Ɗayan bayan ɗaya suka soma shigowa cikin main falo, twins ne a gaba daga bayan su Captain Yaseer ne sanye cikin pilot suit dinsa da bai kai ga cirewa ba, bai jima da ƙarasowa ƙasar ba, su twins ne suka je ɗauko shi a airpot.
Justice Nadeem da Ziyad sun saka shi a tsakiyar su, shigar su keda wuya saiga Mommy Turai tare da Jazz sun shigo suma, fuskokinsu da fara'a, a mutunce suke gaisawa da junansu, hayaniyar hirar da suke yi ce ta cika falon yayin da suke tafiya atsanake suna tunkarar interior din sa.
"Mommy Zaki bai zo bane?" Ziyad ne ya tambaya yana kallon Turai, ta ce, "Bai zo ba wlh, daddynsa ya faɗa mun sunyi waya yace bazai samu damar halarta ba saboda ayyuka da su ka yi mashi yawa, amma yace a kira shi video call idan aka fara don ya samu jin abun da za a tattauna..."
Ziyad ya ce, "Na so ace ya zo wlh, munyi missing nashi, amma bakomai zamu yi magana idan an kira shi video call din.."
Turai ta ce, "Ai wannan karon naga bakowa ya samu damar halarta ba, kowa ya shiga busy, wasu suna school wasu kuma aiki ne ya ruƙe su.."
"Mutumina ya gajiyar aiki? Na ga ko kakin baka samu ka cire ba.." Justice ne ya faɗa yana dafa kafaɗar Yaseer, yamutsa fuska ya yi tamkar baison furta maganar ya ce, "Alhamdulillah, bana so a fara meeting din batare dani ba, bayan haka na yi missing naku sosai, bazan iya jure rashin ganin ku ba, tun da jirginmu ya yi landing nake ta zumudin in ƙaraso don inga yan uwana..." Murmushi suka saki, gaba ɗayan su sun ji dadin maganar shi.
Zayn ya ce, "Muma mun yi kewarka Bro, kuma mun yi murnar ganinka..." Sumar kan Zayn ya shafa da yatsunsa da zolaya ya ce, "Nima na yi kewarku, dangin lord shiva, ay na ga yau indiyancin ne ya motsa, kun yi gayu abun ku" Dariya suka saki.
Zaid Ya ce, "Aikin daddy ne, shine ya matsa mana sai mun saka kayan india..." Jazz dake sauraronsu murmushi ne dauke akan fuskar shi, yana jin dadin yadda suke fira da junan su burge shi su ke yi, ba halin ya saka musu baki saboda shakkar Captain Yaseer ya ke ji, Ya tsani bare yana da girman kai sosai, haka zalika Zayn halin shi kusan ɗaya dana Yaseer bambancin su kaɗan ne.
Lokaci ɗaya suka Ci burki ganin babu kowa A falon, ko gifcin mutun babu, kallon juna suka yi..Justice ya ce,"Bangane ba! Ina mutanan gidan nan ne? Ba dai har sun kammala meeting din ba?" Ya faɗa a ɗan rude.
Captain Yaseer ya ce, "In kuwa hakane basu kyauta mana ba Allah, duk saurin da na yi ace har an gama, ai dana sani ban zo ba ke nan.." Ya faɗa fuskarsa a haɗe ya ɗago da wuyan hannunsa yana duban diamond wrist watch dinsa.
"Wataƙil mun makaro ne, amma ni abun da bangane ba Ina mutanan gidan ne? Babu kowa kodai sun bar gidan ne?" Zaid ne ya tambaya,
Zayn ya ce, "Ko dai sun canza gurin da za a yi meeting dinne?"
"Nafi tunanin haka, cos duka baifi karfe hudu da rabi ba akwai sauran time" A cewar Captain.
Mommy Turai ta ce, "Gaskiya bana tunanin sun canza wurin yin meeting din, ko a wurin birthday din Owais sai da Baba Obie ya ƙara jaddada mana a nan za'a yi, kuma ina ji a raina ba'a gama meeting din ba sai dai idan wani abunne na daban..."
"Bari na kira daddy na ji ina su ke ne..." Jazz ne ya faɗa tare da zaro wayarsa daga aljihu, har ya fara danna wayar kwatsam Idanunsa suka sauka akan rigar shaddar dake yashe kan floor..
Cikin sauri ya nufi rigar duk suka bi shi da ido, Ya zukunna tare da ɗaukar rigar ya kanga ta a hancinsa.
Dubansu ya yi fuskarsa da ruɗu ya ce, "Rigar daddy ce, na ji ƙamshin turarensa.." Maganar da ya yi ta jefa su a a ruɗani, Turai ta ce, "Hakan na nufin yana acikin gidan nan kenan! To amma ina suka shiga? Sannan meyasa ya cire rigarsa ya bar ta akan floor"?
Ta faɗa a rude, ɗan dafe kai Captain Yaseer ya yi, cike da rashin walwala ya dan ja da baya, juyawar da zai yi keda wuya idanunsa suka sauka akan dattijuwar dake a kwance kan doguwar sofa rai hannun Allah.
A firgice ya daka tsalle ya ja baya yana faman zare hazel eyes dinsa, labbansa na kerma ya furta, "Wa'inna hu min sulaiman wa innahu bismillah!Kuna ganin abunda nake gani kuwa? Wacece tsohuwar nan?" Gaba ɗaya ya bi ya ruɗe yayi zaton ba mutun bace.
Hankulansu a tashe suke kallon tsohuwar gaba ɗaya basu lura da ita a kan kujerar ba saboda sun bata baya shiyasa basu ganta ba, kuma Sofas din suna da yawa two sets ne.
gaba ɗaya sun razana da ganin ta, basu san wacece ita ba.
Ziyad ya ce, "Ko dai baƙuwa ce muka yi?" Girgiza kai Yaseer ya yi, "Bazai yiwu ba, bana tunanin mutunce, sai dai idan Aljana ce, ni hankalina bai kwanta da ita ba, jibarta fa ka ga ni.." ya faɗa yana nunata da yatsan sa dake ɗan kerma.
"Duk ƙasusuwa a jikin ta, kamar mai fama da cutar ƙanjamau..."
ya faɗa yana yamutsa fuskarsa..
Ta6e baki Zayn ya yi, "Na fi tunanin mutum ce, amma waya kawo mana bare a family dinmu? Bai kamata aga wannan halittar a gidan mu ba." A wulaƙance ya faɗa, kwata kwata basu damu da halin da take a ciki ba, har gwara justice da bai tanka ba shida Ziyad.
Jiki a sanyaye Turai ta nufe ta duk da tana jin fargaba, zukunnawa ta yi daga gaban sofa din ta ƙura mata idanunta, tsantsar tausayinta ne ya kamata ganin jinin dake ɗan ɗiga daga hancin ta, gashi a wahalce take jan numfashi, ta fahimci bata acikin hayyacinta sai sambatu ta ke yi ƙasa ƙasa.
A hankali ta shafa forehead ɗinta da tafin hannunta ganin fatar wurin ta yi tamoji tamoji ta yi duhu kamar ta ta6a ƙonewa.
"Ina tunanin bata da lafiya, amma wacece ita? Wa ya kwantar da ita anan? Ta ya za'abar majinyaciya ita kaɗai batare da likitan da zai duba ta ba.." Ta faɗa cikin nuna tausayawa.
Yaseer dai tsoronta Yake ji sai faman zazzare eyes ɗinsa ya ke yi.
Twins ma duk sun sha jinin jikin su.
"Jazz zo ka dubata pls, mu taimaka mata kada ta rasa ranta.."
Matsawa Jazz ya yi gaban kujerar ya zauna saman hand sofa din, kafin Ya daura tafin hannunsa saman kan Khala a hankali ya kamo tafin hannunta ya ƙura mashi ido yana nazari akan ta, har wuyanta ya shafa.
"Jazz baka da hankaline! Kasan wacece ita da zaka ta6ata, salon ka kwaso mana cuta?"
Zayn ne ya faɗa da tsawa, Ko kula sa Jazz bai yi ba hankalinsa na akan Khala da tausayin ta ya fara kama shi.
Ziyad ya ce, "Koma wacece ita ina ji araina mutunce ita, dole akwai wanda ya kawota gidan nan, abunda yakamata mu yi shine mu tuntu6i baba a waya muji ina suke, in ya so sai mu tambayeshi game da ita..."
Ya ƙarasa maganar tare da zaro wayarsa daga aljihu ya shiga kiran layin Baba Obie.
Almost 5 times tana ringing ba'a yi picking ba (rashin sani yafi dare duhu)
"Wayar na shiga amma ba a ɗauka ba" ya faɗa yana dubansu.
Cikin sauri Captain Yaseer Ya zaro wayarsa daga aljihu ya kira layin daddynsa His excellency Abdul Razak..
Shima Almost 5 times tana ringing ba'ayi picking ba..
"Me zai hana mu je part din baba? Nasan ba su wuce can"
Zaid ne ya faɗa, basu tsaya 6ata lokaci ba suka dunguma izuwa sashen baba Obie ya rage saura Turai tare da Jazz dake duba momma.
Tunkan su ƙarasa suka hangosu zazzaune bakin door room din baba Obie sun raku6e jikin ƙofar, kwata kwata basu motsi sai numfashin su dake fita da ƙarfi, ga wani bugun barazana da zuciyoyin su ke yi, fuskokin su sunyi sharkaf da jirwayen hawayen su, idanun su sun kaɗa jawur sun kumbura tamkar yaji ya shiga cikin su.
Wani irin faduwar gaba suka ji, lokaci ɗaya yanayinsu ya sauya zuwa tsantsar tashin hankali da fargaba, a hanzarce suka ƙarasa gabansu kusan atare suka zube kan gwiwowinsu suna fuskantar su.
Cike da tashin hankali suke tambayar su meya faru da su? Meya sanya su yin kuka? Meke damun su?"
Hakika sun razana da ganin halin da iyayensu suke a ciki, basu ta6a ganin rauninsu irin na wannan ranar ba, ko magana basa iya yi sai dai suka dinga bin su da raunatattun idanunsu da suka galabaita.
gaba daya gumi ya wanke jikin su kamar babu iska a wurin.
Magiya suka dinga yi masu akan suyi masu magana su fada musu meke faruwa amma babu alamun zasu tanka musu.
Labbansu duk sun faffashe sakamakon cizon su da suka dinga yi cikin fitar hayyaci, sunyi zugudum kamar hotuna, daga wanda ya zabga tagumi da hannayensa biyu, sai wanda ya langwa6e kansa jikin door room din baba Obie, Sir Mubarak ya dage sai tauna farcensa ya ke yi da hakoransa baima san yana yi ba, tsabar damuwa ne da fusatar zuciya ke addabarsa..
"Inna lillahi wa'inna ilaihirraji'un! Na shiga uku! Daddy! Uncles! Meke damunku? Meya saka ku zubar da hawayenku? Baba Ya mutu ne?" Ziyad ne ya faɗa arude tare da tallabo fuskar Senate da tafukansa yana kokarin tursasa masa don yayi maganar.
"Dan Allah ku faɗa mana abunda ke faruwa? Hankalinmu ya tashi da ganin halin da kuke aciki, pls daddy ka faɗa min! Me ya jefa ku a halin da kuke aciki ? Ina baba Ya ke? Me kuke yi a kofar dakin sa, ko dai ya mutu ne?"
Cikin shesshekar murya Captain Yaseer Ya fada tare da dafa kafadun daddynsa da tafukan hannayensa.
"Uncles pls, kuyi mana magana, dan Allah kuce wani abu! Gaba ɗaya bakwa acikin hayyacin ku, yanayin ku ya nuna kuna acikin mawuyacin hali na damuwa, idanunku sun kumbura alamar kunsha kuka, wai meya faru ne??" Zayn ne ya fada yana rarraba idanunsa akan fuskar Hateem da Sharafudden, kusan atare suka sadda kawunansu ƙasa batare da sun tanka ma shi ba!
Zaid Ya ruƙo hannayen mai girma Sharafudden acikin nashi cikin raunanniyar murya ya furta, "Mun shiga uku, pls Uncle ku yi mana magana ko hankalinmu ya kwanta, wai meke damunku ne? Gaba ɗaya kun raunata babu wani mai walwala acikin ku? Idan baba Ya mutu ne ku fada mana..."
Cikin sanyin jiki Justice Ya tallabo fuskar mahaifinsa, "Dad ka yi min bayani pls, meke damunku ne huh? Meya faru? Ni ban taba ganin ku a mawuyacin hali irin na yau ba, dan Allah daddy ka fadamin kada zuciyata ta buga don bazan juri ganinku acikin wannan halin ba.."
ba irin magiyar da basuyi musu ba amma shiru basu tanka musu ba."
hakan ya ƙara jefasu cikin damuwa har ta kaiga sun fashe da kuka, suma ubannin nasu wani sabon kukan ne ya 6alle musu, aka rasa me lallashin wani, suna kuka suma suna kuka yayin da suke fuskantar junansu, Hakika zuciya ta karaya, tayaya zasu yi ma ƴa'ƴanasu bayanin abun da kakan su yake aikatawa? Wani hali zasu shiga idan suka ji? Ya zasuyi da rayuwar su? Yaran da basu san wani abu wai shi tashin hankali a rayuwarsu ba, tun da suka taso nasara da gatanci suka sani basu taba neman wani abu sun rasa ba, wannan ne karo na farko da zasu fara fuskantar mummunar jarabawar rayuwa mai wuyar gaske, amma duk bama wannan ba tunanin da yafi tsaya musu a ƙahon zuciya ya'yansu da suka rayu tsawon shekara da shekaru cikin uƙubar rayuwa har suka mutu basu san su wanene iyayen su ba? Ba don addu'o'in da suke ta nanatawa a cikin zukatansu ba, da tuni zuciyarsu ta daina bugawa saboda depresssion din dake barazanar yi musu illah.
A lokacin baba Obie Ya daɗe da yin shiru, shiyasa suka ƙara rikicewa basu san awani hali ya ke a ciki ba yana a raye ko ya kashe kan shi!
_______________________________✍️
"Jazz meke damun ta? Ko ta suma ne uhm? Mom Turai ce ta faɗa tana duban shi, yayin da ya ke tsoma mayafin khala da ya cire a cikin bucket mai ɗauke da ruwan sanyin daya ɗebo, A hankali ya ke matsa mata shi a saman kanta da wuyanta har izuwa kafafun ta.
Girgiza mata kai ya yi, "Bata suma ba, but she needs medical attention, da bukatar a yi gaggawar kai ta asibiti..."
Har ta buɗe baki zata yi magana kenan, Unexpected suka jiyo sautin koke koke da sallallamin da ake yi..
A sukwane suka miƙe tsaye suna duban hanyar da suke tsammanin daga nan koke koken ke fitowa kafin suyi wani motsi, ƴan aikin gidan suka shigo agurguje cike da tashin hankali suke ambaton Inna lillahi wa'inna ilaihirraji'un! Sai faman yarfa hannayensu su ke yi sautin muryoyin su ma daƙyar su ke fita saboda tashin hankalin da suke a ciki..
Har suna haɗa baki ita da Jazz gurin tambayar su meya faru?
"Wayyo Allah! Inna lillahi! Aunty Saratu! Tana a ɗakin Hajjaty rai hannun Allah kwance cikin jini, dan Allah ataimaka kada ta rasa ranta, wlh bamu san meya faru da ita ba, fuskarta duk ta 6aci da raunuka.." Kaitsaye maganganun ƴan aikin suka dira acikin kunnuwan kowa dake a bangaren kasantuwar da ƙaraji suke yin maganar.
Lokaci ɗaya hankulansu da ya gushe suka dawo jikin su, arude suke nanata sunan Saratu da suka jiyo a cikin kunnuwan su.
Especially twins wadanda tuni sun jima da barin gurin, duk da rashin kuzarin Jikinsu hakan bai hanasu miƙewa ba gaba dayansu suka baro part din baba Obie tsabar saurin su ƙarasa har suna bangaje junan su, kafin su iso falon tuni Jazz da Turai da yan aikin sun nufi ɗakin Hajjaty aguje.
Tunkan su karasa ga dakin suka soma jiyo koke kokensu,
Lokacin da suka shiga dakin kusan suman tsaye suka yi, sa'ilin da idanun su suka sauka akan fuskar hajiya Saratu, Turai ce ta kwantar da kanta saman cinyoyinta sai kuka ta ke yi kamar ranta zai fita twins ma kukanne ya balle musu..
Cikin raunanniyar murya Hateem ya furta. "Who's she?" Ya fadi hakanne saboda bai gane fuskar wacece ba, sakamakon jinin da ya wanke fuskarta.
Cikin shesshekar kuka abla tace"Aunty Saratu ce, bamusan me ya faru da ita ba, ni ce ɗazu na zo duba jikin hajjaty da bata da lafiya, ina shigowa na taras da mutun kwance a ƙasa cikin jini ga glass ya sossoke fuskar ta, wlh na yi zaton hajjaty ce amma dana duba ta dakyau sai nagane aunty Saratu ce saboda launin fatarsu ba ɗaya ba, na yi mamakin ganinta adakin hajjaty saboda bata ta6a takowa sashen yan aiki ba...."
Ta karasa maganar tana matse kwallar ta, hankalinsu idan ya yi dubu toh ya tashi, abin da ya ruɗar dasu shine meya kawota dakin yar aiki? Meya faru da ita?" Wa kuma yayi mata wannan ɗanyan aikin? Saboda sun gane buga kanta aka yi a jikin mirror tun da gayanan sunga madubin ya zube ƙasa..
"Ina ita wadda ke ɗakin??" Zayn ne ya tambaya a fusace fuskarshi sharkaf da hawaye, amsa mashi suka yi da basu ganta ba.
Sharafuddeen bai tsaya bata lokaci ba, ya yi hanzarin matsawa ya sanya hannayenshi biyu ya ciccibi hajiya saratu ya daura akan kafadarsa ya juya a gaggauce ya fuce daga dakin su twins dake ta kuka kamar ransu zai fita gani suke kamar hajjaty ce ta yi mata haka, dama sun tsaneta basu kaunarta, bayin Allah sai bin bayan sharafuddeen suke yi kamar jela.
Sune har bakin Entry Hall, Yana fitowa da ita ya nufi Escorts dinsa dake sintiri agaban motocinsu, tunkan ya karasa ya daka musu tsawa a rude suka dube shi da hannu ya yi masu alamar su buɗe mashi mota, a hanzarce suke bude backseat na daya daga cikin motocin su, jiki na bari zayn ya fara shiga ya zauna yana ta kuka, bayan daddy Sharafudden ya shigar da ita cikin motar, zaid ya shiga suka saka ta atsakiyar su.
gaba daya suka kankameta suna cigaba da kuka.'
In weak Voice Prime minister Ya ce, "Twins ku daina kuka, baku ga halin da take a ciki bane? Addu'arku take bukata, kuyi hakuri In sha Allah zata ji sauƙi, kuma koma wanene yayi mata aika aikar nan zamu kama sa ne sannan ya karbi hukuncin abun da ya aikata" ya fada yayin da yake datse murfin motar, kalaman shi sun ɗan tausasa zuciyar su..
Umarni yaba escort din da zaiyi driving dinsu da ya kai su Asibitin Villa, batare da 6ata lokaci ba escort din ya shiga driver's seat ya zauna tare da yiwa motar key ya ja ta da matsakaicin gudu ya bi titin da zai fitar da shi daga estate din..
Motar su bata kaiga fita daga estate ɗin ba, sai ga Jazz ya fito kafadarsa dauke da Khala, gaba daya hankulansu suka ƙara tashi ganin ta, sam sun manta da ita saboda gushewar da hankalinsu ya yi, umarni Sharafudeen yaba wani Escort din da ya buɗe wata motar, bayan Escort din ya buɗe, Sharafudeen ya kar6i khala daga hannun Jazz, a mazaunin baya na motar ya shigar da ita cikin kulawa ya zaunar da ita tare da jingine kanta jikin seat, basu barta ita kadai ba jazz ne ya shiga cikin motar ya zauna daga gefen ta Hajiya Turai ma ta shige ta zauna cike da fargaba, Jazz ya daddafe ta a jikin shi duk da baisanta ba ya ji ajikin shi tana da alaka da baba Obie..'
Akan Idonsu Motar ta fuce daga eatate din tabi bayan motar da aka dauki hajiya Saratu tare da wasu motocin na securities..
Acikin Mota Twins sai magiya suke yi ma mommynsu, akan kada ta mutu ta barsu ta taimaki rayuwarsu, Idan suka rasa ta basu san ina zasu sa ransu ba, kwata kwata bata acikin hayyacin ta, bata san ma wake akanta ba..
Kafin su karasa Villa, Mai girma Sharafudeen ya kira gimbiya malika a waya bayan tayi picking ya sanar da ita game da zuwan su Hajiya Saratu ta ce ai su har sun shirya zasu dawo nan saboda baƙin da suka yi sun tafi.
Ya ce mata ba wannan ba yanzu, Su aje maganar dawowa Estate, so yake ashirya medical team din da zasu duba lafiyarsu kafin su ƙaraso, Jin wannan maganar ya ɗaga hankalin ta dama tunda suka fara wayar ta ji muryarsa kamar babu walwala, a ruɗe ta ce, "Meke damun ta ne? Ko bata lafiya ne? Amma ba ɗazu muka rabu da ita lafiya agurin celebration ba?"
Bata kare maganar ba yace"Eh amma ba ita kadai bace, tana atare da yar'uwar mu, ki yi abunda na ce pls, a tabbatar an duba su yadda ya dace su, zamu yi magana anjima." badan ta so ba, muryarta da damuwa tace, "Toh shikebnan, Allah ya kawo su lafiya, ka kula min da kanka." da ga haka su ka yi sallama.
Gaba dayan su suka koma falo, anan suka zauna kan carpet din da ke atsakiyar kujerun falon, bayin Allah daga wannan sai wannan, kuma ransu ya 6aci da abunda aka yiwa Saratu, sunyi mamaki suna a mawuyacin halin nan a haka aka samu wani mara imanin ya zagaya ta baya yaje ya cutar da ita, damuwarsu ta ƙara ninkuwa.
Har lokacin sunƙi sanar da ya'yan nasu meya faru! Sunyi magiyar har sun gaji sunyi shiru sun zubawa sarautar Allah ido.
Yan aikin gidan kuwa bayan da aka tafi da hajiya Saratu, jiki asanyaye suka koma part dinsu, suna taya juna alhinin abun da ya faru da ita, su abunda da ya daure musu kai me ya kawo hajiya Saratu dakin Hajjaty? Bayan basu jituwa ko kaɗan! Ina kuma hajjatyn take? Tayaya akai madubin dakinta ya fashe har ya sossoke fuskar Aunty saratu?
Sun rasa wa zasu zarga akan lamarin nan! Sun san da wuya in Hajjaty zata iya yin hakan, Gaba ɗaya suna zargin wani mummunan abun ne ke faruwa da ahalin gidan cos sun lura ma gaba daya mutanan dake gidan babu kwanciyar hankali atare da su.
Shin Ya labarin Chief Owais? Bawan Allah Tun lokacin da suka daina jiyo kururuwar da baba Obie ke yi jikin shi na 6ari ya zame jiki daga cikin su ya kewaya ta bayan part dinsa koda ya ga ɗayar kofar a kulle take, sai ya matsa daga gaban katafariyar glass window din dakin baba Obin dake a bayan, nan ma ya taras da ita a garƙame ya yi ta kokarin balle glass din cikin shesshekar kuka yake kwala masa kira yana fadin baba ka buɗe min kofa, kada ka kashe kanka baba, idan ma kana tunanin mutuwa ce mafita agare ka, to kadaina, kada ka mutu ka bar ni, in ka yi min haka baka yi min adalci ba baba..."
Shiru bai amsa mashi ba, dunkule hannayensa ya yi yasa karfi yai ta dukan glass din duk ya raunata yatsunsa amma windown bata buɗe ba saboda quality dinta, dole sai idan ta ciki aka buɗe ta, ko aka yi amfani da remote control din ta, da takaici Ya ishe shi ya dinga bubbuga goshinsa jikin glass din dama akwai tsohon rauni a gurin nan take ya fama sa wani azababben ciwon 6arin kai ne ya fara addabarsa, lokaci ɗaya ya fara ganin biji-biji juwa ta ɗebesa nan take ya yanke jiki ya faɗi ƙasa, bai ƙara sanin inda kan shi ya ke ba, bai mutu ba kuma bai suma ba, sai dai bai san inda kan shi ya ke ba, komai dake faruwa a cikin gidan bai sani ba haka zalika babu wanda ya yi tunanin ina ya ke saboda hankalinsu ba a kwance ya ke ba... (🥺)
___________________________________
Damuwa ce ƙarara akan fuskar Unaisah, ta rasa ina zata sa ranta taji dadi, tayi jiran dawowarshi har ta fara gajiya da jiran shi, tana ta kiran layin sa baya picking.
Bayin Allah har sun kammala shiryawa tun da rana da ya ce su shirya zasu yi celebration na birthday dinsa a gida, bayan tafiyar sa Aunty Ummi ta shiga da su home beauty saloon dinsu tayi masu hadadden gyaran gashi da gyaran jiki, after sallar la'asar suka yi wanka, kowaccensu ta ɗauki wanka na mutunci, Shi kadai suke jiran dawowarshi, Chefs har sun kawo masu ƙaton Cake mai hawa bakwai komai ya kammalu sai dai babu Chief babu alamarsa.
Hakan ya jefa su acikin damuwa, fitowa tayi daga bedroom dinsu jikinta a sanye da fitted gown ta swiss cord lace, gown din tabi shape din jikinta kayan sunyi mata kyau sun fito da kyakkyawar surarta, tana tafiya jikinta na girgiza sautin chunky heels din kafafuwanta ya cika kunnuwansu, kwas! kwas!!
Hannunta ɗaya ruke da head din kayan yayin da dayan hannun yake a ruƙe da wayar ta, idanunta na akan screen din wayar, da take pressing, light make up ne akan fuskarta.
Gyaran gashin da ummi tayi mata fishtail braids ne ya ƙara fito da kyawunta, kitsone masu gwa6i guda biyu wutsiyarsu ta sauko ta gaban kirjinta har kan stomach dinta, ga wani daddan fragrance dake busowa ta jikin ta, fuskarta a yamutse ta nufi cikin falon.
"Unaisah har yanzu bai ɗaga kiran ba?"
Ɗagowa tayi tare da kallon ummi da tayi maganar, suna a tsaye gaban table din da aka ɗaura Cake.
Ummi tana sanye da atampa Chiganvy gold riga da skirt sun kama jikin ta, tudun hips dinta ko cup aka ɗaura sai ya zauna, ta kashe daurin kallabi, Batool kuma kalar kayan Unaisah ne a jikin ta, hatta takalmansu iri ɗaya, Ummi taso ta bambanta musu hair style din amma ta nace ta ce itama irin na Unaisah take so saboda bata son Unaisah tafi ta kyau, amma fa sunyi kyau su dukan su, sun wanku kamar ya'yan Minister of finance..
Girgiza kai ta yi da damuwa ta ce, "Har yanzu bai ɗaga kiran ba, ni dai hankalina bai kwanta ba, ina ji araina kamar ba lafiya, saboda bai saba min haka ba, har message na tura mashi bai mayar min da reply ba.." tana magana tana yamutsa fuska..
Ummi ta ce, "Anya lafiya kuwa? a sanina da chief bai sa6a alkawari, amma ko ya akai shiru bai dawo ba, har an kusa fara kiran sallar magrib?"
Ta tambaya da damuwa akan fuskarta, Batool duk tafi su shiga damuwa duk ta yi sukuku da ita..
"Har daddy na yiwa magana yace shima ya kira shi ba sau ɗaya ba ba sau biyu ba amma bai daga ba, wlh ji nake kamar in bi shi cikin estate din.." ta faɗa tana zum6ura ƙaramin bakin ta..
Murmushi Ummi ta yi, "Allah ya huci zuciyarki gimbiyar Chief Owais, da girman kujerar ki, mu yi hakuri mu jira shi, may be kafin mu kammala sallar magrib ki ga ya dawo gidan..."
Bubbuga kafafunta ta yi akan floor da dan murmushi akan fuskar ta, alamar ta ji dadin kalaman Ummi, "Haba Aunty Ummi, in har sai lokacin zai dawo ni dai bai kyauta min ba Allah.." Ta faɗa tare da goya hannayenta akan kirjin ta.
"Calm down your mind his princess, nasan me kike yi mawa, wato kada kije yin alwala make up ɗinki ya goge, toh kada ki damu kina da ni, zan canza maki wani make up din ne.."
ajiyar zuciya ta sauke tare da kallon Batool da ta yi shiru idanunta sun ciko da ƙwalla, kwata kwata hankalinta ba ya akan su.
"Sis are you okay?" In a cool voice ta ce, "bana jin dadin zuciyata, ji nake kamar wani abu na faruwa da Chief din mu.."
Dafa kafadarta Ummi ta yi, "Na fahimci kun damu sosai, nima na damu da shi, but pls ku kwantar da hankulanku, in sha Allah ba abunda ya faru da shi, zai dawo gida lafiya har ma mu yanka cake atare da shi, wataƙil wani uzurin ne ya ruke shi."
murmushi suka ɗan saki badan hankalinsu ya kwanta ba..
A fakaice Ummi take satar kallonsu daga ƙasa har sama, ta daɗe bata ga kyawawan matasan ƴan mata irin su ba, tana yaba kyawun su sosai, Allah yayi halitta masha Allah tabarakallahu ahsanul khalikin, A ranta take fada, kamar yadda take mamakin kyawunsu suke burgeta suma haka take burgesu, burinsu suma suyi irin body dinta, especially Unaisah in dai zata kalli Aunty Ummi sai tayi fatan dama ita ke da dirinta.
"Ku matso mu yi hotuna kafin ya karaso" Matsawa su ka yi gefe da gefenta suka tsaya, yayin da cake table din ke agabansu ta saita su da camera wayarta ta fara ɗaukar su zafafan hotuna style kala kala ta dinga nuna masu yadda za su yi, bayan sun gama ta nuna masu hotunan, koda suka gani ihu suka sanya suna santin su saboda kyawun da su ka yi a pics din..
"Aunty Ummi ki turamin hotunan In turama Mommy da Aunty Aneeleeh su gani.."
Ta faɗa tana kallon fuskar Ummi, walwalarta ce ta dauke kamar bata taba yin dariya ba.
Ta fahimci indai zata yi mata maganar Benazir ko Anila bata farin ciki, shiyasa ta kasa faɗa mata tasan tarihin rayuwarsu.
"Sai dai ki ɗauki wasu hotunan keda Batool ki tura masu amma banda nawa.." ta fada fuskarta a ɗaure ba annuri..
"Meyasa Aunty Ummi?" Batool ce ta tambaya,
"baku ga babu mayafi a jikina ba? Bai dace a ganni haka ba koda a hotone"
Ta ƙarashe maganar tare da miƙewa ta juya ta nufi Up, bin ta da kallo Unaisah tayi harta hau kan stairs ta ɗan dakata da yin tafiyar, ta rasa meyasa take ji aranta kamar sakacin su Benazir ne ya ja ta rasa babynta, Zuciyarta ce ke tunzurata akan manufarta shiyasa ko sun kira bata ɗaga kiran su, saƙonnin da suka tura mata sun kai ɗari amman ko ɗaya bata buɗe ba balle tasan me suka rubuta a ciki, Shureim ne kaɗai idan ya yi mata sako take dubawa saboda har yanzu akwai ƙaunarsa a cikin zuciyarta.
Har bayan sallar Isha'i ba Chief ba labarin sa, hankalinsu ya tashi matuƙa, saboda damuwar rashin dawowar shi da tayi masu katutu acikin zuciya, hakan yasa bacci ya ƙauracewa idanunsu, hankalinsu ya ƙi kwanciya, gani suke kamar wani abunne ke faruwa da shi, a falo suka raba dare gaba ɗayan su harda Taj, ko cake din da aka kawo masu basu ci ba.
Lokacin da bacci ya fara cin karfin su, Ummi da Batool har sun fara gyangyaɗi, Unaisah dai ba alamun bacci atattare da ita, ta kasa ta tsare sai Chief ya dawo.
"Ummi ku tashi kuje ku kwanta, dare yayi sosai" Taj ne ya fada yana duban su..
Sun langwa6e kansu jikin Sofa, girgiza kai Ummi ta yi, "Bana tunanin zan iya runtsawa in har Chief bai dawo ba, wlh na damu Boss, ace ko waya baya picking?"
Ta faɗa fuskarta a yamutse.
Da damuwa akan fuskarshi ya ce, "Ku yi hakuri kuje ku kwanta, in sha Allah ba abun da zai faru da shi, bafa wata uwa duniya ya tafi ba, yana agidan grandpa dinsa dake a cikin estate din nan, may be yan uwansa ne suka ruƙe shi, amma nasan in sha Allah da asuba zai dawo nan din.."
"Amma in har lafiya, meyasa munata kiran sa baya picking? bayan shi da kan shi yace mu shirya idan ya dawo zamuyi celebration a gida.."
"At least in ma bazai dawo ba, yakamata ya kira a waya ya faɗa mana.."
"Ummi, kuyi masa uziri, Allah kadai yasan me ya tsayar da shi, a sanina da Chief bai cika mantuwa ba, mutunne mai son cika alkawari, sai dai bansan meyasa bai dawo ba, kuma bansan abinda ya hana shi kiran mu ba, amma mu yi hakuri mu jira zuwa gobe.."
Ummi ta ce, "Ni ba rashin dawowar shi bane ya ɗaga min hankalina, kawai muna so muji in yana lafiya sai hankalin mu ya kwanta.."
Dakyar Taj ya samu ya lallashe su har suka hakura da jiran na shi kowa ya nufi bedroom dinsa don ya kwanta.
~______________________________~
ELDERS🔥
Duhu ne ya mamaye ko'ina, ba zaka iya ganin komai dake a kewayen wurin ba.
Yayin da yake a tsaye cikin shiga ta doguwar riga baƙa ta sauka har ƙasan kafafunsa dake a sanye cikin bakaken takalma na fata, Ya lullu6e sumar kansa da hular rigar tasa, baka iya ganin komai na jikinsa in ba ƙwayar idanunsa ba, hatta fuskarsa a lullu6e take da baƙin takunkumi, yayin da ya ruƙe sandar sa a hannun shi na dama.
Tun daga yanayin tsayuwarsa zaka fahimci babu ƙoshin lafiya atare da shi, akwai rauni da karayar zuciya atattare da shi..
Unexpected hasken wutar candles dake a kewayen wurin ya soma kunna kansa, hakan ya bani damar ganin sauran bil'adaman dake a cikin katafaren ɗakin, har saida na firgita da ganin wasu irin dogayen mutane masu ƙirar ƙarfi a jikin su, gaba dayansu suna a zaune kan armchairs din dake a kewaye da shi.
Shigar jikinsu bata da bambanci da tashi, bakaken dogayen riguna ne a jikinsu, sun rufe kansu da hulunan rigunan, kowannansu yana a ruke da sandar shi ta alfarma, gaba daya sun sadda kansu ƙasa.
Hankalinsu ya dugunzuma ainun, basu ta6a shiga mawuyacin hali na farga irin wannan ranar ba, tun da Elder ya fada musu abun da ya faru da shi hankulansu sun tashi matuƙa, wlh sun kaɗu da jin asirin Elder ya tonu, dole su razana saboda basu taba tsammanin asirin shi zai tonu cikin sauƙi ba, shi da yake shugaban su, ina ga su na ƙasa da shi.
Abun da ya daure musu kai ta yadda har sihirin shi yaƙi tasiri a lokacin da khala take tona mishi asiri, bayan haka sun yi mamakin tabya akai ta rayu bayan Elder ya tabbatar musu da mutuwar ta❓
A ƙalla Elders din dake a dakin sun kai su goma sha ɗaya, gaba daya sun tattara nutsuwarsu sun mayar da hankulansu akan Elder da ke kora musu jawabi cikin harshen su na matsafa..
"Haƙiƙa yau na ji kunyar da ban ta6a jin taba a rayuwata, nasan da zuwan wannan ranar amma ban ta6a zaton zata yi silar da zan ji danasani atare da ni ba, hankalina ya tashi, zuciyata ta karaya, fargaba da tsoro sun mamaye zuciyata, bawai don asirina ya tonu ba, sai don halin da na jefa rayuwar ya'yana da suka aminta da ni, nine silar ɗaukakarsu, nine ƙashin bayansu kuma jigo sannan jagora na rayuwar su, kuma nine abu mafi soyuwa agare su, kamar yadda nima na ɗauke su dangina, bugun zuciyata, sune nake gani in ji dadi a raina, sune farin cikina kuma jin dadin rayuwana, amma a yau da asirina ya tonu a gaban idanunsu, na muzanta na ji kunyar da banta6a jin ta ba a rayuwana, na karaya da ganin yadda suke kukan bakin ciki saboda zaluncin dana aikata ma ya'yan su da kuma ha'intar su da na yi a matsayina na uba a gare su, na cuce su na cuci kaina, na kuma cuci ya'yan su dana sadaukar......."
Tun da Elder ya fara maganar sauran Elders din suka kafe shi da idanunsu da suka cika da tsantsar al'ajabi da rudanin maganarsa, gani suke kamar mafarki ne ba gaske ba, jin maganganun da suke fitowa daga bakin shi, asanin su da Elder mutunne mai taurin zuciya, bai ta6a karaya ba, kuma bai ta6a danasanin abunda ya ke aikatawa ba sai yau? Abun ya ɗaure musu kai tamau har sun fara kokwanton anya Elder din su ne? Ko dai musayarsa aka yi musu? Taya ya karaya cikin sauki ya ajiye makaman yaƙinsa?" Gaba daya sun ruɗe matuƙa.
"Harshe na bazai iya misalta muku irin kuncin da na ji a cikin zuciyata ba, naji bakin ciki da takaici mara misaltuwa, na ji radadin da yafi na ƙunar wuta zafi acikin zuciyata, nayi fatan ace na mutu kafin zuwan wannan baƙar ranar"
Ya faɗa cikin raunanniyar muryarsa, a hankali ya dafe saitin zuciyar shi da tafin hannunsa.
Kafin ya ɗaura da cewa, "Jikana dana fi kauna yau da kansa ya shaƙi wuyan rigata kamar zai doke ni, mutuncina ya zube a idanunsu, na yi musu mummunan tabon da har bayan ransu bazai ta6a goguwa ba, na yi zaton tsafina da dukiyata zasu sama min komai na duniyar nan, ban ta6a zaton akwai ranar da tsafina bazai amfane ni ba, a yau na raina karfin sirihina saboda na gane cewa shima tsafin ba gaskiya bane yaudarar kaine, akwai wanda yake da iko da masu tsafin da shi kanshi tsafin wanda idan ya so cikin daƙiƙa zai kar6e sihirin daga gare mu, kamar yadda dangina suka mutu a fagen fama, lokacin da maƙiya suka kawo mana farmakin bazata, mu tsafi gare mu sukuma basu da wannan tsafin amma a haka suka ci galaba akan dangina suka kashe kowa baifi mu shida muka rage ba a lokacin, In har tsafi bazai hana matsafi fuskantar mummunar kaddara ba, kuma bazai hana matsafi mutuwa ba, me hakan ke nufi....."? Ya karashe maganar cikin raunanniyar murya yana duban Elders din dake sauraron shi ..❗
"Bamu gane abunda kake nufi ba Elder! Kalaman ka suna nema su rikita tunaninmu, mun rasa gane ina ka dosa! maganganunka sun jefa mu a ruɗani..." Jan le6e ne ya yi maganar..
"Ka gafarce ni Elder, amma na yi mamakin yadda kayi saurin karaya saboda kawai asirinka ya tonu a gaban ya'yanka? Kada ka bamu kunya mana, Faduwa ba taka bace Elder! Ba'asan Elder da rauni ba, kuma ba'a san su da saurin karaya ba, a sanin mu da kai jarumin namiji ne, wanda ba'a halicci zuciyarsa da imani ko tausayi ba, kaine kake ƙarfafa mana gwiwa akan karmu kuskura mu bari zuciyar mu tayi raunin da zamu ji tausayin wani ko mu karaya.." A cewar Jan Ido...
Da kakkausar murya Jan Wuya ya ce, "Ni kuma baka ta6a bani kunya irin na yau ba Elder! Ina hankalinka da tunaninka suke? Ina dakakkar zuciyar ka take? Ina izzarka da zaluncinka suke! Kaine fa dodon dake tsoratar da wasu Yau kuma kaida kanka ka tsorata saboda asirin ka ya tonu a gaban ya'yanka uhum?"
Ya fada rai a 6ace, "kada ka bari son ya'ya ya rufe maka ido har ka yi abin da zaka yi danasani Elder! Idan ma kana tunanin ajiye kambun zalunci ka ne to ka daina! Saboda ka riga da ka makaro Elder! Tubanka bazai kar6u ba Elder saboda tarin ɗumbun zunuban da ka aikata, Koda ka shiryu hukuma da al'ummar duniya bazasu kyale ka ba, mutuncin nan naka da ƙimarka zasu ruguje za'a cigaba da tsangwamarka kaida ahalinka har sai baƙin ciki ya yi silar barin ku duniya, ka tuna kana da maƙiya kaida ya'yan ka, me kake tunanin zai biyo baya idan suka ji abunda ka aikata? Zasu yi amfani da wannan damar ne gurin cuzguna muku!"
Ya faɗa da kakkausar murya hadi da dunƙule yatsunsa,
"Kuma idan hukuma ta damƙe ka sai ka yi danasanin zuwanka duniya saboda azabtarwar da zasu yi maka, bayan haka idan mutuncin ka ya zube, zaka tashi daga dattijon arziki ka koma ƙasƙantacce, mugu, kuma tantirin ɗan ta'adda a idon jama'a, za'a cigaba da aibata ka ne..."
Ya faɗa yana sakin dariyar shaƙiyanci da alama shi ko a jikin shi bai damu da halin da Elder ya ke a ciki ba, shiru Elder ya yi bai tanka masa ba, hakan ya bashi damar cigaba da yin maganarsa, "Yanzu ya rage naka Elder, ka zauna kayi tunani kafin ka yanke shawara, har yanzu muna da damar da zamu farfaɗo da gidan kurkukun ƙaddara, ka kashe kowa naka da ya san sirrinka, mu cika sharuɗɗan allon tsafin mu, a ganina ba dole saida Iyalanka zaka cigaba da rayuwa ba, kabar kowa naka, mu canza sheƙa...."
"Aminina, ni ina ganin mu ɗauki shawarar Jan Wuya, ita kaɗai ce mafitar dake gare mu, Ba zan so ɗaya daga cikin abunda ya faɗa ya faru da mu ba, ina jiye mana tsoron kalubalen da zamu fuskanta, ni bazan baka shawarar ka kashe ya'yanka ba, amma mu yi nesa da duniyar mutane, inda babu wani mahalukin da ya isa ya tunkare mu koda ba zamu cigaba da yin tsafin ba.." Jan Harshe ne ya yi maganar cikin tausasa murya...
"Har yanzu baku fahimce ni ba, Na lura wasu daga cikin ku basu damu da halin da nake a ciki ba..." ya faɗa yana jan numfashi gami da furzar da shi..
"Ba haka bane Elder, Mun fahimce ka, sai dai mu ba zamu miƙa wuya ba, koda kai zaka yi murabus daga kan muƙamin ka na Elder, Mu muna akan bakanmu, tsafi da rainon yara yanzu muka fara, babu wani mahalukin daya isa yasa mu ajiye makaman yakin mu..."
Wani Elder ne daga cikin su yayi maganar..
Jan Ido ya ce,"Fatan mu shine, ko da ka ji ka gani kana son yin murabus, Ka rufa mana asiri tun da mu bata kaiga faɗin sunayen mu, ko a cikin Elders ba kowa ta sani ba! na gidan kurkukun ƙaddara kaɗai ne ta sani, don haka muna rokanka alfarma ta ƙarshe, a matsayinka na shugabanmu wanda ya yi silar ɗaukakarmu, kuma ƙashin bayan Elders na gidan kurkukun ƙaddara, wanda har abada ba zamu manta da kai ba, saboda kayi mana halaccin da har abada ba zamu iya biyanka ba, mu a wurinmu ka fiye mana kowa na duniyar nan, bauta maka ne kaɗai bamu yi ba, amma ka cancanta har bautar ma mu yi maka..." Elder din da ya ɗauko maganar bai kaiga dire ta ba, sakamakon buga sandar da Elder ya yi da ƙarfi akan floor, tuni kowannansu yasha jinin jikin shi, magana yake son yi saidai ya kasa furta ta saboda raunin da zuciyar shi ta yi..
Daƙyar ya tattara ƙwarin gwiwarsa ya ƙarfafa zuciyar shi gurin furta, "Ni bazan ɗauki huɗubar ku ba, na riga da na gane kuskure na, na yi danasani kuma zan miƙa wuya a gare su, saboda inason su dauki fansar abunda na aikata ma ya'yan su, wataƙil ta silar hakan su yafe mini, kuma a shirye nake da in fuskanci ƙalubale in dai akan su ne..."
Ya ɗan dakata yana jan numfashi kafin ya ɗaura da cewa, " Kuma ina baku umarni! tun wuri ku ajiye makaman yaƙin ku, zaku iya guduwa ku nemi mafaka don ku kare kanku, amma kada ku cigaba da aikata miyagun ayyukan da kuke yi, yakamata ku dauki darasi a kaina, kuna gani dai sihirina bai amfane ni da komai ba...."
Bai ƙare maganar ba, Jan Wuya ya katse shi abun da bai ta6a yi masa ba, yana huci ya ce, "Ya isah haka Elder! Yakamata ka san mi zaka faɗi! Bai kamata kana tursasa mana akan mu bi ra'ayin ka ba, bayan kaine ka janyo mu cikin harkar, ka lasa mana zuma a baki, don haka mu ba zamu fasa ba, ba gudu ba ja da baya, kawai abunda muke so kayi mana shine karka kuskura ka tona mana asiri, tun da mu asirinmu a rufe ya ke, bata fallasa mu ba, kai tun da ka ji zaka iya haƙura saboda zuciyarka ta mutu akan son ya'yanka to ka je ka mika wuya, wanda ya ƙi ji ba zai ki gani ba....!"
Bai karasa maganar ba, Elders suka dakatar da shi ta hanyar daka mashi tsawa, yana huci ya ja baki yayi shiru badan ya so ba..
Cikin fusatacciyar murya Jan Harshe ya ce, "Ka fara wuce gona da iri Jan Wuya! Ka iya bakin ka! in ba so kake in canza maka kamanni a gurin nan ba, tun kan aje ko'ina har ka fara yi mashi magana da tsawa! Wanene kai? Bana tunanin ko darajar takalman ƙafarsa ka kai, kai din ba bawansa bane da ya ɗaukaka ya baka muƙami? Zaka iya biyansa abunda ya yi maka ne?"
Ya faɗa a tsawace yana kallonshi, Maganar Jan Harshe ta ƙona masa rai, Zuciyarsa ta zo wuya, har wani gurnani yake fitarwa saboda 6acin rai..
"Koda Elder ya aje muƙaminsa hakan ba yana nufin ya zama abun wulaƙantawa a gurin mu ba, har abada shine Elder na kurkukun ƙaddara, da izininsa komai ke faruwa, idan ya so cikin daƙiƙa zai ƙwace sihirin dake a jikin kowannanku! Ya kamata ku san da wannan, gargadi ne na yi maku, idan ma akwai wanda ke da wani mummunan kudiri a cikin ku...." Ya fada yana nuna su da sandar hannunsa.
Gaba daya suka sha jinin jikinsu hatta Jan wuya da yake ta tada jijiyoyin wuya saida ya sha jinin jikin shi saboda baida wani ƙarfi in har Elder ya kwace sihirin jikin sa, dama da shi ya ke taƙama, lokaci ɗaya suka sauko daga kan kujerunsu suka zube kan gwiwowinsu, kamar zasu yi mashi sujjada ƙiris ya rage goshinansu su ta6a ƙasa...
Atare suka hada baki gurin furta,
"dodon tsafi ya huci zuciyarka Elder, a gafarce mu Elder, tuba muke Elder, kanmu bisa wuyan mu, zamu yi biyayya agare ka, ka rufa mana asiri kada ka rabamu da sihirin da ke a jikin mu"
Mutum ɗaya ne bai zuƙunna ba a cikin su, Miƙewa ya yi daga kan kujararsa ya nufi Elder da ya sadda kanshi ƙasa, hannunshi da ya ruƙe sandar shi da ita sai kerma yake yi..
Dafa kafaɗunsa Jan Harshe ya yi da tafukansa, tun kafin ya yi magana Elder ya riga shi cewa, "Kada ka ce min komai, ka barni kawai, bazan canza ra'ayina ba, zan bar maka komai har muƙamina, amma ni bazan bar ƴa'ƴana ba, dame za su ji idan na gudu? Ya faɗa cikin rawar murya....
"Rashin ganina zai ƙara jefa su cikin mawuyacin hali, ni dai koda zasu tsane ni ne na ƙwammace in zauna atare da su..."
Kasa ƙarasa maganar ya yi saboda kukan da ya sarƙe makoshin shi.." Cikin raunaniyar murya Jan Harshe ya ce, "Bazan misalta maka tashin hankalin dana shiga ba, naji kwatankwacin raɗaɗin da ka ji acikin zuciyarka, kamar yadda kayi danasani nima na yi danasani aminina, kuskure ne mun riga da mun tabka shi!" Ya fada cike da takaici....
"Amma na ɗaurawa kaina alhakin kowani laifi da ka aikata saboda nine sila, lokacin da ka ƙyamaci abun a zuciyarka, ka nuna cewa ba dole saida tsafi zamu cimma burinmu ba, akwai wasu sana'o'in da zamu iya yi, ni ne na tunzuraka da cewa ba zamu ta6a samun abunda muke so ta cikin sauƙi ba sai ta wannan hanyar, kuma gadonka ne da iyayenka suka bar maka, bai kamata ka yi watsi da shi ba, a lokacin na matsa maka har saida ka dauki shawarata ka haƙa sihirin ka maida shi a jikin ka, wanda nayi imanin da ace babu Evils a jikinka ba zaka ta6a iya kashe rai ba...." Kifa kan shi ya yi akan kafaɗar amininsa sosai ya fashe da kuka mai tsuma zuciya..
Hakan ba ƙaramin ɗaga hankulan Elders ya yi ba, jin kukan Elder, tun da suke da shi ba su taba ganin ko da ɗigo na hawayen shi ba, tabbas sun razana sosai, faɗuwar gaba ta darsu a zukatansu..
"Ka yi hakuri na cutar da rayuwarka, na jefa ka a tsaka mai wuya, amma ka jure ka dauki shawarar Jan wuya, mu yi nesa da duniyar mutane, saboda ina jiye mana tsoron azabtarwar da zamu fuskanta agurin hukuma da kuma tozartar da zamu yi a idon duniya, in ya so idan muka gudu sai mu bar harkar tsafin mu tuba..."
A hankali ya ɗago da kanshi, idanunshi sun kaɗa jawur hawaye wasu na bin wasu akan kuncinsa.
Cikin shesshekar kuka ya ce, "Babu inda zan tafi, wannan karon, babu wanda ya isa yasa in canza ra'ayina, na riga da na yanke ma kaina hukuncin da na ga ya dace dani, zan miƙa wuya, kuma zan tuba, zan kuma kar6i kowani hukunci da za'a yanke min..."
Gaba ɗaya Elders din dake a dakin suka hau yi mashi magiya wasu jahilan cikin su har sujjada suke yi mashi duk don ya ji ƙan su ya canza ra'ayin shi..
"Dama kun daina wahalar da kanku.." ya faɗa yana girgiza kansa.
Cike da sanyin jiki Jan Harshe ya rungumeshi sosai kamar zasu koma mutun ɗaya, cikin karyayyar murya ya ce, "Koda kowa zai juya maka baya a cikin Elders, ka sani kana da ni, alƙawari ne muka daukarwa kanmu tun yarintar mu, duk runtsi duk wuya zamu kasance a tare, a kowane hali na rayuwa, don haka nima na ajiye makaman yaƙi na, ra'ayinka shine nawa, ba gudu ba ja da baya, zamu miƙa wuya a tare, kuma zamu kar6i hukuncin da za'a yanke mana, a tare zamu girbi abunda muka shuka." Ya faɗa jikinshi na kerma.
"Ka faɗa musu ba sai sun sha wahalar nemana ba, zan kawo kaina har abujan, cikin estate dinka, saboda in sauƙaƙa musu..."
Cikin shesshekar kuka ya ce, "A'a bazai yiwu ba, bazan jure ganinka cikin mawuyacin hali ba, ka bi sauran Elders din ku nemi mafaka, na yi maku alkawarin bazan tona muku asiri ba, koda za'a azabtar dani ne akan in fada, shi kaɗai ne gatan da zanyi muku na karshe, kamar yadda kowan nan ku ya sani dokar kurkukun kaddara ne kuma alkawari ne muka daukarwa junanmu wani bazai tona asirin wani ba, don haka ni ma bazan tona asirinku ba, amma ku sani idan har wani daga cikin ku ya yi gigin cin amanata, wallahi! na rantse da izzar mulkina baza ku sha ba, zanyi maku abunda baku ta6a zato ba.." ya faɗa da kakkausar muryarsa mai firgitarwa.
Har saida Elders din suka razana da jin maganar shi...
Ƙara ƙanƙame shi Jan Harshe ya yi, "Kaima kasan abu ne da bazai ta6a yiwu ba, ni bazan barka ba, ka so kanka da yawa, idan na barka kai kadai a cikin kuncin rayuwa ban yi maka adalci ba, kamar yadda bazaka sauya ra'ayinka ba, nima bazan ta6a canza nawa ra'ayin ba, ba inda zan je Obinna, ƙafarka ƙafata, har mutuwarmu..." Ya faɗa yana ƙara jaddada mashi...
"Tun da har kun yarda zaku miƙa wuya, me zai hana ku bamu sihirin dake a tare da ku? In ya so sai mu ƙara da namu, in har dagaske kun tuba to kamata yayi ku bar komai da ya shafi tsafi..."
Jan Wuya ne ya yi maganar, sauran Elders ɗin suka goyi bayansa akan su basu sihirinsu, nan take suka fahimci basu damu da halin da suke a ciki ba, tun da gashi har sun fito da haɗamarsu a fili, wato muƙaman su suke so su basu don su samu damar cigaba da aikata fasadi...💔
Babu wanda ya tanka musu a tsakanin Elder da Jan Harshe sarai sun ji me suka ce a cikin kunnuwansu.
lokaci ɗaya wani hayaƙi mai kama da guguwa ya karaɗe dakin da suke a ciki, kafin wani lokaci kowannansu ya 6ace, dama ba a guri ɗaya suke ba, dabarun sihiri ne da suke kira magician's dream, a mafarki suke haɗuwa da tsakar dare su yi magana da junansu, kowani Elder dake a kasashen ƙetare dana gida Nigeria in har suka yi mafarkin nan to kowannansu zai bayyana ne a cikin sa..🔥✍️
Dare mahutar bawa, sai dai bakowani rai bane yake samun damar da zai huta a cikin sa, haka ta ke a bangaren Obie family, bayin Allahn nan Yadda suka ga rana haka suka ga dare, babu wanda ya runtsa daga su har ya'yansu, a zaune suka kwana saboda depression din da ya yi musu katutu a zuciya...
*DAGA ALƘALAMIN BOSS BATURE🔥*
*Ga me bukatar karanta littafin kurkukun kaddara, 500 ne za'a tura Via Opay, 8103884440 Hafsat Bature Muhammad, shaidar biya za'a tura ta whatsapp, 08103884440*