Kurkukun Ƙaddara Takun Ƙarshe page 59 Complete by Boss Bature


Health College

Kurkukun Ƙaddara Takun Ƙarshe page 59 Complete by Boss Bature

Takun Ƙarshe

Gajiya tafari yi da tsayuwa charging kwata kwata baya sauri, zama tayi gefen gadon su ta dan fara gyangyadi kafin wani lokaci bacci yai awon gaba da ita.

A hankali ya ke saukowa down ya zuba hannayensa Cikin aljihun wondon baccin sa, sam ya kasa runtsawa saboda tunanin a wani hali Unaisah take a ciki? Ta yi bacci ko idonta biyu? Ya damu sosai akan ciwonta, direct ya nufi bedroom dinsu Yana gab da zai shiga ya jiyo shesshekan kukan ta kasa kasa.

Almost 3 times yana kwaɗa sallama shiru tare da knocking door din, ba'a amsa mashi ba Har zai juya sai kuma ya kasa jurewa saboda baya son damuwarta ga kuma kukan da ya ji ta na yi.

A hankali ya tura kofar ɗakin Ya shiga da sallama abakin shi, babu wadataccen haske a dakin sai na bedside lamp da suka bari a kunne, Batool ya hango a kwance kan gadonsu tana ta sharar baccin ta ita kadai abun ta.

Wurga eye balls dinsa yai saitin inda yake jiyo shesshekar kukanta, wani irin sanyi yaji ya ratsa zuciyarshi ganinta a cikin prayer corner tana a zaune kan prayer mat, jikinta sanye da dogon hijabi, hannunta ruke da prayer beads tana lazami, yayin da idanunta ke akan qur'anic stand din data buɗe.

tabbas tajiyo kamshin turaren Chief sai dai bata kawo aranta cewa shine ba kuma kwata kwata ba ta ji motsin shigowar mutum ba saboda tayi nisa a cikin ibadarta.

Unaisah ta yi Namijin kokari ba lafiya gare ta ba, amma saboda ta nema masa rahama gurin Allah yasa ta hana idonta bacci ta tsaya tsayin daka don ganin tayi masa addu'a dama alkawari ta daukar masa zata raba daren ta biyu rabi ta yi bacci rabi ta yi addu'a, samun masoyi mai sonka tsakani da Allah da zai iya yi maka addu'a batare da sanin ka ba zaiyi wuya a duniyar nan.

Hakika ta burge shi sosai, Har ya zagayo ta gabanta bata lura da shi ba, saboda ta ɗan lumshe idanunta, dogayen eye lashes din ta sun jiƙu da ruwan hawayenta.

Kyakkyawar fuskarta ta 6aci da hawayen ta, ɗaga hannayenta tayi sama Cikin harshen larabci ta fara karanta addu'o'i duk akan Danish dinta.

Lumshe idanun shi yai a hankali ya sake bude su kan fuskarta, ya jinjinama irin kaunar da take ma Danish yayi fatan ace shi ya samu soyayyarta, saboda samun mace tagari irin ta zaiyi wuya a fadin duniyar nan, yarinyar da zata iya tashi in the middle of the Night tayi nafilfili don ta yi maka addu'a Omg😘 



A hankali Ya zukunna ta gefen ta, Ya zuba mata lumsassun idanun shi masu ɗauke da bacci.



Bakomai yake kallo ba fa ce eye lashes dinta da soft lips dinta dake kerma sun jiku da hawayen ta sometime har tongue take zurowa ta lashe su baisan ya akai ya tsinci kan shi da kallon ta ba.


A hankali ya mayar da eye balls dinsa kan kwantaccen gashin forehead dinta dark brown ya nannade gwanin ban sha'awa kai komai nata abun ban sha'awa ne.



Kasa yi mata magana yai cos yai tunanin she may feel uncomfortable if she sees him in front of her.


Slowly ya miƙe tare da juyawa ya nufi hanyar fucewa daga dakin

Kamar daga sama yajiyo muryarta a cikin kunnan shi"Wanene" dan dakatawa yai ba tare da ya juya ba, Zumbur ta mike gabanta na faduwa cos tajiyo motsin tafiyar shi.


waro idanu waje tay lokacin da tay arba da faffadan bayan shi, wlh sai taga kamar Danish ne yanayin tsayuwarsa banbancin Danish yafi sa tsayi da kuma doguwar sumar kai, uwa uba launin fatarsu ba daya ba.



"Wanene"? Ta ƙara faɗa cike da fargaba, gudun kada ya tsoratar da ita yasa shi juyowa a hankali suka fuskanci juna tana ganin chief tay saurin share hawayen ta saboda ya hanata kuka, tayi mamakin ganinsa a wannan lokacin  a cikin dakinsu, arude ta furta"barka da dare" ya fahimci rudani dake akan fuskarta hakan yasa shi cewa"I'm sorry na shigo dakin ku batare da izninku ba, na fito ina zagayawane najiyo shesshekar kukanki, Hankali ya tashi sau uku ina yin sallama ba'a amsa min ba, har knocking nayi shiru shiyasa na yanke shawarar shigowa ciki amma ba halina bane"



Cikin sanyin murya ta furta"na fahimce ka, kuma nagode da kulawarka agare ni, ka damu dani sosai"


Sam taki bari su hada ido tun kallon farko da tay mashi ta kawar da idanun ta.


"Kin manta sharaddun da dr ya gindaya maki? I thought I would find you sleeping, although you are doing good thing, but you should continue resting until you've fully recovered, ban hana ki masa addu'a ba, zaki iya yi masa addu'a aduk lokacin da kikai sallah, amma yanzu dare ne Unaisah"


with respect ta amsa mashi da toh.


Shiru suka ɗanyi na wani lokaci, takun tafiyarsa taji da sauri ta dago matsowa yai dab da ita..


Ta sadda kanta kasa tana dan jin faduwar gaba.


In a cool voice yace"a ranar da mu ka kwana a sansanin mu, Danish ya nemi in yi masa alkawarin ko bayan ransa In kula da rayuwarki data mahaifinki da yan uwanki, and I vowed to fulfill his request"


 jin wannan maganar yasata kusa fashewa da kuka jikinta ya kama kerma.


"Ban fada maki don in fama maki raunin dake a cikin zuciyarki ba, sai don inaso ki taimakamin Unaisah,  Ki bani hadinkai gurin ganin na cika masa alkawarinsa, in har kika bani dama duk da ina shiga busy saboda aiki zan yi kokarin ware mana lokacin da zamu dinga ganawa da juna, in sha Allah I'll support you in overcoming the pain that's troubling you."


 dakyar ya ƙare maganin ganin yadda hawaye ke yar tseral kan kuncinta aranta ta ayyana wata irin kauna Danish yakeyi mata? Ya Ilahi, Shi damuwar shi wanda zai kula da rayuwarsu in baya nan wayyo Allah hakika tayi babban rashi arayuwar ta.


batai aune ba taji safkar yatsun chief kan fuskarta gently ya soma share mata hawayen ta.



Muryarsa tamkar ta me yin raɗa ya furta"If you give me a chance, I will replace him, despite knowing I may never fully replace him in your heart" ya ɗan dakata yana mayar da numfashi, ta nutsu tana sauraron shi.


"Na riga shi sanin ki amma ya riga ni haduwa dake, nasan da ace tun lokacin na bayyana kaina agurinki da nima na samu gurbi acikin zuciyarki, sai dai kash na makaro amma har yanzu ina da sauran dama Unaisah, nasan kun shaku da juna ke da shi, kun sha wahala a tare, kun yi rayuwa a guri ɗaya, kun san sirrin juna, nikuma bansan komai dangane dake ba, amma idan kika bani dama nayi maki alkawarin zan canza maki rayuwarki...." 


da wata irin siga ta jan hankali yai mata maganar, har saida taji wani irin yanayi atare da ita, kalamansa sun ta6a zuciyarta.


Ɗagowar da zatay keda wuya karan hancinsu ya gogi na juna razanar da ta ɗanyi ne yasa ta ɗaga ƙafa zatay baya aikuwa gaba daya ta tafi zata kife kasa saboda rashin kwarin jikinta.


Cikin zafin nama yai hanzarin damko waist dinta Ya janyota gaba daya ta fada kan broad chest din shi, wani irin faduwar gaba taji, She could feel his heart beating rapidly, lumshe idanunta ta danyi sam ta kasa motsawa daga jikin shi, ta rasa gane me take ji? Amma tabbas taji wani irin sanyi da kwanciya hankali yana ratsa zuciyarta.


har ga Allah bai janyota da wata manufa ba, gudun kada ta fadi yasa shi rukota sai kuma abun ya nemi ya jefasa a wani yanayi mara misaltuwa, nutsuwa yai yana kallon fuskarta tay lamo a jikin shi kamar jinjira.


Damuwar rashin Danish ta fara affecting brain din ta, komai ya faru Danish take gani a yanzu haka ji take kamar a jikin Danish ta faɗa shiyasa ta kara narke masa.


abunka ga mabukacin dake bukatar duk wani abu da zai sanyaya mashi zuciya.


"Unaisah" shiru bata amsa mashi ba.


"are you sleepy? Ya tambaya yana leken fuskarsa.


Still bata motsa ba, Batool ce ta fara mutsu mutsu kamar zata farka, hakan yasa shi raba ta daga jikin shi ya ɗan jijjigata dakyar ya samu ta buɗe idanunta wadanda suka kaɗa jawur kamar an watsa masu barkono.


"Muje ki kwanta" kamar gunki tay shiru babu alamun zata ɗaga ƙafarta, kamar bata jin me yake cewa.


Sungumarta yai kan Shoulder inshi Ya nufi bed da ita, Cikin kulawa ya kwantar da ita..


"Kada Ki kwana Da hijab a jikin ki, Ki cire sannan ki yi addu'a" sai lokacin ta dan jinjina ma shi kai.


Ajiyar zuciya ya sauke kafin Yai hanzarin juyawa ya fuce daga dakin.



Sai bayan daya fitane ta samu kanta, maganganunsa ne suka dinga yi mata yawo akai a haka har bacci mai dadi yai awon gaba da ita.


"ANEELEERH🌹*


ba ita ta tashi farkawa ba sai wuraren ƙarfe huɗu na dare dayake tasa abun aranta har mafarki saida tayi, idanunta biji biji ta buɗe su ta dubi agogo, kafin ta curo wayar daga chargy harta cika, Kunna wayar tayi Haskenta na kawowa taga abunda ya karya zuciyarta hoton Ana ne da baby junaid akan wallpaper dinta sunyi murmushi a hoton.


Bata samu wayar da password ba, lalube ta cigaba dayi mata ta shiga whatsapp dinta, tana tsaka dayin scrolling ta fada Archived anan taga wani Group da Ana ta bude ita da sisters dinta,, Shiga ciki tayi ta soma karanta firarsu.


_sister, ke da kike zaune cikin rufin asirin Allah, meyasa kika ce kin gaji da zama gidan? Bayan irin sabon da kikayi da Aneelerh, gashi muma ta silarki mun samu taimako a gurin ta_


_ba zaku gane ba, Ni kadai nasan halin da nake aciki, bawai don son raina nakeso In bar gidan ba, kawai hankalina ba akwance Yake ba, ni dai kawai inaso nabar gidan ne_


_kinga in wani abu ke damunki, ki fada mana, mu nemi mafita a tare_


_kada ku ɗaga hankulanku, babu komai, kawai inaso nadinga ganinku kullum akusa dani, saboda kuka dai ne dangin da kuka rage min a duniya_


_idan kina so mu dawo kusa dake, toh ki sama mana aiki anan abujan mana, sai mu dawo, muma munfiso mu zauna kusa da ke_


_bazan bari ku dawo nan ba, sai ni kusa ma min aiki in dawo nan_


_meyasa_


_nafison zama a Jos din fiye da nan_


Dakatawa Aneelerh tayi da karanta sakon, aranta ta ayyana meyasa Ana take gudun zama abuja? Bayan kafin zuwansu tafi kowa daukin zasu dawo nan"!  Girgiza kai ta danyi kafin ta yanko wata firar tasu ta ci gaba da karantawa..


_janet tace"Ana! Kina cikin hayyacinki kuwa? Meyasa kike magana kamar wata musulma"? esther tace"Na fara zarginta, cikin kwanakin nan kullum in zakiyi magana a group chat dinmu sai kin sanya mana abun addinin musulunci bayan mu ba musulmai bane_


_Voice note ta tura masu"nagaji da 6oye maku da nake yi, ku yan uwana ne babu wani sirri atsakanin mu, nasan zaku goyi bayana" su kace muna sauraronki"Na musulunta, Yau wata biyu kenan, amma babu wanda ya sani, ko Aneelerh ban fada mata ba, A boye nake yin sallah ta"_


_"Dagaske kike ko wasa" janet ce ta fada_


_"Na ta6a maki wasa irin wannan"? 

Janet tace"a'a"_


_Ana Tace"toh, Dagaske nake Ana ɗinku Yanzu musulmace ni, na yi imani da Allah kuma nayi imanin cewa Jesus da muke bautamawa bawan Allah ne kuma manzon sa ne"_


Esther tace"nagaza yarda Ana, kamar dai kin haukace, taya zaki bar addinin iyayen mu da kakannin mu"?



_Dogon voice note ta tura masu mai dauke da bayanin abunda Yaja hankalinta harta musunta tace ita kawai ta kaɗaitu da son addinin musulunci saboda kyawawan dabi'un Aunty Anila, tana burgeta tana sonta tana son yadda take janta ajiki, da yadda take kyautata mata, bata ta6a nuna wariya tsakaninsu ba, tana son tayi koyi da komai nata, yanayin mu'amalarta, kyawawan halayanta, da yadda take karatun al'qur'ani, hatta shigarta ta musulunci burgeta takeyi dama kuma ta ta6a yi mata tayin addinin tun farko farkon fara aikinta gidan Uzair ta nuna bataso, tun daga nan bata kara takura mata ba, tadaice mata tayi bincike sosai akan addinin musulunci zata gane abunda take son fahimtar da ita, kunji abunda yasa na musulunta kuma sai nagane shine addinin gaskiya, kuma Inaso ku musulunta don mu gudu tare mu tsira a tare_


wani chat nasu da Anila ta duba, yan uwan Ana ne su ka yi mata voices da murnarsu suka fada mata sun musulunta, tayi murna kamar kamar me sukace ta za6a masu suna tace ita sunan data canza ma kanta sunan nana Aisha, Ita kuma janet ta sanya mata sunan Khadija, sai Esther Zainab, bayan ta raɗa masu sunan janet tace sufa ko alwala basu iya ba, bayan haka basu san komai ba, tace kada su damu zata dinga koya masu kur'ani da hadissai acikin group din nasu itama da apps na musulunci take amfani da kuma sauraran karatun malamai da wa'azinsu ta haka ta ke samun Ilmi.


Lokacin da Aneelerh ke karanta Chat din, hawayene Cike tab da idanunta, wani irin murmushin farin ciki tadinga saki kamar wata zautatta, aranta ta ayyana ashe ana ta musulunta bata sani ba? Allahu akhbar, Abunda yafi faranta ranta, hada Yan uwanta ta musuluntar.


taji dadi da Ana ta musulunta ta silar ta, A hankali ta furta"Alhamdulillah Ya Allah na gode maka..." har sujjada saida tayi.


yanzu A ina zan samu ana? Ta jefa ma kanta tambayar? yanke shawarar kiran layin Yan uwanta tayi sam ta manta dare ne ta shiga danna masu kira babu wanda yayi picking, Zuciyarta cike fal da farin ciki ta jingina bayanta Jikin gadon su, kiraye kirayen sallar asubahi da aka fara ne yasa ta aje wayar, ta mike ta shiga toilet don tayi alwala.


Bayan ta sallame  sallar, ta zauna tayi addu'o'in da ta saba yi daga cikin harda Ana tayi ma addu'a sosai, kafin ta mike ta dauko wayar Ana ta koma kan gadonta, Gallery ta shiga ta dinga budo hotunan Ana dana yan uwanta.


Ta shagala tana kallon su Unexpected yatsan ta ya danno  video ba tare da sanin ta ba, shesshekar kukan da tajine Yasa Ta  mayar da hankali akan videon..


wani irin faɗuwar gaba taji, Lokaci daya ta zazzare idanunta wadanda bakomai ne acikinsu ba face tsantsar tashin hankali da rudani gami da al'jabi, ta yi matukar razana da jin abun da kunnuwan ta suke jiye mata, gaba daya ta rude, gumin tashin hankaline Ya fara tsastsafo mata ta ko'ina a jikin ta, kafin kace me Tsigar jikinta ta fara tashi haikam, La66anta na kerma ta shiga ambaton inna lillahi wa'inna ilaihirraji'un! Allahumma ajirni fil musibati...


tsabar kiɗimar da ta yi ne Yasa tadinga sambatu kowace addu'a tazo bakinta furta ta kawai takeyi, har saida takaiga junaid dake bacci ya farka a firgice sakamakon sallallamin dayaji Mommynsa nayi.


Yana buɗe idanunshi suka sauka akan fuskar Aneelerh wadda ta jike sharkaf da gumi, Idanunta sun kaɗa jawur har wani zazza6i zazza6i take ji a jkin ta..."


Kusan sau uku Junaid yana ambaton sunanta bata ji shi ba, saboda kwakwalwarta ta tafi hutun wacin gadi, abune da bata ta6a zata ba.


"Aunty Aneelerh? Kina ina ne nake jin kukan baby junaid" muryar zahra ce ta fargar da ita, a firgice ta zabura ta sauko daga kan gadon ta watsa da gudu ta shige toilet taja ta rufe.


lokacin da zahra ta shigo junaid kadai ta gani zaune sai kuka yakeyi idanunshi akan kofar toilet din dakin.


da sauri ta nufe shi ta zauna gefen gadon tare da daukar shi ta rungume a kirjinta"junaid lafiya kake kuka? Ina mommyn naka kota shiga wanka ne"? Da yatsa Ya nuna mata toilet door din"nan ta shiga da gudu, inata kiran shunanta bata amsa ba..." da ɗan mamaki ta dubi kofar toilet din kafin ta maida dubanta ga junaid"i'm sorry, Yi shiru, mu jira ta fito" kwa6e fuska yayi "to ai jiya nace ta hada min tea bata kawo ba, har bacci ya ɗoke ni" kallon cup din dake ajiye kan Table tayi"Ko shi ne wannan ta ajiye maka" sai da tay maganar ya lura da cup of tea din da Aneeleeh ta ajiye.


Zahra tace"shine ma, amma naga Ya huce, Bari naje na hado maka wani hada noodles zan dafa maka"


 Aneelerh dake acikin toilet tafukan hannayenta biyu toshe da bakinta gudun kada kukan ya kubce mata, tana cikin halin ha'ula in nan tajiyo muryar junaid daga waje yana kwankwasa kofar toilet din"mommyn ki fito"


gaban faucet taje ta wanko fuskarta ta buɗe kofar ta fito, a tsaye ta same shi ya ruƙe qugun shi fuskar shi a daure kamar wani babban mutum.


"Junaid, i'm sorry, jiya na kawo maka tea din sai na iske kana bacci" da shagwa6a yace"tea dinma ya huce, aunty zahra zata haɗo min wani kuma ma zata dafa min noodles..."


"Yawwa, Yanzu mu shiga toilet inyi maka brush, kafin ta dawo" amsa mata yai da toh, cikin sauri taje ta ajiye Wayar Ana Cikin rigar pillownta ta zuge ta, kafin ta dawo ta ɗauki junaid ta shiga toilet da shi.


da shigarsu ba'afi minti talatin ba, sai ga zahra ta shigo hannunta ruke da madaidaicin tray mai dauƙe da plate biyu na noodles da zafinta tare da cups of tea ta ajiye kan table din gaban gadon, ta zauna tana jiran fitowar su don taji motsin ruwa a toilet.


Wayar hannunta ta cigaba da dannawa, Har zuwa lokacin da Aneelerh ta fito bayanta a goye da baby junaid, har wanka tayi mashi ta lullu6e shi da towel dinsa.


Yana ganin abunda zahra ta kawo masa ya fara Washe baki, tun da ta fito take ta kokarin kaukauce ma zahra don kada su hada ido..


"Auntyna Barka da safiya kun tashi lafiya? 


"Lafiyalou zahra, Hope kina lafiya" da fara'a tace"lafiyalou"


"Sannun da kokari zahra, baki gajiya dayi mana dawainiya" ta fada tare da daura junaid kan gadon. 


"Haba Aunty Aneelerh, wata irin dawainiya"? Ta faɗa tare da mikewa ta nufi closet din kayan junaid"Yaushe zai koma school ne?


Ta fada yayin da take dauko mashi kayan da zai sanya


"In sha Allah next week zai koma" 



Riga da wando ta dauko mashi, da kanta ta sanya mashi, Aneeleeh dake a zaune ta zabga uban tagumi kamar wadda ta rasa mafaɗi a duniya


Zama zahra tayi kusa da ita, ta daura junaid kan laps dinta, tea ta fara bashi Ya shanye duka kafin ta dauki fork ta soma nannado noodles tana tura mashi abaki yana ci.



sam bata lura da Halin da Aneelerh take aciki ba, sai surutu takeyi tana fadin"Aunty Aneelerh ba zaki ci bane,?  Shiru taji bata amsa bata ba, juyowa ta danyi tare da leƙa fuskar ta, gabanta ne ya faɗi ganin tsantsar damuwa akan fuskarta, idanunta sun kaɗa jawur.


Da karfi zahra ta furta"Aunty Aneelerh"! Firgigit tayi tare da kallonta razanar da tayi yasa Zahra jin fargaba.


Adabarbarce ta furta"am...um...zahra.. Har kin sa mashi kayan..." a ruɗe zahra ke kallon ta duk tabi tasha jinin jikinta..


"Aunty Aneelerh, Lafiyarki kuwa? Kinga yadda idanunki suka kumbura, kumatunki sun yi ja, kamar kinyi kuka, gaba daya ma kin sauya min kwata kwata babu nutsuwa atare dake"


 dakyar ta daidaita nutsuwarta cikin sanyin murya tace"bakomai wlh,  lafiyana lou, kawai tunanin duniya ne..." girgiza kai zahra tayi"wlh kallo daya mutun zaiyi maki ya fahimci baki cikin nutsuwarki, auntyna in akwai abunda ke damunki, ki fadamin dan Allah sai mu nemi mafita a tare..." 


murmushi ta danyi"Zahra ki yarda kawai babu komai" gyaɗa kai tayi"shikenan, ga noodles din nan ki ci pls, kada ki zauna da yunwa ni zan tafi gurin aiki har na kusa yin late"



"Nagode da kulawarki zahra, ki kula min da kanki" tana murmushi tace"kema haka" kar6ar junaid anila tay don taci gaba da ba shi abincin.


Zahra Harta kusa ficewa daga dakin ta tsinkayi muryar Aneelerh"Uncle na nan ne"? Zahra bata kawo komai aranta ba tace"Eh,  yana nan dakinsa"


"Okay, " fuce wa zahra tayi daga dakin..


Bayan tafiyar zahra, da rabin awa ta fito Hannunta dauke da baby junaid ta nufi dining area, tunkafin ta karasa ta hango mutanan gidan gaba daya sun hallara akan dining chairs zahra ce kadai babu atare da su.


tsayar da idanunta tayi akan Uncle dan iya daya hakimce kan kujera Ya ƙwama wani uban glases akan idanunsa, Ya tasa farfesun yan ciki shake da plate sai sharbar romo ya ke yi kamar ƙaramin yaro, yanayin fuskarta ne ya canza zuwa matuƙar bacin rai, fusata, da tsantsar tsana Aranta ta furta Mugu bashi da kama, Cike da rashin kuzari ta karasa cikin girmamawa ta gaishe da su da fara'a suka amsa mata, mami ta mika hannu ta kar6i junaid ta zaunar da shi kan laps dinta nan fa ya fara zuba mata shagwa6a.


Tun da ta zauna mami ta yi serving dinta duk cokali daya idan tay sai ta dago ta kalle shi gabanta sai faduwa yakeyi, hakanan yaji kamar Ana kallonsa yana kokarin dagowa tay saurin kawar da idanunta, a dabarbarce ta shiga tura chips abakinta, Mayar da kansa yai ganin ba abunda ya zata bane.


"Aunty Anila ya maganar komawar Junaid School ne? Tun da yaji sauƙi ya kamata amaida shi, karatu yana ta wuce shi" 


"Zahrama ta tambayeni dazu, in sha Allah sati mai zuwa zai koma" 


Mahboob Yace"Allah Yakaimu lafiya" ta amsa da ameen


Junaid dake zaune saman Laps din mami tana bashi abinci tuni ya haɗe fuskar shi muryarshi da shawaga6a yace"Allah ni bazan koma ba, dodo zai ɗauke ni in naje.." dariya su ka yi Abie yace"jikana mai abun ban mamaki! Wani irin dodo ana zaman lafiya"? Yana faman zumbura baki yace"wanda Ya kashe..."  a firgice Anila tay sauri katse shi da karfi ta furta"junaid! Ya isa haka, kamanta abunda na fada maka" da sauri ya rufe bakinsa da tafin hannunsa, dariya su ka yi inka cire Uncle ɗaya wanda hankalinsa kwata kwata baya akan su, Anila kam Ajiyar zuciya ta sauke ganin ba su ɗago komai ba sun maida abun wasa, agogon hannunsa ya duba kafin ya mike Abie yace"har za'a fita"?


Uncle yace" Yau hutu nake har gobe ina gida" Ya fada tare da juyawa ya nufi bedroom dinsa.


Mami tace"wai nikam Ina zahra ne? Ko har an tafi aikin"?


Ummi tace"eh tun dazu ta wuce, tazo tayi min magana cikin bacci naji ta" ummi tace"nima kam naso naji ta tana knocking yau fitar wuri akayi kenan, Abie Yace"zahra badai hankali ba, bata iya tafiya aiki batare dabi kowannan mu tayi mashi sallama ba" Mahboon yace"dama tayine don afada" dariya sukayi, Ummi tace"na fahimci kana kishi kaji an yabi zahra" ta6e baki yayi Anila dake kallonsu daya bayan daya wani irin tausayin su ne Ya kamata.



A Obie Estate kuwa, Yau shirye shiryen Tarbar baba Obie su ke yi, kasantuwar yau ne ranar da zasu dawo daga Lagos, maids din gidan tun safe suka fara gudanar da aikinsu.


Tsaye take a gaban dressing mirror tana ɗan jujjuya jikin ta, wani hadadden Saree ta sanya launin ja mai adon duwatsu sai sheki suke, yayi bala'en yi mata kyau kamar amarya, ta zuba adon Zabba da awarwaro a hannayen ta, ga wasu jerin gemstone necklaces a wuyanta masu daukar ido, ta saki doguwar sumar kanta a abayanta baka wulik sai sheki take, A hankali take kokarin gyara Earrings din dake a kunnanta, yayin da idanunta ke kallon cikin madubin, Ita kanta ta yaba da haɗuwarta, Sareen jikinta ya nadu sosai ya zauna mata, ɗan light makeup tay akan fuskarta tayi kyau, daddaɗan ƙamshin turarenta dana bakhhoor burner din data Kunna Ya gauraye iskar ɗakin da wani irin kamshi mai dadin shaka.


Murmushi ta dan saki har dimple dinta Ya lotsa, ta fito sak ba'indiyarta ta usili, wani irin annurin farin ciki ne ya bayyana akan fuskarta, bakomaine yasa ta farin ciki ba face murnar dawowar Pravin Jiya sunsha waya da shi yana fada mata irin kewarta da yai yace mata ta shirya mashi kanta don idan ya dawo sai ya fanshe kwanakin da baya nan.


Cikin harshen indianci ta furta"Ina jiran ƙarasowarka my lovely husbad"


 ta faɗa tana yar dariya.


High heels ta ɗauko ta zura a kafafunta ta fito ta nufi kitchen don ta duba masu aikin gidan.


*HAJIYA SARATU*



Tana a kwance kan katafariyar bedmatress dinta tayi nisa a baccin ta, Ta wawware kafafuwanta daya tay dama daya tay hagu sai jan minshari takeyi, Sleeping gown ce a jikin ta, zanen kitson da ke akanta ya kara fiddo da kyawun fuskarta duk da babu annuri akanta.



Iphone dinta dake ajiye  saitin kunnanta ce ta fara ruri da karfi sautin ya addabi kunnanta, har saida ta fara kokarin farka cikin magagin bacci da bacin rai ta dinga katse kiran almost 4 times a na hudu ne ta fusgo wayar ta kara kunne rai a6ace ta furta"wai wanene ke son takura mini ne"?


"Jatuminki ne" ras taji gabanta Ya fadi jin muryar baba Obie, a rude ta zabura ta miƙe fuskarta ya amutse cike da jin nauyin furucin da tay sam takasa magana saboda kunya.


Murya na rawa ta furta"baba i'm sorry, wlh bansan na furta ba, Kiran wayarka ne ma ya tashe ni daga bacci bansan kai bane ka kira..."


 bata kare maganar ba ya katse ta"Auta Ko da bani bane abun da kikai ya dace? Idan abokan aikin ki ne fa"?


"Baba ka gane mana, daga bacci na tashi, ban gama wartsakewa ba" 



"Pravin bai fada maki yau zamu dawo bane"? Yamutsa fuska tay"ya fada min"?


"Shi ne kuma kike ta baccin asara, ba zaki tashi kije ki gyara kanki ba"? 


Haɗe rai ta yi "baba wani irin gyara kuma"?


sautin dariyar shi tajiyo"its Okay, yanzu haka muna akan hanyar zuwa airport"



"Okay, zan zo in tarbe ku, Yanzu zan shirya Allah ya kawo ku lafiya" ya amsa mata da Ameen kafin sukai sallama.


Saukowa tay daga gadon tana ƙuƙuni kan maganar gyara da baba obie yai mata.


"Haba Akan me zan takura kaina, Gyara ya wuce mutun Ya dawo ya iske iyalinsa daya bari cikin koshi lafiya, Nifa ba baiwar Namiji bace ehe.." ta ƙarashe kukunin tare da bude toilet door ta shige.



Lokacin da ta ƙaraso Kitchen din kamshin abinci ne ya daki hancin ta har can cikin makoshinta kamshin ya ratsa.


Sam basu lura da zuwanta ba, gaba daya Hankulansu na akan girke girken da sukeyi.


Gyaran muryar da tay masu"Aikinku na kyau" atare suka dube ta, kamar yau suka fara ganinta tayi masu kyau, murmushi suka saki tare da gaishe da ita cikin girmamawa, da fara ta amsa masu.


"Ya kamata kuyi sauri ku kammala, sun kusa karasowa"


Sofia tace"in sha Allah kafin su karaso zamuyi kokari mu gama"

Hajjaty tace"yanzu dame dame ku ka kammala"? Safa ce ta lissafa mata.


"Okay, naji kince hada dambun Nama, pls Ki dan zuba min shi tare da juice, wlh yunwa nake ji" ta fada tana shafa cikin ta, dariya sukai cikin raha tana lura da satar kallonta da sukeyi tasan da wuya in basuyi gulmarta ba kamar ko ta sani gulmace ke cin su.


Bayan Safa ta zuba mata dambun naman a plate ta haɗo mata da glass na juice a kan madaidaicin tray ta daura mata tare da muka mata tasa hannu ta kar6a tare da yi mata godiya ta juya ta fuce.


fitarta keda wuya Abla tace"wannan gayu haka hajjaty, Kamar wadda zataje gasar kyau"? Ta fada baki asake, sofia tace"ni dai wlh tana burgeni, inason mace mai tsafta da iya daukar wanka, amma abunda bangane ba Wa takeyi ma kwalliya ne? Naga dai ba wani guri take zuwa ba kullum tana a gida"


"Kun cika sa ido, Nifa bansan gulma wlh, naga dai ba yau ta fara yin kwalliya ba" safa ta fada tana jifarta da harara.


"Ba yau ta saba ba amma na yau yasha banban, yau fa baba Obie da pravin zasu dawo meyasa zata ca6a adon nan sai kace wadda zata tarbi Mijinta, ko dai hajiya saratu batay gayun nan ba bana tunanin ma ta tashi daga bacci, sai ita zakakka abun nata na nema ya wuce gona da iri ya kamata ta tsaya a matsayinta na yar aiki" Ta kare maganar tana hura hanci

Fashewa sukayi da dariya..

"Pls Ya isa haka Sofia, nasan meke damunki, Bakin cikine da hassada, Saboda kinga hajjaty Allah ya zuba mata ruwan kyau gashi tafi ki matsayi shiyasa kike kishin ta" 


tsoki Sofia taja"Allah ya kiyaye inyi mata hassada Ni kawai na fara zargin akwai wanda takeso ta mallaka agidan nan shiyasa take caba ado nan don taja hankalin sa, In kuwa hakan ta faru mu zamu zama bayinta, kuna gani dai haka Harriet ta aure Sir mubarak to wai mu ko bamu da farin jini ne a gurin mazan family din nan" ..fashewa sukayi da dariya.


"Duniya tayi maku dadi, wato Na lura gaba daya kun manta da marwa" acewar Abla, Atare suka hada baki gurin furta Alah sarki marwa ko awani hali take? Safa tace"jiya nayi waya da innarsu ta fada min jikin nata da sauki har ta fara kokarin yin magana"

Sofia tace"baiwar Allah tadaiji jiki sosai, Alah ya bata lafiya, ko ta samu ta dawo bakin aikin ta, In sha Allah nima da anjima zan kira inji ya jikin nata" 


_____________________________________✍️


A hankali take tafiya cikin takun dattako, wata hadaddiyar egyptian abaya ce a jikinta mai tsadar gaske, tay rolling head scarf, yayin da Idanunta ke amanne da farin glases, Ko hoda bata shafa ba amma ba ƙaramin kyau ta yi ba, hannunta daya na a ruke da purse dinta, ga wani daddadan fragrance dinta dake tashi.


Har zata gifta idanunta suka hango mata hajjaty, wani uban burki ta ci  ganin yadda ta caba ado kamar wata amarya.


"Ke zonan" ta fada da ɗaga murya, hajjaty bata san da zamanta ba, har takusa shiga part dinsu na maids ta tsinkayi muryar Hajiya saratu rass taji gabanta Ya fadi arude ta juya tana kallon ta, da hannu tay mata alamar tazo.


Hankalinta ya tashi don tasan kiran hajiya saratu ba alkhairi bane.

Jiki asanyaye Ta nufe ta aranta tana ta ambaton la'ila ha illa anta subhanaka inni kuntu minazzalimin.

Koda ta karasa nesa da ita ta tsaya cikin sanyin murya tace"gani aunty saratu" harara ta galla mata har saida tasha jinin jikinta.


"Uban wa kikai ma wannan adon"? sunkuyar da kanta kasa tay, aranta ta furta"mijinki nayi mawa, a fili kuma tace"Aunty, kamar dai yau kika fara ganin nayi kwalliya"? Ji tay kamar ta kwasa mata mari saboda fusata"karki kuskura ki kara kirana da sunan aunty, in banda munafurci sai da kika saisaici ranar da kikasan mijina da baba zasu dawo tukunna kika caba adon nan ko? A cikin su wa kikai mawa"? Ta fada tana cije lips dinta hadi da matsowa kusa da hajjaty, jikinta sai kerma yake tray din hannunta kamar zai kife kasa, Cikin rawar murya tace"Allah shine shaidata, Ni banyi kwalliyar nan don daya daga cikinsu ba, nayi ne saboda in burge kaina" idanunta cike tab da kwalla ta kare maganar.


Da hannu hajiya saratu ta cafko pallu din sareen data laga kan kafadarta..


Ta soma goge mata kwalliyar fuskarta ran hajjaty ya 6aci sosai duk ta cabe mata kwalliyarta.


Murmushin mugunta hajiya saratu ta saki da alama ta manta da abunda hajiya laura ta fada mata"Idan kin koma ɗaki, Ki cire sareen nan, Yau nafi son naganki cikin uniform na ma'aikatan gidan nan fatan kin fahimce ni" jinjina mata kai tay"Toh" 

"Yawwa zaki iya tafiya" har zata juya ta kuma kiranta

Da yatsa ta nuna tray din hannunta"meye a ciki"?

Muryarta tamkar zata fashe da kuka tace"dambun nama ne"

"Samun wuri, Wato ke har kin riga masu gidan dandana girki ko? Ta fada tare da kai hannu ta buɗe plate din Ta duma hannu ta dibi dambun naman ta tura abaki tana tauna, bakinta a cunkushe tace"kafin in dawo kisa a shirya min Lunch dina, komai da aka dafa za'a zuba min.." ta fada tare da kara dumbuzar dambun naman ta tura abaki, kafin ta dauki Juice ta kur6a, duk hajjaty tana atsaye tana kallonta.


Tsoki taja"duk na bata hannuna da maiko ni da zanje airport tarbo mijina" cikin sanyin murya hajjaty tace"yakamata ki wanke" ta fada tare da nuna mata Sink din dake a kusa da in da suke.


 harara ta galla mata"nifa komi zakiyi ba zaki taba burgeni ba.."


Ta fada tare da zaro hanky daga purse dinta ta mutsustsuke hannun dashi duk don kada hajjaty taji dadin ta bi shawarar ta, juyawa tayi ta nufi hanyar fita daga falon.



Binta da kallo Hajjaty tayi har ta bace ma ganinta, murmushi ta saki  ta danyi mamaki da ta ci abun hannunta musamman a kwanakin nan data lura kamar batason ko hanya su hada, tabbas ta bata mata rai amma har yau Allah bai sanya mata tsanarta ba, Ita dai tana so su dinga mutunci da juna.



Juyawa tayi jiki asanyaye ta nufi dakinta.


 kaitsaye hajiya saratu ta nufi hamshakiyar motarta, a hanzarce Officern da zaiyi driving dinta yai hanzarin bude mata cardoor har ta zura kai zata shiga muryar Twins ta katse mata hanzarin ta"Mommy" gently ta juyo tare da kallonsu, yayin da suke fitowa daga Entry hall sun dauki wankan suit kamar a turai.


Murmushi ta sakar masu, Suna karasowa ta haɗa su duka tayi hugging dinsu gwanin ban sha'awa..


Bayan sun gaishe da ita ta amsa masu tare da cewa"my twins Ina zuwa haka? Yau dai ba aiki na sani ko za'a fita yawon bude ido ne" zaid yace"No, daddy ya fada mata time da jirginsu zai karaso shiyasa muka shirya don muje tarbo su"


"Kunyi tunani mai kyau, Nima yanzu haka airport din zanje, me zai hana mu shiga mota dina"  


Bayan sun shiga suka sanyata tsakiya suna zaune a gefe da gefenta. 



Sai da motarsu ta haura kan titi kafin ta dubi zayn"ya zahra? Two days ban tuntube ta ba, amma nasan kai kana waya da ita"


 yamutsa fuska yai a dakile ya furta"may be tana lafiya" wani kallo ta wurga mashi"oh baka da tabbaci ma? Thats mean baka kiranta awaya"!



"No ba haka bane mommy, Kinsan yanayin aikina bakasafai nake samun lokacin yin waya ba" girgiza kai tay"banji dadi ba, yakamata kana bata kulawa zayn, nan bada jimawa ba zata zama matarka" daure fuska yai, zaid sai faman kunshe dariya yakeyi..


"Mommy hannunki kamshin nama yakeyi ko hancina ne" Ya fada tare da ruko hannunta Yakai saitin hancin shi yana shinshinawa.


"Kai Zayn Allah ya wadaran naka ya lalace, ka cika sa ido" ta fada tare da dago purse din hannunta, ta kwala mashi akai" dariya suka sanya gaba dayansu da alama dai suna acikin farin ciki.


__________Hajjaty___________



Bayan da ta dawo daki, zama tayi daga gefen gadonta, ta ajiye din akan table din gabanta, A tsanake ta fara cin dambun naman fuskarta dauke da murmushi wato abunda hajiya saratu tay yabata dariya, aranta ta ayyana in da ni muguwace kamar yadda kike fadi wlh da abinci kadai zan iya kashe ki saratu.


Wayarta ce ta soma ringing, tayi azan Pravin ne cike da zumudi ta janyo wayar daga kan pillow ganin ba pravin bane yasa murnar ta koma ciki amma taji dadi data ga kiran daga kayin marwa ne.


Picking call din tay tare da kara wayar a kunnnata.


"Ina wuni inna, ya jikin marwan"? Bata kare maganar ba, Muryar Marwa ta katse ta da cewa"Aunty Hajjaty Nice marwa dakai na" 


Da mamaki ta furta"Wai dagaske Marwa kece? Allahu akhbar amma natayaki murna naji dadi da bakinki Ya bude Marwa Ya jikin naki"


"Da sauki, yatsun hannayena ma sun warke har abinci Ina ci dakaina" tsantsar farin ciki ne Ya cika hajjaty"Alhamdulillah Ya Allah mungode maka, Allah ya kara maki Lafiya marwa, Allah ya kara tsare ki daga sharrin Aljanu".


"Ameen aunty, nagode da kulawarki agare ni" shiru sukayi na dan wani lokaci kafin hajjaty tace"kinji kwana biyu ban kira na tambayi lafiyarki ba, wlh na shiga busy ne amma kina araina, bari na hada ki da su Abla ku gaisa" har ta yunkura zata mike Marwa tay saurin katse mata hanzarinta"Aunty akwai wani abu da nake son fada maki sirri ne" jin wannan maganar yasa hajjaty ta koma ta zauna ta nutsu tana sauraronta.


"Kiyi hakuri ki yafe min, Abunda ya faru dani hakkinki ne ke bibiyana, baki min komai ba, amma saboda kwadayin abun duniya na rufe ido na kar6i tayin aikin leken asiri da aka sani akanki" wani irin faduwar gaba hajjaty taji gaba daya tabi ta rude murya na rawa tace"ban.. bangane me kike nufi ba!"


Marwa bata boye mata komai ba ta sanar da ita zargin da hajiya saratu takeyi akanta da kuma aikin data bata don tayi mata leƙen asiri don ta gano me take kullawa.


"Marwa Dama kece kike tsoratar dani"?


Cikin shesshekar kuka marwa tace"wallahi nice, nayi danasani hajjaty, baki min laifin komai ba hasalima kin kaunace a lokacin da wasu ke kyamatata, da zuciya daya kikai jinyata, na dade banga mace mai kyakkyawar zuciya irinki ba, kina da hakuri ga son taimako...."


 kasa karasa maganar tay saboda kukan daya kwace mata.


Zafafan hawayene suka wanke fuskar hajjaty tabbas hankalinta ya tashi da jin abun da hajiya saratu tasa ay mata ashe tsanar da tay mata har takai ta sa adinga bibiyarta? Laifin me tay mata?

Numfasawa tay kafin ta furta"marwa ki daina kuka, wlh na yafe maki, har ita hajiya saratun, Allah ya yafe mana baki daya, kuma naji dadi da kika gane kuskurenki" 



Bayan Marwa ta tsagaitawa da yin kukan tace"bawai iya wannan ne abun da na kira in fada maki ba..."


A kagare hajjaty tace Ina sauraron ki marwa.


"Bansan ya zaki ɗauki abun ba, amma kiyi hakuri ban fada maki don in tada maki hankali ba face sai don In ceto rayuwarki saboda Kyautatamin da kika yi, Da farko nayi danasanin aikin da hajiya saratu ta sakani amma daga baya Naji dadi saboda silar aikin Allah ya nuna min wani mugun abu dake rayuwa agidan nan" Yawu hajjaty ta hadiya kutt zuciyarta cike fal da fargaba ta furta"marwa menene? Fada min dan Allah!


Numfasawa marwa tay kafin ta daura da cewa"Aunty PRAVIN shine silar ciwo na, Saboda Ya gano nice nake yi maku leken asiri shine Ya daura mini cutar kuturta Ya toshe min bakina" 


 bata kare maganar ba sakamakon tsawar da hajjaty ta daka mata"Ya isa marwa! Bana son karya ki rasa wa zaki wa kazafi sai pravin? Taya pravin zai iya daura maki ciwo? Sai kace dai Aljani"!



"Saboda shi din mugun matsafine, kece bakisan wanene Pravin ba, tun farkon fara aikina gidan nasan munanan dabi'unsa, Ya saba Bibiyar mu yana laluban jikinmu dayi mana barazana akan in muka tona masa asiri zaisa a koremu daga aiki....." 


wani irin faduwar gaba hajjaty taji daram dararam kamar ana mata luguden ta6are a kirjinta, Jikinta sai kerma yake kaf kaf idanunta azazzare cike da tashin hankali wlh ji take kamar a farmaki sam takasa yarda da maganar marwa taya ma wai pravin dinta zay aikata hakan? 



"Naji kin shiru, dama nasan ba lallai ki fahimce ni ba, amma ki sani wlh rantsuwar dan musulmi ba kazafi nayi masa ba, Halinsa ne, a daren ranar dana tashi da ciwon kuturta shine mutun na karshe daya shigo dakina, bayan na fito daga wanka naje gaban madubi kwatsam na hango mutun abayana ya goya hannayensa akan kirjinsa a razane na zabga salati na jiyo na dube shi nace pravin taya akai ka shigo dakina bayan na kulle kofa? Yana dariya yace min Nice na kira shi, daban shiga gonar shi ba da abunda zai kawo shi dakin, Hankalina ya tashi nayi azan yazo ya yi min abunda ya saba yi mana ne amma sainaga akasin haka yana matsowa kusa dani naja da baya har saida ya kure ni jikin bango, Ina zare ido nace in har bai fita ba, zan yi  ihu in tona ma shi asiri kowa yasan ya shigo dakina still yana dariya yace ko nayi ihu abanza babu wanda zaiji, da naga bani da wata mafita yasa na fara rokon shi akan kada ya ta6a ni yace shi ba wannan ya kawo shi ba, yana so in fada masa wanene ya sanyani aikin yi maki leken asiri? Nayi mamaki jin yai magana akanki saboda ni a iya sanina farko daya kawo ki gidan nan ya kira ki da sunan yar uwarsa marainiya wadda ta rasa mijinta bai ma nuna kina da mahimmanci agare shi ba, A lokacin sai nace mashi Meye alakarka da ita? Kuma taya kasan Ina yi mata leken asiri? Yace saboda ke matarsa ce, maganar taya akai yasan ina yi maki leken asiri bata shafeni ba kawai yana son yaji waya sanya ni, na watsa mashi harara nace Munafukin banza wlh saina tona maka asiri agurin hajiya saratu, maciya amana, yace taya za'ay in tona mashi asiri Ina tunanin zai kyale ni ne bayan nasan sirrin shi, injira inga abunda zai faru dani, yana fadan hakan Ya juya ya fuce yana huci, bayan fitarsa na fara zumudin gari ya waye saboda na kudiri aniyar da sassafe zanyi sammako inje in fadawa hajiya saratu alakar dake atsakaninku dama abunda nake nema kenan"


Ta dan dakata da bata labarin tana mayar da numfashi kafin ta daura da cewa"Aunty kwatsam tsakar dare ina tsaka da bacci na fara jin yatsun hannayena sunayi min kaikayi, a furgice na farka ina kikarin motsa labbana naji sunki budewa aunty adaren ranar naga bala'e ban kara komawa bacci ba....." 


kasa karasa maganar tayi saboda kukan daya ciyota..." 


Tunda tafara labarta mata abunda ya faru gaba daya Ta rude tabi ta rikice ta rasa tunaninta, ta razana matuka idanunta azare take jujjuya eye balls dinta, wani irin gumi ne ya fara tsastsafo mata akan goshin ta..wa'iyazubilla bata san sa'adda wayar ta zame daga hannunta ta fada kan floor.


fadawa tay kan mattress Ta lumshe idanunta da suka kaɗa jawur, Hakika hankalin ya tashi Ahakama bata gasgata maganar Marwa ba, saboda ta yarda da pravin ta cikin sauki bazata yarda don afada mata wani mugun abu daya shafe shi ba, Ita tasan wanene Mijinta, In har bashi ya bude baki ya fada mata da kanshi cewa ya aikata ba to ba lallai ta yarda ta cikin sauki ba, kawai tayi believing marwa karya takeyi mata sai dai abu daya dayasa ta jin farga harya haifar mata da kokwanto shine taya akai Marwa tasan akwai aure a tsakaninta da pravin❓


Fashewa tayi kuka tana fadin wallahi karyane, Ni nasan wanene Mijina, pravin ba matsafi bane,  kuma baya bin mata, sharri ne kawai akeso ayi masa wlh marwa dana san zaki fadamin wannan maganar da banyi jinyarki ba saboda ke din ba mutuniyar kirki bace, Makira algunguma kawai kinaso ki shiga tsakanina da mijina ne..." kamar mahaukaciya ta dinga sambatu tana bubbuga mattress da hannayenta gashin kanta duk ya hargitse..." 


_________________________________✍️



*Chief Owais🔥🌹*



Time da motarshi ta kunna kai cikin gidan baba Obie, tunkafin SA din dake driving dinsa yayi parking Idanunsa suka sauka akan Security details din daddynsa ta window glass din motar yake hango su, sunyi tsayuwar dakaru agaban dankara dankaran motocin su.


Tuni yanayin fuskarsa Ya canza zuwa tsantsar bacin rai, yanzu baida abu mafi tsana a duniyar nan daya wuce mahaifinsa! Baya son ganin shi, ko sunan shi baya son ji, yanzu har takaiga ba zarginsa yakeyi ba tabbaci yake da shi akan cewa yana ɗaya daga cikin Elders na gidan kurkukun ƙaddara shiyasa kwata kwata yanzu baya jinsa amatsayin Uba, Ya toshe duk wata hanya da zata hada su, yanzun ma daya san yana agidan da baizo ba. 


Fitowa Yayi daga Cikin Motar, Farar jallabiyace a jikin shi ya naɗe kanshi da arab turban saboda baya son wani yaga raunin dake akan goshinsa, saboda baya son ya daga masu hankali, Walking slowly Ya nufi main palour, with respect maids din dake sintiri suke gaishe da shi bai ko kula su ba ya nufi part din baba Obie tunkan Ya karasa Ya dinga jiyo muryoyin Uncles dinsa suna fira cikin raha ..


Knocking door din yayi,"wanene"? Hajiya saratu ce ta tambaya daga cikin dakin.


"Owais ne"


"Okay, Come In" tura kofar yayi tare da sa kai Ya shiga da sallama abakin shi, kusan a lokaci daya suka dube shi.


baba obie yana daga kishindige kan Tattausan Rug Ya tada kansa saman Pillow, daga gaban shi wooden tray ne na fresh fruits da aka kawo ma sa, Hajiya saratu ce ka bashi Kayan marmarin a baki Yana sha.


yayin da Senate Lateef da Sir Mubarak suke a zaune kan Sofa, Mai girma sharafudeen Yana a zaune kan arm Chair, Ya dauki wankan suit...


"Zauna mana," Hajiya saratu ce tay maganar ganin yayi tsaye kamar mai nazarin wani abu.


A hankali Ya zauna cikin girmamawa Ya gaishe da su, da fara'a suka amsa mashi, kafin ya matsa kusa da baba Obie ya sumbaci forehead dinsa.


"Sannu da dawowa baba, Ya gajiyar tafiya"? fuskar baba Obie da murmushi Yace"Yawwa shalelena, gajiya tabi jiki musamman da na ga rabin raina" dan murmushi yayi"nayi kewarka, bayan haka Naji dadi da Allah ya dawo min dakai cikin koshin lafiya" still fuskar baba obie da murmushi yake kallon shi, Har cikin ran shi yaji  dadin maganarshi.



Tun shigowarshi bai bari sun hada ido da daddynsa ba, shi ko Ya kura masa ido fuskarsa ba walwala ganin yanda Owais yaba banza ajiyar shi, Ko irin gaisuwar nan da suka saba yi in suka hadu da juna baiyi mashi ba, hakan ya jefa shi a yanayi na damuwa.


Hajiya saratu tace"owais ina ka shiga ne? Kusan two weeks bama ganin gifcinka, ko an kira ba'a samunka"! Senate yace"abunda zance kenan, Kwata kwata baya leƙo mu, ko dan kaga kakan naka baya nan ne? Dama albarkacinsa muke ci halan" 


"Ba haka bane, wlh kuna araina, aikine ya boye ni" 


Sir mubarak yace"kufa haka kuke dakai da dan uwanka baku da magana sai ta aiki kamar agogo bakwa gajiya" dan murmushi yayi Baba Obie yace"karfa ku takura ma shi tom, in ba haka ba yanzu zan kora ku waje, kowa Ya kama gabansa kubarni da abun kaunata"


 dariya suka sanya banda mahaifinsa wanda ya zabga ubam tagumi.


"Baba Ya aminin naka, na lura kaji dadin zama agurinsa, kai da kace zakai 3 weeks sai ga shi har ka kara kwanaki akai" yar dariya yayi Owais"ba zaka gane ba, wlh kamar kar mu rabu, dakyar fa escords dinshi suka rabamu a airport,  wlh har kwalla saida na zubda saboda tausayinshi daya kamani"


dakyar ya kare maganar, kwalla cike tab da idanunshi.


Jikinsu duk yayi sanyi, tausayin baban nasu Ya kamasu

Sir mubarak yace"har yau har gobe ina mamakin amintakarku baba, na dade banga abokai masu rukon amana da kaunar juna, da suka taso tunkuruciya batare da wani abu ya raba su ba irinku, Ina alfahari da ku, Allah ya ƙara dankon zumunci atsakaninmu da shi"


 kalaman Sir Mubarak sun faranta ranshi da fara'a yace ameen

Senate Lateef Yace"baba mezai hana ya dawo nan mana, tunda shi ba iyali gare shi ba, a legos dinma ba wani dangine da shi ba, kai kadaine dai danginsa" numfasawa baba Obie yai kafin yace"ba yadda banyi da shi ba akan ya dawo nan mu zauna, amma yaƙiya shi dai yafi sha'awar zaman legos, hada sabo ke dawainiya da shi amma in sha Allah idan ya halarci family meeting din da zamuyi zanyi kokarin jan hankalinshi akan Ya dawo nan din.." 



"Ina pravin dinne? Ina so inyi mashi bangajiya" chief ne ya fada, hajiya saratu tace"Yana adaki"


"Okay, ya fada tare da kallon Sir mubarak"Uncle, Ina zaki? Tsawon kwanaki banji duriyarsa ba, ko na kira bana samun layin sa"



"Ay Zaki tun satin daya wuce suka koma canada.." hajiya saratu tace"ba sallama"? Ta fada ranta adan bace.


Senate Yace"gaskiya ba a kyauta mana ba"  Sir mubarak yace"kuyi hakuri, ai ba jimawa zaiyi ba, Idan za'ayi family meeting zai halarta ne" 


gaba daya hankalin sharafuddeen baya atare da su, bawan Allah Hankalinsa na akan dansa dake ta kakkauce masa..


"Baba Ina neman alfarma, agurin kowannanku" acewar Chief, gaba daya hankalinsu ya dawo kanshi..

Baba Obie Yace"ina sauraronka fadi kaitsaye"


Shiru ya ɗanyi jimm kafin ya ce"inaso a yi family meeting a ranar birthday dina"


 da dan mamaki suke kallon shi, basu ta6a canza date na family meeting din su ba.


"Alfarma nake nema, Idan kowa Ya amince min, amma idan bazai yiwu ba, ba damuwa"


Numfasawa baba obie yayi tare da cewa"owais, wannan ai ba wani abu bane, canza date bazai zama matsala ba, nidai bani da damuwa na amince maka, sai dai bansan ra'ayin iyayen naka ba" ya fada tare da nunasu da hannun shi.



Hajiya saratu tace"haba bakomai wlh, nidai na amince masa"


"Nagode Auntyana" murmushi tasakar mashi


Senate lataeef Yace"ka yi tunani mai kyau owais, kaga kowa zai halarci birthday dinka har ma wadanda basa kasar saboda family meeting, Nima ta bangarena na amince" 


fuskarshi asake Yace"nagode Uncle senator" ya maida dubansa kan sir mubarak wanda ya hade rai 


"Thats impossible, akan me za'a canza date da aka saba yin family meeting saboda kai? Gaskiya ni ban amince ba," hankalin Chief ba karamin tashi yayi ba, hatta sauran Uncles din nasa sunyi mamakin maganarshi haka baba Obie ma baki asake yake kallon shi, cikin sanyin murya chief yace"Shikenan, tun da baka amince ba, na hakura nima abarshi a kwanan watan da akeyi" dariya Sir mubarak yayi"zolayarka kawai nakeyi, kasan ni bani da matsala Owais, tun da har baba ya amince nima na amince maka, Allah ya nuna mana lokacin da rai da lafiya" sanyine ya ratsa zuciyar chief cike da jin dadi Yace"ameen Uncle dina thank you"


 

"Sharafuddeen Me ke damunka ne"? Muryar Baba Obie ce ta dawo da shi daga duniyar tunanin daya lula, murmushi ya kakaro kan fuskarsa babu komai baba,"


"Ina fata kaji alfarmar da ɗan naka yake nema agurinmu"? Jinjina kanshi yayi"naji baba, Allah ya nuna mana lokacin" iya abunda ya furta kenan.


Wayar Chief ce tayi ringing, mikewa yayi da sauri Yayi masu sallama Ya fuce daga dakin don Ya daga kiran da aka yi mashi..


Bayan ya kammala yin wayar juyawar da zaiyi keda wuya yayi arba da daddynsa bawan Allah fuskarsa A yamutse yake duban shi.


"Owais, Laifi me nayi maka? Meyasa kake guduna ko kallona baka son yi? Why Owais kayi blocking duk wata hanya da zan iya magana dakai" ya fada amarairaice.


kallon tuhuma Owais Ya doka masa da kakkausar murya yace" ka daina boye true colour din ka, yanzu na riga da nasan ainihin wanene kai! kuma wlh alwashi na dauka saina tona maka asiri kowa yasan abunda kake aikatawa..."


waro idanu waje mai girma sharafuddeen yayi da tsantsar rudani akan fuskarshi yace"owais wannan wani irin zancan banza ne? wani irin asirine kake ikirarin zaka tona min"? 




Banza yayi dashi bai tanka ma shi ba, matsawa Yayi kusa da shi"owais Ka fadamin dan Allah, me na aikata? Idan ma saboda Sleeping pill din dana bakane yasa kake zargina wlh banyi da wata manufa, nayi ne saboda naji tsoron in rasa ka" 


harara Chief Ya galla masa, ji ya ke kamar ya shaƙe wuyan uban nasa saboda tsanar da yayi masa.



Hannu yakai yana kokarin ta6a turban din dake akansa da sauri Owais Ya cafke wrist dinsa a tsawace ya furta"Don't even think about touching me, or you'll face unforeseen consequences"!


Hankalin Sharafudeen ba karamin tashi yayi ba, He couldn't believe that wai owais ne ke yi masa magana kamar zai doke sa? Babu tausasa harshe? Anya bai fara shaye shaye ba? Ko dai har yanzu ƙwayar maganin bancin daya bashi ce ke aiki ajikin shi❗❓


*DAGA ALƘALAMIN BOSS BATURE🔥🔥🔥✍️*




*Ga me bukatar karanta littafin kurkukun kaddara, 500 ne za'a tura Via Opay, 8103884440 Hafsat Bature Muhammad, shaidar biya za'a tura ta whatsapp, 08169856268 ko 08103884440*

1 Comments

Idan kuna da tambaya akan abinda Baku game ba ko kuma kuma Neman littafin da babu a nan kawai ku ajiye tambayarku a ta comment ko wani shawara da Zaku bamu.

  1. Aslm .muna godiya sosai Allah yasaka da khairan, munji shiru kwana biyu kurkukun kaddara Allah dai yasa lpy

    ReplyDelete
Previous Post Next Post

Sponsored Link

Sponsored Post