Gare ku Mata Masu Fama da Wari Gaba
Warin farji abu ne da mata ke fama dashi a fadin duniya wanda suke iya samunsa sau daya ko biyu a rayuwarsu, abubuwan dake kawo irin wannan abu kala kala ne kamar su infection cututtukan saduwa, rashin kula
1. In warin farji daga infection ne yana farawa da kaikayi, gun yayi jaa da ciwo, wannan abu nasa mata suji kunya
Sa panties na cotton yanasa farji ya samu iska, hakan zai rage warin da wuri da yawan canja pant din duk awa 12 saboda tsaftace gun.
2. Rage wanka da ruwan mai zafi sosai saboda zai kashe miki important bacteria na farjin
3. Rage shan abu masu suga da yawa a cikinsu
4. Daina sa kayan dazasu matseki ko kamfe
5. Rage yin douching
6. Wanke farji da yogurt ko ki tsoma wani abu kamar soso cikin yogurt din saiki saka sosan cikin farjin yayi kamar awa 2-3
7. Amfani da APPLE CIDER VINEGAR: yana taimakawa kwarai wajen kawar da warin farji, zaki samu kofi daya na ruwa saiki hada da chokali 1-2 na ACV din kisah ko wace rana, ko ki zuba kofi biyu cikin ruwa a abin shiga ki shiga ciki tsahon munti 20 duk sati ko kiyi yadda Mukai bayani akan yogurt
8.Cin abubuwa masu dauke da vitamin c, wannan shima na taimako wajen kara rigakafin jiki.
9.Amfani da “bakin soda” yana taimakawa wajen kawar da warin farji,kiasaka rabin kofi a cikin ruwa saiki shiga ciki tsawon minti 20, bayan nan saiki wanke da ruwa da kuma clean towel
10. Wanke farji kafin sex da kuma bayan sex ya zama kina aikatawa ko yaushe
11. Cin citrus fruit kamar su lemo, inibi sunada vitamin c sosai
12. Ki dan fesa turare kadan a cinyoyinki da gwiwa, hakan zai dansa kanshi
13.Amfani da ganyen gwaiba na taimakawa sosai wajen kawar da wari
14. Dena wanke farji da sabulu, saboda wasu nada chemical din dazasu kasha miki bacteria masu amfani a farjinki