Kurkukun Ƙaddara Takun Karshe Page 48 Complete by Boss Bature

Kurkukun Ƙaddara Takun Karshe Page 48 Complete by Boss Bature

Takun Ƙarshe

 Walking slowly chief ya isa bakin bathtub ɗin ya zuƙunna kan kafafunsa ba tare daya kau da ido daga kallon fuskar Danish ba.


Allah kadai yasan farin cikin da ya mammaye zuciyar sa wanda misalta shi ma bazai yiwu ba, Yau da ya rasa ɗan tahalikin nan Allah kadai yasan halin da zai shiga.


Abun da ya faranta ranshi da baije ko'ina na, ko da suka bata mashi rai bai yi fushi ba, bawan Allah sai ya dawo gida yayi kwanciyar shi cikin ruwa hakan na nufin bazai iya rayuwa ba tare da yan uwansa ba, duk runtsi duk wuya yana atare da su.


Cikin sanyin murya ya sake ambaton sunan shi"Danish" Shiru bai motsa ba, cike da fargaban kada ace wani abun ne ya faru da shi chief ya daura tafin hannunsa na dama saman forahead dinsa ya shafa shi har zuwa kan karan hancin sa.



Ba zato ba tsammani yaji Danish Ya damƙi wuyan Hannun sa, eye lids dinsa na kerma dakyar ya buɗe idanun shi da su kai mashi nauyi ya dubi chief.


Da wata irin kakkausar murya yace"saboda yan uwana na dawo nan"



Wani irin faduwar gaba Unaisah taji, yayin da take kokarin shigowa toilet din cike da fargaban me zata taras jin shiru chief bai fito ba shiyasa ta yanke shawarar bin bayan shi.



Lokaci ɗaya ta sauke nannauyar ajiyar zuciya lokacin da kunnuwanta suka jiyo mata muryarshi, tayi matuƙar yin mamaki saboda ita lokacin data shiga toilet din jibgegen wolf tagani zaune cikin bathtub ɗin shiyasa ta raza, yanzu ta gane shi ne ya rikiɗa ya dawo mutun.


 wani irin tsantsar farin ciki ne mara misaltuwa ya wanke zuciyarta, dama saida ranta ya bata zai dawo, hasashen da tayi ya tabbata maganar da ummi tayi ce ta tuna mata da ranar daya rikiɗa kafin ya zama maciji da jikin shi ya dauki zafi rau cikin kwami ya shiga ya tsuma kanshi da ruwan sanyi.


yanzu ta gane idan ranshi ya 6aci yana son yayi cooling temper dinsa ruwan sanyi yake shiga, taji tausayin shi, shi dai rayuwarshi wani sa'i kamar bata mutane ba.


"Danish, ka tada min hankalina, daga ni har yan uwanka da abokan aikina, babu irin neman da ba ayi maka ba a garin nan, saboda kai ko abinci na gaza ci, ban ta6a tsammanin damuwar da nayi dakai takai har haka ba..." ya faɗa yana kallon cikin idonshi.


"Da na san ranka zai 6aci da ban matsa maka mun tafi head quarter ba, banji dadin abunda big guy yayi maka ba, na tsawatar mashi kuma ya gane kuskuren shi, bazai ƙara gigin bata maka rai ba"


yanayin yadda chief ke yi mashi magana da sigar lallashi ba karamin kwantar mashi da hankali yayi ba, zuciyarshi taso ta karaya da jin irin kaunar da yake yi mashi, tun daga kan facial expression dinsa yaji ya yarda da duk wani abu daya faɗa masa.


 "Kayi hakuri idan na bata maka rai, sannan inaso Ka faɗa min duk wasu sharrudda da zamu bi don mu zauna dakai lafiya batare da mun 6ata maka rai ba saboda naji jiki ba kaɗan ba lokacin da aka sanar dani ka fita nayi zaton bazan ƙada ganinka arayuwata ba" softy ya fada tare da tsamo hannun Danish daga cikin ruwan ya haɗe yatsun hannun su cikin na juna, yayi shiru yana sauraron shi.


"Sannan Alfarmar da zan roko a gurinka, nasan baka yarda da ni ba, amma dan Allah ko dan saboda yan uwanka kada wata rana kayi fushi ka koma inda ka fito.." ya ɗan dakata yana kallon yanayin fuskar Danish.


"nasan za ka yi tunanin kodan saboda ina son ka bamu hadin kai shiyasa nake lallashin ka, ba haka bane, Kamar Yadda Allah ya jarabci Uncle dina da kaunarka nima haka nake jinka a zuciyata"


Unaisah dake atsaye bakin toilet door din gaba daya tana sauraran maganar chief, zuciyarta ta karaya da tausayin su, aranta ta ayyana wannan wata irin zazzafar kaunace suke yi ma shi? Anya Danish bai da alaƙa ta jini da su? 


Lumshe idanun shi yayi tare da numfasawa slowly ya ware eyes dinsa akan fuskar Chief


Baiyi tsammanin zai tanka ma shi ba, in weak Voice Danish Yace"ban ruƙe ka a zuciyana ba, amma ku daina bata min rai in na nuna bana son abu kada ku tursasa min, ni bana so na cutar da kowa, shiyasa na ke6e kaina saboda in sanyaya zuciyata, kamar yadda kake jina a zuciyarka nima haka nake jinka, haɗin kaine kawai bazan baku ba, sannan ka yi hakuri da bata maka rai da nayi, I didn't realize I was rude to you and disrespected you until he told me."


 runtse idanu chief yayi gam na dan wani lokaci bai furta komai ba, har cikin ranshi yaji dadin maganar da Danish Ya furta mashi na cewa shima yana jin shi kamar yadda yake jin shi, yasan sannu a hankali wata rana zai samu amincewar shi.


Phone ringing dinsa ne Ya sa shi hanzarin buɗe idanun shi tunawa da bakin su, wrist watch din hannun shi ya duba.


"Danish, Ka fito daga cikin ruwan nan haka, Inaso Ka shirya, nasan kana jin yunwa, zan sa ashirya mana dinner"


Amsa mashi yayi da Okay


Fitowa Chief yayi daga toilet din, Ya zaro wayar daga trouser pocket dinsa, misscalled ya gani da layin big guy.


Kira ya danna masa bayan yayi picking, big guy ya sanar da shi cewa yanzu haka suna akan hanya sun dauko su commender daga airpot.


fuskar shi da fara'a ya furta Alhamdulillah Allah Ya kawo ku lafiya, bai sanar dashi game da ganin Danish ba, ya bari sai in ya zo gidan ya ganshi.


Bayan sun yi sallama, Ya kira layin Ci ya sanar da shi game da ganin Danish yace ya sanarma sauran abokan aikin su, Ci yayi farin ciki sosai harya shawarce shi akan su lalla6a shi kada su yi duk wani abu da zai 6ata ma shi rai.


Sai da ya kammala yin wayar ya lura babu Unaisah a dakin, ranshi ya bashi may be ta fita ne don ta sanar da uwanta.


bayan fitar Chief da yan mintuna, A hankali Danish Ya futo daga ciki, har ya cire kayan jikin shi, short kadai Ya bari, sumar kanshi dake a jike ta manne ma fatar bayan shi da gefen fuskar shi, tamkar babu kuzari a jikinshi da wata irin kasala yake taka kafafun shi, a duk lokaci daya rikiɗa ya dawo suffar shi ta mutane ba karamin jiki yake ji ba.



Gaban dressing mirror ya dakata da tafiya ya dafe gaban mirror ɗin da tafin hannun shi ɗaya.


Kunnuwan shi ne suka soma jiyo ma shi motsin mutun a dakin shi, yayi zaton chief ne hakan yasa bai damu daya ɗago da ido ya kalle wanene ba.


"Meyasa ka tafi batare da ka fada min inda zaka je ba? Kasan irin tashin hankalin dana shiga na rashin ganin ka"? Da sauri ya kalle ta ta cikin madubin


Tana tsaye abayan shi ta goya hannayenta kan kirjin ta, abayan labulen dakin shi ta la6e saida taga chief ya fita tukunna ta fito don ta samu damar zazzaga mashi masifa.


Har sai da gabanshi ya ɗan fadi ganin yadda idanunta suka kumbura sun kaɗa jawur ko ba afada masa ba yasan tasha kuka tamkar ranta zai fata.


tuni yasha jinin jikin shi yasan ba zai tsira daga fushinta ba dole ta hukunta shi.


Bai aune ba, yaji ta faɗa kan faffaɗan bayanshi ta zagayo da hannayenta kan broad chest din shi ta fashe da wani irin matsanancin kuka, ta rufe idanunta da ke tsiyayar da ruwan hawaye ta dunkule yatsunta kamar yar dambe ta dinga bugun kirjin shi da karfi, duk da hakan bata huce ba sai da ta gartsa mashi ciwo har sau uku akan fatar bayan sh


Ko kaɗan baiji zafin abun da tayi mashi ba, ya fahimci irin radadin da taji na rashin shi yasan tayi tunanin Ya koma kurkuku ne.  Cikin shesshekar kuka take fada mashi abunda ya faru bayan tafiyar shi.


Zuciyar shi ta karaya ya kara jin tsantsar kaunarta da sonta acikin zuciyar shi, yadda takusa salwantar da rayuwarta saboda shi! Duk da fushin da take da shi na abunda ya faru tsakaninsu hakan baisa ta daina damuwa da shi ba, kamar ma ana kara mata zazzafar kaunar shi.


yayin da yake wannan tunanin idanunshi sun cicciko tab da kwalla a hankali yake kallon hannuwanta dake akan kirjin shi ta gama naushin nashi yanzu tsunkulin kirjin shi ta ke yi duk fa don ta huce radadin daya kunsa mata, zuciyar shi tayi matuƙar karaya saboda tausayin rayuwarsu daya kama shi, yana jin tsoron ranar da mutuwa zatayi masu yankan kauna, yasan dole wata rana ɗaya ya riga ɗaya mutuwa acikin su, fatanshi Allah yasa in ma mutuwarce ta fara daukar shi saboda baisan yaga mutuwar Unaisah, ko ma ta ɗauke su atare saboda yasan ba lallai ta iya surviving batare da shi ba, yana ɗaya daga cikin dalilin dayasa yaki yarda ya bada hadin kai saboda shi ya san me zai biyo baya.


Lumshe idanun shi yayi yayin da siraran hawaye suka fara yar tseral kan kuncinsa, shesshekar kukan ta da yake ji a kunnansa ba karamin karya masa zuciya ta ke yi ba.


Sai da tayi mai isarta, tayi shiru tana kara makalkale jikin shi yana jin duk wani motsinta a jikinshi harta bugun zuciyarta da dumin jikinta duk yanaji anasa jikin..


In a weak voice ta fara magana taja jan numfashi


"Ban hana ka tafi duk inda zaka je ba, amma ka fara tunanin wani hali zan shiga kafin ka yanke shawarar tafiyar, sannan in ma zaka tafi toh ka tafi dani, idan ba haka ba zan hadiyi zuciya na mutu ne"


bata kare maganar ba, yai saurin ruko hannunta acikin nashi ya janyota ta dawo ta gabanshi yayi saurin rungumeta tightly a kirjin shi kamar zasu koma mutun daya.


hijab din jikinta ta jiƙe sharkaf da gumi kamar babu a.c adakin tsabar hucin da jikinta keyi mata ba, da alama Unaisah ta manta da hudubar aunty umminsu ta kuma manta da sharuddan data gindaya mashi na kusantar inda take sai gashi yau saboda halin data shiga na gudun kada ta rasa shi yasa ta kunsata kanta da shi ta kuma rungume shi saboda tana bukatar jin dumin shi a jikinta, tausayinshi da kaunarshine suka rufe mata ido har tagaza gane abunda take badai dai bane ta manta.



Sunyi shiru babu mai magana acikinsu, ko motsi basa sonyi saboda yanayin da suka tsinsu kan su mai wuyar fassaruwa ji suka inama zasu dawwama ahaka sai dai Allah baya barin wani dan wani yaji dadi ko ba mutuwa akwai kaddara da zata iya raba su 🥺



Da wata irin kasala Yasa hannu yaja hijab din jikinta ta zame ta dawo kan kafadarta.


ya cusa hannunshi cikin lallausar sumar kanta ya nannaɗeta gefe guda ya fiddo da kunnnata na dama.


Saitin kunnan ya daura tausasa red lips dinsa cikin sanyin murya mai dadin sauraro ya furta"kamar baki yarda da kaunar da nake maki ba? Meyasa zaki ɗaga hankalinki bayan kinsan cewa bazan iya rayuwa batare da ke ba,  idan ma kina tunanin hakan toh ki daina...." ya faɗa cike da bata tabbaci har cikin kunnnata take jin iskar numfashinsa..


"mutun yana rayuwane tare da ƙaddararsa sannan bai isa ya guje mata ba, nima haka take agurina, bazan taba tafiya nabarki ba in har bake kika bani iznin in tafi ba, ke kadaice zaki bani umarni in bi, gaba ɗaya burin rayuwana akanki ne da yan uwana, bazan ta6a rabuwa babu ku ba, duk runtsi duk wuya zan kasance atare daku"


bai ƙare maganar ba ta tari mumfashin shi da cewa"ka yi hakuri da abun da ya Omar yayi maka, nasan shine ya bata maka rai, nima raina ya 6aci zanyi mashi magana yadaina bata maka rai" ta fada ba tare da ta dago kanta  ba.



Murmushi ya danyi har cikin zuciyarshi yaji dadin maganarta shiyasa yake kara kaunarta saboda kaunar da take masa, zata iya bata mashi rai amma wani bai isa ya daga masa yatsa ta kyale shi ba.



"Ki kyale shi, ba laifinsa bane, ni ne na 6ata masa rai, komai ya faru ni naja ma kaina.."



Hankalin shi Yayi mugun tashi da abunda idanunsa suka gane mashi, tsabar kidima da tashin hankali har wani jiri jiri yake gani acikin idanunshi, da sauri ya dafe kofar dakin gudun kada  jiri ya kwashe shi ya kife ƙasa, Yayi danasanin zuwa dakin Danish dayasan zaiga abunda zai jijjiga

kwakwalwarsa da tashi hankali da baiyi gigin zuwa ganin Danish ba!.


Ya gaza yarda da abunda idanun shi ke nuna mashi da kuma abunda kunnuwanshi suke jiyo mashi.


 Angel dinsa ce kwance ajikin namiji sun kankame juna kamar anta da jini? Wlh bai ta6a zaton zatay mashi haka ba, ta karya zuciyarshi ba kadan ba.


bazai juri kallon su ba, adaddafe Ya juya yabar kofar dakin dama yazo ne donya ga Danish Chief ne Ya bashi labarin sun ganshi, bawan Allah da farin cikinshi ya zo don ya bashi hakurin abunda big guy yayi mashi ashe da rabon yaga abun da zai hana shi runtsawa adaren yau.


shi mamakin shi tayaya Unaisah har tasan dadin ta rungumi namiji? A tunanin shi batai wayon da za ta yi hakan ba, bayan haka yana yi mata kallon mai hankali bai ta6a zaton zatay abunda tasan haramun ne ba.


yana tafiya kamar zai kife kasa saboda jirin dake shirin kwasar shi, babban tashin hankalinshi ya zaiyi ya raba alaƙar su? Saboda ya fahimci azababbiyar kaunace atsakaninsu ko romeo da juliet albarka, kai wannan har layla da majnoon sun shallake sai yanzu ya gane dalilin dayasa ɗazu ta haukace tabi bayan Danish har mota takusa hankadeta ashe sone Ya makantar da ita.



shi azaton shi shakuwace atsakaninsu ashe shine bai fahimta ba, bakomai yake tunawa ba face alkawarin daya daukarwa kanshi na mallaka ma chief Unaisah, tun kafin ma ta bayyana ya bashi ita, sadakine kadai bai biya, ba yadda za'ay ma ya amince ma soyayyar Unaisah da Danish! Ko ta halin ƙaƙa sai ya raba su, bama zai ta6a yiwuwa ba, ay bata isa tasa shi zubda girman shi ba, bare aje ga batun bashi kunya.


Acikin zuciyarshi yake ta sambatu kamar wani zautattace.



Peck ya manna mata akan forehead dinta ta lumshe idanunta tana jin wani irin abu yana ratsa tsigar jikin ta.


numfashi ta ɗanja tare da sauke shi kan kirjin shi iskar ta daki fatar shi.


tana kokarin ɗago da kanta kamar daga sama tajiyo muryoyinsu Batool daga waje suna ambaton sunan Danish a ruɗe ta raba jikin ta daga nashi tayi saurin komawa bayan curtain ta 6oye tana faman sauke ajiyar zuciya.


Bin labulan yayi da kallo baiso suka katse masu hanzarin su ba, murmushi yayi wanda bai wuci fatar la66ansa ba, daga gani yaji dadin faranta masa rai da tayi.


Kamar an korosu suka fado dakin ko sallama babu, da karfin suka hada baki gurin furta"Danish"! Juyowa yayi tare da kallonsu, gaba ɗayan su ne babu wanda babu acikin su.


Wani irin annurin farin ciki ya gani akan fuskokinsu, bayin Allah tun da suka dawo daga headquarter tashin hankalin bacewar shi Ya hana su canza uniform din jikinsu ko wanka ba su yi ba.


harya motsa lips dinsa zai yi magana bai yi aune ba gaba daya suka nife shi suka fada kan jikinshi kamar zasu kayar da shi kasa, saboda yadda suka baibaye shi kamar ƙudajen zuma, gaba daya sautin kukan su ya cika dakin nashi.


dayasan halin da zai jefa su da bai tafi yabarsu ba, a zaton shi sun daina damuwa da shi ashe har yanzu ba abun da ya sauya na daga kaunar da su ke yi ma shi.



Dakyar ya samu suka kyale shi cikin shesshekar kuka suka fara korefe korafe akan tafiyar da yayi yabar su.


Haris daya fara zazzaga mashi masifa kamar zai rufe shi da bugu  kowa yana fada masa irin tashin hankalin daya shiga, murmushi yadinga sakar masu kamar zaiyi dariya saboda sun bashi nishadi sun kuma faranta ranshi, ita Batool da tafi su jin jiki pillow ta dauko ta fara buga mashi kan kirjin shi aikuwa kamar jira suke gaba daya suka fara  wasa da pillows suka dinga kwala mashi ta ko'ina.


tun yana murmushi yana kokarin kare kanshi harya fara tiƙar dariya kamar sakarkaru haka suka saki baki suna kallon shi cike da mamakin ganin Dariyar shi.


 Duk abun da ke faruwa akan idon Unaisah gaba daya ta shagala da kallon fararen hakoranshi masu kyau da tsari sai dariya yakeyi kamar zai shaƙe.


ba su kyale shi ba har saida ya faɗa kan gadon shi yana fadin ya isa haka na kar6i laifi na bazan kara tafiya nabarku ba.." jefar da pillows din su ka yi kan mattress din sai haki suke suna kallon shi sun kewaye gadon shi.


"Waya faɗa maku na dawo" ya tambaya yana kallon su,


Atare suka hada baki gurin furta"daddy Taj" 


"Banyi zaton kun damu dani har haka ba..." bai kare maganar ba suka fara naɗe hannayen shirts dinsu alamar zasuyi bugu dabi'arsu ce tun a prison..


"Ku kyale shi ya gane kuskuranshi" muryar Unaisah ce ta dakatar da su, atare suka jiyo tare da kallon ta, tana tsaye atsakiyar dakin duk a tunaninsu daga waje ta shigo ba su san cewa tana la6e jikin labule ba.


Haduwa sukayi gaba suka zauna gefen gadon shi, ba zasu iya tuna when last suka nishadantu da Danish irin na yau ba, ya sakar masu fuska sun yi fira cikin raha sunyi nishadi kamar lokacin da suke a prison.



Jin shiru Unaisah bata dawo ba, tun da tace ta jira har yanzu bata ji duriyar ta ba, gajiya tayi da zaman dakin shiyasa ta fito don ta neme ta, sai kuma ta taras babu su a falon har zata juya idanunta suka sauka akan taj dake zaune kan sofa ya zabga uban tagumi kamar wanda ya rasa mafaɗi a duniya, tun daga kan yanayin fuskarshi ta fahimci babu lafiya atare da shi, kamar akwai wani abu na damun shi.


Karasawa tayi gaban sofa din da yake ta ambaci sunan shi shiru bai tanka mata ba, har saida ta maimaita kusan sau uku na karshen ne ta ɗaga murya a ɗan firgice ya dago da ido ya kalle ta, murmushi tasakar mashi, da sauri ya fara kokarin danne damuwar shi ya ɗan saki murmushin yake yace"Ummi ya kike, kin wuni lafiya" bata amsa mashi tambayarba sai cewa tay"yalla6ai meke damunka ne? Kusan sau uku ina kiran sunanka baka amsa min ba, anya lafiya" still da murmushi akan fuskarshi ya furta"ummi ba komai lafiyana lou, ba abun da ke damuna"


Tunani tayi kodai rashin Danish ne yasa shi shiga halin damuwa hakan yasa tace"Ya mukaji da abun da ya faru na 6atan Danish? Wlh nima ɗazu Batool ke fadamin, Hankalina ya tashi ba kaɗan ba.." bata kare maganar ba taj yace"oh bakisan An gan shi ba..." waro idanu waje tayi"dagaske"? 


"Eh, ay yanzu haka su Unaisah suna acan dakin shi" wani irin ihun farin ciki ta saki tare da firta Alhamdulillah kusan sau uku tace"wlh naji dadin ganin shi da akayi, saboda hankalina ya tashi musamman ganin yadda yan uwanshi suka gaza cin abinci saboda rashin shi.


"bari naje naganshi" har zata jiya taj ya kira sunan ta tajiyo ta dube shi.


"Idan kin shiga dakin, pls ki kirasu, su zo su shirya akwai baki da zasu zo bayan sallar magbrib"


 amsa mashi tay da toh, zumudin son ganin Danish Ya hana ta tambayi su wanene bakin da sauri ta juya ta nufi upstairs.


Bin ta da kallo taj yayi har ta 6ace ma ganin shi, sunkuyar da kan shi ƙasa yai kamar bawan dake neman gafara, abun duniya ya ishe shi tun dazu bakin cikin abunda yagani yake ta nanukarsa, idanunshi sunki daina tariyo mashi abun takaicin daya gani....



Lokacin da takarasa bakin kofar dakin tunkan ta shiga ta fara jin hayaniyarsu yadda kasan gidan biki ko suna sun cika ko'ina da surutun su.


knocking kofar tayi almost 3 times ba wanda ya buɗe mata, zafin dumi Ya hana su ji bugun kofar, murmushi tasaki tare da tura ƙofaf ta shiga ciki


Tsayawa tayi tare da goya hannayenta kan kirjinta tana kallon ikon Allah sun cike dakin shi, wasu akan couch wasu gefe gadon shi har saman gadon.


ta fahimci yau ba karamin nishadi suke ji ba.


Kokari take ta hango Danish din duk sun rufe shi dakyar idanun ta suka hango mata bayan shi ya kifa kanshi jikin pillow, Unaisah tana kishingiɗe gefen shi sun shagala da kallon juna, sun bar su Batool sai ɗumin surutu suke .


Yanayin fuskartane Ya canza zuwa tsantsar mamaki da rudani, tun da take rayuwa agidan bata ta6a lura da zanan tottoo din shi ba, tasan yana da shi amma bata ta6a ganin dukanshi ba, sai yau datayi arba dashi babu riga a jikin shi, abunka ga farar fata zanan ya fito 6aro 6aro bakomai ne ya rudar da ita face ganin zanan tattoo dinsa sak irin na big boss kamar anyi copying tattoo din big boss an manna mashi abayan shi.


wannan abu ya bata mamaki har ta gaza yi masu magana saboda kallon Abun al'ajabin daya ruke ta..


__________________________💓✍️


Safa da marwa take yi atsakar dakin ta, fuskarta babu walwala ga dukkan alamu akwai wani abu dake damunta wanda yayi silar shigarta halin da take a jiki...


Sallamar dr shureim ce ta katse zancen zucinta, kamar dama jiran shi takeyi da sauri ta nufe fuskarta ayamutse tace"shureim fita zaka yi ne"?

Girgiza mata kai yai"a'a, wurinki nazo inaso muyi magana ne" ya fada tare da wuce ta ya zauna gefen gadonta, itama ta zauna tana kallon shi cike da son jin wata magana ne zasuyi....


"Meke damunki ne? Yanayin fuskarki ya nuna kamar bakya jin dadi"? 

"Shureim lamarin Benazir yana ɗaga min hankali, kai baka lura ba har yanzu da yanayin ta ba? Wani lokaci tana abu kamar mai ta6in hankali ni tsorona kada ta haukace..." ta faɗa sukuku babu walwala, maimakon taga tashin hankali akan fuskarshi sai taga ya saki tausasan murmushi arude tace"lafiyarka kuwa? Ko bakaji abun da nake magana akai bane" ruko hannayenta yayi acikin nashi, fuskarshi da fara'a tace"mommy zan fada maki gaskiya amma kada ki fadamawa kowa..." cike da mamaki tace"toh, Ina sauraronka"  ta fada tana kallon cikin idanun shi

"Benazir taji saukin abinda ke damunta, haukan da kika ga tanayi pretending ne, har tambayarta nayi meyasa take yin hakan? Sai ta nuna min bata son asan ta samu lafiya... Baki asake hajiya layla take sauraron shi tayi mamakin jin hakan aranta ta ayyaba lallai benazir ashe haryanzu tana nan da dabi'arta nayin karyar ciwo.


"Amma shureim baka tunanin akwai wani dalili dayasa benazir take pretending? In ba haka ba taya mutun da lafiyarshi zai za6i zama mai ta6in hankali" ta jefa mashi tambayar 


Shiru yayi jimm shi kanshi yayi wannan tunanin amma koda ya tambayeta sai tace mashi bakomai.


"Gaskiya bana tunanin akwai dalilin dayasa yakeyin hakan cos na tambayeta tace min bada wata manufa ba saina rashin son a rabata da azeezaty" 


Girgiza kai hajiya hajiya layla tayi"ni nasan kayana shureim, Benazir bata ta6a yin abu batare da dalili ba, dole akwai dalili, ni fa najima ina zargin da akwai wani abu da Benazir ta sani ko ta aikata wanda har yaja akayi mata asiri..."


 maganar hajiya layla ta ɗan ɗaga hankalin shi tunawa da bibiyar rayuwar Benazir da akeyi acikin gidan dama kuma yana zargin wanda yayi mata asiri ne yake son karasa kasheta bayan haka itama Benazir din zai iya yiwuwa maganar hajiya layla ta zama gaskiya.


amma saboda bayason ɗaga mata hankali shiyasa yaki sanar da ita zancen bibiyar rayuwar Benazir da akeyi sai dai ya yanke shawarar zai je dakin Benazir don ya tambayeta meya faru da ita aranar data kulle dakin ta.



Yayi zurfi acikin tunaninshi muryar Hajiya layla ta katse shi"kaima kana tunanin abunda nake tunani ne ko kuwa" murmushin yaƙe ya sakar mata"mami bana so ki sanya damuwa aranki, hasashen da kike ba lallai ya zama gaskiya ba, zai iya yiwuwa wani tayi ma rashin kunya kinsan wasu mutanan da bakar zuciya ga mugunta arai watakil ita ta manta da ta bata masu rai shine su kuma da babu Allah aransu suka yi mata asiri don su kuntata rayuwarta, ko kuma wanda ya aikata mata hakan yayi ne da niyar ya ɗauki fansar wani abu da ku ka ta6a yi masa..." dafe kirji hajiya layla tayi da tafin hannunta alamar ta shiga uku itama fa tayi rashin mutunci lokacin da Alhaji ubaid Yake akan mulki tunma kafin ya hau kujerar gomna ba mutunci ne da ita ba, yanzu ne tayi hankali ta gane Allah ɗaya ne.


"Ni fa ban fada maki donki tashi hankalinki ba, inaso ne na kwatanta maki ba lallai hasashen ki ya zama gaskiya ba, banaso ki matsa ma benazir kan ta ta fada maki meyasa take pretending, mu kyaleta kawai iyakacinmu da ita addu'ane kawai ubangiji Allah Ya kare mana ita daga sharrin duk wani abin cutarwa..." amsa mashi tayi da Ameen ita dai hankalinta bai kwanta da lamarin benazir ba.


sun jima suna fira adakin harya bata labarin zuwansu gidan su Azeezaty duk don ya kara kwantar mata da hankali taji dadi kamar ta zuba ruwa akasa tasha tsabar farin ciki.



__________________________💓✍️


akwance take kan gadonta, jikinta sanye da night dress, ta ruƙe wayar ta a hannunta, ta nutsu tana kallon hoton fuskar Unaisah dake akan wallpaper din ta... bata gajiya da kallon fuskar ƴarta, takan wuni tana kallon hotunan su Unaisah ba tare da gajiya ba.


 kwantar da wayar tayi kan kirjinta ta ɗage kai sama tana kallon ceilling.


bakomai take tunawa ba face shawarwarin da Aneelerh ta bata akan yadda zata shawo kan Taj ta hanyar kyautata mashi tun shekaran jiya take tura mashi love messages har yau yaki mata reply kamar tay hauka, ta rasa ya za ta yi ta shawo kanshi har jaraba kiran shi tayi tun da ya ɗaga sau ɗaya yaji muryarta bai kara picking call din ta ba.


ɗago wayar tayi ta shiga cikin whatsapp dinta, a chat dinsu da Anila tayi copying contact  din Unaisah data turo mata..


Cike da marmarin son Jin muryarta ta sanya number din tana kokarin yin saving kwatsam ba zato ba tsammani taga number din already akwai ta a contact list dinta da sunan God gift, Yarinyar da ta kira wrong number a matukar rude ta kurawa contact din ido batare da kyaftawa.


lamarin ya daure mata kai tunani tayi ko dai Aneeleerh wrong number ta tura mata?


zuciyarta ce ta raya mata bakya tunanin duk itace? Dama kuma sunansu iri ɗaya Unaisah hakan na nufin yartace yarinyar da suke waya? Ta jefa ma kanta tambayar, kokwanto ta farayi anya kuwa itace? Yarinyar fa ta fadamata ba abuja suke ba.


"Bari dai na jaraba kira inji" call ta danna almost 20 times ba'ay picking ba, damuwace karara akan fuskarta, jin knocking ɗin room door dinta yasa  ta yin saurin aje wayar kan side drawer ta fara haɗe rai zatay pretending...


A hankali ta shigo dakin, Jikinta sanye da dogon hijabi, a tsakar dakin ta tsaya tana kallon Benazir kamar tana jin shakkar tunkararta,   tayi mamakin Ganin zeenatu adakinta yau wata rana tun lokacin da aka sallameta ba ta kara kusanta kanta da ita ba.


aranta ta ayyana watakil iskokan dake akanta ne suka saketa shiyasa ta fara neman su shirya da juna


Kurama juna ido sukayi batare da kyaftawa ba, har na tsawon mituna kafin zeenatu tay karfin halin firta"Aunty Benazir, zan iya shigowa ciki"?


Ɗaga mata gira Benazir tay ba tare data furta mata kalma ba, wucewa tayi kan gadon ta haye tare da juya mata baya


sunyi shiru kamar basu ta6a sabawa da junan su ba


"Aunty benazir ina Azeezaty? Nasan kuna waya da ita, ba ta6a tambayarki ni ba"? Kallon bayanta Benazir tayi kafin tace"kina nufin babyna"? Tace Eh


"Tana tambayarki, duk in mu ka yi waya sai tace in gaida mata ke.." dadine ya lullu6e zeenatu har batasan sa'adda ta aje kunyar gefe guda ta juya suka fuskanci juna ita da benazir


"Itama ta damu dani, kamar yadda na damu da ita kuma tana so na" ta tambaya tana kallon benazir dake kallon ta..


Ɗaga mata gira tay alamar eh


Murmushi tasaki"yaushe zaki kiramin ita mu gaisa"?


"Gobe in sha Allah" washe baki tayi tana faman kyafkyafta blue eyes din ta...


Ita yanzu tausayi zeenatu ke bata, shiyasa kwata kwata bata ruƙe ta aranta ba.


Ganin kallon da Benazir ke yi mata yasa tay saurin rufe idanunta, cike da jin nauyinta tace"Aunty benazir dan Allah ki yi hakuri da abun da na maki" murmushi Benazir tayi"zeenat laifin me kika min"?



"Banje asibiti na duba lafiyarki ba, bayan kin dawo ban kula ki ba" yar dariya Benazir tayi"haba karki wani damu wlh, nayi maki uziri ya shureim ya fada min bakyajin dadi .." ajiyar zuciya ta sauke har taji sanyi aranta, ta ɗan buɗe idanunta akan fuskar Benazir miƙa mata hannu tayi"nayi missing dinki ba kaɗan ba sisterna rabin raina, da naganki adakina naji dadi, dariyar farin ciki zeenatu tasaki tare da kama hannun Benazir ta ruƙe shi gam a cikin nata.


_________________________________✍️


Bayan sallar Mabrib, gaba dayan su sunyi wanka sun shirya cikin shiga ta mutunci yan matan sun sanya abaya sunyi rolling kamar larabawa, mazan kuma sun sanya   jallabiya kusan kalar shigar da su kayi aranar dinner din Hateem sun yi kyau sosai.


a falo suka hallara mutun ɗaya ke babu acikin su Danish da har yanzu bai karasa shiryawa ba, Ummi ma tana atare da su ta dage sai daukar su pics take yi saboda sunyi mata kyau


"Wai su wanene bakin da zasu zo ne"? Sajeed ne yai tambayar idonshi akan Unaisah, yasan dakyar in batasan su wanene ba, 


"Nima bansani ba, na kosa naga su wanene mu kara hakuri su karaso Allah yasa muga alkhairi"


 su ka amsa mata da ameen, su jemimah sai yan guje guje suke atsakar falon ita da azeeza da parvin kamar wasu tsararrakin juna har saida ummi ta tsawatar masu kafin suka daina wasan..

"Ku nutsu pls, manyan bakine su zasu zo.."


"Aunty ummi su wanene wai"? Akagare Hanna ta tambaya tana kallonta


Ummi tace"nima bansan su wanene ba, amma boss ya fadamin bakin chief ne, tun da naji hakan nasan ba kananun mutane bane, shiyasa nace ku nutsu kada ay abun da za'aji kunya..." 


kallon juna su ka yi, duk sun kagara da su ga su wanene...


Shigowa falon Taj yayi hannayen shi zube cikin aljihun jallabiyar shi,  kwata kwata babu annuri akan fuskarshi kamar wanda aka fada ma sakon mutuwar shi.


 Kwata kwata basu lura da shi ba har saida Javed Ya ambaci sunan shi kafin hankalinsu yakai gare shi, Unaisah na ganin shi ta nufe shi da sauri donta fada mashi abun farin cikin daya faru na bayyanar Danish azatonta bai sani ba.


tana karasowa Taj yayi saurin kauce mata kamar bai ganta ba, fuskarshi a haɗe ya nufi su Naufal Ya mika masu hannu daya bayan daya ya yi musabaha da mazan kafin Ya maida hankali kan su sarah da fara'a yake amsa masu gaisuwar da su ke yi mashi.


gaba ɗaya ta gaza ɗaga kafafunta    saboda faduwar gaban da taji, hankalin ta ya tashi da ganin abun da daddynta yayi mata, kokwanto tayi anya ya ganta? Ko dai bai lura da ita bane? In ba haka meyasa zai shareta ya nufi yan uwanta?


ta sanyawa ranta cewa bai ganta bane saboda bai ta6a mata hakan ba, cike da kwarin gwiwa ta nufe shi a lokacin yana tsaye, ta fada bayan shi ta rungume shi tana fadin"daddy ni baka ganni ba ne..." rai aɗan bace ya furta"unaisah ki sake ni, tun kafin na bata maki rai" ya fada tare da janye hannunta Ya jefar da shi gefe ɗaya.


aruɗe ta kalli fuskar shi, ya haɗe rai kamar ba daddynta ba, ta rasa gane meke faruwa da shi ne.


Babu wanda Ya lura da abunda Ya faru tsakaninsu, Hankalin yan uwanta baya akan su

Duk da haka bata kawo komai aranta ba, ta kuma cewa"daddy, chief ya fada maka an ga danish a cikin toilet dinsa..." banza yayi da ita tamkar baiji maganar ba, hakan ba karamin ɗaga mata hankali yai ba.


komawa tayi cikin yan uwanta ta tsaya zuciyarta cike fal da tunanin sauyawar daddyn nata, fatanta Allah yasa ba wani abu ke damun shi ba.


*✊DAGA ALƘALAMIN BOSS BATURE🔥✍️


2 Comments

Idan kuna da tambaya akan abinda Baku game ba ko kuma kuma Neman littafin da babu a nan kawai ku ajiye tambayarku a ta comment ko wani shawara da Zaku bamu.

Previous Post Next Post

Sponsored Link

Sponsored Post