Lokacin da sheikh Imam zai tafi rokonsa suka dinga akan kada ya tafi yabarsu, ya zauna atare da su, ya fahimci kamar suna jin tsoron ya tafi yabar su, gani suke kamar idan ya tafi zasu kara shiga cikin damuwa ne, lallashinsu yayi tare da basu hakuri yace in sha Allah kullum zai dinga kawo masu ziraya sannan su jure su danne damuwarsu kada su bari tun yanzu agane halin da suke a ciki, yakamata su cigaba da zuwa masallaci yin sallah saboda mutane sun damu da rashin zuwansu, su cigaba da gudanar da komai kamar yadda sukeyi ada, cike da ladabi suka amsa mashi da toh har bakin motarsa suka rako shi, har zai shiga ciki ya juyo ya fuskance su, idanunsa cike tab da kwalla, suma idanun nasu kwallarce ta cika su, bayin Allah sun koma abun ban tausayi, kafin tafiyarsa yace ma Owais ya jira kiransa, sannan yace ma sharafuddeen next zuwan da zaiyi zasu raka shi asibiti ya dubo jikin Hajiya saratu da momma daga bisani ya yi musu sallama ya tafi har saida sukaga motar shi ta bace ma ganin su tukunna suka koma ciki jikinsu asanyaye... 🥺
Sheikh Imam yana driving yana share kwallar dake kokarin gangaro masa kan kuncin sa, bakomai ya ke tunawa ba face labarin rayuwar prisoners daya ta6a Zuciyar shi, ga tausayin Ahlin Obie daya mamaye zuciyar shi, shiyasa ya za6i ya tafi yabar su saboda ya samu damar da zai huce radadin da ya ke ji a zuciyar shi..
_____________________________🔥✍️
Da marece💔
a lokacin gaba ɗayan su suna a falo zazzaune kan Sofas zun zabga tagumi kamar masu zaman makoki, damuwar rashin dawowar chief ne ya hana su sukuni, Unexpected suka jiyo motsin shigowar mutun falon, ransu ne ya basu shi ne ya dawo, Kusan atare suka mike cike da zumudin ganin shi, kwata kwata basu lura da halin da ya ke a ciki ba, jikin su na bari suka nufe shi don suyi mashi sannu da zuwa, sai dai ko kallo basu ishe shi ba, bai kula kowannansu ba hatta Taj Da Unaisah, kaitsaye ya juya ya nufi part dinsa batare daya waiwaye su ba, Ya Ilahi, jikinsu ba karamin sanyi yayi ba, ganin yadda Chief ya sauya babu annuri ko walwala akan fuskarsa, abun dayafi daga hankulansu share sun da yayi, Batool har kuka saida ta yi..
Kasa jurewa su ka yi hakan yasa suka wanki kafa suka nufi part dinsa, a bakin kofar dakin suka tsaya gaba dayansu, suka soma yin knocking din kofar hadi dayi mashi magiya akan ya taimaka ya bude musu kofar amma yayi shiru bai tanka musu ba, babu alamun zai bude masu kofar.
Lamarin Ya ɗaure musu kai, sunyi matuƙar damuwa da shi, Yadda ya wuni a cikin ɗaki ba ci ba sha, haka suma suka wuni abakin kofar dakinsa baci ba sha, lokacin salla ne kadai ke tayar da su, haka zasuje suyi sallar ko sun dawo bakin kofar a datse suke taras da ita, da suka matsa da rokonsa akan ya fada musu mai ke damunsa dakyar yace su taya shi da addu'a Allah ya yaye mashi abunda ke damun shi, Ya kuma kawo masa mafita acikin lamuransa, badan sun so ba, suka amsa ma shi da toh, kuma su ka daukar mashi alkawarin zasuyi mashi addu'a, yayi wannan maganar ne acikin dakinsa yayin da suke awaje suna sauraron shi, Zuciyar su ta karaya ba kaɗan ba.
Almost hours, Chief bai leƙo daga part dinsa ba.
Wuni su ka yi kamar marasa lafiya, saboda damuwar da su ka yi da shi.
Ko sun kira layin shi baya yin picking.
10 Best Dating Apps 2024 - Abokiyar Hira Hausa Novels
__________________________________ELDERS🔥
gaba ɗayan su suna a kwakkwance kan wasu hadaddun Plush poolside loungers dake a cikin Katafaren Gidan Gonar su, aljanar duniya an kawata shi da kayan alatu kamar ba za'a mutu a barshi ba, kwata kwata babu riguna a jikinsu sai short, kirjinsu da bayansu a zane yake da tattoo na tambarin kurkukun ƙaddara, sun rufe rabin fuskokin su da gold mask su shida ne gefe da gefen su matasan yan mata ne masu jini a jiki sanye da short gown a jikin su, launin ja, sun saki gashin kansu ta baya, hannayen su ruke da madaidaicin tray mai dauke da expensive bottles na whisky wanda a kalla farashin kowace kwalba yakai 1.5 million dollars, cikin kulawa su ke yi serving dinsu a cikin wasu hadaddun crystal glasses yayin da wasu daga cikin yan matan suke yi masu tausar kafadun su.
daga gabansu wani tankameman Swimming pool ne makil da ruwa launin pure blue sky, ga wasu haɗaɗɗun Floating bean bags da ke shawagi saman ruwan, tantiran karuwai ne kwance asaman su masu dirarran jiki, sanye da swim suit da suka bayyana tsiraicin su, kowaccensu ta manna Sunglasses a idanun ta, saboda haduwar su idan ka kallesu saika sake kallon, sukai su goma sha biyar, daga ganinsu ba jinsi da ya bane, hankalinsu kwance suke shakatawarsu ga iska dake ratsa fatar su..
A hankali ya ke zukar cigarettes din dake a hannunsa idan ya shaƙa har ta hanci yake buso hayakin ta tsabar kwarewa...
"Maganar da Jan harshe ya faɗa ta kona min rai, na kwana da ita acikin zuciyata, arayuwata na tsani mutumin da zai yi min magana da tsawa, bayan haka ya kira ni da kaskantacce, har ni zaice wai ban kai darajar takalmin Elder ba? Kawai saboda sun taba taimakona arayuwa nayi aiki a karkashinsu shine har suka samu damar da zasu yi min gori...." rai abace ya faɗa.
News:
Power Outage: Northern Leaders Meet In Kaduna, Seek Solution
President Bola Ahmed Tinubu has expressed concerns over the ongoing blackout in the Northern region. The north has been in darkness for days as a…
Jan le6e yace"ni banga abun damuwa ba, yanzu fa tasu ta ƙare, kabarsu suji da kunyar duniya, ai sun tabka babban kuskure da suka amince zasu mika wuya, ban taba sanin elder maloho bane sai wannan karon da ya karaya, saboda son ya'ya ya rufe mashi ido, har shawara ka basu basu dauka ba, saboda dakikanci da shafewar basira, ka jira ka gani da kansu zasuyi danasani...."
gaba ɗaya suka bushe da dariya da wannan budaddiyar muryar tasu mara dadin ji...
Jan Ido yace"ni abun daya bata min rai, meyasa suka ki bamu sihirinsu bayan sunce sun tuba? Anya ba tuban muzuru su ka yi ba? saboda nayi mamaki wallahi, Mutanan da suka gaji sihiri suka san dadin shi zaiyi wuya su tuba ta cikin sauƙi"
Ya ƙarashe maganar yayin da yake miƙa ma matashiyar dake a gafensa hannu cikin sauri ta tsiyaya masa whisky a glass ta miƙa masa ya kar6a tare da kaiwa baki yana kur6a.
"Bakin ciki ne da hassada don kada mu samu cigaba, Watakil kuma saboda suna jin fargaban mu farfado da ran kurkukun kaddara, ko kuma suna jin tsoron mu ci amanar su..."
acewar jan le6e, wata yar iskar dariya suka sanya..
A hankali jan wuya ya kur6i whisky din dake a hannunsa kafin yace"yakamata mu san abunyi, ni hankalina bai kwanta da alkawarin da Elder ya ɗaukar mana ba na cewa bazai tona mana asiri ba, yadda ya mutu akan kaunar jikan nan nashi kuna tunanin ba zai iya fada masa komai ba idan ya matsa masa? kuma ina kokwanto dakyar in ba makirar tsohuwar nan tasan ni ba, Kada sai mun saki jiki su fallasa mu..." maganarsa ta dan daga hankalin Sauran Elders din..
Jan Le6e yace"bana tunanin Elder zai iya cin amanar mu, mun riga da munsan halin shi mutunne mai rukon amana, ko da zasu azabtar da shi, bazai faɗi sunayen mu ba,...."
bai Ƙare maganar ba, Jan wuya yace"hmmm dan adam ba abun yarda bane, ni ban yarda da kowa ba, kawai mu nema ma kanmu mafita..." bai kare maganar ba, jan ido yace"me kake nufi"? Wani makirin murmushin gefen fuska ya saki tare da kallon su, sai da Ya zuki tabar hannunsa kafin yace"ku yi amfani da brain dinku mana, idan har muna so mu zauna lafiya batare da fargabar wani abu ba, to fa dole sai mun kawar da Obie family, saboda sun san komai game da kurkukun kaddara da kuma sirrinmu, tun kafin labarin ya fita duniya ta sani, muyi gaggawar tura masu Evil giants under cover of night, su kashe su duka batare da sanin kowa ba, and no one will suspect a thing, kunga daga nan zamu ci gaba da cin karen mu babu babbaka...."
har ya Ƙare maganar tashi elders din basu tanka mashi ba, kamar shawarar tashi ba ta kwanta masu arai ba..
Jan le6e yace"wannan shawarar daka bamu bamai 6ullewa bace, ko kamanta gargadin da jan harshe yayi mana"?
ya tambaya yana kallonsa bai jira amsar shi ba ya dasa da cewa"Idan ka manta bari na tuna maka, Har yanzu Elder shi ke a ruke da masarrafinmu, idan muka kuskura muka ce zamu ci amanar shi wallahi zai yi mana tsiya ne! elder zai iya rufa mana asiri amma abu dayane zaisa ya tona mana asiri ya kuma ƙwace sirihin jikinmu shine idan muka ci amanarsa, Saboda shi baya yafewa wanda ya ci amanarsa, Kuma kai kana tunanin Evil giants zasu Iya farmakar Ahlin Obie bayan Elder Yana araye..."? Ya jefa masa tambayar, nan da nan annurin fuskarsa ya ɗauke ɗuff..
Jan ido yace"kayi tunani mai kyau Jan le6e, ba zamu iya cin galaba akan ahlin Obie ba har sai bayan ransa.."
Shiru su ka yi na ɗan wani lokaci, young ladies din da ke a kewaye da su sun yi zururu da idanun su, ga gajiyar da suka farayi da tsayuwa ba halin su ce zasu zukunna..
"Abun da ya kamata mu maida hankali akai yanzu, shi ne Mu nemo Jan kunne duk inda ya shiga acikin garin nan, saboda shine mai rauni a cikin mu, Idan mukayi kuskuren da Jami'an isod suka riga mu kama shi zai tona mana asiri ne da zarar sun fara azabtar da shi saboda ba shi da juriya ko kaɗan...."
acewar jan le6e, kusan atare suke mike daga kishingiden da suke sam sun manta da batun wani jan kunne dama bawani mahimmanci suke bashi ba, saboda Obie yasa suke tarayya da shi...
"jan kunne baida amfani agurinmu, ko da mun kama shi sai dai mu kashe shi, tun da asirin shi ya riga daya tonu..." jan wuya ne ya faɗa da kakkausar muryarsa.
Jan ido yace"wayarsa a kashe take, wataƙil ya jefar da ita wani gurin don kada jami'ae su bi diddiginsa, duk da sakarcin shi wani lokacin yana da wayau, amma hakan bashi zai hana mu ƙyale shi ba, dole mu kashe shi..." ya karashe maganar tare da kur6ar giyar dake a hannun sa...
"Ranar da muka yi zaman tattaunawa a mafarki, shi kadai ne bai halarta ba, zai iya yiwuwa ya gudu yabar kasar ne.." ya faɗa yana kur6ar whisky dinsa..
"ba zai yi mana saukin kamawa ba, saboda karfin sihirinsa Ɗayane da namu"! Jan le6e ne ya fada rai a6ace..
Jan wuya yace"kubar komai a hannuna, zan nemo shi da kaina, Kuma zan kashe shi..." tuntsirewa sukayi da dariya hahahaha...
"Ya batun dawo da ran gidan kurkukun ƙaddara? Kada ku manta Har yanzu muna da sauran dama fa, idan har muka cika sharuɗɗan da ake buƙata zamu jefi tsuntsu biyu ne da dutse ɗaya, na farko zamu iya canza location din gidan kurkukun ƙaddara, abu na biyu in har mukayi nasarar cika sharuddan karfin sihirinmu zai ƙaru, ta yadda ko Elder bazai Iya ja da mu ba, ..." wani irin annurin farin cikine Ya cika su, jin abun da Jan le6e ya fada, Jan ido yace"tayaya hakan zai yiwu"? Shu'umun murmushi jan le6e yayi"kada ku manta, tun kafin ku san Elder na riga ku sanin shi, atare mukayi yawan duniyancin mu, duk wani sirrin shi na sani, wannan maganar dana faɗa naganta ne a rubuce cikin tarik sijnil ƙadar wanda mahaifin Elder ne ya rubuta littafin da alƙalamin shi tun da dadewa..."
wata irin shewa suka sanya har saida suka tsorata matasan yan matan dake yi masu hidima.
"Amma fa wanda ya riga cike sharuddan a cikin mu, shine zai maye gurbin Elder, shi kuma Elder zai rasa karfin sihirin sa ta yadda bazai iya sarrafa evils din jikin mu ba"
Wannan maganar da jan le6e ya faɗa ta faranta ran Jan wuya, sai faman sakin shu'umun murmushi yakeyi aransa harya fara tunanin yadda zai riga su aiwatarwa saboda ya samu karfin ikon Elder, tsabar hadamarsa yafi so yafi kowan nan su karfin sihiri, ta hakane kadai zai iya mayar da su karkashin ikon shi, don ya cigaba da juyasu son ran shi 😳
💘UNAISA ANGEL💋
A cikin kunnanta ta jiyo sautin dirar Mota a gidan, baiwar Allah a lokaci bacci ne ke kokarin ɗaukarta, tana a kudundune cikin duvet dinta ta kasa runtsawa saboda tunaninsa, ranta ne ya bata shi ne ya shigo gidan..
Jikinta na 6ari ta sauko daga kan gadon, Batool tana akwance gefe daya tayi nisa a baccinta, ta kudundune kanta cikin duvet din ta, Night gown ce a jikin ta Ja, Mayafi ta dauka ta yafa ma kanta, ko takalma bata saka ba, garin saurin ta fita daga dakin har tuntube tayi amma hakan bai dame ta ba, burinta kawai ta je ta dubo in shi ne.
Tana fitowa daga dakinsu ta nufi main falo unexpected Ta hango shi yayin da yake tafiya akan stairs, aranta ta ayyana dama yana fita a irin wannan lokacin idan sunyi bacci?
tayi kewarsa cikin kwanakin nan daya juya masu baya, daga yanayin yadda yake tafiya ta fahimci babu kuzari atare da shi kamar wanda yasha ƙwaya, Cikin sauri tabi bayanshi sai dai kafin ta karasa tuni Ya shige bedroom dinsa, tana isowa bakin kofar room din tayi knocking shiru babu alamun zai bude mata, cigaba da bubbuga kofar tayi tana ambaton sunan shi tare da yi mashi magiya akan ya bude mata kofar.
abun daya ɗaga hankalinta sautin nishin da ya ke saki har cikin kunnanta take jin shi, ganin baida niyar bude mata kuma bai bata iznin shiga ba, hakan yasa batai wata wata ba, ta fara kokarin danna code din kofar da ya ke ya taba nuna mata tun farkon da suka fara shakuwa da junan su, abun daya sa bata taba gigin yi mashi katsadan din ta shiga batare da izninsa ba, saboda ba muharraminta bane, kuma bai dace ta fada masa daki batare da izninsa ba, batasan awani yanayi zata taras da shi ba.
Nishin da taji yanayi ne yasa ta razana har bata san sa'adda ta saka code din kofar ta bude ta, a fujajen ta dira kafafunta cikin dakin, wani irin burki taci, lokacin da idanunta suka hango mata shi, har ya cire kayan jikin shi, yana daga tsaye gaban gadonsa ya bata baya, boxer short ne kadai a jikin shi, Ya ruƙe Syringe mai dauke da ruwan allura a cikin shi, yana kokarin caka ta a upper arm din sa..
"My hubby...." dakatawa yayi jin muryarta a cikin kunnan shi, kwata kwata baisan da zamanta adakin ba, hatta knocking din da ta dinga yi baiji ba saboda hankalin sa baya a tare da shi, kawai so yake yayi ma kansa allurar ko ya samu sassaucin radadin da zuciyar sa ke yi masa, kwana biyu rabon da yayi bacci saboda pressure din daya daura wa kansa na gano su wanene Elders, bai da wani kwanciyar hankali idan har ba gano su yayi ba.
A hankali take tafiya tana tunkarar shi, daga bayan shi ta tsaya tana duban gefen fuskarsa daya jike sharkaf da gumi..
"Me ke damun ka? Meyasa ka juya mana baya? Ka hana zuciyata sukuni, saboda kai ko bacci bana iyayi, na rasa gane kanka acikin kwanakin nan! ..." ta fada tana dan girgiza kanta idanunta sun cika da kwalla..
"Why would you inject yourself? Aren't you well?” Ta fada araunace.
da wata irin kakkausar murya ya furta“I don't want to see anyone close to me! Don't you dare take one step closer to me! ki fuce min daga daki..."
gabanta ne ya faɗi a rude take kallon bayansa, kamar ba daga bakinsa kalaman ke fitowa ba.
Ta razana sosai, Cikin rawar murya tace"Husband to be, yau ni kake kora daga dakin ka? Me yake damunka ne? A tunani na damuwarka tawa ce, bai kamata ka boye min ba, Pls ka fadamin zan taimaka maka mu shawo kan matsalar..."
numfashi Yaja tare da furzar da shi, ganin taki tafiya yasa shi daka mata tsawar da ta tsoratar da ita
“Don’t you dare make me repeat what I said! Get out of my room before I do something bad.”
gyada kai tayi, idanun ta cike tab da kwalla ta soma ja da baya tana cigaba da kallon bayansa, ta lura ko kallon ta baison yi, abu kamar aikin asiri in a short time ya canza musu.
A hankali ta juya takai hannu zata buɗe ƙofar, sai kuma ta fasa saboda zuciyarta dake azalzalarta akan kada ta tafi, ta tsaya taji meke damun sa.
Sakin handle din kofar tayi da tunanin tayi ko karta aikata abunda zuciyarta ke saqa mata, ga tunanin nasihar dadynta amma bata jin zata iya barin shi a halin da yake ciki, juyawa tayi slowly ta nufe shi tana karasawa batay wata wata ba, ta faɗa kan bayansa, she slowly wrapped her arms around his waist, ta daura tafukanta a saman shafaffen cikinsa, lokaci ɗaya ya tsinci kanshi awani irin yanayi mai wuyar fassaruwa, har baisan sa'adda Ya saki sirinjin hannun sa ba, wata irin kasala ta haifar masa, lumshe idanun shi yayi a hankali yana jin bugun zuciyarta da hucin numfashinta on his neck.
Yatsunsa taji akan hannunta yana kokarin banbareta don ya rabata daga jikin shi, cikin sauri ta furta"na roke ka, dan Allah, dan soyayyar da kake yiwa manzon Allah SAW kada ka kore ni, ka barni atare dakai, inaso naji meke damunka, ko ban sama maka mafita ba, zan tayaka addu'a Allah ya yaye maka damuwarka, baka taba barin mu cikin damuwa ba, taya kake tunanin ni zan iya barin ka a mayuwacin hali irin wannan"?
Kalamanta sun sanyaya zuciyarshi, sai dai baya jin zai iya fada mata abunda ke damunsa, baisan ya zasu dauki abun ba idan suka ji cewa kakansa ne Elder mamallakin gidan kurkukun kaddara, mutumin daya azabtar da rayuwarsu, Ya Ilahi, Ji yake kamar kowa zai juya masa bayane..
wata irin kara mai tattare da bakin Ciki Ya fasa, tuni shatun jijiyoyin goshinsa dana wuyansa suka fito ruɗu ruɗu saman fatarsa, tun da ya yi tsawar gaban ta ya faɗi rass hankalin ta ya ƙara ta shi duk tabi ta ruɗe..
Nauyin jikin shi daya sakar mata ne yasa ta gaza jurewa saboda yafi karfinta nesa ba kusa ba, aikuwa gaba daya suka faɗa saman bedmattress dinsa.
a rubda ciki ya faɗa yayin da take akwance saman bayansa, sam sun kasa motsawa har na tsawon mintuna, dakyar ta yi kokarin raba jikin ta daga na shi, da wata irin kasala ta mike zaune tare da zuba mashi idanunta da suka cicciko da kwalla.
Duk da batasan meke damunsa ba, amma hankalinta ya tashi ta kuma ji tsantsar tausayin sa acikin zuciyar ta, jikinta harya fara daukar ɗumi saboda zafin jikin shi da ta goga silar haɗuwar da fatarsu tayi.
ya kasa jure radadin da yake ji ne, baiso ya bayyana rauninsa a fili ba, duk yadda yaso ya danne damuwarsa ya kasa bawan Allah.
Cikin shesshekar kuka ta dinga tambayar shi meke damunshi har ta haƙura ta yi shiru saboda yaƙi furta kalma, daidaita nutsuwarta tayi cikin sanyin murya ta fara zuba mashi kira'ar alqur'ani mai tsuma zuciya, lokaci ɗaya ya fara jin tamkar ana wanke damuwar da ke acikin zuciyarsa, bacci ne ya ziyar ce shi a hankali ya fara lumshe idanun..
bata kaiga dire ayar data janyo ba, kwatsam ta fara jin gyangyaɗin bacci har bata san lokacin da ta sulale gefen sa ta kwanta ba, Kafin wani lokaci, wani wahalallan Bacci yayi awon gaba da su, ikon Allah kenan bai kaiga yin sedative injection din da ya so yayi ba, sai gashi silar karatun qur'anin da Unaisah tayi masa yasa shi yin bacci...💔
sai da suka shafe tsawon awanni bakwai suna yin baccin, tun karfe ɗaya da rabi na dare, har karfe bakwai na safe basu farka ba kamar wadanda suka sha sleeping pills.
Tun da garin Allah ya waye Batool taga babu Unaisah a dakin, har toilet ta duba bata ganta ba, hankali atashe ta nufi dakin aunty ummi don ta dubo ko taje can, tana zuwa taga babu unaisah nan ta fada ma Aunty ummi bata ganta adaki ba, hankalinsu atashe suka fito neman ta, sako da lungu na gidan sun duba basu ganta ba, kuma basu kawo ma ransu tana adakin Chief ba, har dakin Taj suka shiga a lokacin yana a zaune kan darduma Yana jan cazbaha bayan sun gaishe da shi, Ummi ta tambaye shi Unaisah batazo nan ba, yace musu ko gifcin ta bai gani ba amma kada su damu yasan duk inda taje ba zata wuce cikin gidan ba, ya fada tare da dauko wayarsa ya danna mata kira tana ta ringing ba'ay picking ba..
__________________________________🔥💋
A hankali ya soma kokarin bude idanunsa da sukayi mashi nauyi ga wata kasala data baibaiye jikin shi, jin hucin numfashin mutun a gefen shi kasa kasa cikin natsuwa ya ke fita, yasa shi saurin karasa bude idanun nasa.
tamkar wanda ya yi loosing memory dinsa, ya ɗan razana da ganin mace a kwance saman gadon shi tana bacci, kuma suna fuskantar juna, kitson kanta yabi da kwallo, dan mayafin da ta yafa ma kanta tuni ya bar jikin ta, kwakwalwarsa ce ke kokarin tariyo masa abun daya faru!
Nannauyar Ajiyar zuciya ya sauke, tunawa da komai daya faru tun farkon shigowarta, yayi mamakin baccin daya sha, wani iko na Allah kwata kwata babu inda keyi masa ciwo, saima wata lafiya dayaji a jikin shi, kamar ana dawo masa da kuzarinsa, yana ji aransa silar kira'ar qur'nin da Unaisah tayi mashi ne, kuma dama shi qur'ani waraka ne.
Slowly ya zame hannayensa daga kan gefen fuskarshi, Ya daura tafinsa saman lallausar sumar kanta da aka kitsa, A hankali Yake shafa gashin nata har na tsawon mintuna, kafin ya dan dago da face din tata, hakan ne ya bashi damar kallon fuskarta dakyau, wata irin nutsuwa ce ke shigar shi, yayi fatan ace bai farka daga baccin daya dauke shi ba, saboda kwanciyar hankalin daya samu..
Tunawa da sallar asubahi da bai yi bane yasa shi saurin mikewa ya sauka daga kan gadon, shaf shaf ya fada toilet yayi wanka kafin Ya dauro alwala, Ya fito waist dinsa daure da towel, Ya nufi walk in closet dinsa Ya shirya kansa cikin jallabiya, kafin ya nufi prayer corner dinsa after Ya gama sallar, yayi addu'o'i har da hawayensa, kafin daga bisani Ya mike Ya nufi gadon, a hankali ya kwanta yana fuskantarta, yaso ya tashe ta tayi sallah sai dai ya kasa yin hakan saboda bai son ya katse mata baccin ta, ya lura kamar ba ta samu isasshen bacci, ya fahimci hakanne saboda alamar daya gani saman kwarin idanunta da sukayi ja, kuma yasan shine silar shigarta halin da take a ciki, tsantsar tausayinta da kaunartane suka mamaye zuciyarsa ko gajiya da kallon ta ba ya yi, mutumin da saboda kamun kansa da gujewa abun da zai sabawa mahaliccinsa bai ta6a bari ya ke6anta kan shi da macen da ba muharramarsa ba, balle har su hada shimfida, amma yau saboda halin da yake a ciki ya kasa ankarar da kanshi kuskuren yin hakan saboda a buqace yake da son samun wanda zai kwantar masa da hankali..
Akan idonsa ta fara yamutsa pinkish lips dinta da suka bushe ƙamas.
ziraran eye lashes dinta sai kerma suke yi, Tunawa yayi da ranar farko daya fara ganin fuskarta lokacin data kira sa video call da kuruciyarta, a ranar kasa runtsawa yayi saboda tunanin yar tahalikar nan..
Da alama baccin nata ya ƙare, ƙoƙari take ta bude idanun ta da suka kumbura saboda kukan da ta sha, daura tafin hannunsa ya yi a saman gefen fuskarta, a ɗan firgice ta zare idanun ta.
kaitsaye suka shiga cikin nashi wani irin shock taji ganin Chief agabanta, ganin yadda ta ruɗe ne yasa shi sakin tsadaddan murmushin nan na shi, baisan ya ƙara jefa ta a rudu ba, duk tabi ta dabarbace sam takasa ci gaba da kallonshi, saboda yanayin data tsinci kan ta..
"Na samu bacci silar karatun alkurnin da ki ka yi min, I can't thank you enough baby..."
ya faɗa tare da dan shafa sajen gefen fuskarta da ya kwanta luff, shiru tayi tana jin yadda zuciyoyinsu ke bugawa saboda kusancin da suke da juna..
“I’m so sorry, I made you cry, nima bada son raina ba, banso kika ga raunina ba, na kasa jure abunda ke damuna ne.." ya fada yana kare mata kallo.
In a cool voice tace"ba laifin ka bane, daga zuciyarka ne, I understand that something bad happened that put you in this difficult situation of worry, but I want you to know that I will never leave you in such a situation, It is my duty to calm you down, and I will help you find a solution after that, I will remind you, no matter what, kada ka bari hankalinka ya gushe, jarumtakar nan taka da nutsuwarka su nakeso na gani atare da kai, komai ya same mu arayuwa muyi hakuri mu mika lamuran mu ga Allah shine zai nema mana mafita".
har cikin ranshi yaji dadin kalamanta masu sanyaya zuciya, harya fara tunanin irin rayuwar farin cikin da zasuyi idan sukayi aure, zai more rayuwarsa saboda samun mace tagari kamar ta.
"Ka fada min meke damunka pls, amma idan sirrinka ne da bai kamata in sani ba, to kada ka sanar dani, kuma koda baka fadamin ba, nayi maka alkawarin zan tayaka da addu'a Allah yaye maka damuwarka ya kuma kawo maka mafita acikin lamuranka"
bai san sa'adda ya saki murmushi ba wanda har sai da fararen hakoransa suka bayyana, saboda dadin kalamin ta, ita kanta batasan ya akai ta samu kwarin gwiwar furta masa su ba, kamar ancire mata jin nauyin sa hada karin tausayinshi daya mamayeta.
“My secret is yours, Unaisah, Even if no one understands me, I’m sure you will understand me, sai dai bana jin zan iya fada maki abunda ke damuna a halin yanzu saboda banaso na daga hankalin ki, amma nasan zaki ji agurin daddynki idan na fada masa" cike da kasala ta dago da kanta, ta fuskance shi idanunsu suka shiga cikin na juna, hakan yasa numfashinsu ya dinga gaurayewa dana juna saboda qarin kusancin da suka samu da junansu..
Tsananin tausayinsa ne ya kara kamata, ganin yadda cheeks dinsa su kayi suntum, reddish eyes dinsa sun kara ciza launinsu hasken ya rune zuwa ja, bakomai take hangowa cikin idanun nasa ba face tsantsar damuwa da tashin hankali.
Cikin muryar raɗa ya furta
“Thank you for taking care of me, I can't wait to have you as my wife…”
kunyar shi ce ta kama ta, dama dakyar take jure kallansa saboda nauyinsa da take ji..
"Ku yi hakuri, jiya na bar ku kuna ta jirana, ban kuma kira na fada maku bazan dawowa ba, banji dadi ba"
"Kada ka damu, komai ya wuce.."
"Kin lura da time..." ya fada tare da nuna mata katafariyar agogon dake manna jikin bangon dakinsa .. ' kallo daya tayi mata tare da jinjina kanta..
"Ki shiga toilet dina ki yi alwala...
Saukowa tayi daga kan gadon ta nufi toilet dinsa, tana tafiya kamar wadda ƙwai ya fashe mawa akai, gabanta nata faduwa, kwata kwata bata son shiga toilet dinsa saboda glass wall din dake gare sa wanda ke a waje na iya ganin komai na cikinsa, batasan ya zatayi amfani da shi ba, abun da take ma zullumi kada Chief ya gane mata budurcin ta anata wautar 😂
Agaban kofar toilet din ta tsaya tana dan zazzare idanunta kamar wadda tayi ma sarki karya fadawa suka turketa.
ita a wurin ta kauyacine ta tambaye shi ya ake amfani da toilet din, kanta ya kwance, ranta ne ya bata ta juya baya taga idan yana kallon ta, juyowar da za ta yi keda wuya, idanunta suka sauka akan nashi yayin da yake gyara kwanciyar shi.
Idanunta ne suka dinga nuna mata kamar murmushi ya ke sakar mata, zuciya da sake sake saita dinga ayyana mata da gangan yace ta shiga toilet dinsa don ya ganta..
lumshe idanun shi ya danyi, lokaci daya ƙwaƙwalwarsa ta fara tariyo masa maganganun da suka tattauna tare da grandpa dinsa.
"Wife to be...." can kasan makoshi ya furta..
Kamar jira take ya kira sunanta, jikinta na bari ta baro bakin toilet din, don batajin zata iya shiga.
Daga gaban gadon ta tsaya tare da amsa mashi "Naam ..."
"Idan ba zaki manta ba, last time mun yi magana akan hotunan dake a cikin diary din yarinyar nan, har yanzu baki tuna komai dangane da su ba..."?
Ya tambaya akagare da son jin amsar ta, shiru tayi jim tana kokarin tunanowa, bakomai ya fado mata arai ba face hotunan nan na dakin su da suka tsin ta, dama tana ta kokwanton kamar a cikin diary din suke.
Cikin sauri ta furta"Na tuna, bari naje na dauko maka"
Calmly ya furta okay, cikin sauri ta fuce daga dakin har wani ajiyar zuciya take saukewa.
Mikewa zaune yayi tare da jingina bayansa jikin head board dinsa, dawowarta kaɗai ya ke jira..
Bayan ta koma dakin bata iske kowa ba, sai da tafara shiga toilet ta watsa ruwa tayi alwala sannan ta fito ta dauko hijabi tayi sallah a tsanake, bayan ta gama ta dauko hotunan data ajiye a cikin drawer chest, cikin sanda ta wuce part dinsa batare da wani yaganta ba.
After some minutes Yaji motsin shigowarta, da sauri ya kalle ta, karasowa tayi tare da samun wuri gefen gadon ta zauna, hannun ta ruke da hotunan ta miƙa masa"tun da jimawa na tsince su a karkashin gadon mu, a lokacin ina tsaka da neman wayata, bansan su wanene akan hoton ba, kuma ban san waya kai hotunan dakin mu ba.."
kar6ar hutunan yayi daga hannunta, ya shimfida su akan tafinsa tare da daura idanunsa akansu, lokaci daya yanayin fuskarsa Ya nuna tsantsar radani da mamaki..
"A daren ranar da muka baro part din daddyna, mun dawo nan saboda wayata da nake nema, ni da Batool muna tsaka da neman wayar acikin dakinmu, kawai sai naji Batool tace min a ina kika samu wadannan hotunan? Nan nake fada mata inda nagansu, sai tace To ay mutumin aunty Ummi ne wannan, Ita kuma wannan kin tuna ƙawarta baturiya wadda sukazo airport atare wata fara sol launin idanunta blue, da tayi wannan maganar nan take sai na tuna ta, itace kawar aunty Ummi mai suna NATASHA, sai nace mata Amma taya akai tasan Mutumin aunty ummi ne wannan, shine tace Zata faɗa mini, amma dan Allah kada in fada ma aunty Ummi, saboda ta ta6a gargadin ta, akan bata son ta ta6a mata waya, sai nace mata naji ba zan fada ma Aunty ummin ba..." tun da tafara Kora masa jawabi, Chief owais ya kafe ta da idanunsa da suka cika da al'ajabi
"Shine tace min wai ranar aunty ummi ta shiga toilet aka kira wayarta, garin ta dauka kawai tayi picking call din, nan tagan shi kwance acikin kwamin wanka, kumfa ta lullu6e jikinsa sai fuskarsa kadai ta iya gani, a fahimtana shi baiga fuskar Batool ba, ita kadai ce ta gan shi watakil ta kare front camera din wayar da yatsan ta tun da ba sanin takan waya tayi ba, koda ta fada mini hakan, mamaki ne ya kamani, har na fara kokwanton maganarta, saboda nayi mamakin ta yadda har ta iya ruke kamannin fuskar mutumin da tagani farat ɗaya a video call bayan haka waye ya kawo hotunan adakin mu"? Ta fada tamkar tana tambayarsa..
"A tunanina Aunty Ummi ba zata taba yin gangancin da zata kawo hotunan dakinmu ba, tun da har ta ta6a gargadin Batool akan daukar mata waya thats mean bata so tasan sirrin ta"
tunkan ta karasa maganar ta lura da yanayinsa da Ya sauya, shiru tayi tana jiran jin me zaice..
Miƙa mata hoton Alhajin yayi"me zan yi da shi" ta faɗa tare da ruke hoton a hannun ta.
"Kin san wanene wannan mutumin"? Girgiza mashi kai tayi..
Murmushin takaici ya dan saki tare da cewa“He is your mom's uncle, Alhaji Musa Wadata, former president of our country After that, his sister Hajiya Laura is my daddy's second wife"
Bai karasa maganar ba, ganin yadda ta zabura ta mike tsaye tana zazzare idanun ta cike da rudu akan fuskarta..
Labbanta na kerma tace"tayaya hakan zai yiwu? Me ya kawo hotonsa a dakin mu"!
"Ina zargin mutumin nan yana ɗaya daga cikin Elders na gidan kurkukun kaddara, in har ya zamana dagaske hotunan nan sune acikin diary din yarinyar, a labarin da kika bani, ta ta6a fada maki nickname din mahaifinta ne Jan wuya, sannan a shafin farko na diary din ta akwai nickname din sa a rubuce, jan wuya kuma yana ɗaya daga cikin Elders kamar yadda Danish ya faɗa mun nicknames dinsu da suke amfani da su a gidan kurkukun, bayan haka kawar ummin nan, zai iya yiwuwa mahaifiyarta ce ko marikiyar ta ..."
tashin hankalin da ba'a saka mashi date, da tsantsar rudani suke kallon kallo atsakanin su, cikin rawar murya tace" In kuwa hasashenmu ya zama gaskiya, to kenan bai rabu da Aunty Ummi ba? Yana atare da ita, Sannan shine ya sadaukar damu! Ni da babyn Uncle shureim..."?
Dakatawa tayi da yin maganar kamar an tsikare ta, lokaci daya takuma zare idanunta alamar ta tuna wani abu
"Are you okay," ya faɗa yana dubanta, Jinjina mashi kai tayi adabarbarce tace"shine.. ! wallahi shine.. mutumin nan shine Jan wuya mahaifin Unaizah, saboda Ina zargin Yarinyar Wurinsa yar uwar Unaizah ce saboda kamannin su ya 6aci, kamar twin sister din ta ce, a ranar dana fara ganin ta sai da na razana..."
Nan ta labarta masa farkon haduwar su da Zeenatu, wlh sai yanzu ya gane dalilin dayasa farko daya daura idanunsa akan hoton unaizah yai tajin kamar yasanta aran shi, ashe saboda kamanninta da zeenatu ne, Ya San ta, tun da kuruciyarta, lokacin da Hajiya sarah take zumunci da hajiya saratu tana yawan zuwa da ita estate ɗinsu kafin daga baya ta ɗauke kafa da zuwa..
gaba daya sun rude da lamarin, Cikin sauri ta kuma cewa"bayan haka, rannan ina tsaka da neman Sim card din da daddyna ya saka min acikin backpack din Unaizah, aranar ne ma Na curo texbooks din ina dudduba su, ina da tabbacin silar neman sim dinne yaja har hotunan suka faɗo daga cikin diary din batare dana ankara ba, wani abu daya daure min kai, ina a zaune tsakiyar gadonmu Ina tsaka da neman sim din saiga sajeed Ya shigo dakin mu kamar baya a cikin hayyacin shi..."
nutsuwa Chief yayi yana sauraranta yayin da take basa labarin, idan tana bada labari tiryan tiryan babu kuskure kamar yar jarida sai ya dinga tuna mommynta, ya faminci halayenta da dabi'unta sunfi karfi ta bangaren mommyn ta.
"Da ya sake jaraba Kiran layin wayarsa, kwatsam sai muka ga kiran ya shiga sai dai ba'a daga ba, daga baya munyi waya da me lambar har na bata hakuri nace wrong number ne na kira, amma sai na nemi alfarmar inaso mu dinga zumunci da ita saboda ta kwanta min arai na, toh daga nan ne muka shaku da junan mu, kusan kullum sai ta kirani, ko bata kira ba, to ni zan kirata ne, wlh bantaba sanin mommyna bace, sai a ranar dana kira layin ta, bayan ka fayyace min komai daya faru da ita, nayi al'ajabin taya akai sajeed yayi guessing number din zeenatu"?
Dafe kansa yayi da tafin hannunsa, gaba daya suka zurfafa tunanin su.
"A labarin da kika bani, kince Sajeed Ya fada maki zai iya gane fuskar mahaifinsa Idan ya gansa ko"? Jinjina mashi kai tayi"Eh, haka ya faɗa mini, kuma wani abun daure kan nidai dana kalli hoton akaro na farko sai naga sunyi kama da Sajeed kamar yayi kakinsa.."
baisan ya akai ya kara jin ƙarfin gwiwa atare da shi ba.
"Babe abun da nakeso dake, komai da muka tattauna a tsakaninmu mubar shi a matsayin sirri, kija baki ki yi shiru, har yanzu bamu kai ga tabbatar da abun da muke zargi ba tukunna, masu iya magana sunce idan baka iya kama 6arawo ba, shi barawon sai ya kama ka, ina fata baki fada ma auntynku Ummi kinsan labarin su ba"!
Jinjina mashi kai tayi"ban fada mata ba"
"Good Girl, kibarni da ita, ni zan tuntubeta dakaina, agurin ta zan samu karin bayani dangane da shi, in har ta bamu hadin kai, zamu yi amfani da ita gurin kama sa, don ba ƙaramin shaidani bane, mutunne mai hadarin gaske, tunkararsa abune mai wuya, kamasa bazaiyi mana sauki ba, dole saida dabara sai kuma mun hada da addu'a..."
Har ya ƙare maganar bata farfado daga duniyar tunanin data lula ba, maganganun Unaizah ne suka fara dawo mana acikin kwakwalwarta, tabbas za ta yi farin ciki kuma zatayi bakin ciki idan hasashen su ya zamana gaskiya akan Uncle din mommynta, hakan na nufin Unaizah yar uwarta ce ta jini! ya ilah, wlh Alwashine ta daukarwa kanta, sai ta kashe shi da hannun ta..
Cikin sanyin murya tace“idan har muka tabbatar da zarginmu akansa, nima zan bada gudummuwata gurin hukunta shi, saboda nayi ma Unaizah alƙawarin abu biyu, kafin mutuwarta, ta rubuta min wasika don in ba Mommynta da daddynta su karanta, abun da yasa ban baka wasikar ba, saboda amana ce ta bani, sannan ta roke ni akan in daukar mata fansar cin zalun da mahaifinta yayi mata, tana so in kashe shi da hannu na..."
kasa karasa maganar tayi saboda kukan daya sarke makoshin ta, sakamakon tunawa da Unaizah, ta fama raunin da ke kwance a cikin zuciyarta.
Sauko wa yayi daga kan gadon, ya tsaya daga gabanta suka fuskanci juna, tuni ta jima da sakin hoton hannun ta Ya fadi kasa.
cikin shesshekar kuka tace"Ka taimaka min dan Allah, nasan bani da karfin da zan iya kama shi, amma in har kuka kama min shi zan iya kashe shi, wlh na tsani mutumin nan fiye da yadda na tsani mutuwa ta, ban taba ganin mutun mara imani, tantirin fasiki kuma azzalumi irinsa ba, inaso yaji radadin da Unaizah taji a lokacin da take akan gabar mutuwa, zan hada masa jini da majina akan fuskarsa, fiye da yadda Unaizah tayi kukan bakin cikin daya kunsa mata, Ka taimaka min hubby, ku barni in kashe shi na roke ka..."
hawayen dake sauka kan kuncin ta ya soma sharewa da tafin hannunsa.
"Kukan ya isa haka Unaisah, in har ya zamana shi ne mutumin da muke zargi, ni Chief nayi maki alkawarin zan taimaka maki gurin cimma burin ki akansa, koda hakan zai saba ma doka ne, Ni zan yi maki hanyar aiwatar da hakan ta cikin sauƙi, a hannun ki zai mutu Unaisah, sai kin azabtar da shi kafin ki kashe dan iskan..."
batasan sa'adda ta soma sakin murmushin farin ciki ba, gani take kamar har ma sun riga da sun kama shi saboda zumudin ta aika shege lahira, ada fansar mutun daya tayi niyar dauka akansa amma ayanzu da take zargin Uncle din mommyntane, Sai ta kara fansar mutun biyar akansa, Fansar auntyn Ummi da fansar abun da yayi ma mommynta, da kuma fansar prisoners, Cikon fansar mutun na biyar da zata dauka shine Uncle Uzair in har akayi bincike aka gano sune suka kashe shi 🔥
Batai aune ba taji ya manna mata peck on her Cheeks, cike da jin kunyar shi ta sunnar da kanta kasa..
Bata bar bedroom dinsa ba, har saida suka yi breakfast atare, suka ciyar da junansu kafin daga bisani tay mishi sallama bayan ta roke shi ya taimaka ya sauko down ya gaisa da su aunty ummi da batool saboda sun damu da shi yace mata karta damu zai zo su gaisa..
*Daga Alƙalamin Boss Bature🔥✍️*
*Ga me bukatar karanta littafin kurkukun kaddara, 500 ne za'a tura Via Opay, 8103884440 Hafsat Bature Muhammad, shaidar biya za'a tura ta whatsapp, 08103884440*