jinjina kai chief ya yi tare da kallon Taj, wanda gaba ɗaya hankalin shi baya akan su, Ya langwa6e kai jikin sofa, har yanzu damuwar Unaisah ta hanashi sukuni baida wata walwala.
"Taj"! A hankali Ya dubi Chief daya kira sunan shi Na'am..
"What's wrong with you? tun zaman mu anan banji kayi magana"!
murmushin karfin hali yayi in a cool voice yace"Sir bakomai, idan ma akwai abunda ke damuna bai wuci tunanin yadda zamu kawo karshen kurkukun kaddara ba"
murmushi chief yayi wanda bai wuci fatar la66ansa ba.
"In sha Allah komai ya kusa zuwa karshe, bi'iznillah mu ne da nasara"
da kwarin gwiwa ya furta maganar, suka hada baki gurin faɗin"Allah Ya tabbatar mana da alkhairinsa"
kafin wani yakuma magana, sallamar Salsabeel ta katse su atare suka dago tare da kallon shi, cikin girmamawa Ya gaishe da su, da fara'a suka amsa amsa mashi
"Ay min afwa, Uziri ne Ya ruke ni, nabarku kuna ta zaman jira na" big guy yace"kada ka damu bismilla zauna mana" zama yayi kan kujerar dake a gefen Taj, ya maida duban shi ga chief ya nutsu yana jiran jin me zai ce.
Big guy ne ya zayyana ma shi komai da suka tattauna agurin meeting, ya ƙara da cewa"ko yau muka samu wanda zaiyi mana jagora zuwa gidan kurkukun, a shirye muke da mukai farmaki, yanzu haka da nake maka magana mun riga da mun tadani rundunar dakarun Sojoji, da kuma makaman yaƙi, ku kadai muke jira Salsabeel! We don't need to waste time!.
Chief ya ɗaura da cewa"nayi alkawarin bazan ƙara takura ma Danish game da zancen kurkukun ƙaddara! Salsabeel kai kadai ne kasan ta wace hanya zamu iya samun haɗin kanshi, saboda kafi mu sanin wanene shi, pls ka taimaka mana Salsabeel, muna so muje mu gane ma idon mu abunda suke aikawata mu kuma kawo karshen su...."
yanayin yadda chief ke yi mashi magana da raunin murya ba karamin karya mashi zuciya yayi ba, ji yake inama ace zai iya yi masu jagora da kan shi basai sun bukaci Danish ba wlh da babu abunda zai hana koda hakan zai yi silar rasa rayuwarshi..yayin zurfi cikin tunanin shi muryar Taj ta dawo da shi hayyacin shi
"Kayi shiru baka ce komai ba, gaba dayanmu mun ƙagara da muji daga gareka, Salsabeel mun yi imanin zaka sama mana mafita in sha Allah, pls kada ku sagar mana da kwarin gwiwar mu, hatta commender james shima ya shirya bada gudummuwarshi gurin kai farmaki, haka zalika Rundunar Sojojin Nigeria suma sun shirya tsaf lokaci kadai suke jira mu faɗa masu"
ya faɗa yana duban Salsabeel"saura kai Salsabeel ka bamu gudummuwarka mun san ka yi kokari amma muna bukatar ƙari"
Dukar da kanshi ƙasa yayi lamarin na nema yafi karfin shi baisan ya zaiyi da Danish ba, shi kadai zai kawo masu cikas, baisan yadda zaiyi ya tankwara shi ba, amma tabbas yana da tabbacin mutun ɗayane duk duniyar nan zai sa shi abu yayi, Cikin karyayyar murya.
yace"Yalla6ai, Ku bani mintuna shabiyar In ba damuwa, inaso zanyi magana da Danish din"
big guy yace"muna jiranka" miƙewa yayi cikin takun sauri Ya nufi cikin gidan.
Yana shiga falon Ya hango Unaisah tare da Danish su biyu zaune kan rug, sun tasa notebooks agaba tana koya mashi karatu, tsakanin jiya izuwa yau, ta janye sharuddan data gindaya mashi duk da bata sakar mashi fuska.
Sam basu lura da shi ba, har saida yayi masu gyaran murya kafin suka dago tare da kallon shi, suna ganin shi suka mike tare da gaishe da shi ya amsa masu sam ba walwala ya dubi Danish.
"Inason yin magana dakai" ya faɗa tare da juyawa ya nufi upstairs
sai da ya fara kallon Unaisah tace"yana jiranka, ka tafi, ni zan tsaya anan idan kun gama maganar sai mu ci gaba da karatun"
amsa mata yai da toh kafin Ya bi bayan Salsabeel, a dakinsa Ya same shi tsaye, cikin lalama Salsabeel Ya fara magana.
"Danish ka bani mamaki! Ina hankalinka da tunaninka suke? Kamar baka da zuciya a kirjinka ka rasa su wa zaka rufa ma asirin sai waɗanda suka cutar da rayuwarka? Danish baka da burin daukar fansa akansu? Ko dan saboda mu kawo karshen zaluncin su mu kuma ceto rayuwar sauran yaran dake a hannunsu yakamata ka basu hadinkai, mutanan nan sun shirya tsaf don sukai farmaki a mutu ko ay rai kai kadai suke jira pls Danish kada ka bani kunya mana, a yadda nasanka kai mutunne mai tausayi da son taimako kuma da kake cewa sune iyayenka masu sonka karyane elders baxasu taba zama masoyanka ba iyayenka daka kullata a ranka zai iya yiyuwa basu suka sadaukar da kai ba suma suna cen suna kewarka ka wani ne a danginka kayi tunani mana. .." tunda ya fara maganar facial expression din Danish bai nuna ya karaya da kalaman Salsabeel ba.
Bai ma bari Ya karasa maganar ba, Ya katse shi da cewa'I can't, please don't pressure me i don't want anything to disturb my peace of mind, Salsabeel you know who the elders are! basai nayi maka bayani ba, ka kuma san su wanene Evil giants, sannan ka san kurkukun kaddara gaba da baya, tayaya kake tunanin zasu iya kai masu farmaki su yi nasara akansu? Inajiye masu tsoron su rasa rayukansu saboda basu da karfin da zasu Iya cin galaba akan su"
bai kare maganar ba Salsabeel Ya katse shi cikin marairaice fuska yace"Danish! Wannan ba hujja bace! Allahn daya halicci elders din shi ne zai basu nasara, saboda sun dogara da shi kuma sunyi imanin zasu iya cin galaba akansu, kawai ka yi abun da suke so"
"Bazan ta6a fahimtar abunda kake fadi ba, ka daina wahalar da kanka salsabeel, banaso mu samu sabani atsakaninmu pls na roke ka ka kyaleni, kaima kuma ka fita sabgarsu in har ba so kake rayuwarka ta salwanta ba..."
duk yadda Salsabeel yaso ya shawon kanshi Yaki fahimtarshi ya kangare ya sanya taurin kai da kafiya, tun yana lallaba shi ta lallama har takaiga Ya cakumi Gaban rigarshi da hannayenshi cikin jin kunar rai ya dinga zazzaga mashi masifa kamar zai rufe shi da bugu ta inda yake shiga batanan yake fita ba, a karashe yace tunda na bika ta lallama ka ki bani hadinkai, zan bi dakai ta tsiya ne, hanyar da baka isa ka guje mata ba, dole kaje ko kana so koba so.."
bayan ya fita daga dakin akan stairs ya tsaya yana faman fitar da hucin bacin rai, yaji haushi da takaicin hali irin na Danish, duk da yanayi mashi Uziri saboda sanin cewa bashi kadai bane har yanzu elders suna iya sarrafa shi amma A halin Yanzu daga zuciyarshi ne bawai Evils din jikinshi bane.
Abunda ya fahimta dangane da Danish baya son rabuwa da Unaisah shiyasa yaki basu hadin kai, gani yake kamar in yabisu suka je kai farmakin rayuwarshi zata Iya salwanta batare daya cika burin shi akan Unaisah ba gyaɗa kai yai da alama ya kamo bakin zaren saukowa down yayi bai ganta a falon ba, kaitsaye ya wuce bedroom din su, yayi knocking almost 3 times kafin ta buɗe mashi kofar yaci sa'a ita kadai ce a ciki.
"Ya salsabeel yau kai ne adakin mu" dakyar ya kakaro murmushi kan fuskarshi yace"ni ne Unaisah, tun da kika ganni kinsan abune mai mahimmanci ya kawo ni gurin ki"
cike da mamaki tace mashi toh, daga gefen gadon suka zauna suna fuskantar juna, ta tsare shi da idanunta cike da ƙagarar son jin wata magana zai mata
"Unaisah Kin san meya faru lokacin da chief ya shiga da Danish Questioning room a headquarter wanda yayi silar fusata Omar har suka samu sabani..." aɗan ruɗe ta girgiza mashi kai"ba komai na sani ba, kaɗan na fahimta daga furucin ya omar"
Nan take Salsabeel Ya labarta mata abun da Ya faru tsakanin Danish da Chief,shi ma abakin big guy yaji komai.
ranta ya sosu da jin abunda Danish yayi ma chief, babban abunda ya fi bata takaici daya ce ma chief ba gaskiya ya ke faɗi ba, they've never hurt him Suna sona shi kuma sune iyayen shi, bayan su bashi da wasu iyaye a duniyar ranta yayi mugun 6aci ba kaɗan ba, sam ta kasa magana sai jinjina kai take.
"Unaisah babu irin magiyar da banyi ma Danish ba, akan ya amince ya basu hadin kai yakiya, nayi lallashin nayi roƙon duk abanza wlh da raina ya baci kamar in rufe shi da bugu saboda ya bata min rai..." ya faɗa rai a6ace ya ɗan dakata Yana kallon unaisah dake kallon fuskarshi
"Wallahi da ace zan iya jagorantarsu zuwa gidan kurkukun kaddarar da tuni nayi hakan Unaisah, sai dai ni yanzu bani da wani karfin ikon da zan iya yin hakan, bayin Allahn nan sun shirya tsaf sun tanadi rundunar sojoji da makaman yaƙin da zasu farmake su abu ɗaya ne zaiyi masu cikas wanda zai yi masu rakiya zuwa gidan kurkukun kaddarar, Unaisah basu san hanyar da zasu bi ba, ba su san a daidai ina ginin yake ba! Shin akan ƙasa Yake ko karkashin kasa Yake? Bayan haka ke kinsan yadda ginin yake wani irin kurman ginine mai rikitarwa da tsoratarwa in har mutun baida ilmi akan shi wlh tuni zai zauce, Danish shine makamin da zamu iya tunkararsu da shi ..." da yai wanann maganar bakomai ta tuna ba face lokacin data saci hanya ta fita matakalar bene ta dinga mayar da ita baya, ga wannan rudin mai rikita kwakwalwar mutun ya dinga ganin abun da babu azahiri.
"Kinyi shiru baki ce komai ba, yakamata Mu ne mi mafita Unaisah, In ba haka ba elders zasu cigaba da aikata zalunci, kwara muyi amfani da wannan damar kada muyi gangancin da zata kubce mata..'
tsantsar damuwace akan fuskarta cikin sanyin murya tace"Yaya Salsabeel menene mafita? Kafi kowa sanin halin Danish, Yana da taurin kai da kafiya, Idan ya fadi abu babu wanda Ya isa Ya canza ra'ayin shi...." bata ƙare maganar ba, Salsabeel yai saurin furta"akwai mafita Unaisah" a kagare tace"menene mafita" shiru yayi jim yana jin shakkar yadda zata dauki abun amma daya tuna irin burin da take dashi na son ruguza kurkukun kaddara sai ya samu kwarin gwiwar ce mata"Unaisah, duk duniyar nan mutun ɗaya ne kacal zai iya tursasa mashi Ya bashi umarni kuma Ya bi shi sau da ƙafa..." da ruɗu akan fuskarta tace"wa kenan"?
Nuna ta yai da index finger din shi waro idanu waje tayi kamar wadda taji wani mugun abu
"Ke Unaisah! Basai nayi maki dogon bayani ba, kin riga da kinsan irin tsantsar kaunar da Danish ya ke yi maki, wanda ko sauran yan uwanshi da suka taso atare bai ta6a yima kwatankwacin shi ba, wlh nayi imanin in har kika bashi umarni yaje zai je..."
da matukar tashin hankali ta girgiza mashi kai labbanta na rawa tace"I can't... I can't change his mind Danish won't listen to me ya Salsabeel kai fa ka fadamin wasu lokuttan ba shi bane zai iya wuni baya a hayyacinsa taya kake tunanin zan iya bashi umarni ya bi"?
Ta fada idanunta azare take kallon shi, ita babban tashin hankalinta a haɗa ta dashi don ta shawo kanshi bataso su sake samun sabani bayan haka tana jin tsoron tayi silar jefa rayuwar masoyinta cikin haɗari, da alama soyayyarshi na nema ta rufe mata idanunta..
"Unaisah Zaki Iya, Ko ba don saboda son da yake yi maki ba, idan ba zaki manta ba na ta6a fada maki dalilin dayasa suke kiranki da kaddarar kurkuku" kura mashi ido tayi batare da kyaftawa ba.
"Ma'anar hakan shine ke kaɗaice zaki iya tarwatsa tarihin kurkukun ƙaddara! Kamar yadda yazo a allon tsafin su, duk da bamu da tabbaci Allah kadai yasan gaibu amma In Allah Yasa hakan ya zamana gaskiya ne kinga kenan wannan wata hanyace da zaki yi amfani wurin kawo karshen su, Ki zamar masu mummunar ƙaddarar da zatayi silar tarwatsa su.
maganar salsabeel ta farfado da tunaninta na son kawo karshen kurkukun ƙaddara amma bataji zata iya tursasa danish don ya yi masu jagora.
Muryarta tamkar zata fashe da kuka tace"ya Salsabeel na fahimce ka, amma bana jin zan iya tursasa ma Danish, Ina matuƙar jin tsoron in jefa rayuwar shi cikin hadari, in har wani abu ya faru dashi bazan ta6a yafe ma kaina ba, idan ma zuwan ya zama dole sai da shi to ku haɗa da ni.
kasa karasa maganar tayi saboda kukan daya tokare makogwaronta nan hawaye suka dinga zarya kan kuncinta.
Zuciyarshi taso ta karaya da maganarta,
Shesshekar kukan tane Ya fargar da shi, Cikin sigar lallashi yace"in har kin yi imanin cewa Allah shi ke tsare bawansa bai kamata kina tunanin Zai rasa ransa a gurin Yaki ba, ay bashi kadai zaije ba Unaisah baga mu ba ko mu baki damu mu mutu ko muyi rai ba? Wlh Unaisah jininmu akan akaifa yake babu gudu ba ja da baya ko da zamu rasa ranmune sai mun yi yaƙi da dukkan karfin mu, mun dogara da Allah kuma munyi imanin shine zai bamu nasara akan kyakkyawar niyar da muke da ita na ganin mun kawo karshen zaluncin kurkukun kaddara...."
Kwata kwata bata gane me yake cewa ba, ita fa damuwarta akan Danish ne cikin karyayyar murya tace"ni abun da nafi jimawa har yanzu shi ba musulmi bane, I don't want him to lose his life as an unbeliever! ya makomarsa zata kasance?..." ta faɗa tana kallon fuskarshi da idanunta wadanda suka kaɗa jawur da su
shi kanshi abun na damun shi, baida burin daya wuce Danish ya musulunta ko dan ya tsira da imaninsa, amma yasan bamai yiwuwa bane in ba wani iko na Allah ba, saboda wadannan evils din na jikin shi.
"Mu cigaba da taya shi addu'a in sha Allah zai musulunta, ni dai yanzu damuwana ki yi kokari kisa ya amince mana..." kifa kanta tayi jikin pillow, sam bata son maganar gani take kamar tursasa mata yakeyi don ta ingiza danish ga fadawa halaka..
Sarai ya fahimci daga ita har Danish din Giyar soyayyace ke dibarsu, shiyasa har suke neman su bijire..
Gwiwar shi ta sage, cike da rashin kwarin jiki Ya miƙe ba tare daya kauda idanun shi daga kallon ta ba Yace"banzo nan donna bata maki rai ba, kodan na tursasa maki nazo ne don mu hada hannu gurin cimma burin da muka dade muna jiran ranar da zamu aiwatar da shi, kada ki manta nayi ma mahaifiyata alkawarin zan kawo karshen zaluncin Elders bayan haka kema kin min alkawari watakil Yanzu kin manta nasani..." wani irin radadi take ji acikin zuciyarta tana maijin bakin cikin gaza amsa mashi bukatar shi
"Zan tafi Unaisah, ki zauna kiyi nazari da hankalin ki, Zan jira har zuwa lokacin da zaki aiwatar da abun da na sanyaki, bana so kiyi danasani mara amfani..." ya fada tare da juyawa ya nufi kofar fita daga dakin Harya ruke handle din Ya dan dakata tare da juyawa ya dube ta, still bata dago da kanta ba sai kuka take yi
"Kina tunanin zaman Danish agidan nan shi zaisa Ya tsira da ranshi? Abunda baki sani ba dokar elders ce duk wanda ya san sirrinsu dole su kashe shi, in har baije Ya farmakesu ba, to su zasu farkama ke shi ne akowani lokaci" ya na fadan hakan yasa kai ya fuce
Fitar shi keda wuya ta kuma fashewa da wani sabon kukan kamar ranta zai fita, maganar salsabeel ta fara tariyowa farkon haduwarsu agidan kurkukun ƙaddara
_inaso ki ɗaurawa kan ki nauyin yin hakan ko dan saboda rayukan dake rayuwa acikin kurkukun nan cikin mawuyacin hali! Akwai ire iren ku da yawa wadanda basu ji ba basu gani ba, An kulle su an hanasu sakat, Kullum ne sai an rasa rayuka agidan kurkukun nan, kashe mutane suke yi tamkar kyankyasai, Idan har bamu kawo ƙarshen kurkukun nan ba to kuwa zasu cigaba da aikata 6arnar da babu ranar dainawa, Muna matuƙar jin tausayin yaran da ke rayuwa a kurkukun nan, Dan Allah Unaiserh ki taimaki rayuwar su! Ki daure ki jure wurin ganin kun tona asirin abun da ake aikata......" hannayenta Ya ruƙo a cikin nashi ya dinga yi mata magiya sautin muryar shi kamar zai fashe da kuka_
_"NAYI MAKA ALƘAWARI Idan Allah ya bani damar fita daga kurkukun nan zan tona asirin su harma mu bada gudunmawa wurin ganin an kawo ƙarshen su, Bi'iznillahi_
Tuna wannan yasa ta ƙara sautin kukan nata.
A bangaren Salsabeel bayan ya koma backyard din kamar yadda yabarsu Chief haka ya taras da su zaune suna jiran shi.
Bawan Allah duk Ya rasa kuzarin shi, su Unaisah sun bata mashi rai ba kaɗan ba..
Hankalin su baya akan shi har saida yai masu sallama kafin su ka dube shi, zama yai kan kujera ya sunkuyar da kan shi ƙasa tun daga yanayin shi suka fahimci akwai damuwa..
"Salsabeel ka yi shiru baka ce mana komai ba! Ya kuka ƙare da shi"? Cikin kulawa Taj yai maganar..
Cike da jin nauyin su ya girgiza kai,
"Danish ya bani kunya, ban ta6a zaton zai bijire min ba..." tun da suka ji hakan damuwa ta bayyana akan fuskokin su don sun riga sun hasaso karashen zancen na shi..
Rai a6ace Omar yace"meyasa zamu wahalar da kanmu akan shi? Yaron nan fa ɗan rainin wayau ne, idan muka ce zamu bishi ta lalama bazai ta6a bamu haɗin kai ba, kwara mu bi shi ta ƙarfi da yaji mu ci ubanshi har sai ya miƙa wuya..."yana huci ya faɗa kamar zai haɗiyi zuciyarsa saboda bacin rai..
Chief ya ɗaga mashi hannu badan Ya ƙarasa maganar ba yaja baki yayi shiru fuskar shi a murtuke..
"In har bashi yayi niya ba, ko da zamu rasa damar da muke da ita na zuwa gidan kurkukun bazan bari a tursasa masa ba, itama Unaisah ban amince ayi amfani da ita gurin shawo kan shi ba, cos zai ga kamar ni na sanya ta ne" Salsabeel ya ɗan kalle sa cos shi harya riga daya tuntu6i Unaisah.
Cike da takaici Big guy ke kallon chief da yai maganar
"Haba Owais, Saboda shi kawai zamu fasa niyar mu"?
"Omar, ba ina nufin zan fasa aikin mu bane, sai dai mu nemi wata hanyar..." bai ƙare maganar ba, Big guy ya mike yana huci ya kama hanya zai bar backyard din..
Damuwa ta hana Taj furta kalma baima san me suke cewa ba.
Miƙewa chief yayi da sauri yabi bayan Omar, don bazai bari su sabamu sabani tsakaninsu ba dama kwanakin nan yana jin haushin fifita Danish da yake yi.
Bayan tafiyar su, ya rage saura Taj da Salsabeel sunyi shiru babu mai magana acikin su.
Ganin yadda Taj ya zabga uban tagumi ne yasa Salsabeel furta"Sir are you Okay"?
Yamutsa fuska yai"kada ka damu, i'm okay, just banji dadin yadda ɗan uwanka yaƙi bamu haɗin kai ba" ya fada yana kallon Salsabeel
"Amma Salsabeel babu dabara da zamu iya yi don mu shawo kan shi"?
Shiru Salsabeel yayi yana nazarin maganar shi, wata dabara ce ta faɗo mashi arai da sauri Ya dubi Taj
"Akwai hanya ɗaya" akagare Taj yace"Ina sauraronka"
"Ƴarka Unaisah, Ita kaɗai ce zata Iya sa shi dole yayi..." lokaci ɗaya Taj ya haɗe rai, annurin fuskar shi ya ɗauke, saboda zafin maganar Salsabeel daya ji.
"Meyasa kace haka"?
Murmushi Salsabeel ya ɗanyi kafin ya fara zayyana masa dalilinsa nacewa haka!
"in har ta umarce daya je zai je, saboda ya mutu akan Sonta, ba irin magiyar da banyi mata ba akan taje ta rokar mana shi amma taƙiya saboda gudun kada ta yi silar da zai rasa ranshi, amma ina da tabbacin in har ka yi mata magana zamu iya cin galaba akan ta saboda kai mahafinta ne, bazata ki bin umarninka ba"...
Tun da ya fara magana Taj ya tsare shi da ido batare da kyaftawa ba, bakomai yake tunawa ba face abunda idanun shi suka gane mashi, ɗari bisa ɗari ya yadda da maganar Salsabeel saboda shi shaidane akan mahaukacin son da suke ma junan su, duk da ya ɗauke ƙafa akanta amma yana jin zai iya zuwa gurinta don ya jarabata"
Har salsabeel ya ƙare maganar Taj bai sani ba, gyaran muryar da yayi mashi ne ya fargar da shi
"Pls, ka taimaka koda sau ɗaya ne ka jaraba yi mata magana.." fuskar shi amarairaice ya fada..
Wayar Taj ce tay ringing, kallon Salsabeel yayi"it is Okay, zan jaraba" ya faɗa tare da miƙewa Yai picking call din
"Sir, ina fata lafiya, naji shiru baku dawo ba"
"Boss, Ka sallami Salsabeel ya tafi, kaima zaka iya tafiya..." amsa mashi yai da toh..
"Chief yace ka tafi, zai neme ka" mikewa yayi"pls sir, sai naji daga gare ka" jinjina mashi kai yai batare daya fur ta kalma ba.
_________________________________✍️
Su Batool na zaune a falo suna fira kusan su dukkansu in ka cire Unaisah da Danish sai ummi su kadai ke babu a cikin su...
Sam basu lura da shugowarshi ba fira taja hankalin su, ganin babu Unaisah yasa shi juyawa ya nufi bedroom din...
Adai dai lokacin ta fito daga bathroom, sanye da yar rigar wanka, zuciyarta cike fal da tunanin abunda suka tattauna da Salsabeel
Wayar ce ta fara ringing, har zata dauka taji anyi knocking din kofar
"Wanene"?
"Ki buɗe kofar ki gani" ras ta ɗan ji gabanta ya fadi jin muryar daddynta, tana jin shakkar shi yanzu ba kadan ba saboda canzawar da yayi mata.
"Unaisah ba zaki buɗe min ƙofar bane"! Jikinta na 6ari ta je ta buɗe ƙofar, shigowa ciki yai tare da aza idanun shi kan fuskarta wani irin tausayinta ne ya kama shi.
Cikin rawar murya tace"daddy Ina wuni" ta fada tana kallon shi
Shiru yayi bai tanka mata ba hakan ba karamin karya mata zuciya yayi ba.. Kasa jurewa tayi batasan sa'adda ta faɗa kan kirjin shi ta kankame shi tana tana kuka tace laifin me na maka daddy? Meyasa ka canza min? Ka daina sakar min fuska, idan na gaishe ka dakyar kake amsa min idan na kira wayarka baka ɗagawa, daddy don soyayyarka da manzon Allah ka fadamin laifin me nayi maka sai in nemi yafiyarka, wlh bana so kana fushi dani Daddy, kaifa mahaifina ne kasan hukuncin wanda iyayensa ke fushi da shi ...."sambatu taci gaba dayi batare data raba jikinta daga nashi ba..
Zuciyarshi ta karaya da jin furucinta, ta bashi tausayi ba kadan ba, ga kaunarta dake kara ninkuwa cikin zuciyarshi, jiya dakyar ya runtsa hatta Danejo saida ta lura da yanayin shi ba irin magiyar da batai mashi ba akan ya fada mata gaskiyar abunda ke damunshi amma yakiyi saboda bazai iya tona ma yarsa asiri ba, kamar tona ma kansa ne..
Baiwar Allah muryarta harta disashe, Unxpectedly taji ya ɗaura tafukan hannyenshi akan sumar kanta ya ɗan shafa bayanta cikin sigar lallashi
Kafin ya fara magana
"Unaisah, kin bani mamamki, kinyi min abunda ban ta6a zato ba..." a firguce ta dago tana kallon fuskar shi
"Ina yi maki kallon mai hankali, kuma mai jin tsoron sabawa Allah ashe nayi kuskure Unaisah, na yaudari kaina.." cike da tashin hankali ta furta"daddy ni din? Me nayi maka"? girgiza kai ya danyi cike da takaici ya zayyana mata abunda Ya taras sunayi adakin Danish...
Dafe kai ta yi da tafin hannunta, wani irin faduwar gaba da tashin hankali taji
"Idan shi jahili ne baida addini, ke ay ba irinsa bace, Kinsan babu kyau unaisah, ina tarbiyar dana baki? Baki ji komai ba kika biye mashi kuka rungume juna, haba Unaisah baki kyauta ma kanki ba, nima kuma baki kyauta min ba, wlh kin karya min zuciyata, kin samin fargaba saboda zullumin kada ya lallata min rayuwar yata...."
kusan suman tsaye tayi, jikinta ya fara kakarwa kamar mazari ga kunyar shi data lullu6e ta, tasan bata da gaskiya shiyasa ta sunnar da kanta ƙasa cikin sanyin murya ta furta"daddy, na kar6i laifina, amma dan Allah kada ka zarge mu, wlh bamu ta6a aikata wani abu daya sabama Allah ba, duk da Danish baida addini ba ɗan iska bane daddy, bazaiyi abunda zai cutar dani ba, idan yayi ba daidai ba ina faɗa masa babu kyau a addinina kuma baya musa min, abun da ya faru ranar bana a cikin hayyacina daddy, hankalina ya tashine naji matuƙar tausayin shi kuma naji tsoron kada na rasa shi shiyasa na rungume shi, amma wlh ba shine ya fara rungumata ba, ni ce daddy...."
yanayin yadda take yi mashi magana jikinta na kerma ba karamin rauni ta sanya mashi ba, yayi niyar yayi mata fada sosai amma sai yaji bazai iya ba, ya yarda da maganarta yasan Unaisah bazatai mashi karya ba.
"Meke atsakaninki da shi"? Ya tambaya yana kallon ta
Kamar mai in ina ta fara yan kame kame tana fadin"amm..umm..dama.."ta ɗan kau da idonta gefe kamar bazata karasa maganar ba tace"bazan boye maka ba, dama najima inason in faɗa maka, nasan zaka goya min baya akan abunda nakeso...." tashin hankali idanun shi aware yake kallon ta.
"Daddy Allah ya jarabce mu da son juna ni da danish, soyayyar dake tsakaninmu bazata misaltu ba, har rayukan mu zamu iya sadaukarwa akan junanmu, daddy wlh ina son danish, shi kadai ne namijin da nake da burin in aura..." bata ƙare maganar ba, sakamakon tsawar da Taj Ya daka mata wadda tay silar rikicewarta arazane Ta zazzare grey eyes dinta akan fuskar shi Yana faman fitar da huci yace"Impossible Unaisah! Wlh bazan lamunta ba, ba zaki sa nayi karamar magana ba, baki isa ki kunyata ni ba, kina hauka ne unaisah? Meye abunso atare da shi? Yaron da baida adinini arne ne, ga jahilci cike da kai, sannan bashi da wani galihu, bayan haka ina yake da halin da zai iya ruke min ke!?
wani irin jiri jirin tashin hankali ta gani acikin idanunta kalaman daddynta sunyi matuƙar ɗaga hankalin ta, tayi mamakin furucin da yayi akan danish kamar dai ya manta cewa komai ya faru arayuwar shi bayin kan shi ba ne...
"Unaisah Ina burin da kike shi na son auran attajirin me kuɗi? Mai ilmin addini dana zamani mai cikakken asali wanda zai gatantaki Ya tarairayeki ya baki kyakkyawar kulawa?
"Daddy, na jima da soke wannan burin, ba dole sai na auri miji mai kudi zan samu farin ciki ba, sau dayawa wasu masu ilmin basu aiki da shi daddy, ni kawai miji na gari nake nema kuma na samu daddy, duk abunda ka lissafa Danish zai iya bani fin su, saboda yanayi min soyayyar da bazai iya cutar dani ba, yana yi min son da zai iya hana kanshi farin ciki saboda farin ciki"
Ta ɗan numfasa kafin taci gaba da cewa" ka kira shi jahili daddy banji dadi ba, bayan kasan ba shi yaja ma kanshi hakan ba, idan ka amince min, zanyi amfani da son da yakeyi min in musuluntar da shi..."
bata ƙare maganar ba, Ya dakatar da ita ta hanyar ɗaga mata hannu! wani irin kululun bakin cikine Ya tokare makogwaronsa, Ya ma rasa me zaiyi ya huce haushin sa, Yayi mamaki wai har Unaisah ta iya gaya mashi da bakinta bata ji kunyar shi ba lallai ba karamin so take ma shi ba, zata iya komai akan shi..
Kafadunta Ya dafa da tafukansa Ya jijjigata har saida Sumar kanta ta yarfo ta gaban fuskarta fashewa tayi da kuka don ta gane bai fahimce ta ba..
Da kakkausar murya ya furta"Bazan ta6a amince ma soyayyarku ba, ba son shi kike ba, tausayin shi kike ji, tun wuri ki cire zancen zaki aure shi, saboda na riga da nayi maki miji sadakinki ne kadai bai biya ba, kuma yana sonki, shine za6ina unaisah in har ba bijiremin zakiyi ba, bana so ki bani kunya kada kisa na karya alkawarin da nayi masa, ki cika min burina Unaisah, danish ba dole saida ke zai iya rayuwa ba, ga sauran yan uwanki nan sai ya zabi daya acikin su, Unaisah burin kowace uwa ta sama ma ya'yanta uba nagari ba jihili ba.
abun da Taj bai sani ba tuni tajima da sumewa, idanunta daya gani a kakkafe shi yasa shi gane hakan..cikin jin faduwar gaba ya hadiye sauran maganarshi da bai amayar ba, saboda tashin hankali, Ashe nashi wasane bai ta6a ganin true love ba sai yau, ay yayi zaton daga layla da majnoon andaina samun irin soyayyar nan, sungumarta yayi kan fadar shi ya kwantar da ita kan gadon su, Ya fito daga dakin jiki na kerma Ya tafi dauko ruwa kafin dawowar shi, Batool ta shigo dakin fuskarta dauke da murmushi ta zauna gefen gadon tana kallon wani sabon salon kwanciya agurin Unaisah, tayi zaton dadin baccine yasa ta dauki tsawon lokaci bata leko waje ba.
"Sister Ya kamata ki tashi, Aunty Ummi ta hanamu baccin marece.."
ta fada tare dakai hannu ta ɗan bubbuga ƙafar Unaish shiru bata farka ba,
"Unaisah wani irin bacci ne wannan kamar mai fama da cutar bacci" ta fada tana kara bubbuga legs din ta.
Adaidai lokacin Taj ya fado dakin hannun shi ruke da robar ruwa me sanyi, Yana ganin Batool yaci burki gaban shi na faduwa yasan muddin tasan Unaisah suma tayi sai ta yi kukan da zai jawo hankalin sauran yan uwanta.
Jin motsin adakin yasa Batool ta juyo ganin daddyn Unaisah yasa ta miƙe da fara'a tace"ina wuni daddy, i'm sorry watakil ka yi sallama banji shigowarka ba..." yawu ya haɗiya dakyar ya tattara nutsuwarsa yana kokarin danne damuwar shi yace"lafiya lou daughter.." da alamun rudu kan fuskarta tace"daddy naga water bottle a hannunka.." washe baki yayi"eh ni zan sha ne, kishi nake ji" murmushi tayi"ko kazo ganin Unaisah ne" a kagare ya daga mata gira"bacci take, yanzu nake kokarin tadata" da sauri yace"kinga bari ni in tashe ta, kije gurin ummi naji kamar tana nemanki..." kamar taso ta ɗago shi, ta lura kamar wani abu badaidai ba, amma sai batayi mashi gaddama ba, ta fuce daga dakin, ajiyar zuciya ya sauke bayan ya datse ƙofar dakin, ya zauna gefen gadon da sauri ya cire murfin robar ya yayyayafa mata ruwan kan fuskarta.
dogon numfashi taja tare da sauke ajiyar zuciya..
"Unaisah, Pls ki yi hakuri ki tashi, kinji! I won't hurt you anymore..."
dakyar ta iya buɗe idanunta wadanda suka kada jawur ta dube shi
Wani irin ciwon kaine Ya far mata...
Cikin disasshiyar murya tace"daddy, kada ka raba ni da Danish, zan iya rasa raina.."
Kwata kawata baya son tana fadin zata rasa ranta akan Danish, Ranshi baci yake kamar ya hadiyi zuciya, kuma yana akan bakanshi bazai janye ba.
"I'll think about it, Yanzu bana son duk wani abu da zai ɗaga hankalinki, kwanciyar hankalinki nakeso..." hankalin ta ya ɗan kwanta, gani take kamar daddynta zai duba mata ne.
"Amma daddy, baka son Danish ko"? Girgiza mata kai yai"Ina son shi Unaisah, Kuma ina jin tausayin rayuwar shi, maganganun da kikaji nayi ɗazu rainane Ya 6aci bawai don ina nufin hakan ba, ni kawai banaso kina sakar mashi jikin ki ne"
cikin kwantar da murya ya faɗa.
Ruko hannun shi tayi a cikin nata"daddy pls ka min alkawarin ba zaka raba ni da shi ba"!
Dafe kai yai da tafin hannun shi, ji yake kamar ya kifa mata mari saboda haushin da yake ji in ta ambaci sunan Danish
"Kina so In amince ma Soyayyarku?In kuma ba shi damar Auren ki"? jin wannan maganar daga bakin daddyn nata yasa ta miƙe zaune cike da zumudi tace"Eh daddy..."
Numfasawa yayi kafin yace"Zan baki Umarni, If you do what I say, I promise to fulfill your dream of marrying your choice".
gabanta ne ya ɗan faɗi duk da batasan umarni da zai bata ba, taji fargaba sosai..
"Daddy, wani irin Umarni ne? Ka faɗa min in sha Allah zan yi maka biyayya" ta faɗa cike da jin fargaban amsar da zai bata..
Ido cikin ido su ke kallon jun.
"ki bashi Umarnin, ya yi mana jagora zuwa Gidan Kurkukun ƙaddara..."
wata irin razananniyar faduwar gaba taji, kamar zata zauce ta daddafe kanta da tafukanta dama saida ranta ya ayyana mata abun da zai umarce ta da tay...
"Inaso in tabbatar da kaunar da ya ke yi maki, ta hakanne zan gane shin jarumtakarsa takai in mallaka mashi lu'u lu'u na?
ya faɗa yana kallon idanunta da suka rune zuwa Jajawur kamar Jan gauta.
Cikin shesshekar kuka tace"daddy, pls ka bani wani umarnin daban, wannan is too hard for me! I can't force him I don't wanna put his life in danger"
Kwata kwata babu annuri akan fuskarshi, ya haɗe rai sosai saboda yana son ta ɗauki maganar shi serious
"Unaisah, karna kuskura na ƙara ji kin furta kalmar kada ki jefa rayuwarsa cikin hadari! Ke ba musulma bace? Ba kiyi imani da Allah ba? Ko baki yarda da ƙaddara ba? Ko kuwa ƙarancin tawakkali ne ke damunki"? Runtse idanunta tayi tana jin wani iri yanayi a zuciyarta mara dadi
"Ba haka nasanki ba Unaisah! Kin canza min! Ina zuciyar imaninki take? na fahimci so ne ke nema ya rufe maki ido, Unaisah kin manta mummunar ƙaddarar data rabamu? Kin ta6a tunanin zaki ku6uta daga kurkukun ƙaddara? Kin ta6a tunanin zamu sake haɗuwa? Ikon wanene yin hakan"?
In a weak voice tace"Allah"
"Toh inaso ki sanya ma ranki, duk wani abu da zai faru da shi muƙaddari ne daga Allah, tun zuwan shi kurkukun kaddara bazai hana Allah ya jarabce shi da wata ƙaddarar ba, har kwarama yaje can yayi jahadi gurin ceton rayuka...."
nasiha ya cigaba dayi mata tun bata fahimtar shi har ta fara yin amanna da maganar shi...
"Daddy, ni damuwana he's not a muslim, banson ya mutu batare daya kar6i kalmatusshada ba"
ta faɗa hawaye na bin fuskarta...
Ruko hannayenta yayi acikin nashi ya ruƙe su gam kafin yace"In sha Allah zai musulunta Unaisah, idan sheikh imam yazo zamu nemi taimakon sa"
"Amma daddy, nima ina neman alfarma agurinka"!
"Wace alfarma"?
"Ku tafi dani, Nima ina son in bada gudummuwata..." waro idanu waje yayi aranshi ya ayyana bazai yiwu ba, amma a fili sai yace"Zan yi magana da chief, kinsan dokar aikinsu babu mace, amma in har ya amince zamu tafi dake" ajiyar zuciya ta ɗan sauke, fatanta Allah yasa Chief ya amince mata, dalilin dayasa ta za6i tabisu saboda abu biyu, na farko don ta kashe Jan wuya, duk da batasan wanene shi ba, kuma batasan ko yana ɗaya daga cikin members na kurkukun ƙaddara ba, sai dai taji aranta dakyar in ba ya cikin Elders, abu na biyu donta ba Danish kariya, koda Ajali zai riske shi, toh su mutu atare zaifi mata kwanciyar hankali.
Kiraye kirayen Sallar isha'i da aka fara yi ne, yasa Taj miƙewa ya dube ta"zan tafi, kiyi kokarin aiwatar da umarnina, in sha Allah silar biyayyar da zakiyi min, ba zaki ta6a danasani ba, saima ya zama silar farin cikin ki na har abada" cikin sanyin murya tace "in sha Allah daddy, zanyi masa magana, duk yadda mukai zan sanar dakai"
"Gobe da safe, in tashi da labari mai dadi" jinjina mashi kai tay
Miƙa mata hannu yayi da sauri ta sauko daga kan gadon ya rungumota, yana ƙara lallashinta da bata baki har saida ya tabbatar taji hudubarshi kafin su ka yi sallama da juna kamar karsu rabu..
_________________________________✍️
Idan muka koma bangaren Benazir sam ta kasa walwala, maganganun Zaki sun tsaya mata arai, sun hana ta sukuni gani take kamar batayi masa adalci ba, tayi kuka sosai har zazza6i saida ya lullu6eta, Wlh Yabata tausayi bata ta6a ganin rauninsa ba sai awannan lokacin, yayi mata taimakon da har abada bazata ta6a mantawa da shi ba, ya bata lokacin shi! Ya bata kulawarshi! Ya bata ci da sha Da suturu harma da aikin yi, ya kuma ruketa agidan sa na tsawon shekara goma sha bakwai bai ta6a goranta mata ba, sun shaku da juna, ya zama tamkar uba agare ta!
babu wanda yasan wani abu dangane da zuwan Zaki, daga Ita sai Alhaji musa suka san da maganar, fatanta Allah yasa kada Uncle musa yayi ma Daddynta maganar don batason duk wani abu da zai daƙile maganar komawarta dakin Mijin ta, taso taji daga bakin uncle me Zaki ya fada masu sai dai takasa ma tunkarar shi saboda bata son taji abunda zai hana runtsawa.
Har kiran Layin Zaki tayi don ta kara bashi hakuri amma kwata kwata kiran baya shiga..
Tunani ta somayi me zatayi don ta saka mashi?
Zuciyarta ta bata amsa da cewa me zai hana ta hada shi da Aneelerh! aranta kuma ta ayyana zaiyi wuya su sasanta cos zaki bazai kara gangancin fadawa tarkon son macen da kaddara ta rabata da mijinta, kamar dai ita 💔
_________________________________✍️
Har wuraren ƙarfe shaɗaya na dare bata runtsa ba, saboda matsananciyar damuwar data addabi zuciyarta, sai faman juyi takeyi kan matress kamar me fama da ciwon ciki, maganganun daddynta dana Salsabeel ne suka dinga dawo mata cikin kwalwar kanta, bata san ya zatayi ba, bata da wata mafita daya wuce ta amsa bukatarsu sai dai tana jin tsoron tayi silar jefa rayuwar man dinta a cikin haɗari amma idan ta tuna burin da take da shi na kashe jan wuya, da kuma nasihar daddynta sai taji kamar ana kara mata kwarin gwiwarta.
*CHIEF OWAIS*
Bacci ya ƙauracewa Idanun shi, Ina zai sa ran shi yaji dadi? chief irin mutanan nan ne waɗanda idan suka kwallafa rai ga abu suka saka buri da naci da komai in har ba su ga sun Cimma nasara ba to fa hankalin su bazai ta6a kwanciya ba..
Ya ƙuntata kanshi Ya hana zuciyar shi sukuni, baisan taya zai 6ullowa lamarin ba, Danish Yana nema Ya zamar ma shi ciwon kai...
Yayin da yake wannan tunanin safa da marwa yake a tsakar bedroom ɗinsa, boxer short ne kaɗai a jikin shi, fuskarshi a yamitse ba annuri..
Jefi jefi in damuwar ta addabe shi tafin hannunsa yake cusa cikin sumar kanshi ya yamutse ta kamar ɗan mahaukaci wani lokaci da karfi ya ke bugun iska da hannayen shi.
Phone ringing dinsa ne ya katse hanzarin shi, kamar bazai duba mai kira ba, zuciyarshi ta takura mashi akan ya duba, juyawa yayi a sukwane cikin rashin kuzari ya dauko wayar dake aje kan mirror chair, yayi mamakin ganin almost 16 missed calls, picking call din yayi tare da kare wayar a kunnan shi yai shiru yana jiran jin me zaice
"Owais, ya ake ciki game da kai farmakin?..."
"Only a few days remain"
"Ko zaka Iya faɗamin menene shirin ku a yanzu ni kuma zan ƙarfafa maku gwiwa"
Har yanzu bai yarda da mutumin ba, shi mugu bashi da kama, zai iya bayyana ta suffar mutanan kirki don ya shiga jikin mutun...
"I'm sorry to say, bazan iya faɗa maka ba, in har dagaske kana son taimakona ba dole sai kaji me muke shiryawa ba"
"Hakane, Ka faɗi gaskiya, Owais, shawarar da zan baku shi ne, Ku sanya malaman addini su tayaku addu'a, sannan ku ma iyayenku magana su tayaku da addu'a, ku kuma yawaita sadaka ga marayu da mabuƙata suma su tayaku da addu'a, ku nemi kariya daga wurin Allah, in sha Allah badai mutun da Aljan ba sai Allah...." bai ta6a jin 6oyayyan mutumin ya burge shi irin na yau ba yaji dadin shawarwarinsa
Har ya buɗe baki zai yi mashi godiya yaji ɗuff yai rejecting call din..
Hakanan Yaji Yana ra'ayin ganin Unaisah, wall clock Ya kalla ƙarfe 11 na dare, yasan i war haka tayi bacci
Jaraba kiran layinta yayi, tana fara ringing ta yi picking yayi mamaki bai zata zata ɗaga ba ..
Kara wayar yayi a kunnan shi yama rasa me zai ce mata.
Sanyayyar muryartace ta ratsa kunnanta
"Barka da dare chief, ka wuni lafiya"?
"Why are you still not sleeping"
"I woke up for the night prayer" yaji dadin jin hakan
"Okay, if you dont mind I want you to bring me the girl's backpack"
"Toh" rejecting call ɗin yayi, sai da yayi unclocking ɗin kofarsa don ta samu damar shigowa, kafin ya shiga bathroom don yayi wanka.
Saukowa tayi daga kan gadon ta tsaya gaban mirror tana kallon kanta ta cikin madubin.
Silk Pyjama ne a jikinta, riga da wando launin blue sky, rigar tana da dogon hannu sun yi matuƙar yi mata kyau.
Lallausar Curly hair dinta tabi da kallo, duk Ya har gitse saboda rashin kwanciyar hankali ta manta when last tayi fixing dinsa.
Fragrance set ta ɗauko ta feshe ko'ina na jikinta da shi, cikin kankanin lokaci daddadan kamshin turarenta ya buɗe ɗakin
ta ɗauko veil ta yafa ma kanta kafin ta saka flat shoe a kafarta.
Back pack din ta dauko, ta daurata kan mattress, ta curo wasiyar da Unaizah ta bata guda biyu ta boye su cikin diary ɗinta, don bata jin zata iya rabuwa da su tunda kamar amana ta bata, tafison ta damƙa ma iyayenta da hannunta.
Goya jakar tayi abayanta, ta fito daga ɗakin, gidan shiru babu kowa a falon alamar duk sunyi bacci adakunansu..
Bata nufi ko'ina ba sai ɗakin Chief, tana ƙarasa bakin kofar takai hannu zatayi knocking sai taji ƙofar ta fara kokarin buɗe kanta ta ɗanyi mamaki
Almost 3 times tana yin sallama ba'a amsa mata ba, ta kutsa kai ta shiga ciki, bata ga kowa ba, sai dai taji sautin safkar ruwa daga toilet dinsa, wurga ido tayi tare da kallon glass wall din toilet nasa yayi duhu sama ka dai take iya gani..
Gajiya tayi da tsayuwa, ga wata kasala da take ji, wasa wasa ta fara gyangyaɗin bacci, har ta saki backpack din hannunta ta fadi kan floor ba tare data lura ba..
Lokacin daya fito waist dinshi ɗaure da towel fari kyal, fatar shi tayi freshi danshin ruwa ya jiƙata...yana kokarin ɗaga kafa ya nufi dressing mirror ba zato ba tsammani ya hango mutun kwance kan rug kamar an jefar da ita a gurin ta baje sai sharar bacci take yi, ga backpack ɗinta yashe gefe ɗaya...
Yayi mamaki cos bai tsammaci zai iske ta adakin ba, ya daisan ya cire security din kofar, abun da ya fi daure mashi kai ta yadda bacci yayi awon gaba da ita akan rug dinsa, kamar wadda tasha kwaya..
Walking slowly ya nufi rug din Ya zuƙunna daga gabanta, ya nutsu yana kallonta, yanayin yadda take fitar da numfashi cikin nutsu kirjinta na sama da kasa ba karamin tafiya tayi da imaninsa ba, kamar jinjira la66anta sai kerma suke.
Sai yanzu yayi tunani me ya hanata bacci da wuri? tabbas akwai damuwa aranta wanda silar hakan ta kuntata kanta ta hana idanunta bacci shiyasa da tazo dakinshi baccin yaci karfinta har yai awon gaba da ita batare da sanin ta ba..
Baya jin zai iya tada ta daga baccin, bai shirya katse mata jin dadin ta ba, baccin da takeyi sauki ne agare ta.
Yanke shawarar canza mata gurin kwanciya yayi, A hankali ya sanya hannayen shi biyu ya tallabota ya dago da ita tare da miƙewa Ya nufi katafaren gadon shi da ita, kusan itace mace ta farko da zata kwanta akan shi,
A tsakiyar mattress din Ya shimfidar da ita, duk da baccin da takeyi hakan bai hanata jin dadin sauyin gurin kwanciyar da akayi mata ba, numfashinta har canzawa yayi, lallausan duvet ɗinsa ya janyo ya lullu6e ta shi har zuwa kan kirjinta, kasa janye idanun shi yayi daga kallon ta gaba ɗaya ya shagala da kallon kyakkyawar sexy face dinta wani irin yanayi ya fara ji a jikin shi hakan yasa shi saurin miƙewa Yabar gaban gadon, badan bai yarda da tsoron Allahn shi ba sai don gujewa sharrin shaidan...
Can cikin bacci kunnuwanta suka soma jiyo mata daddaɗar kira'ar karatul qur'anin shi, kamar amafarki take sauraron karatun a lokaci yana zaune kan darduma jikinshi sanye da farar jallabiya, raba dare yayi yana kai kukansa gurin Allah, bayan ya kammala ya buɗe kur'ani yacigaba da karantawa.
Yana tsaka da karatun, tayi wani kwakkwaran juyi cikin bacci ta dinga mirgino kiris Ya rage ta kundumo ƙasa, yana gani yai hanzarin miƙewa yai saurin tallabota da hannayen shi biyu..
Zuƙunnawa yayi gaban gadon ya bi ta da kallo, ganin kamar tana kokarin buɗe idanunta, biji biji ta fara ganin kamar mutun a kusa da ita aranta ta ayyana anya ba mafarki take ba"?
Murya na rawa ta furta"Batool" shiru ba'a amsa mata ba
"Aunty ummi" still ba amsa mata ba
"Sajeed" nan ma shiru ba'a amsamata ba
Murza idanunta tayi da yatsunta, don ta samu damar ganin wanene...wani irin faduwar gaba taji lokacin da idanunta suka washe ganinta ya dawo normal, kokwanto ta farayi anya Chief ne? Ko dai mafarki ta ke ba? Taya za'ai chief ya shigo dakin su"? Kwata kwata ta manta abun da ya faru.
Tunani tayi ko Danish ne ya koma mata Chief,
Cikin disasshiyar murya ta furta"Danish"
Jin shiru bai amsa mata ba, yasa ta fara kokarin miƙewa da wata irin kasala a jikin ta, zama tayi tare da jingina bayanta jikin headboard.
"Kin tashi lafiya"? sexy voice dinsa ce ta ratsa kunnanta, firgigit ta ware idanunta sosai akan fuskar shi wani irin faduwar gaba taji, a rude ta kalli bedroom din sai yanzu ta gane adakin wa take..nan take ta tariyo abunda ya faru daren jiya bayan ta zo dakin shi bacci yaci karfinta adakin shi...tsabar rudu jikinta na kakarwa ta zabura zata sauko daga kan gadon ai kuwa gaba ɗaya jiri ya kwasheta kiris ya rage ta kifa kasa da sauri Chief Ya janyota ta fado kan laps dinsa, wata irin kunyace ta kamata, ta runtse idanunta la66anta na kerma tace"i'm really sorry, I didn't know I fell asleep in your room dan Allah ka yi haƙuri ka yafe mini"
Ƙamshin turarenshi ya hana ta ƙarasa maganar saboda ratsa makoshinta da yayi.
Batai aune ba taji numfashin shi na kokawa da nata numfashin
Jin shiru bata ji move dinsa ba yasa ta ɗan kyalla ido ɗaya don ta ga wani hali yake ciki
Unexpectedly suka haɗa ido cikin na juna, sam ta kasa runtse idanunta..
gani take kamar amafarki wai yau gata ga chief, ya ɗauketa kamar yar jinjira..bakomai take tunawa ba face maganganun daddynta, duk da bai fito fili ya faɗa mata wanene mijin da yayi mata ba, taji aranta Chief ne, kuma tabbas taga abunda yake kokarin ankarar da ita, Chief ya haɗa komai da zaisa mace ta so shi.
Matsawo yayi da fuskarshi saitin tata, har tsinin hancinsu ya gogi na juna anata wautar tayi azaton kiss zai mata abaki, gaba ɗaya tabi ta dabarbarce kamar wadda electric shock ya kama, ƙayataccen murmushi ya sakar mata har dimples dinsa ya lotsa aransa ya yi mamakin kamun kanta cos yadda mata ke hauka a kanshi da wata ce ta samu kusancin nan da shi tuni zata ƙwaye masa.
Ya riga da ya fahimci me zuciyarta ke raya mata..
A hankali ya sauke ta kan floor din. da sauri ta miƙe tare da sunnar dakanta kasa.
Veil dinta dake ajiye kan gadon shi ya dauko ya yafa mata akai tare da naɗe mata shi.
"Thank you.." tafiya tasoma yi zata bar dakin ya dakatar da ita"ban gama magana da ke ba" tsayawa tayi tare da juyowa ta dube shi
Zama yayi gefen gadonshi, da yatsan shi Ya nuna mata backpack din data kawo ma shi
"Buɗe min jakar" da sauri ta dawo ta zukunna ta bude backpack din..
"Ki curo komai dake aciki" ta amsa mashi da toh, bayan ta kammala curo kayan dake a cikin jakar ta jerasu kan floor.
"Ki buɗe min textbooks din, Inason ganin meke a cikin su.."zama tayi dirshan kafin ta fara bude shafukansu harta kammala Ya rage saura Diary din Unaizah..
"Zaki iya karanta min" ɗaga mashi kai tayi alamar eh a gogo ya kalla saura rabin awa afara kiran sallah asubahi.
Kasa kunne yayi yana sauraronta, yayin da idanunshi ke akan tausasan pinkish lips dinta ta zaƙe sai karanta mishi takeyi da zazzaƙar muryarta.
Kafin ta kammala karantawa tuni idanunta sun cicciko tab da kwalla, saboda akwai chapters na rayuwar Unaizah da suka ta6a zuciyarta, duk wani abu daya faru da ita mai dadi ko mara dadi sai da ta rubutashi.
shi kanshi chief dake sauraronta zuciyarshi ta karaya da jin irin rayuwar sharholiyar da yarinyar tayi tare da iyayenta batare da sun tsawatar mata ba, saima suka bada gudummuwar gur6ata rayuwarta, hakan na nufin dama cen mahaifinta ya sadaukar da ita shiyasa ya wulakanta rayuwarta ya hana tasan addinin shi don kada Allah ya tuhumeshi aranar gobe kiyama saboda shi jaki ne.
Cikin shesshekar kuka tace"na gama karantawa"
Mika mata hannu yayi ta bashi diary ɗinta, shafin farko ya duba shi anan yaci karo da corners na hotuna guda uku babu biyu sai ɗaya daya rage na Unaizah.
A cikin zuciya ya karanta sunayen dake akasan gidan hoton
_My lovely dad, Red Neck, and my first love, my momma, and me, Unaizah, Yar gidan daddy_
ya shafe mintuna Yana kallon hoton Unaizah ya rasa a ina ya ta6a ganin fuskar nan!
"Red neck, sunan wanene"? Cikin kunnanta ta tsinkayi muryar shi
Sai lokacin ta tuna da sunan mahaifin Unaizah, da sauri tace"Nickname din daddynta ne, Jan wuya" jinjina kanshi yayi
"Kin ta6a buɗe diary din nan"?
"Eh, amma ban ta6a karanta rubutun ciki ba sai yau" Ya juyo mata shafin farko da yatsa ya nuna mata wurin da ya kamata hotuna su kasance.
"Ina waɗannan hotunan suke, ko lokacin da kika fara buɗe diary din haka kika gan shi da hoto ɗaya"?
Bata san ya akai ta tsinci kanta da jin faduwar gababa, shiru tayi tana kokarin tunanowa sai dai ta kasa,
ganin kamar ta rudene yasa chief aje diary din, Ya janyo drawer chest din gadon shi, Ya curo diary dinshi hadadden gaske, mai gidan key a jikin shi ya buɗe tare da nuna mata shafin farko, Hoton daddynsa ne mai girma sharafuddeen tare da Mommynsa Malikat sarauta, Ga hoton shi a tsakiyar nasu lokacin baifi shekara shabiyar ba.
"Kinga yadda nawa ɗiary din Yake! Kuma naga kamar kusan iri ɗayane da nata, zai iya yiwuwa akwai hutanan a jiki cos ga shaidanan alamar an ta6a manna hotuna a jikin corners din, watakil cikin rashin sani kin ta6a buɗe diary din hotunan suka faɗi without your knowlegde" ❓❗❔❕
*DAGA ALƘALAMIN BOSS BATURE🔥✍️*
*Ga me bukatar karanta littafin kurkukun kaddara, 500 ne za'a tura Via Opay, 8103884440 Hafsat Bature Muhammad, shaidar biya za'a tura ta whatsapp, 08169856268 ko 08103884440*