Kuskure Ɗaya page 8 Complete by Jiddah S Mapi

Kuskure Ɗaya page 8 Complete by Jiddah S Mapi

 

Kuskure Ɗaya

KUSKURE ƊAYA

🌸🌸🌸🌸🌸🌸

        Na

_Jiddah S Mapi_

*Chapter 8*

*Make your payment for complete is ₦300 via 6037523268 hauwa shuaibumapi keystone, evidence of payment via 08144818849*

                  ~Koda ya fito daga wanka sallaya ya shinfiɗa ya zira jallabiya ya idar da sallan sannan ya tashi ya cire jallabiyan, boxer fari ne a jikinshi ya nufi gaban mirror ya fara shafa lotion, jamal ne ya shigo baiko kalleshi ba yaci gaba da abinda yakeyi, tea ɗin da aka ajewa haydar ɗin ya ɗauka ya shanye, ta cikin madubi ya kalleshi tareda cewa "idan da poison a ciki kuma fa?"

waro ido yayi yana buɗe baki "meya kawo wannan maganan?"

tashi yayi yana ciro kayan da zaisa yace "idan an kawomin abu ka daina sha sabida kasan rayuwata a koda yaushe zan iya mutuwa ta kowane hanya"

jamal yace "to ai naga kun fara shiri da momy kamar baya, me zaisa kayi zargin hakan?"

murmushi yayi yana gyara zaman kwalan riganshi yace "har yanzu ban gama yadda da ita ba, saina tabbatar da abinda take nufi kafin na yadda da ita"

rigan uniform ɗin ya rike a hanu, da briefcase ɗinshi, yana rike da car key yace "muje"

tare suka fita, Dady ya gani da alama yayi tafiya yau ne ya dawo domin manya motoci ya gani a cikin gidan da kuma kofan da sauri yake shirin shiga motarshi domin bayason ko ganin Dady, daga nesa ya kwala mishi kira "Aliyu?"

tsayawa yayi domin Dady yana tare da manyan baki, duk sunsa manyan kaya da huluna masu matukar tsada, tare suka karaso inda yake Dady ya nuna kamar ba komai tsakaninsu dama hakan yake yi a duk lokacin da suke cikin mutane baya nuna asalin halinshi, hanu ya buɗe mishi alaman yazo, a hankali ya rungumeshi a kunne ya raɗa mishi "ka kiyaye duk wani motsinka gwargwadon nuna halina a cikinsu gwargwadon wuyan da maminka zatasha"

sakinshi yayi yana murmushi yace "har zaku tafi asibitin baiyi safe ba?"

girgiza kai yayi yace "no Dady ai da safiya ake kama fara"

nuna abokanshi yayi yace "meet my friends wannan baka ganeshi ba? shine wanda ya nemi takaran shugaban kasa ai muna fatan shine next president namu"

durkusawa yayi alaman girmamawa ya gaishesu, hanu suka mishi duka gaggaisa, ɗayan yace "ya akaji da ɓatan mahaifiyarka? muna fatan Allah ya bayyana ta cikin koshin lafiya"

kallon Dady yayi sai kuma ya kallesu yace "ameen ya Allah"

daga nan ya buɗe motarshi ya shiga jamal kam ya jima da fita yana jiranshi a kofa, fita yayi da sauri dan bayaso su kara mishi magana, yana fita ya ɗagawa jamal hanu suka kama hanya.


koda yaje sun gama duba marasa lafiya kamar kullum, shima ba wani daɗi yakeji ba har yanzu kanshi na ciwo, office nashi ya koma, a lokacin tunanin meerah ya dawo mishi sabo, duk yadda yaso ya kawar ya kasa saida ya cigaba da tunanin, jamal ne ya shigo da ledan drip a hanu, ganin yayi nisa cikin tunani harda lumshe ido yace "nifa ban gane ba haydar, nasan dai baka soyayya hasalima baka kula kowace mace, meyasa kake murmushi kai kaɗai kuma kake yawan tunani ko dai ka fara soyayya ne?"

shiru yayi mishi kamar ba zai amsa ba, sai kuma ya kalleshi shima da alaman tambaya yace "ya ake gane an faɗa soyayya?"

aje drip ɗin yayi ya tafa mishi kafin yace "i can't emergen abokina ya faɗa soyayya, yau kaine kakeso na faɗa maka yadda ake faɗawa soyayya?"

tsaki yaja "banason iskanci idan ba zaka faɗa ba shikenan"

"me zai hanani faɗa?"

zama yayi akan desk yace "idan kaga kana yawan tunanin mutum ko kuma ta rinƙa yimaka gizo, ko ka rinƙa tuna duk wani moment ɗin da kake ganinta, to alama ne na ka faɗa soyayya"

jin yayi shiru yace "amma faɗamin wace Lucky girl ɗin ka samu? wacece tayi nasaran sace zuciyar da mata fiye da dubu sukayi kokarin sacewa basu dace ba? wacece tayi wannan nasaran zanso ganinta na jinjina mata"

kawar da kai yayi yace "me zaisa nayi soyayya bayan kasan duk wacce ta zauna dani rayuwarta zai iya shiga cikin gagarumin matsala ba zanyi gangancin jefa rayuwar innocent girl cikin damuwa ba"

cikin rashin jin daɗin maganan jamal yace "ƙaddara idan ta tashi ba ta yadda bata zuwa, faɗan haka kamar kana wasa ne da ƙaddara"

har jamal ya gama magananshi bai yi magana ba, sanin halinshi yasa Jamal tashi ya ɗau drip nashi ya tafi, jujjuyawa yake akan table ɗin yana kallon p.o.p.


"unty meerah nima yau nayi lafiya da kaina zanyi mana girki"

najwa ce take magana tana ɗauraye tukunyan dake hanunta, riga me shara shara ne a jikinta light pink, kasancewar rigan babu kauri yasa kana iya ganin farin fatarta daya bayyana, wando baƙi three quarter tasa sannan tasa wani hula me faɗi, tayi kyau sosai kamar ka saceta ka gudu, meerah kujera ta janyo ta zauna a gefe tace "to bari na bawa idona abinci yau pretty zatayi girki"

dariya tayi har gefen kumatunta ya lotsa yace "unty meerah kada ki gyarani duk yadda zanyi so nake na tabbatar da iya girkina"

"to shikenan"

hura wuta tayi ta fara jajjaga attaruhu da albasa, da mamakin meerah taga bata soya manja ba ta zuba ruwa da attaruhun ta ɗauko magi da gishiri da kuma ajino ta fara zubawa babu kakkautawa, gishiri ta cika cokali sau uku ta zuba, ɗago kai tayi bayan ta rufe tukunyar, ido suka haɗa ta sakar mata murmushi, zama tayi a gefe tana jira ya fara tafasa, jim kaɗan ya fara tafasa tsalle tayi dan buɗe tukunyar kada ya zube, da gudu taje ta ɗauko shinkafa, wankewa tayi ta zuba sannan ta kuma rufewa, duk haɗa ido da zasuyi da meerah sai tayi mata murmushi, meerah shiru tayi, littafi taje ta ɗauko a ɗaki ta zauna akan turmi tace "unty meerah kafin ya dahu bari naci gaba da karanta mana littafin, kinsan bana gajiya da karanta littafin AKWAI DALILI mun tsaya inda Anmol taje prison"

jijjiga kai tayi a hankali, buɗe littafin tayi ta fara karantawa, tayi nisa sosai meerah taji kaurin abincin amma bataso ran najwa ya ɓaci tunda tace kada tace komai har sai ta gama girkin, waro ido najwa tayi jin Attaruhu ya fara bin hancinta ga wani warin konewa da yake, yar da littafin tayi da gudu taje ta sauke tukunyar akan wuta, tsalle ta fara tana yarfa hannu jin ya ƙonata, da sauri meerah taje tana duba mata hanun, rikicewa tayi tana cewa "kin kone? sannu, yana miki zafi? bari nasa miki ruwan sanyi, yana miki zafi?"

ganin idonta ya cika da hawaye jikin najwa yayi sanyi, zame hanun tayi a hankali duk da zafin da yake mata ta maida fuskanta normal tace "ba wani konewa da nayi" ta karashe maganan tana turo ɗan karamin bakinta, hamdala meerah tayi, duk da haka bai hana tasa mata ruwan randa me sanyi ba, riketa tayi tace "to hajiya ameerah samu waje ki zauna kici abincin kanwarki me daɗi"

akan kujeran ta maidata ta zauna, kitchen ta shiga ta ɗauko plate da cokali, zuwa tayi ta buɗe abincin a hankali ta fara zubawa, cokali tasa musu kana tazo ta aje a gaban meerah, ɗaki taje ta ɗauko sallaya ta shinfiɗa ta zauna itama tace "muci"

meerah tana ganin shinkafan tasan ko kwatan dahuwa baiyi ba, cokali ta ɗauka ta ɗiba ta kai bakinta, tauna ɗaya da tayi saida taji kamar ta tsala ihu tsaban barkono, ga shinkafan kamar bai taɓa ruwa ba, ganin yadda najwa ta kafeta da ido alaman "yayi daɗi?"

gira ta ɗaga mata sannan tayi mata alama da babban yatsanta irin good ɗinnan, cikin murna ta rungumeta "yeeee unty meerah naji daɗi ashe na iya girki"

tare sukaci abincin, meerah badan tanaso ba saidan batason ganin ɓacin ran ƴar uwarta tace "ki karamin"

kara mata tayi ita kuma ta ɗau ruwa tace "yaji yayi yawa bazan iya cinyewa ba"

meerah ta daure ta cinye sannan tace "kinyi kokari"

ɗauke plate ɗin tayi ta wanke kana ta dawo tace "unty meerah yau weekend ne muje yawo mana"

meerah tace "kinason fita ne?"

gyaɗa kai tayi, tace "okay tashi ki shirya"

da gudu ta tashi ta manna mata kiss a gefen kumatu, cikin murna ta ɗibi ruwan wanka, farin ciki meerah takeji ganin najwa ta samu sauki da kanta take komai, hakan ba karamin daɗi yakesa tanaji a ranta ba, da sauri ta fito daga wankan tana rike towel nata da yake faɗuwa, meerah wanka ta shiga jim kaɗan ta fito, har najwa ta shafa mai da powder, sai lipstick data shafawa pink lips nata, kafin ma ta gama shiri har tafi kyau yin kyau, murmushi meerah tayi a ranta tana godewa Allah da irin kyawun da yayi musu, musamman najwa wacce ko macece ta ganta saita kara kallonta, wajen kayansu taje, leshi pink ta ciro mata ɗinkin dogon riga fited da hannayen rigan me faɗi, duk da kayansu ba me yawa bane meerah tana kokarin siya musu kaya me kyau, mika mata tayi, tana murmushi tace "unty meerah kamar kinsan kayan da nakeson sawa a raina kenan"

tace "dama ai duk abinda kikeso na sani, fuskanki kaɗai idan na gani ina gane me kikeso me kuma bakya so"

murmushi tayi ta fara kokarin sa kayan, meerah tana shafa mai tace "ki rinƙa jin kunyan canja kaya a gaban mutum"

zuwa tayi ta juya mata baya tace "kijamin zip ɗin"

jan zip ɗin tayi, itama meerah tasa wani atamfa me adon pink a jiki, ɗinkin riga da skirt ne, wani mayafi najwa ta yafa sannan tasa flat shoe ta fesa turarensu me ƙamshi, duk da ba tsadadden turare bane me arha ne, amma haɗin hannu amma yana bala'in ƙamshi, kallonta meerah tayi bayan itama ta yafa mayafin, najwa tace "muje"

girgiza kai tayi, da sauri ta kalli jikinta tace "menene?"

meerah tace "wannan mayafin yayi karami, ya kamata ki karanci yanayin jikinki najwa, kinada halittan daya kamata ki rinƙa ɓoye kanki badan komai ba saidan tsoron kada ki haɗu da miyagun mutane su cutarmin dake"

yamutsa fuska tayi kana tace "unty meerah na rufe bayana fa ki gani mana"

janye mayafin meerah tayi kana ta bata na jikinta wanda yafi wancan ɗin girma ta yafa mata najwa ta ɓata rai tana kallonta harta rataya mata jaka me kyau a kafaɗarta, hanunta ta rike tace "muje"

har sun fita kofa meerah tace "laa kinga na manta kuɗin da zamu ɗanyi siyayya bara na ɗauko"

komawa tayi taje cikin drower ta buɗe ta ciro kuɗaɗen da take adanawa domin fita da najwa wuraren da zaisa ta rinƙa mance damuwanta, Allah ne kaɗai yasan irin ihu da tsawan da madam tayi mata a wajen siyar da abinci kafin ta tara kuɗin nan, fitowa tayi ta rufe kofan tasa makullin a cikin jakan dake hanun najwa, jerawa sukayi suna tafiya mutane sai kallonsu suke, tsaki najwa taja tace "wai nikam wani irin kallo ne mutane suke binmu dashi kamar basu taɓa ganinmu ba? ƴan kauye kawai"

meerah tace "kiyi hakuri dole idan mutum yayi kyau a kalleshi"

mashin ta tara musu tace a kaisu ShopRite, bayan sun shiga najwa ta kalleta "dama unty meerah kinada kuɗin kaimu ShopRite? ai nayi zaton gidansu unty faty zamuje"

girgiza kai tayi

"duk abinda zai saki farin ciki ina tanadawa, da fatan zakiyi farin cikin fitanmu yau?"

rike hanunta tayi tace "kwarai kuwa koda baki fita dani ba ganinki yana sani farin ciki"

me mashin yace "amma gaskiya kun birgeni na daɗe banga yaya da kanwa wacce suke san juna kamar ku ba, ina fatan kada ku fara soyayya nan kusa"

najwa tace "banida burin daya wuce naga unty meerah ta samu me sonta sun fara soyayya harma suyi aure"

me mashin yayi murmushin gefen baki kana yace "ba zaki gane bane zata iya san mijinta fiye dake hakan zai nesantaki da ita"

a fusace tace "dakata! yayata ba zata taɓa barina a halin da nake ciki tafi san mijinta fiye dani ba, ni nasan irin soyayyan da take min koda shi ɗin wanene"

yace "Allah baki hakuri"

abinda basu lura ba shine meerah tunda suka ambaci kalman soyayya gaba ɗaya ta faɗa duniyan tunanin, ita kaɗai take murmushi, lumshe ido tayi tana ganin fuskan haydar wanda ya kasa gushewa daga tunaninta, har suka isa ShopRite bata daina murmushi tana lumshe ido ba, najwa ta sauka a mashin ɗin, tace "muje unty Meerah"

da mamaki ta kalleta ganin tanata murmushi bama tasan sun isa ba tace "unty meerah?"

ɗan bugunta tayi, firgigit ta dawo hayyacinta, da manyan idanunta ta kalli najwa "na'am kina magana?"

gyaɗa kai kawai ta iya yi da tarin mamaki, bata taɓa ganinta cikin wannan yanayin ba, amma ta lura tun jiya take wasu irin ɗabi'u wanda sukafi kama da shauƙi, biyan me mashin kuɗinshi tayi kana ta rike hanunta suka shiga ciki, direct wajen kayan abinci suka nufa najwa ce take zaɓa musu abinda zasu siya.


"gaskiya naji daɗi sosai haydar daka kawoni nan da kanka, ban taɓa tsammanin zaka katsar da aikinka ka kawoni ba"

momy ce take magana yayinda suke tafiya tareda haydar, yayi matukar kyau cikin shadda black color da black ɗin hula, farin fatarshi ya haska sosai sai ƙamshi yake amma fuska babu walwala, badan yaso ba ya kawo momy shoprite sabida yanaso me aiki ta taimakawa mami tayi wanka, hakan ba zai faru ba saiya kawar da hankalin kowa na gidan, shiyasa na momy tace ya kaita shoprite motarta ta samu matsala kuma batason shiga mota wanda ba tinted ba, da sauri ya yadda ba dan yaso ba sai dan mahaifiyarsa, kallon wayarshi yake yana duba duk abinda yake faruwa a asibitinshi, duk wani lungu da sako saida ya maƙala camera ta yadda ko baya cikin asibitin yakan iya ganin duk abinda yake faruwa, haydar mutum ne me matukar basira yasan duk wani takunshi, wani lokaci nawaf yake turawa pin ɗin idan yana busy yaci gaba da kalle mishi duk abinda yake faruwa, tuntuɓe sukayi da sauri ya ɗago a lokacin ta juya baya domin ɗaukan turaren da unty meerah tace mata ta ɗauka, kasancewar tana cikin murnan ɗaukan turaren baisa tayi masifa akan bigeta da yayi ba, momy ce ta fara dube duben abinda zata ɗauka, kallonshi tayi ganin hankalinshi yana kan waya tayi saurin ciro wayarta tayi text kamar haka "yanzu zamu fito be ready, ina fatan yau burinmu ya cika"

da sauri ta kashe wayan ta kalli katon kwalin sabulun dake gabanta, tace "yawwa ga abinda ya kawoni kuma na samu, muje"

yana kallon waya ya kama hanyan tafiya tana biye dashi, daidai bakin kofa sukaji karan fashewan kwalban turare, juyawa yakeda niyan yi momy tayi caraf ta riko hanunshi, bataso mission nata ya ɓaci, idan ya koma ciki tasan ba zasu samu su aiwatar da komai akan lokaci ba, kallonta yayi tace "muje sauri nake naje gida fitsari nakeji"

gyaɗa kai yayi sukaci gaba da tafiya.


najwa ce ta yar da kwalban turaren atake ya tarwatse a wajen, jin muryan Abba a cikin kunnenta yasata shiga wannan halin, cikin kakkausan murya yace "hello pretty"

wannan maganan yasa ta yar da kwalban turaren, waro manyan idanunta tayi tana komawa baya yayinda shi kuma yake binta duk wani taku da tayi domin nesa dashi sai yayi domin kusanta da ita, mannuwa tayi da jikin bango jikinta yana ɓari, musamman pink lips nata da lipstick ɗin ya kara musu kyau, bakinshi ya kai kunnenta, a lokacin daya kusanta da ita sosai mumfashinta ya kusan ɗaukewa, baki ta buɗe cikin rawan murya tace "help!!! hel...."

hanu yasa zai rufe mata baki meerah ta rike hanun, kallonta yayi fuskanta ya sauya kala idanunta sunyi jajur alaman tana ciki tsananin ɓacin rai, a tsakiyansu ta tsaya yayinda najwa ta makale a bayanta cike da tsananin tsoro, kokarin kwace hanunshi yake meerah tayi mishi mugun riko, da zuciyarta ta rikeshi bada karfinta ba, wani irin tafasa zuciyanta yake, saida ta gama aika mishi kallo kafin ta saki hanunshi ta nuna mishi hanyan fita, dariya yayi sosai harda rike ciki zaiyi magana yaga ta zubawa waje ido, a tsorace ta zaro ido tareda buɗe bakinta, kafin yayi magana ta fita da gudu ganin wani me baƙin kaya da facemask yana shirin ɗaukan ran haydar wanda yake shirin shiga mota, gudu ta fara sosai ganin ya ɗaga katon karfe ya saita kan haydar, rungumeshi tayi ta baya lokacin daya kai karfen daidai kanshi, haydar jin runguman da akayi mishi da kuma karan saukan abu da yaji, ya juyo a mugun firgice, idanu ya zaro ganin meerah tana silalewa kasa kanta yana fitar da jini, da ihu yace "meerah? meyasa kikayi haka? meerah ki buɗe ido meyasa kika tare min wannan mummunan hatsarin?"

wani irin kallo ya watsawa wanda yake sanye da facemask, aje meerah yake da niyan yi domin kamo shi, sakin karfen yayi a kasa ya juya yabar wajen da wani irin gudu, tashi yayi zai bishi momy tace "no haydar ka fara kula da wacce ta ceci rayuwarka ni zanji da meshi"

da gudu ta fara binshi haydar kuma ya ɗaga meerah yana kiran sunanta a rikice, baisan sanda hawaye suka fara wanke mishi fuska ba, sata yayi a motan ya shiga, kanta da yake jini ya ɗaura akan kafarshi, hawayenshi yana ɗiga akan fuskanta, yace "meerah kada ki mutu dan Allah ki buɗe ido, meerah karo na huɗu kenan kina ceton rayuwata meyasa zakimin haka? da kin bari abin ya sameni nasan yadda zanji da ciwon sabida na saba da wahala da ciwo, amma ke macece kinada rauni ba zaki iya ba"

yana magana yana gudu domin isa asibiti, koda suka isa da gudu ya buɗe marfin motan ya ɗaurata a kafaɗanshi, bai saurari kowa da suke shirin taimaka mishi ba ya kaita vip room ya kwantar da ita akan gadon, da gudu ya fita jamal ne cikin tashin hankali yace "meke faruwa haydar?"

ture jamal yayi ya haura stair, baisan ya akayi ya sauko ba da kayan aiki a hanunshi, jamal kallonshi yake kamar ya haukace haka yakeyin komai, ganin ya shiga VIP room ya bishi, jikinshi yana rawa ya kasa yin komai, sai kiran sunanta da yake "meerah? meerah? dan Allah kada ki mutu"

kuka ya fashe dashi kamar karamin yaro, jamal ya dafashi cikin lallashi yace "ka daina kuka ba zata mutu ba"

hannun jamal ya damke yace "dan Allah ka taimakeni i love her"

gyaɗa kai yayi yace "relax zata samu sauki"

fara duba ciwon jamal yayi sannan ya duba yanayin bugun zuciyarta shi dai yana zaune a gefe yana kallonsu ya kasa yin komai.


dariya Abba ya kwashe dashi harda rike ciki, kallon najwa wacce ta manne da bango yayi kana yace "yayar taki ta gudu, kinga taje taimakon wancan kyakkyawan saurayin"

maida fuskanshi yayi kalan tausayi yace "wayyo Allah pretty ɗita batada sa'a a rayuwarta, kowa kinta yake yau gashi yayarta ma ta gaji da taimakonta kullum taje taimakon masoyinta"

manyan idanunta ta zubawa haydar lokacin daya ɗauki meerah a kafaɗa ya shigar da ita mota, tana iya hango tsananin soyayya akan fuskarshi, kyasta hannu Abba yayi kana yace "kinga ta zaɓeshi akan kanwarta bata damu da halin da kanwarta take ciki ba tasan kina iya rasa rayuwarki a hanuna amma me? taje taimakon wanda takeso"

najwa ji tayi ranta yana tafasa kirjinta yana bugawa da karfi, da kyar ta buɗe baki tace "ba zaɓanshi tayi akaina ba"

wani dariyan ya kuma kwashewa dashi kafin ya ciro wayarshi daga aljihu yace "na nawa kuma? sau nawa tana zaɓanshi akanki? kin manta ranan da kika koma gida naje na sameki? to ai a ranan tana tare dashi"

hoton meerah da haydar ya nuna mata a hospital, sunyi kyau lokacin meerah tana murmushi ne shi kuma yana kallonta, bugun zuciyar najwa ya tsananta, ta zubawa wayan ido, da alama maganganun Abba sun fara tasiri a zuciyarta, ya kuma nuna mata wasu hotunan na lokacin da take ciroshi a mota itada me adaidaita, amma anyi hoton kamar suna cikin yanayin jin daɗi domin kamar editing ne, maida wayan yayi cikin aljihu ganin yadda ta fusata, matsowa yayi dab da ita cikim raɗa yace "ki mallakamin wannan abin ina me tabbatar miki yayarki ma ba sanki take ba"

girgiza kai tayi idanunta suna zubar da hawaye masu zafi tace "ko zaka kasheni ba zan mallaka maka ba Abba..."

buga bangon yayi da karfi har saida ta kankame kanta tsaban tsoron da taji, fuskarshi babu alaman wasa yace "kinada taurin kai najwa, zaki bani ne ko saina kasheki anan?"

ganin zai kai hanunshi wuyanta ta tsala ihu "taimako! taimako jama'a ku taimaka min"

abinda bata sani ba shine Abba ya biya makudan kuɗaɗe wa masu shoprite domin su sallami kowa su barshi da najwa kawai a ciki, tsoronta ya tsananta ganin ba kowa, hanunshi ta bige da gudu ta kama hanyan fita, kafa yasa mata ji kake tim ta faɗi ƙasa, karan azaba ta saki kafin ya karaso taja da ciki har zuwa bakin kofa, da kyar ta tashi ta fara gudu cikin azaba, Abba yana biye da ita.....

_Jiddah Ce....✍🏻_

08144818849

Post a Comment

Idan kuna da tambaya akan abinda Baku game ba ko kuma kuma Neman littafin da babu a nan kawai ku ajiye tambayarku a ta comment ko wani shawara da Zaku bamu.

Previous Post Next Post

Sponsored Link

Sponsored Post