Kurkukun Ƙaddara Takun Ƙarshe page 65 Complete by Boss Bature


Health College

Kurkukun Ƙaddara Takun Ƙarshe page 65 Complete by Boss Bature

Takun Ƙarshe

A bakin door room dinta suka tsaya, fuskokinsu ɗauke da damuwa.

"Aisha meyasa baki tuntube ni ba a lokacin da abun ya faru? saboda laifin ya shureim ya shafe ni? mun yi zaton kina a Sudan ashe kina a gida, da ace kin sanar dani ke kinsani ni me iya tsaya maki ce, wlh zan tayaki faɗa ne don ganin na kwatar maki hakkin ki, amma bansan komai ba, sai dai na ji labari bayan na dawo gida, abun da yafi ƙona min rai tafiyar da ki ka yi batare da kin neme ni ba, kuma baki yi tunanin kije gidan su Anila ba......" 

daƙyar Benazir ta ƙare maganar tana jan numfashi saboda Zuciyarta dake tafarfasa.

Idanunta na akan door room din Aisha, suna jiyo shesshekar kukan ta daga cikin dakin.

"Lokacin da naji abun da ya faru tsakanin ki da ya shureim da kuma kazafin da akayi maki, Har jinya nayi gadon asibiti saboda baƙin cikin da na ji,  wallahi Allah shine shaida ta, nayi bakin cikin da bazai misaltu ba, Na ji zafin hukuncin da baba Imam ya yanke maki cikin fushi batare da ya yi bincike ba, mu shaida ne akan ki Aisha sannan mu shaida ne akan Yaya Shureim abun da ya faru a tsakanin ku sharrin shaidan"

Aneelerh ta ɗaura da cewa,"Ni kaina sai dai naga sakon ki, har kiran ki na yi ba ki yi picking ba, har messages na tura maki akan ki faɗa min ina kike ko ki zo gidanmu amma babu amsa, Aisha meyasa ki ka zabi ki tafi ki bar mu? Bayan kinsan irin kaunar da muke yi maki, ko bayan tafiyarki bamu manta dake ba, a Kullum muna cikin damuwar rashin ki, tunanin mu ina kike? Kina raye ko kin mutu? Meke faruwa a cikin rayuwar ki....  "

 Aneelerh bata ƙarasa maganarta ba, Dr Shureim ya katse ta, cikin sanyayyar muryarsa mai tattare da rauni ya ce,"Pls Aisha, mu manta da abunda ya wuce, ki yafe mini, Ki yi hakuri Aisha, dan Allah ki fito mu yi magana, gaba ɗaya ɗokin ganinki mu ke yi" 

Babu alamun zata tanka masu.

"Pls Ku dawo ku zauna mana, indai Ummi ce tana a gidan nan, duk da bansan meya faru a tsakaninku ba amma na tausaya maku, in har kuka bamu hadin kai in sha Allah zamu yi kokarin sasanta ku da ita"  

Taj ne ya yi maganar daga inda yake a zaune, Jikin su asanyaye suka baro kofar dakin Ummi ba don sun so ba, suka koma falo kowannan su ya zauna kan Sofa, kwata kwata babu walwala akan fuskokinsu, Idanunsu sun kaɗa jawur saboda kukan da suka sha, babu mai magana a cikinsu kowa da abunda yake saƙawa a cikin Zuciyar shi.

Taj dake fuskantarsu, A tsanake ya ke nazarin yanayin su sam ya kasa dauke ido daga kallon su.

"Pls ina son insan meye alaƙarku da Aisha ne? A nan take zaune?"

Murmushi Taj ya ɗan yi tare da kallon Dr Shureim da ya yi maganar.

A tsanake Taj ya zayyana masu alakar dake a tsakanin su da Aisha, tun daga kan aikin da U.s armies suka saka ta, ya ƙara da cewa,"Tamkar uwa take a gurinsu, tana kula da su sosai..." 


Ajiyar zuciya suka sauke gaba daya hankalin su ya kwanta da jin a nan take da zama don basu son su kara rabuwa da ita.


A bangaren Ummi bayan data shige daki ta yi locking door din, tana kuka ta fada kan gadon ta, Batool dake a cikin toilet tana jiyo shesshekar kukanta ta fito hankalinta atashe ta haye kan gadon tana tattaba bayanta, "Aunty Ummina! Meke damunki? Meyasa ki ke kuka? Waya 6ata maki rai!"


 Kwata kwata Ummi bata saurare ta ba, hakan yasa ta fashe da kuka itama tana fadin, "Dan Allah aunty Ummi ki daina kuka, bana so! Ki faɗa min meke damun ki?"


dakyar ta iya furta,"Bana jin dadin Zuciyata, zafi take yi mini! Babe na rasa Fatima na, I've lost my Batool ta mutu, na yi babban rashi! Baki ji radadin da nake ji ba..."


sambatu ta dinga yi mata, Batool data gama ruɗewa  ta kasa gane inda maganganun ta suka dosa.


"Aunty Ummi, ban mutu ba, Ina a raye, ba ga ni a kusa dake ba?" ta faɗi hakanne saboda ta yi zaton ita Batool din take nufi.


Tana kokarin tallabo fuskar Ummi da tafukanta don ta miƙar da ita zaune saboda karfin hali irin nata..


Ba ta yi aune ba, Ummi ta janyota kan chest ɗinta ta rungumeta sosai, duk don ta samu relief na radadin da take ji, damuwace ta mamaye zuciyar Batool lokacin da fatar jikinta ta haɗu data Aunty Umminsu, saboda zafin da jikinta ya ɗauka har a jikinta tana jin shi.


Ruɗewa ta yi cike da tashin hankali take fadin,"Baki da lafiya Aunty Ummi, you're burning up, in wani abu ke damunki ki fada min zan taimaka maki har ki samu sauki.. "


 ta faɗa tana ƙoƙarin ƙwace kanta daga rukon da Ummi ta yi mata don ta samu damar zuwa ta faɗa ma daddy Taj da Unaisah halin da take aciki sai dai sam Ummi  taƙi bari ta motsa.


Tunawa tayi da addu'a, cikin sauri ta fara karanta yan addu'o'in da ta iya a cikin zuciyarta ta tottafa mata saman wuyanta.



Kafin Ta ɗaura hannayenta biyu akan bayanta cikin sigar lallashi ta ke ɗan bubbuga bayanta kamar ta samu karamar yarinya.



Ji ta yi inama ace Batool ce ɗiyarta, Murnar da za ta yi ba zata misaltu ba, tana son Batool sai dai ita bata fito daga mahaifarta ba, tasan duk mun daran daɗewa, wata rana Batool zata ga iyayenta ne.


Cusa yatsun hannayen ta ta yi acikin sumar kan Batool, yayin da zuciyarta ke tariyo mata fuskar babynta, bazata taba mantawa da suffarta ba, tana ji aranta tabbas da ace tana a raye kuma ta girma, ba abun da zai hana su yi kama da Batool saboda kamanninta da Dr Shureim, ta dade tana ganin kamanceceniyar su sai yau ta ƙara tabbatar da hasashen ta. 


"Aunty Ummi da sauki?"

Cikin disasshiyar murya ta furta,"Ki cigaba da yi min addu'a, Allah yaye min abunda ke damuna" Da sauri ta amsa mata da toh .



Time da aka fara kiran sallar  la'asar, Taj yace ma su Anila su shiga daki su yi sallah, bayan ya nuna masu ɗaya daga cikin bedroom dinsu Sajeed suka tashi suka shiga, Dr Shureim ya ce ya tashi su tafi masallaci, sam ya ma manta da ƙafarsa dake ciwo har ya yunkura zai mike kafar ta fara yi masa zogi ba arziƙi ya koma yana nishi, anan Dr shureim ya fahimci baida lafiyar ƙafa har ya tambayi meke damunshi ne? ya ce mashi ya samu rauni ne a cinyar sa ta dama amma da sauƙi, cikin nuna tausayawa Dr shureim ya yi masa sannu da jiki, har ya ce in bazai iya zuwa masallacin ba ya yi zaman shi tun da lalurace, Taj yace ma shi kar ya damu, zai iya zuwa ai yana da wheelchair, ya faɗa tare da kai hannu Ya janyo kan kujerar sa da ya 6oye tsakankanin Sofas, ya janyota  ta dawo ta gaban shi, ya yi ta ƙoƙarin miƙewa yana kasawa har saida Dr. Shureim Ya taimaka mashi ya zauna a akanta, tukunna suka tafi.



__________________________________✍️


Tana a kwance tsakiyar gadonsu, ta ƙurawa ceilling idanunta da suka kaɗa jawur, hawayen da suka cika idanunta a hankali suke gangarowa kan kuncinta, bakomai take tariyowa ba face fuskar Benazir, wai dama itace mahaifiyarta da ta yi watsi da ita? Tana yi mata kallon mutuniyar kirki ashe ba haka bane ta yaudari kanta, abin da yafi ƙona mata rai, jinyar ta da ta yi, ta bata abinci a baki, ta yi hugging dinta har ma ta sumbace ta saboda kaunar da ta ke yi mata bisa rashin sanin wacece ita, but now that she knew the truth, she hated her more than anything in the world, abun da yafi tsaya mata a rai meyasa ta gudu tabarta bayan ta jefar da ita cikin kwamin wanka? In bata sonta meyasa bata kashe ta ba tun lokacin da ta  haife ta, Laifin me ta yi mata da yaja har ta tsane ta?


 Tabbas tana son ta tunkareta gaba da gaba don taji amsar tambayoyin ta.. ranta yakai maƙura a gurin 6aci, sai faman yin juyi ta ke yi akan gadon kamar mai fama da ciwon mara.


_______________________________🌹✍️



Around ƙarfe biyar na marece, motar Chief ta kunno kai cikin main gate, bayan driver dinsa ya tsayar da motar a parking space cikin hanzari ɗaya daga cikin security Officers din da ke sintiri yai hanzarin zuwa gaban car door ya bude masa motar, fitowa ya yi daga ciki jikinshi sanye da Suit.


With respect Security Officers din suka sara mashi, har zai juya muryar driver dinsa ya katse shi


"Sir, should I bring in the suitcases?" He nodded, then turned away, ya nufi falo.


Cikin sauri SA ɗin ya buɗe tanƙameman boot din motar Chief, ya soma fiddo wasu hadaddun akwatina, guda biyu bayan ya gama ya rufe boot din, ya ruƙo handles dinsu ya bi bayan Chief da su.


Chief bai taras da kowa a falon ba, Kaitsaye Ya nufi Upstairs saboda a gajiye ya dawo he needs some rest, duk da yafi bukatar ya gana da su.


Bayan shigar shi dakin, SA din Ya shigo mashi da akwatinnan ya ajiye su kafin ya fuce.


Shaf shaf ya rage kayan jikin shi Ya shiga bathroom don ya yi wanka. 


Bayan wani Lokaci ya fito daga part dinsa ya dauki wankan blue sky voile, sai kamshi ke tashi a jikin shi, walking magestically ya nufo down.


tun kafin ya ƙaraso takun tafiyarsa yaja hankulansu ga duban shi, a lokacin sun dawo falo suna jiran shi.


A hanzarce suka mimmiƙe tsaye, kaitsaye ya nufi Dr Shureim, side hug ya yi masa tare da ruko hannunsa sukayi musabaha, Dr shurem ya ɗan yi mamakin saukin kan Chief yadda ya tarbe shi kamar sun saba da juna.


With respect Aneelerh da Benazir suka gaishe da shi tare da yi mashi sannu da dawowa, fuskarsa da fara'a ya amsa masu.


Gaba ɗaya Ya lura da yanayin fuskokin su kamar ba walwala akai.


Sarah mashi Taj ya yi daga zaunen da ya ke bai motsa ba ya yi mashi sannu da dawowa, mayar masa da martanin sarawar ya yi kafin ya amsa gaisuwar da ya yi masa tare da miƙa masa hannu suka gaisa da juna.


Daga bisani ya zauna gefen Taj, ya kasance suna fuskantar su Dr shureim..


"A yi mini afwa, na barku kunata jirana." Ɗan murmushi suka yi gaba dayansu.


Dr shureim ya ce, "bakomai wlh, Allah yasa dai bamu katse maka aiki ba" 


Fuskarshi a sake ya ɗan jinjina kan shi,


Tunkafin ya tambayi wani abu Taj ya yi hanzarin daukar wayar Ana dake ajiye gefensa ya kunna masa videon tare da miƙa masa ya sa hannu ya kar6a tare da daura idanunsa akan Screen din wayar ya nutsu yana kallon videon, bayan ya gama kallo shiru ya yi yana ɗan jinjina kan shi.


Lamarin ya ɗaure mashi kai tamau, kuma tunanin su ya zo ɗaya dana Taj.


Gyaran murya ya yi masu a hankali suka mayar da dubansu gare shi.

Tambayoyi ya fara yi ma Anila dangane da Ana da kuma Uncle din ta, bata boye masa komai ba duk abunda ya tambaya sai ta bashi amsa.


Bayan Ya kammala yi mata tambayoyin, Taj ya ce, "Benazir, ki yi masa bayanin abun da ke damun ki" cikin sanyin murya ta amsa mashi da toh,


A tsanake ta kwashe komai da ya faru da ita a gidan Uncle musa ta sanar da Chief, ta ƙara da cewa, "Ban sanar ma kowa ba, Yaya Shureim ne kaɗai ya sani, bayan haka yanzu an ɗaga ƙafa da kawo min harin."


Yanayin fuskar Chief ya nuna tsantsar ruɗani da al'ajabi, kallon Dr Shureim ya yi wanda gaba daya hankalin sa baya akan su, duba da yadda ya sadda kan shi ƙasa.


"Za ki iya suffanta mini mutumin da ya kawo maki hari a cikin toilet?"  


Ta amsa da eh, kafin ta fara siffanta mashi mutumin.


 Kallon kallo suka jefawa juna tsakanin shi da Taj, lamarin ya daure masu kai, saboda gaba ɗaya yadda Benazir ta suffanta mutumin, baida bambanci da giant ɗin kurkukun Ƙaddara, amma abun tambayar anan meyasa ake son kashe ta? Zurfin tunani Chief ya shiga har na tsawon yan mintuna, kafin ya ɗago ya dubi Benazir suka haɗa ido cikin na juna.


"A lokacin baya, kafin ƙaddara ta rabaki da gidan mijin ki, babu wanda ki ka ta6a yi ma laifi kuka samu sa6ani a tsakanin ku har ta kai ya ci wani alwashi a kan ki?"


 Girgiza kai ta yi,"Gaskiya ni ba wanda wani abu ya taba haɗa ni da shi..." 


Bata ƙare maganar ba, ganin irin kallon da Taj ya yi mata, nan take ta fahimci me yake nufi wato yasan halinta ciki da bai.


Gyaran murya ta dan yi, "A lokacin baya nasan bana jin magana, idan nace ban taba samun sabani da wani ba to na yi ƙarya, amma bana tunanin na yi laifin da har za'ayi yunƙurin kashe ni"


"Bakya tunanin wanda ya yi maki kurciya shine yake nema ya kashe ki saboda ya ga kin dawo a raye, may be akwai wani abu da ya haɗa ku ko sanin sirrin wani wanda baya son asirin shi ya tonu ta silar bayyanar ki shiyasa yake nema ya halaka ki..." 


Maganar Chief tasa ta jin faduwar gaba, zurfin tunani ta shiga yayin da ƙwaƙwalwarta ke kokarin tariyo mata abubuwan da suka faru a lokacin baya kafin ta gudu daga gidanta, sai dai ta kasa tuna komai kamar an wanke mata brain dinta.


"Ki yi kokari ki tuna Benazir, ba ƙaramin taimako zaiyi mana ba"


 Taj ne ya yi mata maganar cikin kwantar da murya, har kallon shi saida tayi kamar wani abu bai shiga tsakaninsu ba, Chief yana lura da duk wani motsin su haɗi da karantar yanayinsu ta fuskarsu.


 Cikin kunnanta ta tsinkayi muryar Aneelerh dake yi mata magana cikin raɗa, "Please ki tuna Benazir, ni nasan baza a rasa wadanda kuka taba samun sabani da su ba, ko ya ya ne ki yi tunani pls"


Wani abu da Chief ya lura da shi shine satar kallon Dr shureim da take yi, hakan yasa shi zargin akwai abun da ta sani, kuma tana so ta fada sai dai bata son Dr Shureim ya ji shiyasa take satar kallon shi a fakaice.


Fahimtar hakan yasa shi cewa, "Kada ki damu, zan baki lokaci, bayan kin koma gida kiyi kokari ki tuna in ya so sai ki kira Taj a waya ki sanar da shi"


 Nannauyar ajiyar zuciya ta sauke fuskarta da ɗin murmushi ta ce, "In sha Allah idan na tuna zan kira in sanar da ku" 


Shiru suka dan yi na wani lokaci.


"Meke damun shi ne?" Chief ne ya fada idanunsa akan fuskar Dr Shureim ƴan hawayen da suka cika idanun shi sai kokarin sauka kan kuncinsa suke yi.


Taj ya ce, "Yawwa Sir, namanta ban fada maka ba...." A hankali Chief ya mayar da hankalinsa akan Taj, komai da ya faru bayan fitowar Ummi Ya sanar da shi, jinjina kai ya yi tare da kallon su Anila, "Zan iya sanin menene alaƙar ku da ita?"?


Har suna haɗa baki gurin furta eh saboda suna son ya taimaka masu tunda agidanshi take da zama.


"Yaya Shureim," Benazir ce ta kira sunan shi, cike da damuwa ya ɗago ya kalle ta, a kunne ta yi masa raɗa, "Suna son sanin menene alakar mu da Aisha, zan iya faɗa masu komai da ya faru? tun da ka ga agurinsu take da zama may be idan su ka ji su taimaka mana"


Ya ɗan ji nauyin maganar, amma a halin yanzu baida za6i,


Cikin sanyin murya ya ce, "Idan kina ganin zasu sama mana mafita, ki fada masu komai," 


Ajiyar zuciya ta sauke, kafin ta maida dubanta akan Taj da Chief.


Nan ta fara basu labarin rayuwarsu, da alakar su da Aisha, da kaddarar data raba su da juna, bata 6oye masu komai ba, da yake ta iya bada labari ko mistake bata yi.


Lokacin data ƙarasa basu labarin idanunta cike tab da ƙwalla, yayin da su kuma tsantsar mamaki da al'jabine ya kamasu, A sanin su da Ummi tantiriyar Karuwace da ta yi ƙaurin suna a America, ashe kaddara ce ta canza mata rayuwa, sun ji tausayinta sosai, har ta kai ga sun yi shiru jimm suna ɗan jinjina heads din su, shi dama Taj ya daɗe yana yi mata kallon sani, sai yanzu da Benazir ta bada labarinsu, Ya tabbatar ma kansa Bintu Imam ce.


 

"Dan Allah ku taimaka mana, kada ku bari Aisha ta koma America, ku ruke mana ita har sai mun sansanta tsakaninta da mahaifinta da kuma mu, muna so ta koma kamar yadda take a da, sauyin da muka gani atare da ita ya tada mana hankali, wlh kallo ɗaya da nayi mata na fahimci ta canza rayuwarta" 


Chief ne ya ce,"Na yi maku alkawari In sha Allah, Aisha ba zata koma America ba, zan cigaba da ruke ta anan har sai na cika maku burukan ku, saboda nima na damu da ita na tausayama rayuwarta sosai, na ji zafin abun da ya yi silar rabata da mahaifinta da kuma halin da ta jefa rayuwarta, wanda nayi imanin tsinuwar da mahaifinta ya yi mata ce ke bibiyarta, bayan haka Dr Shureim..." 


Ya amsa mashi da na'am idanunsu acikin na juna.


"Kaima na tausaya maka sosai, labarinku ya ta6a zuciyata, kun bani tausayi, please ka cigaba da hakurin da ka saba yi, in sha Allah ni Chief na yi maka alƙawarin Ummi won't leave this house until everything is settled"


Maganar Chief ta kwantar masa da hankalinsa, wani dadine ya ji ya lullu6e zuciyar shi, Anila Da Benazir basu san sa'adda suka saki murmushin jin dadi ba, har suna hada baki gurin yi mashi godiya.


"Ina fata mun gama magana, ko akwai sauran wani abu?" Cikin kulawa Chief Ya faɗa yana duban su,


"Unaisah, ta ƙi kula ni...." gaba daya ta fada mashi abunda ya faru tsakaninta da Unaisah, har cikin ranshi bai ji dadi ba, amma ya fahimci Unaisah, baiga laifinta ba, dole ne dama ta ƙi accepting din ta saboda ta ƙullace ta aranta.


"Kada Ki damu, Ni zan yi mata bayanin da zata fahimta, In sha Allah"


 Ita dai Anila tunaninta ya fara komawa gida fargabanta kada Junaid ya saki baki ya furta dodon da ya kashe Anah a gaban Uncle.


"Akwai gargadin da nake so na yi maku gaba dayanku, daga rana irin ta yau inaso ku dauki kanku a matsayin jami'an sirri, kada ku kuskura ku faɗa ma wani damuwarku, sannan kada ku bari yanayin ku ya nuna! Duk wani abu da muka tattauna anan to mu binne shi anan!" Ya faɗa yana nuna floor da index finger ɗinsa.


"Sirrinku a cikin zuciyarku, In zai yiwu ma, ku daina tunanin abun cos kuskure kaɗan zai iya jefa rayuwar ku cikin hadari. Tun da har kun fada mana komai, from now on Case din yabar hannun ku, yanzu yana a hannunmu, kuma in sha Allah zamu cigaba da yin bincike akai"


Gaba ɗaya sun yi amanna da maganar shi, kuma sun daukar mashi alƙawari zasu kiyaye.


"Yakamata mu tafi, na ga an kusa fara kiran Magrib" Aneelerh ce ta faɗa tana duba wrist watch din hannunta.


Taj ya ce, "Zamu ruƙe wayar Ana a hannun mu, har zuwa time da zamu kammala bincike. Mungode sosai, Allah ya maida ku gida Lafiya"


Atare suka hada baki gurin furta Ameen muna godiya muma da aka kar6e mu hannu bibbiyu tare da fatan nasara.


Dakyar Dr shureim ya mike fuskarsa sam ba walwala, ya so ace zai iya ganin Aisha kafin su tafi.


Daƙyar ya iya furta,"Please zan iya samun phone number din Aisha?"


Taj ya ce, "Mi zai hana." ya ɗauko wayarsa ya lalubo layin Ummi ya mika masa, yatsun hannunsa har kerma suke saboda zumudin ya kar6a, shaf shaf yayi copying dinta bayan ya gama ya mika ma Taj tare da yi mashi godiya.


 Benazir dake kallon shi ta kasa gane me ya hana shi mikewa? A ganinta ko rakiya ne yakamata ya yi masu.


"Muje nayi maku rakiya" Chief ne ya fada tare da mikewa, ya ruko hannun Dr shureim a cikin nashi suka yi gaba, Aneelerh da Benazir suna a biye da bayan su.


Bin su da kallo ya yi har saida suka 6ace ma ganinsa, lumshe idanun shi yayi a hankali yake tariyo komai da ya faru tun farkon zuwan su Benazir.


Unexpectedly ya ji an sumbaci forehead dinsa, a firgice ya buɗe idanun shi, har saida gaban shi ya fadi da ya yi tozali da Benazir ta sunkuyo da kanta saitin fuskarshi, nan da nan ya haɗe rai,


"Baki tafi ba?"


"Taya zan tafi kana fushi dani" Ɗaure mata fuska ya yi.


"Pls abunda ya faru ɗazu ka yafe mini, raina ne ya 6aci," Ta fada tana kashe mashi murya.


"Na ji, ya wuce."


"Yaushe zaka maida ni ne? Na gaji da jira." Wani kallo ya yi mata mai kama da harara ya ce, "Toh rasa kunya 6eran tanka, ke baki ji kunyar furta in maida ki ba? Hauka nake da zan dauki macen da take ruƙe kwalar rigana kamar zata doke ni!"


 Ya fada babu wasa akan fuskarsa.


Marairaice fuska ta yi kamar zata fashe da kuka ta ce, "Pls ay na baka hakuri, wlh na gane kuskure na, don Allah ka daina wahalar da ni mana, nafa san kana sona har yanzu." ta faɗa tana yi mashi farfari da idanunta.


Hakan da tayi ba ƙaramin sace zuciyar shi ta yi ba.


"Ka yi shiru bakace komai ba," Ta fada da yar shagwa6arta.


Ɗagowa ya yi suka hada ido cikin na juna wani kallon so da kauna suke jefawa junan su, bakomai take tuna mashi ba face Unaisah.


"Wallahi wannan karon idan ka mayar dani, zan yi maka biyayya sau da ƙafa, zan tarairayeka kamar jinjiri, yanzu fa na canza ba Benazir din da ka sani ada bace, ka ga yanzu na iya girki, na iya gyara gado, na iya wanki, wlh har wanka zan dinga yi maka...." 


Duk yadda ya kai ga hana kanshi sakar mata fuska baisan sa'adda ya tuntsire da dariya ba, saboda kalamanta sun bashi dariya, kuma dagaske take fada masa babu wasa akan fuskarta.


"Oh, kina nufin yanzu kin gane an halicci hannayenki don ki girka ma ƙato abinci?" Ya fada tare da ɗage mata gira, dariya ta saki har dimples dinta ya lotsa.


"Bama iya girki ba, komai zanyi masa." Tabe bakinsa ya dan yi.


"Yakamata ki tafi suna jiranki." Ɗan bubbuga kafafunta ta yi kan floor, "Taya zan tafi baka bani amsa na ba?"


"Zamu yi magana a waya" Ba don ta so ba tace, "ka yi mini alƙawari?" Jinjina mata kai ya yi. 


"Okay, ka rama min kiss da na yi maka." Zare idon shi ya ɗan yi bata jira amsar shi ba ta manna mashi peck ta juya tana dariya ta nufi Kofa, bin bayanta ya yi da kallo har ta bace ma ganin shi.



________________________________________✍️



Around ƙarfe tara na dare, Benazir ta fito daga bedroom dinsu, hannunta a ruƙe da wayarta, har ta sanya kayan bacci a jikin ta, sai dai baccin ya ƙauracewa idanunta, a hankali take tafiya yayin da zuciyarta ke ta azalzalarta akan ta kira Taj ta faɗa masa abunda ta kasa sanar da su ɗazu, sai dai tana matuƙar jin shakkar ta fitar da sirrin gani take kamar zai koma masa ne, amma in ta tuna halin da Aisha ta shiga, da irin uƙubar da Dr Shureim Ya sha akan yarinyar sai kawai ta ji ƙwara ta fada kawai ko da hakan zai yi silar rasa rayuwarta ne, ta ma san ko bata fada ba, hakan bazai hana a cigaba da yunƙurin kashe ta ba.


Tana Ƙoƙarin juyawa ta koma ɗaki ta ji motsin shigowar mutun Falon, da sauri ta kai idanunta ga duban shi, Alhaji Musa ne ya shigo cikin takun nan nasa na izza yake tafiya fuskarsa ba annuri, ya zuba hannayensa cikin aljihun wandon shaddar Jikin shi, hakanan ta tsinci kanta da jin faduwar gaba, cikin sauri ta juya da sauri ta faɗa bedroom din ta, kamar munafuka ta dinga leƙen shi, waro ido ta yi ganin ya dan dakata da yin tafiyar, alamun ya ji ajikin shi ana kallon shi, jikinta na kerma ta datse kofar ɗakin.


A hankali yake bin ko'ina da kallo, ganin ba abunda ya yi zata bane yasa shi gyaɗa kai ya cigaba da tafiya Ya nufi part dinsa.


Nannauyar ajiyar zuciya ta sauke tare da hadiyar yawu, tunani ta soma yi a ina yakamata tayi wayar cos bata so wani ya ji koda kalma ɗaya da zata furta ne.


 Ɗaura idanunta ta yi akan Zeenatu da ke a kwance kan bedmatress tayi nisa acikin baccin ta, Cikin tafiyar sanɗa ta nufi gadon ta janyo duvet ta lullu6e mata jikinta gaba daya.


har ta nufi toilet zata shiga sai kuma ta fasa, tunawa da babu kyau yin magana acikin toilet.


Gaba daya kanta ya ɗaure, tsoro take ji, ga shi abun ya dameta so take kawai ta fallasa sirrin da ta daɗe da shi a cikin zuciyarta, ba zata iya jira gobe ta yi ba.


Akan Mirror Chair ta zauna, ta fara danna wayar ta kira layin Taj ta kurawa screen din wayar idanunta tana jiran ya yi picking.



Lokacin da kiran ya shigo layin Taj, yana a kwance kan gadonsa har ya fara bacci kiran ya katse shi.


Kasantuwar ya aje wayar a kusa da kunnansa, ransa a ɗan 6aci ya janyo wayar ko da ganin kiran Benazir cikin sauri ya daidaita nutsuwar shi.


Bayan yayi picking ya kara wayar a kunnansa.


Ko sallama bata yi mashi ba ta ce, "shine ko ka kira ka tambayi mun isa lafiya ko?"


Cikin disasshiyar muryarshi ta wanda bacci bai ishe shi ba yace, "I'm sorry Ummu Unaisah, wlh kuna araina, tun dazu nake ta zucci zuccin in kira ku.." 


Da shagwa6a ta ce, "Hankalinka kwance ma bacci kake yi, Ni gani nan damuwar rashin ka a kusa dani ta hanani runtsawa sai faman tunanin ka nake yi" Har cikin ranshi ya ji dadin kalamanta, murmushi ya yi, "Waya fada maki ni ban damu dake ba? Nima kin tafi kin barni da tunanin ki, da zarar na rufe idanuna ke nake gani,"


 Sautin dariyarta ne ya cika kunnan shi.


( Allah sarki tsohuwar Zuma😂 har wani ƙara kankame pillow yake yi a kirjin shi, da alama Benazir tayi winning heart din Taj.)



"Ina babynmu?"


"Tana a bedroom din su, may be ta yi bacci"



"Okay," shiru su ka dan yi jimm har saida ya furta, "Akwai wani abu da kike son fada mini ne?"



Cikin sauri ta ce, "Eh dama dazu akwai tambayar da ku ka yi mini ban samu na amsa maku ba, saboda Yaya Shureim yana a wurin bana so yaji..."


 Cike da zumudi Taj ya ce,"Okay, Ina sauraron ki Ummu Unaisah" 


Calmly Ta soma ba shi labari.   


"Kafin dawowar mu Jos, A lokacin ina a gidan Uncle Musa, ban kai ga sanin komai da ya faru tsakanin Yaya Shureim da Aisha ba, na ta6a kama Uncle yana yin wata waya ta sirri, wuraren karfe ɗaya na dare ban runtsa ba, dama dabi'atace idan ina yin Chatting bana yin bacci da wuri, to adaren ranar na fito daga ɗakina dake a cikin gidan sa, hannuna ruke da wayata ina tafiya ina yin chat da niyyar daukko ruwa, gaba daya na shagala har na sauko down batare dana ankara ba, Na shiga zagaye falon gidan kafin na nufi walkway din da zai sadani da backyard din gidan na tsaya, kwatsam kunnuwana suka soma jiyo mun muryar mutum yanayin waya ƙasa kasa kamar baya son wani ya ji shi, a firgice na kalli saitin inda nake jin maganar sa a hankali cikin sanda na karsa bakin kopar da zata 6ula da kai bayan gidan, a zaune na hango shi kan ɗaya daga cikin kujerun shaƙatawar dake a wurin, a lokacin na dan ji tsoro saboda ban tsammaci zanga mutun a irin wannan lokacin ba, amma sai na dake saboda ina son in san wanene kuma ina son jin wayar mecece ya ke yi a tsakar dare! Ni abunda yafi daure mun kai duk rooms din dake acikin gidan da falo ya rasa inda zaiyi waya sai a backyard, hakan yasa na dasa masa alamar tambaya, aikuwa cikin sanɗa na matsa gaban tukwanan furannin da ke a bayanshi na zukunna tare da kasa kunnena ina sauraron shi.


"Kada ku bari ta yi 30 Mins a cikin ramin, zamu iya rasata ne, ku kasance a ankare, da zarar kun ga jami'an sun tafi da shi, kuyi hanzarin haƙa ramin ku ɗauko Jinjirar, Sannan bayan kun cire ta daga ciki, Ku kashe daya daga cikin karnukan ku, Ku je ku zuba ƙasusuwan shi a cikin ramin"


 Lokacin da naji wannan maganar wani irin faduwar gaba na ji duk da ban fahimci inda zancen nashi ya dosa ba, gaba daya nabi na rude amma a haka na toshe bakina na cigaba da sauraron shi saboda ina son inji karashen zancen na shi.


"Bana so a samu matsala, dole sai kun yi taka tsantsan! ka da ku yi gangancin da wani zai gan ku, idan ba haka ba kun sauran sauran," 


Ya faɗa tare da yin rejecting call din ganin ya miƙe yasa na yi saurin zuƙunnawa ƙasa da rarrafe na dinga tafiya cikin sanɗa sai da na ga nayi nisa da backyard din, tukunna na mike da sauri na koma dakina na ja kofa na datse.


Aranar na kwana da tunanin wacece naji Uncle Musa yana bada umarnin a haƙa ramin da take a ciki a curo ta? Kuma yace a kashe kare a zuba ƙasusuwan shi a cikin ramin? Menene manufarsa ta yin hakan?"


 A lokacin gaba daya na ruɗe, na kasa gane komai, dakyar bacci 6arawo ya yi awon gaba da ni, tun daga ranar ban kara samun kwanciyar hankali ba, saboda tunanin wayar dana kama Uncle musa yanayi atsakar dare, zuciyata ta dinga azalzalata akan in tunkare shi in tambaye shi game da wayar da na ji yanayi, sai dai tsoro da fargaba sun hanani yin hakan, bayan haka bansawa raina wani mugun abun ya ke yi ba saboda na yarda da Uncle Musa, daga baya ma sai na watsar da zancen na cigaba da yin harkokin gabana.


Taj da ya kasa kunne yana sauraronta, tuni ya mike zaune saboda mamakin daya daure zuciyar shi.


Benazir ta ɗaura da cewa, "Lokacin da na kudiri Aniyar saina gano koma wanene ya shiga tsakanin Ya shurem da Aisha, da kuma munafukin da ya ƙulla mata makirci a ƙasar Germany, Lokacin da na saci hanya na shiga dakin Aunty Zainab na tambaye ta meya faru a tsakanin Dr Shureim da iyayen mu saboda ina zargin bakomai suka faɗa mana ba, bayan zainab ta fayyace mini komai, Hankalina atashe na koma ɗaki na, inata wasi wasi akan wayar nan dana ta6a kama Uncle Musa yana yi a bayan gidan sa, sai da na zurfafa tunanina nayi dogon nazari kafin na gano wayar nan fa da Uncle musa yake yi akan babyn Ya Shureim ce.


Amma abun da ya ɗaure min kai shine Meyasa Uncle Musa zai yi haka? A raina na ayyana ko dai yana son ya yi mashi hankaline saboda rashin hankalin da ya yi na binne ƴarsa, amma kuma dana kara yin tunani sai na gano wannan fa yafi karfin abunda nake hasashe, ganin an dauki kwanaki Uncle Musa baida niyar fallasa shi ya dauki yarinyar, bayan da kunnanshi ya ji irin bakar wahalar da Ya Shureim yasha bayan ya binneta kuma ya yi danasani, to amma meyasa da farko Uncle Musa ya nuna baisan komai ba?


 Bayan mun yi waya da Ya Shureim har ya fada mini yasha jaraba kiran layin wayar Uncle don ya nemi taimakon sa, amma baya samun shi, tun daga nan ne na fara zargin da akwai wata mummunar manufa atare da shi.


Ban tunkare shi da maganar ba, saboda a lokacin ka zo mini da maganar zaka turo magabatan ka ayi maganar auren mu, shiyasa na watsar da maganar na bar komai araina. Bayan mun yi aure da kai, A lokacin Daddyna har ya samu nasarar lashe zabe ya zama gwamnan jihar wanda tun da ya hau mulkin bai ƙara lafiya ba, saboda ciwon ƙafa da ya matsa mashi, ba irin maganin da ba'ayi mashi ba amma ciwon yaki ci yaƙi cinye wa. Wani iko na Allah da zarar an fita da shi kasar waje don a nema masa lafiya sai ciwon nashi ya warke, amma da zarar an dawo da shi Nigeria ciwon na shi yake komawa sabo, a karshe da yan jam"iyarsu suka fahimci ciwon nashi bame ƙarewa bane, sai suka shawarce shi da ya aje mulkin yaje ya nemi lafiyarsa, Shekara daya yayi kafin ya sauka, zaman Jahar ya gagare shi silar hakan iyayenmu suka koma Dubai da zama, Ni kuma saboda auren da na yi ne yasa suka barni a Jos.


A lokacin Uncle Musa ya zama Shahararran dan siyasa, ganin sa yayi mini wuya saboda bai cika zuwa Jos ba tun da iyayen mu suka koma Dubai, ya ɗaga ƙafa da zuwa Jos daga Abuja sai ƙasashen waje, Kuma duk in na kira phone numbers dinsa bana samu.


A ƙarshe na yanke shawarar tura mashi text message, na rubuta mashi komai dana ji ya fadi a cikin wayarsa, sannan na yi mashi barazanar ko dai ya dawo da babyn Shureim, Ko kuma in tona masa asiri a gurin Daddy da Mommy har da ma Ya Shureim din.


Da tura mashi saƙon ko minti biyar ba'ayi ba, sai ga kiran Uncle Musa ya shigo wayata, na yi mamaki sosai saboda tunda nake kira ba'a picking.


Bayan na ɗaga ko sallamata bai amsa ba ya ce, "Benazir! Ni za ki yi ma kazafi? Yaushe kika ji ina yin wannan maganar? Bayan haka ni miye haɗina da yarinyar Shureim da har zansa a binno ta daga rami? Me zanyi da gawa..."? 


Bai ƙare maganar ba na ce, "Haba Uncle, wlh baka isa ka raina mini hankali ba! Da kunnena na ji ba gaya min a ka yi ba, Wlh babyn Shureim tana araye kuma ta na a gurin ka, Kai kasan inda ka kaita, kuma na rantse idan har baka dawo masa da ƴar sa ba, saina tona maka asiri.." 


Ina ƙarashe maganar na kashe wayar, cike da saran zai neme ni.


Aikuwa ba zato ba tsammani a yammacin  ranar da na yi waya da shi sai ga kiran shi ya shigo waya ta, a lokacin baka a gida, bayan na ɗaga kiran na ji yace in fito wajen gidana ya turo da escort dinsa yana jirana a cikin Mota.


Na ɗan ji fargaba amma da ya ke lokacin ina jin tashen rashin ji, bana jin fargaba kuma bana jin tsoron tunkarar koma uban wanene.


Batare da saninka ba, na bi Escort dinsa acikin mota ya kawo ni guest house din Uncle Musa dake anan Joss.


Bayan na fito daga motar, escort din ya rakani har cikin falon gidan, Ina shiga na taras da shi a zaune saman Sofa ya ɗaura ƙafa daya kan ɗaya, fuskarsa kwata kwata babu annuri kamar bai taba dariya ba, Nima na haɗe rai fiye da yadda ya haɗe ta shi fuskar, tunkafin ya bani iznin in zauna na samu guri kan sofa din dake fuskantar shi, na zauna tare da ɗaura ƙafata ɗaya kan ɗaya hakan ba karamin daure mashi kai ya yi ba.


 Tambayar farko da ya yi min shine in fada masa gurin wa na ji maganar dana fada masa?"


Na ce in har yana so in fada masa to ya fara kawo min Babyn Shureim.


Lallashina ya fara yi duk dan in faɗa masa, na sanya kaifi nace wallahi ya daina wahalar da kanshi saboda bazan faɗa ba, dole sai ya fara kawo mini yarinyar.


Shu'umin murmushi ya saki tare da cewa bai damu ba in je in fada ma duk wanda zan fadamawa, saboda bani da hujjar da zan iya tuhumar shi, balle har in tona masa asiri, kuma in bi a hankali in ban iya kama barawo ba sai barawon ya kama ni.." na yi dariya hada shewata na ce, "Ka bani mamaki Uncle, ina yi maka kallon mutumin kirki ashe kai din mutumin banza ne! Ka yi zaton bansan komai ba?"


 Na faɗa ina zare mashi idanuna, a lokacin yanayin fuskarsa ya sauya zuwa tsantsar al'ajabi da rudani.


"Benazir Ni kike kira mutumin banza? Ido cikin ido batare da jin shakkata ba? Kin manta matsayina agurin ki?"


Harara na galla masa, "Na je na fada Uncle, Wallahi Hakkin Aisha bazai ta6a bari ka gama da duniya lafiya ba, Ka cuce ta Ka cuci Yaya shureim ka kuma cuci Babyn da suka haifa"!


Ina magana hawaye na shararowa kan kuncina. 


"Ashe dama duk kyautatawar da ka yi mana ba don Allah bane, sai don saboda wata mummunar manufa taka, baiwar Allah Aisha saida ta nuna batason zama agidan da ka kama mana haya a kasar germany saboda hankalinta bai kwanta da shi ba, sannan ta nuna rashin jin dadin ta akan zaryar da kake yi cikin gidan duk weekend sai ka zo ka kwana ga kudi da kake kashe mana, ni da kaina na kare ka agurinta na nuna mata cewa kada ta damu Uncle dina mutunne mai son yin alheri kuma dukiyar ka ta halal ce kasuwanci kake yi, sai daga baya na gano komai, arzikin da kake taƙama da shi ba ta hanyar halal ka tara shi ba, mu ka raina ma wayau da sunan kasuwanci kake yi, bayan haka ina zargin kana a ƙungiyar asiri ta yan shan jini, kuma kaine ka haɗa Aisha da mahaifinta, wato ka yi amfani da damar da kake da ita, a lokacin da kake zuwa ka kwana a gidanmu, sai ka bari dare ya yi sai ka saci hanya batare da sanin mu ba ka  ke shiga ɗakin Aisha, ka dauketa video da hotuna, wama ya sani ko asiri kake yi mata shiyasa har batasan kana yi mata hakan ba, wallahi ka ci amanar yardar da na yi maka! kuma na rantse da wanda raina yake a hannunshi in har baka dawo mana da babynmu ba saina fallasa asirin ka...."


 Tun kafin in ƙarasa maganar, Uncle Musa ya doka min tsawa yana huci kamar mayunwacin zaki, saboda tsabar fusata da bacin rai jikin shi ya dinga fitar da gumi, abun da ya daure mashi kai ya kuma ɗaga hankalinsa shine ta yaya akai duk nasan abunda yake ƙullawa?" Sam ya kasa magana sai huci yake fitarwa, Idanunsa sun kaɗa jawur.


Ganin baida niyar yin magana yasa naci gaba da cewa, "Kuma kaine ka shiga tsakanin Yaya Shureim da Aisha, ka yi masa asiri kasa yayi mata fyaɗe ba'a cikin hayyacin sa ba, komai dake faruwa kana bin diddiginsu kana samun information a gurin yan leƙen asirin ka, Hatta Mahaifinmu baka ƙyalesa ba, kana amfani da sihiri gurin juya shi don yabi ra'ayin ka, bayan haka kaine ka turama Daddy videos din Aisha daka dauka tare da kai sai ka 6oye fuskarka don karsu gane kaine kabar fuskar Aisha saboda tsabar mugunta da zalunci irin naka! kuma kai ne shaidanin da ya tunzura mahaifinmu akan karya kuskura ya yarda Shureim ya auri Aisha in ba haka ba zai rasa kujerar da yake nema kuma mutane zasu juya mashi baya saboda abun kunyar da Shureim ya akaita, munafukin Allah kaita faɗa masa kauli da ba'adi har saida ka shiga tsakanin daddy da Ya Shureim...".



Ban kai ga ƙarasa maganar ba ya katse ni ta hanyar bugun table din gabansa da hannunsa, Jikinshi har wani jijjiga yake yi saboda bacin rai.



"Benazir! Bana so ki jefa rayuwarki a cikin hadari! Ina mai gargadin ki, Tun wuri ki yi gaggawar janye zargin da kike yi mini, tun kafin ki yi danasani" Na yi tsalle na dire na ce, "Wlh Uncle bazan janye ba, saboda ni akan gaskiyata nake, ba zargin ka ni ke yi ba, tabbaci gare ni, kai baka yi mamakin tayaya akai nasan sirrinka ba uhum? Na faɗa ina kallon cikin idanunshi, wlh a lokacin ya razana dani ba kadan ba, amma da yake shu'umin mutunne sai ya dake ya tirje akan cewa ba gaskiya nake fada ba, ƙazafi nake yi masa.


raina a 6ace na juya zan bar falon ban ma jira ya karasa maganar shi ba, har na kusa fucewa Ya dakatar dani ta hanyar kiran sunana na tsaya ina jiran jin me zai ce.


"Ki fada mini komai kike so a duniyar nan zan yi maki shi, amma maganar zaki tona min asiri bata taso ba, Ki yi watsi da maganar nan, nifa Uncle dinki ne, In kika tona mini asiri kamar kin tona ma family din mu ne, ki dawo mu sasanta tsakanin mu" A hankali na juyo na fuskance shi.


"Baka so zaman lafiya ba Uncle, ai wlh in har kana son sasanci to ka dawo mana da babynmu, ni kuma nayi maka alkawarin babu wanda zaiji maganar nan! Ni ita kadai nake so bandamu da abunda kake aikatawa ba, wannan tsakanin ka da Allah ne, duk wanda ya yi da kyau ya sani, kuma dai akwai mutuwa akwai hisabi kowa zai girbi abunda ya shuka ne..." Dafe kanshi ya yi da tafin hannunsa kamar mai fama da ciwon kai,


"Meyasa kin fiye taurin kai da kafiya ne? Yakamata ki iya bakinki Benazir! Har yanzu bakisan wanene ni ba! Sabo da kaza bai hana in yankata! Wlh zan iya salwantar da rayuwarki, kuma idan na kashe ki na kashe banza."


A lokacin gabana ya faɗi na kuma sha jinin jikina amma ban bari ya gane hakan ba, saima na yi dariya na ce, "Idan ma kana tunanin kashe ni shine mafita agare ka, to ka daina, saboda hujjojin dana fada maka ina da su, bani kadai ke da su ba, Nima ina da mutanene da nake yin aiki tare da su, idan yau ka kashe ni, wlh zasu fallasa asirin ka ne duniya tasan me ka ke aikata, ka ga kuwa baka da wata mafita da ya wuce ka bini ta lalama"


 Maganar da na yi ta ɗaga hankalinsa matuƙa, Zuciyarshi ta hasala kamar ya rufe ni da bugu haka yake ji.


Har na ɗaga kafa zan fuce na sake tsinkayar muryarsa a cikin kunne na, "Ko don saboda abun da ke a cikin ki, Yakamata ki yi takatsantsan idan ba haka ba, zaki jefa rayuwarsa a cikin haɗari ne..." 


Wani irin faduwar gaba na ji, saboda a lokacin bansan ina ɗauke da juna biyu ba, cikin sauri na dafe cikina tare da zare idanuna akan fuskar shi, gaba daya na bi na ruɗe, Murmushin mugunta ya sakar mun saboda ya gano lago na..


"Benazir, nafi karfin ki nesa ba kusa ba, wlh baki isa ki ja dani ba, ƙaramar yar iska mai kwana da wando, saboda baki da hankali ki rasa wa zaki tuhuma sai ni? Kinsan wanene ni kuwa?? Ki fara sanin wanene ni kafin ki yi ja in ja dani, Sannan zan ƙara tuna maki, kina da miji, kina da juna biyu, kina da iyaye, kuma kina da ya ya mafi soyuwa a gare ki, Ina fata Kin fahimci abunda nake nufi???" 


Yana karasa maganar ya juya ya nufi up batare da ya sake waiwaye na ba, har saida ya 6ace ma ganina kafin na kawar da idanuna daga barin kallon sa.


Har na dawo gida ban daina tariyo maganarsa a cikin kunnena ba, Saboda hankalina ya tashi sosai, Lamarin Uncle Musa ya fara bani tsoro, na riga da na gane mugun mutunne shi, mara imani, kuma tantirin shaidani nasan zai iya aiwatar da komai don ya rufawa kansa asiri..


Bayan sati biyu na je ganin likita batare da saninka ba, bayan doc yayi mini gwaje-gwaje sakamakon ya nuna ina dauke da ciki na sati biyu, nan fa hankalina ya ƙara tashi kwata kwata ban yi farin ciki da cikin ba a lokacin saboda zai zama rauni na, kuma ina jin tsoron in haife shi saboda fargaban kada Uncle Musa ya salwantar da rayuwarsa, Ko ya ɗauke sa kamar yadda ya dauke ɗiyar Ya Shureim, wannan dalilinne yasa nayita yunkurin in zubar da cikin Angel, wlh Allah shine shaidata badan bana son shi ba, Kawai a lokacin muna yawan samun sabani da kai saboda bani da kwanciyar hankali, Damuwa tayi mini katutu, kullum cikin zullumi da fargaba nake yi saboda nasan Uncle Musa bazai ƙyale ni ba, kamar yadda ya fada dole ya dauki mataki akaina, kuskuren da na yi shine ƙin sanar da kai, Na ƙi faɗama kowa nabar abun a matsayin sirri, saboda gudun kada na faɗa ya koma mashi karshe inja ma kaina da kuma dangina don har lokacin ban saduda na kyaleshi kan fito da yarinyar Yaya Shureim ba, ka ji dalilin da yasa a duk lokacin daka kamani ina yunkurin zubar da cikinta ka tuhume ni dalili, sai ince maka bana son ya'ya, kuma bana son cikin saboda zai bata mini shape ɗin jikina, Amma a zahirin gaskiya bada son raina ni ke yin hakan ba, gaba daya rayuwar aurena da kai wani abun sai daga baya na gane bayin kaina bane, nasan bana jin magana, amma wlh Taj na so mu yi zaman lafiya sai dai na kasa faranta maka, saima cuzguna makan da nake yi hakanan bakai mini komai ba, kawai sai inji haushin ka, da tsanarka acikin Zuciyata, hatta mai aikin gidanmu Janet na ji na tsane ta, laifin da bai kai ya kawo ba idan ta yi mini bana ƙyale ta, saina azabtar da ita...." 


Kasa ƙarasa maganar ta yi saboda kukan da ya ƙwace mata, Haƙiƙa Zuciyar Taj ta karaya, tsantsar mamaki da al'jabi sun ruke zuciyar shi tamau, duk da sanyin A.c din dake a dakin hakan bai hana shi fitar da zufa ba, jikin shi har tsuma yake yi, wani irin tausayin Benazir ne ya kama shi ya yi danasanin zarginta da ya dinga yi, ashe bayin kanta bane, makircine aka shirya mata.


Numfasawa ta yi, cikin shesshekar kuka ta ci gaba da cewa, "Bayan wani lokaci, ban ƙara jin ɗuriyar Uncle musa ba, har lokacin da cikin Unaisah Ya cika wata tara cuf, nima kuma ban ƙara tuntubarsa ba ko in yi tunanin sanar da wani game da sirrin, a tunanina saboda bana son in jefa rayuwar ahalina Cikin hadari ne, a daren ranar da naƙuda ta kama ni, da ni da kai muna a kwance kan gadonmu mun yi nisa a cikin baccinmu, kwatsam ba zato ba tsammani, na fara jin naƙuda na taso mun, a firgice na farka daga baccin hannayena daddafe da cikina, ina ta faman cizon le6e saboda radadin da nake ji a jikina.


 Zufa duk ta wanke jikina, naita kokarin kai hannu don in tashe ka daga bacci amma nakasa, na yi kokarin in yi koda addu'a ne nan ma abun ya ci tura saboda haƙorana sun game gam, Taj ban ƙara sanin me ya faru dani ba, nadaisan bana a cikin hayyacina na sauko daga kan gado ina jan ƙafa na tura ƙofar toilet na shiga. Wlh Taj haihuwar Unaisah ikon Allah ne, kwata kwata bana a cikin hayyacina a haka na kar6i haihuwana da kaina amma bansan na yi ba, bansan dame na yi amfani gurin yanke cibin ba, a lokacin dana haifeta saida na kalleta cikin jini, na rungume abuna ina kuka tana kuka, abun da nake ta gudun in haifa sai gashi na haifeta, kuma sai na ji na kamu da ƙaunarta fiye da komai na duniyar nan, ina tsaka da kallonta, Kwatsam na fara jin ana ambaton sunana da wata iriyar murya mai matuƙar tsoratarwa, kuma nan take na dinga jin bakin ciki a cikin zuciyata, na ji na tsani komai in har ban je na amsa kiran da bakuwar muryar ke yi mini ba zan iya rasa raina ne, saboda yadda tsigar jikina ke tashi kamar ana tunzurani, yadda kasan ana zare raina ban ma san sa'adda na kwantar da Unaisah cikin bathtube ba, cikin hanzari duk da rashin ƙwarin jiki na fuce daga cikin toilet din, ko waiwaye ban yi ba na nufi gate, baba mai gadi yana adakinsa yana bacci baisan na fita ba, saboda wani ƙarfine ya zo mini bangaza ɗaya na yi wa kofar jikin gate din mu dake a kulle nan take ta buɗe nasa kai na fuce da gudu na bi santar mu. Ban ƙara sanin meya faru ba, sai dai na wayi gari na ganni a kwance kan gadon asibiti magashiyan rai a hannun Allah, bayan dana dawo hayyacina na tambayi nurses din dake kula dani akan meya faru da ni? anan suke faɗamin wani matashi ne ya bankaɗe ni da motarsa akan titi shine ya kawo ni asibitin, abun da ya ɗaure mini kai, ni da na ke a Jos meya kawo ni Abuja? Ban sanya damuwa araina ba saboda lokacin burina kawai in yi nesa da dangina saboda bana son su a kusa da ni.💔


Tun kan ta ƙarasa bashi labarin ya soma ambaton Inna lillahi wa'inna ilaihirraji'un! cikin karyayyar Murya ya ce, "Benazir! Dama haka komai ya faru baki ta6a sanar da ni ba? Kika sa nayi ta zargin ki, Ya Salam!! Pls ki yafe mini"!


In a cool voice ta ce, "Ba laifin ka bane, rashin sanine ya jawo hakan, Nima ka yafe mini 6ata maka rai da na yi a zaman mu na aure.."


"Ki manta da komai ya wuce, saboda ke ma bayin kanki bane, Ina tunanin Uncle dinki shine Ummul aba'isin komai da ya faru, yanzu ina so ki faɗa mini kece kika tura min sakon In sake ki!"


"Bani bace Taj, saboda ni ban tafi da waya ba, ni bansan wanene yayi mini hakan ba amma ina zargin Uncle Musa, saboda bayan na dawo gida Daddy da Mami sun faɗa min ana tura masu sakonni ta layin wayata, wai hada sakon da nace ni na gudu da son raina kuma na shiga duniya kada suyi tunanin zan dawo gare su kuma kada su sha wahalar nema na..." Dafe kai Taj ya yi da tafin hannunsa, Idanunsa sun kaɗa jawur da su.


"Benazir, Ni kuma saƙon da aka tura mini da bakuwar number ne, Idan bazan manta ba, abun da aka rubuta a cikin sakon shi ne ka sake ni Taj, kuma kada ka yi tunanin zan dawo na tafi kenan har abada, har kiran layin na yi amma saina ji shi a kashe kuma daga ranar ba'a ƙara tura min saƙo ba, tun ina sa ran dawowarki har dai na fidda rai"



Fashewa ta yi da kuka tana fadin, "Shiyasa kowa ya ƙullace ni aranshi saboda ana zargin da son raina na tafi, Koma wanene ya yi min hakan bazan ta6a yafe masa ba, Allah ya isa wlh sai Allah ya yi min sakayya, lallashinta ya shiga ya har ya samu ta yi shiru, shima ya yi shiru na ɗan wani lokaci, sai sautin Numfashin junan su da suke ji ta cikin wayar, so yake ya bata labarin rayuwar Unaisah a gidan Kurkukun ƙaddara saboda Yana zargin dasa hannun Uncle dinta sai dai ya kasa saboda baya son ya ƙara ɗaga hankalinta, ganin halin damuwar da ta shiga, gaba daya ya fahimci bibiyar rayuwar su ake yi, tun daga kan Benazir, da Aisha da Dr Shureim, da kuma Iyayensu suma ba'a ƙyale su hakanan ba.


Jin shirun ya yi yawa ne yasa shi tunanin ko ta yi bacci ne .


"Benazir?"


 In a low voice ta ce, "Na'am'


"Pls, Ki kwantar da hankalinki, nasan ba zaki rasa ciwon kai ba saboda kukan da kika sha, dan Allah kada ki sanya damuwa a ranki, maganar Uncle din ki zan faɗa ma Chief in sha Allah, duk yadda mu ka yi da shi zamu tuntu6e ku, yanzu ki kwanta ki yi bacci..." 


Bai ƙare maganar ba ta katse shi da cewa, "Don Allah Taj, ku taimaka mana, har yanzu ina ji araina Babyn Shureim tana a raye, kuma tana a gurin Uncle, shi kadai yasan inda ya aje ta, amma nasan in har kuka yi bincike akan shi zaku gano komai..."


Kwantar mata da hankali ya cigaba da yi saida suka raba dare suna yin waya kafin suka yi sallama, A daren ranar Taj bai iya runtsawa ba, saboda maganganun da suka tattauna da Benazir sun hana shi sukuni, har dai ya gaza jurewa ya kira layin Chief saboda yasan ba lallai bane idan ya yi bacci ba saboda a irin lokacin yana yawan tashi yin nafila, Cikin sa'a Chief ya yi picking call dinsa, a nan ya sanar da shi sun yi waya da Benazir, ya ce ya duba whatsapp dinsa ya tura mashi recording din da ya ɗauka na tattaunawar da suka yi, Chief ya amsa mashi da toh.


Bayan Chief ya kammala sauraron audio din da Taj ya tura masa, har sujjada saida yayi saboda nuna godiyarsa ga Allah da ya fara kawo masa sauƙi a cikin lamuransa ya kuma ƙara yin addu'ar neman nasara akan abun da suka sa a gaba.


After Two days, ana gobe za'a yi family meeting, kiran sallar asubahin farko Private jet din Prime minister ya yi landing a  Airport, Mai girma Sharafuddeen tare da Security details dinsa ne suka je dauko su acikin dankara dankaran motocin su, wannan karon daga shi sai Escorts dinsa suka zo Nigeria batare da iyalinsa ba, kuma bakowa ne yasan da zuwan nashi ba sai family dinsa, ko yan jarida ba a bari sun san da zancen zuwan na shi ba.


 Kaitsaye suka wuce Vila da shi, Sai da ya fara huce gajiyar da ya kwaso, Har bacci ya yi a dakin ɗan uwansa Sharafudden kafin zuwa marece suka shigo Estate.


Gaba daya yan'uwansa suka hallara a main falo din baba Obie don su tarbe shi, Yana shigowa falon suka nufe shi cike da tsantsar farin cikin ganin shi, ɗaya bayan daya suka dinga yin hugging dinsa, burinsa ya ƙarasa ga mahaifinsa sun hana shi motsawa kowa ɗokin ganinsa yake yi. Daƙyar ya samu suka kyale shi ya nufi Baba Obie dake ta sakar mashi murmushi ya rungume shi kamar zai maida shi cikin jikin shi, su Hajiya Saratu baki yaƙi rufuwa saboda murnar ganin Yaya Hateem, kowa ya buɗe baki sai ya tambaye shi ina iyalinsa? Meyasa bai zo da su ba? Ya ce masu su kwantar da hankalinsu suma zasu zo ne, amma a halin yanzu gimbiya da su Yazrin sun tafi Dubai gurin danginta hidima ce gare su, ita kuma Faryat bata samu hutun makaranta ba, shiyasa bata samu damar zuwa ba.


Lokacin da marece ya nutsa, sai ga kiran his excellency Abdul razak ya shigo wayar Baba Obie ya sanar da shi sun ƙaraso Abuja yana a aiport, Batare da 6ata lokaci ba Baba Obie ya tura da motocin Escorts suka dauko shi, bai jima da ƙarasowa ba sai ga motocin His excellency Deen na Kaduna sun iso cikin Estate din. Sun yi farin cikin sake haduwa da yan uwansu saboda sun yi kewar juna, Baba Obie sai haba haba yake da su, saboda murna bakinsa ya ƙi rufuwa. A daren ranar saida suka raba dare suna hira da mahaifinsu kamar ba zasu yi bacci ba har saida Baba Obie ya ce suje su kwanta su huta tukunna suka yi sallama da shi, Hateem dai ruƙe shi ya yi  a ɗakinsa yace tare zasu kwana saboda ya yi kewarsa, hakan ba ƙaramin dadi ya yi ma Prime minister ba, a kan gadon Baba Obie suka kwanta, zai kwana da tunanin mutumin da ya kwallafa rai da son ganinshi, ɗazu da Chief ya zo gaishe da shi har tambayar shi ya yi ina baby boy dinsa? Yana lafiya? A lokacin hankalin Chief ba karamin tashi ya yi ba, amma saboda baya son ya ɗaga masa hankali yasa shi cewa yana nan cikin ƙoshin lafiya, amma baya a gidansa yanzu, yana a camp din su na isod, yana kar6ar training.

Dakyar ya samu ya shawo kan Hateem har ya haƙura da maganar Danish amma fa yace duk yadda za'a yi kafin ya koma yana son ganin sa.

~________________________________🍁~

*_🔥🔥🔥The Chief Owais Birthday Celebration and Family Gathering🔥🔥🔥_*

*Daga Alƙalamin Boss Bature🔥✍️*

*Ga me bukatar karanta littafin kurkukun kaddara, 500 ne za'a tura Via Opay, 8103884440 Hafsat Bature Muhammad, shaidar biya za'a tura ta whatsapp, 08103884440*

Post a Comment

Idan kuna da tambaya akan abinda Baku game ba ko kuma kuma Neman littafin da babu a nan kawai ku ajiye tambayarku a ta comment ko wani shawara da Zaku bamu.

Previous Post Next Post

Sponsored Link

Sponsored Post