Kurkukun Ƙaddara Takun Ƙarshe page 63 Complete by Boss Bature


Health College

Kurkukun Ƙaddara Takun Ƙarshe page 63 Complete by Boss Bature

Takun Ƙarshe

Bata tashi farkawa ba, sai Bayan sallar Magrib, bakinta dauke da sunan Allah, tana kokarin motsawa don ta miƙe taji wani azababben zafi agabanta, ga wata kasala data baibaye sassan jikinta, tunani to soma yi meya faru da ita? A ina take"? jin iska na ratsa jikinta yasa tay saurin shafa jikin nata, lokaci daya gabanta Ya soma faduwa jin babu sutura a jikinta cikin sauri ta yunkura ta miƙe zaune, tana kallon kanta kafin ta yi saurin kallon gefenta, shureim ta gani a kwance kan gadon batare da sutura a jikin shi ba, sai dan bargon daya lullu6e ass dinsa, sam ta kasa tuna komai amma tabbas taji a jikinta raping ɗinta yayi Inna lillahi wa'inna ilaihirraji'un fashewa tayi da matsanancin kuka tamkar ana zare ranta, Koken da ta ke yi ne ya farkar da shi, a firgice ya bude idanun shi da suka kada jawur ya dube ta da su, baiyi aune ba yaji saukar zazzafan mari kan kuncinsa ta shaƙe wuyanshi tana kuka ta furta"nashiga uku! yaya shureim ka kashe min rayuwata, ka gama dani! Ka wulakanta martabar jikina ka goga min ƙazantar Zina, Allah Ya isa tsakanina da kai, bazan ta6a yafe maka ba..." 



zafafan hawayene suka wanke fuskarshi kwata kwata baiji zafin marin da tayi mashi ba saboda ruɗun da kwakwalwarsa ta shiga gaba daya yabi ya rikice yana kokarin tariyo abunda ya aikata mata, saboda baya a cikin hayyacinsa komai ya faru, wlh ko a mafarki bai ta6a sha'awar ya kusanci macen da ba muharramarsa ta aure ba, balle Aisha da yake yi mata kallon kanwarsa, tana kuka Yana kuka Yace"Aisha bayin kaina bane, ba halina bane aisha, ke shaidace akaina, wlh ni ba mazinaci bane..."


 bai ƙare maganarba ta Fasa tsawa tana huci tace "babu abunda zaka fada min ya shureim, wlh sai Allah yayi min sakayya, da kasan irin burin da nake dashi akanka da ba kai yi min haka ba, da tunfarko ka fadamin kana son Jikina, Ni mai iya aurenka ce don in dinga biya maka bukatarka saboda son da nake maka, amma ka rasa ta hanyar da zaka neme ni sai ta hanyar Zina"?


Tana magana Jikinta na kerma, Idanunta sun kada jawur kamar an watsa mata barkono.


Cikin disasshiyar murya tace "ka karyamin zuciyata yaya shureim, ka cuceni, ka zalunce ni, Inayi maka kallon mutun mai tsoron Allah, ashe kaima fasiki ne, kana daya daga cikin mazan da basa son mace don Allah sai don surar jikin ta, kaja mun aikata zunubi, Yanzu da wani ido kakeso In kalli Babana, da mutanan da sukeyi min kallon mutuniyar kirki! Inna lillahi wa'inna ilaihirraji'un..." duk yadda yaso ya shawo kanta ya kasa, taki ta saurareshi balle ta fahimce shi, saukowa tayi daga kan gadon jikinta duk ba kwari dakyar ta mayar da rigarta da gudu ta shuge toilet tana kuka ta kulle kofar, tabar shureim a zaune kan gadonta yana ta kuka kamar karamin yaro, sau uku yana marin kanshi saboda bakin ciki da takaicin abunda ya aikata ma Aisha, Matar da yayi burin ya aura.


"Ya Allah ba halina bane, Kafi kowa sanin bawan nan naka, Ni maijin tsoronka ne mai gudun saba maka ne, kullum ina rokonka akan ka kareni daga sharrin zuciya da sharrin shedan amma meyasa Hakan ta faru dani? Meyasa na aikata ma Aisha haka"?...


Cikin shesshekar kuka yajiyo muryarta daga cikin toilet tana fadin"Yaya shureim ka tashi ka tafi tunkafin Aunty laura ta dawo"..


Jiki asanyaye Ya sauko daga kan gadon Cike da danasani Ya mayar da suturarsa, Wlh Yaji kunya mara misaltuwa, Yaji radadin da har yau In ya tuna sai yaji ɗaci aran shi.


______________________________________✍️


Lokacin da su Benazir suka lura babu malama Aysha a gurin partyn nanfa hankalinsu ya tashi suka dinga nemanta sako da lungu na gidan, har layin wayarta suka kira akashe.


Hankalin su atashe suka tuntu6i Aunty Laura da maganar, tace kada su damu, ta koma gida dama bada son ranta tazo ba, bayan Kammala partyn suka biyo Aunty Laura gidan don suga idan ta dawo, bayan sun shigo gidan suka Nufi dakinta, adatse suka iske kofar, Knocking su ka yi tare da ambaton sunanta, Tana jinsu tayi shiru bata amsa masu ba, har saida suka fara gajiya da bubbuga kofar su ka fara tunanin ko bata nan ne.


A lokacin da basuyi tsammani ba, sai ga kiran ta ya shigo layin Benazir, cikin sauri Benazir tayi picking up tana tambayar ina ta shiga ne? Suna ta neman ta.


Cikin raunanniyar murya Aysha tace kada su damu, tana acikin dakin, ta kwanta ne saboda  bata jin dadin jikinta amma da sauki.


Cike da tausayinta Benazir tayi mata sannu da jiki kafin ta mika ma Anila itama tayi mata sannu.


Daga bisani su ka yi wa Aunty Laura sallama suka tafi, zuciyoyinsu cike fal da tunanin yanayin da sukaji Muryar Aisha.


Tun daga Ranar Aisha ta ɗauke Kafa da zuwa gidan aminnanta, Babu wanda yasan abunda ya faru tsakaninta da dr shureim, ita kadai tayi ta nukunuku ta ki yarda Aunty laura ta gane halin da take a ciki, saboda bata son kowa ya sani ta fiso ta rufawa kanta asiri.



Tsawon kwana uku bata bude wayarta ba, baci ba sha, ba bacci, ta killace kanta adaki, wani irin depression ne Ya kamata ga ciwon rabin kai da take fama da shi, In ta fara kuka har sai hawayenta sun kafe tukunna take dakatawa, kusan kwana ta ke yi tana yin istigfari tare da kai kukanta gurin Allah.


Saboda tayi imanin shi kadai ne zai kawo mata mafita, Hankalin Aunty laura ba karamin tashi yayi ba, ganin Aisha na neman ta halaka kanta, Ta rasa gane meke damunta gaba daya ta hana kanta sukuni, ta rame tayi duhu, idanunta kullum a kumbure suke saboda kukan da take sha, ba irin magiyar da batayi mata ba akan ta faɗa mata meke damunta amma taki sanar da ita, sai dai tace ta tayata da addu'a Allah ya yaye mata abunda ke damunta, tace toh In sha Allah zatayi mata addu'a.


Idan muka koma bangaren Dr shureim tun washe garin ranar da abun Ya faru, Yabar Kasar, Ya tafi Egypt saboda bazai Iya cigaba da jurar zama yana ganin Aisha da abun kunyar daya aikata mata ba.


Bayan makonni da afkuwar Lamarin, Sheikh Imam Ya dawo Nigeria, Bayan ya huce Gajiya a dakinsa, Aunty laura ta jera mashi abincin shi akan rug din dakinsa, Kasa cin abincin yayi saboda faduwar da gaban shi keyi, kuma yaji shiru Aisha bata leko ta yi mashi sannu da zuwa ba, kamar yadda ta saba yi mashi.


"Ina mamana? Ko taje islamiya ne, Aunty laura tace aa tana adaki Yace ta kira ma shi ita.


Fitowa tayi daga dakin ta shiga dakin Aisha, tayi mamakin ganinta a kudundune cikin bargo jikinta sai kerma yakeyi kamar wadda sanyi ya kama.


Hankali atashe Aunty Laura ta haye kan gadon tare da yaye bargon, gabanta ne ya fadi rass, ganin yadda idanun Aisha suka juye, tsabar zafin da jikinta ya dauka tamkar naman da aka gasa da wuta, arude Aunty laura ta zabga salati Ta watso aguje ta nufi dakin sheikh Imam Ta sanar da shi halin da Aisha take aciki, abincin da bai ci ba kenan, jikinshi na 6ari yabiyo bayan Aunty laura suka nufi dakin Aisha, Suna shiga suka taras da Amai na fita daga bakinta.


"Inna lillahi wa'inna ilaihirraji'un" arude Sheikh Imam Ya furta, baiyi wata wata ba, Ya sungumi Aisha Ya fuce da ita da gudu Laura tabi bayanshi, Suka shiga mota.


Kaitsaye Suka Nufi Asibiti da ita, aranar saida aka kwantar da ita saboda jikinta yayi tsauri.


A asibitin suka kwana, Sheikh Imam bai runtsa ba, Yadda Ya ga rana haka yaga dare, har fada saida yayi ma Aunty Laura akan sakacinta na rashin kula da Aisha, gaya nan har ciwo yakamata batare da ita ta sani ba, Aunty laura dai sai hakuri take bashi tace ba laifin ta bane, nan ta fayyace masa halin da Aisha ta shiga bayan tafiyarsa, ta kara da cewa ba irin magiyar da banyi mata ba akan ta fadamin meke damunta amma takiya sai dai tace Intaya da addu'a, Sheikh Imam ya damu sosai, Babban abunda ya kara daga masa hankali ramewar da tayi, kamar ba Aisharsa ba.



Basu sanar da kowa game da ciwonta ba, a duk lokacin da su Benazir suka kira Aunty Laura su kai mata korafin sun kira layin Aisha basa samu sai tace masu su yi hakuri ayyuka ne su ka yi mata yawa, kwanansu ɗaya a asibitin baci ba sha saboda damuwar Halin da Aisha take a ciki, Bayan dr din dake kula da Aisha ta gama bincikenta akan lafiyarta, ta kira Sheikh imam don suyi magana acikin Office din ta.


Bayan sun shigane Dr din Ta dube shi dakyau fuskarta da damuwa tace"Sheikh, naji dadi da Ya kasance Ni Ce amintacciyar Likitar dake duba Iyalanka, Saboda kai malamina ne, ni kuma dalibarka ce, ni me rufa maka asiri ce don kare martabarka" Cike da gamsuwa sheikh Imam Ya jinjina mata kai da alamun rudu akan fuskarsa.


Takardar dake a hannunta ta miƙa masa jiki asanyaye ya kar6a har zai buɗe muryar Dr din ta katse shi.


 "Sakamakon gwajin da mukayi ma Aisha ne"


A hankali Ya soma karanta sakamakon, abun mamaki sai taga yana dariya maimakon taga tashin hankali akan Fuskarshi don ta san muddin Ya karanta sai Hankalinsa ya tashi ba kadan ba.


"Sheikh Lafiya naga kana dariya" mika mata takardar yayi"Ki duba dakyau, wannan sakamakon bana Aisha bane, watakil kunyi mistake ne, Aisha da bata da aure, Ina ita Ina ciki"? Ya fada da murmushi akan fuskarta, Idanun Dr dinne suka cicciko tab da kwalla saboda tsananin tausayin shi daya kamata.



"Dan Allah, Ki bani na Aishana inaso in san meke damunta, wannan kuma ku nemo mai shi ku bata, kada asamu matsala..." 


girgiza kai Dr din tayi cikin rauni na murya tace"Kayi hakuri Sheikh, kai malamine nasan kayi imani da Allah ka kuma yi imani da kaddara, wlh result din Aisha ne, Tana dauke da juna biyu, Nima dana ga sakamakon saida na karyata kaina saboda nasan Aisha bata da aure, sannan Aisha kamilar macace, amma dana zurfafa bincike na sai na gano dagaske Cikine a jikin ta...." 


bata ƙare maganarba sakamakon Tsawar da Sheikh Imam Ya doka mata tamkar zai fasa dodon kunnanta, Tuni tasha jinin jikin ta.


Yana Huci Ya furta"Kin bani mamaki dr Husaina, kin kuma ji kunya wlh, baki taba yi min karya ba sai yau, wannan sakamakon da kika nuna min bana Aishana bane, mamana bazata taba aikata zina Ba, Ƴata kamila ce, mai jin tsoron Allah bazata taba aikata abunda zai sabawa Mahaliccin ta ba, Na yarda da ƴata Aisha bazata ta6a ruke koda hannun Namijin daba muharraminta bane, don haka ki gaggauta janye kazafin da kike kokarin yi mata, watakil biyanki akayi don kiyi mata ƙazafi, dama akwai masu jin haushin daukakar da Allah yayi mata watakil kema kina daga cikin su...' 


kwata kwata Dr husaina bataji haushin kalaman Shiekh Imam ba, sai ma tausayin shi daya ƙara kamata.


Kekketa Takardar yayi, Tare da watsa pieces din saman table din gabanta, Ya juya afusa ce Yabar Office.



Yana tafiya Visitors dake zarya acikin asibitin sai kallon shi sukeyi ganin Sheikh Imam wasu har gaishe da shi sukeyi amma bai kula su ba, Yana shiga dakin da aka kwantar da Aisha Ya iske Aunty laura zaune kan kujerar dake a gefen gadon ta zabga uban tagumi..


Tana jin motsin shigowarshi ta mike tana tambayarshi me dr tace.


Rai a6ace yace"ba zamu cigaba da zama acikin asibitin nan ba, Gida zamu tafi inyaso sai muyi jinyarta acan" 


"Amma ba'a sallame mu ba, kuma jikin nata har yanzu da sauranshi..."


 bata ƙare maganar ba, Ya daka Mata tsawa"Ki ruko Aisha mu tafi" jikinta na bari ta taimaka ma Aisha ta mike baiwar Allah ko tafiya bata iyayi sai layi take kamar zata kife ƙasa a haka suka shiga mota da ita.


Bayan sun dawo gida Aunty Laura Ta matsa mashi akan ya faɗa mata me doc Husaina tace akan ciwon Aisha Nan ya kwashe komai da suka tattauna ya sanar da ita, itama a lokacin biye mashi tayi suka karyata maganar Dr husaina.


Cikin da laulayi ya zo ma Aisha, bakar wahala take sha, wani sa'in tana a kwance kan gado take fara kwarara amai ta sauko da gudu ta fada toilet ta karasa shi acan.


Gashi kullum Cikin yin zazzabi takeyi, daga bayane Aunty Laura ta gano Ciki ne da ita, Bazan Iya misalta tashin hankalin da Aunty Laura ta shiga ba, a daki ta same ta kwance kan gado tace taji tsoron Allah ta fada mata gaskiya! Akwai ciki jikinta ko babu? saboda ta fara kokwanto akan yanayin ta, Kafin ta sanar da ita saida ta fara rokonta akan karta fada ma baba Imam tabarshi a matsayin sirri atsakaninsu duk da tasan watarana dole ne Yaji, Aunty laura tace tayi mata alkawarin bazai taba ji abakinta ba.


Anan ta labarta mata komai daya faru tsakaninta da shureim, a lokacin Aunty Laura ta zabga salati tana sallallami, Jikinta Ya kama bari Saboda razanar da tayi, ta girgiza ba kadan ba, musamman dataji cewa Shureim ne yayi mata aika aikar, Babban tashin hankalinta Idan Sheikh Imam Ya gano Cikin ne dagaske, to fa  itace mutun tafarko da zai fara tuhuma saboda ita ta matsa ma Aisha akan suje Partyn.


 Aunty Laura tayi kuka kamar ranta zai fita, saboda tausayin Aisha daya kamata, Yarinya Kamila da ita an zubar mata da mutuncin ta, dr shureim Yasha tsinuwa agurin Aunty laura, tace dan iska munafuki mai fuska biyu, kamar Na Allah, In sha Allahu sai yaga sakayyar abunda yayi mata, daga bisani ta lallashi Aisha taja ta ajiki sosai, ta dinga bata hakuri hadi dayi mata nasiha har hakuri ta bata akan Tursasa matan da tayi akan taje, gani take ma kamar itace Silar komai daya faru da Aisha.


A haka aka cigaba da rayuwa, Har Ila Yau sheikh Imam yaki yarda cewa Aisha ciki gare ta, wani'sa'in agaban shi zatayi amai amma ko kadan bai yarda ya zargeta da ciki ba, Iya bakin gwargwado tana samun kyakkyawar kulawa agurin Baba Imam, baya barinta cikin damuwa, Ya hana a kaita asibiti kuma Ya hana dr Husaina zuwa agidan, Ko tazo da niyar duba Aisha tun daga bakin gate security Officers ke korarta.


 lamarin ya daure mata kai, ita burinta kawai ta taimaka ma sheikh Imam su nemi mafita gudun kada kimarshi ta zube sai dai Yaki bata damar ganawa da shi, Har court taje ta same shi a office dinshi Amma Yaki sauraronta, badan taso ba tahakura da bibiyar shi.


Saboda zullumi da fargaban abunda zai biyo baya In sheikh Ya san Aisha tana da ciki, yasa Aunty Laura ta rame, kamar mai fama da zazzabi har saida sheikh Imam Ya lura da canjin da tayi, ko da ya tambayeta meke damunta sai tace mashi Ciwon aisha shine silar damuwarta, hakuri kawai yake ba.


Dubarace ta fado mata arai, ta sami Aisha da zancen su zubda Cikin kawai, Aisha tace bazata iya ba, bata son ta kuma aikata wani zunubin na kisan kai bayan wanda suka aikata, ita bazata iya kashe rai ba, laifin da shureim ya aikata mata bazai shafi abun dake a Cikin ta ba.


Aunty laura taita kokarin tunzurata don ta amince asamu arufawa kai asiri amma Aisha ta yi kunnan Uwar shegu da maganarta, ganin tasa kafiya yasa Aunty laura ta dinga zuba mata maganin zubar da ciki aboye take barbada mata shi cikin abinci ko cikin abun sha, sai dai wani Iko Na Allah tun da tasoma yunkurin 6arar mata da ciki Allah bai nufa ba, saima kara lafiya da ta ke yi.


Lokacin Da Cikin Yakai wata Biyar, Ya fara bayyana a jikinta, daga ka kalle ta zaka gane tana da ciki Amma sheikh Imam Ya kasa Yarda Ciki ne saima yace ture akai mata, Ajiyar Aljanu ce, haka ya dinga banka mata ruwan addu'o'i tana sha, In zataci abinci sai ya tofe shi da addu'a in zata kwanta bacci sai ya shigo har daki gaban gadonta yayi mata addu'a, Zuciyar Aisha ta karaya da ganin irin Yardar da mahaifinta yayi da ita, shiyasa ta kasa buɗe baki ta furta mashi Ciki ne a jikin ta, sai dai in suna atare yanayi mata addu'a ko yana bata abinci abaki, tayi ta zubar da hawaye tana kallon shi, ya dinga lallashinta yana fadin mamana kiyi hakuri Allah yana tare da bayinsa masu Hakuri, ki jure ki cinye jarabawar nan, In sha Allah koma wanene yake nemanki da sharri kanshi zai koma, mutanene ba Allah aransu bakin ciki da hassada sunyi yawa azukatan mutane.


Wani sa'in in yanayi mata maganar sai ta dinga Yunkurin buɗe baki don ta fada mashi gaskiya amma sai ta kasa, In Aunty laura na akusa taga tana kokarin fada masa sai tayi saurin janye hankalin shi da tunanin wani abun.


Saboda Lalurar Aisha Yasa Sheikh Imam Ya hana ta fita ko kofar falo bata leƙawa, saboda baison wani yaga Aljiyar da aljanu sukayi mata a zargi ciki ne, duk wanda yazo nemanta gida sai dai suce mashi bata nan tayi Tafiya Sudan gidan Kawunta, babu wanda yasan Aisha tana agida har su Benazir.


Daliban Aisha na islamiya, Da abokananta malamai da duk wani mai sauraren wa'azinta sai da ya damu da rashin ganin Aisha, saboda Allah yayi ta da farin jinin mutane suna son Aisha.


A kwana a tashi ba wuya gurin Allah, Cikin Aisha Ya Cika wata tara Cuf, tashi dakyar zama dakyar haka ta ke fama, a daren wata ranar Juma'a ne nakuda ta kamata, Aunty Laura ta matsa akai ta Asibiti ganin yadda take shan wahala, amma Sheikh Imam Ya hana yace ciwonta bana asibiti bane, sai dai ya bata ruwan addu'a tasha, a lokacin Aunty Laura, har yunkurin fada mashi gaskiya tayi amma saboda tsoron Kada ya saketa Yasa taja baki tayi shiru, ta bar shi ya gani da idon shi.


A falo ya zauna yana jan cazbaha, Ya baro Aunty laura adakin Aisha.


Bayan wani Lokaci, Kukan Jariri Ya cika kunnen shi, Wani irin Bugu Zuciyar shi tayi tamkar zata fasa kirjin shi, Tsantsar tashin hankali da rudanine Ya bayyana akan fuskarshi, cikin sauri Ya miƙe Ya shiga dakin Aisha, dira kafarshi keda wuya ba zato ba tsammani idanun shi suka sauka akan Jinjirin da Aunty Laura ta ruƙe a hannunta.


Lokaci daya yanayin fuskarshi ya sauya, A lokacin Ayshah tana a kudundune Cikin bargo Aunty laurace ta taimaka mata tayi wanka bayan ta kar6i haihuwarta.


Jikinshi na kakkarwa ya karasa shiga dakin a gaban Laura ya tsaya yana ƙarewa Jinjirar kallo idanunshi azazzare.


Babyn Fara Sol da ita, Idanunta dara dara farare kamar an diga zaiba, ga wata yalwatacciyar sumar kai har gaban goshinta gashin ne a nannaɗe, kallo daya zakai mata kagane Ba jinsin bakar fata bace.


A lokacin Jikin Aunty Laura kerma yake kamar mazari, Ga wani bugu da kirjinta keyi mata saboda tsoron Hukuncin da Shiekh Imam zai yanke mata.


Numfashi yaja tare da miƙa hannu Ya kar6i jinjirar daga Hannun Laura, Ya kura mata idanu Yana kallon ta.


Ya kasa yarda da abun da Zuciyarshi ke raya mashi, ya yi fatan ace mafarki ya ke yi ba gaskiya ba, wani kululun bakin cikine da takaici Ya tokare makoshin shi..


Muryarshi na rawa ya furta"Shegiya agidana? Gidan Alkali sheikh Imam? Sanannan malamin addinin islama! Me yi ma wasu fada da nasiha akan aikata Barna"? Yau agidana aka aikata barna? Ni sheikh? yata Aisha ce ta haifi Shegiya acikin gidana? Batare da Aure ba? inna lillahi wa'inna ilaihirraji'un..." 


wani makokon bakin cikine ya mamaye zuciyarshi, hannayenshi na kerma Ya mika ma Laura yarinyar da sauri tasa hannu ta kar6a, jikinshi na kerma ya zauna Gefen gadon Aisha Cikin sanyin murya ta wanda ya karaya ya furta"mamana, tayaya kika samu Ciki? Wanene yayi maki aika aikar nan"?


Kunya da bakin cikine suka sa Aisha tagaza furta kalma, taki fitowa daga cikin bargon jikinta sai kerma ya ke yi.


Shurun da tayi ne ya bata masa rai, Ya doka mata tsawar data firgitar da su, Har Jaririyar saida ta fashe da kuka


Yana Huci Yace"Ba zaki bani amsar tambayar da nayi maki ba"?


Aunty laura tana kuka tace"Abien Aisha tsautsayine da kaddara..."


Bata kare maganar ba, Ya zabura ya miƙe ya nufe ta gadan gadan, batai aune ba Taji safkar maruka zafafa kan kuncinta, Har saida shatun hannayensa suka fito rudu rudu akan kuncin ta, gefen bakinta ya fashe jini ya fara ɗiɗɗiga.


"Allah Ya isa tsakanina dake Laura, Kin cuce ni kin cuci kanki kin kuma Cuci Aisha, sannan kin Cuci malama Batool! Kin ci amanata, nasan komai ya faru da Aisha kece Sila, kece kika ja komai, shashasha mara hankali"


 Fashewa tayi da kuka Jinjirar hannunta sai kuka takeyi.


"Kunyi tunanin bansan komai bane? Duk abunda ke faru agidan nan an fada min, Kece Kika matsa ma Aisha kuka tafi partyn dana hanata zuwa, kina amfani da biyayyar da takeyi maki gurin Cutar da rayuwarta.."


 Cikin shesshekar kuka tace"wallahi Allah shine shaidana, Ni ban ta6a Cutar da Aishaba, na ruke amanar da ka bani, Kai ka sani in ba ni ba wa kake tunanin zata kula maka da yarka kamar yadda na kula maka da ita"? 


Bai kula ta ba, Ya koma ga Aisha Ya sanya Hannu Ya yaye bargon data lulluba da shi wata irin zabura tayi ta mike zaune jikinta na kerma ta dinga girgiza kai batare data iya furta kalma ba.


"Ki gaya min wani fasikin ne yayi maki ciki"? 


Cikin rawar murya ta zayyana mashi komai daya faru.


"Dan Allah ka yafe min baba, Ba laifina bane, bayin kaina bane, Na rantse maka da wanda raina yake a hannunsa Bada son raina komai ya faru ba, dr shureim shine Ya yi min fyaɗe, baba kayi hakuri kayi hakuri, nasan nakarya maka zuciya, Naji kunya baba, nayi abun kunya, har rokon Allah nayi ya dauki raina in huta saboda bakin cikin abunda yaya shureim yayi min..." 


sambatu tadinyi yi mashi...

Bai san sa'adda hawaye suka cika idanun shi ba.


Cikin raunanniyar Murya yace"Aishana, meyasa lokacin dana hanaki fita partyn bakiji maganata ba? Meyasa? Har ni zansa maki doka ki karya saboda Wannan shashashar ta tursasa maki" ya fada yana nuna Aunty laura da yatsa.


"Aishana baki taba yi min gardama ba, ban taba hanaki abu kika ƙiyi ba sai akan Paryn nan! Kika bijiremin, Ni dama saida raina ya bani wani abu zai iya faruwa shiyasa Na hanaki zuwa, da ace kinbi maganata da duk hakan bata faru ba, Kinga illar Kin bin Umarnin Iyaye ko"? 


jinjina mashi kai ta yi Jikinta nata kerma.


"Aisha, Kinbiyewa Son zuciyarki, Kin cuce ni Kin Cuci kanki, Kin kuma Cuci mutanan da suka yarda da mu, sannan Kin zubarmin da mutucina kema kuma Kin zubar da naki mutunci, kinja mana abun kunyar da shiga cikin mutane zai gagaremu, Kin karya alkawarin da kikayi min na kare mun mutuncina da kimata a idon duniya, masuyi maki kallon mutuniyar kirki da zarar sunsan abun kunyar da kika aikata zasu fara yi maki kallon fasika mai fuska biyu, da Ina alfahari dake amma A yanzu babu wannan Aishana, Kin lalata komai, farin Cikin da kika sama min tun ranar haihuwarki a yau kin bata shi, Kin dasa min bakin cikin da har abada bazan ta6a warkewa daga radadin da naji ba, Aisha Ina da makiya wadanda suke son ganin bayana, Idan har sukaji abun kunyar da kika aikata zasuyi min dariya, kuma zasu yi amfani da hakan gurin ganin raunina..." 


fashewa tayi da kuka tana fadin"baba kadaina fadin maganganun nan bana jin dadi baba, Kaifa malamine, kafi ni sani baba, Abunda ya faru dani Kaddara ce, wata irin addu'ar neman tsari ce bakai min ba? Nima haka inayi ma kaina amma hakan bai hana kaddara ta afkamin ba, saboda Allah ya riga daya kaddara faruwar hakan, babu wanda Allah baya jarabta baba, Annabawan Allah sun fuskanci jarabobin rayuwa basu taba gazawa ba, ya kamata kaima kayi koyi da su, baba wannan ne karo na farko daka fara fuskantar jarabawa mafi muni arayuwarka sau ɗaya tak yarka tayi ciki batare da aure ba, Dan Allah baba Mu dauki Hakan amatsayin Kaddararmu, muyi hakuri mu jure, baba Kafi jin kunyar duniya akan ta lahira? Mutane bazasu amfane mu da komai ba saboda basune zasuyi mana hisabi ba"! 


Maganganun Aisha sun karya Zuciyarshi, har ya gaza yanke mata hukuncin da yayi niyar yi mata.


Mikewa yayi da sauri Ya fuce daga dakin, Yana fita Aunty laura ta mika mata Jinjirar dake ta kuka"ki bata nono Tasha yunwa take ji" Kar6ar jinjirar Aisha tayi, ta fara shayar da ita idanunta akan fuskar Jinjirar yayin da take tsotsar nono sai kallon fuskar mamanta takeyi, hawayen Aisha dake gangarowa ta cikin idanunta kaitsaye yake sauka saman fuskarta, tayi azan In ta haifi yarinyar zataji tsanar ta saboda bata sameta ta hanyar aure ba, amma sai ta ji tsantsar kaunar yarinyar fiye da komai na duniyar nan.


Aunty laura ta kara lallashin Aisha har saida ta kwantar mata da hankali.


"Aisha nayi danasani da nayita kokarin zubda maki Ciki saboda inajiye maki bakin mutane da kuma abunda zai biyo baya idan mahaifinki Yaji, wlh yanzu da kika tunasar damu sai naji jikina yayi sanyi, da na kashe yarinyar nan da nayi danasani na har abada, baiwar Allah gata kyakkyawa kamanninta sak dana Ubanta, Allah ya raya mana ke bisa tafarkin addinin islam, Allah yasa ki gaji Kyawawan halayan Mamanki"


aisha na murmushi ta amsa mata da ameen.


"Bari naje na shirya maki Abinci nasan kina jin yunwa"


"Aunty Laura, Baki gaji ba? Naga kin raunata" murmushi tayi kada ki damu Aisha, duk raunin da zan ji bai kai wanda kika ji ba.


Ta fada tare da fucewa ta shiga kitchen da kanta Ta hada mata farfesu bayan ta gama ta kawo mata adaki.


A bangaren Sheikh Imam bayan daya Koma dakinsa safa da marwa ya cigaba dayi, Zuciyarshi cike fal da tunanin ta yadda zai bullowa lamarin saboda bayason asirin abun da ya faru da yarshi aisha ya tonu a idon duniya, yana jiye masu tsoron tozarcin da zasu fuskanta agurin mutane..


A bangaren Dr shureim tun bayan daya Koma Egypt gurin aminsa, Bai kara samun kwanciyar hankali ba, saboda damuwar abunda yayi ma Aisha, Sai da ya shafe sati daya cur bai runtsa ba, abinci sai anyi dakyar ake samu yaci, ya yi duhu ya rame saboda tunanin A wani hali aisha take aciki, ga wani irin azababben sonta daya kara nunkuwa acikin Zuciyar shi, har takaiga baya iya bacci batare da yayi mafarkinta ba, Sometimes sai yayi tunaninta ya ke samun nutsuwa a cikin zuciyar shi, kusan kwana yakeyi akan darduma yana istigfar tare dayi ma Aisha addu'ar Allah yaye mata damuwarta ya kawo mata sauki acikin rayuwarta, saboda yasan zunubin daya aikata mata bazai barta ta zauna lafiya ba, dole su fuskanci kalubale ita da Mahaifinta.



 tun yana boye abunda ke damunshi har amminsu ta lura da rashin walwalar shi ta dinga tambayarshi meke damunshi yaki fada mata, ta kasa jurewa ta kira iyayen shi ta sanar da su halin da Dan su ke a ciki, da jin hakan Hajiya layla ta bashi Umarnin ya dawo Nigeria, saboda ammi tace ta rasa gane kanshi, baya bacci baya son cin abinci, wanka ma saita matsa mashi ya ke yi kamar karamin yaro.


Bayan ya dawo Nigeria, Iyayenshi suka tasa shi agaba da tambayar meke damunshi? yaƙi ya sanar dasu, Ba irin lallashin da basuyi mashi ba amma duk abanza.


Saida Ya samu nutsuwa ya kira Benazir a dakinsa ta same shi ya tambayeta Ina Aisha? Tace mashi rabon ta da Aisha kusan wata tara da kwanaki, Aunty Laura tace masu ta tafi sudan gurin kawunta, Ko sun kira layinta basa samu kuma koda zata tafi ba ta yi masu sallama ba"


Hankalin shi ba karamin tashi yayi ba, Zuciyarshi ta karaya sosai.


Ana haka saiga kiran Sheikh Imam Ya shigo wayar shi, wata irin kunyace ta kama shi kamar bazai daga kiran ba sai kuma Ya daga, Ko sallamar shi sheikh Imam bai amsa ba Yace shureim Inason ganinka, Ka same ni agidana, Ya amsa mashi da toh.


Bai bata Lokaci ba, Ya shirya kanshi cikin shadda Ya nufi gidan Sheikh Imam A garden Ya taras da shi zaune kan kujera fuskarshi babu walwala kamar bai taba dariya ba, tuni Shureim Yasha Jinin jikin shi.


Bayan daya zauna kan kujerar dake fuskantar sheikh Imam Malik Ya yi shiru Yana sauraron shi..


Kallo ɗaya sheikh Imam yayi mashi Ya lura da irin ramar da yayi daga gani yana acikin damuwa.


"Akwai wata rana, dana farka tsakar dare, na fito daga daki Ina zagaye Gidana, dama Ina yawan yin hakan sometimes bana iya bacci batare dana tofe ko'ina da addu'a ba, ina gab da zan gifta dakin aisha Najiyo shesshekar kukan ta, Kasan me naji tana fadi"? ya tambaya da tsantsar bacin rai Yana kallon fuskar Shureim daya gama rudewa, Girgiza kai yayi"aa baba'


"Addu'a takeyi Allah ya cika mata burinta na ganin ta auri yaron makwabtana data mutu akan kaunarsa batare da sanin shi ba.."


 wata irin karaya Zuciyar dr shureim tayi.


"Nayi mamaki a wannan lokacin, saboda Aisha bata taba bude baki ta fadamin ga wanda takeso ba, amma a lokacin danaji tayi addu'ar nan ni kuma sai nayi alkawarin zan aura mata yaron nan da take so saboda in cika mata burin ta.."


 zafafan hawayene suka wanke fuskar Dr shureim.


"Yarinyar da tayi dakon soyayyarka acikin zuciyarta na tsawon shekaru, ta hana idonta bacci don ta roki Allah ya mallaka mata kai ita ka wulakanta rayuwarta Shureim? Ya faɗa rai abace.


"Inayi maka kallon mutumin kirki kamili, mai jin tsoron Allah, ashe  na yaudari kaina! shureim ka sani ka take sani? Da yata ka aikata zina? Sannan baka taba waiwayonta ba, Ka haura kafa kabar kasar, Sai jiya na samu labarin ka dawo! Baka damu da halin da ka jefata ba shureim! Har yabonka nakeyi saboda na yaba da kyawawan halayenka amma ka tashi ka watsa min kasa a ido"


Fashewa da kuka dr shureim yayi kamar karamun yaro, shima sheikh Imam din hawaye ne ke zarya kan kuncinsa.


Cikin karyayyar murya mai tattare da danasani dr shureim Shureim Ya soma bashi hakuri Yace ya amsa laifinsa amma wlh baisan Ya akaita ba, Allah shine shaidarshi bai ta6a kusantar zina ba, bai ta6a sha'awar Ya kusanci Aisha batare da aure ba, Amma ya karbi laifinsa kuma Yana neman alfarmar ya bashi aurenta saboda su rufawa kansu asiri.


Sheikh Imam yace yaji amma yana so yaje gida Ya fada ma iyayensa abunda Ya aikata sannan Ya sanar da su zai auri Aisha, Duk abunda su ka ce Yazo ya sanar da shi, Jikinshi na 6ari ya mike har tambayar sheikh yai Aisha tana nan cikin gidan? Yace mashi eh, ya sake cewa zai iya ganinta? Imam Yace aa bai amince Yaganta ba, har sai bayan an daura auransu.


Bayan komawar Dr shureim gida ya kira Alhaji ubaid da Hajiya layla a falo Benazir ce kadai ke babu a cikinsu. 


Bayan sun nutsu, Dr shureim Ya fayyace masu komai daya faru tsakanin shi da Aisha Sannan Yace Ya yanke shawarar zai aureta..


Tunkan Ya kare maganar Hajiya layla ta fara zazzaga masifa tana fadin wallahi bada yawunta ba, bai isa Ya bata masu suna agari ba, sai dayaga zabe ya kusa zai zo masu da wannan maganar mara dadin ji? Salon yaja masu zagi agurin Jama'a? ta inda take shiga bata nan take shiga ba.


Da farko Alhaji Ubaid yaso Ya fahimci dr shureim Har fada yayi masa akan abunda yayi ma Aisha, sannan yace ya amince masa zaije suyi maganar aurensu da sheikh Imam din, Shureim Yaji dadin maganar Mahaifinsa hajiya layla sai banbamin bala'i takeyi, Ita damuwarta ba akan abun kunyar da shureim yayi ma aisha bane, face Takarar da Alhaji ubaid Ya tsaya ga zabe ya kusa In har abokan adawarsu suka Ji abun nan zasu nemi bata masu sunane, a karshe su rasa kujerar da suke nema.



Bayan kwana daya da afkuwar Lamarin, Alhaji Ubaid Ya canza magana, ya kira shureim Ya fada masa yayi hakuri amma gaskiya bazai bari ya auri Aisha ba, saboda yayi bincike ya gano aisha ba mutuniyar kirki bace, dama can ta saba bin maza, har videos dinta na batsa wanda tayi tare da maza an tura masa awaya, sannan abun da ya faru tsakanin shi da ita ya yarda bayin kanshi bane, laifin Aishar ne itace shaidaniyar dataja Hankalin shi donta biya bukatar kanta.


Hankalin dr shureim ba karamin tashi yayi ba, ya dinga salati Yana karanto duk wata addu'a da zata sanyaya zuciyarshi, ranshi ya 6aci matuka da jin kazafin da mahaifinsa yayi ma Aisha, Yace wlh daddy karyane, wannan maganar ba gaskiya bace, kaji tsoron Allah, kaji tsoron ranar da zaka koma gare shi, Aisha ba fasika bace, mutuniyar kirkice ita, abunda aka fada maka akanta karyane, kai kasan wacece aisha tuntana karamarta kamilar macace mai kamun kai, daddy kada ka biyewa son zuciyarka! Nasan siyasa ce ke nema ta rufe maku ido shiyasa kuke gudun in auri Aisha kuma maganar nan har yanzu ma ba Wanda yasan da ita daga gidansu sai nan, dan Allah kubarni in aureta in rufa mata asiri, Nine fa nayi silar jefasu a halin da suke aciki ita da mahaifinta, meyasa ni ba za ku ga laifina ba sai laifinta ta? Ita da nayiwa fyade"? 


hajiya layla Ta balbale shi da masifa tace"ko yaki ko yaso aisha ba mutuniyar kirki bace, abunda mahaifinsa ya fada akanta gaskiya ne, dama ita can bata yarda da ita ba, munafukar kullum tana yawo cikin hijabi kamar ta Allah, ashe maza take bi, gashinan zata bata mata tarbiyar ɗa, don haka ta yanke duk wata alakarsu da sheikh Imam malik, zumuncinsu Ya kare.


Gaba daya suka juya ma Dr shureim baya, duk wannan abun dake faruwa Benazir bata sani ba, Saboda bata agidan ta tafi Abuja gidan Uncle Musa.



Shiekh Imam malik ya yi ta Jiran zuwan Alhaji Ubaid Ko shureim don Yaji daga garesu amma Yaji shiru wai malam yaci shirwa.


Har dai ya yanke shawarar zuwa gidan da kanshi don yaji ya ake ciki.


Bayan ya isa Security Officer din dake tsaron Gidan Ya shiga yayi mashi sallama da Alhaji Ubaid.


Sai ga Jam'in ya dawo yace mashi Ya shiga daga ciki.


A falon gidan Shiekh Imam Ya zauna kan Sofa Yana Jiran fitowarsu, Tsawon mintuna Sai ga Alhaji ubaid da Hajiya layla sun fito daga part dinsu, akan sofa suka zauna suna fuskarshi, tun daga yanayin fuskarsu Ya fahimci babu lafiya, kamar basu taba yin dariya ba, Koma arzikin gaisuwa bai samu ba.


ya yi tsammanin zasu bashi hakuri kan abun kunyar da dansu yayi ma yarsa, amma sai yaga akasin hakan, bayan da ya kora masu jawabin abunda ya kawo shi Alhaji Ubaid Yace Yayi hakuri ya rungumi kaddara, Amma shureim bazai auri Aisha ba, saboda sun yi bincike akanta sun gano ba mutuniyar kirki bace ta saba bin maza.." 


bai dire maganar ba Sheikh Imam Ya doka masa tsawa Rai amatukar bace Yace"amma baka da Mutunci Alhaji Ubaid, ka bani mamaki, mutumin banza mutumin wofi, yau da kanka kake yiwa aishana kazafi? Yarinyar data taso agabanka tuntana karama kasanta farin sani, har alfahari kakeyi da ita saboda kyawawan halayanta, ba kamar yarka Benazir ba da kowa yasan bakin halinta data gada awurin jatumarta, Ni ban ta6a aibata yayanka ba saini zaka aibata nawa Ubaid? Akwai dan iskan dayawuce danka daya keta mata haddi? Nayi zaton in masifa ta same ni kaine mutun na farko da zaka fara rufa min asiri ka sharemin hawayena ashe na yaudari kaina!!...." 


Dakyar ya ƙare maganar hawaye wasu nabin wasu akan kuncinsa Yaji zafin maganar Alhaji Ubaid.


Hajiya layla ranta Ya 6aci matuka da jin yadda sheikh Imam Ke gaya magana akan ya'yanta, dama ba mutunci gareta ba, tana da sonkai, nata kadai ta sani, ko da take zumunci da su Albarkacin Alhaji ubaid suke Ci.


Nan ta shiga surfa mashi ruwan masifa zagi ta uwa ta uba kamar zata dokesa, saboda rashin kunya, kwata kwata sheikh Imam bai damu da maganganunta ba saboda yasan halinta, Bata da kunya fitsararriya ce, kuma dama ita tabarmar kunya da bori ake naɗeta.


Alhaji Ubaid kasa magana yayi, saboda Zuciyarshi da tayi rauni saboda maganar Sheikh Imam malik ta karya Zuciyar shi, Ya danji tausayin shi amma da ya tonu hudubar da shaidan yayi mashi saiya canza ra'ayin shi.


Ya mike Ya fara gaya ma sheikh Imam magana Yace"ya jira ya ga abunda aka tura masa, zaisan ba kazafi yayi ma Aisha ba" Ya juya ya nufi dakinsa sheikh Imam Yana atsaye jikinshi na kerma zuciyarshi cike fal da tunanin menene Alhaji Ubaid zai nuna masa"?


Bai karashe zancen zucin ba, sai Ga Alhaji Ubaid Ya fito hannun shi ruke da wayarsa Ya miƙa ma Sheikh Imam"gayanan ka gani da idonka"


 Yatsun hannunsa na kerma Ya kar6i wayar lokacin daya daura idanunsa akan Screen din wayar saida Zuciyar shi takusa dakatawa da bugawa saboda tsabar firgitar da yayi, a lokacin Jikin shi yadinga tsuma idanunshi suka kada jawur, baisan sa'adda Ya saki wayar Ta fadi kasa Ya juya cikin fitar hayyaci ya fuce daga gidan Yana tafiya kafafuwanshi na hardewa kamar zai kife kasa.


Bayan fitarshi Zainab mai aikinsu Taje ta fada na Dr shureum abunda Iyayensa sukayi na sheikh Imam Malik, Ransa ya 6aci a zuciye yaje ya same su ya dinga yi masu fada kamar zai doke su, Yace basu kyauta ba, meyasa zasuyi ma sheikh Imam haka? Shifa makwabcinsu bayan haka sunyi zama na amana, amma saboda rashin adalci da son zuciya sun rufe ido akan rashin gaskiya suka ci mutuncin shi, babban abunda yafi kona mashi rai abunda suka nuna ma Sheikh Imam ya gani, yaji zafi sosai, amma su ko a jikinsu.



Aisha tana zaune cikin dakinta a kan gado, tana tsaka da shayar da babynta, Baba Imam ya fado dakin Afujajan ko sallama baiyi mata ba, Jikin shi na zubda Gumi Yakai hannu Ya damƙi ƙeyar Aisha da ita da yar duka Ya wurgo su tsakar falo Ta kife kasa Yarinyar ta fashe da kuka kamar ranta zai fita, Da gudu masu aikin gidan suka fito sakamakon Kukan Aisha da suka jiyo, Aunty Laura dake a cikin dakinta tana tsaka dayin waya tajiyo kukan Aisha dana jinjirarta, batasan sa'adda ta jefar da wayar kasa ta watsa da gudu Ta shigo falon tana haki, Gabantane ya yanke ya fadi ganin Sheikh Imam tsaye yana huci kamar mayunwacin zaki ga Aisha da jinjirarta yashe a kasa suna kuka.


Inna lillahi wa'inna ilaihirraji'un Ta faɗa tare da nufar Aisha donta taimaka mata ta mike sai dai kafin Ta karasa Sheikh Imam Ya doka mata tsawa Yace"karki kuskura ki taba ta! Idan ba haka ba, abakin aurenki" cak ta tsaya jikinta na kerma.


"Allah Ya isa tsakanina dake Aisha, Allah Tsine maki Albarka, In sha Allah sai kinga sakayyar abunda kikai min" waro idanu waje Aunty laura tayi, Hankalinta amatukar tashe, gashi ba halin tayi magana balle ta dakatar da shi, maids din suka daura hannayensu asaman kansu cike da tashin hankalin jin furucin sheikh Imam ga yarsa, ba su taba zaton zai yi mata haka ba, su din amintattunsu ne, koda asiri Ya tonu agidan suka gane Aisha tana da ciki basu ta6a nuna sun sani ba saboda basa son abunda zai zubar da martabar sheikh Imam da ita Aisha.


 "Kin cutar da rayuwata kin yaudareni Aisha, Idan aure Kikeso Meyasa ba zaki fada min ba inyi maki!? Sai kika zabi ki zubarmin da mutunci na, inayi maki kallon mutuniyar kirki ashe ke din fasika ce, mara tsoron Allah, Dama tun farko banso Kika je Germany karatu ba saboda hankalina bai kwanta ba, ashe bayan da kika je karuwanci ki ke yi acan, naga komai Aisha an nuna min videos dinki da hotunanki tare da kato, Yau silarki An zageni anci mutuncina Aisha wlh nayi danasanin haihuwarki da akayi"❗

*DAGA ALƘALAMIN BOSS BATURE🔥✍️*

*Game bukatar karanta littafin kurkukun kaddara, 500 ne za'a tura Via Opay, 8103884440 Hafsat Bature Muhammad, shaidar biya za'a tura ta whatsapp, 08169856268 ko 08103884440*

Post a Comment

Idan kuna da tambaya akan abinda Baku game ba ko kuma kuma Neman littafin da babu a nan kawai ku ajiye tambayarku a ta comment ko wani shawara da Zaku bamu.

Previous Post Next Post

Sponsored Link

Sponsored Post