KUSKURE ƊAYA
Na
_Jiddah S Mapi_
*Chapter 10*
*Kuskure ɗaya is 300 via 6037523268 hauwa shuaibumapi keystone, evidence of payment via 08144818849*
~Tunda ya fita ta kasa zama sai safa da marwa take, tana leka kofa, hanunta ta dunƙule tana runtse ido da addu'a, bai jima sosai ba ya dawo da sallama a bakinshi, da gudu taje wajenshi tace "magani ka ɗauko?"
har yana mamakinta, rikicewan yayi yawa, bai kulata ba kawai yaje inda najwa take kwance, treating ɗinta ya fara, meerah sai addu'a take a fili tana kuka, da rike hanun najwa wanda yake motsi, alluran da yayi mata me zafi ne hakan yasa ta fara buɗe ido tana jin azaban zafin ruwan alluran da yake ratsa jikinta, ido huɗu sukayi dashi, wani irin kallon tsana ta aika
mishi, shima kallon tsanan yayi mata suka kawar da kai a tare, murmushi meerah tayi batasan time ɗin data rike hanunshi tace "na gode sosai na gode"
zame hanunshi yayi yace "ki samo ruwan sanyi ki rinƙa shafa mata a fuska da tafin kafa akai akai"
da sauri ta tashi tace "Tom"
tana fita najwah ta watsa mishi harara, baiko kalleta ba ya ɗauki properties ɗinshi zai tafi, muryanta baya fita sosai tace "kada kayi kuskuren rabani da yayata"
juyowa yayi ya kalleta, murmushin gefen baki yayi yaci gaba da tafiya, cikin dauriya ta kuma cewa "idan ka rabani da ita zan rabaka da komai naka"
cak ya tsaya ba tareda ya juyo ba yace "ki daina shaye-shaye domin zai iya taɓa miki lafiyan ƙwaƙwalwa, gashi ma ya fara"
tashi tayi a fusace tace "nice ƴar kwaya?"
fita yayi yabarta, zuciyanta yana tafasa har tana huci, da meerah suka haɗu a kofa tana rike da roba da ruwa me sanyi a hanunta, murmushi tayi mishi me sanyi, shima yayi mata murmushin, tace "zaka wuce?"
gyaɗa kai yayi, cikin sanyi tace "to na gode sosai"
yace "ki kula da kanki"
a hankali tace "to"
tafiya yayi tana tsaye tana kallonshi har ya fita, shiga ɗaki tayi da murmushi akan fuskanta, daina murmushin tayi lokacin da idonta ya sauka akan najwa, ɗauke kai najwa tayi, karasawa tayi ta fara goge tafin ƙafan ba tareda tayi mata magana ba, har ta gama babu wanda yayi magana cikinsu, tashi tayi zata fita najwah tace "ina fatan kin bashi kariya me kyau baiji ciwo ko kaɗan a jikinshi ba?"
shiru tayi jikinta yayi sanyi, a hankali ta juyo ta koma ta zauna a gefenta, hanunta ta rike tace "najwah kiyi hakuri banyi hakan dan na..."
hanu ta ɗaga mata "no need"
shiru tayi bataji daɗi ba, fita tayi ta fara dafa abinci, jikinta duk a mace ga ciwon kai, harta gama ta kawowa najwah, ci tayi kaɗan saboda yunwan da takeji, komawa tayi ta kwanta, itama meerah ta kwanta domin kanta yana ciwo, shiru ɗakin yayi kowa da abinda yake tunani, meerah fuskan momy take gani, gaskiya bata yadda da wannan matar ba da kwai abinda take shiryawa, ji tayi ta kasa nutsuwa da barin haydar kusa da matar, sai take ganin kamar ba sanshi take ba kamar wani shiri takeyi, haka kawai taji tanason kareshi daga sharrin matar, kodai itace ta haifeshi?"
da sauri tace "zai iya zama itace ta haifeshi amma babu kama"
tunani babu irin wanda batayi ba, najwah ma tunanin take "nice me shaye-shaye? lalle sai nayi saurin shiga tsakanin unty meerah da wannan mutumin, banajin kwanciyan hankali a duk lokacin da suke tare, sai naji gabana yana faɗuwa anya ba wani abinda yake bibiyan meerah dashi na sharri?"
kallon meerah tayi sannan tayi magana a ranta "tabbas idan tana tare dashi inajin faɗuwan gaba da rashin nutsuwa sosai"
haydar shi kaɗai yake tsaki idan ya tuna da magananta, anya wannan zata bari suyi kusanci da meerah? to ina iyayensu da suke zaune su kaɗai? wannan ta kwancen itace me taurin kai da gani tana wahalar da meerah, tsaki ya kuma ja yace "nonsense da ganinta batada kamun kai"
harya isa gida bai daina jin haushinta ba, salma ya gani ya ɗaga mata hannu, da sauri tazo ta durkusa kasa "gani yallaɓai"
yace "ya mamin?"
shiru tayi, da sauri yace "meya sameta?"
a hankali tace "gaskiya hukunta ya dameta ta rinƙa birgima, nayi ta kiranka baka dawo ba sai daga baya na fahimci cikinta ne yake ciwo"
da sauri yace "muje na ganta"
girgiza kai tayi "Abbanka yace kada kowa yaje duk wanda ya shiga duk abinda ya sameta shiya janyo mata"
tsayawa yayi baije ko ina ba, sai kuma yace "zanje saide duk abinda zai faru ya faru"
momy ce tace "Haydar meyasa kakeso ka zamewa mahaifiyarka damuwa a rayuwarta?"
da mamaki yace "matsala?"
jijjiga kai tayi tana aje flask akan dining, karasowa tayi inda yake ta rike hanunshi, akan kujeran dining ta zaunar dashi itama ta zauna ta zuba mishi abinci sannan itama ta zuba, kallonshi tayi tace "ci mana"
ganin baisa hanu ba tayi murmushi tace "meyasa baka lura duk lokacin da kayi kusanci da maminka a lokacin abbanka yake kara tsananta da kuma azabtar da ita?"
ganin yayi shiru da alama magananta zaiyi tasiri tace "ina ganin nesanta kanka da ita shine zaifi mata sauki domin kuwa duk wani abinda yake faruwa a gidannan abbanka yana kallo, me zai hana ka nisanta kanka da maminka ka daina zuwa kusa da ita ko hakan zaisa ta kwana lafiya koda sau ɗaya ne a rayuwarta?"
shiru yayi ya zuba mata ido, gaskiya take faɗa domin duk lokacin da yaje wajen mami sai Abba ya tsananta muguntanshi akanta, tashi yayi yabar wajen, tabi bayanshi da kallo tana yin shu'umin murmushi, haɗuwa sukayi da nadiya wacce take mika tana hamma da alama daga bacci ta tashi, lumshe ido tayi tace "ya haydar"
kafin yayi magana ta rungumeshi, da sauri ya tureta yana aika mata kallon gargaɗi, tana tsaye a wajen harya shiga ɗakinshi, wanka ya shiga yayi a cewarshi zai wanke dattin daya taɓa a jikin najwah, saida yayi wanka me kyau kafin ya fito ya zira jallabiya me taushi ya shinfiɗa sallaya, salla yayi kafin ya koma gado ya kwanta, tunani ya fara kamar kullum "waye yake nema ya kasheshi? da farko yana zargin momy amma yanzu yana ganin ba itace ba, domin kuwa idan da itace meshi ba zai taɓa jimata rauni ba, meerah itace take zame mishi kariya a duk sanda wani abin yake shirin faruwa dashi, da farko nawaf kaninshi shine yake kareshi daga komai saide yana ganin kamar zai jefa rayuwar nawaf a haɗari hakan yasa ya kaishi karatu kasar India ba tareda kowa ya sani ba, har Abba bai san inda nawaf yake ba, domin kuwa babu wanda ya kai Abba tsanan ƴaƴanshi"
A ranan sun yini da najwah bata saki jikinta sosai ba, duk meerah a tsarge take tana ganin kamar najwah zata riketa arai tace taje wajen haydar ta kyaleta, da dare bayan tasa mata abinci taci, magani ta bata tasha, ido najwan ta zuba mata ganin jikinta a sanyaye ta riko hannunta tace "unty meerah ki saki jikinki kinsan dai ba zan taɓa iya yin dogon fushi dake ba ko?"
rungumeta tayi tace "dan Allah najwah kiyi hakuri bada sona na barki ba"
girgiza kai tayi tana murmushi tace "komai ya wuce amma inaso kimin alkawari ba zaki kara zuwa wajenshi ba koda kuwa me zai sameshi"
a hankali tace "na miki alkawari ba zan kara zuwa ba"
murmushi tayi tace "that's my sister, yanzu ya kikejin kan naki?"
a hankali tace "da sauki"
kwanciya tayi ta ɗaura kanta a ƙafan meerah ta lumshe ido, a hankali take shafa kanta tayi shiru tana aikin tunani.
*washe gari*
wayan daya bata ta aje ta saman gado, breakfask take haɗa musu da wanda najwa zata tafi school dashi, najwah kwance take ta lulluɓa kanta da bargo sai baccinta take cikin nutsuwa da kwanciyan hankali kamar ma ta manta zataje makaranta yau, meerah ta ɗaga murya tace "najwa tashi ki shirya kinyi late fa"
cikin muryan bacci tace "to"
kara lulluɓa bargon tayi wannan karon harda kanta ta rufe, taci gaba da baccinta, meerah girkin take a tunaninta najwa ta fara shiri, flask ta ɗauka ta zuba mata na zuwa school sannan ta juye musu sauran a plate, zuwa tayi tana cewa "zo muci saiki tafi"
waro ido tayi ganin bacci take, dire plate ɗin tayi a kasa ta fita zuwa waje, ruwan me sanyi ta ɗibo a cup tazo ta tsaya akanta, yaye bargon tayi zata kwara mata ruwan, da gudu najwa ta buɗe ido, dira tayi a gadon ta fita daga ɗakin "wayyo Allah unty meerah kiyi hakuri"
dariya meerah tayi "da kin tsaya ai"
wanke jikinta tayi dan tace ba zatayi wanka ba akwai sanyi, mai ta shafa a hankali take yin komai kamar batayi late ba, uniform ɗin tasa kana ta zauna suka fara cin abincin, har meerah ta koshi ta tashi ta shirya najwah bata gama cin abinci ba, ɗauke plate ɗin tayi, shagwaɓe fuska tayi "dan Allah unty meerah ban koshi bafa"
"bakida niyan ci tashi muje"
tana tura baki ta tashi suka fita, rufe kofan meerah tayi kana ta ɓoye makulli a karkashin dutse, jerawa sukayi suna tafiya meerah tace "yau banda kuɗi da mun hau mashin"
najwa tace "kullum kinayi ya kamata ranan da bakiyi ba ki daina damun kanki"
shiru tayi tace "nasan ba zaki iya ba dauriya kawai kike"
tace "mu daina wannan maganan"
sabon hira suka fara har suka isa school ɗin, najwa ce ta shiga meerah kuma ta juya zata tafi, malaminsu najwa ya tsayar da ita ta hanyan kiran sunanta, saida gabanta ya faɗi taje inda yake, cikin nutsuwa ta durkusa ta gaisheshi, amsawa yayi yace "muje ciki akwai maganan da zamuyi"
shiga sukayi ciki ta zauna akan kujeran office ɗin ta zuba mishi ido, yace "malama meerah muna gab da koran kanwarki a wannan makarantan"
da sauri tace "me tayi?"
yace "kanwarki batada tarbiyya bata mutunta malamanta ga taurin kan tsiya idan tace zatayi abu tofa dole sai tayi babu wanda ya isa ya hanata koda ko nine, muna barinta ne saboda darajan da kike bamu amma ba dan haka ba da mun daɗe da korarta a school ɗinnan"
ƙasa ta sauka tace "dan girman Allah kada ku koreta wallahi zan mata magana, idan ta daina zuwa school bansan ya zanyi ba, itace last hope nawa kaima ka sani"
shiru yayi badan wannan me hankalin ba zai koreta amma tunda ta bada hakuri dole yayi hakuri yasa ayi mata faɗa, a hankali yace "ba komai amma kiyi mata magana, ranan da akace babu ke to rayuwarta zata shiga cikin matsala domin kuwa zata rasa abubuwa da dama"
da sauri tace "insha Allah ba zata rasani ba"
yace "Allah yasa"
"Ameen na gode"
tashi tayi ta fita, bataji daɗi ba ace najwa batasa hankali akan karatu ba, duk faɗi tashin da take saboda najwa ta samu rayuwa me kyau ne a gaba, da wannan tunanin ta isa inda take wanke wanke domin samun kuɗi, har kasa ta durkusa ta gaida madam, harara ta ɓalla mata kana tace "yau ba wanke wanke zakiyi ba abinci zaki rinƙa kaiwa mutanen da sukayi mana ciniki"
a hankali tace "tom"
zama tayi a gefe tana kallon yadda madam takesa abinci a takeaway, tace "zo ki rinƙa sawa a leda idan mun gama saiki fara kai musu be fast"
tashi tayi taje ta fara sawa a leda, sun ɗau lokaci kafin suka gama, kwatancen inda zata fara kaiwa tayi mata, nan take meerah ta fara kaiwa kowa nashi, ta gaji sosai da kyar take tafiya harta iso wajen madam, mika mata babban takeaway tayi tace "ga wannan hotel ɗin submitt zaki kai"
waro ido tayi tace "hotel?"
harara ta banka mata "ba zaki kai bane?"
shiru tayi, tana tuna idan taki kaiwa ina zata samu kuɗin siyawa najwa magani da biyan school fees da kuma kuɗin abincinsu?"
cikin tsawa tace "nace ba zaki kai bane?"
karɓa tayi tace "zan kai"
a hankali take tafiya jikinta a mace, kuɗin mashin ɗin da aka bata ta shiga dashi, a kofan hotel ɗin aka tsaya, me mashin ɗin kanshi wani irin kallo yake aika mata, da sauri tace "lafiya malam?"
ciro wayanshi yayi ƴar karama keeypad yace "samin sha ɗayanki zamuyi magana gobe ki gayamin inda zamu haɗu karki damu kuɗi ba matsala bane"
idonta ya cika da hawaye tace "ka fara taimakawa kanka da kuɗi kafin ka taimaka min"
tafiya ta fara yace "taimakon juna zamuyi ai, karki nuna bakisan komai ba mana bayan gashi kin kawo kanki wa wani"
bata juyo ba tafiya kawai take, ita kaɗai tasan raɗaɗin da takeji a ranta, shiga cikin hotel ɗin tayi har zuwa ɗakin da aka faɗa mata, knocking tayi ya buɗe kofan yana kallonta, mika mishi tayi "gashi"
bai amsa ba sai kallonta yake, tace "gashi mana malam"
murmushi yayi ya rike kugu yace "shigo mana"
tace "ba shigowa nazo ba sako aka bani na kawo maka"
ganin ba zata shigo ba yasa hanu zai karɓa ya haɗa da hannunta yana shafawa, sakin ledan tayi ya faɗi kasa, maruka masu zafi ta wanke fuskanshi dasu, dafa kunci yayi yana kallonta, juyawa tayi zata tafi a fusace, fizgota yayi ya fara marinta kamar zai tsinke mata kumatu, gefen bakinta saida ya fara fitar da jini, faɗuwa kasa tayi idanunta suna juyawa jin wani marin daya kara mata, ganin zaiyi kanta da duka taja da ciki da kyar ta samu ta tashi tabar wajen, yace "nonsense da kin tsaya ai"
kuka take harta fita daga hotel ɗin kasancewar an sallameta da kuɗinta na yau, kawai ta wuce gida, faɗawa tayi akan gado ta rinƙa rusa kuka harta gode Allah.
Najwah takaddunta take tattarawa wanda bata rubuta komai a cikinta ba, malamin daya gama musu karatu yace "ke baki rubuta komai ba ina zakije?"
kallo ɗaya tayi mishi ta watsar sannan taci gaba da tattara takaddun har ta zuba a jaka ta goya jakan a bayanta, raɓawa tayi ta gefenshi zata wuce yace "ke najwah kina ganin ba cutar da kanki kike ba? baki rubuta komai ba kuma zaki tafi gida?"
tsayawa tayi tace "ba sai na rubuta ba duk abinda ka rubuta yana rubuce a ƙwaƙwalwa ta"
yace "karki raina min hankali mana"
murmushi tayi tace "me zan samu idan na raina maka hankali?"
hanunta tasa akan igiyan jakan tana wasa dashi ta juya bawa Black bot baya, duk abinda yake rubuce akan bot ɗin ta fara karanta mishi idonta a rufe, bashi ba har malaman da suke wucewa da kuma sauran ɗaliban saida suka tsaya kallonta, saida ta gama karantawa ko harafi ɗaya bata ɓata ba kafin ta buɗe ido tace "najwah tasan me takeyi koda sau ɗari zakuyi mana lesson a rana ɗaya najwah zata iya karanta komai ba tareda ta manta ko rabin harafi ba bale ɗaya"
cigaba tayi da tafiyanta, class ɗinne ya kaure da tafi, harta malaman saida suka tafa mata, ashe tasan meta taka shiyasa bata note, ko sau ɗaya bata taɓa nunawa kowa irin baiwan da take dashi ba, fita tayi bata kula kowa ba, gani tayi meerah bata zo ba tafiya kawai tayi domin yunwa ta fara ji.
*Jiddah Ce...✍🏻*
08144818849