Dalilin da ke sa Yawan Fitsari ga Mace Mai Ciki
Mafi yawancin Mata masu ciki an san su da yawan lailai, amma wadansu basa laulayi kwata-kwata in ka gansu ma ba zaka dauka suna da cikinsa, sai dai kawai nunawar da yakan yi a jikinsu.
Yawan fitsari na ɗaya daga cikin abinda ke damun mata masu ciki, amma hakan ba matsala bane.
Me ke kawo Yawan Fitsari ga Mace Mai Ciki?
Dalilin da ke kawo Yawan Fitsari ga Mace Mai Ciki abu guda biyu ne wanda suna hada da.
Na Farko:
Watannin farko na lokacin da mace ta sami ciki akwai wani abu da ake kira d hormonal changes, Wanda waɗansu dag cikin hormones na jikin ta ke ƙaruwa waɗannan hormones din sun haɗa da Progetrol da HCG dukka sukan ƙaru a jikin mace ta kuma yanayin gudun jini wato (Blood Flow) a turance, yakan sanya mace ta riƙa yawan fitsari na wani lokaci. Da zarar cikin Kum ya girma zata daina, Amma hakan ba matsala bane kuma ba'a shan magani.
Na Biyu:
Lokacin da ciki yayi girma ya kai aƙalla wata bakwai (7) zuwa wata tara (9), wannan girman cikin yana danne bladder (inda fitsari ke taruwa) shima yana kawo Yawan fitsari, shima wannan ba matsala da zarar ta haihu komai zai koma daidai.
Shawara Ga Maza.
Ya kamata Maza su kula sosai domin lokacin da mace ke da ciki tana buƙatar kulawa sosai ta wajen abinci, Magani da kuma ba'a son mace mai ciki da dinga shiga damuwa ko ɓacin rai, domin hakan na iya shafar abin da ke cikinta.
Maza ku ji tsoron Allah ku kula da matan ku musamman masu ciki, idan tana son abu kana da hali ka yi mata.
A lura ba kowani irin aiki ya kamata Mace tayi ba musamman aikin ƙarfi.
Daga - Dr. A'isha Yusuf
Tags
Kiwon Lafiya