A washe garin ranar, ba zato ba tsammani Sheikh Imam malik yayi musu zuwan bazata, batare da wani daga cikin su ya gayyace shi ba. Babu wanda yasan da batun zuwanshi saboda bai sanarma kowa ba.
tun jiya da yaje masallaci yin sallar Magrib bai ga kowa na family din Obie ya halarci sallar ba.
kuma a sanin da yayi musu basu da wani masallaci da sukeyin sallah in ba masallacin shi ba, tun nan abun ya fara da mun shi, ya yi ta tunanin anya lafiya, mutanan da duk in lokacin sallah yayi sune zaka gani a sahun farko.
Zuciya da saƙe saƙe har ya fara tunanin ko dai sun canza masallaci ne? lokacin da aka kira sallar isha'i mutane sunata taruwa domin yin sallah yaita baza idanu cike da sa ran ko zai ga gifcin su sai dai har aka ƙare sallar babu su babu alamarsu, abun ya dame shi matuka, ba shi kadai ya lura ba, har jama'ar dake yin sallah a masallacin saida sukayi ta tambayar ina ahlin Obie? Meyasa basu zo masallaci ba? kodai ba lafiya ne"?
Wadanda suke zumunci da dattijon arziki har jaraba kiran layin shi sukayi bai daga ba, suka kira layin ya'yansa ba wanda yayi picking, haka shima sheikah imam ba irin kiran da bai yi ma baba Obie ba awaya amma baya shiga kwata kwata.
sai da takaiga ya kira ya'yan shi dukansu babu wanda wayarsa ke shiga, Hakan Ya kara jefa shi a hali na damuwa, daren jiya dakyar ya runtsa saboda tunaninsu da yayi mashi katutu a cikin zuciyar shi.
lokacin sallar asuba nayi bayan ya farka daga bacci, yayi shirin zuwa masallaci cike da sa ran zaiga ahlin Obie sun halarta.
bayan ya isa masallacin ya yi ta sa ran ganinsu har masallata suka kammala hallara ya tada sallah, bayan ya gama sallar, yayi nasihar daya saba yi abayan kowace sallar asuba, anan ne mutane sukai ta tambayarshi meye hana Ahlin Obie halartar masallaci tun jiya? Ko an kira su awaya ba'a samu, ko dai sun canza masallacin da suke yin sallah ne ko sun yi tafiya ne "?
abun daya sa suke tambayarshi Imam saboda sun san yafi su kusancin da baba Obie, cike da damuwa yace musu baida masaniyar akan abunda ya hanasu zuwa masallaci amma in sha Allah zaije Estate din ya dubo a wani hali suke a ciki, gaba daya sunji dadin maganar shi, har suka ce idan ya isa, komai ake ciki kada ya manta ya kira ya sanar da su ko hankalinsu zai kwanta, Yace musu in sha Allah zasu ji daga gare shi.
Ko masaukinsa bai wuce ba, daga masallaci Ya shiga motarshi yana driving yana tunanin su, kaitsaye Ya nufi Obie Estate.. 💔
Tun da Motarshi ta shigo estate din Ya tsinci kanshi da jin matsanancin faduwar gaba da bai taba jin irin ta ba.
Da sunan Allah abakinsa, ya tsayar da motar a parking space yana fitowa securities dake zarka suka dinga gaishe da shi cikin girmamawa, fuskarsa da fara'a yake amsa masu kafin yayi hanzarin wuce hannunsa ruke da cazbaharsa Ya nufi Katafaren falon gidan bai kaiga shiga ba, ya tsaya daga bakin kofar yayi sallama, shiru ba'a amsa mashi ba, kusan sau bakwai yana doka sallama shiru kamar yayi magana da bango, lamarin Ya daure mashi kai, da har zai tafi sai kuma Ya fasa saboda baya jin zai iya tafiya batare dayasan awani hali suke a ciki ba..
Da zuciya ɗaya ya kutsa kai cikin falon, Yana shiga yaci burki yana kallon abun da yayi matuƙar daure masa kai aransa ya furta dama suna nan, ina tayi musu sallama basu amsa min ba"?
Mr. Romantic Novel Complete
Wlh tun daga yanayin da ya riske su ya fahimci babu lafiya atare da su, akace labarin zuciya a tambayi fuska, karasa shiga ciki yayi, kwata kwata basu san da zaman shi a falon ba, babu alamun sunji motsin tafiyar shi, yadda kasan gangar jikinsu ce kadai zazzaune kan Sofa, ruhinsu baya atare da su, damuwa ta ƙara gusar da hankalin su, saboda rashin baccin da basuyi ba jiya, idanunsu sun kara kumbura, sunyi jawur kamar garwashin wuta, gaba ɗayan su babu riguna a jikinsu sai gajerun wandunan da suka bari..
"Inna lillahi wa'inna ilaihirraji"un...." Shiekh iman ne Ya furta Yana lekan fuskokinsu, ya razana da ganin Halin da suke a ciki, har yatsunsa ya fifita saitin fuskokin su don yaga ko akwai rai a jikin su amma babu alamun zasu kyafta idanun su, Ya rasa gane suma sukayi ko kuwa wani abunne? Amma fa hankalinsa Ya dungunzuma ainin.
"Hateem! Sharafudeen! " ya fada yana kallon faces dinsu, kamar hotuna, saboda rudu Ya kasa gane suna numfashi ko basayi, juyawa yayi kan sauran"Abdul Razak! Deeni! Wai baku ji ina magana? Meke damunku ne? Meya faru daku? Kuna acikin hayyacin ku kuwa eye"?
Juyawa yayi kan Sir mubarak arude Yace"Mubarak! Wai dan Allah meke damunkune uhum? Mayesa bakwa motsi? Suma ku ka yi ne ko kuwa wani abunne ya faru da ku.." fuskarsa ya mutse da damuwa
bai ƙare maganar ba, ya tsinkayi muryar mutun abayansa Yana karanta addu'ar tashi daga bacci.
a hanzarce ya juya dan ganin wanene! Wani faduwar gaba yaji ganin wasu daga cikin matasan familyn kwance akan floor suna bacci, kamar marasa galihu, hankalinsa ya kara tashi matuka.
a hankali Ya mike zaune yana miƙa hadi da yin hamma, Cikin sauri Imam Ya nufe shi cike da sa ran zai samu amsar tambayarsa agurin sa..
Zukunnawa yayi agabansa cikin rawar murya yace"Nadeem, meke damun iyayenku ne? Meke faru wa da ku ne"?
"Gaba daya na rude hankalina ya tashi, kamar babu lafiya atare da ku.." ya kare maganar cike da sa ran zai samu amsoshin tambayoyin shi agurin Justice.
yamutsa fuskarsa yayi cike da damuwa ya fayyace masa halin da suka risƙe su a jiya.
tamkar zai fashe da kuka ya kara da cewa"shiekh ka taimaka mana, mun rasa gane kansu, ba mu san meke damun su ba, babu magana sai kuka, jiya daga mu har su babu wanda ya runtsa, ko ruwa bai gifta makoshin mu ba, bayan haka bamu ga baba ba, Kofar dakinsa a kulle take, ko da muka same su abakin kofar dakinsa, munyi tsammanin ya mutune, saboda mawuyacin halin da muka taras da su yafi kama dana wanda ya rasa abu mafi soyuwa agare shi, amma koda muka tambaye su ya mutune basu tanka mana ba, ko magana basa iyayi..."
araunace ya karasa maganar, ta ko'ina kan shiekh imam ya kulle ya ce"dama sun taba yin irin hakan"? Arude justice ya dubi Uncles din nashi, don kwata kwata bai san abun ya munana har haka ba, har kwara jiya sun motsa lokacin da yan aiki suka fara koken abun daya faru da Saratu...
Girgiza kai Justice yayi"ban taba ganin sunyi ba, amma ina tunanin Zuciya ce, saboda grandpa ya ta6a yi sau biyu daɗewa tun kafin na mallaki hankali na, lokacin da Senior mom ta rasu da kuma lokacin da Kanwarsa ta rasu.."
sheikh Imam bai ƙarasa sauraran maganar Justice ba, Ya juya jikinshi na 6ari ya samu guri daga tsakiyar Sofas din da suke, afujajen Ya zauna dirshan tare da tankwashe kafafunsa yayin zaman cin tuwo..
- Sirrin Rike Miji
Yadda ake gane Sha'awar Mace ta Tashi
Amfanin Yayan Kabewa Ga Mata Da Maza
"A'uzubillahi minasshaidanirrajim, Bismillahirrahmanirrahim..."
ƙira'ar alkur'ani mai girma Ya cigaba da yi musu tun yanayi kasa kasa har ya ɗaga muryarsa da karfi idan yaja aya saiya dire ta yake jan numfashi kafin ya daura da wata, kankace me tuni ya haɗa gumi akan fuskarsa yanayi yana duban su.
justice daya langwa6e kansa, Yayi shiru yana jin yadda kira'ar shiekh ke ratsa zuciyar sa..
Kaitsaye Sautin ƙira'arsa ya ratsa dodon kunnuwansu, har izuwa sassan jikin su, Unexpected zuciyoyin su suka fara bugawa da matsanancin karfi, Numfashin su ya fara fita da sauri da sauri
Gaba daya bai lura ba, saboda ya sadda kan shi ƙasa, Yana tsaka da karatun kwatam ba zato ba tsammani suka fara dawowa hayyacinsu, wata irin nannauyar ajiyar zuciya gami da atishawa da tari suka dinga saki a jere a jere.
"Ruwa.. Ruwa.. " cikin disasshiyar murya Hateem Ya firta..
Jikim Justice na bari ya mike garin sauri hada tuntube ya nufi kitchen area, jim kadan Ya dawo da gudu, ya rugume bottle waters masu sanyi a kirjin shi.
bayan ya cire masu murafan robunan ruwan Yabi su daya bayan daya ya mika musu ruwan yatsun hannayensu na kerma suka kakkarba tare da kaiwa baki suka fara sha, makoshin su har sauti ya ke fitarwa kwat kwat!! Kamar zai ballo..
At same time ziyad da captain Yaseer dake kwance kasa suna bacci suka farka sakamakon kira'ar imam data cika kunnan su kamar wadanda suka sha kayan maye a kasalance suka miƙe zaune tare da jingina bayansu jikin Sofas.
Kowan nan su saida ya shanye ruwan dake acikin robar sa, kafin suka jefar da robobin...
Sai lokacin ƙwaƙwalan su su ka dawo bakin aikinsu, sunyi mamakin ganin gari ya waye, ko da suka ga shiekh Imam dake a zaune Yana kira'ar alkur'ani, kusan atare suka sauko daga kan sofas din ko mikewa sun gaza yi saboda rashin kuzarin jikin su, da rarrafe suka ƙarasa gaban shi, gaba daya suka kewaye shi kamar zasu lullu6e shi da karajen su, babu wanda bai jigata ba a cikin su, jiya izuwa yau saboda tashin hankali Har faɗawa sunyi, kwarin idanunsu sunyi ja musamman masu hasken cikinsu cheeks dinsu sun yi ja.
shesshekar kukan su ce ta cika kunnuwan shiekh imam malik, baisan sa'adda ya dakata dayin karatun alkur'anin ba yabisu da kallo mai cike da ruɗani, hankalinsa ya tashi da jin yadda juraman maza kamar su suke kuka da idanunsu..
hankalinsa atashe ya fara tambayarsu meke damunsu? Me yasa suka fita hayyacinsu.
rurruƙe hannayen shi sukayi cikin raunanniyar murya su suka soma fadin .
"Baba Imam mun shiga uku, mun bani shiekh, muna a cikin musiba, baba yaja mana bala'e, zuciyoyin mu sunyi rauni, hankalinmu ya tashi, anyi mana bakin tabon da bazai taba goguwa ba..."
gaba daya sun ruɗa Imam malik Ya rasa gane ina maganganunsu suka dosa.
Tun da suka fara yin magana su Captain suka shiga rudani, sun rasa gane ina zancen su ya dosa? Shin me baba ya akai ta ne?
"baba ya kunsa mana bakin cikin da har abada bazai taba barin Zuciyoyin mu ba, Ya ha'ince mu, Ya zalunce mu, ya kashe mana rayuwa, kuma ya cuci kan shi, sheikh tun jiya gobara ta kama ci acikin zuciyoyinmu bamu iya kashe wutar dake konata ba sai da kayi mana karatun alkur'ani mai girma tukunna muka samu sassaucin radadin da muke ji" wani irin faɗuwar gaba Imam malik yaji adabarbarce yake rarraba idanunsa akan fuskokin su..
"Baba Imam ka tayamu rokon Allah ya dauki ranmu mu huta, watakil hakan ya zama sauki agare mu, saboda bazamu iya cigaba da rayuwa ba, da wani ido zamu dubi duniya? kowa zai juya mana baya, zamu zama abun gudu, baba imam bakin ciki zai kashe mu,...." ya fahimci wani mummunan abune ya faru da su kuma daga maganganunsu ya gane baban su ne ya jefa su a halin da suke a ciki..
Jikinsa ne yayi sanyi tamkar babu laka, tsantsar tausayinsu ne Ya kama shi, tun kafin ma yaji abun da zasu fada masa..
A hankali ya soma ɗaura tafukan hannayensa asman kawunansu kamar kamun ciwon kai ya ke yi masu, addu'oi ya soma karantowa yana shafe masu kai..
cikin ikon Allah nutsuwa ta fara shigar su, numfashin su dake fita a hargitse ya fara daidaita, wani irin gumi ne ya soma wanke goshinsu alamar zazzabin jikinsu ya fara sauka..
"Ba sai kun fada min abunda ke damun ku ba, na riga dana sani, sai dai karin bayani da zan nema..." arude suke kallon shi da tsantsar al'ajabi .
"Shiekh, taya akai ka sani? Mun shiga uku, shikenan kowa ya riga daya san miyagun ayyukan da baba ya ke aikatawa, kowa ya sani, tamu ta kare, mun bani .."
Senate Lateef ne ya fada tare da daura hannayensa asaman kansa..
Cikin sanyin murya Imam yace"Lateef, babu wanda Ya sani, daga Allah, sai ku sai kuma ni, nima din bakomai na sani ba.."
"Kwana daya da banganku a masallaci ba, Hankalina Ya tashi, bani kadai ba, hatta jama'ar dake halartar masallacin sun damu da rashin ganin ku, kowa muka kira layinsa a cikin ku bama samu, shiyasa na yanke shawarar zuwa nan din dan in duba ku, saboda naji araina ba hakanan ku ka ki zuwa masallaci ba..." ya dan dakata tare da jan numfashi kafin ya kuma cewa" Ba jiya bane ku ka yi family meeting ba? Ina Owais ina kuma sauran ahlin naku"?
Sai lokacin suka tuna da shi, Kowa Yana ta kan shi, cike da rashin ƙwarin jiki sharafudeen Ya mike tare da juyawa a hanzarce ya nufi cikin gidan ya bazama neman sa, saboda yaji aransa bai fita ba, watakil ya fada wani gurin daban..
"Bakowane Ya samu damar halarta ba..." His excellency deen ne ya fada yana sharce kwallarsa, da yatsan hannunsa Ya nuna su Justice yace "su kadai ne, suka zo, sauran Uzirurrukane suka ruƙe su..."
kwata kwata bai nemi su faɗa masa ainihin abun da ke faruwa da su ba.
Takun tafiyar su ne Yaja hankulansu ga duban inda sautin ke fitowa, Sharafudden ne ya 6ullo Hannunsa ruke da damtsen Owais dake ta layi kamar wanda yasha kwaya..
Gwanin ban tausayi suke kallon shi, Hankali atashe su justice suka mike tare da nufar shi, kwata kwata basu san yana a gidan ba, sakar musu shi Sharafudeen yayi, cikin sauri suka tallabesa tare da rungumesa suna tambayar shi meke damun shi? Meke faruwa da shi? A ina ya kwana?
"Can na tsinto shi a back room din baba, Ina tunanin tun jiya acan ya kwana..."
Hankalinsu Ya kara tashi basu taba ganin Owais a mawuyacin hali irin wannan ba, ko magana bai iyayi, fuskarsa duk jirwayen hawayen sa..
"Ku miko min shi nan" sheikh Imam ne Ya fada Tare da mika musu hannu, Ruko shi Captain yayi ya taimaka masa Ya karasa ga imam, Jikin nasa ne babu kuzari gaba daya ya durkushe saman gwiwowinsa agaban Imam Malik.
tallabo keyarsa yayi tare da janyoshi Ya fado kan kirjinsa, cikin sigar lallashi Yake dan bubbuga tafin hannayensa akan bayansa, a hankali ya fara karanto addu'o'i yana tottofa masa asaman sumar kan shi..
"tun da yanzu kun riga da kunsan komai babu batun boye boye a tsakanina da ku, maganar gaskiya daliline yasa na shiga jikin ku don in samu kusanci daku saboda in tabbatar da abun da nake zargi akan family din ku..." da rudu suke kallon Imam, maganarsa ta daga hankulan su, owais daya fara dawowa hayyacin sa, cikin kunnansa ya tsinkayi maganar Sheikh Imam da mamaki ya dago da kansa yana dubansa..
yadan numfasa kafin ya daura cewa"ni Allah yayi min wata baiwa In har zan zauna tare da mutum mai bakin sihiri a jikin shi wlh sai naji a jikina, Mahaifinku da surukinku pravin na dade da sanin suna da sihiri a jikin su amma ban taba bayyana maku ba, saboda bani da isassun hujjojin da zan tunkare ku da maganar, lokacin dana fara kutsa kaina ga mahaifinku har na samu ya yarda dani rana ta farko daya gayyaceni don inzo in gana daku, sai da gabana ya fadi ganin yadda kukeyi masa biyayya sau da ƙafa, kun yarda da mahaifinku kuna son shi, jikina yayi sanyi dama tun kafin na gane ma idona, sai da naji abakin mutane amma dana gani da ido abun ya karya zuciyata, nayi al'ajabi yadda kuka kasance masu kyawawan halaye da dabi'u kun fita daban, samun irinku zaiyi wuya, Allah bai rageku da komai ba, sai dai kash mahaifinku yayi muku cikas, 6atacce ne ku kuma tsarkakakku ne, wallahi a lokacin koda na fadamaku ba zaku yarda dani ba, zama ku iya tunanin turo ni akayi don inyi masu kazafi, watakil ma kusa a daure ni, shiyasa naja bakina nayi shiru, amma duk da haka ban hakura ba, saboda Allah ya jarabceni da kaunarku, naji inason in taimake ku shiyasa nabiyo ta bayan fage batare da sanin kowa ba, na fara kiran Owais ta boyayyiyar number, na fada masa ya bincika family dinsa akwai bara gurbi a cikin su...." dafe kai Chief Owais yayi da tafin hannunsa bakinsa abude da tsantsar mamaki yake kallon Imam wai ashe shine boyayyan mutumin dake kiransa awaya..
"Sheikh dama kaine boyayyan mutumin dake kirana awaya? Ya fada arude, murmushi Imam malik ya sakar masa"Nine Owais, nasan za ka yi mamaki, kamar yadda kake amfani da brain dinka nima haka nake amfani da kwakwalwata, ban taba bari ka gane nine ba, na toshe duk wata hanya da zaka iya bin diddigin layin da nake kiran ka da shi, bayan haka duk idan zamuyi waya ina canza murya saboda bana so ka gane nine..." dafe kansa yayi da tafukansa Shiekh Imam Ya basa mamaki, yayi zaton malamin addinin islama ne ashe bayan kasancewar shi alkali har ilmin computer gare shi saboda ba karamin wahala ya bashi ba, yasha ya zauna ya baje basirar sa gurin gano wanene boyayyan mutumin dake kiransa amma ya kasa kamar Aljani haka ya koma masa, kowa dake awurin yayi mamaki sosai..
Ruƙe hannayensa Chief yayi"meyasa tuntuni baka fito fili ka fada min kaine ba? Why pls? Da ka fadamin ay da tuni na dauki mataki akai"
Shafa sumar kanshi imam yayi"Owais, koda na fada maka ba zaka yarda ba...."
"Dan Allah ku fada mana meke faruwane? Tun jiya kunbarmu a duhu, ku sanar damu mana! Kunce baba Ya kulle kansa adaki, meyasa yayi hakan? Wani laifine ya aikata da da yaja har kuka shiga mawuyacin halin nan.."? Cike da damuwa Ziyad ya tambaya yana binsu da kallo gaba daya fargaba ta hana su bude baki su furta..
Captain yaseer daya gama Fusata zuciyarsa tazo wuya rai a6ace yace"nagaji da jiran ku fada mana, gaba daya kun tada mana hankalinmu, kuma kunki ku sanar damu meke faruwa, wlh da nasani da banzo ba.." ya fada yana girgiza kansa..
Marairaice fuska justice yayi tare da kallon sheikh Imam tamkar zaisa kuka yace"Dan Allah baba Imam ka fada mana tunda su sunƙi su sanar damu, pls ku taimaka ku fada mana meke faruwane mun kasa gane inda zancenku ya dosa...."
bai ƙarasa maganar ba, Chief Owais Cikin raunaniyar muryarsa da ta disashe ya fara zayyana musu abunda ya faru jiya kafin a fara family meeting, tiryan tiryan ya fayyace musu tun daga biri har wutsiyarsa..
Tashin hankalin da ba'a saka mashi date, tun kan ya karasa suka fara jefawa junansu kallon kallon mai nuni da tsantsar al'ajabi da rudani hadi da tsantsar tashin hankali, ga wani irin faduwar gaba da suka fara ji, Lokaci daya suka zazzare idanunsu jin abun da basu taba zata ba, murya na rawa Justice ya furta"ba zai ta6a yiwuwa ba Owais, wannan wani irin labarine mai kama da almara? Bazai ta6a zama gaskiya ba wlh, Owais ka sake bincike watakil kunyi kuskure, Baba bazai ta6a zama daya daga cikin azzaluman mutanan ba, ka bani mamaki Owais ka rasa wa zakai wa kazafi sai baba? sai kace bakasan halin shi ba"? Cikin fusatacciyar murya ya fada tsabar bacin rai shatun jiyoyon wuyansa sun fito rudu rudu kan fatarsa..
"Tayaya zaku yarda da abunda wata tsohuwa bare ta fada? Wallahi karya takeyi maku, ba momma bace, wanda ya mutu baya dawowa ba, ni batai min kama da mai hankalin ba, makiya ne suka turota don tayi ma grandpa kazafi, Ai wlh da nasan abunda makirar matar nan ta aikata, da tun lokacin dana ganta kwance kan sofa, zan danne hancinta da fillow har sai ta bakunci lahira...."
Captain yaseer daya gama rikicewa jikinshi na 6ari ya dubi Imam malik daya sadda kanshi ƙasa "shekh pls kayi masa rukiya, Owais Ya haukace, He needs a psychiatrist to examine his brain, he's not well, Owais would never say this in his right mind, saboda wlh bayin kansa bane, Owais ba zai taba fadin maganar nan da hankalinsa ba, zai iya yiwuwa aljanunne suka shige shi, dad...Uncles pls kuce mana karyane abunda Owais ya fada akan grandpa, ni nasan ba acikin hayyacinsa ya fada ba, Baba ko kiyashi bazai iya kashewa ba, balle rai..."
tashin hankali Ya hana Ziyad furta kalma, kunnuwansa sunjiye mashi abunda ya fi karfin jin shi, baima san sa'adda ya fara unbottoning din rigarsa ba, saboda wani zafi daya taso mashi, still basu gasgata maganar owais ba, amma fa sun kaɗu ba kadan ba saboda sunsan mawuyacin abune Owais yayi masu karya saboda ba halinsa bane, kawai suna jin tsoron su gaskata abunda ya fada musu ne.. Gaba daya ubannin nasu sun kasa magana saboda sun razana da ganin yadda suka ɗaga hankulansu, ta wani bangaren zuciyarsu ta karaya da jin kalaman dake futowa daga bakunansu, bayin Allah saboda yardar da sukayiwa kakansu sun kasa yarda da maganar da aka fada musu akansa..
runtse idanu shi yayi gam a hankali wasu zafafen hawaye suka fara shararowa kan kuncin sa, cikin shesshekar muryarsa mai rauni ya furta"sheikh ni dama nasan za'a rina, baba ya karya mana zuciya, wlh ba kazafi nayi masa ba, shine Elder na gidan kurkukun kaddara kamar yadda kukaji, zaku Iya tuna yaran da nake ruko agurina? Wanda nace maku sojojin america ne suka tsince su a dajin Evil forest kuma suka damƙa case din mu a hannun hukumarmu? To wadannan yaran suna daga cikin fursinonin kurkukun kaddara, A Lokacin sun ku6uta daga gidan kurkukun ne, ai kowa daga cikinku ya gansu a ranar farewell dinner din Uncle Hateem.." nan fa kwakwalensu suka fara tariyo masu fuskoki yaran masu bala'en kama da wasu daga cikin su, still basu gasgata maganar shi ba, amma fa sun fara shan jinin jikinsu, maganarsa ta haifar musu da kowanto..
"Bayan mun kai farmaki, Munyi nasarar ceto wasu daga cikin yaran, A yanzu haka suna akwance gadon asibiti karkashin kulawar likitoci, Aminina omar shima an kwantar da shi tare da dan uwan yaran Salsabeel, har yau basu farfado daga Coma ba, Idan har yanzu baku yarda ba zan iya nuna maku videos din yaran da muka kubutar..."
Wayarsa ya zaro daga cikin front pocket din aljihunsa ya kunna masu video din fursinonin ya nuna masu gaba daya suka leƙa suna kallon su, gasu nan a kwankwance saman gadajen asibiti jikinsu sanye da patient uniform, har sheikh imam saida ya kalla, ya kuma kunna masu videos din su Unaisah daya dauka yayin tattaunawarsu a questioning room, wlh sun girgiza gaba dayansu ashe basu ji komai ba agurin khala, sai yanzu da suka ji ainihin labarin azabtarwar da akeyi masu agidan kurkukun ƙaddara, abun ya taba zuciyarsu sosai, kamar zasuyi hauka saboda tausayin su daya kama su, su Captain duk sun yarda dagaske ne abunda owais ya fada musu sai dai basu yarda kakansu Obie yana daga cikin azzaluman da suka azabtar da su ba, saima cewa sukayi koda zasu yarda labarin na zahirine amma bazai taba yiwuwa baba ya aikata ba, saboda su sun yarda da shi sun kuma san halin shi, sheikh Imam Ya kasa furta kalma, saboda raunin da zuciyarshi tayi, baiyi zaton abun ya munana har haka ba, sai ambaton Inna lillahi wa'inna ilaihurraji'un yakeyi Bai ma san sa'adda ya zabura ya mike tsaye jikinsa na 6ari Ya kama zarya a tsakar falon ba, Cazbahar hannunsa tuni ta jima da barin yatsunsa ta faɗa kan floor, har kwalla saida ta zubar masa bai bari sun gani ba yayi saurin sanya tafin hannunsa ya goge ta, hakika Baba Obie ya karya Zuciyar Imam malik, bai taba zaton zai iya aikata makamancin rashin imanin nan ba, abu biyu dayafi kona masa rai ya karairaya zuciyarsa irin yadda suka shafe shekaru suna aikata fasadi a doron ƙasa batare da an kama su ba, Yaji takaicin irin azabtarwar da sukayiwa yaran da basu ji ba basu gani ba, abun takaici yaran jininsu ne, babu imani ba tausayi suke azabtar da su, labarin da owais ya basu ya fama masa tsohon raunin da ke a cikin zuciyarsa, Bazai ta6a mantawa ba, yaso ya fada musu ainihin dalilin dayasa ya fara zargin ahlinsu sai dai ya kasa ganin halin da suke a ciki, abun dayafi damunsa makomar Ahlin Obie, ya'yansa masu daraja da kima a idon duniya, babu na banza acikinsu, kowa yabonsu yakeyi saboda kyawawan halayensu da dabi'unsu, amma fasikin mutumin nan saida ya zubar masu da mutuncinsu! Bai kyauta ma kanshi ba, da alama abun ya taba zuciyar imam so yake yayi kuka don ya fitar da abunda ke ransa sai dai ya kasa saboda bai son suga rauninsa hakan zai iya ƙara jefasu a mawuyacin hali..
a karo na biyu ya share kwallarsa yayin daya basu baya, saida ya daidaitsa nutsuwarsa ya daure ya cije cike da karfin hali ya juyo ya fuskance su a lokacin sun kasa yin kukan na zuci sukeyi mai radadin gaske...
Cikin sanyin murya ya tambaye su tun da suke arayuwarsu sun taba fuskantar mummunar kaddara ko wata jarabawar rayuwa irin wannan"? har suna hada baki gurin furta aa sukace su tun da suka taso rayuwarsu basu ta6a fuskantar kaddara mara kyau ko wata jarabawar rayuwa ba, nasara da jin dadin rayuwa kadai suka sani, idan ma akwai abun daya taba sanyasu kuka da idanunsu to bai wuci ranar da suka rasa mahaifiyarsu ba, acewar su His excellency, gyada kai sheikh imam yayi idanubsa cike tab da kwalla yace"wannan ne karo na farko da zasu fara fuskantar mummunar jarabawar rayuwa, yace shi tunda ya taso rayuwarshi yana jin labarai iri iri na irin jarabawowin da mutane suke fuskanta wasu su daga hankalinsa wasu su sashi zubar da kwalla saboda tausayi, amma bai taba jin kaddarar data girgiza shi irin tasu ba, yajiye masu bakin ciki da takaicin abunda mahaifinsu ya aikata musu, ya tausayawa rayuwarsu, amma kada su karaya, nan ya fara yi musu nasiha mai tsuma zuciya...
_Abun da akeso a yayin da Allah ya jarabce bawa da wata mummunar kaddara, Ana kwadaitar da su da su amsa jarabawan da hakuri da godiya suyi biyayya ga Allah, domin hakan yana tabbatar da gafara da lada daga Allah, kuma Allah yana tare da masu hakuri, sannan dukkan tsanani yana a tare da sauki_
_Wani lokaci Allah yakan jarrabi bayinsa da musibu domin ya daukaka su, kuma ya kankare zunubansu, kamar yadda Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) yake cewa_
_(For every misfortune, illness, anxiety, grief, or hurt that afflicts a Muslim, even the hurt caused by the pricking of a thorn, Allah removes some of his sins.")_
_“Duk wata musiba, ko rashin lafiya, ko damuwa, ko bakin ciki, ko cutarwa da ke damun musulmi, ko da wata ƙaya ce da ta same shi, Allah yana kankare masa wasu daga cikin zunubbansa"_
A cikin suratul Ankabut ayata 2
_Allah buwayi yace"Ashe Mutane Suna Tsammanin Cewa Za'a Barsu, (Don Kawai) Sunce Munyi Imani, Alhalin Kuma Su Baza'a Jarabcesu / Baza'a Fitinesu Ba?_
_Acikin suratul Surah Al-Baqarah Allah yana cewa_
_Wa lanablu wannakum bishai’im minal khawfi waljoo’i wa naqsim minal amwaali wal anfusi was samaraat, wa bashshiris saabiroon._
_"Kuma lalle ne, zamu jarrabe ku da wani abu na tsoro da yunwa da nakasa daga dukiya da rayuka da 'ya'yan itace, kuma ku yi bushara ga masu hakuri."_
_"Ku tuna cewa hikimar Allah da iliminsa sun wuce fahimtar mutum, Maimakon tambayar dalilin da ya sa Allah ya jarrabe mu, ya kamata mu mai da hankali ga amsa jarabawowin da imani, da hakuri, da godiya_
_Annabi Muhammad (SAW) ya ce, "Babban lada yana tare da fitintinu masu girma, idan Allah ya so mutane sai ya jarrabe su, kuma wanda ya yarda da shi ya samu yardarsa"_
_Kaffarar Zunubai Allah yana iya jarraba mutane domin ya tsarkake su daga zunubansu, kuma idan suka yi haquri za a gafarta musu zunubansu._
_And sometimes Allah tests us with calamities and sometimes with blessings, to show who will be thankful and who will be ungrateful, and who will obey and who will disobey, then He will reward or punish them on the Day of Resurrection _
_Kullum ka ɗauka cewa kana cikin jarabawa ne, domin dukkanin rayuwarka jarabawa ce, Allah zai jarabceka da abubuwa daban daban, waɗanda ka sani da waɗanda baka sani ba, tsammaninka kayi juriya kayi haƙuri_
_Ba kullum ne zaka samu rayuwarka ta kasance maka yadda kake so ba, akwai ranar farin ciki, sannan kuma akwai ranar baƙin ciki, akwai ranar samun riba, sannan kuma akwai ranar (faɗuwa) yin asara"_
_Haka jarabawar rayuwa take, amma babu makawa duk abinda ya faru gareka, idan kayi biyayya ga Allah, sannan kuma kabi manzonsa, haƙiƙa zaka kasance daga cikin masu cin nasara a duniyarsu da kuma lahira"_
Tunda Imam Ya fara yi musu nasiha jikin su yayi sanyi lakwas, Imani ya kara shigarsu, nasihar shi ta ratsa zuciyarsu sosai, musamman daya tunasar da su irin yadda annabawa suka fuskanci jarabawowin rayuwa masu tsanani kuma sukayi hakuri sukai biyayya ga Allah, sai suka ga tasu jarabawar bakomai bace somun ta6i ne, sannan yace yasan basu fara ganin komai ba, sai lokacin da abun ya fallasa duniya ta sani a wannan lokacinne zasu fara fuskantar kalubalen rayuwa amma baya son su karaya, kuma su daina jin fargaban mutane su sani, laifin nan basu suka aikata ba, Allah ya sani, kuma yana atare da su, don haka su mika lamuransu gare sa, sannan su dage da yiwa kansu addu'a akan halin da suke a ciki, shima zai tayasu, In sha Allah wata rana sai labari, zai zama kamar ba'ayi ba, sai dai tashin zance, kuma kada su kuskura duk runtsi duk wuya su jefa kansu a mawuyacin hali saboda maganganun da mutane zasu fada akansu, koda zasu rasa mukamansu ne kada su karaya, mutane basu da wuta basu da Aljanna ba zasuyi masu hisabi ba, kada su ji kunyar laifin da basu suka aikata ba, koda za'a cuzguna masu ne, ayi musu kazafi, ko azage su aci zarafin su, kada su kuskura su canza daga yadda suke, saboda sau dayawa mutane suke jaza ma mutun bakin cikin da zai zaiyi silar da zai tsani kansa ya kuntata har yayi tunanin kashe kanshi bayan yin hakan kuskure ne babba ba...💔
Yayin da yake yi masu nasihar ya haɗa gumi akan fuskarsa kamar babu A.c a falon, har lokaci bai zauna ba, yana daga tsaye yana fuskantar su batare da gajiyawa ba, wlh ji sukayi kamar ana wanke damuwar dake a cikin zuciyarsu, ga wani sanyi dake ratsa jikinsu, imam ya karfafa masu gwiwarsu, Ya farfado da jarumtakarsu, aransu har sunji zasu iya fuskantar kowani irin kalubale da zasu fuskantar...
"Kuma ku sani, Nima ina atare daku, zan tayaku yaƙi atare zamu cinye jarabawar nan da take tunkaro mu, in sha Allah, zan tsaya maku tsayin daka don ganin baku tozarta a idon duniya ba" ya faɗa yana kara jaddada musu da murmushi akan fuskarshi, wannan maganar da yayi ta faranta ransu, har basu san sa'adda suka saki murmushi akan fuskokinsu ba, kusan atare suka mike tare da nufar shi, atare suka hada baki gurin yi mashi godiya kamar zasu durkusa kasa, sun ma rasa bakin magana, sukace su basu san dame zasu iya biyanshi ba, saboda basu da abun da zasu biyashi da shi Allahne kadai zai iya biyan shi, Bazan iya misalta dadin da imam malik yaji ba, daya bayan daya yabisu ya rungume su a kirjinshi..
Daga bisani Ya umarce su da suje suyi wanka kuma in akwai sallar da basuyi ba toh suyi gaggawar ramata dama so yake ya samu su samu natsuwa sannan yayi masu magnar sallar, babu musu suka amsa mashi da toh..💔
Gaba dayansu a part din iyayen su mata da ke a cikin gidan Suka shiga, wanda tun bayan rasuwar su, basu daina amfani da shi ba, masu aikin gidan suna shiga su gyara shi akai akai, kullum zaka taras da part din a atsaftace kamar akwai me rayuwa acikin sa, aduk time da suka ji kewar iyayen su mata, idan suka zo gidan a part din suke huce gajiyar su.
Bayan sun yi wanka sukayi sallah, daga bisani suka fito falo, kamar yadda suka bar sheikh Imam haka suka taras da shi, a kewaye da shi suka zazzauna, ya tambayi ina yan aikin gidan suka ce tun jiya suka hana wani daga cikin su shigowa main falo..
Sheikh Imam yace a kira su, don su girka musu abinci, bai kare maganar ba, Prime minister ya tari da numfashin shi da cewa"basai an kirasu ba, daga rana irin ta yau, ko ruwan gidan ba zasu ƙara sha ba..."
sauran ma suka goyi bayan maganarsa, sheikh imam bai musa masu ba, sai dai yace shi bazai barsu da yunwa ba, yana ji kamar Allah ne ya kaddara zuwansa gare su don ya taimaka musu don haka suyi hakuri su bar shi yayi aikin shi Yana kwadayin ladar da zai samu ta silar taimakon su da zaiyi.
Badan sunso ba, suka amince masa amma fa bisa sharadin ba zasu ci abincin gidan ba.
A karshe shi ya basu shawarar tunda matayensu suna da restaurant na hadin gwiwa kuma bada dukiyar mahaifinsu suka gina shi ba, halal din su ne, me zai hana su kira manager ayi musu order na kayan abinci da duk wani abu da zasu bukata naci..
Shawarar shi suka ɗauka, batare da bata lokaci ba, Mai girma sharafuddeen ya dauko wayarsa bayan ya kunnata ya kira hajiya laura, lokacin data daga kiran nashi kuka yaji tanayi tare da tambayarsa meke faruwa ne? Jiya taga an kawo hajiya saratu asibitin su rai hannun Allah, fuskarta duk ta baci da raunuka garin ya ya hakan ta faru da ita? har su twins ta tambaya suka ce mata hajjaty suke zargin tayi mata haka! Shin dagaske ne? Kuma wacece dattijuwar da aka kawo su a tare? Sannan suna ta kiran layinsa basa samu tun jiya bai dawo villa ba" kamar yar jarida ta tsare shi da tambayoyi ga kukanta daya cika kunnansa.
bai bata amsar tambayarta ba, sai dai ya kwantar mata da hankalinta, yace tayi hakuri su jira shi idan ya dawo villa zaiyi masu bayanin komai, dakyar ya samu ya shawo kanta kafin daga bisani ya bata umarnin tayi musu order na kayan abincin dana sha daga restauranta dinsu akawo masu anan estate dinsu..." maganarsa ta jefa ta a rudani tana kokarin ƙara tambayar shi ya katse kiran..
Cikin abunda baifi mintuna ba, Delivery Vans (motocin daukar kaya) biyu suka fara shigowa estate din, masu dauke da tambarin Royal Courtyard Restaurant.
bayan sun tsayar da motocin a parking space, Delivery staffs suka fara fitowa daga cikin motocin kafin suka fara jigilar ɗauko Containers na kayan abinci da kayan sha daga cikin motar suna kaiwa Cikin Store din gidan..
Lokacin da suke shigowa, Maids din gidan dake lekensu daga sashen su, Sunyi mamakin ganin restaurant staffs suna shigowa ciki da kayan abinci, bayin Allah har sun fara tunanin ko dai wa'adin aikin su ne Ya kare, nan fa hankalin su Ya tashi, dama jiya sun kwana da fargaban abun daya faru da hajiya saratu, zuciya da sake sake sai ta dinga ayyana musu Hajjaty ce ta yi silar abun daya faru da ita, shiyasa ta gudu daga gidan, gayanan zata ja musu ba'la'e idan laifin ta ya shafe su basu san ina zasu sa kansu ba, har saida ma'aikatan gidan suka kammala aikinsu, tukunna maids din suka koma cikin part dinsu cike da zullumi.
Dakyar Sheikh Imam ya samu suka ci abincin kadan badan suna jin dadin shi ba.
Kasa tafiya yayi, saboda ya damu da su, gani yake idan ya haura kafa ya bar gidan zasu kara shiga mawuyacin hali ne, Hakan yasa bai je ko'ina ba, afalon gidan ya zauna atare da su Yana ƙara kwantar musu da hankali..
Su ka ce su yanzu damuwarsu suna son su san awani hali baban nasu Yake a ciki? Yana araye koya mutu, don tun daya gama kururuwarsa adaki basu kara jin koda tarin sa ba, ganin yadda suka nuna damuwarsu Yasa shi ce musu su taso su tafi part dinsa, gaba daya suka mimmike tsaye Yace Ma Chief ya ɗauko mashi abincin da zai ci, store Ya shiga ya hado masa lunch a madaidaicin tray, Ya fito suka dunguma Izuwa Part din baba Obie.
kwankwasa kofar dakin Sheikh Imam yayi tare da ambaton sunansa kusan sau biyar bai amsa ba, cike da damuwa Chief yace bazai bude ba, amma su zagaya ta bayan dakinsa, akwai glass windown da ya fara kokarin fasawa jiya ya kasa, yasan zuwa yanzu quality din glass din Ya ragu zai kara jaraba fasa shi..
In a weak voice Justice Yace nima zan taimaka abude tagar, captain da ziyad ma sukace zasu taimaka gurin balle tagar...
Batare da bata lokaci ba, suka zagaya ta bayan dakinsa cike da sa ran zasu iya balle kofar..
Bayan sun Isa gaban Window din, suka fara kokarin fasa glass din, abunka ga majiya karfi sun haɗu, Naushi suka dinga sakar ma glass din har saida Ya fara barazanar fashewa.
Kubi a hankali kada ku raunata kanku, shiekh Imam ne yayi maganar..
Dakyar da sidin goshi suka samu faskeken glass din Ya fara Tsastsagewa, naushi daya Hateem Ya sakar mashi gaba daya ya zube kasa har saida suka dan ja da baya..
Lokacin da suka dago da idanunsu ba zato ba tsammani suka hango sa a zaune Tsakiyar gadonsa sanye cikin doguwar riga baka mai hula, basu iya ganin fuskarsa ba saboda ya basu baya.
duk da haushin shi da suke ji hakan bai hana sunji sanyi aransu ba, ganin shi araye ba kamar yadda suka zata ba..
labbansu na kerma suka hada baki gurin ambaton sunan shi Baba.
Shiru bai amsa musu ba, kuma da alama yana jin muryoyin su acikin kunnanshi.
Ba irin magiyar da basu yi mashi ba, akan Ya juyo ya fuskance su amma yayi shiru ba alamun zai yi abunda suke so kuma bai tanka musu ba, hakan yayi matuƙar taba zuciyarsu, su ziyad da basu gasgata abunda owais ya labarta musu ba ayanzu sun fara kokwanto akan kakan nasu l.
wani sabon kukan suka kuma fashewa da shi ganin yadda lokaci daya mahaifinsu ya jefa kanshi a mawuyacin hali ya kuma jefa su suma...
Shiekh Imam Yayi kokarin sanya shi yayi magana kodan saboda ya'yanshi da suka damu da shi, amma yayi shiru bai tanka masa ba..
badan sun so ba suka hakura dayi mashi magana, Jikin asanyaye suka fara zame jiki suna barin bayan dakin nasa saboda ganin sa da su ke yi yana kara fama raunin da ke a cikin zuciyar su.
Imam malik yaso yayi magana da shi saboda akwai wani abu dayake so ya fada masa sai dai ya ƙyalesa zuwa lokacin da zasu ke6a saboda idon ya'yansa dake a gurin.
Chief ne kadai Ya rage a bakin tagar yanata kallon bayansa, ba dan akwai makarin daya toshe tagar da dakin ba, da ba abunda zai hana ya dira.
tray din abincin daya zo masa da shi ya fara kokarin turawa ta cikin tagar yaki shiga, dakyar yayi dibarar aje tray din kasa ya dauki warmers din ya dinga jefa su ta tagar ta yadda abincin ciki bazai 6are ba, saboda ya datse murfinsu sosai, hada drinks din Ya jejjefa cikin dakin bayan ya kammala ya sauke ajiyar zuciya..
Cikin raunanniyar muryar shi Ya furta"baba kana jina, jiya ina ta kiran sunanka baka amsa min ba, anan na kwana, wai meyasa kayi min haka baba? Kaga halin da ka jefa kanka damu kanmu ko? Muna zaman mu lafiya, gaba daya ka lalata farin cikin mu, Jiya babu wanda ya runtsa saboda tashin hankali baba, ka kuntata kanka muma ka kuntata mu, ina kaunar da mukeyiwa juna baba? Yanzu ka sanya katanga atsakanina dakai..."
kasa karasa maganar yayi, kumburarrun idanunsa sun cicciko tab da kwalla, Sai kallon bayan shi yakeyi yayi tunanin zai motsa sai dai ko gizau baiyi ba, kamar gunki.
In a broken Voice Ya furta"shikenan, ni zan tafi, ga abinci nan na kawo maka, dan Allah, ka taimake ni kaci, kada ka zauna da yunwa, kuma bana so kaje wani wuri, dan Allah kada ka tafi kabar mu, nasan zaka iya 6acewa idan ka so, amma pls kada ka tafi pls.."
Harya juya zai bar bakin tagar, kwatsam Ya tsinkayi muryarsa wlh bai taba jin muryar data daga hankalinsa irin tashi ba, kamar ba muryar kakansa ba muryar tayi rauni ta kuma disashe..
"Owais, nasan meyasa ka roke ni akan kada in tafi, ba dan kana sona bane, sai dai baka son in gudu batare da ka mika ni ga hukuma an yanke min hukunci ba ko"?
Kamar ba shi yayi maganar ba, dan ko kadan bai motsa daga yadda yake ba.
Shiru owais yayi batare daya iya furta kalma ba, tabbas babu karya a maganarsa,
"Hakane, Inaso ka tsaya ka kar6i hukuncin da za'ayi maka, ta hakane zaka samu yafiyarmu, kuma ta hakane zaka samu sassauci, In har ka mika wuya batare daka bamu wahala ba, amma maganar nadaina sonka, ka daina, tabbas na tsaneka baba, ka karya min zuciyata, ka ci amanar yardar da nayi maka, amma ya zanyi? Inason ka wlh, har yanzu ina kaunar ka, amma ba kamar da da nake ma kallon dattijon arziki mutumin mai mutunci, kuma wlh kaunar da nakeyi maka bazata hana in hukuntaka ba, dole hukuma tayi aiki akanka baba, dole ka girbi abunda ka shuka baba, tabbas idan nabiyewa son zuciyata, zance ka gudu ne saboda kaunar da nake maka, amma in na tuna hakkin rayukan dake akanka, da zaluncin da ka aikata, sai inji bazan iya kyale ka ba, saboda koda na kyaleka wlh Allah bazai barka ba, dole ka ga sakayya tun agidan duniya, nima kuma in ban dauki mataki akanka ba, Allah zai kamani ne wlh..." cikin shesshekar kuka ya kare maganar..
"Jikallena, kada ka damu, kakanka ba inda zaije, nayi maka alkawarin ina nan, kuma zan mika wuya saboda inason ku dauki fansar abunda nayi maku, in har hakan zaisa ku yafe min, duk da nasan ban cancanci ayafe min ba, Owais bazan iya misalta maka halin da nake a ciki ba, danasani bata da dadi ko kadan, gayanan naja ma kaina..."
a hankali ya kifa kansa saman bedmatress din sa, duk akan idon Chief owais, baisan ya akai ya ke jin kamar tausayinsa na shigar shi ba..
"Kai kenan, Inaga wadanda suka yarda dakai, wadanda sukeyi maka kallon jagoran rayuwarsu, kasan kuwa halin da muka shiga jiya izuwa yau? Bai amsa mashi ba yayi shiru kamar ma kuka yakeyi..
"Ka taimaka ka bude min kofar dakinka, Inaji ajikina baka da koshin lafiya, zan kira doctor ya dubaka"
In a low voice ya furta"wata irin zuciyar imani gare ka Owais uhum? Meyasa zaka damu dani? Ko da yake nasan kanayi ne don kada inyi rashin lafiyar da zatayi silar mutuwana batare daka hukuntani ba...."
katse shi yayi"ba haka bane baba, na damu dakai .." bai kare maganar ba ya katse shi"bana bukatar likita Owais, Azzalumin mutun irina bai cancanta aduba lafiyarsa ba, Yaran da muka azabtar agidan kurkukun kaddara, da yawansu idan suka fara ciwo, likitocin mu basa duba lafiyarsu, illa iyaka idan muka ga zasu gaza sai musa Surgeons su farke cikin su su debi sassan jikin su, shine ni zaka ce ka kira doctor ya dubani? Na cancanci hakan Owais..."
bai kare maganarba, Zuciya ta debi Chief Ya daki karfen jikin tagar, Yana faman cizon lips dinsa Ya furta"Ya isa haka baba! Bana son ji! Kabarni inji da abunda ke damuna..." ya fada yana jan numfashi..
Dakyar ya tausasa zuciyarsa, Yai karfin halin Furta"Ina so ka fada min, su wanene sauran Elders..."
"Kaje ka tambayi Aurora ta fada maka"!
"Tace bakowa ta sani a cikin su ba, kuma a halin yanzu tana a kwance gadon asitibi batasan inda kanta yake ba, Kai kadaine zaka Iya fada min su.."
cikin karyayyar murya ya furta"aurora bata da lafiya? Meke damun ta"? Bai amsa masa ba Yace"ba wannan na tambayeka ba, baka cancanki ka sani ba, kaida kaso ka kashe ta Allah bai nufa ba, kawai ka fadamin su wanene sauran Elders saboda tace min kun kai ku goma sha biyu, shida suna jagorantar gidan kurkukun kaddara, sauran shiddan kuma ba'a kasar nan suke ba, sune suke safarar yara daga kasashen waje suna shugo maku da su gidan kurkukun ƙaddara.."
"Owais, naso ace zan iya fada maka su wanene su amman ba zan iya ba, dokar aikin mu ce, amana ne kuma alkawari ne a tsakanin mu, wani bazai tona asirin wani ba, don haka kayi hakuri ba zaka taba ji abakina ba, nidai na mika wuya, Aminina basai kun sha wahalar kama shi ba, shima ya mika wuya zai kawo kan shi, su kuma sauran ba zasu taba canza ra'ayin su ba, tun da har kun ceci rayuwar sauran yaran da suka rage, kuyi ƙoƙari ku sanya musu tsaro, sannan taimakon da zanyi maku shine ku yi gaggawar gano su wanene sauran Elders din ku kama su, idan ba haka ba, kama ni da kukayi kamar kun kashe maciji ne baku sare kan shi ba, ko dai ku kamo sauran Elders din, ko kuma ran kurkukun kaddara ya dawo fiye dana da..."
wani irin faduwar gaba Chief yaji, Cikin rawar murya ya fara yi masa magiya akan ya fada masa su wanene in ba haka ba taya zai iya gano su? su da suke matsafa kama su zaiyi masa wuya.
Baba Obie yace"Owais, Kai fa musulmi ne, meyasa zaka nemi taimakon matsafi uhum? Shiru yayi bai tanka masa ba.
"Ka nemi taimakon Allah Owais, shi kadaine zai kawo maka mafita, duk da banyi Imani da Allah ba, amma bayan da asirina ya tonu na zauna nayi nazari na gane cewa Allah yana da karfin ikon da babu wani mahalukin da yake da shi, zai iya mayar da abu mara yiwuwa ya zama mai yiwuwa tabbas naga ishara akaina Owais, Dan Haka inaso ka mika lamuranka gare sa, kuma bana so damuwar abun da na aikata yasa kayi rauni Owais, bana so kayi sanya, bana so ka karaya, jarumtakar nan taka da kwazon ka, da kaifin basirarka su nake so ka farfado da su gurin bada himma akan aikin ka..."
hakika yayi mamakin kalaman baba Obie, Har cikin ransa yaji dadi daya fara gane Allah daya ne, kuma Yaji dadin karfafa masa gwiwa da yayi duk da bai samu abunda yakeso agurin sa ba..
"Danish Yana araye ko ya mutu"? Kamar daga sama yaji ya tambaya..
"Bani da masaniya akan hakan, tun ranar da muka je kai farmaki ya fada cikin rijiya tare da sabon garkuwar ku amma meyasa ka tambaye ni bayan nasan kasan komai"?
"Hmmm, kawai Ina mamakin wani abu ne, amma ina kokwanto owais.."
"Zan iya sani"?
"Kawai kayi abun da nace maka owais, shi kadaine taimakon da zan iya yi maka ayanzu, sannan idan har aka kawo maku farmakin bazata, Kayi gaggawar sanar dani Owais..."
yaso ya kara yi mashi wasu tambayoyin amma saiya hakura ya bari zuwa wani lokacin yanzu hankalinsa ya karkata akan gano su wanene sauran Elders din..
_"kaddara da bugun zuciyar kurkuku, Ku sanya musu tsaro, rayuwarsu tana a cikin hatsari, da su ka ɗaine za'a iya dawo da ran kurkukun kaddara a halin Yanzu"_
Lokacin da Obie ya furta maganar shi ta karshe, Chief owais bai jiyo shi ba.
baisan Ya tafi ba saida yaji shiru babu motsin mutun tukunna ya sauko daga kan gadon Ya nufi kayan abincin da Owais ya jefo masa ya zukunna yana tattara warmers din guri guda..
*Daga Alƙalamin Boss Bature🔥✍️*
*Ga me bukatar karanta littafin kurkukun kaddara, 500 ne za'a tura Via Opay, 8103884440 Hafsat Bature Muhammad, shaidar biya za'a tura ta whatsapp, 08103884440*