Kurkukun Ƙaddara Takun Ƙarshe page 61 Complete by Boss Bature


Health College

Kurkukun Ƙaddara Takun Ƙarshe page 61 Complete by Boss Bature

Takun Ƙarshe

Zaune yake a mazaunin driver na motarsa, ita kaɗai ya ke jira su tafi, har ya fara gajiya da jiran ta, wayarsa ya zaro daga front pocket din rigarsa ya danna mata Call.

"Idan kika ƙara minti ɗaya baki fito ba zan koma ciki ne." Yana fada yayi rejecting call ɗin, jingina kanshi jikin headrest ya yi tare da lumshe idanun shi.

Sam bai ji tahowarta ba, sai dai ya ji motsin buɗe cardoor din, buɗe idanunsa yai tare da kallon ta baki a buɗe ganin yadda ta ca6a ado kamar wadda zata je gidan surukanta, Wani hadadden Code lace ta saka orange riga da skirt sun ɗan kama jikinta, mayafin kayan a kafaɗa ta daura shi, ga wani hadadden daurin dan kwali da ta yi, baƙar sumar kanta ta sauko har mid back dinta, fuskarta ta sha make up....,sunkuyar da kai ƙasa ta yi ganin kallon da Dr Shureim ɗin ke yi mata. 

"Benazir, wa ki kai ma kwalliyar nan? sai ka ce wadda zata je bikon mijinta?" Tuntsirewa ta yi da dariya, ta yi mamakin jin ya canki abunda ta shirya, don wannan kwalliyar da ta yi saboda Taj ta yi ta, yau ta ɗaura ɗamarar janyo hankalin shi gare ta.




"Zai iya yiwuwa."


ta faɗa tana sakin murmushi, ta6e baki ya yi tare da ɗan girgiza kan shi ba tare da ya kawo komai a ransa ba, Kafin ya yi wa motar key a hankali ya yi reverse, a tsanake Ya ke yin driving ɗin su...


"Zeenatu ta ganki da zaki fito daga gidan?"


Ya tambaya yayin da yake juya sitiyari.


"Eh, amma bata nuna zata bini ba, naji tace zata bi Aunty Sarah Office, may be shiyasa bata damu  da ta biyo mu ba."


Tafiyar mintuna ƙalilan Suka ƙaraso layin su Aneelerh, Bayan Baba mai Gadi Ya buɗe masu gate Dr Shureim ya shigar da motar ciki, a parking space ya dakata.


"Mu shiga ciki" Girgiza kai ya yi, "ki fara shiga zan shigo daga baya" amsa mashi tayi da toh,


Fitowa ta yi ta nufi cikin gidan, bakinta ɗauke da sallama ta shiga...


"Muryar wa nake ji kamar Benazir?" Murmushi ta saki tare da sauke idanunta akan Mami da Ummi dake zaune a falo suna kallo a tv, gaba ɗaya suka ɗago suna kallonta bayan sun amsa sallamar da ta yi...


"Wlh ni ce Mami, na yi maku zuwan bazata ban kira na faɗa ba" ta fada tare da karasawa ta dan duƙa gaban sofa ɗin da suke a zaune ta gaishe da su.


"Ina wuninku, fatan na same ku lafiya"


A tare suka haɗa baki "lafiya lou, ya mutanan gidan naku?"


"Suna nan lafiya, Sun ce agaishe masu da ku."


"Ina Zeenatu da Shureim namu"? A cewar Mami,


"Yaya Shureim shi ya kawo ni, yana a waje, shi ya ce in fara shugowa zai biyo ni, mun baro Zeenatu a gida za su je office tare da Mommynta."


Mami tace"Allah Sarki, na ji kin ce kin yi zuwan bazata baki kira kin fada ba, nan ay kamar gidan ku ne Benazir, naji dadin zuwanki..." Still fuskarta dauke da murmushi..


Ummi ta ce"Ga mutuniyar taki can, ta ɗaura aure da zaman ɗaki, dan Allah Benazir in kin shiga ki yi kokarin kwantar mata da hankali, kwanakin nan mun rasa gane kanta," 


"Bata da lafiyane?"


Mami ta ce, "Hmmm, ta sanya damuwa a ranta ne, wai kwanakin nan tana yawan yin mafarkin su Uzair shine fa duk tabi ta hana kanta sukuni..."


"Subhanallah!" Fuskarta da damuwa ta faɗa tare da miƙewa ta nufi dakin Aneelerh..


A bakin kofar dakin ta tsaya, kusan sau uku tana doka mata sallama shiru ba'a amsa mata ba, har saida ta fara gajiya da tsayuwa, a ƙarshe ta yanke shawarar shiga ciki.


Tana Shiga idanunta suka sauka akan Aneelerh dake a kwance kan gado, ta ƙurawa Ceiling idanunta ko kyaftawa bata yi, lamarin ya daurewa Benazir kai, a ranta ta ayyana wannan wata irin damuwace da zata sa aita maka sallama baka ji?


Ta karashe zancen zucin tare da kai hannu saman kafar Anila ta 6aka mata bugu, wata irin zabura ta yi, a firgice ta miƙe zaune tana zare idanunta muryarta na rawa ta furta,"Na shiga ukuna!" hannunta ɗaya dafe  da saitin zuciyarta.


 Hankalin Benazir ba karamin tashi ya yi ba, ganin yadda Aneelerh ta rame kwata kwata bata a cikin nutsuwarta. 


"Ni ce fa..." Nannauyar ajiyar zuciya ta sauke lokacin da ta sauke Idanunta akan Benazir don sam bata lura da ita ba.


Numfashi ta dan ja tare da sauke ajiyar Zuciya ta ƙaƙaro murmushi kan fuskarta..


"Benazir ke ce? Meyasa baki fada min zaki zo ba?" Bata tanka mata ba har saida ta samu guri ta zauna daga gefen gadon kafin ta maida hankalinta kan Aneelerh.


Duk tabi ta dabarbarce ganin irin kallon da Benazir ke yi mata, washe baki ta shiga yi tana kokarin danne damuwarta ta ce, "Sannu da zuwa Benazir, ya ki ke? Ya su Mami? Ina ya Shureim da zeenatu?"


Cike da damuwa Benazir ta furta, "Don Allah meke damunki haka Aneelerh? sau uku ina doka sallama baki amsa ba, nama yi zaton kin shiga toilet ne ko bacci kike yi, ashe idonki biyu kina a kwance kin takura kan ki, why pls dubi yadda kika rame? Fuskarki duk ta yamutse kamar wata tsohuwa" Ta fada tana ƙare mata kallo..


A rude Anila ta girgiza kai muryarta da in-ina ta ce,"Lafiyana lou ba abun da ke damuna..."


Kaitsaye Benazir ta ce, "ƙarya ne wallahi, Dole akwai abunda ke damunki sai dai idan baki son fadamin ne."


Murmushi ta dan yi,"Bafa wani abu bane, kawai ina yawon yin mafarki akan Uzair...." tunkan ta kare maganar Benazir ta tari hanzarinta, "Mami ta faɗa min hakan, amma ban yarda ba Anila, Look, nifa nasan wacece ke, mafarkin Uzair bazaisa ki shiga damuwa har haka ba, bayan kinsan mafarki ba gaskiya bane, in ma hakanne a yadda nasanki da tawakkali Addu'a zaki dage kina cigaba da yi masa bawai ki tsananta damuwa ba, kawai ni yanzu ki fadamin meke damunki kinsan tsakanina dake babu 6oye-6oye, Kinsan sirrina nasan naki, kuma dai abokin kuka shi ake fadawa mutuwa, pls In har kin yarda da ni...." 


Shiru Anila ta yi jim tana tunanin kodai ta fadawa Benazir watakil ta taimaka mata su nemi mafita, ruƙo hannayen Benazir ta yi acikin nata, suka ƙurawa juna ido..


A hankali hawaye suka fara zarya kan kuncin Anila, hakan ba ƙaramin ɗaga hankalin Benazir ya yi ba.


"Zan fada maki saboda na yarda dake, amma dan Allah ki rufa mini asiri Benazir, bana so kowa ya sani mu barshi a matsayin sirri tsakanina da ke.." A ƙagare Benazir ta jinjina mata kai. 


Nan take Anila ta fayyace mata komai, tun daga ranar da suka je gidansu Hajiya Adama da abunda ya faru bayan dawowarsu game da 6atan Ana, da inda suka ga Baby Junaid a sume cikin drawer shelve da yadda Junaid ya burkice masu suka rasa gane kanshi, komai saida ta sanar da ita, har wayar Ana ta curo daga cikin pillow case ta kunna mata videon ta mika mata don ta gani da idanunta.


tunkan ta Ƙarasa kallo yatsun hannunta keta kerma kamar wayar zata kife kasa, idanunta azazzare cike da tashin hankali ga wani irin faduwar gaba da take ji, labbanta na kerma take ambaton Inna lillahi wa'inna ilaihirraji'un, Allahumma ajirni fi musibati wa'akhlifni khairan minha..., bata ƙare sallallamin ba Anila ta yi saurin toshe mata bakinta da tafin hannunta gudun kada wani ya ji yo su.


Tuni hawaye sun wanke fuskar Benazir, Sai faman girgiza kai ta ke yi.


Cikin muryar rada Anila ta ce,"Allah abun tsoro dan adam abun tsoro, muna nan sake da baki ashe muna a tare da mugun iri acikin mu! Benazir ki fada min taya hankalina zai kwanta? Wai Uncle dina shi ne yake aikata wannan fasikancin a cikin gidan nan? Babban tashin hankalina Ina Ana? Yau kusan wata uku babu ita Benazir, ina jin tsoron ace ya kashe ta...." Ta fada tana kuka ƙasa kasa.


A hankali Benazir ta zame hannun Anila data toshe mata baki da shi.

Hawaye wasu na bin wasu akan kuncinta ta ce, "Anila dama Ana ta 6ace shine baki fadamin ba tun lokacin da abun ya faru?"


"Na yi zaton da son ranta ta gudu shiyasa ban fadamaki ba saboda na saka ran zata dawo." 


Jinjina kai Benazir ta shiga yi.


"Mugu bashi da kama Anila, munafuki kamar na Allah, wlh bazamu kyale shi ba, dole mu ƙwatarwa Ana hakkinta sannan mu maka dan iska gurin hukuma...." 


bata kare maganar ba Anila ta yi saurin katse ta, "Pls ki daina ɗaga murna bana so wani ya ji, yanzu me yakamata mu yi? Kin dai ji ta ce mutunne mai hadarin gaske in har muka yi kuskuren da maganar ta koma masa zai iya salwantar da rayuwarmu tunda ba imanine da shi ba, Allah kaɗai ma yasan munanan ayyukan da yake aikawata bayan wannan da Ana ta fada."


Jinjina kai Benazir ta yi yayin da kwakwalwarta ke tariyo mata abubuwan dake faruwa da ita a gidan Uncle Musa, yunƙurin kashetan da ake yi ga kuma kurciya da aka yi mata, tun rana ta farko da aka fara yi mata take zargin akwai wanda ke bibiyar rayuwarta.


Anila da ta zuba mata ido ganin ta yi shiru bata da niyar yin magana yasa ta dafa kafadarta, "Benazir kin yi shiru ba ki ce komai ba?" Numfasawa Benazir ta yi kafin ta ce, "Aneelerh, akwai damuwa, nima fa akwai wanda ke bibiyar rayuwata a gidan Uncle Musa, kusan sau hudu ana yunkurin kashe ni....." 


Waro idanu waje Anila ta yi, cike da ruɗani  take kallon Benazir ya yin da gabanta ke faduwa rass rass!!!


Nan Benazir ta labarta mata komai da ya faru da ita tun farkon zuwanta gidan..


"Aneelerh wallahi ba don Allah yana kawo min ɗauki ba, da tuni an jima da kashe ni, don ma yanzu babu tabon yatsun hannun mutumin a wuyana ya goge dana nuna maki kin gani"


 Hankalin Anila fa ya tashi sosai, duk tabi ta rude, "Benazir! anya ba iska bane? In ba haka ba wanane zai yi maki hakan agidan Uncle Musa? Gidan dake a tsare da Security Officers taya wani bare zai iya shigowa har dakin ki ya yi yunƙurin kashe ki??" ta fada tana zare idanunta...


Girgiza kai Benazir tayi, "Wlh Anila ba iska bane, mutunne! Abunda yasa na kara karfafa zargina saboda abu biyu, na farko kurciyar da aka yi mini! Aka rabani da dangina, Na biyu labarin da Ana ta bada, Shine ma ya farfaɗo da tunanina, koma wanene mutunne kuma yana amfani da sihiri kamar yadda Ana tace Uncle ɗan-iya yana amfani da sihiri gurin sarrafa ta"


Da ƙwarin gwiwa ta yi maganar tana duban Anila wadda gaba daya ilahirin jikinta rawa yake yi kamar mazari.


"Ina zargin mutumin da yayi min kurciya shine yake son kashe ni.."


 Cikin shesshekar kuka Anila tace, "Inna lillahi wa'inna ilaihirraji'iun! Banazir mun shiga Uku! Wanene wannan? Laifin me ki ka yi masa da ya ja har ya ke son raba ki da rayuwarki? Wai dan Allah meyasa hakan ke faruwa da rayuwarmu? Daga wannan sai wannan?"


Maganar Anila ta sake tuna mata abunda ta faɗa mata game da Taj, cikin saurin ta ce, "Anila! Kinsan tunanin da nake kuwa??" Girgiza kai tayi da sauri, "A'a." 


Gyara zama Benazir ta yi,


A labarin da kika bani na abunda ya faru da su Uzair, kin tuna Alhazawan da suka yi ma leƙen asiri? Har suka rikiɗa suka handame uba da ƴa'yansa saboda yayi masu leƙen asiri...?" Cikin sauri Anila ta jinjina kai,"Kwarai kuwa haka ne!"


"To baki tunanin ko halin da nike ciki nada alaƙa da hakan, sai nike ganin kamar idan muka fada ma Taj komai zai taimaka masu gurin yin binciken da su ke yi akan Alhazawan nan da kuma 6atan Uzair?  Kuma kinga Taj yanzu jami'e ne shi, sannan yana a gidan Director General In har muka je masu da maganar wallahi ina mai tabbatar maki zasu dauki mataki akan Uncle dan-iyan, tunda su jami'ai ne sun fi mu sanin ta yadda zasu bullowa lamarin, ko ya kika gani?" wata irin nannauyar ajiyar zuciya Anila ta sauke, Wlh sham ta shafa'a ta manta da cewa Taj jami'in bincike ne ai da tuni ta sanar da shi komai.


"Ban ta6a sanin ni shashasha bace sai yau da kika ankarar dani, Mu da muke da jami'i a hannu, Wlh gaba ɗaya kaina ya kwance tsawon kwanakin nan inata neman mafita, kwata kwata tunanina bai bani in tuntubi taj ba, nama manta da cewa shi jami'i ne sai yanzu da kika tuna min." 


Murmushi suka sakar ma Juna.


"Yanzu ya za a yi? Babu buƙatar 6ata lokaci, da zafi zafi ake bugun ƙarfe, ƙwara muyi amfani da damar da muke da ita tunkafin lokaci ya kure mana" A cewar Anila.



Benazir ta ce, "Ay daga nan sai gidan DG, Nifa dama da shirina nazo wlh, na ma manta ban fada maki abunda ya kawoni ba saboda halin dana riskeki..."


"Anila kusan One month bana samun Unaisah a waya! Shima Taj kona kira baya picking? Baki ga na rame ba nima? Damuwa ce wllh, Gashi kwanakin nan sai munanan mafarke-mafarke na ke yi akanta da ni kaina, Ina ji araina kamar wani abu na faruwa da su..." 


Fuskarta a marairaice ta faɗa, Anila ta ce, "Ai bake kadai ba, Ni kaina Idan na kira bana samun su a waya, wlh hankalina ba a kwance yake ba, don ma tashin hankalin videon nan da na gani ya dauke mun hankalina almost 2 weeks ban neme su ba."


"Ba surutu yakamata mu tsaya muna yi ba, na baro Dr Shureim a waje yana jirana, ki tashi ki shirya mu tafi." 


_________________________________✍️


"Shiru Har yanzu basu fito ba," A cewar Ummi, Mami ta ce, "Kinsan ƙawaye In aka haɗu ba'a gajiya da fira,"



Ummi ta kuma cewa,"Kuma na ji ta ce ita da yayanta ne, shi ba zai shigo bane? An bar shi a waje yanata jira." 


"Nima abunda na gani kenan, bari na je na yi masu magana su je suce ya shigo." tana kokarin mikewa sai ga Benazir da Anila sun nufo falon hannunsu ruƙe cikin na juna.


 Ba zaka ta6a gane sun yi kuka ba, kowaccensu ta gyara fuskarta ko alamun hawaye babu, dubai abaya Anila ta saka ta yi rolling veil akanta ko makeup bata tsaya yi ba.


"To fa Ina zuwa kuma? Ai da yanzu nake niyyar shigowa inji me ake kitsawa ne, Kun yi zamanku shiru a ɗaki."


Murmushi suka saki, Mami ta kuma cewa, "Yakamata kuyi wa Shureim magana ya shigo ciki mana."


Sai lokacin Anila ta ce, "Dama zamu fita unguwa ne."


"Ina zaku je ne?" Kallon juna suka dan yi kafin Benazir tayi saurin cewa, "Gidan Hajiya Adama, tuntuni ni ke ta so inje Allah bai nufa ba, sai yau na yanke shawarar zan zo Anila ta rakani, dama itace ta fadamin sun dawo nan da zama...." Fara'a Mami tasaki, "Kai Amma kinyi tunani mai kyau, nima nayi kauron baki ne amma wlh abun na araina, tuntuni nike ta so in shawarci Anila ta raka ki ku je su gan ki, ni nasan zasu yi murnar dawowarki." 


Ummi ta ce, "Nifa wlh na yi zaton ma sun san da dawowarta, ashe ba'a fada masu ba, gaskiya ba'a kyauta masu ba"


"Ai yau zamu wanke laifinmu, zan basu mamaki, har gida zan kai masu Benazir" A cewar Anila, dariya su ka yi, Mami ta ce, "Ku tafi yana ta jiranku gashi ko ruwa ba a kai mashi bama, in kun isa ku gaishe mana da su, sannan kada ku daɗe dan Allah, zan ma kira Abie dinku in faɗa masa"


"Zasu ji, in sha Allah bazamu dade ba." 


A bangaren Dr Shureim, har ya gaji da jiran Benazir jin shiru bata fito ba, buɗe motar ya yi tare da fitowa da niyyar ya bisu, ƙarar horn din motar da ya ji ne yasa shi ɗan dakatawa ya juya yana kallon motar dake kunno kai cikin gidan.


Ta gaban shi motar ta wuce ta yi parking a gaban entry hall, bayan ta kashe motar ta fito tare da zagayawa other side din motar ta buɗe backseat, ta ɗauko baby Junaid dake ta sharar bacci jikin shi sanye da uniform dinshi, dayan hannunta ruke da food basket dinsa, Two weeks kenan da komawarsa School.


"Yaya Shureim ina wuni?" Ta faɗa da fara'a akan fuskarta,


Fuskarshi dauke da murmushi yace, "lafiya lou Zahra, ya kike? Ya gajiyar aiki?"


"Alhamdulillah, Kai kadai ka zo ne"?


"Benazir na kawo tana ciki." ya fada tare da kallon Junaid, "Junaid bacci ake yi, ankwaso gajiyar school."


 Murmushi Zahra ta yi tare da cewa, "Mu shiga daga ciki" Ta faɗa tare da yin gaba yabi bayanta, har sun kusa shiga falon sai ga Benazir da Anila sun fito suka yi kacibus da juna.



Da fara'a Zahra ta gaishe da Benazir ta amsa mata da fara'a itama akan fuskarta.



"Aunty Benazir why zaki bar ya Shureim a waje fisabilillah?"


Yar dariya Benazir tayi, "Bafa ni na hana shi shigowa ba, shine ya ce in fara shiga zai biyoni daga baya."


Bayan Anila ta gaisa da Dr Shureim ta ce ma Zahra unguwa zasu fita, ta kula da Junaid, sai zuwa anjima zasu dawo."


Bata nemi sanin inda zasu je ba ta ce, "Allah ya dawo daku lafiya." 


Suka amsa da ameen, bayan Zahra ta shige ciki Dr Shureim ya dubesu da dan mamaki yace"Bangane ba! ina zaku je ne?"


"Yaya Shureim mu je zamu faɗa maka."


Bai yi musu ba suka nufi motar, bayan duk sun shiga ya tasheta suka tafi. 



_____________________Obie Estate🔥



Koda suka ƙaraso main gate na estate din basu sha wahalar shiga ba, Security Officers basu dakatar da su ba, Saboda sun gane fuskar Anila kuma tayi masu bayanin cewa gurin Hajiya Saratu suka zo, suna jin hakan suka basu permission din shiga.


Bayan Motar su ta shiga cikin estate din kaitsaye suka nufi villa ɗin Owais, Tunkan su ƙarasa Security Officers din dake tsaron gate din suka nufo motar hakan yasa Dr Shureim yin packing din ta.


Officers shidda ne suka yiwa motar tasu ƙawanya,


Knocking window glass din aka yi, "Get out of the car!" ɗaya daga cikin su ne ya umarta.


Bayan sun fito suka fuskance su.


"Su wanene ku? Daga Ina kuke? Wa kuka zo nema?"


Da hannu Dr Shureim ya nuna Benazir da Anila, "Ai sai ku yi masu bayani, Ni dama ban so zuwa ba, don nasan ba lallai mu samu shiga ba, amma  kuka matsamin, yanzu ba ga irinta nan ba." ya faɗa fuskarsa a haɗe don shi baya son abunda zai haɗa shi da masu kaki...


"Ki kira Taj din a waya, Ni nasan kona kira ba lallai ya ɗaga ba."


Benazir ce ta faɗa idanunta akan Officers din da suka zuba mata ido har saida Dr Shureim ya ankara da mayataccen kallon da suke binta da shi, ransa ya 6aci cikin harshen larabci yace ta lullu6e jikinta da mayafinta.


Da sauri ta gyara mayafin ta lullu6e kirjinta da kanta sa6anin da da yake akan kafadarta, duk da haka basu daina kallonta ba, ta ji haushi ita da ta yi kwalliya don Taj ya gani sai gashi wasu na nema su riga shi gani.


Almost 3 times Anila tana doka masa kira baya picking, hankalin su ba ƙaramin tashi ya yi ba.. 


"Ya zamu yi Benazir! Ya ƙi ɗagawa wlh"


"Keep trying, idan ba haka ba wadannan masu fuskar shanun ba bari zasu yi mu shiga ba."


Cikin harshen larabci ta yi maganar..


Murmushi Dr Shureim ya yi tare da ɗan girgiza kanshi jin abunda yar'uwarsa ta fada, jami'an kuwa sun baza kunne da yake ba arabi da ace da hausa ko da turanci ta fada da taci na jaki.


Taj na ƙoƙarin fitowa daga toilet yana ta gungura wheelchair dinsa ya jiyo muryar Batool tana kwaɗa masa kira,"Daddy, wayarka tana ringing, wani ne ke kiranka" 


Har ya nufi ƙofar dakin sai gata ta faɗo ko sallama babu, tana ta haki ta miƙa masa wayar tana fadin, "A falo ka barta saman hannun kujera." 


Bai kar6i wayar ba sai cewa ya yi ta karanta mashi sunan me kiran, ɗan zare ido ta yi kafin ta dubi sunan da ya bayyana akan screen din wayar.


"An..An..Antin Yu.. nai..sah.." daƙyar ta ƙare karatun a lokacin har kiran ya katse, Murmushi Taj ya sakar mata, "Auntyn Unaisah ne, kin yi kokari daughter, Allah ya yi maki albarka."


Ya faɗa tare da kar6ar wayar, sai faman sakin murmushi ta ke yi, tana son taji an yabeta in ta yi abu.


"Ina ƴar uwar taki ne?"


"A ɗaki na barota kudundune cikin bargo."


"Bacci ta ke yi ne?"


Girgiza kai ta yi, "Waya ta ke yi da Chief, Daddy baka ji yadda take kashe mishi murya ba hada shagwa6a fa," fashewa yayi da dariya har fararen hakoransa suka bayyana.


"Shaƙa mini in ji me take ce masa?"


 Da biyu ya yi maganar saboda yana son yadda Batool take kwaikwayon maganar Angel dinsa, aiko da yar shagwa6a ta ce, "Shine ka tafi baka jira na tashi daga bacci ba, pls kada ka daɗe ka dawo gida bazan jure zama batare dana sanyaka a idanuna ba" 


Tuntsirewa Taj ya yi da dariya, Itama dariyar ta kama yi yadda kasan uba da ƴarsa.


"Daddy, ka ji daɗi?" Ɗaga mata kai ya yi, "Sosaima, kema da kika bani labarin ga wannan" Ya fada tare nuna mata robar peanut  din da ya aje kan drawer bai kaiga fara ci ba, da sauri taje ta dauka tare da yi ma shi godiya.


Fitowa ta yi daga ɗakin jikinta a sanyaye, kwata kwata babu walwala, a saman stairs ta zauna hawaye cike tab da idanunta take kallon Peanut din da daddy Taj ya bata, A hankali ta soma ɗebowa tana afkawa a baki tana ci, hawaye na sintiri kan kuncin ta, Allah kaɗai yasan me ke damun ta.


Fitar Batool ke da wuya, wani kiran na Anila ya sake shigowa wayar tasa, picking ya yi tare da kara wayar a kunne.


Bayan sun gaisa ne Anila ta fada masa gasu a bakin gate na gidan security sun hana su shiga ya taimaka ya yi masu hanya su shigo.


Shiru ya yi yana tunanin hanyar da zai dakile shigowarsu saboda baya son suga halin da yake a ciki, ga Chief ma baya nan, bayan haka ba'a son ma kowa yasan wani abu dangane da farmakin da suka kai, in har su Anila suka gan shi zaune kan wheelchair dole hankalinsu zai tashi harma su nemi jin me ya faru da shi..


"Taj na ji ka yi shiru baka ce komai ba?" Muryar Anila ce ta katse tunanin da ya ke.....

Muryarsa a dabarbarce ya furta, "Anila meyasa baki kira kin fadamin zaku zo ba?"


"Banyi tunanin yin hakan ba, saboda na ga Almost weeks kona kira bana samunka."


"Anila, sai dai ku yi hakuri ku koma gida, yanzu bama nan mun je yin meeting a headquarter ɗin mu." 


On the Other Hand Anila ta zabga salati tana fadin, "Inna lillahi wa'inna ilaihirraji'un, dan Allah Taj ka taimaka ka bada iznin a barmu mu shiga ciki, wlh zamu jira har zuwa lokacin da zaku dawo gidan, Don Allah Taj, wlh wani abune mai mahimmanci ya kawo mu, It's urgent, please help." 


Ta fada tana kallon Benazir data yamutsa fuska kamar zata sanya kuka.


Shiru Taj ya yi yana nazarin maganarta, tun daga kan yanayin muryarta ya fahimci da akwai wani abu da ya kawota gidan,


"Okay, ku ɗan jira" 


Ta amsa mashi da toh, rejecting call din ya yi, ya shiga tuntu6ar layin Chief, almost 5 times tana ringing bai yi picking ba, ana shidda ne ya ci sa'a Chief ya ɗaga kiran..


"Yalla6ai mun yi baƙi, Anila ce tare da Benazir, Wlh bansan da zuwansu ba saboda basu faɗamin ba, sai dai kawai ta kira a waya ta fadamin suna a bakin gate an hanasu shigowa, wlh da nasan da zuwan da bazan bari suzo ba, amma na ji Anila tace matsalace ta kawo su."


 Koda jin wannan maganar Chief ɗin ya ce zai yi magana a basu iznin shigowa ciki.


Godiya Taj ya yi masa bayan sun yi sallama, ya zura wayar Cikin aljihun jallabiyar sa. 


A hankali Motar Dr Shureim ta karaso cikin parking space, bayan ya tsayar da ita. suka fito daga ciki, kallon kallo Benazir da Anila suka jefawa junan su.


"Yaya Shureim ko zaka jira mu anan?" Benazir ce ta yi maganar saboda basa son su shiga dashi ba don komai ba sai don kada su ƙetare iyakarsu ga kuma gargadin da aka yi masu.


"Ba damuwa, ku shiga zan jira ku, but pls kada ku daɗe." 


Amsa mashi su ka yi da toh kafin suka nufi main door na falo, suna ƙarasawa ƙofar ta zuge suka shiga bakinsu ɗauke da sallama, wani sanyayyan sanyin Ac ne na daban ya ratsa fatar jikinsu har wani lumshe idanu suka yi.


Time da suka buɗe idanun nasu kaitsaye suka sauka akan Taj dake a zaune kan Sofa ya nutsu yana jiran ƙarasowarsu, Ba zaka ta6a gane yaji rauni a cinyarsa ba saboda ya lullu6eta da jallabiyar jikinshi, Sofa ɗin ma daƙyar ya samu ya yi dubarar da ya zauna akanta, da ɗayar ƙafarsa me lafiyan ya tura wheelchair din ta koma tsakankanin sofas saboda baya son su ganta.


Ta wutsiyar idanunshi ya ke hangosu yayin da suke nufo shi.


Anila ta yi mamakin ganinsa bayan ya ce mata basa nan ashe yana nan, komi yasa ya boye mata da farko? Ta ayyana a cikin ranta.


 Har saida suka ƙaraso kafin ya ɗan ɗago da niyyar ya kallesu karaf idanun shi suka shiga cikin na Benazir, har saida ya ɗan ji gaban shi ya faɗi saboda kyan da ta yi ma shi, amma da yake namijin duniya ne sai ya haɗe rai tare da kawar da idanun shi.


Murmushi Anila ta yi kafin ta gaishe shi ya amsa mata fuskar shi asake.


Cikin sanyin murya Benazir ta gaishe da shi a daƙile ya amsa mata..


"Ku zauna." 


A kan Sofa mai mazaunin mutun uku suka zauna suna fuskantar shi....


Gaza jurewa Benazir tayi idanunta cike tab da ƙwalla ta ambaci sunan shi"Taj!" Shiru bai tanka mata ba..


"Nasan har yanzu fushi kake dani, amma meyasa idan na kira baka picking? Har saƙo na tura maka akan ka taimaka ka haɗani da Unaisah saboda idan na kira bana samun layinta amma kwata kwata ba response..."


Hannu ya ɗaga mata tuni ta haɗiye maganarta, "Dama wannan ne abun da ya kawo ku?"


Ƙasa-ƙasa da murya Anila ta raɗa mata "pls ki aje wannan maganar gefe, ki yi haƙuri mu yi abinda ya kawo mu, kinga daƙyar muka samu aka bamu damar shigowa ciki." Jinjina mata kai ta yi alamar ta gamsu.


Mayar da dubanta ta yi akan Taj, "Dama issue ne akan yar aikin gidan mu Ana data 6ace yau wata Uku kenan."


 Jin wannan maganar Yasa Taj ya maida hankali akan Aneelerh.


Dakatawa ta ɗan yi ganin kuku ya nufo su hannun shi ruƙe da wooden tray na fruit da cool drinks ya ajiye masu kan table, bayan ya tafi Aneelerh ta cigaba da zayyana masa komai da ya faru har izuwa kan videon da ta gani...." tunkafin ta kai ƙarshen zancen yanayin fuskar Taj ya sauya zuwa tsantsar mamaki, tashin hankali da kuma ruɗani...


"Zan iya ganin Videon??"


Da sauri tace "Eh," Ta faɗa tare da zaro wayar daga cikin handbag dinta ta shiga  pressing dinta, bayan ta kunna masa video ta miƙe taje gaban shi ta miƙa ma shi.


Bayan ya kar6a, lokaci ɗaya hankalinsa ya tashi matuƙa, saboda tsabar girgiza da kidima duk da sanyin A.c din falon saida ya fara zubda gumin zufa lamarin ya ɗaure masa kai, Lallai sun zo da case mai girma, abun da ya ɗan jefa shi a rudani a bayanin Ana ya fahimci shi Uncle ɗin Anila matsafine kuma abun da yake yi ma Ana yayi kamanceceniya da cin zarafin da Elders su ke yi wa prisoners a lokacin da suke yin jinin al'ada.


A dabarbarce ya furta, "Anila dama Ana tana nan?"


Idanunta cike tab da ƙwalla tace, "Eh, atare da ita muka dawo gidan Uncle din" 


Jinjina kanshi ya yi Idanunshi sun kaɗa sun ɗan yi ja,


"Ku sha lemun" Ya faɗa yana nuna masu drinks din..


Miƙa hannu Anila tayi ta dauki Juice ta tsiyaya masu a glass cups, saboda dadin da ya yi masu kusan duka suka shanye..


"Tanimu Ja'afar Falgore, inkiya Ɗan-iya shine full name na uncle dinki ko?"


Ya tambaya yana kallon Anila, Jinjina mashi kai ta yi alamar eh, a ransa ya furta karen yan siyasa zai aikata fiye da hakan, ya ƙarashe zancen zucin nashi tare da aje wayar Ana a gefen sa.


Har ya zaro waya zai dannawa Chief kira maganar Anila ta dakatar da shi...,


"Benazir na ji kin yi shiru baki ce komai ba? ba zaki fada masa abunda ke faruwa dake ba?"


Cikin karyayyar murya ta wanda ke shirin saka kuka tace,"Ba ki ga ko kallona bai son yi ba, Even if I tell him, he won't take me seriously."


A hankali Taj ya dubi Benazir da tayi maganar, idanuwansu suka shiga cikin na juna, da sauri ta kawar da nata idanun gefe ɗaya.


"Ina sauraronki! Faɗamin me ke damunki?" Wani sanyi ta ji ya ratsa zuciyarta jin ya kula ta, aikuwa ta gyara zama ta fara labarta masa abun da ke faruwa da ita, nutsuwa ya yi yana sauraronta, dan dakatawa ta ɗan yi tana haki kamar wadda tasha gudu.


Da hannu ya nuna mata Mineral water,"Ki sha" da sauri ta dauka ta ɗan kur6a.


Bayan ta ajiye taci gaba da bashi labari..


*bari mu koma baya don jin meya faru a ranar da Benazir ta dawo daga gidansu Anila bayan ta fada mata komai dangane da batansu Angel harta kulle kanta a daki, a ƙarshe da aka bude dakin aka iske ta kwance a ƙasa rabin jikinta a cikin toilet👇*



Bayan da ta gama shan kukanta tamkar ranta zai fita, lokaci ɗaya ta fara Jin azababben ciwon kirji, tana jiyo bugun kofar da suke yi mata haɗi da yi mata magiya akan ta bude amma taƙi saboda bata son ganin kowa a kusa da ita, a kan floor ta kwanta tana cigaba da sharar ƙwalla.


"Pls idan kina saurarena ki tashi ki kunna karatun alkur'ani kada ki kwana a haka, yakamata ki yi hada nafila..." Muryar Dr Shureim ta jiyo acikin kunnanta.



Daƙyar ta iya tattara ƙarfin da ya yi saura a jikinta ta mike ta nufi toilet don tayi alwala kamar yadda Dr Shureim ya shawarce ta.


A gaban sink ta tsaya tare da kunna faucet, ta soma yin alwalar sai dai  gaba ɗaya hankalinta baya a tare da ita, ta lula duniyar tunanin ina zata ga Taj da ƴarta? Tana tsaka da yin alwalar hasken electric bulb din dake a saman ceilling ya fara wasa ya kawo ya dauke, bata kawo komai aranta ba ta yi tsammanin electricity din gidan ne ya samu matsala, hakan yasa taci gaba da yin alwalarta.


Bata yi aune ba, unexpectedly glass din madubin da take fuskanta ya fara tsattsagewa, a razane ta ƙura ido tana kallon abun mamakin gani take kamar idanunta ne ke nuna mata ba dai dai ba, dama bata a cikin hayyacinta damuwa ta fara zautar da ita, miƙa hannu ta yi da niyar ta shafa madubin don ta tabbatarwa kanta abunda take gani gaske ne ko ƙarya kwatsam! madubin ya tarwatse da kan shi glass din ya zubo kan floor, har ta kware baki zata fasa ƙara ta ji an fusgo hannuwanta izuwa cikin madubin, ta ƙarfi da yaji ake kokarin janta cikin shi, fashewa ta yi da matsanancin kuka na tashin hankali ta dinga yan buge-buge tana ƙoƙarin kufcewa yayin da hannayen da suka rurruke nata suka ja kusan rabin jikinta cikin madubin, daddagewa tayi da iya ƙarfinta na ƙarshe ta shiga karanta ayatul kursiyu bata kaiga direta ba ta ji an wurgo da ita gaba ɗaya gangar jikinta ta dawo cikin toilet ɗin kanta ya daki floor, A zabure ta miƙe ta watsa a guje ta nufi ƙofa sai dai me? Kafin ta ƙarasa ƙiiiii taji kofar ta datse kanta, fasa ƙara ta yi da ƙarfi take ambaton sunan Yaya shyureim dana Mommyn su don su kawo mata a gaji, bugun kofar ta dinga yi kamar zata 6alle ta, gurnanin mutun ta jiyo a bayanta jiyowar da zata yi keda wuya tayi arba da wani gabjejejn mutun ƙaƙƙarfa jikinshi sanye da baƙaƙen kaya ya rufe ko'ina na jikin shi, zazzare mashi idanu ta yi kamar mai fama da farfaɗiya ta dinga farfari zuciyarta na bugawa da tsananin fargaba ta dinga sambatu tana fadin, "Na shiga Uku!!! Wanene kai? Wallahi kada ka ta6a ni, kada ka matso kusa dani, zan ƙona ka da ayar Allah..., bata ƙare maganar ba ya ɗaura gabjejen tafin hannunsa kan wuyanta ya damƙe shi ya jata tana kuka da yan buge-buge ya nufi bathtube da ita, wani irin ruwan zafi ne ya kwararo ta cikin faucet har tiriri yake yi kamar za'a zabka kaza haka ya soma ƙoƙarin tura kanta cikin ruwan, wanda hucinsa kaɗai bala'e ne tsaf zai ƙona fatar mutun, fashewa tayi da kuka tana ihu ga bleeding da hancinta ya fara yi,


 Sai yakushin hannunshi take yi don ya saketa, yana gab da zai tsumbula kanta cikin ruwan, ta furta wata addu'ar neman tsari da Dr Shureim ya koya mata, wallahi ko second ba a ƙara ba mutumin ya 6ace 6aat hasken toilet din ya daidaita, madubin ma ya maida kansa yadda yake, hannunta dafe da wuyanta dake mata raɗaɗi take kallon Ikon Allah, Wato addu'a tayi a rayuwa musamman in kayi imani ba tare da kokwanto ba, ganin ya 6ace yasa ta zabura aguje ta nufi kofar toilet ɗin ta dinga bugunta daƙyar ta samu ƙofar ta buɗe sai dai kafin ta fuce wani irin jiri ya ɗebeta gaba ɗaya ta yanke jiki ta faɗi yaraf har goshinta ya fashe sakamakon dakar floor da kanta ya yi. 


Hankalin Anila dana Taj ba ƙaramin tashi ya yi ba, Sun yi matuƙar girgiza da jin abunda ke faruwa da Benazir.


"Kin taba faɗa ma wani?" Ɗaga kai ta yi,"Eh, Yaya Shureim ne kadai ya sani, amma ban faɗa masa na ranar dana shiga toilet ba saboda ban farfado cikin hayyacina ba.


Cike da al'ajabi yake ɗan jinjina kanshi yayin da zuciyarshi ta cika fam da tashin hankali, Komai da suka faɗa yayi shige da case din da suke aiki akai, yanzu ya fara yarda da abunda Anila ta faɗa masa akan Benazir.


Chief ya kira bayan ya yi picking gaba daya ya fayyace masa abun da su Aneelarh suka sanar da shi, tashin farko ya ce wannan babban al'amari ne, kuma ya ji dadin zuwan su, in ba damuwa su jira shi ya dawo yana son yin magana da su.


Ɗagowa ya yi tare da kallon su Aneelerh, "Ya buƙaci yana son magana daku, zaku iya jira har lokacin da zai dawo?"


Aneeleerh ta ce, "Ba damuwa zamu jira shi"


Faɗa mashi ya yi kafin su ka yi sallama ya aje wayar gefen ta Ana...


"Naga baku sha fruit din ba," Ya ɗan tambaya idanunsa akan Benazir dake ta kallon shi..


"Ni wlh hankalina kwata kwata ba a kwance yake ba, bana jin cin komai"


"Look Aneelerh, Ki kwantar da hankalin ki, tun da har ku ka yi dubarar tuntu6armu in sha Allah komai zai tafi dai dai" jinjina kai ta yi ..


"Ina su Unaisah ne?" Benazir ce ta tambaya


"Suna a daki" ya bata amsa batare da ya dubeta ba...


"Zan iya ganin ta" girgiza mata kai ya yi"A'a!"


"Meyasa? pls Taj, almost one month ban ji muryar ƴata ba? Dan Allah meyasa ka ke yi min haka? Laifin da na yi maka tsakanina da kai ne, banga dalilin da zaisa ka shiga tsakanina da ƴata ba, saboda ni na yi wahalar naƙudarta na kuma haifa maka ita..." ranta a 6ace ta yi maganar tana aika masa da harara.


"Sau nawa kina yunƙurin zubar da cikin nata don kada ya 6ata maki shape?"


Bai ƙare maganar ba Anila ta yi saurin furta, "Dan Allah Taj ku daina, ba girman ku bane, bai kamata aji maganar nan daga bakin ka ba, Benazir koda da son ranta ta gudu tabar Unaisah amma ai tayi nadama ko? Allah ma muna yi masa laifi ya yafe mana yakamata kaima ka yafe mata." 


Murmushin gefen fuska ya ɗan saki, "Ni zolayarta nake yi, amma komai ya wuce awurina, sannan ni ba hanata Unaisah na ke yi ba, tayi rashin lafiyane har kwantar da ita asibiti saida aka yi, bana so na ɗaga maki hankali ne shiyasa ko kin kira bana ɗagawa ....." 


Bai ƙare maganar ba sakamakon kalmar Innalillahi wa'inna ilaihirraji"un da Benazir ta furta tare da miƙewa tana yarfa hannu ta furta "Meke damunta ne? Wani irin ciwo ne ta yi? Don Allah ka haɗa ni da ita! Dama saida na ji a raina wani abu na faruwa da ita, har mafarkinta nake yi ashe bata da lafiya...." Ta faɗa har hawaye sun zubo kan fuskarta,


Da damuwa akan fuskar Anila ta ce, "Taj, meke damun Unaisah ne? Meyasa baka sanar dani ba?" 


"Calm down your mind, Unaisah ta ji sauƙi yanzu, bari na kirata ku gaisa."


Ya faɗa tare da ɗaukar wayarsa yana ƙoƙarin danna mata kira Unexpectedly suka jiyo shesshekar kukanta!


Kusan a tare suka kai duban su gare ta, tana a tsaye jikinta sanye da Satin fitted gown black colour tabi shape dinta, bata ɗaure sumar kanta ba,ta sake ta har mid back dinta, ƙafafunta na sanye da highhill masu ɗan banzan tsini....


Jikinta sai kerma yake yi kamar mazari, yayin da idanunta dake fitar da hawaye ta tsayar da su akan Benazir, ashe tunda Taj da Benazir suka fara sa'insa ta fito daga daki kaitsaye maganganunsu suka sauka acikin kunnanta.


"Daughter meyasa kike kuka? Ko jikin ne?" Da damuwa akan fuskar Taj ya tambaya.....


Da index finger ɗinta ta nuna Benazir,


"Dama kece mahaifiyata wadda ta haifeni a wulakance! ta barni a cikin kwamin wanka sannan ta gudu ta tafi ta barni! Dagaske kece Aunty Benazir?"


Rai a matuƙar 6ace ta faɗa da tsiwa tana fitar da numfashi mai huci.


"Ki amsa min tambayata??" Ta faɗa tana zare mata gray eyes dinta...


Tsabar ruɗu da tashin hankali ya hana Benazir furta kalma, wani irin shakkarta take ji....


"Shirun da kika yi ya tabbatarmin da abunda kunnuwana suka jiye min."


 Ta faɗa tare da maida kallonta akan Aunty Aneelerh cikin jin ƙunar rai ta ce,"Aunty Aneelerh, I know you won't lie to me tell me, who is she?" 


Yawu Aneelerh ta haɗiya ƙutt, cikin sanyin murya ta ce,"Pls Unaisah, zo ki zauna za mu yi maki bayanin komai..." 


Fashewa tayi da kuka tare da girgiza kanta, "Daddy, Aunty Aneelerh meyasa kuka 6oyemin cewa itace matar nan data gudu ta barni? Kuka sani na je nayi jinyarta a asibiti, bayan kunsan irin tsanar da tayi mini, bata taba sona ba, wallahi dana san kece bazan taba yin jinyarki ba koda zaki rasa ranki ne" with a burning heart ta faɗa tana aika mata harara.


"Why didn't you kill me at birth if you couldn't care for me? You left me in the bathtub and abandoned me for years, You never thought to return and check on the child you left behind!, wlh hakkina kaɗai bazai bari ki gama da duniya lafiya ba...." 


Bata ƙare maganar ba sakamakon tsawar da Aunty Aneelerh ta doka mata, "Unaisah ya isa! Ya isa haka!! Har yanzu ita mahaifiyar kice, karna kuskura na ƙara jin kin gaya mata maganganu marasa daɗi"


Fashewa da kuka Benazir tayi, baiwar Allah tama rasa ina zata tsoma ranta taji dadi.


"This woman will never be my mother! I don't like her, I hate her, I don't want to see her, You're heartless and don't deserve to be called a mother! Dan Allah na roƙe ki ki fuce daga gidan nan in har ba so kike ni in bar maki gidan ba" 


Cike da takaici Taj ya dafe forehead ɗinsa da tafinsa, dama saida yayi fargaban zuwan ranar nan, shi yasan za'a rina saboda Unaisah ta ƙullaci Benazir aranta, haushinta take ji sosai, tsanar ta samo asali ne tun daga kuruciyarta.


Bata saurari kowannan su ba ta juya a zafafe ta nufi kofar dakinsu, da gudu Benazir tabi bayanta ta kai hannu tare da ruƙo hannun rigarta, aikuwa cikin fushi Unaisah ɗin ta bangajeta har saida ta yi taga taga zata faɗi, cikin sauri Aneelerh da ta biyo bayanta tayi saurin tallabota.


 Rushewa ta yi da matsanancin kuka tana fadin wai ƴar da ta haifa ce ta ke gaya mata magana kamar zata doke ta? "My own daughter calls me heartless! Na shiga Uku Aneelerh ta tsaneni bata son ganina! Wayyo Aneelerh zuciyata zafi ta ke yi min..."


Gaba ɗaya hankalinsu ya tashi da abunda Unaisah ta yi, abun da ya ƙara ƙona ma Benazir rai yadda Taj ya yi banza da su ko motsawa baiyi ba daga kan kujerar da yake balle ma harta sa ran zai taimaka mata su shawo kan Unaisah, tayi masa mummunar fahimta, batasan lalurace ta hana shi miƙewa ba, dama da haushin shi aranta saboda tasan shine ya cusa ma Unaisah tsanarta acikin zuciyarta shiyasa harta ƙullaceta arai in bashi ɗin da ya fada mata ba, Uzair da Aneelerh ba zasu ta6a tona mata asiri a gurin Unaisah ba dole sai in a wurin Taj ta ji.


Bawan Allah Taj damuwa ce ƙarara akan fuskarshi, kwata kwata bai ji daɗin abun da Unaisah ta yi mata ba.


"Aneelerh, Ku dawo ku zauna, ku barni da Unaisah, zanyi magana da ita." 


Rai a6ace Benazir ta nufe shi kamar zata doke shi ta damƙi gaban jallabiyar shi da hannyenta biyu tana huci ta ce, "You caused everything Taj, I hope you're happy now, kaine ka cusawa Unaisah tsanata a cikin zuciyarta, saboda kaine ka faɗa mata cewa na haifeta nabarta acikin kwamin wanka, wai laifin me na yi maka ne? Wace irin tsana ka yi minne???"


Runtse idanun shi ya yi batare daya iya furta kalma ba, cikin sauri Aneelerh ta damƙi hannun Benazir ta soma kiciniyar 6am6are shi daga wuyan Taj, "Wai miye hakane Benazir? Idan rai ya 6aci ai hankali bai kamata ya gushe ba, Taj bazai ta6a faɗa ma Unaisah abun da ki ka yi don yasa ta tsane ki ba..."


"Ki barni Aneelerh, wlh bazan ƙyale shi ba, yadda ya saka mata ƙiyayyata acikin zuciyarta dole ya je ya saka mata soyayyata a cikin zuciyarta, saboda shine ummul aba'isin komai, wlh he must fix what he ruined." 


Ta ƙarashe maganar tare da bangaje Aneelerh, ta ƙara kakkama gaban rigarshi, ɗaurin kallabin kanta tuni ya jima da zamewa, doguwar sumar kanta duk ta hargitse kamar mahaukaciya, yana jan numfashi da ƙarfi ya furta, "Benazir ki sakar min rigata, mara kunya, har yanzu bazaki ta6a canzawa ba, tsakanin ni da ke wanene mai laifi? Da har zaki ce ni ne silar komai? Bayan kece ummul aba'isin duk wani abu da ya faru..." 


Ya faɗa yana buɗe idanunsa da suka kaɗa jawur ransa ya 6aci ganin Benazir na neman ta ɗaura masa laifi.


"Tabbas, Ni na faɗa ma Unaisah, kuma Allah shine shaidata ni ban faɗama Unaisah don ta tsaneki ba, fa ce sai don ta tausayamin ta daina azabtar da ni, saboda a lokacin da tana ƙarama mugun halinta sak irin naki ne, bata jin maganata kusan kashe ni ta yi da baƙin cikinta, kin tashi kin tafi kin barni da jinjira ke baki yi tunanin taya zan iya rainonta ba ne? Benazir in bazaki iya godemun ba bai kamata kiji haushina ba!"


 Yana huci ya ƙare maganar, fashewa tayi da kuka tamkar ranta zai fita, Still taƙi sakin gaban rigarshi.


Hankalin Aneelerh ba ƙaramin tashi yayi ba, ganin takasa shawo kan Benazir ne yasa ta watsa da gudu ta nufi hanyar fucewa daga falon don ta je ta gaya ma Dr Shureim, tasan shi kaɗaine zai iya dakatar da Benazir saboda bad temper dinta in takai maƙura a 6acin rai ko mai iskokai bazai nuna mata yadda ake bori ba.


*UMMIN AMERICA🔥*


Su biyu ne a zaune kan rug din dakinta, ita da Batool sun ƙurawa laptop screen idanunsu, wani korean drama ne su ke kallo ita da Batool, Ummi ta toshe kunnuwanta da Headset kwata kwata bata jin wani sauti daga waje saina abunda take kallo.


Batool ce ta fara jin hayaniyar mutane a cikin gidan, tun tana jin maganganun nasu ƙasa-ƙasa har ta fara ji da ɗan karfi.


"Aunty Ummi" Shiru bata amsa mata ba, bubbuga kafaɗarta ta yi, a ɗan firgice ta dube ta, "Babe lafiya?"


"Kina jin hayaniyar mutane acikin gidan nan?"


"Banji me kika ce ba," Ta faɗa tare da zame headset din ta maida hankalinta akan Batool, "Kamar wasu ne ke faɗa acikin gidan nan, naji hayaniyarsu a cikin kunnena, ki saurara ki ji" Ɗan zare ido Ummi ta yi tare da yin shiru ta kasa kunne a hankali ta fara jiyo maganganunsu...


"Su wanane? Ko munyi baƙi a gidan ne?"


Girgiza kai Batool ta yi, "Wallahi nima bansani ba, kawai yanzu na jiyo hayaniyar su kamar faɗa su ke yi...."


 Da sauri Ummi ta miƙe, mayafinta data bari akan gado ta ɗauka tare da yafa shi kan kafaɗarta...


"Ki ci gaba da yin kallon, bari na je na gano mana meke faruwa." Ta amsa mata da toh da sauri Ummi ta fuce daga ɗakin......✍️


Dira ƙafarta keda wuya unexpectedly ta tsinkayi muryar Dr Shureim a cikin kunnuwanta..


"Benazir baki da hankali ne? Meye haɗin ki da shi? Mutum da girmansa zaki shaƙe gaban rigarsa!"


 Ya faɗa yayin da yake shigowa falon cikin sauri idanunsa akan Benazir da har lokacin bata saki kwalar Taj ba, Anila tana abiye da bayan Dr. Shureim gaba ɗaya hankalinsu ya tashi sosai, batai aune ba Dr shureim Ya damƙi hannunta ya fusgeta gefe ɗaya har saida tayi taga-taga kamar zata faɗi.


Rai a matuƙar 6ace ya dubeta kamar zai kife ta da mari.


"Uban meya haɗa ki da shi? Dama dalilin da yasa kika matsamin in kawo ki gidan kenan? Saboda kawai ki tada husuma?"


Tana shessheka ta ce,"Yaya Shureim Taj ne fa, My Ex-husband, Uban ƴata dana haifa, Azeezaty itace yarinyata Unaisah....." 


A ruɗe Dr shureim yake kallon Benazir sam ya kasa furta kalma saboda yadda maganar ta dira a cikin kunnansa ta rikita lissafin kwakwalwarsa.


Juyawa ya ɗan yi tare da kallon Anila wadda jikinta keta kerma saboda fargaban kato6arar da Benazir ta yi masu, bayan irin gargadin da aka yi masu akan kada su fallasa asirin Taj yana a raye.



"Inna lillahi! Benazir meyasa kika faɗa masa? Meke damunki ne? Kin manta amana na faɗa maki, kuma kika yi alƙawarin ba zaki faɗa ma kowa ba!" Ta faɗa a faɗace kamar zata doke ta.


Taj dai tun da ya sunnar da kan shi ƙasa bai ƙara ɗagowa ba saboda halin damuwar da zuciyar shi ta shiga.


Tana kuka ta ce, "Ai wallahi ƙwara kowa ma ya san yana a raye, in ba haka ba baƙin cikin shi zai kashe ni ne! "


Gaba ɗaya Dr Shureim ya gama ruɗewa, sai faman rarraba idanunsa yake yi akan Taj da Benazir da Anila.


Dakyar ya shanye mamakinsa da wata irin raunanniyar murya ya furta, "Dan Allah ku fahimtar dani! Na kasa ganewa, shin dagaske shine Taj mijinki! Azeezaty kuma itace ƴarki Angel?"  Ya tambaya yana kallon su...


Cikin sanyin murya Anila ta ce, "Hakane Yaya Shureim." Ɗan zare idanunshi ya yi tare da maida idanunshi kan Taj da tsantsar mamaki yake kallon shi.


"Bawan Allah, ka ji tsoron Allah ka faɗamun gaskiya, da gaske kaine Taj mijin Benazir?" Jinjina mashi kai Taj ya yi alamar Eh.


Baki asake ya kuma mayar da duban shi akan su Anila kamar waɗanda suka yi ma sarki ƙarya sunyi zuru zuru...


Gaba ɗaya sun kasa furta kalma sai kallon kallo suke jefawa junansu...


"Yaya Shureim! Benazir!! Aneelerh!!!


 Muryarta na rawa ta furta sunayen su, Kaitsaye sautin muryarta ya daki dodon Kunnuwansu, wata zabura suka yi a firgice suka kai dubansu inda take a tsaye saman stairs fuskarta sharkaf da hawaye idanunta sun kaɗa jawur tamkar an watsa barkono acikin su, yanayin fuskarta ya nuna tsantsar ruɗani da tashin hankali gami da al'ajabin ganin bayin Allahn nan, Tayaya zata manta fuskokin su?  Bayan irin haddar da ta yi masu...



"Is that really you? Or am I dreaming? I can't believe my eyes!"


Tashin hankalin da ba'a saka mashi date!  Al'ajabine ya ɗaure zukatansu ya hana la66ansu motsawa sai dai idanu da suka bita da su batare da ƙyaftawa, Yau tsawon shekara goma sha takwas da ɗauriya rabon su da yar tahalikar nan tun da ƙaddara ta raba su da ita, ba zasu ta6a mantawa da Aishatu bint Sheikh Imam Malik ba! Ba zasu ta6a manta raɗaɗin da suka ɗanɗana na abun da ya rabasu da ita ba.


"Dama Kunsan Juna ne?" 


Daƙyar Taj ya furta maganar yana dubansu, yayi mamakin ganin yadda suka ƙame atsaye idanunsu azazzare kamar waɗanda suka ga wani mugun abu.

Benazir ce ta yi ƙarfin halin furta, "ƘAWATACE AMINIYATACE, ITA ƊIN TAMKAR YAR UWA TA JINI TAKE A WURINMU! YAU SHEKARA GOMA SHA TAKWAS RABON MU DA ITA, TUNDA ƘADDARA TA RABA MU❗❓


*(WAIWAYE ADON TAFIYA)*

*WACECE AISHATU BINT IMAM MALIK? MENENE DANGANTAR AISHA DA ANEELERH DA BENAZIR DA KUMA DR SHUREIM? WACE ƘADDARA CE TA RABA SU❗❓👇*

*DAGA ALƘALAMIN BOSS BATURE🔥*

*Ga me bukatar karanta littafin kurkukun kaddara, 500 ne za'a tura Via Opay, 8103884440 Hafsat Bature Muhammad, shaidar biya za'a tura ta whatsapp, 08103884440*

1 Comments

Idan kuna da tambaya akan abinda Baku game ba ko kuma kuma Neman littafin da babu a nan kawai ku ajiye tambayarku a ta comment ko wani shawara da Zaku bamu.

Previous Post Next Post

Sponsored Link

Sponsored Post