Kurkukun Ƙaddara Takun Ƙarshe page 60 Complete by Boss Bature


Health College

Kurkukun Ƙaddara Takun Ƙarshe page 60 Complete by Boss Bature

Takun Ƙarshe

Cikin sanyin murya ya furta"Owais, bayan dana hana ka zuwa kai farmakin sai da kaje ko? Ka daina jin magana ta Owais! " ya faɗa idanunsa akan ciwon goshinsa daya ɗan leƙo batare da saninsa ba.

"Lafiyata bata shafeka ba! Kuma Daga Rana Irin ta yau babu ni babu kai! Ni ba dan ka bane, kakane shine mahaifina mutumin kirki ba irinka ba, Kuma na rantse ka jira ka gani..."

 yana ƙarasa maganar Ya jefar da hannun sa daya ruƙe, Ya juya azafafe Yabar Part din Ko sallama bai je yayi ma baba Obie ba. 

Ya tafi Yabar Sharafudeen cikin rudani, bai taba zaton owais zaiyi masa haka ba, Kai ko a mafarki, Ji yayi bazai Iya jurewa ba, Cikin sauri Yabi bayanshi Yana fitowa Ya hango Motar Owais dake fita, da sauri ya nufi Security Details dinsa tunkafin ya karaso suka bude mashi cardoor din motarsa Ya shiga ciki, ya basu Umarnin su kai shi Gidan owais.

Chief yana zaune seat din baya na motar, ya rufe gefen fuskarsa da hanky, Idanunsa sun kaɗa jawur, bai ta6a karaya da rayuwar duniya ba irin wannan karan yayi fatan ace ba'a halitto shi acikin ta ba, wai mahaifinsa matsafi ne! fasiki mai shan jini da cin naman mutun, Ya Ilahi! 

"Sir, motocin mahaifinka suna abiye da bayan mu" SA din dake driving dinsa ne yayi maganar, aransa ya furta wato mutumin nan saida ya biyo ni!


Motarsu na shiga main gate na villa dinsa Ya ba Security officers Umarnin karsu kuskura su bar kowa ya shigo gidan.


Bayan ya fito daga Motar, Cikin  sauri Ya Part dinsa Yana kokarin Haura wa kan stairs Unexpectedly muryar Shi ta katse hanzarinsa"Owais? Lalacewar taka har takaiga ni kake bada Umarnin a hana shugowa gidan ka"?


Dafe kanshi yayi da hannu ɗaya wani irin kululun bakin cikine Ya tokare makoshin shi Ya tsani jin koda muryarsa.


a cikin kunnansa yake jiyo takun tafiyar shi bai motsa ba har ya karaso ya zagayo ta gaban shi suka fuskanci juna.


 Gabansa ya dan fadi ganin hawaye na sintiri kan kuncin mahaifinsa.


Cikin raunanniyar murya yace"owais, Dan Allah ka fadamin Laifin me namaka? Wlh Hankalina bazai ta6a kwanciya ba in har baka fadamin ba..." Zuciyarshi taso ta karaya, amma In ya tuna wanene Mahaifinsa nasa sai yaji kamar ana kara rura wutar ƙiyayyarsa a zuciyarshi.


Bai ko kula shi ba, Ya nemi ra6awa ta gefen shi zai wuce, cikin sauri Sharafudeen Ya damƙi Arm dinsa.


Cikin karyayyar murya yace"Owais, in har ba so kake zuciyata ta buga in mutu ba, ka fadamin  laifin me nayi maka da yaja har kake zargina! wai ni owais, mahaifinka"!


Kallo mai cike da tsana Chief Ya watsa mashi kafin yace"kafi kowa sanin laifin da ka aikata min, zaifi ka fita sabgata, don bazan taba fahimtarka ba, kawai ka jira lokacin da zan fallasa asirinka a bainar jama'a.."


 ya faɗa tare da bangaje hannun sharafudeen Ya kara gaba Ya shige part dinsa Yayi locking room door dinsa rai a6ace.

 


A bangaren Mai girma sharafudeen Kasa motsawa yayi, al'ajabi da bakin Cikin maganganun da Owais ya gaggaya masa sun ruƙe zuciyarshi tamau sun hana kafafunsa motsawa, Ya rasa ya zaiyi bai ta6a sanin Owais yana da kafiya da taurin kai ba Sai yau da Allah ya nuna masa, tunani ya soma yi waya kamata Ya kira ya fada masa halin da yake a ciki!.


Tsadaddar Wayarsa Ya zaro Ya daga aljihu ya shiga call logs Ya danna ma Number din da yayi saving da jini ɗaya kira, Tana fara ringin yayi picking..


A mutunce suka gaisa da junansu kafin Yace"pls ko zaka kira Owais, kuyi magana, akwai wani abu da ke damunsa yaƙi fadamin may be kai ya sanar dakai" tun daga yanayin muryarsa prime minister Hateem Ya fahimci dan uwan nasa yana acikin damuwa.


Othe other hand prime minister yace"Okay, Don't worry, I'll call him Just calm down and take care of yourself for me"


"Okay, Nagode kaima ka kula min da kanka" bayan sunyi sallama ya juya ya tafi zuciyarsa a hautsine..



*ANEELERH*



Ta fi karfin rabin awa tana safa da marwa a tsakar dakin ta, tana ta tufka da warwara akan yadda zata bullowa lamarin, tun da ta saurari maganganun Ana gabanta keta faduwa, Hankalinta yaƙi kwanciya, damuwarta Ina Ana? Tana raye ko ya kashe ta? batajin zata Iya hakura taja baki tayi shiru batare da tayi gaggawar daukar mataki ba ko dan ta kwatarwa Ana hakkinta, ta kuma ku6utar da family dinta, zuciyarta ce ta dinga azalzalarta da tunzurata akan taje ta tunkare shi kaitsaye ta fada masa ta san komai sannan tayi masa barazana in har bai fada mata ina take ba zata tona masa a asiri uban kowa yasan me ya ke aikatawa sannan ta kaishi kara gurin hukuma.


Kwakkwaran Numfashi taja, fuskarta babu annuri ta fito daga dakin bata iske kowa a falo ba, Mami da ummi suna a kitchen suna aikin lunch.



Bata nufi ko'ina ba sai ɗakin Uncle dan Iya, da kwarin gwiwa take tafiya yayin da bugun zuciyarta ke ƙaruwa Ga tsoro tanaji amma ahaka ta dage ta durfafi dakin nasa har takusa kutsa kai Cikin ɗakin taji kamar an ruke kafafunta dakatawa tayi da yin tafiyar, nan take brain dinta ta fara tariyo mata maganar Ana.


  _watakil lokacin da zaku kalli video din nan, bana a raye na mutu, saboda yace bazai kyaleni ba dama yake jira da zai kashe ni, kuma kunga ni kadaice agidan, yanzun nan naga shigowar shi shiyasa na gudo daki don in samu damar yi maku video, dan Allah don sonku da manzon Allah saw Aduk lokacin da kuka kalli videon nan kuyi gaggawar kaishi ƙara gurin hukuma, sannan ku gudu daga gidan nan, kada ku bata lokaci, saboda shi din mutum ne mai hadarin gaske, ya sha yi min barazana akan In har na kuskura na fada ma wani abun da ya ke min wlh sai ya kashe ni bayan haka zai kashe duk wanda na fadamawa shiyasa nakasa sanar daku_

 


Tuna wannan maganar yasa Aneelerh taji tsoro ya mamaye zuciyarta, tayi shiru tana sauraron gargadin da zuciyarta ke yi mata.



_Kada ki kuskura Anila! Ba zaki Iya ja da shi ba, in har yasan kin san sirrin shi kashe ki zaiyi, mutane irinsa basu da imani zasu iya aikata komai donsu rufawa kansu asiri, Kwara ki nemi wata mafitar...." 


tayi zurfi cikin tunaninta kwatsam Ta tsinkayi muryar mutum abayanta 



"ANEELERH"! Ras gabanta Ya fadi jin muryar mutumin datazo nema, tuni taji tsigar jikinta na tashi, Yan hanjin cikin ta suka hau kadawa.


"Ko ba ita bace"? Zazzare Idanu tayi, Cikin sauri Ta daidaita nutsuwarta, A hankali ta juyo ta fuskance shi, Yana atsaye Cikin riga yar shara da gajeran wando, Junaid Ya jima Yana fada mata Uncle dinta mummuna ne ba ta6a ganin muninsa ba sai yau data gano mugun halinsa.


zuba mata jajayen idanun shi yayi, Cikin rawar murya ta furta"am.. um..un uncle barka da rana, dad..dama kai nake nema, um.. inaso ne dama in tuna maka maganar...." 


cike da rudani yake kallonta Jin yadda take yin magana a dabarbarce kamar mara gaskiya amma bai kawo komai aransa ba yasan Anila da kunya may be tana jin nauyin yi masa magana ne shiyasa ta ruɗe.



Murmushi yayi tare da cewa"Anila kenan, to meye abun rudewa aciki? Kawai don zakiyi min magana? Waini sai yaushe zaki daina jin kunyata? Sai kace ba Uncle dinki ba"? kakaro murmushin yaƙe tayi kan fuskarta batare da ta tanka masa ba.


Dafe kai yai"kash Kiyi hakuri kinji shiru tun da kika tura min credentials ɗin ki, har yanzu ba'a neme ki ba, kema ce baki tuna min, kinsan uncle din naki da mantuwa abubuwane sunyi yawa akaina bakasai nake tunawa ba, In sha Allah zan tuntubi Md din asibitin mutuminane ai..." washe baki tayi tace"bana so na takura maka ne, nasan uzirurrukane sukai maka yawa, shiyasa bana yi maka magana, yau ma don naji kace kana gida shine nace bari na tuna maka"


"Allah sarki, nasa maki rai kina ta faman jirana, ki kara hakuri In sha Allah yanzun nan dana shiga daki zan kira shi awaya in tuna ma shi, Ki ma fara shirye shiryen fara zuwa aiki"


ya fada tare da tafa hannayen sa.


Washe baki ta kumayi alamar taji dadi tace"nagode uncle, Allah yasa ka da alkhairi Saina Ji daga gare ka, Allah ya tabbatar mana da alkhairinsa"


"Ameen Anila, ai baki da wata damuwa, ke da kike dani? Asibitin Obie ai namune ke sai ma kin zabi albashin da kike so a yankar maki Allah wallahi" fashewa tayi da dariya tana fadin"kai uncle, Ina kara gdy da kulawarka agare ni" batai gangancin da zai gano ta ba, lokacin da ta baro gurinsa wata nannauyar ajiyar zuciya ta sauke tafin hannunta dafe da saitin Zuciyarta.



Tana shigowa falo taja tunga ta tsaya tana tunanin meya kamata tayi? dafe kai tay kamar mai fama da ciwon kai.



Aranta ta ayyana Ko dai ta sanarma Mami? Can kuma ta girgiza kai ba lallai su yarda ba, ko da ta nuna masu video din tun da bayani ne Ana tayi bawai videon abun da ya  ke yi mata ne ba, Bakowane zai gasgata maganarta ba kai koda zasu yarda hadari ne Ta gaya ma wani acikin gidan hankalinsu zai tashi a karshe ma garin nukunuku Ya gano su.


Gaba daya Aneelerh ta ruɗe, kwakwalwata na neman rikicewa..

Juyawar da za ta yi ke da wuya tayi arba da mami dake ta kallon ta.



Washe baki tayi adabarbarce ta furta"ma.. mi dama yanzu nake niyar shigowa kitchen din don in tayaku aiki"! Wani kallo mami ta yi mata.



"Aneelerh lafiyarki kuwa? Tun dazu Ina tsaye abayanki baki lura dani ba har kiran sunanki nayi kusan sau uku baki amsa min ba, meke damunki ne!" yawu ta haɗiya ƙut jikinta na tsuma tace"mami ki yarda dani babu komai, ba abunda ke damuna" 



"Anya Anila? Ko dai baki da lafiya? Ta fada tana karewa fuskarta.


 girgiza kai tay"lafiyana lou mami"

Ba don ta yarda da maganarta ba tace"toh," har zata juya ta dan dakata"Kunyi waya da mahboob ne"?


"A'a,"


"Kinsan ba kai gare shi ba, kada yabar mana yaro da yunwa, Ki kira shi ya dawo da junaid gida" amsa wa tay da toh.


"Naji kince zaki ta ya mu girki, mun kammala ay, ga gidan nan ki kara gyara shi" ta amsa mata da toh.


Mami na barin gurin ta sauke ajiyar zuciya.


________________________________________✍️


*PRAVIN*


Cike da zumudin son ganin ta, ya shigo dakin tashin farko yai arba da awarwaron ta akan floor inda ta watsar da su, Hankalinsa ba ƙaramin ta shi yai ba, a yadda yasan Hajjaty da tsafta ba karamin abu zaisa tabar dakinta a yamutse ba gyara ba, hakan yasa shi fahimtar babu lafiya.


Sam bai lura da ita ba, har saida ya karasa tsakiyar dakin, Idanunsa suka sauka akanta tana a kwance kan gadonta bayan data gama koke koken bacci ne yai awon gaba da ita, from head to toe yabi ta da kallo kamar mahaukaciya, naɗin sarin jikinta duk ya warware, har inners din ta sun fito, ga gashin kanta a hargitse kamar bata gyara shi ba, aransa ya ayyana meya faru da ita? Meke damunta"?


damuwace karara akan fuskarta, hawa yai kan gadon ya matsa kusa da ita, da ya dubi fuskarta sai da yaji gabansa ya fadi, Gaba daya kwalliyar da tayi ma fuskarta ta baci da jan bakin data shafa ma lips dinta.


Lumshe idanun shi yayi tare da sake buɗe su kan fuskarta

A hankali ya Shafa fuskar da yatsun sa har izuwa kan wuyanta ya dire su kan kirjin ta.


Numfashi ta ɗan ja tare da sauke shi da hucin zafi.


Baya so ya katse mata baccin ta, amma yana son yaji meke damun ta.


Can kasan makoshi ya furta"My lovely wife, am back, nayi kewarki sosai" 


ya faɗa tare da manna mata sumbata kan lips dinta.


ya saba duk in ya dawo daga aiki ko ya dawo daga tafiya ya shigo dakinta zai taras da ita tayi gayu ta gyara ko'ina na dakin don ta faranta masa kuma zata watso da gudu ta rungume shi sannan ta yi kissing din shi  amma yau sai yaga akasin hakan taya ba zai damu ba?


Hannunshi ya zura ta bayanta yana kokarin kwance igiyoyin rigarta bai aune ba yaji ta damƙi hannunsa, da sauri ya kalle ta, A hankali ta buɗe idanunta wadanda suka kada jawur ta sauke su a cikin nashi, gaban sa ne ya ƙara faɗuwa ganin yadda idanunta suka yi ja kamar an watsa barkono acikin su.



Arude ya furta"kin tada min hankalina, meke damunki ne? Gaba daya dakin a hargitse babu gyara, ke kanki ba acikin nutsuwarki kike ba, wai meke faruwa ne"?


Maganganun marwa ne suka soma dawo mata a cikin zuciyarta, Siraran hawaye ne suka wanke fuskarta, hakan ba karamin daga hankalinsa yai ba, duk yabi ya rude cikin rawar murya yake yi mata magiya akan ta fada masa damuwarta..


Lumshe idanunta ta danyi kafin ta kuma bude su akan fuskarta.


Zuciyarta naci gaba da tariyo mata abun da marwa ta faɗa mata akansa.


Tayi zurfi acikin tunaninta Muryar Pravin ta katse ta ransa adan bace ya furta"wai ba zaki fada min abun da ke damunki ba ne? Kina ji ina magana kin share ni"! 


Numfashi taja tare da sauke shi da karfi.


Ta yi saurin daidaita nutsuwarta cikin disasshiyar murya tace"sannu da dawowa.


"Ba wannan na tambayeki ba, ki fada min meke damunki"


"Kada ka damu, babu komai"


 "Karya kike yi, Dole akwai abunda ke damunki"


"Hakane, bana so na tada maka hankali ne, wlh Cikina ke ciwo, kasan halin da nake shiga idan na fara ciwon ciki" girgiza kai yai"ban yarda ba, kawai ki fada min abunda ke damunki"? Ya fada fuskarsa a daure.


Tunani ta soma yi ya zatay da shi? Don bata jin zata iya fada masa abunda marawa tace akan shi, tasan bazaiji dadi ba in yaji anyi masa kazafi kwara ta bar abun acikin zuciyar ta.


Kurama juna idanu sukayi har na tsawon mintuna goma, sai da ransa ya gama baci jin tayi shiru taki tanka masa, yana huci yace"yau ni kike boye ma abunda ke damunki? kina da wanda yafi ni ne? Okay, kada Allah yasa ki fada"


Saukowa yai daga kan gadon Har ya kusa fucewa daga dakin tayi saurin mikewa ta duro daga kan gadon ta nufe shi da gudu ta faɗa bayanshi tare da zagayo hannayenta kan kirjin shi


Dakatawa yai da yin tafiyar da kakkausar murya ya furta"kin shirya fadamin"? 


"eh" batare daya juyaba yai shiru yana sauraronta.


"Hajiya saratu ce ta bata min rai, taci mutuncina pravin, ni bansan wata irin tsana tayi min ba..." 


karya ta shiga shirga mashi abun da ba halin ta ba, duk don ta samu ta kawar masa da tunanin abunda ke damun ta.


Ransa ya baci da jin abunda hajiya saratu tayi mata.


Cikin shesshekar kuka ta kara da cewa"ita ce ma ta cabemin kwalliyar da nayi maka"


 ta fada tare da ruko sareen dai dai Inda hajiya saratu ta goge mata kwalliyar da shi ta nuna mashi da yar shagawaba tace"ka gani ko"?


 Runtse idanun yai ji yake kamar yaje ya shake wuyan hajiya saratu.



Yana huci yace "bazan ƙyale ta ba, dole In rama maki cin zalun da takeyi maki, mara mutunci kawai.." still da shagwa6a ta tallabo fuskarsa da tafukanta"babe, Ni ban fada maka don ka rama min ba, wlh na yafe mata, kawai banji dadi bane, amma komai ya wuce, mu kyale ta kawai"


Jinjina mata kai yai tace"ina fata kun dawo lafiya? Ya baba Obie? Ya kuka baro aminin nasa"?

"Mun baro shi lafiya, Baba Obie Yana a part dinsa, da anjima ki shiga kiyi ma shi barka da dawowa" 



"Okay, fada min me kake son in kawo maka"?



"Bana jin yunwa, Naci abinci agurin hajiya saratu, A yanzu nafi bukartar ki"


 ya fada tare da daukarta kamar Yar baby, Dariya ta saki tana kallon shi..

Jujjuyata yai kafin ya nufi gadon su da ita, ya jefa ta a hankali, tana daga kwance tana kallon shi yayin da yake a tsaye yana Unbuttoning din rigarsa.


"Ba zan raga maki ba, almost one month, dakyar nake Iya bacci saboda rashin ki"


Tace"nima haka, ba raga maka zanyi ba, ka tafi ka barni da kewarka"


_________________________________✍️


Shigowa dakin ta yi, tana kokarin Yaye veil din da tay rolling, taga wayam babu pravin data bari yana cin abinci adakin.



"Ina ya shiga ne? Ko ya shiga toilet"! Ta fada aranta, tare da nufar toilet door ta danyi knocking shiru ba'a amsa mata ba, sai dai taji sautin safkar ruwa alamar ana amfani da shi.



Watsa hannayenta tayi, ta koma ta zauna daga gefen gadon, Ta curo waya daga cikin yar purse dinta ta danna na Hajiya laura Kira.


"Mara mutunci, Sai yau kika tuna dani? 


"Banson iya shege matar Yaya, don kar in tuhume ki shine kika rigani magana ko"?


Fashewa hajiya laura tayi da dariya"Sorry aminiyar arziki, bana fada maki zanje dubai ba? Sai jiya na dawo agajiye wlh" hajiya saratu tace"kai haba, Ashe kun dawo, Ya gajiyar tafiya"


"Alhamdulillah, gajiya tabi jiki, akwai fa kaya, munyi sabuwar ɗauka, Na tura maki videos ta whatsapp yakamata ki hanzarta zabar wanda kikeso tunkafin akwashe kizo kina cizon yatsa"


Hajiya saratu tace"Amma naji dadi wlh, dama ga hidima muna da ita, dazu Owais ya nemi alfarmar ayi family meeting a birthday dinsa, kuma kinsan In Owais zaiyi birthday, ko biki albarka saboda yarda baba Obie ke ji da shi ina mai tabbatar maki za'ai harka ta arziki" dariya suka sanya gaba dayansu


Laura tace"amma da mamaki Owais daya saba yin birthday a canada inda aka haife sa kice wannan karan A Nigeria za'ae, Amma fa naji dadi wlh, Allah ya nuna mana lokacin lafiya"


Sun dan jima sunayin waya da hajiya laura kafin su ka yi sallama.



Gallery ta shiga ta buɗe hotunan da tayi ma Parveen aranar dinner din Hateem batare da sanin ta ba.


Kamar ibada kullum saita kalli hotunanta, ta6e baki ta ɗanyi.


_____________UNAISAH ANGEL



Tana a kwance kan gadonsu, Ta lumshe idanunta yayin da brain dinta ke tariyo mata memories dinsu da Danish, wani sa'in ta yi murmushi wani sa'in ta zubda kwalla, Amma yau tunanin nata ya kasu gida biyu, saboda kalaman da Chief ya furta mata adaren Jiya da su ta wuni aranta, bata ta6a zaton mutun me matsayi irinsa zai iya aje girmansa da komai donya ja ta a jiki ba.


"Unaisah" muryar Ummi ce ta dawo da ita daga duniyar tunanin data lula


Su biyu suka shigo dakin, Hannun Batool ruke da wooden tray mai dauke da dinner dinta akan table ta daura mata shi.


"Su daddy sun dawo"


Ummi tace"a'a may be sun tsaya yin sallar isha'i ne naji an fara kira, yanzu dai ki daure ki tashi kije ki yi wanka"


 Maƙe kafaɗa tayi"Pls aunty Ummi, dan Allah kibarni, Bana son maganar wankan nan nafi jin dadin jikina a haka, Ni wlh tsoron ma taba ruwan nake"? Baki asake ummi ke kallon ta.


Batool tace"pls Ki daure kiyi wankan zaki ji dadin jikin ki, baki ga yarda kika koma ma ba? Kamar yar mahaukaciya"



Ummi tace"fada mata dai, Gashin kanki ko kyan gani babu, Pls ki tashi kiyi amfani da ruwan zafi zaki fi jin dadin jikinki" girgiza kai tay 


Ummi ta dubi Batool"in muka bita ta lalama bayi zatay ba, Abun da za'ay ki kama hannunta ni in kama kafafuwan mu shiga da ita ciki muyi mata wanka" kafin ummi ta karashe maganar suka ga ta zabura ta mike tsaye tana girgiza 


dariya suka kwashe da ita.


"Dan Allah ku kyaleni, tun da nace bana son wankan, Ba jikina bane wai"


Basu tsaya sauraronta ba, Ummi ta haye ta cafko ta tare da daukarta saman kafadarta, tana ta zabga mata masifa akan ta kyaleta hada ambaton sunan daddy.


 Shigewa Ummi tayi da ita cikin toilet.


Jim kadan ummi ta fito bayan ta wanke mata gashin kanta, ta barota a cikin toilet din, kafin ta fito Batool ta dauko mata kayan da zata sanya.


Bayan ta shafe mintuna, sai gata ta fito tana ta faman daure fuska, Jikinta a sanye da bathrobe..


Kallo daya tay masu ta wuce ta nufi gaban dressing mirror ta zauna, ummi ta fara gyara mata gashin kanta cikin kankanin lokaci ya fara sheƙi.


"Zaki iya shafa lotion din ko in shafa maki" yamitsa fuska tay"zan iya" murmushi suka saki, kamar babu laka a jikin ta kwata kwata bata da kuzari, dakyar ta shafe jikinta da body lotion bayan ta kammala tace su fita zata saka kaya ummi tace"wani dare ne je mage bai gani ba Unaisah? Time da baki a hayyacin ki kin san sau nawa inayi maki wanka"?


 Ras gabanta ya fadi waro idanu waje tay har zata fasa zazzaga masifa Batool tace"zolayarki takeyi"


 cije le6e ta yi, dakyar ta mike ta nufi kayan da Batool ta aje mata kan bedmattress ta dauka ta nufi wurin closet dinsu can cikin dakin ta shige don kada su ganta.



Jim kadan suka jiyo takun tafiyarta a tare suka dube ta, oversized shirt ce  tare da wando plazzo Green colour, ta daura veil din kayan a saman shoulder dinta.


Ummi tace"ku dai Allah yayi maku ruwan kyau, dama kika rame sai kika kara kyau, musamman Collarbone dinki ya kara kawata kyawun kirjin ki" yamutsa fuska tayi cikin sanyayyar voice dinta tace"Anya aunty Ummi ba sharri kike min ba? Kashin wuya ne abun kyau"? 


Batool tace"wlh dagaske yayi maki kyau" tabe baki tayi


"Kizo ki zauna ki ci abincin ki" ta fada tana nuna mata tray din.



Jiki asanyaye ta nufi gafen gadon ta zauna, Batool tayi serving dinta, sam takasa Cin abinci, ko kamshin shi bata son Ji.


"Pls ki daure ki ci ko kin samu karfi a jikin ki" girgiza kai tay"bana jin dadin shi, Ko naci amayar da shi" 


Duk yadda sukaso taci abinci takiya, Suna tsaka da rarrashinta su ka ji yo dirar motoci a cikin gidan.


Jikinta na kerma ta mike tsaye ummi na tambayarta ina zataje tace"Su daddy sun dawo zataje gurin su"


"Batool taimaka mata ku tafi, kwarama da suka dawo watakil idan shi ya yi maki magana asamu ki ci abincin"



Fitowar su daga dakin yayi daidai da shugowar su falon.



Taj ne Agaba kan wheelChair dinsa Sai faman gungurata yakeyi, Chief da sheikh Imam suna abiye da bayansa A masallaci suka hadu da shi bayan sun kammala sallah Anan harya yai mamakin ganinsu yace ashe sun dawo sau uku yana zuwa gidan neman sa saidai ace mashi baya nan ya kuma tambayi meya faru da su? Ganin rauni a kafar Taj, Chief yace in ba damuwa yazo su tafi gida sai su karasa magana acan.



Takun tafiyarsu ne Yaja hankulan su Chief ga kallon direction din da suke, kaitsaye idanunsa suka sauka a cikin nata, kayan jikin ta sunyi mashi kyau.


Karasowa sukayi Cikin girmamawa suka gaishe da sheikh Imam 



Kasa amsawa yayi saboda hankalinsa daya tashi ganin goshinta a nade da bandage, ta rame ba kamar yadda yasanta ba ita.


"Subhanallah, Unaisah meke damunki"? Murmushi tay, 


"Bani da lafiya, amma naji sauki"


Chief yace"mu karasa ciki" gaba daya suka nufi falon kowa ya samu guri ya zauna, Ummi tana a labe bakin kofar dakin su..


"Chief, Hankalina ba akwance yake ba, Inaso nasan meya faru daku? Farmakin da kuka je kaiwa anyi nasara ko kuwa? Naga Taj da rauni a kafa, ga Unaisah ma ba lafiya, kaima haka naga ciwo a goshinka, Sannan Ina sauran yaran suke ne"?


 aruɗe ya tambaya yana dubansu.


Gyaran murya Chief yai kafin ya soma magana calmly.


"Ba zamuce bamuyi nasara ba, Alhamdulillah munci rabin yakin munga tasirin addu'a, abubuwa da dama sun faru masu dadi da marasa dadi..."dan dakatawa yai yana kallon Unaisah dake a zaune gefen daddynta ta daura kanta saman kafadarsa lumshe idanun ta tayi don batason jin karashen zancen na shi.


"We lost Danish, Salsabeel ya samu karaya a hannunsa, Umar has a brain injury, gaba daya an kwantar da su a asibiti, su Commender ma Sunyi rashin daya daga cikin sojijin su, sauran yaran suna a part din Taj..." 



Muryarsa na rawa ya furta"danish Ya mutu ne"?


"Bamu da tabbacin ya mutu ko yana raye, saboda bamu ga gawarsa ba" tashin hankalin da damuwane tsantsa akan fuskar Sheikh Imam, Ya girgiza da jin basu dawo Danish ba, wlh yaji zafi acikin zuciyar shi..


Girgiza kai yai idanunsa cike tab da ƙwalla.


Ya dan jima batare daya furta kalma ba, Can ya numfasa cikin karyayyar murya yai masu nasiha akan suyi hakuri da rashin da sukayi Su mika lamuransu gurin kada su sare, Danish kuma zasu tayashi da addu'a in ya mutu Allah yajikan shi In kuma yana araye Allah ya bayyanar da shi.


Sannan Ya bukaci yana son yaje ya duba su Salsabeel chief yace idan suka tashi zuwa zai kirashi sai suje atare su duba jikin su saboda asibitin ba a kusa yake ba.


Shiru sukayi falon yai tsit kowa da abunda yake sakawa acikin zuciyar shi.


"Ina auntynku? Ko itama tana a dayan bangaren ne"?  Kaitsaye maganar shi ta dira a kunnan Ummi tayi mamakin Jin sheikh Imam ya tambayeta.


"Tana anan tare da mu" Batool ce ta bashi amsa..


Batay niyar fitowa ba amma saboda maganar sheikh Imam yasa ta fito jikinta sanye da dogon hijabin data dauko a cikin closet din su Unaisah.


Har kasa ta zukunna ta gaishe da shi fuskarsa da fara'a ya amsa mata, ta danyi mamaki mutumin da ko kallonta baisonyi amma yau haryake tambayar tana ina.


"Hateem Yasan da maganar"! Girgiza kai chief yai"ban sanar da shi ba ko da zaiji ba yanzu ba,"


Sheikh yace"Allahu akhbar, Allah baya barin wani don wani yaji dadi, Hateem yaso yaron nan kamar dan cikinsa, nasan in yaji hankalinsa ba karamin tashi zaiyi ba"


 ya fada fuskarsa da damuwa jikinshi duk yai sanyi, Zuciyarsa ta karaya, saboda shi kan shi yaso yaron kuma bakomai yafi daga masa hankali ba face kin kar6ar shahadar da baiyi ba.



"Sheikh ga Unaisah nan, Har yau bata daina sanya damuwa aranta ba, dakyar muke samu tayi bacci, dan Allah ay mata nasiha.." Taj ne yai maganar.



Ya tambayi meye silar ciwonta, Taj ya fada masa komai.


Tsananin tausayin su ne Ya kama shi, Cikin sanyin murya ya farayi masu Nasiha har na tsawon mintuna talatin kafin Ya gama gaba daya jikinsu yayi sanyi lakwas, Imani ya kara shigarsu sosai.



Har wurare karfe 9 Shiekh Imam yana agidan daga bisani yai masu sallama Chief Ya rakasa Har cikin motarsa sai da yaga tafiyarsa kafin ya juyo.


Time daya shigo falon ya tsinkayi muryar Ummi tana fada ma Taj Unaisah taki cin abinci.


Da damuwa akan fuskarsa yace"Why Unaisah? Baki so ki samu lafiya ne? Ai ta fama dake akan kici abinci"



Muryarta kasa kasa ta furta"Zuciyata ke tashi,duka abincin da naci da safe dana rana saida na amayar da su a toilet, ban fadi maku bane saboda bana son in tada maku hankali, abincin ma bana jin dadin shi ..." 



Kafin wani ya furta kalma muryar Chief ta katse su.


"Gobe idan dr yazo duba ki ki fada masa aman da kike yi, amma bazan bari ki kwana da yunwa ba, Fada min me kike son Ci" 


ya fada tare da dafe Sofa da hannayensa Yayin da idanunsa ke akan fuskarta.


Saboda nauyin shi da take jine yasa ta ce"zan daure naci wanda aka kawo min"


"Ina abincin nata yake" Batool tace"yana a daki" 



"Je ki ɗauko min" mikewa ta yi da sauri ta nufi dakinsu.


Jim kaɗan sai gata ta dawo hannayen ta ruke da tray ta ajiye shi kan rug.



Zagayowa yayi tare da samun wuri Ya zauna a gaban tray din, mamakin chief ya rukesu Musamman daya Kira Unaisa Ya nuna mata gaban tray din Yace tazo taci abinci" 


Ta dan zaro idanu tare da kallon Taj fuskarsa ɗauke da murmushi yai mata alamar taje mikewa tay jiki ba kwari ta zauna tana fuskantarsa, yayin da tray din  ya raba tsakanin su.


Coconut water ya dauka da sauri ta mika yatsun hannunta dake kerma da niyar ta kar6i Glass din

Batai aune ba taji ya kanga mata strawa din a baki, wata irin kunyace ta kamata, adan rude ta saci kallon su ummi da Taj fuskokinsu dauke da murmushi..



Ganin ta ki motsa lips dinta yasa shi furta"ki sha" yawu ta hadiya ƙutt kafin a hankali ta fara zukar shi, abunda tagaza sha dazu sai gashi ta kwankwade shi duka batare da ta ankara ba har saida ya janye straw din daga bakinta.



Spoon ya dauka Murya na rawa ta furta"zan iya ci da kaina" ta fada tana kyafkyafta gray eyes din ta

Hakan ba karamin Jan hankalin shi yai ba.


"Ki bari ya baki mana Unaisah, Baki ga yadda hannunki ke kerma ba taya zaki iya ruke spoon" Ummi ce ta yi maganar aranta ta ayyana Samun wuri.


Batool sai faman hadiyar yawu take yi, ba yunwa take ji ba, Amma yadda taga Chief na ciyar da Unaisah yasa taji dama ya bata itama.


Taj kuwa Ransa fari fat da farin ciki kamar ya zuba ruwa a ƙasa ya sha, Burinsa yana daf da cika, abun da ya daɗe yana jira abunda yafi burgesa yadda Chief ya nuna kulawa agare ta agaban shi inaga idan sukai aure? Allah kadai yasan gatancin da zata samu a gurin sa, Shi yasan Unaisah ta gama morewa.


Tun tana jin kunyar ya bata abaki har ta dan saji jiki ganin daddynta bai nuna wani abu ba..

duk in ya bata one spoon sai sun haɗa ido da juna launin idanunsa da take kallo bakomai yake tariyo mata ba face kyawawan idanuwan Danish kasancewar launin idanunsu daya hatta shape dinsu kamar an zana saboda kyau.


"My Angel" muryarsa ce tay mata gizau a cikin kunnanta...


Lumshe idanunta ta danyi wasu zafafan hawayene suka taru a cikin su sam bata son kowa ya gani.



Nutsuwa ya yi yana kallon fuskarta, tuni Ya dakata da bata abincin ganin halin da ta shiga.


"Unaisah" muryarta na rawa tace"Naam"


"Pls don't shed your tears"!


 jinjina mashi kai ta yi.



"Na koshi da abincin, Ina so zan shiga toilet" bata jira amsar shi ba, Ta mike har zata fara tafiya taj yace"har kin kammala cin abincin ne"? danne damuwarta tayi"Eh, Inaso zan shiga toilet"


Da sauri ta nufi dakin su, Tana shiga toilet taja kofa ta datse, tare da jingina kanta jikin bango wani jiri jiri take gani kamar zata kife kasa, sai faman jan numfashi takeyi tare da zare gray eyes dinta.


Har yanzu ta gaza yarda cewa man dinta baya atare da ita, bata taba zaton zata iya rayuwa batare da shi ba.


Duk irin burin da ta ci akan shi in sunyi aure zata kyautata mashi saboda halaccin da yai mata yanzu gaba daya plan dinta Ya lalace.



Saitin Zuciyarta ta dafe da tafin hannunta"My man, na gaza yarda cewa ka mutu, Ina ji araina kana raye, shiyasa har yanzu zuciyata take harbawa, don da ace baka raye babu makawa saina bika nima"



*Mr President*


Around ƙarfe shabiyu na dare bai runtsa ba, ya wuni da bakin cikin da owais ya kunsa masa, har ciwon kai saida yai, kayan bacci ne a jikin shi ya zuba hannayensa a cikin aljihunsa wandonsa, Sai sintiri ya ke yi a tsakar katafaren bedroom din Hajiya laura,  ya rasa meke masa dadi? Komawa yai window Ya dafe glass din da tafin hannunsa Ya zuba ma sararin samaniya idanunsa da suka kaɗa jawur..



"Why Owais? why? girgiza kai ya danyi"Ni nasan bayin kanka bane Owais, akwai wanda ke son Ya shiga tsakanina dakai, amma meyasa zaka zargeni kamar bakasan wanene mahaifinka ba"?


Bai aune ba Yaji tayi hugging dinsa ta baya tare zagayo hannayenta kan flat tommy insa.


"My big boss, pls ka fada min meke damunka? gaba daya yau nakasa gane maka, kwata kwata babu walwala a tare dakai.


"Ina da damuwa amma bazan iya fada maki ba kawai ki tayani da addu'a Allah ya kawo min mafita"



Kwantar da kanta tayi kan shoulder dinsa"in sha Allah zanyi maka addu'a, amma pls muje mu kwanta, dare yayi sosai kana bukatar hutu"


"No kije ki kwanta bana jin bacci yanzu" zagayowa tayi tagan shi tare da jinginar da bayanta jikin window glass din a hankali yake dubanta, Nightgown ce a jikinta shara shara rigar.




Kashe murya tayi"ko dai kazo muje mukwanta ko kuma In kira Sarauta In fada mata abun da ke faruwa tunda ni kaki sanar dani" tana fada ta juya zata nufi cikin dakin donta dauko waya da sauri yakai hannu Ya damƙi waist dinta Ya janyo ta ta dawo Jikin shi.


"Ba sai kin kirata ba, naji zan kwanta" kashe mashi ido daya ta yi"ai da ka bari na kirata, kai kasan me zai biyo baya"


Baisan ya zaiyi da laura ba, sometimes indai yana tare da ita koma mashi take yarinya duk da yana jin dadin hakan sosai.


Lallaba shi tayi harta samu yabita suka kwanta.


______________________________bayan wani lokaci


A kwana A tashi ba wuya wurin Allah, yau Wata daya Cuf dakai farmaki gidan kurkukun Kaddara.


meya faru a yan kwanakin nan a kowani Family?


A bangaren Aneelerh cikin kwanakin da suka gabata, ta kasance cikin tsananin damuwa abun duniya ya ishe ta, ta rasa ya za ta yi, kullum tunanin ta wa yakamata ta tunkara da maganar? Ga shaida tana da ita a hannu sai dai tasan mawuyacin abune a yarda da ita, bayan haka tana jin tsoron ta sanarma wani maganar ta koma masa, akarshe ta jefa rayuwarsu cikin hadari.


 tuntana 6oyewa har sai da ta kai ga kowa na gidan Ya fahimci Akwai abunda Ke damunta saboda yawan razanar da takeyi da zarar ankira sunan ta, In tana cin abincin Yatsun hannunta kerma suke kaf kaf, bayan haka takan raba dare bata runtsa ba.


Babu irin magiyar da basu yi mata ba akan ta fadi abunda ke damunta tace itafa ba bakomai lafiyarta qalou, Har abie Yasa aka kirata a falo suka zauna duka mutanan gidan Ya matsa mata akan ta fadi meke damunta a karshe tayi masu karya tace dama a kwanakin nan tana yawon yin mafarkin Uzair da Taj shiyasa ta shiga damuwa, har kuka ta yi masu, duk don su ɗauki maganarta Serious, tausayin ne ya kama su, gaba daya suka haɗu suna lallashinta hada uncle dan iya shine kan gaba, har ila yau bata ta6a yin kuskuren da zai gane tasan wani abu game da shi ba.


___________________________________✍️



Idan muka koma bangaren Unaisah, sai dai muce Alhamdulillah, jikinta ya fara murmurewa, damuwarta ta ragu saboda gatancin da take samu agurin mutan dake bata kulawa, Aunty Ummi, Batool, Taj uwa uba Chief, cikin kankanin Lokaci Shakuwa mai karfi ta shiga tsakaninsu, baya gajiya da bata lokacin shi, kulawar shi, soyayyar shi.


 kullum ne sai sun haɗu da juna, mafi yawan lokutta atare su ke yin breakfast da dinner agaban kowa yake bata abinci abaki tun tana jin kunyarsa yanzu  har ta saba da wayewar shi ganin Taj bai taba nuna ya damu da hakan ba saima dadi da ya ke ji.



Haƙiƙa Chief yayi namijin kokari gurin samun lafiyarta, kullum cikin faranta mata rai ya ke yi, Yanzu atare suke motsa jiki a gym room dinsa, bayan haka  atare suke yin Kallo a tv room dinsa, har garden din gidan suke zuwa atare su yawata ba karamin nishadi take samu ba, komai ta ke so shi ya ke yi mata, saboda tsantsar kulawar da yake bata ko tari tayi wanda bai kwanta masa arai ba sai ya kira dr don yazo ya duba ta, saboda baya wasa da lafiyarta.


duk wani abu da daddynta Ya fada masa wanda tafi so tuntana Yarinya sai da Chief yasa aka kawo mata shi agidan.


Saboda kyautatawar da yake yi mata ne yasa ta fara Jin shi sosai a cikin ranta, da tunanin shi take kwana da shi take ta shi, In ta farka daga bacci shine mutun na farko da take kwaɗayin ta hada ido da shi.


Har yanzu Danish Yana aranta sai dai ta rage damuwa da rashin shi, ta dauki dangana tama fidda rai da shi, saboda ya taba fada mata bazai iya tafiya yabarsu ba, tabbas da ace yana a raye da tuni ya dawo gare su amma yau har one month shiru babu alamun shi.


Abu daya da bata fashi shine yi mashi addu'a har yau bata fasa tashi tsakar dare tayi nafilfili saboda shi ba 💔


A bangaren yan uwanta dake a part din Taj Har yau basu san meke wakana ba, abu biyu ne  ke damun su, Kulle su da akayi a part din taj da kuma rashin dawowar su Unaisah Part din, amma saboda yawan kiransu video call da sukeyi Yasa hankalinsu Ya dan kwanta In suka bukaci suna son yin magana da Danish ita keyi masu wayau ta gyara muryarta ta koma irin tashi da yake ta kware gurin iya kwaikwayon muryar Danish Ba zaka taba gane ba shi bane, Ta hake take shawo kan su, ko da sun nuna suna son suyi video call da shi sai tace masu sun manta Danish baya kallon camera? In ta fadi hakan sai suce eh sun tuna fa.


 wani sa'in kamar zasu saka mata kuka su dinga mata magiya akan su dai suna so su dawo nan su zauna atare da su, tace su kara hakuri suma suna jirane sai su Danish sun tafi sai su dawo nan.


Alhamdulillah duk da suna a kulle part din Taj suna samun kulawa chief bai barsu hakanan ba, ya sanya masu duk wani abu na more rayuwa da zai shagalar da su ya kawar masu da damuwarsu, Basu da matsalar komai, Hutu kawai suke sha, rana ta farko da Unaisah tayi video call da su saida ta yi mamakin ganin yadda Kumatun parveen suka cuccuko, sunyi kiba sunyi haske kamar ya'yan turawa, Duk in zasu yi waya sai sajeed Ya tuna mata akan ta fada ma Danish Yar uwarsa dake a prison dan Allah kada su manta da ita su taimaka su ɗauko ma shi ita...💔

__________________________________

✍️


Idan Muka Koma Obie Estate tuni sun fara shirye shiryen Bithday din Owais da family meeting  kasantuwar saura kwanaki kalilin ya rage, prime minister harya kira baba Obie awaya ya fada masa ranar da zai shugo Nigeria yakuma ce su fara shirin tarbarsa.


saboda gabatowar ranar  Baba Obie Yasa aka fara gyara Estate Din tare da ƙawatasa yadda kasan Masarauta saboda kayan alatun da aka wadatasa da su.



A bangaren Hajjaty tuni tayi watsi da maganar Marwa, kuma tayi blocking contact dinta saboda bata bukatar ta karajin koda muryarta, tun da tayi ma Praveen kazafi taji ta fita aranta.



BENAZIR💔



A Zaune take kan Mirror chair, Hannunta ruƙe Da wayarta, hotunan Unaisah take kallo Idanunta sun cuccuko tab da kwalla, Baiwar Allah Hankalin ba akwance yake ba, ta damu da rashin samun su awaya, In ta kira Unaisah kiran baya shiga, shi kuma, Taj ko ta kira baya picking sometimes rejecting call din yakeyi  har sako ta tura ma sa tace dan Allah idan ma bazai kula ta ba,  ya hada ta da Unaisah tana son yin magana da ita, shiru bai kirata ba kuma bai mayar mata da reply ba, ta rasa ina zata tsoma ranta taji dadi! Gashi since last da sukai waya da Unaisah Bata kara bacci Cikin kwanciyar hankali ba, saboda munanan mafarke mafarken da ta ke yi akan ta da kuma tana ji aranta wani abu na faruwa da su, Har tunanin zuwa estate din ta yi sai dai tasan Ba lallai ta samu hanyar shiga ba ko da taje, tunda ba wani gareta ba, Taj da take takama da shi baya kula ta amma tasan indai ta nemi Anila da maganar zata taimaka mata suje tunda dama ita ta hadata da su kuma ta san Taj yana ganin girman Aneela.


 Kifa kanta ta yi gaban mirror tana shesshekar Kuka.


"Aunty Benazir" Cikin kunnanta ta tsinkayi muryar Zeenatu, Kasa dagowa tayi saboda bata son yanayinta ya jefa zeenatu a hali na damuwa


Shigowa dakin zeenatu tay, jikinta sanye da jallabiya fara.


Ganin Benazir zaune ta kife kai gaban mirror yasa ta nufe ta.


"Aunty Benazir, lunch is ready, we're waiting for you" ta fada tare da karasawa gaban ta.


Jin shiru bata dago ba yasa zeenatu tayi tunanin ko bacci ta ke yi.


Dafa bayanta tayi"aunty Benazir, Wake up pls, " taji tayi shiru bata tanka mata ba.


tasan in har ba magana ta yi mata ba, ba tafiya za ta yi ba, a yanzu bata son kowa a kusa da ita tafi son kadaici.



"Zeenatu! Pls ki kyale ni, basai kun jira ni ba, Ki tafi kawai ku ci abincinku," 


ras gabanta ya dan fadi jin yadda  Benazir take magana cikin shesshekar kuka arude ta furta"Aunty Benazir! Meke damunki? Baki da lafiya"? 


Bata san sa'adda ta daka mata tsawa ba"bansani ba, Zeenatu! Nace ki kyaleni, Ki rabu dani, bana son ganin kowa akusa dani..."


 zazzare blue eyes dinta tayi, abunka ga shagwababba ta fashe da kuka ta juya ta fuce da gudu ta nufi dining area.



A lokacin Mami da Hajiya sarah tare da Dr shureim da Alhaji Ubaida suna azaune kan dining Chairs har sun fara cin abincin, Kukan zeenatu ne yaja hankulansu ga dubanta, azabure suke mike suna kallonta, Ta na karasawa ta fada jikin mommynta tana ci gaba da kuka, Hankali atashe suka dubi juna kafin suka maida idanunsu akanta.



" Zeenatu meya faru? Ina Benazir din? Wa ya tabaki"? Alhaji ubaid ne ya tambaya.


Mami tace"ki bude baki kiyi magana mana! Wani abunne Ya hadaki da Benazir dinne"?


Dago da ita Hajiya sarah tayi"Daughter, Daina kuka, Fada min meya faru"! Cikin kula tayi maganar tana share mata hawayen fuskarta

Cikin shesshekar kuka tace"Ah.. an.. aunty Benazir ce take kuka, Nace tazo muci abinci shine ta daka min tsawa tace in tafi bata son ganin kowa a tare da ita"  



Dr shureim bai tsaya ya karasa sauraron maganar Zeenatu ba, Ya zame jiki Ya nufi dakin Benazir tunkafin Ya karasa shiga Ciki yajiyo sautin kukanta, gabansa na faduwa ya afka ciki Ta cikin madubi Ya hango fuskarsa sharkaf da hawaye ta zabga uban tagumi kamar wadda ta rasa gata a duniya, da sauri ya nufe  arude ya furta Benazir! Lafiya kike kuka? Meke damunkin ki ne? 



mikewa tayi ta nufe shi ta kwantar da kanta saman kafadar shi tana kuka, bubbuga bayanta ya somayi da hannunsa cikin sigar lallashi yace"pls ki fadamin damuwarki, Zan taimaka maki mu nemi mafita, amma kukan nan bazai amfane ki da komai ba, saima yajaza maki ciwon kai"


 dakyar ta hadiye kukan tace"yaya shureim ina ma mutuwa zata zama hutu agareni wlh dana mutu na huta, nagaji nagaji da azabtarwar da zuciya keyi min akan rashin mijina da yata, yaya shureim bana jin dadin komai, hankalina ba akwance yake ba, Ina so nagan su..." dakyar ta karashe maganar..



Gaba daya a kunnan su Mami da basu dade da shugowa dakin ba, Gaba dayansu sunyi tsaitsaye cirko cirko suna sauraron maganar Benazir, tausayinta ne ya kamasu mami tuni idanunta sun ciko tab da kwalla, batasan ya zatay ba, ita kanta zataso Benazir ta hadu da bayin Allahn nan ko ta samu nutsuwar hankali..


Zeenatu dake kuka kalaman benazir sun karya mata zuciya, wani kukan takuma fashewa da shi.


"Benazir, Kiyi hakuri, Ki kara jurewa dan Allah, Na roke ki, sanya damu arai bazai haifar maki da komai ba, saima ta fama maki raunin dake a cikin zuciyarki, bana so a koma yar gidan jiya, dan Allah Benazir kiyi hakuri zamu tayaki da addu'a kema ki dage in sha Allah zasu bayyana"


 Hajiya sarah ce ta yimaganar cikin sanyin murya.


Girgiza kai Alhaji ubaid yai shi kanshi abun na damun shi.


"Kinga kukan Ya isa haka, Kiyi shiru, in sha Allah Idan Uncle dinku ya dawo zanyi magana da shi ya taimaka yasa a yi cigiyar su agidan jaridu watakil adace..."  



gaba daya tunaninsu har yanzu babu labarinsu ita kadai tasan Da zaman su..



A hankali ta dago daga kan kafadar dr shureim Idanunta sun kada jawur ta dube su ji take kamar ta fada masu Taj da Unaisah suna nan kuma tasan inda suke, ko dan ta samu su tayata neman yafiyarsa.



Girgiza kai tayi"nagode da kulawarku agareni, Amma basai an yi cigiyarsu a gidan jaridu ba, Aneelerh ta fada min sunyi iyakar bakin kokarinsu gurin yada hotunansu a social media da Gidan jaridu amma har yau babu labarinsu...." ta dan dakata kafin ta daura da cewa"dan Allah kada ku damu da halin da nake a ciki, bawai don banyi imani da kaddara ba, wlh nayi kokarin In manta da su a cikin zuciyata amma abun Ya faskara..."


 ta faɗa tana matse kwalla.

Kallonsu Dr shureim yayi"pls Ku barni da ita, ku je ku ci abincinku, Zan yi mata nasiha" Alhaji ubaid yace"yawwa shureim pls kayi kokarin shawo kanta, bana so ciwonta ya tashi" amsa mashi yai da toh, fita su ka yi ya rage saura su uku


Kallon zeenatu yayi, Tana atsaye bakin kofar sai shesshekar kuka take.


"Calm down your mind, Ki kawo min lunch din ta a daki" ta amsa da toh ta juya ta fuce..


Ruko hannunta yai suka zauna kan gadon ta.


Nasiha ya farayi mata cikin kwantar da murya har saida taji zuciyarta ta dan lafa da radadin da takeyi mata.



Sai da yaga ta samu nutsuwa sosai kafin yace"akwai inda ke maki ciwo" girgiza ma shi kai tay"a'a ya shureim, lafiyana lou"


"Okay, " ya fada tare da sauke ajiyar zuciya.


Shigowa zeenatu ta yi cikin dakin, hannayenta ruƙe da tray mai dauke da lunch ta mika ma dr shureim Yasa hannu ya kar6a yadago ya dube ta"thanks, yanzu sai hankalin ki ya kwanta, tunda auntyn naki ta daina kuka" murmushi tadan saki.



"Ki je ki ci abincin ki" 


 Cikin sanyin murya ta amsa mashi da toh.



Bayan fitar Zeenatu daga dakin Ya maida hankalinsa akan Benazir, A baki ya soma bata abincin tana ci, sai kallon shi takeyi har saida Ya tsargu da kallon Yace"Akwai wani abu ne"? 

"Yaya shureim dan Allah ka taimaka ka kaini gidansu Anila Inason ganinta."


"Da yaushe"? 

"Ko yanzu kace sai in shirya mu tafi"

"Kin fada mata ne"?

Shiru tayi jim don rabon da suyi waya da Aneelerh kusan two weeks babu wanda ya tuntubi wani amma saboda tana son Taje din yasa tay mashi karyar sunyi waya harma ta fada mata zasu zo

Yace toh idan sun kammala Cin abincin zai kai ta.

Dadine Ya lullubeta bayan sun gama cin abincin,  Ya fita don yaje ya shirya

Jikinta na rawa ta dauki waya ta danna ma Anila kira, don ta sanar da ita batun zuwansu, almost 3 times tana doka mata kira ba'a picking a karshe ta hakura da kiran nata ta fada toilet don tayi wanka.

*DAGA ALƘALAMIN BOSS BATURE🔥✍️*

*Game bukatar karanta littafin kurkukun kaddara, 500 ne za'a tura Via Opay, 8103884440 Hafsat Bature Muhammad, shaidar biya za'a tura ta whatsapp, 08169856268 ko 08103884440*

2 Comments

Idan kuna da tambaya akan abinda Baku game ba ko kuma kuma Neman littafin da babu a nan kawai ku ajiye tambayarku a ta comment ko wani shawara da Zaku bamu.

Previous Post Next Post

Sponsored Link

Sponsored Post