Zubewa yayi kan gwiwowinshi a karshe Ya yada kafadunsa kan floor.....
Yadda take a haukace, Ahaka Taj Ya nufi part dinsa da ita, sautin koke koken da takeyi ne yaja hankulan jami'an dake kai komo A compund din gidan zuwa ga kallon ta, gaba daya hankalinsu ya dawo kan su, Kamar mazurai haka suka zuba ido suna kallon Unaisah dake ta kokarin kwace kanta daga jikin daddynta, sun kwadaitu da ganin santala santalan cinyoyin ta, Yar rigar baccin duk ta nannade dama bata wuci gwiwarta ba...Bacin rai Ya hana Taj Ya lura da abunda ke faruwa..
Agaban kofar shiga falon part dinsa, Ya danna Password din ƙofar, ta bude kafin Ya shiga da ita ciki, adai dai Lokacin Yan uwanta sun kabbara sallar La'asar da ake ta kira, anan falo Danejo ta shimfiɗa masu prayer mat sun daidaita sahun su.
Kwatsam su ka jiyo kukan Unaisah hakan Ya ɗaga hankulansu a rude suka katse sallar, gaba daya suka kai dubansu ga Taj, sun firgita da ganin yadda Ya daukota a saman kafadarshi, sai hauka ta ke yi mashi, har suna hada baki gurin tambayar Taj meya faru da Unaisah.
bai bi takansu ba, Ya nufi bedroom dinshi da ita, adai dai lokacin Ummi da danejo sun sallame sallamarsu kusan atare suka mike tare da bin bayan shi.
Sai dai kafin su ƙaraso Taj ya datse ƙofar ɗakin.
A saman gadon shi Ya wurgar da ita gaba ɗaya ta kife kan mattress din gashin kanta ya tarwatse
Yana huci Yace"shashasha, wlh kin bani kunya, wlh badan kaunar da nakeyi maki ba da yau saikin yabawa aya Zakin ta, bugun tsiya zanyi maki, wawuya kawai, ban ta6a zaton za ki min haka ba, har yanzu kina nan da kafiyarki ta kuruciya, saboda soyayya bakya ganin kowa da gashi, shi kadai kike tsoron ki rasa, na fahimci ma kinfi damuwa dashi akaina, nima fa hadani za'aje kurkukun, amma kwata kwata bata ni kike ba..."!
Daƙyar ya ƙarasa maganar saboda ƙululun baƙin cikin daya tokare makoshin sa.
A hankali Hawaye masu ɗumi suka wanke fuskarsa.
Dagowa tayi agalabaice tana kuka ta girgiza mashi kai muryarta ashake ta furta"daddy ba haka bane, ka fahimce ni, kaifa mahaifina ne, wallahi na damu dakai, har abada bazan ta6a samun madadinka ba..."
bata kare maganar ba, Ya juya zai bar dakin yana huci, durowa tayi daga kan gadon da gudu ta nufe shi harya ruke handle din ƙofar, tay saurin rungumeshi ta baya ta zagayo da hannayenta kan stomach dinsa, ta maƙyalƙyleshi cikin shesshekar kuka take lallashin shi tare da bashi hakuri..
su ummi sai bugun kofar sukeyi don ya bude masu.
Hakan da tayi masa ba karamin sanyaya zuciyar shi tayi ba, tuni ya sauko daga kan dokin zuciyar da ya hau, A hankali Ya ruko hannunta tare da janyo ta ya dawo da ita ta gaban shi, Yayi hugging dinta tightly, a hankali yake shafa sumar kanta, duk da halin damuwar da take a ciki sai da taji sauƙin radadin da take ji a cikin zuciyarta.
cikin sanyin murya yace"komai ya wuce Unaisah, na daina fushi dake, raina ne ya 6aci amma yanzu na fahimce ki, kiyi haƙuri dukkanmu addu'arki muke bukata, amma kukan nan da kike yi da sanya damu aranki bazai ta6a canza mana kaddararmu ba, saboda addu'a ce kadai take canza kaddarar bawa, Ki yi mana addu'a Unaisah In sha Allah, zamu dawo cikin koshin lafiya.."
cikin kwantar da murya yakeyi mata nasiha, su Ummi dake tsaye bakin kofar dakin sunyi shiru suna jiran ya bude masu ƙofa..
daga bisani ya ruƙo hannunta suka shiga toilet, Ya wanke mata fuskarta, suka fito daga toilet din still hannun shi ruke cikin nata suka zauna kan gadon shi..
"Daddy, bazan kara kuka ba, zanyi maku addu'a, Allah ya kare min ku ya dawo min daku lafiya" tsananin tausayinta ya kama shi damuwar shi a haka zai tafi yabarta gashi yaji alamun zazza6i a jikin ta.
"Yawwa my daughter, yanzu kin share min kokwantona akanki, ni dama nasani, ƴata mai biyayya ce, zatayi abunda daddyn ta yake so.."
ya faɗa tare da shafa gefen fuskarta data kumbura jawur, wlh shi kadai yasan irin yadda yakeji azuciyarshi duk in ya tuna inda zasuje da kuma yarsa tilo da yake da ita, bayason wani abu ya faru kawai dai yayi imanin komai zai faru da su mai kyau ko mara kyau mukaddari ne daga Allah, Bawa bai isa ya guje ma kaddararsa ba.
"Banaso sauran Yan uwanki, su gane wani abu, pls kija baki kiyi shiru, ko da sun tambayeki me yasa kike kuka, ki fada masu wani abun daban, nasan kina da wayau basai na maki bayani ba "
jinjina mashi kai tay,
Rungumota yayi akan kirjinshi, ya fara janta da fira Yana tariyo mata kuruciyarta duk da halin damuwar da take aciki saida taji sanyi aranta.
"Nan dakina ne, Zaki Iya zama aciki kafin mu dawo, ga toilet ki shiga kiyi wanka.." amsa mashi tayi da toh..
Sumar kanta yaci gaba da shafawa, yadda ya sabayi mata tuntana yar kankanuwarta, ahaka yake samu tayi bacci, aiko cikin sa'a yaji alamun bacci yai awon gaba da ita, ajiyar zuciya ya sauke a hankali Ya kwantar da ita kan gadon, sai da yayi mata addu'o'i kafin Ya mike da baya da baya yake tafiya yana kallon ta idanunsa cike tab da kwalla.
Jiki asanyaye yajuya tare da buɗe room door ɗin Ya fito su ummi na ganin shi suka kewaye shi kamar yan jarida suka tsare shi da tambayar meya faru da Unaisah...
"bata Jin dadin jikinta ne, zanyi magana da dr, zai zo ya duba ta, yanzu bacci takeyi pls idan ta farka ummi ki taimaka mata tayi wanka taci abinci sannan ki sanya mata ido sosai.." basu kawo komai aransu ba, Ummi tace in sha Allah zanyi duk abunda kace.
Kallon Danejo yayi"My wife, Pls ki taimaka ma Ummi, Ku kula da su, " fuskarta dauke da murmushi tace"toh, daddyn Angel, kaima ka kulamin da kanka" sallama yayi masu, kafin fitarshi daga part din a ƙalla ya shafe mintuna biyar yana tunani kafin Ya fuce..💔
_______________________________✍️
*CHIEF OWAIS*
A Hankali Motar shi ta kunno kai cikin wani katafaren Resting Home na mai girma sharafudeen, tun kafin SA din dake driving dinsa yayi parking ta window glass din motar Ya hango Jami'an DSS kewaye da Courtyard din gidan dama kafin su shigo yaga sojoji tsare da gate din gidan hakanna ya dinga jin faduwar gaba.
Motarsu nayin parking bai jira an bude mashi car door ba saboda sauri da kanshi ya bude ya fito, with respect Dss din dake tsaye suka sara mashi, ko kallo basu ishe shi ba Ya nufi main door din falo.
Walking quickly ya haura Uptairs a gaban ƙofar katafaren Master suite na mai girma sharafudden ya ɗan dakata da yin tafiyar.
"Come In" daga cikin ɗakin Ya juyo muryar daddynsa
Da sallama ya shiga ciki a seating area ya hango shi A zaune kan wata katafariyar Sofa, ya dauki wankan tailored suit a jikin shi, yayin da idanun shi ke a manne da farin glasses, Hankalin sa na akan Apple Ipad din da yake pressing.
Madaidaicin table din gabansa na ɗauke da cups na cofee ...Ya daura kafa daya bisa daya.
Tun daga kan yanayin fuskar daddynsa Ya fahinci akwai damuwa, Karasa shigowa yayi tare da zukunnawa kan kafafuwansa agaban daddynsa Cikin girmama Ya gaishe da shi, sam babu walwala atare da shi Ya amsa mashi tare da nuna mashi sofa din dake facing dinsa
"have a seat," ya fada batare daya dago ya kallesa ba.
Jiki asanyaye Chief ya mike ya zauna kan sofa din, Kafin ya maida hankalinsa kan daddyn nasa yana jiran jin me zaice ma shi..
Da ipad din hannunsa ya nuna cup of coffee yace"ka ɗauka kasha naka ne"
yana cikin shan coffeen Muryar daddynsa ta katse shi"Owais, dagaske ne zakuje kai Farmaki.."
Ƙiris Ya rage ya saki cup din hannun shi, A matukar ruɗe yake kallon daddynsa, kwata kwata bai dago ya kalle shi ba, Still Hankalin shi na akan Ipad dinsa.
"Kayi shiru baka ce komai ba, Inaso naji daga bakin ka ne"!
Dakyar Ya iya furta Eh daddy, dagaske ne, amma tayaya akai ka sani? Bayan asirrince muka shirya komai ban sanar da kowa nawa ba..."
Sai da yai wannan maganar mai girma sharafudden ya dago da idanunsa ya dubi cikin idanun shi.
"hmm owais kenan, kada ka manta, tun kafin ka mallaki hankalinka nake sanya jami'ai su bibiyi rayuwarka, sai yanzu da ka girma ka ke tunanin zan daina sanya ido akanka"?
ya tambaya yana kallon shi, lamarin ya daurewa chief kai kuma hankalinsa ya dan tashi.
"Owais, meye hadinka da zuwa kai farmaki? dama shugaba Yana zuwa Yaƙi ne?
"Daddy, Ni na za6i da naje..." bai kare maganarba, ya katse mashi hanzarin shi
"Owais, bazan ta6a yin gangancin da zan rasaka ba, ka riga da kasan irin kaunar da nake maka, kai kadaine ɗa namiji tilo da nake da shi, taya zan zuba maka ido ka dinga yi min wasa da ranka"? A fadace ya fada.
Hankalin chief ba karamin tashi yayi ba, ganin dad dinsa na nema Ya jaza mashi matsala.
"Daddy, pls wanene Ya fada maka zancen zuwa kai farmakin nan! Inaso na sani.." fuskarshi ayamutse ya faɗa
Girgiza kai Sharafudeen yayi"ba bu bukatar ka sani, kuma kada kayi tsammanin cikin jami'an ku ne, a'a ko ɗaya, dan leken asiri nane ya fada min"
"why pls? Daddy kasan banaso!, a matsayina na jami'in sirri bai kamata ka sanya dan leken asiri yadinga bibiyar rayuwana ba, hakan ya sa6ama dokar aikina"!
Ya fada rai abace
"Naji Ubana Obinna, zan dakatar da ɗan leken asirin, amma ka sani, babu kai babu zuwa Kai farmaki, bada yawuna ba wlh..." saukowa yayi daga kan kujerar dayake azaune, Ya zukuna gaban daddyn nasa tare da ruƙe hannayensa acikin nashi.
"Daddy, dan Allah kada ka sage min kwarin gwiwar da nake da shi, daddy kamanta ne? Kaine fa kake karfafamin gwiwa akan aikina, tun da muke zuwa kai farmaki baka ta6a dakatar dani ba sai yanzu daddy"? Ya fada fuskar shi amarairaice.
"pls Kada ka hanani Yin aikin da zan taimaki rayuwar bayin Allah, in kuma kawar da mugun iri a cikin al'umma, daddy, Kasan ni mai biyayya ne agareka, ban ta6a maka gardama ba, amma dan Allah daddy, ka barni inje, na kwallafa rai akan son zuwa, Inaso naje daddy...."
Tamkar zai saka mashi kuka, Ya jima baiga damuwar dayagani yanzu akan fuskar shalelensa ba, idanunshi sun kada jawur kamar jan gauta.
Saidai bayajin zai yarje masa yaje don shi bai shirya rasa shi ba.
"Owais, Ni bawai zan hanaku yin aikin ku ba, kawai hankalina Ya tashi da jin inda zaku je kai farmakin, saboda ɗan leƙen asirin nawa ya fadamin inda zakuje gurin matsafa ne masu hadarin gaske, inajin tsoron Su cutarmin dakai, gaskiya ban amince kaje ba, saboda kai yanzu director General ne, babu zuwa Yaƙi a aikinka, ba dole saida kai zasuyi nasara ba, kawai ka tura Yaranka suje mana"_
ya faɗa babu wasa akan fuskar shi, harya buɗe baki zai kara furta kalma ya dakatar da shi ta hanyar ɗaga mashi hannu"na gama magana Owais," ya faɗa tare Ya duba agogon hannunsa
"I have a meeting, I don't want you to go anywhere, you'll spend the whole day here" yana fadan hakan yasa kai ya fuce.
Dafe kanshi Yayi da tafukan hannayen shi, kamar zai fasa ihu saboda tashin hankalin da zuciyarshi ta shiga! Mamakinsa taya akai daddynsa yasan da zancen farmakin da zasu ƙaddamar? Wai har yasan gurin matsafa zasuje? Bayan haka meyasa tunda Yake zuwa Yaki bai ta6a dakatar da shi ba sai wannan karan❓
Sun riga da sun gama tsara komai, tafiya kadai ta rage masu amma daddynsa na neman Ya kwafsa mashi.
Wayarsa dake acikin Trouser pocket dinsa sai ringing takeyi, yasan bai wuci na hannun damansa ne ke nemansa ba.
Kifa kan shi yayi, jikin Sofa wani irin sarawan Ciwon kai Yake Ji, Ji yayi bazai Iya bari damar nan ta wuce shi ba, Shi kadai ne zai bada Umarni su tafi kai farmakin nan In har basu ji daga gare shi ba, gaba daya plan dinsu zai lalace.
Yana tsaka da tunanin nan kwatsam lokaci ɗaya ya fara Jin wani irin matsanancin bacci na neman yaci karfin shi lokaci daya ya zare idanun shi cike da tashin hankali Ya ke duban Cup din da daddynsa Ya bashi Yasha cofee yunkurawa yayi da wata irin kasala Ya nufi kofar dakin Yaja handle din Yana kokarin bude ta sai dai ga mamakin shi Ya datse kofar ta waje, Kuma dole saida fingerprint ɗin daddynsa ko na mommynsa za'a iya unlocking ɗinta, tashin hankalin da ba asaka masa Rana.
Gwiwowin ƙafafunsa ne suka sage, wata irin juwa ta ɗebe shi gaba ɗaya Ya kife kan floor kamar wanda yasha giya takai mashi karo bai ta6a zaton daddynsa zaiyi masa haka ba, dama saida boyayyan mutumin nan yace mashi kada ya yarda da kowa saboda kowa zai Iya cutar da shi a halin Yanzu da alamun kamshin gaskiya amaganar shi.
Still bai daina kokarin mikewa ba, dakyar Ya zaro wayar shi daga trouser pocket dinsa, yanata faman kiciniyar bude idanunshi dake lumshewa, dakyar Ya lalubo layin Mommynsa Ya danna mata Call, cikin sa'a tayi picking.
"My baby boy, how are you"?
Kokari yake ya buɗe labbansa sai dai yayi masa nauyi, kamar harshen shi ya karye, dakyar ya iya furta"mom... myyy ... in.. Ina a resting home din dad... he locked me in his master suite...I can't open the door...I need your help...come quickly, Mommy."
yana faɗan hakan wayar ta sulbe daga hannun shi.
Yana jiyo muryarta da karfi take ambaton"hello Hello, Owais! Kana ji na? Me ka yi masa ne?
Kalmar karshe da kunnansa su ka ji ta furta kafin kiran Ya katse, bai ƙara sanin inda kan shi Ya ke ba..
(TASHIN HANKALIN DA BA'A SAKA MASHI RANA🤔❓)
__________________________________✍️
Yayin Da Chief Owais ke a garƙame Cikin ɗakin Mai girma sharafuddeen, acan Gidansa kuwa Ƙarfe biyar na maraice dai dai ba ƙari, Dankara dankaran Motocin suka fara shararowa Cikin gidan, kamar a filin daga, Wasu irin Dakarun Sojojine Majiya karfi, masu kirar samudawa, sunyi tsayuwar jarumtaka kan motocin, gaba dayansu Army Combat Uniform ne a jikin su, baka iya ganin fatar su saboda ta ko'ina sun rufe jikin su with protective gear, kowan nansu yana sanye da helmet(hular kwano) Bayan motocin sun yi Parking, cikin zafin nama sojojin dake akan motocin suka diddiro tare da bubbbuɗe Cardoors din, U.s Armies ne su ka fito kowan nan su yana a sanye da kayan yaƙi sun shirya tsaf.
Ta glass door din Falo, Big guy ya hango su, shima harya kammala shirinsa cikin Isod Combat Uniform.
Wata irin damuwace ta bayyana akan fuskarshi Ganin har su commender james sun karaso amma chief bai dawo daga Villa ba, Ya riga daya san halin turawa basu wasa da lokaci, kuma basa sa6a alƙawari, In har suka ji Chief bai nan Bazasu ji dadi ba, zasu ga kamar ba'a ɗauki abun da mahimmanci ba ne.
Kusan sau Hamsin Yana danna mashi Call baiyi picking ba, Hankalin shi ba karamin tashi yayi ba, cike da takaici ya furta"Ya salam,! Chief Ina ka shiga! Pls kada ka 6ata mana shirin mu, dan Allah ka ɗaga kirana, bana so mutanan nan suga gazawar mu"
ya faɗa idanun shi akan screen ɗin wayar shi dake ruƙe a hannun shi..
Layin Boss Ya danna ma Kira, bayan yayi picking Ya ce"boss, akwai matsala fa" on the other hand Taj Ya furta"meya faru Omar"?
"Chief Har yanzu bai dawo ba, Ina ta kira wayarsa baya picking, gashi har tawagar su commender sun karaso..."
Hankali atashe Boss Yace"Ya salam, Yanzu ya zamuyi Omar? Ko dai zaka jaraba kiran daddynsa"
"Har layin daddyn nasa na kira baya shiga"
"To ka jaraba kiran layin mommynsa watakil aci sa'a ta ɗaga"
"Okay, zan jaraba, but pls kuma Ya kamata ku fito Yanzu" ya amsa mashi da toh kafin Ya katse kiran
Yana kokarin kiran Gimbiya malikat Sai ga sako Ya shigo wayar shi da bakuwar number..
Buɗe sakon yayi tare da karantawa
_Omar, I won't be able to come; inform every team of fighters. I have canceled the attack_
(Omar, bazan samu damar zuwa ba, Ka sanar da kowace tawaga ta mayaƙan, Na soke kai farmakin)
Tsabar bacin rai, tuni idanun big guy sun kaɗa jajur, kamar zai fashe da kuka baima san sa'adda Ya jefar da wayar Ta fada kan sofa.
jiri Yaji Yana niyar dibar shi adaddafe ya zauna kan sofa, adai dai Lokacin, yaji Motsin Buɗe kofar main Falon, zumbur Ya miƙe Yai saurin daidaita nutsuwar shi don kada su gane wani abu...
ɗaya bayan ɗaya suka soma shugowa falon, dakyar Ya kakaro murmushi kan fuskarshi ya nufe su da sauri suka sara ma junansu, a mutunce suka gaisa da juna..
Cikin harshen turanci Commender James yace"Omar me kuke Jira ne? Naga banga sauran ba, Ina Chief Yake"?
Fuskarshi da matsananciyar damuwa kamar mara gaskiya sam Ya kasa bude baki Ya basu amsa saboda nauyin maganar da zai furta masu
gaba daya sun fahimci kamar akwai wani abu dake damun shi
"Omar kayi shiru bakace komai ba, Ina Chief dinne"? Yawu mai ɗaci Ya haɗiya, adabarbarce Ya furta"Am..sir.. dama dazu ne daddynsa Ya kira awaya yana son ganin shi, Har yanzu dai bai dawo ba, shi muke jira"
Yamutsa fuska Commender James Yayi da alama ranshi Ya 6aci bai dai ce komai ba.
"Pls mu shuga daga ciki" ya fada tare da nuna masu Cikin falon..
Girgiza kai Commender Yayi"ba zama ya kawo mu ba, bamu da lokacin da zamu 6ata, ka kira Chief kace mashi Yazo Mu tafi"
"Na kira layin shi baya shiga"
"Me hakan ke nufi"? Ya tambaya yana kallon Big guy.
Kafin Ya furta Kalma sai ga Boss Ya na saukowa Down daga second floor, jikinshi sanye da kakin yakinsa karasowa yayi tare da sarah masu commender suma suka sara mashi.
kallon big guy yayi
"Har yanzu baka same shi ba"?
Jinjina mashi kai yai alamar eh..
Cike da damuwa Taj Ya dubi su commender"sir, pls ku ƙara hakuri, watakil wani Uzirinne Ya ruke shi, idan ba damuwa mu shiga daga ciki"
"Taj kuyi kokari ku nemo Chief, idan ba haka ba zamu rasa damar da muke da ita"
ya fada tare da kallon yan tawagarsa"mu je" bin bayan shi su ka yi a kan sofas suka zauna.
ya rage saura Taj da big guy atsaye suna fuskantan juna sam sun kasa magana duk basu ji dadi ba.
"chief bai kyauta mana ba, Ni dama saida raina ya bani da wuya mukai farmakin nan lafiya batare da an samu matsala ba" rai aɗan bace Yai maganar.
Kafin Taj Ya furta kalma, wayar Big guy Ta fara ruri, da sauri Ya duba screen din tamkar zai fashe da kuka Ya dubi Taj"mun shiga Uku, General ne ke kira, may be Suma sun shirya tawagar su"
"Omar, ka kwantar da hankalinka, In sha Allah, komai zaifi daidai, Yanzu ka ɗaga kaji me zaice maka"!
Picking call din yayi tare da kara wayar a kunnanshi bayan sun gaisa
General Noah Yace"Ya ake ciki ne? Na kira layin chief baiyi picking ba, Already mun shirya tawagar Sojojin mu, Umarnin shi kadai suke jira"
yamutsa fuska big guy yayi, da ido Taj yake karfafa mashi gwiwa dakyar Ya furta"Sir, nan badajimawa ba, zakuji daga gare mu" daga haka su ka yi sallama.
Dagowa yayi tare da kallon Taj" hmm kasan meya faru"? Girgiza kai Taj yayi
"Chief ya turo min message, na boye ne saboda inajin nauyin in furta, amma chief Ya soke kai farmakin ayau"
wani irin faduwa gaban Taj yaji arude Ya firta"tayaya hakan zai yiwu Omar? Anya kuwa ka karanta sakon da kyau"
Mika mashi wayar yayi don ya karanta da kanshi bayan ya kammala karantawa Ya kalli Omar"ka yarda Chief ne ya rubuta sakon nan? Girgiza kai Omar yayi"ina kokwanto wlh, saboda Chief kaifi ɗayane baya sa6a alkawari in ba wani kakkauran dalilinne zai hana shi zuwa ba, bayan haka meyasa bai turo min sakon da layin shi ba"? Boss yace"uhum ni nasani ay, Allah kadai yasan meke faruwa, gaskiya ƙwara muje villa din.."
Da sauri Omar Yaje ya sanar da su commender cewa zasuje Villa donsu ga meya tsayar da Chief, commender Yace suyi kokari kada a bata lokaci.
gudu gudu sauri sauri suka fito daga Falon da karfi Big guy Ya kwaɗawa Jami'an dake akusa da parking space Kira Yace su buɗe masu mota, agaggauce jami'an suka bude, Taj ne ya fara shiga big guy na kokarin shiga, ba zato ba tsammani, saiga Motar Chief ta kunno kai cikin gidan da gudun gaske kamar zata tashi sama.
wata irin nauyayyar ajiyar zuciya Big guy ya sauke.
"Boss Ga chief din nan" da sauri boss Ya fito daga motar suka nufi motar Chief, motar Na tsayawa Big guy ya buɗe mashi car door din, kaitsaye idanunsu suka shiga cikin na juna, Ya jigata ba kadan ba.
Huggin dinsa Yayi kamar zasu koma mutun ɗaya a kalla big guy ya sauke ajiyar zuciya yafi sau uku..
"Ka tada min hankali Owais, meyasa ka dade? Ina ta kiran layinka baya shiga" ya fada tare da dago da kan shi har saida yadanji gabanshi ya fadi ganin yanayin fuskar Chief sam babu walwala kamar wanda yayi jinya.
Hatta boss Yasha jinin jikinshi da ganin yanayin nasa.
"Wani abu ya faru ne? arude Ya fada Yana kallon shi
Baya Jin zai iya sanar dasu abun da daddynsa yayi mashi.
dakyar ya iya shanye damuwarshi Ya kakaro walwala kan fuskarshi kafin Yace"bakomai, lafiyana lou, bacci ne ya dauke ni acan, kuma na sanya wayar a silent batare da sanina ba" badan sun yarda da maganar ba suka amince.
boss Yace"Sir mu shiga daga Ciki, tawagar su commender sun karaso, Suna a falo suna jiranka, bayan haka tawagar sojojin nigeria suma sun shirya, gaba dayanmu Umarninka muke jira..." numfasawa yayi kafin ya furta"okay Danish da salsabeel fa? Suma sun shirya"?
"Eh, duk sun shirya" ajiyar zuciya ya sauke.
Bayan sun shiga Gidan, atsaitsaye Ya gaisa da su Commender kafin Ya nufi bedroom dinsa, don Ya shirya...
(Tayaya akai Chief Ya ku6uta daga tarkon da Mahaifinsa Ya ɗana masa"?)
Bayan da ya kira Mommynsa awaya, ba'a fi minti biyar ba, sai ga hamshakiyar motarsu ta shigo a parking space security din dake driving dinsu yayi parking, A hanzarce Gimbiya Malikat ta fito daga mazaunin baya na motar, Jikinta sanye da tsadaddiyar Lafaya lace, hadadden shade din data sanyawa idanunta ba karamin kawatasu yayi ba, takalman kafarta kadai abun kallo ne, tana tafiya p.a ɗinta na take mata baya, wata katuwar mace karkarfa, Jikinta sanye da Suit, tasha kitson zane akanta.
Cikin takun qasaita take tafiya, yanayin fuskarta sam babu walwala, saboda Hankalin ta ya tashi da jin abunda Owais Ya fada mata.
Kaitsaye suka Nufi master suite din Mai girma sharafudden.
Abakin kofar Room ɗin suka dakata da yin tafiya, Gently ta ɗaura Thumb ɗinta akan Biometric scanner ɗin dake jikin handle din kofar, nan take kofar tayi Unclocking ɗin kanta...
Juyawa tayi tare da kallon P.a ɗinta, abunka ga masu Izza a jini, da ido tayi mata alamar ta tsaya anan, with respect ta amsa mata da okay ma'am..
shigarta keda wuya kofar tayi locking kanta..
Ɗakin tabi da kallo, kwatsam idanunta suka hango mata shi kwance kan floor kamar matacce kwata kwata baya motsi.
Numfashin shi ne kadai ke fita.. Hankalinta yayi mugun tashi, a sukwane ta zare shade din dake akan fuskarta..cikin sauri ta nufe shi ta zukunna agabanshi ta sanya hannayenta biyu ta dago da kanshi ta kwantar saman laps ɗinta.
shasshafa fuskarshi tayi muryarta na rawa ta furta"My son! Lafiya ka kwanta kan floor kamar wani mara gata? Meke damunka ne? Owais kana Ji na kuwa?
tariyo maganar da sukayi awaya tayi lokaci ɗaya zuciyarta, ta raya mata ba baccin lafiya yakeyi ba, saboda yanayinsa yafi kama da na wanda yasha kwayar maye.
a hankali ta kwantar da kan nashi kan floor, ta mike tare da kai idonta kan coffee table din dake a seating area.
Cups ta gani biyu akai, matsawa tayi gaban table din, ta dudduba cups ɗin, ita dai bata ga komai ba har ta juya zata koma wurinshi kwatsam idonta ya hango mata packet na pills daga gefen table din kiris ya rage ya shige karkashin sa.
Yatsun hannunta na kerma ta dauki packet din ta soma karanta rubutun dake a jikin shi zaro ido tayi saboda ta gane sleeping pills ne.
Hankalinta ya tashi ba kadan ba! tamkar zata fashe da kuka ta furta"why Owais! Why! Me ya hadaka da maganin bacci mai hadarin gaske.." juyawa tayi tare da kallon shi bawan Allah baimasan inda kanshi yake ba..
fitowa tayi daga dakin hannunta ruke da fakitin, P.a na ganinta tay saurin russina mata..
"Duba min maganin nan" ta fada tare da mika mata roban
"Inaso akawo min antidote dinsa Yanzun nan.."
Jinjina mata kai p.a tay, tare da juyowa ta bar gurin, tana atsaye tana jiran ta, badajimawa ba saigata ta dawo hannunta ruke da Injection ta miƙa mata.
Tasa hannu ta kar6a, tare da juyowa ta koma ɗakin, kasancewar tana da ilmin abun bata sha wahala ba, bayan ta kamma yi mashi allurar.
Zama tayi gefen shi, tana kallon shi, zuciyarta cike fal da tunin meya faru tsakanin shi da mahaifin shi..
Tsawon mintuna ashirin, Ya fara zubda gumi a jikin shi, kamar an yayyafa mashi ruwa, yatsun hannunsa dana kafafunsa suka fara kerma kamar wanda sanyi ya kama, ajiyar zuciya ta fara saki ganin ya fara dawowa hayyacin shi...a hankali ya bude idanunshi wadanda suka kaɗa jawur ya kurawa ceilling din dakin ido kamar ya manta da abunda ya faru.
"Owais,"
jin muryar Mommynasa yasa shi saurin kai idonshi gare ta..wata irin nannauyar ajiyar zuciya ya sauke, da kyar ya tattara karfin jikinshi Ya samu ya mike tare da matsawa kusa da ita, cikin sauri ta rungumoshi kan kirjinta, hannunta daya acikin sumar kan shi..
"My son, are you Okay? ta fada cikin kulawa.
Jinjina mata kai yai alamar eh, bata kara tanka mashi ba, yayi shiru yana faman jan numfashi har saida Ya ƙarasa wartsakewa Ya dawo hayyacin shi kafin ta tambayeshi dangane da kwayar maganin baccin daya sha!
"Kai nake sauraro Owais, ka daga min hankalina, kuma meya hadaka da daddynka, dayaja harya kulle ka adakin sa"?
ta fada tana kallon fuskarshi, still bai dago daga jikinta ba.
Cikin disasshiyar murya ya furta"mommy, zanyi maki bayani, amma ba yanzu ba, pls ki kwantar da hankalinki, ba abunda ya faru tsakanina da shi..."
fuskarta ayamutse tace"meyasa bazaka fadamin yanzu ba"?
A gajiye ya girgiza kanshi"mommy, tafiya zanyi, abokan aikina suna jira na, I don't want to lose the opportunity I have, In har banje ba, all our plan will be ruined"
gefen fuskarshi ta shafa da hannunta"shikenan, Na fahimce ka, bazan matsa maka ba, nasan yanayin aikinku, amma pls, ka kula mun da kanka Owais..." lumshe idanunshi yayi tare da jinjina mata kai, ya ruko hannayenta biyu acikin nashi"mommy, Ina barar addu'arki, nasan kinayi min, amma kwanakin nan ina bukatar ƙari akan wadda kike yi min, bama ni kadai ba, hada abokan aikina .." cikin sanyin murya tace"in sha Allah Owais, zanyi maka addu'a, ay bana mantawa dakai, amma kayi ma daddynka magana akan yayi maka addu'a ?
girgiza kai yayi"a'a mommy, nafi bukatar taki, in har kikayi min kamar yayi minne, and pls, bana so daddy yasan kin bude min dakin nan, kiyi min hanyar da zan fita daga gidan nan batare da wani ya ganni ba..."
ta ɗan rude da jin abunda Yace amma sai bata kawo komai aranta ba, saboda ta yarda da ɗan nata da kanta tayi mashi hanyar barin gidan batare da security officers din da mahaifinsa yasa tsaron gidan sun tuhume su ba.
Kunji yadda akai Chief Ya ku6uta daga tarkon daddynsa ✍️
Fitowar Chief daga Part dinsa tayi daidai da fitowar Danish Da Salsabeel.
Gaba ɗaya Hankulan U.s Army din Ya dawo kan shi, yayi matuƙar jan hankalinsu yadda kasan Diamond a sararin samaniya saboda kyan da yayi Cikin shigar Isod Combat Uniform, Ya rufe fuskar shi da Mask, hadaddiyar sumar kan shi ya daure ta da head ties jelar gashin ta sauka agadon bayansa.
Ƙafafuwansa suna asanye da wasu hadaddun Combat boots ko a kakin yakin bakomai ya sanya ba babu protective gear saboda baya bukatar su.
har ya sauko down basu daina bin shi da kallo ba, tun da Allah ya halicce su basu ta6a ganin Matashin sarauyin da kakin Yaki su kayi ma kyau irin Danish ba ya fita daban acikin su, ya fito a suffar jarumtakarsa, sadaukin namiji mai ji da karfin sa..
Kallo ɗaya big guy yai masa ya kau da kai gefe, taj kuwa sai da yadan sha jinin jikin shi aranshi ya ayyana ba mace ba ko namiji ya kallesa sai ya burge shi, ina ma amfanin kyau irin nashi ba ilmi wannan ay masifa ne bakaramar 6arna zaiyi ba, a ganinsa kyawun shi ne ke ruɗar Unaisah da kuma tausayinsa shiyasa ta ke nema ta zauce akan son shi.
A hankalin Salsabeel Ya ruko hannun Danish acikin nashi.
Bayan sun karasa saukowa down U.s Armies suka fara zuzuta kyawun da kakin su ka yi mashi hatta chief sai da ya yaba, gaba daya suka dunguma zuwa harabar ajiye motocin gidan.
abun daya 6ata ma big guy rai Yana niyar ya shiga Motar da chief zai hau Chief ya ja hannun Danish suka shiga motar, Yaji zafin hakan sai dai Ya hakura Ya shiga Motarsu Taj.
bayan us armies din sun shisshiga motocinsu, da gudun gaske suka fuce daga Estate din saboda Lokaci.
A cikin Mota Chief Ya kira Sheikha Mujeeda, Aransa yana Allah Allah ta ɗaga Yasan ba ta daga kira in ba an fara tura mata sakon neman izni ba amma cikin ikon Allah tayi picking yadan yi mamaki amma da ya tuna maganar da sukai akan Danish sai ya gane dalilin dayasa ta daga kiransa bayan sun gaisa yace mata ɗanta na barar addu'arta zasu yi wani aiki mai hadarin gaske.
yanayin muryarta da damuwa tace In sha Allah zanyi mashi addu'a, In yana kusa ka bashi wayar"
mika ma danish wayar yayi baisan wanene ba Ya kar6a ya kara a kunne yayi shiru baice komai ba har saida gimbiya Mujeedat ta furta"My Son kana lafiya"? arude Ya kalli Chief tare da tambayar who is She? Murmushi Chief yai tare da cewa"matar daddy minister" nan take ya tariyo lokacin farko daya fara ganinta, bazai ta6a manta yadda ta cire mask din fuskarshi ba ta zuba mashi kyawawan idanunta.
Cikin sanyin murya ya gaishe da ita with respect, ta amsa mashi kafin tace"chief ya fada min zakuyi wani aiki mai hadarin gaske, In sha Allah zan tayaku addu'a..." yace mata ya gode, har tana zolayar shi da cewa tasan da daddy minister ne suke waya sai yafi sakin jiki saboda sun saba amma ita kamar baison yi mata magana..
Ko gama wayar basuyi ba ya mika ma Chief saboda wani yanayi dayake ji atare da shi, Zuciyarshi Ta kasa samun sukuni tun kafin su bar garin Ya fara jin matsananciyar kewar Unaisah.
Tafiya yankin azaba sun ɗauki tsawon awanni akan hanya, da misalin sha biyun dare, suka qaraso cikin Dajin da suka haɗa katafaren sansaninsu, dajin yana a kusa da evil forest, katafaren Military base ne mai girman gaske ga wasu Irin Dakarun Sojaji masu ƙira irin ta zakuna kowan nan su yana asanye da army combat uniform dinsa, Cikin takun majiya karfi suke sintiri a cikin sansanin tamkar da rana saboda hasken electricity din dake a ko'ina na sansanin.
Bayan sun fito daga cikin motocin su, duk inda suka gifta cikin girmamawa sojojin ke sara masu tare da yi masu maraba da zuwa, a haka har suka shiga inda masaukinsu yake domin su dan hutu na wucen gadi.
THE DAY👹👺
Asubahin fari suka farka daga bacci, musulman dake acikin sukayi sallah awani ke6a66en wuri dake a cikin sansanin, bayan sun yi kalacin su, gaba ɗaya sojojin suka hallara a filin dambe, suka fara motsa jikin su har dambe sai da su ka yi a tsakaninsu wanda ya kasance kamar gasa ce su ke yi, Danish ya zama zakaran gwajin dafi a wurin an kasa samun wanda zai kayar dashi dayawa sun kara samun kwarin gwuiwa da ganin irin kwazon shi, bayan sun gama damben suka ɗan huta har wuraren ƙarfe shida na marece kafin daga bisani suka fara shirin shiga evil forest.
A helipad din dake a wani sashe na cikin Sansanin Wasu dankara dankaran Jiragen yaƙi ne a jere masu saukar ungulu da aka tanadar masu, ko da ido ka kalle su sai gabanka ya fadi, already fighter Pilots ɗin da zasu Yi jigilar daukarsu tuni sun shige cikin helicopters din.
Bayan komai ya daidaita, har dakarun sojojin sun gama shiga cikin jiragen, Kafin wani Lokaci jiragen suka lula sama, yayin da trucks ɗin makamai dake tafiya akasa suke bin su.
*FATAN NASARA*
____________________________________✍️
*🔥GIDAN KURKUKUN ƘADDARA🔥☠️*
Farkawarta kenan daga bacci, A hankali ta buɗe idanunta tare da kallon rufin gadon, Har na tsawon mintuna, har rama ta qara saboda azabar rashin lafiyar da tayi.
ta wutsiyarta idanunta ta hangi mutun kwance gefenta, da sauri ta wurga idanunta akanta, ajiyar zuciya ta sauke ganin tsohuwa khala, da alama tayi nisa acikin baccin ta, ta ɗan yi mamaki don tunda ta tsinci kanta a dakin khala bata ta6a kwana kan gadon ba, a saman kujera take yin baccin ta a zaune kamar dogari.
Kasa kauda ido tayi daga kallonta, wani irin kaunar dattijuwar take ji acikin zuciyarta, batasan sa'adda ta matsa kusa da ita ba takai hannu ta shafa gefen fuskarta mai tarin tamoji tamoji, ta manna mata sumbata kan goshin ta ta danyi murmushi har chin dimple dinta Ya motsa.
"Bayan ɗan uwana gabriella, bani da abu mafi soyuwa daya wuce ke, Inasonki Khalana.." kamar daga sama ta tsinkayi muryar Khala acikin kunnanta"Nima Ina sonki Jikata" zare brown eyes dinta tayi fuskarta dauke da annurin farin ciki ta furta"Khala, Idonki biyu"? Ta fada akagare da son jin amsarta..
A hankali Khala ta buɗe idanunta akan fuskar Gabriellah.
"Ya jikin naki Jikata"? still da murmushi kan fuskarta tace"Naji sauki, yanzu babu inda keyi mani ciwo"
Tattausan murmushi khala ta sakar mata"haka nake sonji, Na lura kamar Kina farin ciki Yau, saboda tunda nake dake banta6a ganin murmushin ki ba..." yar dariya Gabriel tayi
"khala, kece silar farin cikina, da na yanke kauna da rayuwar duniyar nan, amma silar haduwana dake da kuma alkawarin da kika daukarmin na haɗani da ɗan uwana Yasa naji Ina son na rayu, Ina son na zama jajirtacciya jaruma kamar ke, kuma ina son na ɗauki fansar abunda akayi mana" tunda tafara magana khala ke binta da kallo, arayuwarta tana Son ya'ya musamman idan tagan su cikin nishadi da walwala shiyasa aduk lokacin data ga ana azabtar da rayuwar su take jin kamar ta hadiyi zuciya ta mutu saboda baƙin cikin da takaici.
"Amma khalana, Idan muka yi nasarar ku6uta daga kurkukun nan, atare zamu rayu ko"? Murmushi khala tayi"Idan na fita bansan inda zanje ba, bani da kowa, ko kina da inda zaki ajiye ni"?
Shiru gabriella tayi tare da ta6e bakinta kamar zatay shagwa6a tace"nima bani da kowa, amma dani da ɗan uwana Gabriel, zamuyi aiki tukuru, donmu gina gidan da zamu zauna, nayi maki alkawarin zamu baki kyakkyawar kulawai..."
cike da nishadi khala ke sauraronta..
Kwatsam suna tsaka da yin fira, ba zato ba tsammani, kunnuwansu suka jiyo masu wani irin sautin Bugun ganguna dumdum kamar dodon kunnan su zai fashe, tsabar sautin bugun gangar Ginin Har girgiza yakeyi, hatta gadon da suke kwance akai ya kama girgiza.
gaba daya Gabriella tabi ta ruɗe, baiwar Allah dama ba lafiyar kwalwa gare ta ba, da sauri ta toshe kunnuwanta da tafukan hannayenta.
Tsohuwa Khala kuwa tashin Hankali da farga Ya hana ta motsa sai faman zare idanunta takeyi.
Lokaci ɗaya suka daina Jin bugun gangar, sai kuma suka fara jiyo ɗaddaɗar Busar sarewa tana tashi
lokaci ɗaya yanayin fuskar Khala Ya sauya, aruɗe ta furta"ELDERS"
Cikin ruɗu Gabriellah ta kalle ta cike da rashin fahimtar me take nufi..
Damƙo hannunta tayi acikin nata"akwai abunda na manta ban fada maki ba, daren yau dare ne mai hadarin gaske, bugun gangar da kika ji alama ce dake nuna ƙarasowar ELDERS.
"abunda nakeso dake ki 6oye karkashin gadon nan, kada ki kuskura ko tari kiyi idan ba haka ba zaki jefa rayuwar ki cikin haɗari ne.."
Hankalin Gabriella ba karamin tayi yayi ba, muryarta na rawa ta furta"Dan uwana fa? kada su kashe min shi..."
katse ta khala tayi"babu abunda zai same shi, kiyi abunda nace maki kawai"
saukowa sukayi daga kan gadon da sauri Gabriella ta shige karkashin gadon, ba laifi Yana da faɗi da tsawo, kamar ƙaramin ɗaki, tayi mamakin ganin buhun huna kusan Biyar a karkashin gadon ga wasu akwatinan ƙarfe, jikinta na kerma amma saboda karanbani saida ta yi kokarin kwance buhun don ta ga menena aciki, Sai dai takasa saboda mugun ɗaurine akayi masu, tatta6a jikin buhun tayi sai taji kamar Makamai ne a cikin su...
Komawa tsohuwa khala tayi kan gadon ta kwanta tare da lumshe idanunta, zuciyarta cike fal da fargaban abun da zai biyo baya don tasan muddin Elder ya ƙaraso adakinta zai huce gajiyar shi.
bakomai yafi damunta ba face zuwan Garkuwa, Allah Allah take su karaso saboda batason Elders suyi nasarar Salwantar da rayuka a wannan daren, In har daren yau ya wuce Bata cimma burinta ba, bata jin zata Iya jure rayuwa adoron duniyar nan, saboda in har ta kuskura asirin ta Ya tonu na abunda take kullawa Allah kadai Yasan Mummunan hukuncin da zasuyi mata, donma saukinta daya Elder Yana Ji da ita.
Bata kare zancen zucinta ba, Kamar daga sama Taji dirar wani abu adakinta,
Sautin shu'umar dariyar shi ce ta karaɗe kunnuwanta, Tuni tasha jinin jikin ta.
"Da wata irin Murya irin ta tantiran ƴan'duniya Ya furta"Idan ma bacci kike, toh ki farka..." yunkurawa tayi ta miƙe zaune, tare da kai dubanta gare shi, Yana atsaye cikin wata rantsattsiyar alkebba launin Ja mai adon duwatsu irinta sarakuna..ya lullu6e kanshi da hular alkyabbar, rabin fuskarshi arufe yake da takuntumi, kafafunshi suna asanye da wasu hadaddun takalma na alfarma, yayin da hannunsa ke aruke da sanda ta zallar Zinari.
ba'a Iya ganin fatar jikin shi saboda ya lullu6e ko'ina hatta yatsun hannunsa safa ya sanya masu.
Gabriella dake labe ta kasa kunne tana sauraronsu, da ga inda take tana Iya hangen kafafuwan Elder..
"Taya zan Iya bacci batare dana sanyaka acikin idanuna ba, tun bayan daka tafi kabarni da kewarka, idanuna sunyi maraicin ganin ka, sanyin idaniyata, mijina uban ya'yana, sarki ɗaya tak da ke mulkar zuciyata..." cike da qasaita yake sakin dariya yayin da yake tinkarar gadonta cike da dattako yake taka matakalar gadon.
"Meyasa soyayyar mu bata tsufa ne? Aduk lokacin dana ganki sai inji kamar ana rura wutar sonki a cikin zuciyana, bazan Iya misalta kewarki da nayi ba.
yayin da yakeyin maganar, wani irin kallo khala take binsa da shi mai wuyar fassaruwar, ta tsane shi fiye da yadda ta tsani mutuwarta, shine silar komai 💔
gaba daya tayi zurfi a tunaninta sam ta manta da shi akusa daita, batai aune ba taji ya janyota jikin shi, wani ɗaci taji aranta, sai taji kamar ta hada jikinta da wuta saboda tsanar da tayi mashi..
Sumbatar kuncinta yayi, cikin wani irin salo ya fara sarrafa ta.
Gabriella dake la6e a karkashin gadon, gabanta sai faduwa yakeyi ganin yadda gadon ke girgiza kamar zai rubzo mata, gani take kamar mutumin dayazo ne ke cutar da Khala.
kasa jurewa tayi duk tabi ta rude jikinta sai kakarwa yakeyi bata san sa'adda ta saki ƙara ba, da sauri ta toshe bakinta da tafukan hannayenta.
Lokaci ɗaya Elder Ya raba jikin shi daga na Khala, ido cikin ido suke kallon juna..tun daga yanayinta ya fahimci akwai wani abu da take boye masa.
Kamar daga sama taji Ya furta"kamshin mutum nake ji adakin nan..." arazane ta ware idanunta akan fuskar shi, jinjina mata kai yayi
"Ke da wanene Kuke rayuwa adakin nan? Kuma Yana ina"? Ji tayi kamar ta fasa ihu saboda tashin hankali, batasan ya akai ya gane akwai mutun ba..
.
"Kinyi shiru baki bani amsa ba, Ko kin bani za6i In gano da kaina"?
Yawu mai daci ta hadiya muryarta na rawa tace"bakowa, Ni kadai ce, nayi mamaki da naji kace kaji kamshin mutun bayan ni kadai ce mutum da ke rayuwa a cikin dakin nan.."
"baki saba min karya ba, Amma yau kinyi min, kinsan na tsani makaryaci, saboda alamace dake nuna mutun zai Iya cin amanarka wata rana"
idanunta ne suka ciko tab da kwallo, cikin sanyin murya tace"ka yi hakuri, na gane kuskurena, kasan ba halina bane, dama yarince daga cikin prisoners, inason yarinyar ne shiyasa na taimake ta..."
tun kafin ta kare maganar Ya daka mata tsawa a faɗace Ya furta"meke damunkine? Kina cikin hayyacinki kuwa? Kin manta gargadin da nayi maki?
Kamar ƙaramar yarinya ya rufe ta da faɗa.
"Ki rasa wa zaki kawo cikin dakina sai ƙasƙantacciya Prisoner? Ɗakin Elder? kefa sirrina ce, sai da na fada maki banaso kowa ya rabeki in bani ba"
kokarin bashi hakuri tayi, ko kallo bata ishe shi ba, saukowa yayi daga kan gadon da kakkausar murya ya furta"Tana ina"! Jiki na rawa tsohuwa Khala ta sauko daga kan gadon.
"Pls kada ka rabani da ita, Inasonta, wallahi bada wata manufa na ajiyeta adakin nan ba.." magiya ta dinga yi mashi amma dayake zuciyar irin ta fir'auna ce ko kadan bai saurare ta ba.
Tsoro Ya hana Gabriella fitowa, kirjinta kamar ana luguden ta6are..
"Zaki fito da kafafuwanki, ko kuwa Ni kikeso In fito dake..." cikin karyayyar murya khala ta kira sunanta..
Jiki asanyaye ta fito daga karkashin gadon, wani dan iskan kallo Elder yabita da shi, farat ɗaya Ya gane ƴar wacece.
Dariyar shaƙiyanci Ya saka kafin Yace"wannan Ay yar gurin Jan wuya ce, sadaukarwar Jini ce, bazan Iya barmaki ita ba, dama wata ce daban, Ko ubanta Yaji kin dauke ta sai yazo ya kar6eta ya mayar da ita cikin prisoners, kinga kuwa babu amfanin boyeta agurin ki...."
Gabriel ta ruɗe da jin maganar shi, ta fashe da kuka, idanunta akan fuskar Khala dake kallon ta.
cikin shesshekar kuka tace"kada ki bari arabani dake, kashe ni zasuyi, bana so na koma gurin su, kada ki manta da alkawarin da kikayi min pls...."
Da kallon tuhuma Elder Ya dubi Khala"wani alkawari ne kikayi mata"
"Zan hada ta da ɗan uwanta" ta fada rai a6ace..
"Ku shigo ku dauke ta" suka ji ya fada, kafin wani Ya furta kalma sai ga Giants biyu karfafa sun fado cikin ɗakin, wani irin faduwar gaba Gabriella taji, jikinta na bari kamar mazari ta la6e bayan Khala, ta rurruke hannunta tanayi mata magiya kan kada ta bari su tafi da ita.
shiru khala tayi jikinta yayi sanyi lakwas, Zuciyarta ta karaya.
"Ku maida ta, Cikin Ƴan uwanta,"
Duk yadda Gabriella taso ta kubce masu abun yaci tura, tana ji tana gani suka nuna mata fin karfi akan idonta Giants suka fuce da Gabriella...
Jiki asanyaye ta koma kan kujera ta zauna, idanunta suka cicciko tab da kwalla...
Matsawa yayi kusa da ita tare da sunkuyar da kanshi gab da fuskarta"fushi kike dani"? Ya faɗa tare da ɗage mata gira..
*DAGA ALƘALAMIN BOSS BATURE🔥✍️*
*Ga me bukatar karanta littafin kurkukun kaddara, 500 ne za'a tura Via Opay, 8103884440 Hafsat Bature Muhammad, shaidar biya za'a tura ta whatsapp, 08169856268 ko 08103884440*