Ya faɗa yana ƙoƙarin taimaka mata don ta tuna.
Shiru tayi fuskar ta da alamun ruɗu sam takasa tunawa, Girgiza kai ta ɗanyi"bazan iya tunawa ba, dama hoto ɗaya ne akai..." bata ƙare maganar ba ya katse ta da cewa"zan baki lokaci, ki nutsu kiyi tunani a ina hotunan suke, cos inaji araina akwai hotunan nan biyu da babu jikin diary din, pls ki kokarta ba karamin taimako zaiyi mana ba gurin gudanar da binciken mu"
jinjina mashi kai tayi"in sha Allah zanyi kokarin in tuna" rufe Diary dinsa yai tare da maida shi cikin drawer.
Kiran Sallar asubahin farkone Ya karaɗe kunnuwansu, mikewa tayi da sauri tace"zan iya tafiya" ɗaga mata gira yai alamar eh..
Juyawa tayi da sauri ta nufi kofar fita, bai daina kallonta ba, har saida ta 6ace ma ganin shi.
Cikin tafiyar sanɗa take taka matalar benan gudun kada wani ya ganta ta fito daga ɗakin Chief a irin wannan lokacin, kamar wata munafuka.
Kwata kwata bata lura da mutun agabanta ba, sai yan waige waige takeyi kamar wuyanta zai balle Unexpectedly tayi tuntu6e da faffaɗan kirjin shi.
tsabar tashin hankali kusan suman tsaye tayi tunkafin ma ta kalli fuskarshi ta riga da ta gane wanene!
Ja da baya ta ɗanyi tare da sa tafin hannu ta dafe handrail ta ɗago tare da kallon shi from head to toe tayi mamakin ganin sleeping dress dinsa kalar na jikinta launi ɗaya, idanun shi manne da shade fari ya ɗaure sumar kan shi ta baya, ba karamin kyau yayi mata ba sai dai ta ji shakkar yanayin shi, ya haɗe rai kamar bai ta6a murmushi ba, Allah kadai yasan tun yaushe yake tsaye.
Ido cikin ido suke kallon juna batare da kyaftawa ba
tayi mamakin ganin fuskarshi a yamutse idanunshi sun dan kumbura da alamun rashin bacci atattare da su, ko me ya fito da shi a wannan lokacin? Ko dai damuwar maganarsu Salsabeel ce ta hana shi runtsawa ne"? Aranta ta ayyana hakan.
Shiru babu wanda yayi magana sai sautin numfashinsu dake fita har na tsawon mintuna biyar kafin ta katse shirun nashi da faɗin"My man, me kake haryan zu ba ka yi bacci ba"?
Shiru bai tanka mata ba
"How long have you been here"?
"Tun lokacin da kika shiga bedroom ɗinsa" waro idanu waje tayi sam ta kasa magana sai yan kame kame ta ke yi.
"Me kike yi adakinsa? Har na tsawon awanni hudu"? He asked throwing her a suspicious look She could see the jealousy on his face
Muryarta da inda inda tace"am..um..dama ɗazu ne da dare naje kai mashi backpack ɗin Unaizah daya bukaci yana son ganin ta saboda binciken da suke yi, shi ne da na shiga dakin na iske ya shiga toilet wanka, bansan bacci ya dauke ni ba, sai yanzu na farka..."
kasa karasa maganar tayi ganin yadda ya matso kusa da ita kamar zai rufe ta da bugu tuni tasha jinin jikin ta, bakomai yake kallo ba face kayan baccin jikinta sunyi uban squeezing kamar an kwatosu daga bakin kura, zuciya da saƙe saƙe saita dinga hasaso mashi abinda ya shiga tsakaninta da chief har wani jirin 6acin rai yake gani a cikin idaninsa.
Da wata irin kasalalliyar murya tamkar tame jin bacci ya furta"na yarda dake nasan ba zaki iya cin amana ta ba, amma meyasa zaki je dakinsa ki ɗauki lokaci har haka? Ki rasa inda zaki bacci sai dakinsa"?
Dafe kai tayi da hannu ɗaya harta fara tunanin lallashin shi ta bashi hakuri amma da ta tuna maganar daddynta sai ta samu kwarim gwiwar cewa"Sai me Danish in nayi bacci dakinsa? Fiye da haka ma zan iyayi!" gabansa ne ya fadi cike da mamaki yake kallon ta
"Ka bani kunya my man, ka rasa wa zaka butulce mawa sai Chief? Da ya Salsabeel? i heard everything daya faru tsakaninka da Chief" ta fada tana galla masa harara
"Wai har elders kake ikirarin basu ta6a cutar da rayuwarka ba, kuma sune kake kallo amatsayin iyayenka! Are you crazy? Ko ka fara shaye shaye ne"? Ta fada tana kallon cikin idanunshi, babu alamun zai tanka mata, kamar ana tunzurata ta cigaba da cewa
"Saboda me zaka ƙi ba su haɗin kai? Meyasa zaka rufawa Elders asiri? Ko dai kun haɗa baki da su? In ba haka ba, tayaya zaka rufa asirin miyagun da suka kaskantar da rayuwarka saboda muguwar manufarsu akanka"! Runtse idanun shi yayi gam maganarta ta daki zuciyarshi bai ta6a zaton zaiji kalaman nan daga bakin ta ba.
"Hmmm, dama nasan ba zaka ce komai ba, saboda baka da gaskiya Danish! I have been suspecting you for a long time since we were in prison baka ta6a faɗamin komai dangane da kurkukun ƙaddara ba, ni ban ma ta6a sanin me ake aikatawa a cikin kurkukun ba sai da karanbani na yakaini na gani da ido, meyasa ka boye min a lokacin uhyum"?
Bata jira amsar shi ba ta daura da cewa"Bayan haka ranar da Giants suka zo daukar Batool da hannunka ka miƙata, ta rayu ko ta mutu, baka damu ba, hakan na nufin kaima da sa hannunka ake akaita komai, watakil ma ɗan leƙen asirin su ne halan...." kasa karasa maganar tayi sakamakon bugun handrail da yayi da tafin hannun shi, saboda zafin maganarta dayaji, buɗe idanunshi yayi sun kada jawur ita kanta sai da taji gabanta Ya faɗi amma ta dake ta jajirce don ta harzuƙa shi tayi karfin hali cigaba da magana
"Ka sha faɗamin kai garkuwane agareni, mai bani kariya, zaka iya komai dan farin cikina, Danish Ina son na tabbatar da son da kake min, shin zaka Iya sadaukar da farin cikin ka saboda nawa" ta fada batare da ta kau da ido daga kallon shi ba..
Jinjina mata kai yai alamar eh, murmushin gefen fuska ta dan saki kafin ta haɗe fuskarta tamkar bata ta6a dariya ba.
"Danish, Inaso ka yi masu jagora zuwa gidan Kurkukun ƙaddara..."
bata kare maganar ba Yai hanzarin furta"bazan Iya ba, pls kada ki tursasamin inyi abunda banyi niya ba..." a rude yake maganar
da kakkausar murya tace"nasan zaka Iya ne shiyasa na umarce ka da kaje, saboda ni nasan wanene Man dina, kada ka bani kunya, bansan ka da tsoro ba.."
"Bazan je ba, bana son duk wani abu da zaiyi silar raba mu, suma ina jiye masu haɗarin da zasu jefa rayuwarsu, Ja da Elders ba abune mai sauƙi ba, basu da karfin da zasu iya farmakarsu please understand me..."
fuskarsa ayamutse yayi maganar
"Danish Idan har bazaka je ba, to inaso ka sani zan yanke duk wata alaƙa dake a tsakanin mu! Saboda bazan ta6a auran ragwon namiji ba, matsoraci wanda bazai iya jefa rayuwarshi cikin hadari don ya ceci rayukan Al'umma ba ya kuma kawar da masu aikata zalunci a doron ƙasa.."
waro idanunshi waje yayi tamkar kwayar zata faɗo ƙasa.
"Chief yafika jarumtaka, yana da zuciyar imani da tausayi, baisan mu ba, bai hada alakar komai damu ba, amma saboda kyakkyawar zuciyarshi burinshi Ya taimaki rayuwarmu data sauran yaran dake agidan kurkukun kaddara sannan ya kawar da miyagu a cikin al'umma bai damu daya rasa ranshi ba! a shirye yake da ya sadaukar da ranshi saboda ya ceci rayuka kaifa? Ta jefa mashi tambayar shiru yayi bai tanka mata ba
"Saboda kai na hakura da burina na ganin na auri attajirin mai kuɗi mai asali ɗan babban gida, mai ilmin addini dana zamani, naji zan iya rayuwa dakai ahaka saboda kaunar da nake maka, amma meyasa kai ba zaka iya hakura da ra'ayinka akan nawa ba"?...dakyar ta ƙare maganar saboda hawayen da suka kubce mata tana mai jin takaicin tilasta masan da take kokarin yi.
"Danish baka da komai, in banda kyan da Allah yayi maka, If I marry you, how will I be proud of you"? Cikin shesshekar kuka ta faɗa
"Ace na auri ragon namiji mai tsoron zuwa yaki? Ko arne mara addini? Ko kuwa jahili dabaisan komai ba? Ko matsafi mai goyon bayan matsafa wurin aikata zalunci"!
Kiris Ya rage Ya yanke jiki ya fadi saboda wutar bacin rai data ziyarci zuciyar sa
Maganganunta sun ta6a zuciyarshi ba ƙadan ba, Yaji zafin su sosai, ita kanta ta tsorata da ganin yadda gumi ke tsastsafo ma shi, duk da tana jin tsoron kada Evil's heart dinsa ta motsa, amma dayake idanunta sun rufe burinta kawai ya amsa bukatarta.
Da wata irin karyayyar murya mai cike da 6acin rai ya furta"Angel, mafarki nake ko gaske? Da kanki kike jifana da waɗannan munanan kalaman? ni Angel? Your Shield"? numfashi ya ɗan ja kamar bazai iya karasa maganar ba yace"meyasa zaki min haka? Lafin me nayi maki da cancani cin mutunci daga gareki? Angel kema Kina min kallon jahili? Mara asali? Kuma kika kira ni da matsafi"?
ɗaga mashi gira tai"Hell fucking yeah, ko nayi ƙarya ne"? Kasa magana yayi,
"abu ɗaya ne zakayi wanda zai wanke ka daga gareni, shine Ka cire tsoro, Ka basu haɗin kai akai farmaki gidan kurkukun kaddara, ta hakanne kaɗai zan yarda dakai in kuma har ka bijire min kaki bin Umarnina, wlh na rantse da wanda raina yake a hannunsa muddin baka bada goyon baya ba, na kwammace in mutu da ciwon sonka, akan in aure ka"! Da sauti mai karfi tayi maganar tare dakai hannu ta daki handrail..
duk abunda ke faru tsakanin su babu wanda ya sani
"In kuwa har ka bari Chief yayi nasarar ruguza kurkukun ƙaddara batare da taimakonka ba, zan mallaka mashi kaina..." bata kare maganar ba sakamakon zazzafan marin daya kwasa mata wanda shi kanshi bada sanin shi ba, a karo na farko data fara jin tafin hannunsa akan fuskarta da sunan mari, wa'iyazubillah wani azababben radadi taji ya ratsa sassan jikin ta kamar an watsa mata wuta jirine Ya kwashe ta, ta tafi zata kife ƙasa cikin zafin nama Ya taro ta da hannunshi ya dawo da ita kan kirjin shi, yayi hanzarin daukarta kan kafadarshi Ya nufi bedroom dinshi da ita gudun kada wani ya riskesu a halin da suke a ciki.
Yana shiga ɗakin Ya kwantar da kan gadon shi, kamar matatta, da alama suma tayi saboda azabar da taji.
Hankalin shi idan yai dubu toh ya tashi, Jikinshi sai kerma yake kamar wanda sanyi Ya kama, zafin Kishi Yaja mishi bala'e..
Duk da sanyin A.c din dakin hakan bai hana gumi tsastsafo mashi kan fuskarshi ba, zukunnawa yayi daga bakin gadon yana kallon gefen fuskarta, shi kanshi Ya tsorata da ganin yadda fatar gurin tayi ja sosai, shatun fingers in shi ya fito ruɗu ruɗu.
Yatsun hannayen shi Ya zuba ma Idanun shi Yana kallon su cike da danasanin marin da yayi mata, ya san yadda marin Evil giant yake da zafi, zata Iya kai Sati da radadin dafin marin a jikin ta.
cike da takaici ya dinga bugun kanshi da hannayen shi kamar zai zauce saboda zafin abun da ya yi mata
Tuni hawayen da suka taru cikin idanunshi suka fara Yar tseral kan kuncin shi, abu biyu ya haɗe mashi ga zafin munanan kalaman data jefe shi da su ga takaicin marin da yayi mata.
Cikin karyayyar murya ya furta"ba laifina bane, ke ce kika bata min rai, gashi kinja na mareki bada son raina ba" ya faɗa tare da daura tafin hannunsa saitin inda Ya mare ta, dabara ce ta fado mashi da sauri ya saita fuskar shi saitin tata, sihiri gaskiyar mai shi, ruwan hawayensa dake ɗiɗɗiga kan fuskarta sune suka goge tabon marin da ya yi mata cikin kankanin lokaci fatar ta dawo fara sol kamar ta jinjira, numfashi Yaja tare da sauke ajiyar zuciya a hankali launin idanunsa suka dawo yadda suke.
kallonta da yake yi ahaka yafi masa kwanciyar hankali akan Ya farfaɗo da ita saboda fargaban masifarta.
Daga gefenta Ya raba jikin shi, Ya kwanta tare da lumshe idanun shi, bai ta6a fuskantar tashin hankali irin na yau ba, tayaya zai iya shawo kan Unaisah ta fahimci abunda yake nufi"?
Kwatsam yana a cikin mawuyacin halin nan ba zato ba tsammani ya tsinkayi Muryar Khala a cikin kunnanshi..
"Uhum Garkuwa Namu"
A rude Ya mike zaune yana bin dakin da kallo, cikin sauri Ya share hawayen fuskarsa, jikinshi har 6ari yake garin zumudin ya sauko daga kan gadon, Hasken ɗakin shi ne Ya dauke ɗuff Duhu Ya mamaye ko'ina, bai nufi ko'ina ba sai gaban mirror Ya yaye madubin idanunshi su ka yi mashi tozali da tsohuwa Khala zaune kan armchair, Cikin shigarta ta gado fuskarta a yamutse ba annuri.
Zama yayi kan Mirror chair din with respect ya gaishe da ita, da fara'a ta amsa mashi
Kafin Ya nutsu Yana jiran jin me zata ce ma shi
"Ina fata kun fara shirye shiryen kawo farmaki"? shiru ya yi baice mata uffan ba.
Yanayin dake a kan fuskarshi ta nazarta nan take ta fahimci baida matsaya
Yar dariya tayi"jikana, faɗamin ba, me ake Ciki ne"? dakyar Ya labarta mata abinda ke faruwa bai boye mata komai ba
Girgiza kai tay"yaro man kaza, Har yanzu Jinin Elders ne a jikin ka, amma Alhamdulillah naji dadi da Allah Ya bani ikon ganawa dakai a karo na biyu, saboda na fahimci ka na bukatar in wayar maka dakai, in kuma yi maka karatun ta nutsu ta yadda zaka fahimci su wanene Elders da kuma dalilin dayasa suka raine ka..." aruɗe Yake kallon fuskarta...
"Kasan wacece ni, ka kuma san matsayina agidan kurkukun kaddara, nafi ka sanin komai Danish, duk wani abu da suke aikatawa a tafin hannuna yake" ta faɗa tana nuna mashi tafin hannun ta.
"Abu na farko da baka sani ba, Elders Mayaudara ne, Maha'inta, maciya amana, bansan ko ka san da labarin nan ba, amma inaso ka sani tun kana jinjirinka cikin tsummanka suka sace ka daga wurin iyayenka, suka rabaka da su batare da saninka ba, sannan suka sadaukar da kai zuwa gidan kurkukun ƙaddara, Ni nasan su wanene Iyayen ka, wallahi basu san kana araye ba, an yaudare su ne da sunan ka mutu...." dafe kanshi yayi da hannu ɗaya zuciyarshi cike fal da ruɗanin maganarta, bazai ce tayi karya ba sai dai kokwanton da zuciyarshi keyi bazai bari ya aminta da ita ta cikin sauƙi.
"Bani da isasshen lokacin da zan yi maka bayani, amma atakaice ka zauna kayi nazari Danish, kai ganau ne ba jiyau ba, kasan komai, har yau zubda jinin mutane suke yi kamar kwari, Laifin me suka yi masu? Ahaka zaka rufa masu asiri uhyum? Ita kanta yarinyar da kake gudun rabuwa da ita ba zasu kyale ta ba, wallahi in har baka bada goyon baya an kawo karshen su ba, da kai da ita sai kun salwanta, saboda suna nan suna shirin yadda zasu kashe ku.."
waro idanun shi waje yayi jin abinda tace.
Murmushin gefen fuska ta saki tare da jinjina mashi kai"hmm wai kana tunanin Suna kaunarka? To wallahi ko ɗaya basu ta6a kaunarka ba, sun raineka ne don biyan bukatar kansu, idan kai me hankali ne ga misali nan, Yanzu da suke ganin sunci moriyarka amfaninka ya kare kana neman tona masu asiri ba ga shi har sun ɗauke mukamin da suka baka na garkuwarsu ba, sun ba Jeremiah, kai kuma nema suke su salwantar da rayuwarka saboda kai kadaine kasan sirrinsu dakai kadai za'a iya farmakarsu...."
wani irin gumin tashin hankaline Ya wanke fuskarshi, Maganar tsohuwa khala tayi matuƙar yin tasiri a zuciyar shi.
Kusan sau uku Tana ambaton sunan shi bai amsa mata ba, saboda zuciyarshi ta lula duniyar tunani
Har saida tayi mashi gyaran murya kafin ya dawo hayyacin sa
"Ina Gabriel? Ya rayu ko ya mutu"? ya ɗanyi mamakin jin ta tambayi gabriel ko a ina ta san shi"?
"Yana adakinsa, bacci yakeyi"
"Masha Allah, Naji dadin jin hakan, sai dai, Yar Uwarsa daya bari agidan kurkuku tana acikin mawuyacin hali..."
"Who's she? ya tambaya don sam ya manta da cewa Gabriel Yana da sister.
"His twin sister Gabriella...." a takaice ta labarta mashi rashin imanin da tsohuwa inno tasa giant yayi mata, tsabar 6acin rai jikinshi har tsuma yakeyi
"ta rokeni akan Tana son ganin ɗan uwanta, nayi mata alkawarin ko zan rasa raina ne in dai muna da tsawaicin kwana zan haɗa ta da ɗan uwanta" cikin rauni na murya tayi maganr tare da mikewa daga kan kujerar da take, ta haske mashi Gadon da Gabriella take akwance kamar babu rai a jikinta, sai jan numfashi take dakyar dakyar
"Nayi zaton ta samu lafiya, amma wani abu ya faru jiya wanda Ya ɗaga hankalina, tana daga zuƙunna tayi aman Jini, ta dafe ciki tana faɗin Yan hanjinta suna konewa, Inaji araina Inno ce tayi mata asiri, nadai yi kokarin yi mata yan dabaruna ahaka Jikin da sauƙi amma tana bukatar taimakon gaggawa daga gare ku idan ba haka ba da wuya ta rayu.."
Jikin shi yayi sanyi saboda tsantsanin tausayin yarinyar daya kama shi, yanzu ya tuna ranar farko da aka kawo su har tsohuwa Zafreen tasa aka raba su.
"Danish Ahaka zaka rufa masu asiri? Shikenan babu wani wanda zai kawoma bayin Allah dauki! Haka zamu barsu su cigaba da azabtar da rayuka? Ba zamu ɗauki mataki ba"? Sam ya kasa magana saboda raunin da zuciyar shi tayi
*Da wata irin kakkausar murya ta firta"YA RAGE NAKA GARKUWA, DOLE ƊAYA CIKIN BIYUN NAN YA FARU! KO DAI KA BADA GOYAN BAYA AKAWO MASU FARMAKI, KO KUMA SU SU KAWO MAKU FARMAKI SU GA BAYAN KU..."*
Sau Uku ta maimaita Hakan, kafin ta cigaba da ƙarfafa mashi gwiwa daga bisani bayan ta ƙara jaddada mashi kwanan watan da zasu yi black night, ta bashi wasu muhimman bayanan da zasu amfane su, daga nan ta 6ace ma ganin shi, kifa kanshi yayi gaban mirror ɗin Zuciyar shi cike fal da damuwa, anan wani wahalallan bacci mai nauyi ya yi awon gaba da shi.
Lokacin da Batool ta farka daga bacci taga babu Unaisah adakin, bata damu ba, bayan tayi sallar asuba, taji shiru bata dawo ba, hakan yasa ta miƙe ta fito daga dakin tafara neman ta, sai da tabi ɗakunan Yan uwansu duka ta duba taga babu Unaisah, Hankalinta ba karamin tashi yayi ba,.
Da sauri ta nufi ɗakin Aunty Ummunsu, tayi knocking almost 3 times, kafin ta samu Ummi ta buɗe kofar, tana miƙa hadi da yin hamma ko kayan baccin jikinta bata kaiga cire wa.
"Babe, Har kin tashi"? Daga mata tayi"Aunty Ummi sister tazo nan? Na farka banganta ba"
Girgiza kai Ummi tayi"Bata zo ba, kin duba ko'ina"?
"Eh," ta fada da damuwa
"Kada ki damu, nasan duk inda taje tana acikin gidan nan" ta faɗa tare da ruko hannunta"mu shiga daga ciki, Ki jira ni in shirya sai mu fito tare" amsa mata tayi da toh.
Bayan shigar su ɗakin, Ummi ta kunna mata kallo a laplop ɗinta, kafin ta shiga bathroom don tay wanka.
Nutsuwa tayi kan gadon tana kallon drama, ta shagala da kallon wayar Ummi ta fara ruri.
Ɗauko wayar tayi daga kan pillow, ta duba screen ɗin bata gane me aka rubuta ba saboda bata iya karatu ba..
Da karan banin ta tayi picking call ɗin kamar yadda taga Unaisah nayi, ashe video call ne, yanayin yadda ta ruke wayar yatsan hannunta yayi hiding front camera, wanda Ya kira bazai Iya ganin ta ba, kura idanu tayi aka fuskar mutumin dake kwance cikin bathtub, ruwan kumfa ya rufe Jikin shi fuskar shi kaɗai take Iya gani yayi shiru yaki magana itama tayi shiru taƙi furta kalma zuciyarta cike fal da tunanin wanene Wannan ƙaton.
"Ummi meyasa kike boye fuskarki? jira kike saina maki magana"? Muryar shi ce ta katse shirun ta..
Jin motsin buɗe kofar toilet, yasa ta danna end Call, da sauri ta mayar da wayar kan pillow ta aje.
Ta yi hakanne saboda Ummi ta ta6a gargaɗinta, akan in ankira wayarta bata akusa kada tayi picking dama bata ta6a kuskuren daukar mata waya ba saboda ta fahimci bataso.
Koda Ummi ta fito bata faɗa mata an kira wayar ba, bayan ta kammala shiryawa atare suka fito daga dakin.
Har wuraren ƙarfe tara, basu ga Unaisah ba, gashi Har time ɗin Yin breakfast dinsu ya yi gaba ɗaya yan uwansu sun hallara a dining ita kaɗai su ke jira sun yi neman har sun gaji kuma babu wanda yai tunanin tana adakin Danish.
Can cikin kunnuwanshi suka soma jiyo mashi sautin tarin ta, firgigit Ya farka da kasala Ya miƙe zaune Yana kallon ta da idanunsa waɗanda suka kumbura.
A hankali ta miƙe zaune tana Hamma Wata Irin Yunwa take ji, kwata kwata bata iya tuna abun da ya faru ba, fitsari ne Ya matse, saukowa tayi daga kan gadon da sassarfa ta shige toilet ɗinshi sai da ta gama tana kokarin fitowa idanunta suka sauka akan shi, Ya zafga Uban tagumi da tafukansa kamar wanda Ya rasa gata a duniya.
Nan take komai daya faru tsakanin su Ya dawo mata acikin tunaninta, gefen fuskarta daya mara ta shafa da tafin hannun ta, harara ta watsa mashi taja tsoki, kafin ta juya zata bar ɗakin.
takun tafiyarne Ya fargar da shi, da sauri Ya miƙe ya shagabanta kiris Ya rage kirjinta Ya bangaji na shi
"Bani bukatar Jin komai daga gare ka, bani hanya na wuce"! tana huci ta faɗa tana neman rabawa ta gefen shi don ta wuce
Cikin sauri ya ruƙo Arm ɗin ta, hakan yasa ta dakata da tafiyar
"I want to ask you one question."
shirun da tayi ne yasa shi fahimtar jiran shi takeyi
"baki tsoron ki rasa ni"?
"Danish, ko da Ina jin tsoron In rasa ka, Ka tuna ranka ɗaya ne tak! da shi kadai zaka Iya taimakon dubban rayuka, ka kuma yi silar tarwatsa gang din azzalumai"
"Angel, baki damu dana mutu ba? Ina kaunar da kike mini? Kin za6i da naje na bada raina"? jinjina mashi kai ta yi"nafi maka kwaɗayin ka mutu a filin yaƙi, kwara mu hakura da duk wani buri da muke da shi, mu bada rayukanmu donmu taimaki bayin Allah, in sha Allah ko bamu ji dadi anan ba, zamuji acan, in ba haka ba mutanan nan bazasu ƙyalemu muyi rayuwar farin ciki ba, saboda mun san sirrin su kuma mune na farko da muka gudu daga gidan kurkukun ƙaddara, mun tona asirin su, zasu nemi hanyar kashe mu ne, ka fada min taya zamuji dadin rayuwa da fargaba a zukatan mu? Kaima fa har yanzu suna atare kai, Ka tuna abunda kayi min rannan, wata rana har kashe ni zaka iya yi ba acikin hayyacin ka ba, dan Allah ka fahimce ni, rayuwa bazata yiwu ahaka ba, kana bukatar ka zama cikakken mutun"❗
duk yadda taso ta jure saida idanunta suka cika tab da kwalla kwata kwata bataso Yaga rauninta, tafi son yasan da gaske take don ta samu ya amince.
Batai aune ba, Taji Ya zube kan gwiwowinsa, A hankali ya jinginar da kanshi jikin laps dinta, ya zagayo hannayen shi kan waist ɗinta ya ruƙe ta gam, da wani irin hucin zafi numfashin shi ke fita ya riga daya sadaƙas Angel had already won him over, dole Ya mika wuya, abu ɗaya da bazai ta6a mantawa ba, munanan kalaman da ta furta mashi, tabbas Yana son wata rana ya bata mamakin da zaisa tayi danasanin abunda tayi masa.
Cikin karyayyar murya tamkar ta majinyaci Ya furta"Na amince, zan basu haɗin kai, all because of you, Whatever happens to me, blame yourself .." kasa ƙarasa maganar yayi saboda raunin da zuciyar shi tayi..
Angel dake tsaye kamar gunki tana kallon sumar kanshi, ruwan hawayen ta dake gangarowa kaitsaye suka ɗiɗɗiga saman sumar kan shi, baiwar Allah duk sai taji ba daɗi, Zuciyarta ta karaya da kalaman shi,.
Ta rasa farin ciki zatay da amincewarshi ko bakin ciki? ita dai tasan Ita da kwanciyar Hankali sunyi bankwana.
Yatsun Hannunta na kerma Ta shafa sumar kan shi, dakyar ta banbare hannayenshi daya ruke waist ɗinta da su, ta fuce daga ɗakin, akan flooe Ya kwanta tamkar babu jini ajikin shi.
maganganun mutun biyu ne sukayi tasiri akanshi, Tsohuwa Khala and his Destiny, yaci alwashin duk runtsi duk wuya sai yaga bayan Elders sannan Yana son yaje kurkukun kodan Ya haɗu da tsohuwa khala saboda yana son ta faɗa mashi su wanene iyayen shi saboda ya fahimci su kadai ne zasu iya bashi abun da akeyi mashi gori akai❓
___________________________________________✍️
Idan muka koma Gidan baba Obie, tun da Owais Ya faɗa ma Pravin zancen tafiyar da yake so suyi tare da baba Obie, Hankalin Shi ya tashi haiƙam, gaba daya ya rasa nutsuwar shi saboda bakin ciki Ya tafi batare da ya ƙarasa aiwatar da mummunar kudirinsa ba, wunin ranar a daki yayi saboda damuwa har hajiya saratu saida ta lura da yanayin shi har tambayar shi tayi meke damun shi yace mata bai da lafiya zazza6i ke damun shi ga owais ya nemi alfarmar ya raka baba Obie lagos, baisan ya zaiyi ba yana jin nauyin yace bazai je ba
Hajiya saratu tace bazaima yiwuwa ba, zatayi ma baban magana anemi wanda zai bi sa suje tunda shi ba koshin lafiya gare shi ba.
kafin hajiya saratu tayi ma baba Obie magana Pravin yaji labari awurin hajjaty, a jiya daya shiga ɗakinta ya iske ta zaune tsakiyar gado tana ta kuka ya tambayeta meke damunta, nan take labarta masa baba obie ya kira ta adakinsa ya sanar da ita gobe kafin ya tafi zaisa jami'ai su maida marwa garin su gurin iyayenta, zata fi samun kulawa agurin su su kuma zasu cigaba da bata tallafi.
Da jin wannan maganar, pravin ya washe baki, bai ma tsaya ya karasa jin karashen zancen ba, Ya fuce daga dakin Ya koma dakin hajiya saratu ya tambayeta shin dagaske ne za'a maida marwa garin su tace mashi eh, ay itace ma tayi ma baba obie magana amayar da ita saboda su twins tana son su dawo gidan da zama.
farin cikine ya lullu6e parvin harya manta da karyar ciwon da yakeyi yace mata ay yama ji saukin zazza6in zaibi baba obie suje lagos din, tace mashi a'a gaskiya tafi son ya wartsake in yaso daga baya sai ya bishi, yasa naci akan shi dai zaije tace meyasa zai takura kansa bayan ba koshin lafiya gare shi ba, ya marairaice mata fuska da dadin baki ya shawo kanta harta amince bazata fada ma baba Obie ba.
Washe gari da sassafe, jami'an da za su tafi da marwa, suka doko sallama, a lokacin hajjaty tana adakinta tare da sauran yan aikin gidan sun hadu suna shirya mata kayanta, Baiwar Allah sai kuka take yi su kansu kukan sukeyi na rabuwa da ita, bayan sun kammala shiryata Hajjaty da Abla suka daukota sauran masu aikin na abiye dasu A harabar ajiye motoci su ka iske mutanan gidan sun hallara domin yi mata bankwana.
A lokacin bakowa marwa ke kallo ba face pravin dake ta kashe mata ido yana sakin wani dan iskan shu'umin murmushi duk idan ya fakaici idon mutane, marwa tayi kuka kamar ranta zai fita, saboda bakin cikin zata tafi batare da ta tona asirin wanda yai mata aika aika ba..
har suka shigar da ita cikin mota bata daina gunjin kuka ba, haka ta dinga bugun window glass din motar da hannayenta kamar zata fasa shi.
babu wanda ya fahimci mai marwa take nufi, gaba daya sunyi tunanin zafin rabuwa dasune yasa take yin haka, har alkawari hajjaty tayi mata akan kullum zata dinga kiranta awaya sosai ta kwantar mata da hankali, bayan sunyi mata bankwana Akan idonsu Motar ta fuce daga gidan bayin Allah sunyi kukan Rabuwa da marwa.
Pravin kau ranshi fari tass Kamar ya zuba ruwa ƙasa yasha Hankalin shi ya kwanta baida sauran damuwa, Ya kira zaid awaya yayi masu albishiri na tafiyar marwa, Ya kuma labarta masu maganar tafiyar da zai yi tare da baba obie, sannan Yace su dawo gida Yana son ganinsu kafin su tafi.
Bayan dawowar su twins, murna awurin hajiya saratu kamar ta shekera bata gan su ba, cos tayi kewarsu ko kaɗan batai masu fadan zaman su a hotel ba, haka shima Uban saima tarairayarsu da ya ke yi.
Wuraren ƙarfe shabiyu na yau, gaba daya Yan family din dake a estate din suka yi ma baba Obie rakiya zuwa Airport kamar wanda zai bar kasar, hada Owais da su Senate Lateef kowa da kowa, kamar karsu rabu da shi saboda kaunar da suke ma mahaifin su.
________________________✍️
(After One Day, Bayan kwana ɗaya)
Yana tsaye gaban Dressing Mirror, har ya kammala shirin xuwa Office, jikin shi sanye da kakin shi, fuskarshi kwata kwata babu walwala tamkar bai ta6a dariya ba, saboda matsananciyar damuwar data yi mashi ƙatutu a zuciyarshi, Ga rashin isasshen baccin da baiyi ba jiya idanun shi sunyi ja sun ɗan kumbura.
Har ya miƙa hannu zai ɗauki watch daya daura gaban mirror kamar ance ya ɗago da idanun shi ya kalli mirror Unexpected ba Ya hango shi tsaye ta cikin madubin Ya goya hannayen shi akan kirjin shi, Jean da t.shirt ne a jikin shi.
wani irin faduwar gaba yaji saboda bai tsammaci zaiga mutun adakin shi ba! Taya akai ma ya shugo bayan kofar tana da security? Zuciyarshi ce ta bashi amsa da cewa ka manta sihirin dake ajikin shi? A sukwane ya juyo tare da kallon shi..
Yadda kasan wanda Ya ku6uto daga gidan mahaukata, Sumar kanshi ta yamutse, Fuskarsa ba annuri kamar bai ta6a dariya ba.
hankalin Chief ba karamin tashi yayi ba, ganin yanayin da Danish Ya faɗo ɗakinsa, ya rasa meke damun shi? Yayi rashin lafiya ne? Kai daga ganinsa ba lafiya ba.
muryar shi da ruɗani Ya furta"Danish? Meke damunka? Baka da lafiya ne"? Ya faɗa akagare da son jin amsar shi.
Cikin sanyin murya yace"zan baku haɗin kai, and I will lead you to the Prison of Destiny, I will help you fight them"
kamar amafarki yaji kalaman Danish saboda mamakin daya mammaye shi, hannu yasa ya ɗan murza kunnan shi don ya tabbatar ba makuwa yayi ba yace"dagaske kake ko wasa"?
"I'm serious..." tsabar farin Ciki yasa chief zubewa kan gwiwowinsa yayi sujjada domin nuna godiyarsa ga Allah.
a daren jiya ya raba dare yana yin Nafilfili akan Allah ya shiga lamarinsu ya kawo masu hanya mafi sauki da zasu farmaki Elders sai gashi cikin ikon Allah yau da safe Allah ya kar6i addu'arsa.
Lokacin daya ɗago daga sujjadar tsantsar farin cikine akan fuskarshi, miƙewa yayi tare da nufar Danish yayi hugging ɗinsa tighly kamar zai maida shi cikin shi saboda faranta masa da yayi bai ta6a jin masifar kaunarsa ba irin na yau.
Dagowa yayi tare da dafa kafadunsa suka fuskanci juna.
"Danish, bazan Iya misalta maka farin ciki da nake a ciki ba, Ka faranta min raina, amma kai da kanka kayi ra'ayin ka bamu hadin kai ko wani ya tilasta maka? Saboda yanayin ka ya nuna kamar bada son ranka ba"
Girgiza mashi kai yayi ba tare daya furta kalma ba.
"Kamar baka da lafiya"? Ya kuma tambayarsa
"Lafiyana lou, just ask me anything you want to hear from me, and I'll tell you."
abun nema ya samu da sauri chief ya ruko hannun shi ya zaunar da shi gefen gadon shi.
Kafin ya dauki wayarsa Ya kira landline din kitchen Ya isar da sakon akawo mashi breakfast ɗinsa da baiyi niyar ci ba, amma saboda suji dadin tattaunawa da danish shiyasa ya umarci akawo mashi.
Ba'afi mintuna biyar ba, kuku ya shigo hannayenshi ruke da wooden tray shaƙe da kayan abinci ya aje masu kan table kafin ya fuce daga ɗakin.
"Nasan kana jin yunwa, mu fara yin breakfast, kafin mu fara tattaunawar tamu" girgiza mashi kai yayi"bazan iya cin komai ba.." bai ƙare maganar ba chief ya katse shi"pls kada muyi haka dakai, ko kaɗan ne ka ci"
matsa mashi yayi dakyar chief ya shawo kanshi, bayan sun kammala yin breakfast ɗin, Chief ya cire Coat dinsa Ya rage daga shi sai vest, babu zancen zuwa Office, zuwan Danish Yafi komai mahimmanci a halin yanzu.
A tsakiyar gadonshi suka zauna suna fuskantar juna kamar malami da dalibinsa, sai da ya fara kunna audio recording din wayarsa, kafin ya tattara nutsuwarsa da hankalinsa akan Danish
*Daga Alƙalamin Boss Bature🔥✍️*
*Ga me bukatar karanta littafin kurkukun kaddara, 500 ne za'a tura Via Opay, 8103884440 Hafsat Bature Muhammad, shaidar biya za'a tura ta whatsapp, 08169856268 & 08103884440*