After One week (bayan sati ɗaya dakai farmaki Gidan Kurkukun ƙaddara❓
Hankalin Unaisah ba ƙaramin tashi yayi ba, Jin shiru har tsawo sati ɗaya basu dawo ba, lamarin Ya ɗaga hankalin ta ba kadan ba, dauriya kawai takeyi kamar yadda tayi ma su alkawarin zata daina kuka, kuma bazata sanya damuwa aranta ba, sannan ba zata hana idanunta bacci da kuma cin abinci
Abu ɗaya ne bata wasa da shi, Tashi Yin nafilfili takai kukanta gurin Allah, idan dare yayi, biyu take raba lokacin ta, rabi tayi bacci rabi ta tashi tayi nafila, wani sa'in in ta fara tsayuwar daren Har sai kafafunta sun fara raɗaɗi tukunna take dakatawa.
mafi yawan lokutta akan prayer mat bacci ya ke yin awon gaba da ita, Unaisah da Aunty Umminsu sai batool ne kadai sukasan da tafiyarsu kai farmaki sauran yan uwanta babu wanda ya sani abu daya da suka sani shine har yanzu suna shirye shiryen tafiya amma basu tafi ba, kamar yadda Unaisah ta sanar da su, tayi masu hakanne don kada su daga hankulansu yayin da ita kuma hankalin nata ba akwance yake ba, sai dai suna yawan tambayar meyasa Danish baya leƙo su? kuma su an bar su anan ko nan zasu ci gaba da zama ne kuma yaushe ne zasu je kai farmakin, dakyar suke samu su shawo kansu ita da ummi, harta Danejo batasan komai ba dangane da kai farmaki ta dai san zasu je yin wani aiki kamar yadda Taj ya faɗa mata, abunda yafi damunsu babu wanda ya kira su awaya balle su san awani hali suke a ciki....💔
A daren jiya ne ta farka tsakar dare da matsanancin faduwar gaba sakamakon wani mummunan mafarki da tayi, Hankalin ta ya tashi matuka jin yadda tsigar jikinta da zuciyarta ke tashi, gaba daya tarasa samun nutsuwarta saboda tana ji aranta wani mummunan abu ya faru da su, a lokacin idanunta sun makance burin ta kawai ta ganta a part din Chief don taga idan sun dawo ko basu dawo ba, hijab ta zura a jikin ta, batare da sanin kowa ba ta fito daga dakin daddyta dama anan suke kwana ita da Batool bayan tafiyar su.
Ta sauko down ta nufi main door ta falo, ta dinga ƙoƙarin buɗe ƙofar ta kasa saboda security din dake a jiki, batasan menene password din kofar ba, har jaraba sanya numbers tayi sau biyu ana nuna mata wrong code tare da warning message.
zukunnawa tayi bakin kofar tafukan hannayenta toshe da bakinta don kada yan uwanta sujiyo ta, ta fashe da kuka mai tsuma zuciya, sai da ta gama hasala can zuciyarta ta ayyana mata me zai hana ta jaraba sanya kwanan watan da aka haife ta, cos ta sani tuntana karama mahaifinta baida password da ya wuce date of birth inta, cikin hanzari ta miƙe ta danna numbers din fortunately ƙofar ta buɗe batai wata wata ba ta fuce aguje ta nufi part din Chief, ko tsoro bata ji dare ne fa sosai donma akwai hasken Electricity tamkar rana.
Fitarta keda Wuya Batool ta farka sakamakon fitsari daya matseta Bayan ta fito daga toilet din ta dawo dakin Sai lokacin ta lura babu Unaisah, hankalin ta ya tashi tana fitowa ta hango Ƙofar Falon abude kasancewar Unaisah bata datse ƙofar ba, nan take ranta ya bata fita tayi cikin sauri ta nufi kofar harta kusa Isa kwatsam Ta tsinkayi muryar Ummi cikin Kunnanta.
"Babe Ina zuwa" cak ta tsaya da tafiya, Ummi ta nufo ta cike da mamaki take duban kofar falo data gani abuɗe.
"Ina zaki haka da tsakar dare ko mayafi babu akanki? Wanene kuma Ya buɗe kofar nan? Ko wani ya shigo ne?
cikin rawar murya ta fada mata babu Unaisah adaki, Da jin haka Ummi ta ruko hannunta suka bi bayan Unaisah, fitarsu keda wuya kofar falon ta datse silar bangazar da sukai mata..
Suna fitowa suka hango Unaisah tsaye agaban Security officers din gidan ta ruƙe qugu, ashe sun ganta lokacin da take gudu tana kokarin karasawa ga kofar shiga bangaren Chief.
a hanzarce suka kewata suna tambayarta ina zataje da tsakar daren nan? Gaba daya sun fahimci bata acikin hayyacinta sai haki take muryarta na rawa ta furta wurin Chief zataje.
Officers din sukace mata ay basu dawo ba, don haka ta koma inda ta fito, ta fashe da kuka tana fadin ba inda zataje, ita ta gaji da zama cikn fargaba kawai su kaita inda suke.
rigima ta saka masu duk yadda suka kaiga zare mata ido da yi mata tsawa akan ta koma takiya har takaiga wani Soja yai kokarin kai hannu da niyar ya ɗauke ta aikuwa ta gartsa mashi cizo har saida ta fasa mashi fata, ranshi ya 6aci matuƙa harya daga hannu zai kwasa mata mari cikin zafin nama officer din dake a gefen shi Ya damƙi hannunsa da kakkausar murya yace"karka kuskura, In har ba so kake ka rasa aikin ka ba"
Yana huci Ya fusge hannun shi ya juya yabar wurin, lallashin ta suka cigaba dayi don su samu ta koma tace masu in har suna so ta koma su bude mata kofa ta shiga ta dauko wayarta data bari, Officer din yace ta fada masu inda ta ajiye wayar zasu kawo mata zuwa gobe yanzu dare yayi taje ta kwanta, kin fada masu tayi tace itama batasan inda ta ajiye wayar ba sai ta shiga zata duba, kuma a yanzu take son wayar"
Ba yadda suka iya da ita adole suka kira Layin Agent zahra saeed daya daga cikin na hannun Chief amintattunsa, saboda ba wanda zai iya bude kofar idan ba su din ba.
Saboda rigimar Unaisah yana bacci tare da iyalinsa yayi recieving call din su, bayan sun sanar da shi abunda ke faruwa yace su dauke ta su mayar part din, Officern yace mashi yalla6ai ba fa yadda zamuyi da ita, abokin aikinmu da yai gigin ta6a ta cixo ta gartsa mashi har saida ta fasa Fatar shi, yana can yana jinyar kan shi" da jin hakan agent zahra yace"tafi karfin ku ne? wai ma wacece acikin yaran" kallon ta officern yayi meye sunanki" muryarta ashake tace Unaisah..
"Sir sunan ta Unaisah, tana launin ido ruwan toka" da jin hakan okay yace su jira shi.
Adai dai lokacin su ummi suka karaso tayi mamakin ganin Unaisah tsaye gaban Security Officers, Hijab din jikinta ta jike sharkaf da gumi ta hade rai kamar bata ta6a dariya ba, tambayarsu tayi meke faruwa ne, anan officers din suka sanar dasu komai daya faru, batai mamaki ba ta riga tasan halin kayanta in taso abu kamar zawo take bata da uziri ko kaɗan.
Batool ta tausaya mata sosai, ganin yadda ta fita hayyacin ta, jikinta sai kerma yake, rungumota tayi a jikinta, officers din suna ta kallon su kamar zasu hadiye su...
Bayan yan mintu, Sai ga kiran agent zahra ya shigo wayar officer din daya kira shi, bayan yai picking yace suje bakin kofar ya buɗe ta.
Unaisah ta danyi mamaki jin hakan amma da ta tuna kofar tana da security sai taga ai bakomai bane may be yai amfani da computer ne gurin buɗe kofar daga can inda yake.
Suna zuwa bakin kofar ta zuge da kanta, ajiyar zuciya kowannnasu ya sauke kafin suka shiga ciki baiwar Allah idanunta na akan Second floor ta dinga kallon door room dinsa dake a datse, har gizau ya dinga yi mata ta hango shi tsaye ya dafe handrail fuskarsa ɗauke da murmushi, jikinta yayi sanyi lakwas zuciyarta ta karaya, gaba ɗaya ta shagala da kallon shi, har saida ummi tace tayi sauri ta dauki wayar suna jiran ta kafin ta nufi Bedroom dinsu Batool tabi bayanta, ummi tana a falo tana jiran su.
Suna shiga ɗakin suka bazama neman wayarta, Batool tace sis ki yi kokari ki tuna inda kika ajiye ta, muryarta tamkar zata fashe da kuka tace wlh na manta inda na saka ta, har zanin gado suka yaye tare da kakka6e shi duk basu ganta ba, Har closet dinsu suka duba basu ga wayar ba, suka duba under bed nan ma basu gani ba, cikin hanzari Batool ta zazzago da mirror drawer chest tana lalubawa unexpectedly hotuna suka faɗo kan floor, cikin sauri ta dauƙi hotunan ta kura masu ido tana kallon su farat daya ta gano inda ta ta6a ganin Faces din mutanan dake akan pics din, cike da zumudi ta furta kai Ina kika samu hoton mutumin aunty Ummi da kawarta"
Kaitsaye maganar ta daki dodon kunnan Unaisah a lokacin ta gaji da neman wayar har zata zauna gefen gado ta tsinkayi maganar Batool, mikewa Batool tay da sauri ta nufe ta tare da mika mata hotunan tace ina kika same su"? Da ruɗu ta kar6i hotunan ta soma duba su tana kokarin tunano inda ta gan su sai da ta zurfafa tunanin dakyar ta iya tuna ranar da ta gansu a karkashin gado a lokacin tana cikin neman wayarta.
Numfasawa tayi kafin ta furta" ran nan ne nagansu a karkashin gadon mu shine saina boye su a cikin drawer"
"To ay mutumin aunty Ummi ne wannan" ta fada tana nuna mata hotonsa" Ita kuma wannan kin tuna ƙawarta baturiya wadda sukazo airport atare wata fara sol launin idanunta blue"?
Da mamaki Unaisah ta ƙara duba hotunan dakyau tabbas ta gane fuskar baturiyar kawar aunty Ummin su, farko data fara ganin hotunan sai da tay mata kallon sani sai dai bata iya gano a ina ta ta6a ganin ta ba.
"Amma taya akai kikasan Mutumin aunty ummi ne wannan"? Ta jefa mata tambayar..
"Zan faɗa maki, amma dan Allah kada ki fada ma aunty Ummi, saboda ta ta6a buga min warning, akan kar in daukar mata waya in an kira..." Unaisah tace taji ba zata fada ma Aunty ummin ba..
Nan Batool ta labarta mata ranar da ya kira video call tayi picking, abun daya ɗaure ma Unaisah kai ta yadda har Batool ta iya ruƙe fuskarshi a karo na farko data fara ganin shi a video call.
"Kin tabbata shine"?
"Wlh shine, watakil kuma mai kama da shi ne, amma gaskiya kamanninsu ya 6aci sosai.."
lamarin ya ɗaure mata kai taya akai hoton kawar aunty ummi da saurayinta yazo dakinsu? Ta jefa ma kanta tambayar da bata da amsarta, Ta dai san aunty ummi baza ta yi gangancin kawo hoton saurayinta adakin su ba tunda har ta gargadin Batool akan daukar mata waya thats mean bataso asan komai dangane da abun da ya shafi phone dinta.
Kafin wani ya ƙara furta kalma daga cikinsu suka jiyo muryar Ummi daga waje tana fadin Wai har yanzu baku ga wayar ba ne.
Cikin sauri Unaisah tace ma Batool kada ki fada mata komai dangane da hotunan, nima bazan faɗa mata ba, inaji araina hotunan nan akwai wani abu atattare da su, zanyi kokari insan daga inda suke"
kafin Ummi ta shigo ɗakin su ka yi hanzarin mayar da kayan cikin drawer din, hotunan ma cen cikin wasu notebook dinta dake qasan drawer din ta boyesu.
Adaren ranar basu koma part din daddynta ba, bayan da taga wayar officers suka ce su fito su koma part din daddynta, aikuwa ta sanya masu rigima akan bazata koma ba anan takeson kwana, ganin dare ya nutsa sosai yasa suka kyale ta, taso ta kwana adakin Danish sai dai takasa bude room door dinsa saboda an kulle kuma bata san code din kofar ba, adole ta hakura suka kwana adakinsu ita da Batool, Ummi kuma ta kwana adakinta.
Morning🌄
Zaune suke su Uku akan dining Chairs, sun tasa Abincin breakfast din da aka jere masu kan table agaba sai dai sun kasa ci, saboda rashin kwanciyar hankali tun kayan baccin jiya ne a jikin su babu wanda Ya cire nashi.
"Unaisah, ku ci abinci mana" ummi ce ta faɗa tana kallon su, kamar wadanda sukayi amai da gudawa duk sun faɗa, sai uban kasusuwan wuya..
In a cool voice Unaisah tace "Aunty Ummi, wlh abincin ma bayayi min dadi, turawa kawai nake yi.."
Batool tace"kamar kin shiga zuciyana wlh nima dai babu dadi..." shiru ummi tayi cike da damuwa take kallon su to ita ma dindai ba dadin abincin take ji ba, turawa kawai takeyi..
"Yau tsawon sati guda Aunty Ummi, babu labarinsu, kullum da zullumi muke kwana, tunanin mu meya faru da su? Sunyi nasara ko kuwa? Tayaya zamu sani Aunty Ummi? Ko awaya babu wanda Ya tuntu6e mu...." dakyar ta ƙare maganar saboda kukan dake kokarin 6alle mata, dakyar ta haɗiye shi.
"Jiya har mafarkin Danish nayi, da daddyna, Amma mafarkin baiyi min daɗi ba, shiyasa ban ma baku labari ba..." ta faɗa arauna ce, dafa kafadarta Ummi tayi"mu kara hakuri Unaisah, tun da bamusan meya tsayar da su ba, amma wani jinkirin Alkhairi ne In sha Allah zasu dawo cikin koshi lafiya..." yamutsa fuska tayi batare data furta kalma ba,
Wayar Ummi ce tayi Ringing daga cikin aljihun wandonta, zaro wayar tayi tare da duba sunan me kiranta, kamar mara gaskiya ta dago suka hada ido da su Unaisah har suna hada baki gurin furta"Daddy ne"?
Girgiza kai tay"ba shi bane, Friend dina ne" kafin tay picking call din ya katse mayar da wayar tayi cikin aljihu kafin ta maida dubanta gare su.
A fakaice Unaisah ta kalli Batool suka hada ido batare da ta lura ba, gaba ɗaya sun fahimci bata son yin waya agabansu in har ba daddyn Unaisah ne ya kira ba ko big guy.
"Guys yanzu dai mu daure mu ci ko rabin abincin ne kada ay almubazzaranci"..." matsa masu tayi dakyar ta samu Suka ci kaɗan.
mikewa Unaisah tayi daga kan dining din ta nufi dakin su.
Bayan tafiyarta Batool ta dubi aunty Ummi"yaushe zamu koma part din daddy, kada suji mu shiru"
Ummi tace"nima abun da nake tunani kenan, Bari na kira Danejo awaya in fada mata don ta kwantar masu da hankali" ta fada tare da zaro waya ta danna ma Danejo kira.
zama tayi gefen gadon Su hannunta ruke da iphone dinta data dauko, messages ta shiga ta buɗo Sakonnin daya ta6a tura mata, nutsuwa tayi tana karanta su fuskarta ɗauke da murmushi, bayan ta gama karanta sakonnin ta shiga gallery ta bude hotunan da ta ta6a yi mashi batare da sanin shi ba, yayi mata kyau a pics din har wani lumshe idanu takeyi idan tana kallon su, ta kosa ya dawo ko dan ta cika mashi burin shi, idan ta tuna alkawarin daddynta dayace in har ta bi umarninsa zai bari ta auri zabin ranta sai taji wani dadi ya lullu6e zuciyarta, fatanta Allah yasa suyi nasarar ruguza kurkukun kaddara su dawo cikin koshin lafiya.
Kira ne Ya shigo wayarta, murmushi ta dan saki ganin sunan mommyna ya bayyana akan screen din wayar, picking call ɗin tayi tare da kara wayar a kunnanta..
"Haba my baby, kin daga min hankali kullum saina kira bana samun ki, Almost a week?! Meke damun ki ne? sautin muryarta da damuwa ta tambaya.
"I'm sorry mommy, school ne ya boye ni, bayan haka wayar ma ta samu matsala sai jiya aka gyara min ita"
On the other hand, Benazir kiris Ya raga ta sanya dariya, ta rasa gane meyasa Unaisah take son yi mata karya, bayan ba halin ta bane, since last week ta riga da ta gane itace Unaisah yarinyar da ta kira wrong number tay mata karyar a kano suke yanzu kuma tace tana school bayan a labarin da Aneelerh ta bata Unaisah bata zuwa School.
basarwa tayi tare da cewa"Okay, kada ki damu, nima bazanso na takura maki ba, am babyna Ina daddynki ne? Almost a week bana ganin shi a online.." su6ul da baka tay What's your connection with him?"
yar dariya benazir tayi"son shi nakeyi, tun ranar dana fara yin tozali da shi, don ma yaƙi kulani ay da tuni mun yi maki ƙani..." waro idanu Unaisah tayi can kuma tadan saki dariya, har cikin ranta taji dadin maganar Benazir don kuwa time da ta fara ganin ta saida tayi ma daddynta sha'awar auranta, tadaiyi shiru ne saboda tana kokwanton ko tana da aure bayan haka bata son yayi ma Danejo kishiya ga kuma aunty Aneelerh da take burin ya aura saboda kaninta junaid ya samu Uba nagari.
tayi zurfi a tunaninta muryar Benazir ta katse ta"kinyi shiru babyna, kin san nima na rasa mijina da yata, ina maraicinsu, Aneelerh ta fadamin baya tare da mommynki, shiyasa nakeso nazo na maye gurbinta, ko bakya son in auri daddynki"
murmushin yaƙe tayi kamar tana agabanta tace"inaso, amma bata faɗa maki yana da au..." bata ƙare maganar ba, sakamakon dirar motocin data jiyo acikin kunnanta, rejecting call ɗin tayi tare da jefar da wayar Kan gado, ta fito da gudu ko Mayafi bata ɗauka ba ta nufi hanyar fita daga falon jikinta sai kerma yake tsabar zumuɗi, kafin ta ƙarasa Ummi da Batool suka bi bayanta da ɗan gudun su.
At same time motocin su ka yi parking, a gaggauce Officers dake tsaron gidan suka Yi masu kawanya tare da yin hanzarin buɗe cardoors, Adai dai lokacin Unaisah ta zuro kofarta waje wani burki Taci idanunta azare take Kallon motocin Cike da fargaban wa zata fari gani.
CO ne Ya fara fitowa cikin hanzari ya zagaya bayan motarsu ya buɗe boot ya cure folding wheelChair ya ajiye ta kasa ya fara kwancewa sai da ya daidaita wheelchair din kafin Ya furta"zaku iya fitowa da shi"
Wani irin faduwar gaba taji gaba daya tabi ta rude jin ya furta za'a iya fitowa da shi ko wanene? sai faman rarraba idanu takeyi akan motocin, lokacin da idanunta su kayi mata tozali da mutumin da SA suka rurruko daga backseat na ɗaya daga cikin motocin, jikin shi sanye da patient uniform blue yar riga ce mai tsayi, Cinyar kafarsa ɗaya gaba dayanta a nannaɗe take da bandage daga gani aiki akayi masa a tsakiyar cinyarsa, A hankali suka zaunan dashi kan wheelChair din sai nishi yake yana fitar da numfashi mai huci daga gani babu lafiya atattare da shi.
Cike da tashin hankali ta zare idanunta, la66anta na kerma ta furta"inna lillahi wa'inna Ilaihirraji'in! Daddy"! Da karfi ta furta sunan shi, bawan Allah a firgice Ya dubi inda take har rama yayi saboda azabar ciwo, suma Jami'an suka maida hankali akan ta..
watsawa tayi da gudu tana karasawa gaban shi a slow ta zube kan gwiwowinta, ta fashe da matsanancin Kuka tamkar ranta zai fita Cikin shesshekar kuka ta furta nashiga ukuna! daddy Meya faru dakai? Meya faru da kafarka?
tsantsar tausayinta ne Ya kama shi, Ummi da Batool sun kasa motsawa saboda tashin hankalin da idanunsu suka gane masu, daya bayan daya sauran dake acikin motocin suke fitowa, Chief owais ne jikin shi sanye da Singlet fara sai short, gaba ɗaya goshinshi bandage ne, fuskokin su duk sun 6aci da tabonnin raunukan da suka ji, Wa'iya zubilla, dafe kirji ummi tayi cike da tashin hankali ta furta"inna lillahi wa'inna ilaihirraji'un! Batool kuwa Fashewa tayi da kuka tamkar ranta zai fita musamman data lura babu Danish a cikin su, daga cikin sauran da suka fito daga cikin motocin U.s armies din da suka rage ne su Biyar, babu cikon ɗayansu, sai wasu daga cikin na hannun daman Chief wadanda ba'aje Kai farmakin da su ba.
Akace labarin zuciya atambayi fuska, tunkafin suyi masu bayani suka karanci komai daga yanayin su, Dakyar Taj yai karfin halin janyo Unaisah Ya rungumeta akan kirjin shi, tare da shafa sumar kanta yana faman sauke ajiyar zuciya, har cikin ranshi yaji dadi da Allah yasa ya rayu ashe da rabon zai sake ganawa da yarsa? sai dai abu daya da yake ma fargaba.
hannun Ummi ruke dana Batool suka karaso Gurin su Chief, Fuskokinsu sharkaf da hawaye Murya Na rawa Batool ta furta"Ina Danish din mu"? Shiru sukayi don basu shirya komawa asibiti da wanin su ba.."dan Allah ku faɗa min Ina danish? Meyasa bangan shi ba..." cikin shesshekar kuka tayi maganar, Sunyi shiru suna kallon ta, Chief ma Hankalinsa baya akan su, saboda matsananciyar damuwar data mamaye zuciyarsa.
Unaisah data kwantar da kanta a kirjin daddynta, Hankalinta Idan yai dubu toh ya tashi, tin da taji muryar Batool tana tambayar Danish ta fahimci babu shi su ka dawo! Babu!!babu!! Hasbunallahu wa'ni imal wakeel, acikin zuciyarta ta dinga maimaita duk wata addu'a datazo cikin bakin ta.
Ummi kuwa Jikinta yagama mutuwa Cikin sanyin murya ta wanda Ya kara tayi masu Chief barka da dawowa da tambayar ya jikin su, fuskokin su kwata kwata babu walwala suka amsa mata, Kafin Commender james ya nemi su shiga ciki saboda majinyatan jikinsu da suka jigata, dakyar Chief yake Tafiya saboda rashin kuzari, bawan Allah shi kadai yasan me yake ji a cikin zuciyarshi bazai ta6a mantawa da Danish ba Har abada ya kafa tarihi acikin zuciyar shi, gaba daya abun da suke jima fargaba yadda yan uwan shi zasu kar6i abunda zasu fada masu saboda su sunsan irin kaunar da suke ma Junansu komai zai iya faruwa idan suka ji cewa Danish ya mutu.
"Commender pls, meya faru ne? Hankalina Ya tashi, Ina son nasan Ina Danish ne? Ina Omar? Ina Major"? Suna Ina"?
Girgiza kai commender yayi cikin rauni murya da harshensa na turanci ya furta"Ummi, muje ciki zamuyi maku bayani"
yana fadan hakan yabi bayan Su Chief suka nufi ciki.
mutun uku ya rage a harabar, gaba daya suka zukunna Agaban Taj, Cikin rauni na murya Unaisah ta furta"daddy, Ina Danish"?cike da fargaban amsar da zai bata tayi maganar, tare da dago kanta daga kirjinshi, fuskarta ta 6aci da hawayenta, gwanin ban tausayi ya ke kallon ta.
"Dan Allah Daddy Ka fada mana, Ina Dan uwanmu Danish"? batool ce ta fada still bata daina kukan ba...
Ummi ma tace"tun da kuka tafi, Hankalinmu ba akwance yake ba, saboda zullumi da fargaban awani hali kuke ci, gashi kun dawo ba yadda muka zata ba, babu wasu daga cikin ku, sannan ku kanku araunace kuke, that means something bad happened."?
Ta fada idanunta cike tab da kwalla, yayi shiru yana binsu da kallo...
"Daddy, pls ka fada min, yana raye koya mutu, kada kace zaka boyemin, saboda duk mun daren dadewa dole naji, kwara ka fadamin ayanzu inyi jinyar zuciyata idan ina da rabon cigaba da rayuwa, ay ma nayi imani da kaddara, in ma ya mutun Zanyi hakuri in rungumi ƙaddara..."
wani kallo Taj yayi mata bakomai yake tunawa ba face abubuwan da suka faru kafin tafiyarsu irin haukan da tadinga yi na zai raba ta shi, shine yanzu take kokarin yi mashi burga salon Ya fada mata Ya rasata na har abada.
ganin kallon da ya ke yi mata yasa ta kama in-ina hawaye na cigaba da tsastsafowa kan fuskarta tace"wlh daddy bazan damu ba, ka fadamin kawai.." tana kuka tana dariya tayi maganar kamar zautacciya.
hmmm baiwar Allah bashi ba, hatta ummi ta karaya da ganin yanayinta, kodan saboda Unaisah zataso ace Danish Yana raye.
Da ido tayi mata Taj alamar karya kuskura ya fada mata, don ita tasan me ta gani wlh, Shafa fuskarta yayi da tafukansa Ya kakalo murmushi kan fuskarshi"meye naga kun wani daga hankulanku"?
"Daddy taya hankalinmu bazai tashi ba, kun dawo gaba dayanku ba lafiya, kuma babu Danish da ya Omar"
jinjina kanshi yayi"hakane daugher, amma inaso ki sani dan uwanku yana nan cikin koshin lafiya.."
ba dan sun yarda da maganar ba, Tace"yana ina"? kafin ya bata amsa Ummi ta katse su da cewa"Haba Unaisah, dudufa Yanzu suka dawo, baki ga halin da yake a ciki ba, ki bari Ya shiga Ciki Ya huta mana, inyaso sai muji komai daga bakinsu," dakyar Ummi ta lallashe su suka hakura da yi mashi tambayoyin.
Unaisah da Batool ne suka gungura Wheelchair din Taj ganin ya raunata sunsan ba lallai ya iya gungura kan shi ba, suka nufi main falo din ummi na abiye da bayan su, anan suka iske su commender zazzaune kan Sofas, gaba dayansune da suka shigo, a tsakiyar sofas din Su batool suka dakata da gungura shi, kan floor suka zauna kamar masu zaman makoki, ummin ma ta zauna gefen su.
saida suka huta nutsuwa ta shige su sosai, kafin chefs din gidan suka shiga jera masu Abinci, kamar sarki haka suka dinga lallashin chief donyaci abinci yace masu bazai iya ba, ko yaci bazai ji dadin shi ba, subar shi kawai shi kadai yasan halin da yake aciki, cikin kwantar da murya commender yace"in har bakaci abincin ba, taya zaka samu karfi ajikinka balle harka Iya Karasa aikin ka"!
"What you need now is peace of mind because your brain needs rest to function, Chief worry won't solve anything, it will just lead to loss and regret, just Forget about every bad thing that happened in the prison of destiny, Strengthen your heart and face what lies ahead, that's how you'll achieve success ka fuskanci abunda kasa agaba, ta hakane zaka cimma nasara..." kalamai masu karfafa zuciya Commender james Yaci gaba da furta mashi sauran na hannun damanshi duk suka saka baki gurin kwantar masa da hankali har saida suka samu Ya ɗan lafa, cikin sanyin murya ya furta"nagode da shawarwarinku, in sha Allah zanyi abunda kuka ce, amma Yanzu nafi bukatar wanka, zan shiga ciki, idan na fito zanci abincin.."
yana faɗan hakan Ya miƙe cike da rashin kuzari Ya nufi part dinsa.
Yana shiga Ya faɗa kan gado Idanunsa na fuskartar ceilling, komai daya faru a gurin Yaƙin Ya fara tariyowa Hannunsa daya dafe da saitin Zuciyarshi, Yafi jin Danish Fiye da kowa sai kuma amininsa Omar wanda a halin yanzu yana agadon asibiti rai hannun Allah As a result of his brain injury, ya shiga coma ba lallai ma ya dawo da cikakkiyar lafiyarsa ba, a bayanin da docs su ka yi ma shi kenan.
abu na biyu da ya kwallafa rai akai Shine Elders, Alwashi ne ya daukarwa kanshi Elders ba zasu kai karshen watan nan ba batare daya gano su ba, abun da Yafi tada mashi hankali tsohuwa Khala matar ta tsaya mashi aranshi! Kalmar data fara furta mashi "owais kaine ka girma haka"? Meyasa yake jin kamar ya san muryarta? Meya faru da ita? Hakika tsohuwa Khala tayi masu kokari, ba wai iya makamai ta taimaka masu da shi ba, ta taimaki fursinonin da suka ku6utar, shi Kanshi ya jinjinama jarumtakarsu Ita da Danish sun cancani a yaba masu, don shi ji yake da ace Danish yana raye ba abun da zai hana Ya sauke mukamin shi na director general Ya damƙa mashi saboda ya cancan ta.
A hankali siraran hawaye suka wanke fuskar shi ya ɗan numfasa tare da lumshe idanun shi yana jin wani irin yanayi mara dadi a tattare da shi
aranar da suka kwana a sansani kasancewar a masauki daya suka zauna kafin suyi bacci sun dan ta6a fira da shi har ya dan bugun cikin shi yace ya fada mashi meke a tsakanin shi da Unaisah kar yai tsammanin yana sanya masu ido ne, kawai Ya lura da yadda suke kaunar junansu, a lokacin har saida yai murmushi kafin yace ma shi ya dauka Unaisah bugun zuciyar shi ce, yana tunanin mutun zai iya rayuwa batare da zuciyarshi tana bugawa ba? Dariya chief yai ya girgiza kai yace a'a bama zai ta6a yiwuwa ba, yace mashi toh haka Yake jin Unaisah, a lokacin Chief ya sake tambayarsa ya fada masa wani buri yake so ya cika masa idan suka dawo bayan sunyi nasara, ya danyi jim kamar yana nazari kafin yace baya bukatar komai, kawai shi abunda yake so yai masa alkawarin koda bai rayu ba idan sukaje kai farmakin Ya ruke Unaisah da mahaifinta da sauran Yan uwan shi yabar mashi amanar su ita kadaice alfarmar da zai nema agurinsa.
Bayan ya dawo daga duniyar tunanin daya lula A hankali ya Kife kanshi jikin pillow, fuskarsa ta 6aci da hawayensa..
_______________________________✍️
"Dan Allah ku faɗa mana ina dan uwanmu Danish meya faru daku"? Batool ce ta kuma tambaya...
Cikin sanyin murya Commender Haroon yace"ku kwantar da hankalin ku, Danish bai mutu ba, saboda bamu shaida mutuwarsa ba"
A takaice Ya labarta masu abunda Ya faru a ranar da suka kai farmakin bai boye masu komai ba"
Canal herry yace"munyi babban rashin na har abada ba zamu ta6a warkewa daga radadin da muka ji ba na rashin Danish, zai yi wuya asamu jarumi irin shi a duniyar nan" Ya fada tare da saddar da kan shi ƙasa.
mikewa Unaisah tayi kamar bata acikin hayyacinta kafafunta sai kerma sukeyi ruko hannun ta Taj Yayi"My angel, zauna muyi magana, bafa mutuwa yayi ba, ni nasan zai dawo ne da kanshi In ma bai dawo ba zamu koma ne"
gaba daya hankalinsu Commender na akanta, ta runtse idanunta sosai, jikinta kakarwa yakeyi kamar wadda sanyi ya kama, dakyar ta furta"daddy, Danish Yana acikin rijiya ta gidan kurkukun kaddara tare da evil giant me hadarin gaske? ku ka tafo ku ka baro shi!, sannan Elders basu mutu ba sun yi nasara kenan? ta faɗa tare da dafe goshinta tana huci tace"shiyasa nace ku tafi dani, ni dama saida raina ya bani wani mummunan abu ya faru ashe mafarkin da nayi gaskiya ne"
"Unaisah, Ki fahimta bamu da yadda zamuyi ne, Allah ya riga daya kaddara faruwar hakan, bamu isa mu canza mashi kaddarar shi ba, yakamata ki godema Allah Unaisah baki yi farin ciki ba? Saboda sadaukarwar da Danish yayi Mun ceto rayukan Yan uwanku dake a kurkukun kaddara yanzu haka suna a asibiti a karkashin kulawar likitoci, bayan haka mun ku6uta da ranmu da ba don shi ba da tuni mu kanmu mun rasa rayukanmu"
Bata jira karashen zancen shi ba, ta zame hannunta daga Nashi Cikin sauri ta nufi dakinsu ta shiga ta fada toilet, ta kunna shower da faucet don kada sauti Ya fita, da hannu biyu ta daddafe kanta dake sara mata, Ta daddaga ta fashe da wani irin kuka mai cin rai kamar ranta zai fita, ihu tadinga Yi tana hauka hauka gaba daya shatun jijiyoyin goshinta Ya fito rudu rudu kan fatarta, hatta wuyanta shatun jijiyoyinne, wani irin mahaukacin zafi temperature din jikinta Ya dauka, Idanunta suka kaɗa jawur kamar garwashin wuta, kamar ana rura wuta Cikin zuciyarta saboda bala'en radadin da takeyi mata, sau uku tana buga kanta Jikin sink, har saida fatar goshinta ta faffashe jini ya wanke kyakkyawar fuskarta, nan take Hancin ta ya fara bleeding, lokaci daya tafara jin wani irin azababben ciwon kai mai azabar radadi, juwace ta kwasheta gaba daya ta yanke jiki ta faɗa kan floor, wani irin duhune Ya mamaye ganinta, Ji take kamar ta tsaga kirjinta ta ciro zuciyarta ta jefar saboda tafarfasar da ta ke yi.
Maganganunshi ne suka fara dawo mata acikin kanta ..
_"Angel, baki damu dana mutu ba? Ina kaunar da kike mini? Kin za6i da naje na bada raina"?_
_"Abu ɗaya da nakeso Kiyi min alƙawari shine, Ko bayan tafiyana kada kiyi kukan rashina, kada kiki cin abinci, ko ki hana idonki bacci saboda ni, sannan koda ban dawo ba, kiyi hakurin Jure rayuwa batare dani ba..."_
"Meyasa zaka yi min haka? Ta fada acikin ranta
"Don nace ka bada ranka ba ina nufin ka mutu ba, taya kake tunanin zan iya rayuwa batare dakai ba? Na rasa farin cikin rayuwata, me rage min? ya Allah Ka dauki raina in huta"
Lokaci ɗaya ta fara tariyo farkon haduwarsu agidan kurukukun kaddara, at sight da sukayi tozali da juna sai da ta razana da ganin kyawun shi...In har Danish bai dawo ba, to kuwa tabbas zata dawwama da bakin ciki arayuwarta.....💔
Tana jiyo sautin bugun kofar da suke yi mata, sama sama muryoyinsu ke yi mata yawo akai Unaisah ki bude kofa, pls ki bude, wai baki ji Ina magana! Ba zaki bude ba"?
ko yatsanta bata iya dagawa, saboda halin da ta shiga...
Lokaci ɗaya ta fara jin matsanancin ciwon kirji, hudojin fatar jikinta suka fara fitar da gumi ta ko'ina zuface Ke tsatsafo mata kamar an yayyafa mata ruwa, numfashinta yayi karanci dakyar take Jan shi bata kara sanin inda kanta yake ba💔
*Bayan Wani Lokaci*
*OIH*
Da matsakaicin Gudu Motar su ta shigo asibitin tunkafin suyi parking, Nurses suka fito a gaggauce hannayensu ruke da Stretcher agaban motar suka aje, Jikinshi na rawa ya fito daga backseat na motar, Ya zura hannu Ya dauko Unaisah dake a rungume Jikin Ummi, kwata kwata babu Numfashi a jikinta, Batool sai kuka takeyi kamar ranta zai fita, da kanshi Ya kwantar da ita kan Stretcher din, Nurses suka gungura ta zuwa Emergency ward yayin da Su ummi ke abiye da bayan su.
A waiting Area Ummi da batool suka tsaya Suna jiran tsammani, Chief yana a zaune kan seat Ya dafe forehead dinsa da tafin hannunsa, idanunsa sun kaɗa jajur saboda tashin hankalin da yake fuskanta.
Bayan yan mintuna, Motar Us armies da ta Senior agents ta karaso asibitin, visitor din dake kai komo a harabar asibitin sai kallonsu sukeyi, gaba daya suka fito daga Cikin Motocin hada Taj wanda gaba daya fuskarsa ta jike da hawaye kamar karamin yaro yayi kuka sosai, ga shi ba koshin lafiya gare shi ba, dama ko sallamar shi ba ay ba Ya matsa lamba akan a sallame shi saboda yar shi, dakyar ya samu Chief ya sanya hannu suka sallame shi acan inda aka kwantar da su a (Combat support hospital)
gaba dayansu babu wani mai kwanciyar Hankali, Sun rasa ina zasu sa ransu suji dadi a duniyar nan, Na hannun daman Chief suka kewaya batool da Ummi suka fara lallashinsu da kwantar masu da Hankali, Shima Taj haka suka dinga tausarshi yana azaune kan wheelchair dinsa ya sadda kan shi kasa, Kasa jurewa yayi a karshe ya gungura kujerarsa Ya koma bakin Kofar dakin da aka kwantar da ita, Kasancewar Kofar ta glass ce yana iya hangen Docs din da suka kewaye gadon ta, sun dage damtse suna ta kokarin ceto rayuwarta, leken ta ya dinga yi tana a kwance kan medical bed Sai jan numfashi take duk da sun sanya mata Oxygen mask akan fuskarta.
Addu'o'i Ya dinga yi mata acikin zuciyarsa akan Allah ya bata lafiya..💔
Wunin ranar suna asibiti Har lokacin likitoci suna aiki akanta, Kafin marece docs din suka kammala bincike sakamakon ya nuna tana fama da severe depression and Heartbreak Syndrome, She's in a critical situation, dealing with two major issues simultaneously, docs din ma sunce in har ba'ay kokarin shawo kanta ba, Zuciyarta zata bugawa ne, amma zasuyi iyakar bakin kokarinsu don ganin ta samu lafiya.
Hankalin su Ya tashi matuƙa sun shiga matsananciyar damuwar abunda ke damun Unaisah, duk wannan abun dake faruwa Danejo da sauran Yan uwansu dake agida basu sani ba.
(Get well Soon Unaisah Angel)
*DAGA ALƘALAMIN BOSS BATURE🔥🔥🔥✍️*
*Ga me bukatar karanta littafin kurkukun kaddara, 500 ne za'a tura Via Opay, 8103884440 Hafsat Bature Muhammad, shaidar biya za'a tura ta whatsapp, 08169856268 ko 08103884440*