Kurkukun Ƙaddara Takun Ƙarshe page 55 Complete by Boss Bature


Health College

Kurkukun Ƙaddara Takun Ƙarshe page 55 Complete by Boss Bature

Takun Ƙarshe

Kowa ya shiga ciki wani irin burki yake ci sakamakon abun al'ajabin da idanunshi ya gani, a haka har suka haɗu su duka, Cak duk suka yi sun kasa yin wani ƙwaƙƙwaran motsi, da wani irin matsanancin mamaki da al'ajabi gami da ruɗanin tashin hankali suke duban junansu....ganin abunda basu ta6a zaton ga ni ba, ga kuma sautin da kunnuwansu suka jiyo masu. Wannan shi ake kira bazata!!!

Sun sha ruwan mamaki! Elder da ya gama ruɗewa ya ce, "Ni kaɗai nake ganin abun da idanuna ke nuna min? What the hell is happening? Who killed them? Where are our prisoners?" A tsawace ya ƙarashe maganar.

Jan kunne Ya ce, "Abun da ɗaure kai! Anya ba farmaki aka kawo mana ba??"

Jan wuya yana huci ya furta, "This can't be happening, it's not true. Ƙarya ne, I can't believe it! how is this possible?" 

"Zance Ya 6aci! Tabbas an kawo mana farmaki! Wasu sun shigo kurkukun nan, Kuma Ni na jiyo  ƙara wadda ba tantama ta fashewar Bomb ce." Cike da tabbaci Jan le6e ya yi maganar..



"Kai! Ina ba zata ta6a sa6uwa ba, Ta ya ma har wani zai iya ƙetare dajin Evil forest ya shigo kurkukunmu bayan tsaron da muka sanya? Wannan zancen bazai ta6a zama gaskiya ba!"


 Jan harshe ne ya furta cikin ruɗanin zuciya.



Gaba ɗaya sun ruɗe sosai ganin abun suke kamar a mafarki, bama su gasgata abunda idanunsu suka gani ba, da abun da kunnuwansu suka jiye masu ba.


"Ina! bazai yiwu ba, wannan ba gaskiya bane, Muje Mu duba..." A cewar Jan Ido.


Suna ƙoƙarin Juyawa katsam suka yi arba da Dakarun sojojin da ke shigowa cikin hall ɗin runduna guda suka yi masu ƙawanya, Hannuwan su ruƙe da muggan makaman da Khala ta rarraba masu.


Wlh an shammace su, sun girgiza matuƙa, Ko a mafarki Elders basu ta6a tsammanin wannan ranar zata zo ba, Al'ajabi da rudani Ya hana su Iya furta kalma, sai jinjina kai sukeyi kamar wasu ƙadangaru.


Mamakinsu tayaya akai har aka yi nasarar kawo masu farmakin bazata a gidan Kurkukunsu! Abunda ba'a ta6a gigin yi masu ba, Lallai yau alkadarin su Ya Karye, gaba ɗaya sun ruɗe da lamarin.


Ɗaya bayan ɗaya suke kallon Dakarun Sojojin, Hankalinsu fa Ya ɗugunzuma ainin, amma saboda dakakkiyar zuciya da ƙarfin hali irin na Elders kawai sai suka fashe da wata irin mahaukaciyar dariya mai razanarwa, kai daga gani sun san me suka taka..


"Kun aikata babban kuskure!! Da har kuka shigo gonar mu! Wani tsautsayinne Yasa kuka kawo mana farmaki huh?" Jan Harshe ne ya faɗa yana huci.


Jan Le6e ya amshe, "Rabon ajaline Ya kawo ku..."


Bai ƙare maganar ba, dakarun sojojin suka dare tare da buɗe hanya, Ɗaya bayan ɗaya suka fara shigowa, ba su iya tantance fuskokinsu ba saboda masks da suka saka.


Kallon kallon suka fara jefawa juna tsakanin su da Elders, tsabar yadda zuciyar Chief Owais ke bugawa kamar zata fasa ƙirjinshi saboda zullumin wanda zai gani a cikin danginsa tun kafinma ya ga fuskokinsu, haka shima Big guy hankalinsa ba a kwance yake ba.


"Kune na farko da kuka fara kawo mana farmaki, amman  hakan ba yana nufin kun ci galaba akanmu bane, ba zamu ta6a ƙyale ku ba, sai kun yi danasanin kuskuren da kuka tabka!!!"


 Da kakkausar Murya Jan Ido ya yi maganar.


 Tun da suka fara magana basu tanka masu ba, wani abu da suka lura da shi, Wasu daga cikin Elders ɗin sun ƙi yin magana, wannan yasa su zargin sanannu ne shiyasa suka ƙi magana don kada aji muryoyin su..


Big guy ne ya yi ƙarfin halin furta, "ELDERS, nayi farin Cikin ganinku, ashe dama ana iya ganin ku cikin sauƙi haka?" Ransu Ya 6aci da jin maganar shi,


"Dalla dubeku, wasu bajimaye daku, ko kunya baku ji ba! Mutane marasa imani, wlh da ace tuntuni munsan da zamanku a doron duniyar nan wallahi da tuni mun jima da shafe babinku, mugaye, azzalumai marasa imani, yau dai dubunku ta Cika, wlh saikun ɗanɗani kuɗarku...!"


 Kalaman Big Guy sun yi matuƙar fusata zuciyoyinsu, tun da uwayensu suka haife su a duniyar nan wani ɗan adam bai ta6a tunkararsu gaba da gaba Ya faɗa masu kalaman 6atanci ba sai akan Big Guy.


"Ni bansan ma da wani jinsi zan misalta ku ba, saboda ku ɗin Jakkunane, dabbama tafi ku kyan kai, gaku dai ƙazamai, saboda shafewar basiri da ruɗin duniya da son kai da zalunci kun manta cewa wata rana dole ku mutu kubar duniya ku koma ga mahaliccin ku, Wai ku anya kuna da zuciya a ƙirjinan ku? Wasu irin mugaye ne ku.......!"


Taj da ya ɗauko maganar bai ƙare ta ba, sakamakon wata irin razananniyar tsawa da Jan wuya Ya daka mashi, tuni Ya haɗiye sauran maganar da bai idasa amayarwa ba..


Girgiza kai Chief ya yi, wlh takaici da baƙin cikin ganin Elders Ya hana zuciyarshi salama, Rai a matuƙar 6ace ya ce, "Mai kuke jira ne!" Ya faɗa tare da kallon dakarun sojojin su.


"Ku kama su! Da ransu muke son su, dole su fuskanci hukunci mai tsanani!!!"


Kamar Jira Sojojin su ke yi ya basu umarni suka fara ƙoƙarin kama Elders aikuwa kwatsam! Ba zato ba tsammani suka fara ganin wasu irin samudawan Evil Giants suna faɗowa cikin Hall ɗin masu yawan gaske, Kai da ganinsu sai gaban mutun Ya faɗi saboda ƙirar karfin su, gaba ɗaya su ka cika Hall ɗin, Sai gurnani su ke yi tamkar mayunwatan zakuna..


Sai lokacin Elder Ya buɗe baki ya ce, "Garkuwa, kayi tunanin bazan gane ka bane?" Sautin muryarshi ta canza kamar ta matashin saurayi, A hankali Danish ya cire Mask ɗin fuskarshi, Ya fuskance su da ainihin suffarsa ta jarumta, gaba ɗaya sun girgiza sun kuma kiɗima da ganin shi....


Cikin karyayyar murya Elder  Ya kuma cewa, "Ni nasan ba yin kanka bane, tursamaka suka yi, kada ka manta baka da gata da ya wuce mu a duniyar nan, mune rufin asirinka, mu muka raineka muka gatanta ka, mu ka inganta rayuwarka. Ka manta irin gatanci da muka yi maka ne? Kada ka ce zaka Ci amanarmu.." 


Elder bai kai ga ƙare maganar ba sakamakon tsawar da Chief Owais ya daka masa yana huci, bai kaiga furta kalma ba Jan Harshe Ya ɗaga masa hannu, "Karka kuskura ka ƙara maimaita kuskuren da kayi!! Ba a yiwa Elder tsawa! Idan Yana magana ba'a katse shi!" Wlh ƙarfin halinsu ya yi matuƙar ɗaurewa Chief kai.


Cike da takaici  Garkuwa ya ce, "Babu wanda ya tursasa mini, Ni nasa kaina, maƙaryatan banza, you've been deceiving me for a long time under the guise of privilege"


( ka daɗe kana yaudarata da sunan kune gata na!")


Tuni idanun shi sun cicciko tab da ƙwalla, ga wani ɗaci da yake ji a ranshi.


"Yanzu na riga da na gane cin zalun da kukayi mini, tsawon shekara ashirin tun ina jinjiri na kuka raba ni da iyayena, batare da sanin su ba, kun yi masu ƙaryar na mutu bayan ina raye, laifin me na yi maku??"  Ya faɗa a tsawace kamar zai rufe su da bugu, wlh sun razana da jin abun da ya ce, basu yi zaton zai gano gaskiya ba.



He was extremely angry, maganarsa ma daƙyar take fita saboda 6acin rai,


"You never loved me, you hurt me and violated my right to live. Kun raine ni saboda biyan buƙatar kanku, da ace nasan gaskiya tuntuni, hmmm, da yanzu babu ku a doron duniyar nan, na tsaneku Elders...."


 Bai ƙare maganar ba, Jan le6e Ya tari numfashin shi da cewa, "Kai har ka kai matsayin da zaka Ci amanarmu? Ka manta duk wani abu da kake taƙama dashi agurinmu ka same shi! Ba don mu ɗin ba ina zaka samu ƙarfin halin tunkararmu har ka rako wasu don ku farmake mu? Dube ka dallah! Sun maida ka sauna, shashasha, sakarai sai yadda suka yi da kai..." 


Murmushin takaici ya yi batare da ya furta kalma ba, su Taj da ke sauraronsu kamar su rufe shaggu da bugu suke ji saboda zafin maganarsu, Salsabeel da ya gama fusata rai a 6ace ya zame mask ɗin fuskar shi don su ganshi da kyau.


Nuna shi Elder ya yi da yatsan shi batare da ya iya furta kalma ba saboda ƙululun baƙin cikin da ya tokare maƙogwaron sa...


Cikin zafin rai Jan Harshe Ya furta, "Maci Amana, dama nasan kana acikin su, bakasan cewa nemanka muke yi ruwa a jallo ba? Hmmm, na ji daɗin ganinka ɗan maciya amana, tun da har kayi kuskuren kawo kanka cikin kurkukun nan, to ka sani mun tanadanar maka azaba mai raɗaɗiii..." 


"Ta Allah ba taku ba, dama nasan kun ƙullace ni, naji daɗi dana dasa baƙin ciki a cikin zukatanku, ko ba komai mahaifiyata ta yi nasara akanku saboda itace silar komai...." tiryan-tiryan Salsabeel ya labarta masu shirin da suka daɗe suna yi akan ɗaukar fansar mahaifinsu Habibullah da suka kashe har izuwa taimakon da suka yi ma prisoners gurin tseratar da su,


Haƙiƙa Elders sunji zafin cin amanar da suka yi masu, sai dai basu nuna hakan ba.



Yar dariya Big Guy ya yi tare da cewa, "Na fahimci haushin su kuke ji saboda sun tona maku asiri, idan ku masu hankaline kuyi nazari mana, gaba ɗaya duk wani shirinku lalacewa yake yi...."


"Ga misali nan kun gani, Danish yanzu namu ne, kun raine shi mu kuma zamu ci moriyar shi, garkuwar ku Ya juya maku baya yanzu mu yake goyon baya, kuma dashi zamu yi amfani gurin kawo karshen zaluncin ku"


Ya faɗa tare da yi masu gwalo, aiko ransu Ya 6aci, zuciyarsu ta harzuƙa, Big Guy da ƙarfin hali Ya kuma cewa, "Wai ashe Elders ɗinma matsorata ne, naga kun rufe fuskokinku, In ba tsoro ba, ku buɗe mu ganku mana, Ko kuna jin tsoron kada mu gane su wanene ku?"


Shiru suka yi basu tanka mashi ba.


Sai da ransu ya kai maƙura a 6aci, suka harzuƙa ainun kawai Elder ya ba Evil Giants umarnin su farmake su, Kafin kace me faɗa Ya kaure tsakanin Sojojinsu da Evil Giants, wata irin ƙura da kururuwa ta karaɗe tsakar Hall ɗin, Bugun mutuwa suke yi ma junansu, Abu fa ya ture don ginin wurin har girgiza ya ke yi saboda bala'e, baka jin komai sai sautin naushi da ƙarar buge buge da sukar kibiyoyi.


Lokaci ɗaya Hankulansu Chief ya fara tashi ganin yadda Evil Giants suke kashe sojojinsu, Jini sai ambaliya yake yi, Wani irin kisan rashin imani suke yi masu, cikin ƙanƙanin lokaci sun kashe sojojin sama da hamsin.


 Yayin da su kuma ko ƙwarzane babu wanda ya yi masu saboda Garkuwar kakin dake a jikinsu, bayan haka suna amfani da sihiri gurin 6acewa, sai dai mutun ya ji sun dira a bayanshi kafin ya ankare tuni suke farke cikin shi da akaifun su, Evil Giants Bala'e ne...!


Shu'umin murmushi Elders suka fara saki, dama sun san bazasu iya karawa da Evil Gaints ɗinsu ba.


Ganin suna neman su rasa Sojojinsu yasa Danish yin wata irin suka ya dira a tsakiyarsu, Da gudumar hannunsa Ya dinga tarwatsa kawunan su, da bugu ɗaya yake kashe su, kamar Allah Ya aiko shi, ganin haka yasa su Omar fara sakin kabbara da ƙarfin gaske suma suka afka cikin filin dagar, Cikin Ikon Allah sai gashi sun Ci ƙarfin Evil Giants ɗin, sun bada ƙaimi haiƙan a filin dagar, wani zungureran mashi ne a hannun Chief Idan ya saita shi ya jefa shi kaitsaye mashin yake soƙe kawunan Giants, a lokaci ɗaya sai mashin ya kashe giants sama da goma, da Evils din suka ga haka sai suka rikiɗa suka koma wasu irin mugayen dodanni masu zaƙo zaƙon akaifu suka fara farka cikin Sojojin da ƙwalƙwale idanuwansu.


Duk fa abunda ke faruwa akan idanun Elders suna a tsaye suna kallon su, Abun da ya ɗaure masu kai, ganin makaman da suke faɗa da su yana tasiri akan Evil Giants ɗinsu, kuma abun mamakin da ya sha masu kai sun lura makaman kamar irin wanda maƙeran kurkukun ƙaddara suke ƙerawa ne, har sun fara 6ata rai ganin ana kashe nasu amma da suka ga Evil Giants din sun cigaba da kashe sojojin sai suka fara sakin dariyar mugunta.


Bayin Allah sun ci baƙar wahala, kusan sau biyar Evil Giants suna kokarin kashe Taj sai dai Danish ya hana, duk yadda zaiyi ya kare shi ko ya kawar da shi sai ya yi don baison Unaisah ta rasa mahaifinta, Ya gwammace shi su dake shi akan su ta6a Taj, ba don shi ba da tuni Taj ya sheƙa barzahu.


Big Guy kuwa da yake Allah ya zuba mashi ƙarfi shi da Chief Owais kuma sun ƙware wurin  sanin dubarun yaƙi sosai hakan yasa ko ƙwarzane basu yi masu ba, kamar ana ƙaro masu Giants ɗin don daga sun kashe su wasu ke ƙara kurɗaɗowa ta jikin bango suke shigowa, Kun san ance sarkin yawa yafi sarkin ƙarfi, Kwatsam! Suna tsaka da yin artabun nan wani shaiɗanin Evil Giant ya damƙi Big guy Ya daddage ya ɗaga shi sama kafin ya buga da ƙasa nan take Kan shi Ya fashe jini Ya fara bulbulowa..


Karaf akan idanun Chief, wani irin Ihu Chief Ya fasa ganin zai rasa amininsa, ya yi kukan kura Ya dira agaban Giant ɗin ƙazamin faɗa ya kaure tsakanin su, gaba ɗaya hankalin Sojojinsu baya akansu saboda kowan nan su hankalinshi ba a kwance Yake ba ganin abun na neman fin ƙarfin su koma a ce yafi ƙarfinsu, Giants sun mamaye su ba kaɗan ba....


Duk yadda Chief ya so ya kashe shi abun ya faskara, saboda wani kafirin ƙarfine da shi, da mugunta Giant ɗin ya sakar mashi naushi a tsakiyar cikin shi, nan take ya fara aman jini, duk da haka bai ƙyale Chief ba, Ya daddage ya buga kan shi jikin wani ƙarfe nan take goshinshi ya faffashe jini ya fara bleeding ta hancin shi.


Hakan bai yi mashi ba, saida ya kai shi ƙasa ya damƙi wuyan shi ya fara jan shi a ƙasa ya tunkari wani kaskon wuta da niyyar ya tura kan shi ciki, gaba ɗaya Chief ya fita hayyacin shi ya kasa taimakon kan shi, a dai dai lokacin Danish ya ankara da abun da ke faruwa, ai baisan sa'adda Ya fasa ihu ya saki gudumar dake a hannunshi, sai dai me, kafin Ya kai mashi taimakon gaggawa wasu gungun Evil Giants suka rufe shi da bugun mutuwa suka hanashi motsawa, dama raunin shi suke jira, kamar zaiyi hauka.


A can bangare guda kuwa Taj shima Ya gamu da nashi bala'en, wani ƙasurgumin shaiɗanine ya take cinyar shi da basamudiyar ƙafarshi, nan take kafar ta bada wani sauti rukukus kamar zata cizge, har fashewa saida tayi jini ya fara bulbulowa, Azaba goma da tara Ihun ma ya kasa yi sai juyi yake yi a ƙasa.....


Salsabeel yana tsaka da yin faɗa ya zage damtse sai kashe su yake yi, bai aune ba yaji an damƙi damtsen hannun shi, da sauri ya juyo don ya ga wanene, rass! ya ji gabanshi ya yanke ya faɗi ganin ɗaya daga cikin Elders dama haushin shi suke ji..


Kafin ya yi wani yunƙuri Elder din da ya damƙesa ya murɗe hannun shi, azabar raɗaɗi ya hana ko ihu ya yi, naushi ya sakar mashi a gefen fuskar shi nan take jini ya wanke bakin shi, duk da haka bai ƙyale shi ba, sai da ya damƙi kanshi ya ja a ƙasa ya nufi matakalar bene ya buga kan a ƙasa, bawan Allah Salsabeel radadi ta ko'ina yake ji, saboda rashin Imani hakan bai masa ba, ya ɗaga ƙatuwar ƙafarsa da niyyar ya take kan nasa sai kuma ya fasa sakamakon wani abu da ya ja hankalin shi wanda ya ja har ya bar gurin salsabeel.....


Evil Giant ɗin da ya damƙi wuyan Chief yana ƙoƙarin tura kanshi cikin kaskon wutar, Unexpected ya ji an damƙi hannun shi, Yana huci ya juyo karaf suka haɗa ido da elder, kafin ya furta wani abu Elder ɗin ya murɗe kanshi nan take ya kife ƙasa matacce, ba tare da sun ankara ba ya janye Chief daga filin dagar ya nufi ƙofofin dake a cikin hall ɗin ya wurga shi a cikin wani daki kafin ya ja ƙofar ya datse ta, babu wanda ya lura da hakan.



Daƙyar Danish yafi ƙarfin Evil Giants ɗin da suka rurruƙe shi ya yi kukan kura ya watsar da su, jikinshi ya yi rauni sosai, sun faffasa kakinsa da ƙumbunansu har sun ta6a fatar shi, fuskar shi duk ta 6aci da jinin raunukan da suka ji ma shi.


Wata irin jijjiga ya yi ya rikiɗa ya zama jibgegen Zaki.. Ya afkawa Giants, cikin zafin nama ya dinga  kakkashe su ta hanyar farke Idanunsu, cikin ƙanƙanin lokaci ya kashe Giants sama da ɗari, gaba ɗaya ya zubar da gawarwakinsu ƙasa.


Koda ganin haka nan fa Elders suka fara shan jinin jikin su.. ganin yadda Danish Ya salwantar da rayukan Giants ɗin su, ta ko'ina jininsu ne ke tartsatsi yana sauka ƙasan wurin kamar ƙoramar jini...ga yan hanjin cikin su waje sun zazzago, ransu ya 6aci matuƙa har ƙoƙarin sarrafa shi suka yi da sihirinsu don ya koma yana kashe sojojin don mugunta, sai dai wani iko na Allah Evils ɗin Danish sunƙi responding umarnin da suke basu, lamarin ya girgiza su ba kaɗan ba, sun rasa gane tayaya zasu shawo kan shi.


Basu gama kaɗuwa ba sai ga tawagar U.s Army sun faɗo Hall din, Sun gama da matsafan da sukai saura sun dawo nan don su tayasu yaƙi, ashe duk wani bomb da ya fashe a filin shagalin U.s Armies ne suka dasa su. Bayan sun yi 6adda kama sun saka kayan matsafan da Khala ta basu, suka shige cikin matsafan dake a filin shagalin, Cikin hikima da ƙwarewa suka dasa bombs a saƙo da lungu na ground floor ɗin kurkukun, bayan sun tabbatar da Elders sun fita daga cikin filin dama haka suka tsara saboda basa son Elders su mutu a raye suke son su, da ganin fitarsu a hanzarce suma suka nisanta kansu da filin taron kafin suka danna remote din dake a hannuwan su nan take bama baman suka faffashe.


Hankulansu ba ƙaramin tashi ya yi ba, ganin yadda aka kashe Sojojinsu, koda Elders suka ga sun ƙaru kuma zasu iya yi masu 6arna ba kaɗan ba ga Danish ya zamar masu masifa sai zubda jinin Giants yake yi, hakan yasa suka fara tunanin buɗe rijiyar da Jeremiah yake a ciki, saboda shi kaɗai ne zai iya ƙarar da su kaf cikin mintuna ƙalilan.


Bawai don su basu da ƙarfin yin faɗa dasu bane, kawai rainine a gurinsu su yi gogayyar kafaɗa dasu gurin yin faɗa, sun fi so su nuna masu ƙarfin ikon su.


Kafin su aiwatar da mummunan ƙudurinsu, tuni U.s armies sun haɗa hannu da Danish duk da ba a suffarshi yake ba sun fahimci shine sanin yana iya canza suffa kamar yadda aka sanar masu kuma gashi sun ga yana farmakar Giants, nan fa suka ci gaba da bada ƙaimi suka ci gaba da kashe Giants ɗin.


Kafin ka ce me, tuni sun wanke Hall ɗin da jinin Giants ya malale ƙasa kamar ambaliyar ruwa...hakan ba ƙaramin tada hankalin Elders ya yi ba, ransu ya kai maƙura a gurin 6aci, Zuciyoyinsu sai tafarfasa suke yi saboda tsabar fusata, ga wani gurnani da suke saki kamar mayunwatan zakuna.


Saida suka ƙarar da Giants ɗin, hankalin Danish ya karkarta akan su Taj, gaba ɗaya sun razana da ganin su cikin jini kamar babu rai, Cikin sauri ya nufi Big guy dake yashe ƙasa, ya taimaka mashi gurin ɗaure mashi kan shi da wani jan ƙyalle da ya tsinta a nan, sai nishi yake yi bawan Allah, Shi kaɗai yasan irin azabar da yake ji, daƙyar ma ya rayu.


Jini duk ya wanke fuskarshi, cikin fitar hayyaci Ya furta,"Danish.... Chief, help him! I don't want him to die, go find him, I want to see him before I die...."


Tsantsar tausayinshi ne ya kama su, duk da halin da yake a ciki damuwar shi akan Chief ne, wannan wata irin ƙauna ce 💔


"Danish ! Ina Chief?" Commender ne ya tambaye shi, Girgiza kanshi ya yi yana huci ya furta, "Bansan ina ya shiga ba, amma zan binciko shi."


 Ya faɗa tare da miƙewa, juyawar da zai yi keda wuya yaci karo da Taj wanda ke kwance cikin gawarwaki kamar ba numfashi a jikin shi, Hankalin shi ya tashi matuƙa, cikin sauri ya nufe shi ya taimaka mashi ya miƙar da shi zaune tare da jinginar da shi gefen Big guy, bawan Allah sai sambatu yake yi yana faɗin yar shi, ya bar masa amanarta, ya ruƙe mashi ita, baya so ta yi maraicin rashin shi, kalaman Taj sun karya zuciyar Danish, bai san sa'adda ya ji hawaye sun wanke fuskar shi ba.


In a weak voice ya furta, "Ba zaka mutu ba, zaka rayu, Angel tana buƙatarka, bana so ta rasa ka...."


Ƙafar Taj da ta lanƙwashe ya jata da ƙarfi ta bada wani irin sauti, tsabar raɗaɗin da Taj ya ji ne yasa shi sakin ihun azaba, nan take ya yanke jiki ya faɗi ƙasa sumamme, duk Danish ya bi ya ruɗe, ya kasa gane yana raye ko ya mutu ne? Ya dai samu ya tsayar da bleeding ɗin cinyarsa.


Miƙewa ya yi tare da kallon su Commender da sauran sojojin da suka rayu, gaba ɗayansu babu wanda bai raunata ba, sun jigata sosai, gaba ɗaya sun sare da lamarin.


"Salsabeel!" Hankali a tashe Ya furta lokacin da idanunsa suka hango mashi Salsabeel kwance rai hannun Allah, da gudun gaske ya bi takan gawarwakin dake zube a ƙasa ya nufi gaban benen,  yana isa ya zube kan ƙafafuwansa tare da tallabo kan Salsabeel, wasu irin zafafan hawayene suka wanke fuskarshi ganin hannun shi dake a karye ƙiris ya rage ya 6alle biyu, ƙashi har ya 6ullo ta fatar, da ƙarfi ya fasa ƙara mai sautin gaske shatun jijiyoyin goshinshi suka fito ruɗu ruɗu kan fatarsa, Su Commender dake kallon shi jikinsu ya yi sanyi sosai kamar su zubda mashi ƙwalla saboda tausayi.



Unexpectedly Ginin kurkukun Ya fara Jijjiga kamar zai 6a66ako, lokaci ɗaya kunnuwansu suka fara jiyo masu sautin wata shu'umar dariya ta tantirin shaiɗani mara daɗin saurare.


Tunkafin ma su ga wanene suka sha jinin jikin su, saboda tashin hankali gaba ɗaya sun shafa'a sam sun manta da zaman Elders a hall ɗin waɗanda tuni sun jima da 6acewa, 6at babu su babu alamarsu, sun riga da sun san tsiyar da suka shuka, sun tafi sun bar su da masifa.


Cikin hanzari Danish ya miƙe tsaye, zuciyarsa na dakan uku uku, yayin da rinannun idanunsa ke akan rijiyoyin dake a hall ɗin saboda yasan yana ciki.


"Ina Elders suke? Sautin dariyar da muke ji ta wanene?" Canal Herry ne ya yi tambayar a ruɗe.


"The Elders have disappeared, the only way to escape is to run away before the evil giant emerges from the wall, He's the most dangerous evil giant in the prison of Destiny, and their new prison shield, ba zaku iya ja da shi ba, Ku barni da shi, In ba haka ba, zaku rasa rayukan ku ne!"


Wani irin faɗuwar gaba suka ji, kafin wani daga cikin su ya motsa, Unexpectedly murfin ɗaya daga cikin rijiyoyin ya 6alle da karfi tattare da iska ya yi sama kafin ya ƙundumo ƙasa, gaba ɗaya suka zare ido suna jiran ganin menene zai biyo baya.


A firgice Danish Ya dinga yi masu tsawa yana faɗin su tafi! su barshi da shi, amma suka ƙi tafiya saboda bazasu Iya barinshi shi kaɗai ba.


Lokaci ɗaya wani irin hayaƙi mai haɗe da tartsatsin wuta ya fara fitowa daga cikin rijiyar tuni suka sha jinin jikin su, ashe basu ga komai ba, lokacin da basamudan shaiɗanin ya duro daga cikin rijiyar kusan suman tsaye suka yi tsabar razana da kiɗima.


Wani irin zabgegen mutun, kwata kwata babu sutura a jikin shi, zir yake haihuwar uwarsa, gaba ɗaya jikinshi zanen tattoo ne da zanan aka yi mashi sutura, Ga wasu zaƙo-zaƙon akaifu masu kama da tsinin mashi, lokacin da ya buɗe idanun shi ƙiris ya rage su commender su arce a guje saboda wani irin jajayen idanu gare shi, Idan ka kalleshi sau ɗaya ba zaka ƙara marmarin haɗa idanu da shi ba saboda tsoratarwar da gare shi.


Bakowa bane wannan face sabon Garkuwar kurkukun ƙaddara wato JEREMIAH.


Da ƙarfi commender ya ba sojojin da suka rage umarnin su fara harbin shi, saita shi suka yi da bindigu suka dinga sakar mashi wuta ta ko'ina sai dai ko gizau baiyi ba, har bomb suka wurga mashi ya gangara agaban shi, ya ɗaga faffaɗan tafin ƙafarsa ya murje bomb ɗin, koda ganin haka ai saifa jikin taƙaura ya yi La'asar!


Tun fitowar shi daga rijiyar idanun shi na akan Garkuwa shi kaɗai yake hari, dama da niyyar ɗaukar fansa suka ƙirƙire shi, girgiza jikin shi yayi tare da sakin tsawa mai kuwar gaske, tamkar zai fasa dodon kunnuwansu, duk saida suka girgiza.


Tsautsayi ne ya kai wani soja gaban shi ya ɗaga wuƙa zai caka mashi aikuwa ya damƙi wuyanshi, nan take ya tsinka shi biyu, jini ya dinga tartsatsi ya jefar da gangar jikinsa gefe ɗaya, ai koda ganin hakan nan fa suka fara Ja da baya In ka cire Danish shi kaɗai ne bai motsa daga inda yake ba, ƙarasowar shi kawai yake jira.


Da gudu wasu sojojin suka nufe shi, tunkafin su karasa ya matse yatsun hannayenshi nan take jikinsu ya faffashe kamar anyi jajjagen kayan miya...



Waro idanu waje su Commender suka yi, lamarin ya gigita tunanin su, basu ta6a ganin bala'e da musiba ido da ido ba sai yau da Allah Ya haɗa su da Jeremiah.


Gaba ɗaya gurnanin Jeremiah ya addabi kunnuwan su, Danish dake atsaye ya rasa abun yi, yasan muddin Jeremiah ya baro bakin rijiyar wlh sai ya kashe su kaf ɗinsu da ido kadai zai iya salwantar da su.


Shiru ya yi yana yanke shawara da zuciyar shi lokaci ɗaya ya fara tariyo kalaman Unaisah sai ya ji kamar a lokacin take furta mashi su,


_I love you, Danish! I really love you, i wanna be with you for the rest of my life, I can't live without you, My heart beats for you alone, My soulmate, I'm yours, I don't want you to go and leave me! Please come back to me! don't die! I'll wait for you..."_


Yana so ya gana da tsohuwa khala saboda yaci burin ta faɗa mashi su wanene iyayensa yana matuƙar son ya gansu fiye da komai na duniyar nan, yana kuma son ya rayu saboda Unaisah, amma ya zai yi? Baida wata mafita da ya wuce ya aiwatar da abun da yake ganin dai dai ne.


Su Commender sai kiran sunanshi suke yi don su ji me yakamata su yi kafin Evil din ya farmakesu, Hankalin shi baya atare da su, gangan jikinsa kaɗai suke gani amma ruhinsa yana atare da Unaisah...


Wata irin jijjiga Jeremiah ya yi, A lokacin ya gama daidaita jikin shi, dama abunda ya tsayar da shi kenan, babban kuskuren da zasu yi shine su bari Jeremiah ya baro bakin rijiyar, domin kuwa in har ya dira ƙafarsa duk wani mai sauran rai da babu sihiri a jikin shi sai ya mutu in ba wani iko na Allah ba, aikuwa yana ɗaga ƙafarsa kafin Ya dire ta ƙasa, Danish ya watsa da gudun gaske ya durfafe shi, yana ƙarasawa gaban shi ya daka uban tsalle ya haye kanshi ya cakumeshi da hannuwan shi biyu, da iya ƙarfin shi na ƙarshe ya ingizasu gaba ɗaya suka rubza cikin rijiyar, nan take murfinta ya maida kanshi ya rufe makullinta ma ya datse kan shi, Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un!!!😭😭😭




Da ƙarfi suka dinga ambaton sunan Danish kamar zasu fasa ihu saboda tashin hankalin kada su rasa shi, da gudun gaske su Commender suka nufi rijiyar, suka haɗa hannu duka Sojojin suka fara kiciniyar 6alle murfin, saida ina, abun ya ci tura saboda murfin rijiyar mugun ƙarfene da aka tsaface shi, haka suka dinga zubda gumi suna ta haki tare da jan murfin don ya buɗe amma duk a banza. Duk irin jarumtakarsu ta sojoji saida suka fashe da kuka tamkar ransu zai fita, babu irin makamin da basuyi amfani da shi ba don su buɗe murfin rijiyar abun yaci tura, har bomb suka ɗaura saman murfin don ya buɗe suka ja da baya tare da duƙewa ƙasa, sai dai koda bomb ɗin ya fashe babu abunda murfin rijiyar ya yi.


A gaban rijiyar suka zuzzuƙunna cike da takaicin rasa Danish da suka yi, Suna tsaka da tashin hankalin nan, saiga Chief ya duro ta tagar ɗakin da Elder Ya garƙame shi, daƙyar yake jan ƙafar shi, jini duk ya wanke fuskarshi da gaban kakinsa, babu inda bai raunata ba ajikin shi, hankalin shi ya tashi da ganin gawawwakin rayukan da aka salwantar, nan take ya fara jin matsanancin faɗuwar gaba da tashin zuciya gami da ruɗani...


Kalmar farko da ta fara fitowa a bakinsa shine Ina Danish? Ina Omar? Ina Taj da Salsabeel?" Shiru sojojin suka yi an rasa wa zai bashi amsa saboda fargaban halin da zai shiga, cikin rauni na murya ya furta, "Wai baku ji ina magana ba? Ina Danish ne?" Cikin karyayyar murya Commender James ya ce, "Omar, da Taj da Salsabeel, sun raunata sosai, bamu da tabbacin suna a raye ko sun mutu,"  Ya faɗa tare da nuna mashi inda suke, daƙyar ya iya hangosu, 


Cikin sanyin murya ya ce, "Shi fa Danish yana ina?" Kallon juna su ka yi batare da sun furta kalma ba..


"Kada kuce min ya mutu! Meyasa nake ganin hawaye akan fuskokinku?" A wahalce yake yin magana, daƙyar Major ya bashi amsa da cewa, "Kayi haƙuri Sir, bamu da tabbacin yana araye ko ya mutu...."


"Yana Ina ne??" Ya faɗa kamar zai saka masu kuka, da hannu  lieutanant Jackson ya nuna mashi rijiyar.


Kafin ya labarta mashi abunda ya faru na baiyanar Jeremiah ya ƙara da cewa, "Mun yi iyakar bakin ƙoƙarinmu, sai dai mun kasa buɗe murfin rijiyar, gaba ɗaya bamu ji daɗin abunda ya faru ba, saboda mu rayu, ya sadaukar da kan shi...." Ya faɗa hawaye cike tab da idanun shi.


Cikin rauni na murya Thompson ya ce, "I've never seen a braver person than him, He's the real hero" 


Captain ya ɗaura, "Ni kaina na jima banga mutun mai jarumta irin nashi ba, Ya cancanta ya rayu amma tayaya zamu iya taimakon shi..."? 


Idanunshi cike tab da ƙwalla ya ƙare Maganar, jiri Chief ya fara gani a cikin idanun shi, duk irin juriyarshi saida ya fashe da kuka mai sauti kamar ƙaramin yaro, a sukwane ya zube kan gwiwowinsa ya kifa kanshi ƙasa kamar zai haƙa ƙasa ya binne kanshi saboda wutar baƙin cikin da ke ruruwa acikin zuciyar shi, da sauri su commender suka kewaye shi don su lallashe shi amma ina zuciyarshi ta kai maƙura, Yunƙurawa yayi ya miƙe da sauri suka rurruƙe shi, idanun shi a rufe yake tambayar Ina Elders? Suna a raye ko sun mutu?" Commender Haroon Yace, "Sun 6ace ma ganin mu, ina da tabbacin sun gudu daga gidan kurkukun nan." Dafe kanshi yayi da hannu ɗaya, ji yake kamar ya kurma ihu ko ya samu ya fitar da abunda ke ranshi, bakowa ya faɗo mashi a rai ba face tsohuwa Khala yasan zata iya taimakon su.



Sai da ya fara umurtar wasu daga cikin sojojin yace su ɗauki su Taj su tafi da su, a kafaɗa suka rataya su, basu tsaya 6ata lokaci ba, cikin sauri suka nufi hanyar da zata sada su da ɗakin tsohuwa khala, sai dai me, kwatsam! suna tsaka da yin tafiya gaba ɗaya hasken gidan kurkukun ya ɗauke ɗuff, wani irin duhu baƙiƙƙirin Ya mamaye idanun su, Cikin sauri suka zaro Torchlight ɗin su tare da kunna su haske ya ɗan wadata kaɗan.


Dakatawa Chief yayi da yin tafiya, gaba ɗaya suka kalle shi, tsantsar tashin hankali suka gani akan fuskarshi, a ruɗe ya furta, "Kun kira pilots ɗinmu dake a waje" Gabansu ne ya faɗi, wlh sham sun shafa'a basu tuntu6e su ba, balle su ji meke faruwa a can, sun san tabbas za'a iya farmakarsu tun da Elders sun 6ace.


Cikin sauri Commender ya zaro tactical radio ya kanga a bakinsa, kusan sau uku yana kiran sunayen matuƙan nasu shiru ba'a amsa mashi ba..


A hanzarce Chief ya ciro wayarsa ya kanga a baki da ƙarfi ya dinga furta sunayensu nan ma shiru, wa'iyazubillah!


Tamkar zai fashe da kuka ya furta, "Taya zamu san meke faruwa da sauran sojojinmu da muka bari a waje!"


Dafa kafaɗarsa James ya yi, "Ku kwantar da hankalinku, ba lallai abunda kuke hasashe ya zamana gaskiya ba, zai iya yuwuwa matsalar network ne, saboda na fahimci network da suke amfani da shi iya cikin kurkukun ne yake aiki, wanda ke a ciki bazai iya kiran na waje ba, haka shima wanda ke a waje bazai iya kiran wanda ke a cikin kurkukun ba..." Commender da ya yi maganar ya faɗane don ya kwantar masu da hankali amma shi kanshi yasha jinin jikin shi.


Cike da takaici chief ya ja tsoki kafin suka cigaba da tafiya, a ƙalla sun karya kwana ya kai takwas kafin suka kawo kan dogayen benayen nan, aikuwa suna hawa benayen suka fara maidosu baya, idanunsu suka fara yi masu gizon yan uwansu da suka bari a gida suka dinga ganin su a kan hawa na uku Giants sun rurruƙe su suna kokarin wurgo da su ƙasa.



"Daddy, don't let them kill me! Help me, Daddy" Dafe kai commender Jemes ya yi jin muryar yarsa tilo, saboda ruɗu da tashin hankali ya fara kokarin komawa hawa na ukun don ya taimaketa, damƙar hannunsa Chief ya yi, sai hauka hauka yake yi yana faɗin ya sake shi zai je ya ceci ƴarsa...


Chief yana fitar da huci ya ce, "Ka manta abunda Danish Ya faɗa mana, kafin zuwanmu gidan kurkukun nan? Abun da kake gani ba gaskiya bane, sun yi hakanne don su razanar da mu..." 


Yana ƙoƙarin shawo kan Commender James batare da sanin shi ba, Major smith ya watsa da gudu ya haura hawa na uku, ganin giants ruƙe da matarshi mai tsohon ciki sai kuka take yi tana miƙo mashi hannu don ya taimake ta.


Yana ƙarasawa gaban benan Giants ɗin suka jefo da ita, aikuwa cikin fitar hayyaci ya daka suka ya bi bayanta don ya ceto ta, kafin su ankara tuni Major Smith ya kife ƙasa nan take kanshi ya fashe ko shurawa bai yi ba ya mutu, matar da yabi dama babu ita gizaune kawai Giants ɗin ma duk sun 6ace babu su.


Zuciyar Chief ta karaya sosai, commanders da sauran sojojin jikinsu yayi mugun yin sanyi, wlh sun ji baƙin ciki da takaicin rasa sojan su, Kamar su ɗaura hannu akai su fasa ihu, don ma jarumta irin na sojoji ba yau suka fara ganin irin tashin hankalin nan ba..



Dafa kafaɗar Commender Chief ya yi in a cool voice ya furta,"I'm really sorry..." Girgiza kai Commender ya yi, "Kada ka damu, ajalinshi ne ya yi, ba mu isa mu hana shi mutuwa ba, balle muda muke sojoji dama saida muka bayar da rayukanmu kafin muka kar6i aikin, sannan duk rashi da muka yi bai kai naku ba..." 



Da ƙyar suka shallake benan suka ci gaba da tafiya suna haska hanya da torchlight ɗin hannunsu, wani abun tashin hankalin duk in suka haska bango sai sunga inuwar Evils.


Wani sa'in har gifcin shaiɗanun suke gani...amma da yake zuciyar su ta kangare sun ma daina jin fargaban komai...gaba ɗaya ginin nema yake ya juye masu lissafin ƙwaƙwalwar su sun kasa gano hanyar da ɗakin tsohuwa khala yake lalube kawai suke a duhu, suna tsaka da tafiya kwatsam saiga wata tsohuwa kamar mahaukaciya ta faɗo ta gabansu hannunta tallabe da tsohon cikinta, sai kuka take yi tana roƙonsu su taimaka mata naƙuda take yi, abunka da me tausayi Chief har ya yi niyyar taimaka mata zuciyarshi ta raya mashi, "karka kuskura! kai baka ga ta yadda ta faɗo gaban ku ba..." Kafin ya yanke shawara da zuciyar shi tsohuwar ta daka suka ta haye kan Thompson ta dinga yakushin shi da cizon fuskar shi, cikin xafin nama Chief Owais ya damƙi ƙeyarta ya 6am6areta daga jikin Captain ya daddage ya buga kanta da ƙasa, kafin ta ɗago Commender James ya sakar mata harsashi a tsakiyar kanta, nan take ta sheƙa...


Kallon Thampson suka yi, fuskarshi ta yi jaga jaga da jini gwanin ban tausayi, haka suka dinga cin karo da tsoffin mata matsafa sai hari suke kawo masu, ɗaya bayan ɗaya suke kashe su. Sai da suka gama shan baƙar wahala duk sun jikkata daƙyar suka gano ɗakin tsohuwa Khala, tun kafin su shiga gabansu ke faɗuwa ganin ɗiɗɗige-ɗiɗɗigen jini kan benan da zai kai su ɗakin nata.


Kallon kallo suka jefawa junansu, an rasa wanda zai fara shiga ɗakin saboda zullumi da fargaban abunda zasu taras..


Sun shafe mintuna biyar a bakin ƙofar ɗakin batare da sun iya ta6uka komai ba. Daƙyar Chief ya yi ƙarfin halin tura ƙofar da sunan Allah a bakin shi ya zura ƙafarshi, su Commender suka bi bayan shi.


Wani irin burki suka ci, ganin babu khala aɗakin ta, abun da ya jefa su a matuƙar ruɗani gaba ɗaya ɗakin nata a hargitse yake, hatta gadonta ya jirkice, tukwanan furannin dake a ɗakin duk an faffasasu, Ga jinin da ya malale kasa... YA ILAHI❗❗


*INA TSOHUWA KHALA❓* INA PRISONERS DIN DA SUKA KU6UTAR❓*IN BAKU MANTA BA ITA TA CE SU KAWO YARAN DA SUKA KU6UTAR WURIN TA GASHI BABU ITA❓*


*MEKE SHIRIN FARUWA NE❓* *MEKE FARUWA TSAKANIN JEREMIAH DA DANISH BAYAN SUN FAƊA RIJIYA❓KUNA TUNANIN ZAI RAYU❓*SHIN YA BATUN BIG GUY, TAJ DA SALSABEEL WADANDA A HALIN YANZU BAMU SAN TAƘAIMAIMAI SUNA A RAYE KO SUN MUTU❓😭*


*SU CHIEF ZASU FITA LAMI LAFIYA DAGA GIDAN KURKUKUN ƘADDARA❓*

*INA ELDERS*❓

*DAGA ALƘALAMIN BOSS BATURE🔥🔥🔥✍️*

*Ga me bukatar karanta littafin kurkukun kaddara, 500 ne za'a tura Via Opay, 8103884440 Hafsat Bature Muhammad, shaidar biya za'a tura ta whatsapp, 08169856268 ko 08103884440*

2 Comments

Idan kuna da tambaya akan abinda Baku game ba ko kuma kuma Neman littafin da babu a nan kawai ku ajiye tambayarku a ta comment ko wani shawara da Zaku bamu.

Previous Post Next Post

Sponsored Link

Sponsored Post