Majalisar Amintattu ta Kwalejin Kiwon Lafiya ta Al-Haroon College Of Health Science and Technology da ke Zaria a jihar Kaduna ta Naɗa Sani Musa Daitu matsayin Darakta Sadarwa na Kwalejin.
Kafin muƙamin Sakataren Yada labaran kwalejin, Daitu Shine Sakataren Tsare-Tsare Na Ƙungiyar Matasan Ƴan Jaridu Ta Jihar Kaduna (Kaduna Young Journalists Association KAYOJA).
Mustapha Aliyu Galadimawa shi ne Shugaban Majalisar Amintattun, ya sanya hannu amincewa da Naɗin.
Cikin wani saƙo da ya wallafa a shafukan Sada Zumunta, Musa Daitu ya ce “ina farin cikin sanar da ku cewa, Ni, Sani Musa Daitu, an naɗa Ni a matsayin Daraktan Sadarwa a Kwalejin Kiwon Lafiya ta Al-Haroon da ke Zaria.”
Ya ce, an ba shi muƙamin ne wanda zai riƙe na tsawon shekaru uku (2024-2027), ya na mai alƙawarin zai yi aiki tuƙuru wajen ganin an cimma manufofin ofishin da ma na kwalejin.
Ya ƙara da cewa, zai bada gudunmawa da ƙwarewarsa wajen samar da nasarori da ci gaba musamman kan salon yaɗa labarai da sadarwa na kwalejin.
Har’ilayau, ya miƙa godiyarsa ga Majalisar amintattu ta kwalejin kan damar da suka ba shi ta aiki wajen samar da cigaba a ɓangaren harkar ilimi a Nijeriya.
Sani Musa Daitu, Tsohon Wakilin Jaridar Amana Newspaper Abuja a Kaduna inda ya riƙe muƙamin Mataimakin Shugaban Sashen Watsa Labarai da Al'amuran yau da kullum na Jaridar.