Kurkukun Ƙaddara Takun Ƙarshe page 68 Complete by Boss Bature


Health College

Kurkukun Ƙaddara Takun Ƙarshe page 68 Complete by Boss Bature

Takun Ƙarshe

A matuƙar ruɗe suka juya tare da kallon mai shigowa...

Sandar hannunta ce ta fara zurowa cikin falon, Kafin ta kunno kai, farar jallabiya ce a jikinta ta lullu6e kanta da head scarf ta rufe fuskarta da takunkumi, haka zalika idanunta suna asanye da shade fari, daƙyar ta ke dogara sandar hakan ya bayyana rashin kuzari a tattare da jikin ta, daga gani bata da koshin lafiya duba da yadda jikinta ke kerma.

Cike da tsantsar ruɗani suke kallon ta daga ƙasa har sama, basu san wacece ba, amma maganar da ta furta ta tsaya masu a ƙahon zuciya.

A sukwane Sharafudeen Ya miƙe yana duban ta, Muryarta ta yi masu kama da ta mahaifiyarsu da suka rasa tsawon shekaru wanda basu mance da yanayin sautin muryar tata ba.

Pravin sai faman zazzare Idanunsa ya ke yi burinsa kawai ya ga wacece ita duk da fargabar da ta shige shi saboda muryarta ta yi masa kama da ta wata da ya ta6a sani..

Baba Obie sam ya kasa motsawa, zuciyar shi ta ƙi aminta da abunda kunnuwanshi suke juyo mashi, haka kuma ya kasa yarda da abunda idanunsa ke nuna mashi,  kokwanto ya ke aransa ya ayyana hakan ma bazai ta6a yiwuwa ba, wanda ya mutu ba ya ta6a dawowa, duk da yanayin fuskarsa ya nuna tsantsar ruɗani, sai dai babu alamun fargaba atare da shi saboda ya yi imanin hakan bazai taba yiwuwa ba, sai dai idan fatalwarta ce ta dawo...



"Wace ce ita? Da izinin wa ta shigo estate din nan?" Tambayar da ta cika zuciyoyinsu kenan, gaba ɗaya sun ƙagara da su ji dame ta zo musu.



"Baiwar Allah daga ina ki ke? Wa kike nema ne? Kuma tayaya akai kika shigo estate ɗin?" His excellency Deen ne ya tambaya fuskarsa a murtuke.



Hajiya saratu dake a tsaye bakin kofar shiga part dinta tayi sototo tana kallon Ikon Allah..


Kusan atare Sir Mubarak Da Hateem suka miƙe daga zaunan da suke akan Sofas suka bi ta da kallo...


"Wacece wannan dattijuwar ne? Me ya kawo ta nan? Da iznin wa ta shigo Estate din nan uhum"! Acewar His excellency Abdul Razaq...


"Dan Allah ku yi wani abu akai, matar nan ba mutun bace, ku duba ku ga yadda jikinta ke kerma," Pravin ne ya faɗa yana zare idanun sa..


"Ku kira Security Officers ku tambaye su ta ya akai suka bar bare ya shigo mana estate! Da iznin Uban wa..."


 Senate Lateef ne ya ɗauko maganar yana huci idanunsa akan tsohuwar, ƙoƙari take ta cimmusu sai dai rawar da jikinta ke yi da rashin kuzari  ya hanata yin saurin.


 Tana gab da zata ƙarasa gaban Sofas ta ɗan dakata tana mayar da numfashi.


Cikin sauri Chief ya nufe ta, a hankali ya sanya tafin hannunsa ya dafe bayanta ya taimaka mata ta ci gaba da tafiya suka ƙaraso tsakiyar Sofas ɗin, rai a 6ace Sir mubarak Ya ce,"Kana acikin hankalinka kuwa? Ko ka san ta ne?...." 



Bai ƙarasa Maganar ba tsohuwar ta yi kukan kura ta dira agaban Baba Obie ta jefar da sandar hannunta, bai aune ba ta wanka masa zazzafan mari tare da cakumar gaban rigarshi da yatsun hannayenta dake ta kerma.



 Tashin Hankalin da ba'a saka masa rana! zazzare idanunsu suka yi cikin tsananin al'ajabin karfin halin dattijuwar nan take ran su ya 6aci, ta tako har cikin estate ɗinsu ta mari mahaifinsu a gaban idanunsu!!'


Ransu ya yi mugu mugun 6aci har sun harzuƙa za su kai mata bugu Sharafuddeen ya yi hanzarin kare ta.


Sir Mubarak yana huci ya ce, "Don Ubanki wacece ke?? Uban me ya kawo ki estate din nan? Da me kike taƙama ne?"


Senate ya amshe da fadin, "Sharafudeen ka matsa ka bamu guri! Baka ga abunda ta aikata bane? mahaifinmu fa ta mara agaban idanunmu!"


Cikin rawar murya Pravin ya ce, "Wallahi mahaukaciya ce, daga gani irin mahaukatan nanne masu yin hauka tuburan a dawanau ta gudo Allah Ya hankaɗo mana ita nan, wlh ku yi gaggawar korarta daga estate din nan idan ba haka ba zata manna maku hauka ne..." 



Baba Obie bai motsa ba amma fa ya girgiza sosai, da ruɗu yake kallon fuskarta da idanunsa wadanda suka kaɗa jawur, sam ya kasa magana saboda rudewar da ya yi ya rasa gane wacece ita meyasa ta mare shi?"


"Ba zaku ɗauki mataki ba? Kuna gani a gaban idonku ta mari Baba? Matar nan fa mahaukaciya ce wlh, babu lafiya a tare da ita, da gani tana tattare da baƙaƙen aljanu shiyasa har ta yi nasarar shigo mana nan..."


 Pravin ne Ya faɗa Yana zare idanunshi yadda kasan na kwarton mazuru.


Ran Hajiya Saratu ya 6aci ganin abun da dattijuwar ta yiwa mahaifinsu, cikin fushi ta nufe su tana ƙarasowa bata bi takan Sharafudeen ba, ta damƙi mayafin tsohuwar kokawa ta barke a tsakaninsu, tana huci ta ce, "Wlh bazata sa6uba, na rantse sai kin yabawa aya zaƙinta, ki shigo har estate dinmu ki mari ubanmu a gaban idanunmu? Kina acikin hayyacinki kuwa? Na shiga ukuna! Wai dan Allah uban wanene ya gayyaci tsohuwar najadun nan acikin gidan nan? Da iznin Ubanwa Securities suka bari ki ka shigo.."


 Balbaleta da faɗa Hajiya Saratu ta yi ta inda take shiga bata nan take fita ba.


Sai da suka gama harzuƙa kowa zuciyarshi ta zo a wuya.


Pravin yana ƙoƙarin zaro waya daga aljihu don ya kira Security Officers din gidan, Kwatsam ba zato ba tsammani Hajiya Saratu ta yakice takunkumin dake akan fuskarta, Ta fusge shade din dake akan idanun tsohuwar ya faɗo ƙasa ta bi tasa ƙafarta ta take shi ya faffashe.


 Ɗagowar da za ta yi da niyyar ta wanka mata mari har ta ɗaga tafin hannunta, idanunta suka sauka akan fuskar tsohuwar cak ta tsaya tana zare idanunta, Gaba ɗaya suka daura idanunsu akan fuskarta, Wani irin faduwar gaba suka ji ya ɗarsu acikin zukatansu, Sun ruɗe da ganin fuskarta kamar sun so su gane ta sai dai sun kasa gane wacece ita.



Sai lokacin ta yi ƙarfin halin buɗe baki murya na rawa ta ce, "Saratu, bani bace tsohuwar najadu, kin ga tsohon najadu nan, ubanku Obinna!" 



Ta faɗa tana nunasa da yatsanta sai lokacin ya shaida fuskarta, Wata irin zabura Baba Obie ya yi jikinsa na 6ari ya miƙe tsaye a kiɗime yana zazzare idanunsa! lokaci ɗaya yabi ya rikice, Hankalinsa yayi mugu mugun tashi, kanshi ya daure, Ya yi matuƙar razana da ganinta, tsantsar al'ajabine ya ruƙe shi, ganin abun yake kamar a mafarki sam ya kasa gasgatawa..


Hajiya saratu ta daka mata tsawa tana fadin "Ke! Mahaifin namu ne tsohon Najadu? Baiwar Allah dame kike taƙama ne, wace ce ke wai..."!


Bata ƙare maganar ba Hateem ya daka mata tsawa a ruɗe ta ja baki ta yi shiru, matsawa ya yi kusa da Khala ya dafa kafaɗunta da tafukan hannayen sa, ya kafe ta da idanunshi yana ƙoƙarin gano wacece ita..


Cikin sanyin murya ta ce, "Baku gane ni ba? Hateem! Sharafudeen! Ni ce fa, *AURORA EDWARD* Momman ku!" 



 Ta faɗa tana ƙoƙarin tuna masu ta juya ta dubi su Saratu ta ce, "Saratu! Lateef! Mubarak! Deeni? Razak! Baku gane ni ba ku ma?" Ta fada idanunta cike tab da ƙwalla.


Cikin shesshekar kuka ta ce, "Ba laifinku bane, laifin ubanku ne, Mugu azzalumi, Kun ganshi nan..., Shine ya ɗauke ni tsawon shekara ashirin ya raba ni da ku, ya yi maku ƙaryar na mutu bayan ina a raye...."


Waro idanunsu waje su ka yi suna kallon fuskarta yayin da ƙwaƙwalwarsu ke ƙoƙarin tariyo masu wacece ita saboda ta canza musu sosai, tayi tsufan da bazasu iya gane ta ba cikin sauki.


Saboda tsabar tashin hankali, duk da sanyin A.c din dake a falon hakan bai hana baba Obie fitar da gumi ba, jikinshi Ya jiƙe sharkaf kamar wanda aka tsamo daga teku, Firgici da tsoro sun mamaye zuciyar shi, duk yabi yasha jinin jikin shi.


Pretending ya yi duk don ya ƙara dagula masu lissafin ƙwaƙwalwar su ya ce, "This can't be Aurora Edward, bazai ta6a yiwuwa ba, matata ta mutu kuma mun shaida mutuwarta, wanda ya mutu baya dawowa sai dai idan Aljana ce ke!"


 Ya faɗa a tsawace kamar zai doke ta, bata ko kula shi ba ta mayar da dubanta akan ya'yan ta burinta su gane ta saboda hankalinta ya tashi ganin sun kasa yarda cewa ita ce.


"Hateem, Sharafudden nasan ko kowa bai gane ni ba, Ku zaku gane ni..." 


Ta faɗa tare da tallabo fuskar Hateem da tafukan ta, wata matsananciyar damuwa ce mai tattare da ruɗani ta mamaye zuciyar Hateem da Sharufudeen, kokwanto su ke yi akanta, abu ɗaya da ya yi masu kama dana mahaifiyarsu ajikin ta, shine launin ƙwayar idanun ta.


In a broken voice, Hateem yace "Momma... Is that really you I'm seeing? But how is that possible after you died? Ni dai a iya sanina wanda ya mutu baya dawowa ..." Ya faɗa yana girgiza kansa.


Bai ƙare maganar ba Sharafuddeen ya ce, "Don Allah ki fahimtar damu, kin jefa mu a ruɗani! gaba daya mun ruɗe, tabbas ba zamu manta da mahaifiyarmu ba, amma taya kika rayu bayan kin mutu? Dan Allah ki fada mana! Mafarkine wannan ko gaske..." Ya faɗa fuskarsa sharkaf da hawaye.


Murmushin takaici ta saki tare da juyawa ta dubi baba Obie da ya yi tsaye sototo kamar mutun mutumi.


"Ku tambayesa ina ya kai maku mahaifiyarku tsawon shekaru ashirin bayan ya yi maku ƙaryar na mutu, shine ummul aba'isin komai, shine ya azabtar da mahaifiyarku, wuya ce ta sa na yi tsufan da basu kai na shekaru na ba..." 


La66ansa na kerma ya ce, "Kada ku yarda da ita! Ƙarya take gaya maku, Fatalwa ce ba mutun ba ce, dan Allah ku kawar da ita daga cikin gidan nan, ku  kira Security officers su fitar da ita, Ku kore ta bana son ganinta" Ya faɗa yana nunata da yatsansa dake kerma..


"Don't believe her! I don't want to see her, Crazy ghost, hypocrite, get her out ba mutun bace Aljana ce ku kira sheikh Imam ya yi mata ruƙiya zaku tabbatar da abunda nake faɗa maku..."


Kamar zararre sai sambatu ya ke yi, duk yabi ya dabarbarce ta inda yake shiga ba ta nan yake fita ba.



Murmushin takaici ta sakar mashi, ga wani ƙululun bakin ciki da ya tokare maƙogwaronta, "Haba Obinna, idan har ni aljana ce to kai kuma bakin shaiɗani ne, wannan bawan Allah da kuke gani ba mutumin kirki bane, fasiƙi ne mara imani, daga shaidan sai shi, daga shi kuma sai fir'auna a wurin aikata zalunci...."


bata ƙare maganar ba suka daka mata tsawar da ta razanar da ita, gaba daya sun ruɗar dasu, da ita da baba Obie sun rasa maganar wa zasu ɗauka sai dai sun yarda da mahaifinsu fiye da yadda suka yarda da kansu.


Komai dake faruwa akan idanun Chief Owais da ya ƙame a tsaye kamar gunki sam ya kasa motsawa, tsantsar rudanine da fargaba akan fuskarsa.


Damƙar hannunta baba Obie ya yi ya dinga janta yana faɗin, "Zo ki fice ki bar mana Estate, wuce ki tafi, mahaukaciya, makira annamimiya mai son haɗa uba da yayansa, ni nasan maƙiya ne suka turo ki don ki yi mini ƙazafi..."


Fashewa ta yi da kuka tana kiran sunan Hateem dana Sharafudeen don su kawo mata ɗauki.


"A'uzu billahi minasshaiɗanir rajim tuf tuf, wa innahu min sulaimanu wa'innahu bismillah! Aniyarki ta biki makira algunguma baƙar munahika"


Ya faɗa yana tottofa mata yawu akan ta, sam sun kasa tsayar da shi, al'amarin ya rikita zukatansu.



Tana kuka haɗi da waiwayonsu cikin shesshekar murya tana magana tana miƙa masu hannu,


 "Hateem kada ku bari ya fitar dani, Sharafudeen ka taimaka mini, kada ku bari ya ƙara raba ni daku! Na yi kewarku, Wlh ni ce mahaifiyarku Aurora Edward! Your momma, ban mutu ba, ba fatalwa bace ni, Owais Kada ka bari ya kore ni, Ni kaɗai ce zan iya fayyace maku komai akan shi, Owais kaima ba ka tuna ni ba kakarka momma? ...." Ta faɗa idanunta cike tab da ƙwalla, tana ta ƙoƙarin ƙwace hannunta daga mugun ruƙon da baba Obie ya yi mata sai dai ta kasa saboda babu karfi atare da ita.


Hankalin Pravin Idan yayi dubu toh ya tashi, murnar da yake yi tuni ta koma ciki, ya murtuke fuska, hannayenshi biyu ya ɗaura a saman kanshi alamar ya shiga uku, ƙirjin shi kamar ana luguden ta6are, kafin ka ce me tuni ya haɗa uban gumi, jikinshi ya kama makyarkyata kamar wanda farfaɗiya ta kama.



Har ya kusa fucewa da ita daga falon Sharafudeen ya yi kukan kura ya watsa da gudu ya nufe su, yana ƙarasowa ya bangaje baba Obie gaba daya ya kife ƙasa kafin ya ɗago Sharafudeen ya damƙo hannun Khala ya juyo da ita suka dawo Falon.


Da sauri Hateem ya nufe su ya kar6e hannun Khala dake acikin na Sharafuddeen ya yi hugging ɗin ta akan broad chest dinsa, ya ƙanƙameta sosai kamar zai mayar da ita cikin cikin shi, wani irin sanyi ta ji ya ratsa zuciyarta kamar yadda shima ya ji sanyi a ranshi, rungumar da ya yi mata tasa ya ƙara yarda mahaifiyarsu ce saboda wani yanayi da ya tsinci kan shi wanda uwa da ɗa kadai ke jin irin shi idan jikinsu ya haɗu da na juna.


"Yaya kun yarda da ita? Kun yarda cewa momma ce?" Hajiya saratu ce ta faɗa a ruɗe


"Ta yaya bazamu yarda da ita ba, koda kowa bazai yarda ba mu mun yarda mahaifiyarmu ce, ni tun lokacin da idanuna suka shiga cikin nata, raina ya bani momma ce..." A cewar Sharafuddeen.


"In hakane taya akai ta rayu bayan ta mutu? kuma mun ga gawarta da idanunmu?" Ta jefa ma su tambayar .


Sharafuddeen ya ce, "Shi yakamata ku tuhuma.." Ya faɗa tare da nuna baba Obie


"Saboda na fara kokwanto akan shi!  kuma dama shi borin kunya da hauka ake naɗe shi, in ba haka ba meyasa zai ɗaga hankalinshi don kawai ya ganta? Bayan haka a gabanku baba ya juyamin baya ya hana kowa ya yi magana akan tuhumar da Owais ke yi mi ni, wai har ni zai ce in kare kaina agurin Owais!....." Ya faɗa yana jifar shi da kallon tuhuma.


Bai ƙarasa maganar ba Baba Obie Ya nufo su cike da rashin kuzari, yana fitar da huci kamar mayunwacin zaki ya nufi Khala da Hateem ya rungume, har ya miƙa hannu da niyyar ya damƙo ta, Sharafuddeen ya yi saurin damƙo hannunsa ya jefar da shi gefe ɗaya baima san sa'adda ya daka mashi tsawa ba, dama da haushinshi a cikin zuciyar shi.



Gabansa ne ya yanke ya faɗi jin yadda Sharafudeen ɗan cikinsa ya daka masa tsawa kuma ya jefar da hannunsa, hankali a tashe ya furta, "Na shiga uku..!!!"


"Baba, don't dare touch our momma! Don't touch her! Let her talk, Idan har kana da gaskiya meyasa zaka ɗaga hankali akanta huh? Ka barta ta yi magana mana!" rai abace Sharaudeen ya faɗa yana kallon cikin idanun shi.


 Zare idanu baba Obie ya yi with pure confusion on his face,


Tsantsar mamaki ya hana su Sir mubarak furta magana sai binsu da idanu su ke yi.


nuna kanshi ya yi da yatsan shi, "Sharafuddeen ni kake yi ma tsawa? Ka na cikin hayyacinka kuwa? Inna lillahi wa'inna ilahirraji'un.." ya faɗa yana dafe kanshi da tafukan hannayensa..


"Baka ga komai ba Obinna...."


 Tsohuwar ce ta faɗa tare da raba jikinta daga na Hateem ta dubi baba Obie da wani ƙasƙantaccen kallo mai cike da tsana..


"Dama bana faɗa maka ba akwai ranar ƙin dillanci? Shin ban fada maka duk min daran daɗewa asirinka zai tonu ba? Dama hausawa sun ce rana dubu ta 6arawo rana ɗaya ta me kaya, yau dubun taka zata cika...."


 Girgiza mata kai ya dinga yi idanunsa sun kaɗa jawur tamkar ya fasa ihu haka ya ke ji, ya rasa ya zai yi ya dakatar da ita.."


Cikin raunanniyar murya ya furta, "Kada ki yi min haka! Na roƙe ki, kada ki tona mini asiri, Kada ki raba ni da ƴaƴa na, kada ki raba ni da mutuncina, Ki rufe mini asiri ki agazama rayuwata, ki taimake ni kodan saboda darajar ya'yan mu, In kika fallasa asirina kamar kin fallasa asirin ahalinmu ne, zaki ja mana tozarci a idon duniya...." 


Zubewa ya yi akan gwiwowinsa yana ci gaba da girgiza mata kai hadi da marairaice mata fuska don ta tausaya mashi.


Kallo Ya koma sama, kalaman Baba Obie sun ɗaga hankulansu, sun jefa zuciyoyinsu acikin rudani tunma kafin su ji wani asiri ne nashi da baya son ta tona.


"Lokacin da na dinga roƙonka akan kada ka kashe ni ka barni da raina baka yi hakan ba saboda zuciyarka ta ƙeƙashe babu ɗigon imani a ranka, zalunci kadai kasa a gaba, ba irin magiyar da ban yi maka ba amma ka toshe kunnuwanka kuma ahaka kake tunanin ni zan rufa maka asiri bayan Allah ya tseratar da ni uhm?"


Ta faɗa tana kallonshi da raunatattun idanunta. Ruƙe ƙafafunta ya yi da hannayenshi ,"Dan Allah ki rufa mun asiri, kiyi min rai, kada ki kashe min rayuwata, na yi maki alƙawarin zan shiryu..."


 cikin jin ƙunar rai ta haɗiyi yawu mai ɗaci tare da kawar da idanunta daga barin kallon shi ta dubi sama hawaye na cigaba da zarya kan kuncinta, ranar da ta daɗe tana gargadinsa akan zuwanta, ba irin jan hankalin da bata yi mashi ba amma yaƙi ji yanzu wa gari ya waya?



"Dan Allah ki faɗa mana dagaske momma ce ke? Dama baki mutu ba kina a raye? Kuma me ya faru dake? Me babanmu ya akaita? Dan Allah ki faɗa mana, kun ɗaga mana hankali, Kun ruɗar damu..." Hajiya Saratu ce ta fada fuskarta a yamutse, Sir Mubarak ya ce,"Momma ki faɗa mana gaskiya, muna son mu ji taya akai kika rayu bayan kin mutu? Kuma me mahaifinmu ya akaita maki? Sannan wani asiri ne nashi da baya son ki faɗa?"


Tsantsar tausayinsu ne ya kamata, saboda tasan in ta faɗa su da farin ciki har abada, watakil ma baƙin cikin mahaifin nasu zai yi silar rasa ran wasu daga cikin su.


Amma ya zata yi bata da mafita da ya wuce wannan, saboda alwashine ta daukarwa kanta, Allah ne ya amsa addu'arta shiyasa har ta rayu don ta tona masa asiri don haka bazata butulce ba, mutun azzalumi irin sa bai cancanci a rufa masa asiri ba.


Cikin karyayyar murya tana kuka ta ce, "Ku yi haƙuri! ku yi haƙuri!! ku yi hakuri!!! da abun da zan faɗa, nasan abun da ciwo amma ya zaku yi ubanku ne ya ja maku, shine silar komai...."


Ta faɗa da tsawa tana kuka jikinta har jijjiga ya ke yi, Chief Owais ya kasa furta kalma, sai rarraba idanunsa ya ke yi akan fuskar Obie da Khala haƙika sun jefa shi a ruɗani.


"MAHAIFINKU OBINNA SHINE ELDER NA GIDAN KURKUKUN ƘADDARA, SHI DIN MUGUN MATSAFI NE, BAIDA IMANI, MUGUNTA DA ZALUNCI YASA A GABA, TUN FIL AZAL, DUKIYARSA BATA HALAL BACE, KUMA SHI BA MUSULMI BANE, ARNE NE, IDAN BAKU SAN KURKUKUN KADDARA BA, ZAN FAYYACE MAKU KOMAI, GIDAN KURKUKUN KADDARA GIDAN MATSAFA NE, YA KAFA SHI TSAWON SHEKARU TALATIN DA DAURIYA, ME AKE AIKATAWA A GIDAN KURKUKUN ƘADDARA? ƘANANUN YARAN DA BASU JI BA BASU GANI BA SUKE KULLEWA A CIKINSHI, BA FUCE BA SHIGE, TUN SUNA JARIRAI SUKE RAINONSU HAR SU GIRMA, ZASU TASO BATARE da addini ba, ba salla ba sallati, sai tsantsagwaran jahilci cike da kansu, basu san wanene mahaliccinsu ba, gaba daya sun tauye masu hakkinsu na rayuwa, abu mafi muni suna azabtar dasu azaba mai radadi, su yi lalata da su, su sha jininsu, su kwanta da gawa, su cire sassan jikin su, kai har jarirai basu bari ba da mata masu ciki suna kwanciya dasu, matasan yan mata da suke tsaka da shan azabar Jinin al'ada a haka suke saduwa dasu duk watan Allah idan ya kama, Ni kaina bazan iya misalta rayukan da suka salwantar ba, Nima ina ɗaya daga cikin fursinonin kurkukun kaddara, saboda tsautsayi yasa na yi masu leƙen asiri nasan sirrinsu shiyasa ya shirya makirci ya dauke ni daga gare ku,....."


Bata ƙarasa maganar ba Sir mubarak ya doka mata tsawar da ta yi silar firgicewarta, Yana huci ya ce, "Ƙaryane! Bazai ta6a zama gaskiya ba, kazafi ki ke yi masa, mahaifinmu bazai ta6a iya aikata munanan zunubban nan ba, mahaifinmu mutumin kirki ne, Mai jin tsoron Allah, mutun ne mai zuciyar imani da tausayi, bazai taba aikata abunda kike zarginsa da shi ba...."


Bai ƙare maganar ba senate Lateef da ya gama harzuka zuciyarshi a wuya yai kukan kura zai shaƙe wuyanta, Sharafuddeen ya yi saurin dakatar da shi ta hanyar damƙe wuyan hannunsa, yana huci ya ce, "Ka sake ni Sharafudeen!! Wannan mahaukaciyar matar ta rasa wa zata yi ma ƙazafi sai mahaifinmu? Baka ji munanan kalaman da ta jefe shi da su ba? Wai mahaifinmu ne matsafi? Ɗan kungiyar asiri???" Ya faɗa yana zare idanunsa da suka kaɗa jawur.


Cikin jin ƙunar rai His excellency Abdul Razak ya girgiza kai yana fitar da numfashi mai ɗumi ya ce, "Wlh kodai ku fitar da tsohuwar nan ko kuma in kashe ta a gurin nan, ta ya zaku bar mahaukaciya tana cin zarafin mahaifinmu a gaban idanunmu, wannan ai zancen banza ne, wlh sai munyi shari'a dake dole ki fuskanci hukunci mai tsanani...." 


Deen ya amshe, "Ai ga irinta nan! tun farkon shugowarta yakamata a kore ta, ni bansan uban waye ya bata iznin shigowa ciki ba! Ku kuma kun yi tsaye kamar wasu sakarkaru a gabanku ake yi wa mahaifinmu ƙazafi, daga gani abokan adawarmu ne suka turota don ta tarwatsa zaman lafiyar mu...." Ya faɗa yana nuna su Hateem.


Kalamansu sun cika kunnan baba Obie, wata irin karaya mai haɗe da faɗuwar gaba ce ta ɗarsu acikin zuciyarshi dake yi mashi wani irin mahaukacin bugun barazana, wani kallo yake binsu da shi mai wuyar fassaruwa ganin yadda suka haƙikance akan kazafi ne ake yi masa saboda yardar da su ka yi da shi.


Cikin raunanniyar murya Khala ta ce, "Koda zaku kashe ni bazan fasa faɗar gaskiya ba, na yi maku uzuri saboda nasan irin yardar da ku ka yi wa mahaifinku, hakika ya cutar da rayuwarku, ya zalunce ku, tsawon shekaru kuna tare da mugun iri acikin ku batare da kun sani ba, Ya daɗe yana munafurtarku...."


Ta ɗan dakata tana jan numfashi, sai ƙoƙarin kai mata bugu suke yi amma Hateem da Sharafudeen sun hana, sai ma suka katangeta ta yadda bazasu iya ta6ata ba, hakan ba ƙaramin daɗi ya yi mata ba, tana a tsakiyar su taci gaba da magana.


"Dukiyarsa bata halal bace, Haramun ce tsantsa, ya ciyar daku da haram! Ya tufatar daku da haram!! Ya gina ku da haram!!! Mahaifinku mutunne mai neman duniya ido rufe, baidamu da lahirarsa ba, koda ya ke baiyi imani da Allah ba, burinshi ya shahara, darajarsa ta ɗaukaka duniya tasan da zaman shi, shiyasa ya jefa kanshi cikin halaka da ku kanku saboda kuma bai barku hakanan ba, duk wata nasara da kuka samu, da duk wata ɗaukaka da kuka samu, sun samo asali ne daga abunda mahaifinku ya ke yi maku, shiyasa baku ta6a faɗuwa ba a rayuwarku, ya sanya maku farin jinin da in har kuka shiga mutane sai kun shahara acikin su, haka zalika in kuka ta6a abu zai yi albarka......"


Wannan karon bakinsu ya mutu bawai don sun yarda da maganar ba, sun dai fara wasiwasi acikin zuciyoyin su.


Yanayin fuskokinsu ya nuna tsantsar tashin hankali da damuwa haɗi da rudanin al'ajabin maganarta.


Baba Obie dake a zuƙunne kan gwiwowinsa ya kasa motsawa ji yake kamar an rufa masa bargon azaba a bayanshi saboda tashin hankalin da ya shiga, da wani ido zai dubesu a wannan baƙar ranar, gaba daya ya ɗimauce ji yake kamar ya haƙa rami ya binne kansa, babban abun takaicin sihirinsa ya ƙi tasiri a kanta, ya so tun farko ya dakatar da ita sai dai Allah bai yarda ba, this time around jikinta akwai kariyar ubangiji.


Tsohuwa Khala bata dakata da yin magana ba taci gaba da cewa, "Sau nawa matayenku suna haihuwar ya'ya su zo babu rai a jikinsu ko bayan sun haihu jariran su mutu?" Ta faɗa tamkar tana yi masu tambaya,


Ta ɗaura da cewa, "To waɗannan yaran ba mutuwa su ka yi ba, ku tambayi ubanku Obinna ina yaran ku suke! Ta faɗa a tsawace tare da nuna shi da yatsan ta.


Tashin hankalin da ba'a saka mashi date!, Wlh alƙalamina bazai iya misalta tashin hankalin da suka shiga ba, zuciyarsu ta karaya da ganin yadda ya yi shiru ya kasa kare kanshi daga abunda tsohuwar ke tuhumarsa."


Cikin shesshekar kuka Hajiya Saratu take fadin, "Nashiga Uku! Na bani na lalace! Baba dan Allah ka yi magana! Baba ka ƙaryata tsohuwar nan! Baba ka agazamana zuciyarmu ta raunata! al'amarin nan ya fi karfin zukatanmu! Baba mu mun yarda da kai munsan bazaka iya aikata abunda take jefanka da shi ba, wlh kazafi ta ke yi maka, Mahaifinmu ba fasiƙi bane, mahaifinmu ba matsafi bane, mahaifinmu bazai taba iya aikata rashin imanin da kike tuhumarsa da shi ba, dan Allah baba ka tashi ka ƙaryata tsohuwar nan....!"


 Tana cigaba da kuka ta nufe shi ta dafa kafaɗunsa tana kokarin mikar da shi tsaye don ya yi magana sai dai ya ƙi bata haɗin kai, wasu irin narka narkan shatun jijiyoyine suka fito saman fatar goshinsa..


"Baba ka taimaka min, Ka agazama rayuwarmu, baba ka yi magana, na roƙe ka, dan Allah dan soyayyarka da manzon Allah SAW......"


 Murmushin takaici khala ta yi, "Hmmmm Saratu dama kin daina wahalar da yawun bakin ki, saboda a halin yanzu mahaifinku baida bakin magana, wannan kaɗai ya isa yasa ku gasgata magana ta..."


Ta faɗa tana kallon fuskar baba Obie dake fitar da gumin zufa, shatun jijiyoyin wuyansa sun fito ruɗu ruɗu, jikinshi ya ɗauki wani irin mahaukacin zafi.


"Duk wani jariri da matayenku suka haifa ya zo ba a raye ba sune suke ɗauke shi daga gare ku, da haɗin bakin munafukan likitocin asibitinsa, Ku tambayi munafuki MD Dr Jidanna, da Dr Adam da kuma Dr chisom, da sa hannunsu ake yi maku wannan aika aikar...."


"Zaku haifi ɗa ku ganshi a mace alhalin ba shi bane rufa ido su ke yi maku su yi musayar shi da aljani su ɗauke na gaskiyar su tafi da shi gidan kurkukun kaddara, ku kuma ku dauki aljanin ku yi jana'izarsa ku rufe a ƙabari da sunan jinjirinku ku ka rufe...." ta faɗa cike da takaici,


"Haƙiƙa Obie ya zalunce ku wlh wata shari'ar sai dai a lahira, amma fasiƙin mutumin nan ya daɗe yana aikata luwaɗi da zina da jikokinsa da ya sadaukar a gidan kurkukun kaddara, ya sha jininsu, ya kashe su saboda neman duniya, bashi kaɗai ba harda sauran fasiƙan da suke aikata fasadi a bayan ƙasa, Elders din suna da yawa sune miyagun dake sadaukar da jininsu matsayin fursinoni, da yawa ma ƴa'ƴan naku azaba ce ke kashe su, cikin ka so ɗari baifi ka so goma ne ya rage daga cikin su ba...."


Numfashinta ne ya fara tsaitsayawa, jini ya fara bleeding daga cikin hancinta hakan ba ƙaramin ɗaga hankalin Sharafudeen da Hateem ya yi ba..


Daurewa ta yi duk da azabar da ta ke ji a jikinta a haka ta cije ta ci gaba da cewa, "Na rantse da wanda raina ya ke a hannunshi duk abunda na faɗa maku ba ƙarya bane, idan baku yarda ba, gayanan agabanku ku turkeshi ya fada maku gaskiya...."


 Tsayawa ta yi tana haki fuskarta ta jiƙe sharkaf da gumi, ta dafe saitin zuciyarta da tafin hannunta...


"Kamar yadda na faɗa maku, bashi kaɗai bane Elder, akwai muƙarrabansa da suke take masa baya, Amininsa Ifeanyichukwu inkiya Jan kunne amma a gidan kurkukun kaddara jan harshe shine nickname dinsa, shine Mataimakinsa a tare suke aikata fasadi, abun takaici sun auri junansu tun da daɗewa saboda tsantsagwaran jahilci da tumasanci...."


 Kutumar U! Zaro idanu suka yi kamar ƙwayar zasu faɗo ƙasa, sun shiga matsanancin tashin hankali, maganarta ta ƙara dagula masu lissafi, jin abun suke kamar wasan kwaikwayo.


"Bayan haka, surukinku mijin Saratu, shine Jan kunne na gidan kurkukun ƙaddara..." Tunkan ta ƙarasa maganar hajiya Saratu ta daddafe kanta da tafukan hannayenta, ta dinga girgiza kanta, tsabar kiɗimar da ta yi ne yasa ta dinga sambatu kowace addu'a ta zo bakinta furta ta kawai ta ke yi..


Runtse idanunta ta yi ruɗu yama hana ta iya tantance me Khala take nufi, buɗe idanunta keda wuya Unexpected ta hango Pravin da ya arta a guje ya nufi sashen yan aikin gidan, aikuwa jikinta na 6ari tabi bayan shi...


Khala bata dakata ba, ta ci gaba da cewa, "Sir Benjamin baturen amuruka, abokin mahaifinku wanda suka yi tashen yawon duniyarsu atare da obie da amininsa, shine jan le6e na gidan kurkukun ƙaddara, mugun fasiƙi ne....."


"Bayan shi sai baƙin shaidanin da taƙadarancin sa yafi na fir'auna, zan iya cewa tun da Allah ya halicce ni ban ta6a ganin mugun bawa irinsa ba, bazan iya misalta mugayen zunubban da yake aikatawa ba,  shine mai bada shawara kuma head na kula da bangaren bada horon giants ɗin kurkukun ƙaddara, baida imani ko misƙala zarratin, asalin shi bawan Obie ne daga baya da likafa ta ci gaba sai ya bashi muƙamin Elder...shish.. Shish.....


Kasa ƙarasawa ta yi saboda abun da ya sarƙe maƙoshinta, dama ba koshin lafiya ne da ita ba, jiri ne ya kwasheta a galabaice ta yanke jiki zata faɗi, cikin sauri Sharafudden ya sungumeta ya kwantar da ita akan doguwar kujera, sai kokarin ƙarasa maganar take yi amma ta kasa...


Wai shin Ina Chief Owais? bawan Allah Komai dake faruwa akan idanunsa kuma kunnuwansa na sauraro, kwata kwata baya acikin hayyacin shi, zufar dake tsastsafowa ta saman fatarsa ta jiƙe jikin shi sharkaf, kwata kwata ya gaza yarda da abunda Khala ta faɗa, Gani yake kamar mafarki yake yi ba gaske bane, duk da ya gama raunana zuciyarshi ta karaya da ganin yadda baba Obie ya yi shiru bai tanka ba! Hakan na nufin da gaske ne ba kazafi aka yi masa ba tun da ya kasa kare kan shi, inna lillahi wa'inna ilaihirraji'un! La'haula wala quwata illa billah, da wannan ranar ƙwara mutuwarsa, addu'o'i yake ta nanatawa acikin zuciyar shi..


Jiki a mace Sir mubarak ya zauna kan Sofa, zafi ne ya taso mashi har ta kai ga ya tu6e rigar shi ya jefar da ita ƙasa, ya ɗaura gwiwar hannunsa akan hand sofa ya zagba uban tagumi, kamar wanda ya rasa gata a duniya.


"Deen! kana jin abun da nake ji kuwa? Deen Ka tsunƙule ni dan Allah inaso na tabbatar in ba mafarki nake yi ba..."


Cikin raunanniyar murya His excellency Abdul Razak ya faɗa yana kallon His excellency Deen da ya haɗa uban gumi a jikin shi, girgiza kai ya yi cikin karyayyar murya ya ce, "Ba mafarki bane, kada mu yaudari kanmu! Da gaske ne komai ke faruwa, baba da muke sa ran zai kare kansa daga ƙazafin da tsohuwar nan ta yi masa ya kasa, gashi nan yana ji ya yi shiru..." Ya faɗa yana nuna Obie..


Muryar Sharafuddeen ce ta katse shi da cewa, "Abun da momma ta faɗa akansa ba ƙarya bane, ya aikata ne shiyasa ya kasa kare kansa....."


"In kuwa hakan ya tabbata gaskiya ne, Baba ka kashe mana rayuwa, ka gama da mu, mun mutu, mun bani mun shiga Uku! Inna lillahi wa'inna ilaihirraji'un......"


 Senate Lateef da ya ɗauko maganar bai kaita karshe ba Ya yanke jiki ya faɗi a sume, a firgice Deen da Abdul Razak suka rufa akan shi suna ambaton sunan shi haɗi da bubbuga jikin shi don ya tashi..


"Ruwa, tana buƙatar ruwa..."


 Hateem ne ya yi maganar, cikin sauri Sharafuddeen ya je ya dauko bottle water me sanyi yana gab da zai ƙaraso Ya lura da Owais dake a tsaye baya motsi da alama suman tsaye ya yi, wuce shi yayi ya nufi Hateem ya miƙa masa robar ruwan Ya kar6a yatsun hannunsa na kerma ya kanga ma tsohuwa Khala a baki, kusan rabin ruwan ta shanye sam ta kasa magana idanunta ma sun rufe gam bata iya buɗe su.


Kar6ar robar Sharafuden ya yi daga hannun Hateem  cike da rashin kuzari ya nufi su Deen Ya mika masu bayan sun yayyafa ma Senate Lateef ya farfado yana sambatu kamar mai tabin hankali har yana fadin Allah yasa mafarkine abunda ya ji.



Kar6ar robar ruwan ya yi daga hannun Deen ya je gaban Owais ya daddage ya watsa mashi ruwan a saman fuskar shi, lokaci ɗaya yaja dogon numfashi ya furzar da shi da wani irin zafi.


Kamar mahaukaci haka ya damƙi gaban rigar Sharafudeen hawaye na zarya akan kuncinsa da wata irin karyayyar murya ya ce,"Ka faɗa min kaima kana ɗaya daga cikinsu?"


Ya fahimci ba ya acikin hayyacinshi, tsigar jikinshi duk ta tashi haiƙam zuciya ta riga da ta tsinke.


Tsananin tausayin shine ya kama shi, Cikin sanyin murya ya ce, "Bana ɗaya daga cikin su Owais..."


"Meyasa ka kasa kare kanka lokacin dana tambayeka?"


Girgiza kanshi ya yi, "Saboda na daukarwa baba alƙawarin bazan faɗa ma kowa ba..." Katse shi ya yi, "Wani alƙawari ne ka daukar masa?"


"Shine ya kira ni a waya ya faɗamin zaku je kai farmaki gurin matsafa masu haɗarin gaske, ya gargade ni akan kada in kuskura in barka ka je, nace mashi ai yafi kusa da kai kafi jin ma maganarshi, me zai hana ya yi maka magana, sai ya ce min ba ya son bacin ranka ne yasan idan ya hana ka zuwa baza ka ji daɗi ba, shiyasa ya kasa amma yasan ni idan na yi maka magana bazaka ji komai ba, kawai in baka umarnin kada ka je, nace mashi baba ban ta6a hana Owais ya je kai farmaki ba, hasalima ni nake ƙarfafa masa gwiwa akan aikinsa idan na hana sa wannan karan dole zai ji ba daɗi ne, sai ya fara min faɗa yana fadin har shi zai bani umarni in ƙi bi! Yana magana ina magana, da ni da owais din duka ba a ƙarƙashin ikon shi muke ba? Na dinga bashi haƙuri har saida na amince zan yi maka magana tukunna ya haƙura, Sannan ya ce zai turo da ɗan saƙo da maganin bacci in saka maka a cikin Coffee, saboda in kasa kafiya ka turje akan ba zaka bi umarnina ba, sai in baka kasha coffee din, kuma baya son kasan shi ya sakani, nayi masa alkawarin bazan bari ka sani ba, kaji dalilin da yasa lokacin da na kira ka a resting home dina ka ƙi bani hadin kai ni kuma na baka coffeen dana zuba maganin baccin ka sha...."


 Gaba ɗaya maganganun Sharafudden a cikin kunnuwansu sun ji komai, hankulansu sun ƙara tashi, cikin rawar murya Owais ya ce, "Kana nufin baba shine ya hanani kai farmaki, kuma shine ya sa ka bani maganin bacci, amma a daren ranar ina ka je saboda an faɗa min ba a gan ka ba?" Ya fada a ƙagare da son jin amsar shi..


"Owais ni ban je ko'ina ba, ina a villa, adakin mommynka na kwana zaka iya tambayarta ka ji, bayan haka sanin kowannanku ne Villa tana da tsaro, ba yadda za'a yi shugaban ƙasa ya yi fitar sirri in the midst of the night batare da wani daga cikin security ya bi shi ba, Allah shine shaida ta..." Ya fada fuskarsa a yamutse.


"Hakan na nufin Baba shine ya ƙulla maka makirci saboda ya ɗaura maka laifin sa? Ko don ya shiga tsakanina da kai?"


Jinjina kai Sharafudden ya yi,"Babu tantama Owais, baba shine Master planner ɗin da ke shirya maƙarƙashiya atsakaninmu, bansan meyasa ya yi hakan ba..."


Cikin shesshekar kuka ya ƙarashe maganar, wata irin juwa ce ta ɗibi Chief ya yi taga taga zai kife ƙasa cikin zafin nama Sharafudeen ya janyoshi ya rungume abunsa akan kirjinshi, atare suka fashe da matsanancin kuka tamkar ransu zai fita.


Haƙiƙa baba Obie ya muzanta, kunyar duniya ta kama shi, ya shiga matsananciyar damuwa, bai ta6a zaton wannan ranar zata zo ba, Wani irin azababben ƙunci da bakin ciki da takaici ne suka turnuke zuciyar shi, jin kanshi yake kamar ba mutun ba saboda tashin hankali.


A zabure ya miƙe kamar mahaukaci ya juya jikinsa na 6ari zai bar wurin sai dai kafin ya kai ga tafiya Owais ya hango shi, a zuciye ya 6an6are jikinsa daga na daddynsa ya nufi baba Obie cikin zafin nama ya damƙi damtsen hannunsa ya juyo da shi suka fuskanci juna gaba da gaba, kunya ta hana baba Obie ya haɗa ido da Owais saidai ya sadda kanshi ƙasa.


Cikin raunanniyar murya ya ce, "Baba kai kaɗai ne zaka share min shakku na, Ina so na ji daga bakin ka, da gaske kaine Elder na gidan kurkukun ƙaddara? Kuma kaine mutumin da ya fitar da ni daga fagen yaƙi ya jefa ni a daki uhum??"


Ya faɗa cike da fargaban amsar da zai bashi, wlh ya yi fatan ace zai iya kare kansa sai dai ya kasa saboda asirinsa ya riga da ya tonu.


Gaba ɗaya idanunsu na a kan fuskarshi amsar shi kawai suke jira su ji, batare da ya ɗago da idanunshi ya dube shi ba ya jinjina mashi kai alamar Eh, a lokaci ji ya yi kamar ya haƙa ƙasa ya binne kansa saboda baƙin cikin da ya ziyarci zuciyarshi, raɗaɗin da suka ji yafi na ƙunar wuta zafi..Ya Ilahi!


Zuciya ce ta ɗibi Owais baisan sa'adda ya ci kwalar rigarshi ba, da hannu biyu ya damƙe shi sosai jikinshi na 6ari.


Hakan ba ƙaramin karya zuciyar Obie ya yi ba, duk irin jarumtakar namiji hakan bai hana sun fashe da kuka ba kamar ƙananun yara, gaba ɗaya sautin koke kokensu ya cika falon, wasu suka dafe kawunansu da tafukan hannayensu saboda azabar radadin da zuciyarsu ke yi musu, wlh sun yi danasanin zuwansu duniya a lokacin, sun ji ɗaci a ransu, ranar ta zame masu mafi muni a rayuwarsu. Gaba daya suka kewaye shi suna tambayar shi don me zai yi musu haka? Meyasa ya ci amanarsu ya ha'ince su? Wannan wani irin neman duniya ne? Me yasa ya aikata musu hakan? Wlh Hankalinsu ya tashi matuƙa, duk sun fita hayyacin su, kuka kawai suke yi kamar ransu zai fita..


Hakan ba ƙaramin karya zuciyar Obie ya yi ba, bai ta6a danasanin irin rayuwar da ya daukarwa kansa ba irin yau, saboda Allah ya jarabce shi da masifar son ya'yan shi, Koda ya ke sadaukar da jikokin shi bai ta6a sadaukar da ya'yan shi ba.


daƙyar ya iya haɗiye baƙin cikin shi, da wata irin karyayyar murya ya furta, "INNA LILLAHI WA'INNA ILAIHIRRAJI'UN!!! Na shiga Uku! wlh na daɗe ina fargaban zuwan wannan ranar, dama nasan duk mun daran daɗewa asirina zai tonu ne sai dai ban ta6a zaton zai tonu ta wannan hanyar ba! Ranar da nake jin zullumi da fargaban zuwanta, ranar da nake jiye ma kaina tsoron zuwanta, ya zan yi da rayuwana? ya zan yi da rayuwarku? Nasan na cutar da rayuwarku cuta mafi muni, na zalunce ku, na kuma zalunci kaina, Amma koma dai menene bakin alƙalami ya riga da ya bushe, na riga dana tabka babban kuskure, ban kuma san da wasu kalmomi zan roƙe ku gafara ba, banma cancanci in nemi yafiya agurinku ba, wlh na muzanta, na tozarta, na ji kunyar haɗa idanuna da ku, kaicona!...." 


Bai ƙarasa maganar ba ya fashe da kuka, hawaye suka wanke fuskar shi, mutumin da sun manta when last suka ga hawaye ya zuba daga cikin idanunsa saboda jarumtakarsa ashe tsantsagwaran matsafine, Yana kuka suna kuka an rasa me lallashin wani, daƙyar yake kallon fuskokinsu cike da jin nauyin abun kunyar da ya aikata musu.


"Nasan na biyewa son zuciya, amma wallahi ba laifina bane, Nima gado na yi, tun kakanninmu da iyayenmu na taso acikin matsafa, shine hanyar samunmu, na yaudare ku da musulunci amma ni ba musulmi bane, arne ne ni kamar yadda ta faɗa muku, tun da na taso rayuwata bansan mai kyau da mara kyau ba haka iyayena suka tarbiyantar da ni, duk abubuwan da suka faru son zuciya ne da son ɗaukaka, buri na in tara dukiya, in ɗaukaka in zama shahararre a duniya, ƴa'ƴana ma su ɗaukaka a idon duniya, wannan dalilinne yasa gaba ɗaya kuka ɗaukaka kowannanku na nema masa duniya kuma ya same ta..." Bai ƙare maganar ba HATEEM ya katse shi ta hanyar cakumar shi cikin tsananin tashin hankali ya furta, "Baba! Baba!! baba!!!...." Idanuwansu cikin na juna a marairaice yake kallon shi..


"Meyasa ka za6i ka ciyar da mu haram? Baba duk irin ƙaunar da muke yi maka, kullum burinmu mu kare maka mutuncinka sai gashi kai ka zubar mana da namu mutuncin, ɗaukakar daka sama mana ta tashi a banza wlh! Saboda da zarar mutane sun ji abunda kake aikatawa wlh mun zama abun gudu, za'a juya mana baya ne a tsangwamemu zamu zama abun ƙyama, makiya zasu samu damar cuzguna mana, Baba ka bar mana mummunan tabon da mutane zasu dinga cin zarafin mu da shi! Haba baba! Wlh ka bamu mamaki baba, wai mahaifinmu ne yake aikata munanan zunubban nan?" Ya faɗa yana haɗiyar yawu mai tsananin ɗaci cikin mutuwar jiki ya sake shi..


Sharafudeen ya ɗaura da cewa, "Baba yanzu ina amfanin irin wannan? Wace riba ka samu baba? Ina hankalinka yake? Tayaya ka bari shaidan da zuciya suka rinjaye ka? Kamanta da wata rana zaka mutu ka koma ga Allah, baba Idan ka nema mana duniya lahirarmu fa? Ya kake so mu yi baba? Muna alfahari da kai, kaine abun tunƙahon mu, kaine silar ɗaukakarmu ashe mun yaudari kanmu baba, A yau mutuncinka ya zube acikin idanunmu baka da sauran daraja baba, wlh da wannan bakin cikin daka ƙunsa mana da kashe mu ka yi kamar yadda ka saba kashe ya'yan mutane...!"


Kuka ne ya ci ƙarfinsa har ya kasa karasa maganar..


Baba Obie sai kuka yake yi babu ƙaƙƙautawa..


Senate Lateef ya ce, "Baba wace shafewar basira ce ta same ka? Ni abun da ya dauremin kai yadda har ka iya kashe mutun ka sha jinin shi, ka kuma lalata rayuwar yaran da basu ji ba basu gani ba, baba wa ya koya maka zaluncin nan? Har yanzu na gaza yarda kaine kake aikata hakan Baba, Tsawon shekara nawa kana aikata fasadi a doron ƙasa! Wallah baba da ace ka yi hakuri tun fil azal ka yi rayuwarka cikin talaucinka da sai ya fiye mana kwanciyar hankali, shi arziki da daukaka na Allah ne, sai wanda ya so yake bawa, watakil ma kana ɗaya daga cikin wadanda Allah ya tsaga da rabonsu kaine baka sani ba, ka biyewa son zuciyar ka baba, gayanan ka jefa rayuwarmu a halaka, bayan haka jin dadin duniya ƙalilan ne baba, gaba dayanmu mutuwa zamu yi, komai muka mallaka anan gidan duniya zamu barshi, lahiri itace dawwamammiya, wlh da wannan masifar daka jefa mu a ciki wlh gara ace mun taso rayuwarmu a matsayin musakai marasa gata a duniya da dai irin wannan rayuwar, baba yanzu da ka ɗaukakamu ya zaka yi da mu? sai da ka bari duniyar tasan da zamanmu ana yi mana kallon mutane masu daraja da ƙima, masu martaba a idon duniya, yanzu idan suka ji miyagun laifukan da kake aikatawa me kake tunanin zai biyo baya?" Ya jefa mashi tambayar yana kuka yana girgiza kai.


 kafafunsa ne suka gaza ɗaukarsa ya zube kan gwiwowinsa, idanunsa sun rune jawur, kumatunsa sun yi jajir, duk ya faffasa labbansa da haƙoransa, gemunsa ya jiƙe sharkaf da ruwan hawayensa, Ko'ina na jikinsa zufa ce  take tsattsafo masa kamar babu A.c a falon.


Wlh ya sadaƙas bai ta6a zaton zai ji kunyar zunubban da yake aikatawa ba sai yau da Khala ta fallasa asirin sa a gaban ya'yansa mafi soyuwa a gare shi.


Dukkan ilahirin jikinsa kerma ya ke yi, ga wani irin azababben zazzabi da ya lulllu6esa, mutumin da sai ya yi shekara da shekaru bai yi ciwo ba saboda ƙoshin lafiyar dake gare shi to yau dai hada matsanancin ciwon kai, bazama a raza ciwon zuciya na farat daya ba saboda depression din da ya kama shi, gaba ɗaya suka zauna kewaye da shi kamar malami da almajiransa kuka hada majina, sun kasa tsayar da kan su. 😭


Daƙyar ya iya furta, "Idan na ce ku yi hakuri ban yi maku adalci ba, iya cutarwa na cutar da rayuwarku, ban cancanta na ci gaba da rayuwa ba, nasan a halin yanzu da kuka gano wanene ni kun tsane ni fiye da komai na duniyar nan, don haka na miƙa wuyana a gare ku, nasan na aikata maku ba dai dai ba, Ku yanke mini duk wani hukunci da kuka ga ya dace dani, ku azabtar da ni, sannan ku kashe ni, idan ba haka ba, Ni zan kashe kaina, saboda bazan iya cigaba da rayuwa da abun kunyar da na aikata muku ba..." Yana faɗa yana kuka haɗi da tari.


Sama sama khala dake a kwance kan Sofa take jiyo maganganunsu, baiwar Allah ita kadai tasan halin da take a ciki, ta tona masa asiri burinta ya cika sai dai bata yi farin ciki ba, saboda halin da ya'yan shi suka shiga shiyasa kafin ka fara aikata wani abu mara kyau ka fara tunanin makomarka da kuma halin da zaka jefa wanda ya yarda da kai abun yana da ciwo.


"Ku kashe ni,  in har baku kashe ni ba mutane bazasu ƙyale ni ba, ku kashe ni kawai nafi so na mutu a hannunku, ko dan saboda ku dauki fansar abun dana aikata maku, ku kashe ni na ce, in ba haka ba zan kashe kaina..." 


Zumbur ya miƙe jikinshi na kerma, Lokaci daya gabansu ya fadi ganin jinin da ya wanke gaban wandon shi.


Har suna haɗa baki gurin ambaton sunanshi, Allah sarki duk da abun da ya aikata hakan bai hana su ɗaga hankalinsu a kanshi ba, 


"Mu kai shi asibiti kada ya rasa ranshi!" Sharafuddeen ne ya yi maganar a ruɗe.


 Har sai da baba Obie ya dube shi da raunatattun idanunsa, ƙasa ƙasa da murya ya ce, "Duk abunda na yi maka baisa ka daina damuwa da ni ba Sharafuddeen....?" Girgiza kai ya yi, "Ku yi hakuri bazan je asibiti ba, ku barni a gida, in ma mutuwace ta riske ni a cikin ku...." Yana ƙarasa maganar ya shallake su ya juya a hanzarce ya nufi part ɗinsa, da gudu suka bi bayanshi kafin su ƙaraso tuni ya shige ɗakin ya ja ƙofa ya datseta ta yadda ba zasu iya buɗeta ba. 😭


Yanke jiki ya yi ya faɗi kan floor ya dinga birgima yana bubbuga goshinsa kan floor har saida ya fashe jini ya 6alle masa, daga waje suna juyo kururuwar azabar da yake fitarwa mai kuwar gaske kamar zai fasa dodon kunnuwansu.


Da iya ƙarfinsu na karshe suka dinga bubbuga ƙofar hadi da ambaton sunan shi da karfi.


Chief kamar zai 6alle ƙofar da kafaɗarsa ya dinga bangazarta duk da raɗadin da ya ke ji.


"Baba ka buɗe mana ƙofa, bamu gama magana da kai ba, baba kada ka mutu kabar mu, baba dan Allah ka buɗe bamu gaji da ganin ka ba, akwai tambayoyin da baka bamu amsoshinsu ba, baba! baba!!, zamu iya yafe maka amma ka buɗe mana kofar, baba pls, baba pls, idan ka tafi ka barmu a cikin wannan mawuyacin halin daka jefa mu ya kake so mu yi da rayuwarmu! Ka taimaka mana baba, ka fitar damu baba.. " 


Ba irin bugun da ba su yi ma kofar ba amma ta ƙi 6allewa, a karshe da suka galabaita a gaban kofar ɗakin nashi suka zazzauna suna cigaba da yin kuka kamar masu zaman makoki.


Gaba ɗaya abun da ke faruwa ƴan aikin gidan basu sani ba, saboda anyi masu iyaka da shiga falon dama ƙa'ida idan za'ayi family meeting ba'a buƙatar bare agurin shiyasa kwata kwata basu leƙo ba kuma basu ji sautin koke koken da ake yi ba, saboda akwai tazara tsakanin sashen su da main falo.



_____________________PRAVIN 🥵



Tun lokacin da khala ta fara fallasa asirin su, cikin rawar jiki ya bar falon batare da sanin kowan nan su ba, bai nufi ko'ina ba sai sashen yan aikin gidan.


A lokacin Hajjaty tana a ƙudundune cikin bargo har ta samu bacci ya ɗan dauke ta, kwatsam ba zato ba tsammani kamar daga sama ta ji an cakumeta, ta fasa ƙara tana kokarin kwache kanta cikin ruɗu da tashin hankali, kwata kwata batasan wanene ba saboda bargon da ya lullu6e fuskarta, a saman kafaɗarshi ya sa6e ta, tana kuka tana ihu tare da ambaton sunan pravin don ya kawo mata ɗauki, juyawar da zai yi keda wuya ya yi arba da hajiya Saratu dake shugowa ɗakin afujajan nan take gabanshi ya yanke ya faɗi ya zazzare idanunshi yana kallon ta kamar yadda take kallonshi da tsantsar tashin hankali akan fuskarta..


Numfashinta na fita da hucin bacin rai ta ce,"Munafiki, Gidan ubanwa zaka kai ta eye? Yan iska maciya amana, wato Kun daɗe kuna cin amanata, yanzu da ka ga asirinka ya tonu shine ka lalla6o ka saci jiki ka shugo don ka dauki kwartuwarka don ku gudu ko?" Ta faɗa tana zare idanunta.


Tsawa ya daka mata har saida ta razana, muryarsa na rawa ya ce, "Ki matsa ki bani wuri in wuce tunkafin in yi maki illah!"


Cikin fusatacciyar murya ta ce, "Illah kuma ta nawa? Ka bani mamaki pravin, Ka karya min zuciyata, munafuki dama na daɗe ina zargin Hajjaty ashe tare kuke aikata fasiƙanci, wai a haka na aure ka na haifa maka ƴa'ƴa, Ka cutar da rayuwata pravin, hakkina da na ya'yanka bazai ta6a bari ka gama da duniya lafiya ba wlh, kuma na rantse babu gidan ubanda zaku je, mayaudaran banza, dole ku gurbi abun da kuka shuka..." 



Bata ƙarasa maganar ba, sakamakon naushin da ya sakar mata akan kuncinta, nan take gefen bakinta ya fashe ta fara bleeding, azabar zafin da ta ji ne yasa ta dafe gefen bakin, da mamaki ta furta,"Pravin! yau da hannunka ka dake ni? Inna lillahi..! " Rai a 6ace ta yi kukan kura ta haɗa su duka biyun da shi da Hajjaty ta hankaɗa su gaba ɗaya suka kife ƙasa, bargon jikin Hajjaty ya warware baiwar Allah tuni ta jima da sumewa sakamakon buguwar da kanta yayi dama ya lafiyar gwiwa.


 Ransa ya 6aci matuƙa, a harzuƙe ya yunƙura ya mike Ya nufi hajiya Saratu batai aune ba, ya damƙi ƙeyarta da hannunshi ya jata ta karfi ya nufi mirror tana ta kokarin ta kwace kanta sai dai ta kasa saboda raunin da zuciyarta ta yi yasa ta kasa ta6uka komai.


Yana isa gaban madubin ya buga kanta jikin shi nan take madubin ya fashe, duk ya sossoke fuskarta, tuni ta fara bleeding, kukan ma ta kasa yi saboda zogin azabar da ya ratsa sassan jikin ta, ya ɗago da kan nata ya wurgar da da ita a galabaice ta kife kan floor ta mirgina numfashinta yana ta kokawar ɗaukewa.


Hakan bai masa ba sai da ya take yatsun hannayen ta da tafin ƙafarsa duk ya murjesu suka faffashe jini ya soma tsastsafowa.


kwata kwata babu imani a zuciyarsa, ga idanun nan nasa sun kaɗa jawur kamar an watsa barkono a cikin su, Ya na huci ya furta, "Allah ya isa tsakanina da ku, Dangin matsafa masu arziƙin jini, Duk ubanku ne ya ja min shiga halin da nake a ciki, shine mugun da ya sa na jefa rayuwata cikin halaka ina zaman zamana lafiya, dama ni ban ta6a son ki ba, dukiyarki ce tasa na aureki da kuma kwaɗayin surar jikin ki, Kin daɗe kina baƙanta min rai ke ga mai arziki ɗiyar ƙaruna, ki yi ta min gorin arziƙi don ina zaune a gidan ku, to ai ga irinta nan, yanzu ai kin gane arzikin naku bana halal bane ko? Ya faɗa yana tottafa mata yawu a kan fuskarta.


"Kuɗin jini ne kuke tunƙaho da su, wlh badan ƴa'yan dake tsakanina dake ba da ba abun da zai hana in huce haushina a kanki, zan bar ki da ranki ne ba don na so ba.."


 Ya faɗa yana kallon fuskarta da ta jiƙe sharkaf da jini kamanninta har sun sauya saboda azaba ta gama fita hayyacinta, juyawa ya yi da sauri ya nufi bargon Hajjaty ya janyo shi ya rufa mata a jikinta tare da nannaɗeta a cikin bargon ya mayar da ita kan kafaɗarsa, Ya tsallake hajiya Saratu dake a kwance rai hannun Allah cikin sauri ya fuce daga ɗakin, batare da sanin kowa ba ya gudu daga Estate ɗin......💔


___________________________________✍️



*_(SHIN ME KUKE TUNANIN ZAI BIYO BAYA IDAN SAURAN AHLIN FAMILYN SUKA KARASO SUKA JI ABUN DA KE FARUWA❓GA HAJIYA SARATU AKWANCE RAI HANNUN ALLAH! WA ZAI KAI MATA DAUKI❓ YA RAYUWAR BABA OBIE ZATA KAYA ZAI KASHE KANSHI NE KO KUWA❓ ME KUKE TUNANIN ZAI BIYO BAYA IDAN SAURAN ELDERS SUKA JI  LABARIN ASIRIN ELDER YA TONU❓YA LABARIN PRAVIN DAYA GUDU DA HAJJATY GIDAN UBAN WA ZAIJE❓ DA WANI IDO YA'YAN BABA OBIE ZASU FUSKANCI DUNIYA? KUNA TUNANIN BA ZASU FUSKANCI KALUBALE BA AKAN MUKAMAN SU❓ TAYA ZA'A HADA KOWANI PRISONERS DA IYAYENSA❓ TAYA ZA'A KAMA SAURAN ELDER❓ TO WAINI TAYAYA MA AKAI TSOHUWA KHALA TA RAYU?😳 YANZU NE LOKACIN DA ZAKU ƊAURA ƊAMARARKU TAMAU DON JIN YADDA ZATA KAYA🔥💪_*

*Gani ga wane Ya ishi wane Jin tsoron Allah😭 page din nan ya taba zuciyata)*

*DAGA ALƘALAMIN BOSS BATURE🔥🔥🔥🔥😭*

*Ga me bukatar karanta littafin kurkukun kaddara, 500 ne za'a tura Via Opay, 8103884440 Hafsat Bature Muhammad, shaidar biya za'a tura ta whatsapp, 08103884440*

2 Comments

Idan kuna da tambaya akan abinda Baku game ba ko kuma kuma Neman littafin da babu a nan kawai ku ajiye tambayarku a ta comment ko wani shawara da Zaku bamu.

Previous Post Next Post

Sponsored Link

Sponsored Post