Jan Hankali ga masu amfani wannan Hanya ta Takarar Iyali

Jan Hankali ga masu amfani wannan Hanya ta Takarar Iyali


JAN HANKALI ZUWA GA MASU ANFANI DA WANNAN HANYA TA TAZARAR IYALI DA KUMA MASU SAKA MA CLIENT ITA.

Yau ya dace ayi tambihi ko Jan hankali da Kuma wayar dakai zuwa ga magidanta musamman Mata da kuma metron metron da Nurses dinmu masu applying Implant/Implanom wato ashanar hannu ko rubar hannu.

Expired Date:

Abu na farko Daya dace Mai applying wannan rubar yayi la'akari dashi shine lokacin da rubar zata Kare aiki bawai aba lokacin da take dauka ajiki ba.

Hakkin kowace mace ce ta nemi a gaya Mata, a duba yaushe rubar zata Kare aiki bawai a tsaya lissafin lokacin da take dauka ajiki ba.

Misali:

Duk Rubar da aka saka sama da wata 20 da suka wuce lallai ya zuwa yanzu ta gama aiki zama lafiya acire. Misali Mata ta saka rubar wata 12 da suka wuce Kuma akai rashin sa'a wacce akai anfani da ita xata Gama aiki 2020 Misali kunga zata daina aiki alhalin a wajen matar lissafin aikin ta Bai kareba tunda munsan tana daukan shekaru 3 ne. 

Dan Haka kowace mace tana da ikon ta nemi a gaya Mata ko a karanta Mata expired date na Implanom dinta, wannan zai Bata damar sanin lokacin mutuwar rubar ta Koda kuwa lokacin Daya dace ace ta dauka da ita rubar.

Ga masu Tambaya kuna iya turawa tambayoyin ku, in sha Allah za a amsa maku

Naku Kabir Yusuf Danwurin Dutsi.

Post a Comment

Idan kuna da tambaya akan abinda Baku game ba ko kuma kuma Neman littafin da babu a nan kawai ku ajiye tambayarku a ta comment ko wani shawara da Zaku bamu.

Previous Post Next Post

Sponsored Link

Sponsored Post