Maganin Sanyin Mara

Maganin Sanyin Mara

Sanyin Mara

MAGANIN CIWON SANYIN MARA DA DATTIN MARA.

 Ana hada waɗan nan magunguna guri guda domin magance matsalar datti a mara ko sanyi a mara ko ciwon mara da duk wata matsala data shafi mara mace ko namiji(amma banda mace mai ciki)!

ABINDA ZAA NEMA

1. Kurkum(Tumeric)

2. Kaninfari (clove)

3. Citta(Ginger)

4. Tafarnuwa (Garlic)

YADDA ZAA HADA.

 Kowanne magani da muka ambata a sama zaa samu danyen sa ne, ma'ana wanda bai bushe ba,sai samu jarkar Faro a bare tafarnuwa a zuba a ciki haka nan suma sauran kurkum da citta a bare bawon dake bayan su sai a yayyan kasu a zuba a cikin jarkar a kawo kanin fari a zuba sai a cika jarkar da ruwa.

A barshi zuwa kwana 3 sai a sha kofi daya kullum, idan ya kare sa a hada wani, ana so mutum yayi kamar sau 2 ko 3.

Post a Comment

Idan kuna da tambaya akan abinda Baku game ba ko kuma kuma Neman littafin da babu a nan kawai ku ajiye tambayarku a ta comment ko wani shawara da Zaku bamu.

Previous Post Next Post

Sponsored Link

Sponsored Post