KAWA ZUCI
©SALMA AHMAD ISAH
•°•Dedicated to A & A, AMINA AHMAD ISAH (AMEERA) And AMINA ISAH IBRAHIM (NANAMEERA).•°•
Gaisuwa zuwa ga mutanen kirki, Khadeeja Abubakar Alkali a.k.a Khadeeja Candy da kuma Zainab A Baba a.k.a Abokiyar Hira. Adduarsu gareni ko da yaushe ita ce Allah ya yi riko da hannayena, alkairin Allah ya kai muku a duk inda kuk
بسم الله الرحمن الرحيم
01
Masarautar Dutse, Jigawa state…
“Adda!”
Wata matashiya ta ƙira tana daga tsaye jikin kofar shiga ɗakin mahaifiyarta. Hajiya Samira matar sarkin Dutse ta farko, wadda kowa na fadar ke ƙiranta da Adda ta juyo a nutse ta kalli autar 'yarta Muhibba dake tsaye a ƙofar ɗakinta. Kafin ta juyo ta aje carbin hannunta a kan dardumar da take zaune, ta shafa addu’ar da ta yi. Ta sake juyawa ta kalli Muhibba da ta zauna a saman gadonta.
“Me ya fa faru?”
“Nan da sati wani watan za mu koma school, kuma…”
Wani irin ihu da suka ji an kwalla a cikin sashin Addar ya sa Muhibba kasa ƙarasa maganar da take son faɗa. Kusan a tare suka dubi juna ita da Addan da gabanta ya faɗi, dan ko ba a faɗa ba ta san cewa ihun ba na kowa ba ne face ‘yarta Maryam.
“Adda abin nata ne ya tashi”
Cewar Muhibba tana juyawa da sauri ta fice daga ɗakin da gudu. Ita ma kanta Adda ɗin ba ta zauna ba, bayanta ta bi suka shiga sahin da ɗakin Maryam ɗin yake. Kafin su isa ɗakinta suka ci karo da ita a hanya, ta fito da gudu, yanda ta bangajesu ta wuce zai sa ka gane cewa ba ta cikin hayyacinta, sannan kuma ƙarfin ma ba na ita kaɗai ba ne.
“Wayyo Allah hannuna!”
Muhibba da ta buge hannunta da bango ta furta cikin jin zafin ciwon hannun nata.
“Malam yace kada mu taɓa bari ta fita, mu je mu kamo ta.”
A hanzarce suka fita babban falo, lokacin da Maryam ke gaf da ficewa daga sashin Adda gaba ɗaya, hakan ya yi dai-dai da shigowar SA’AD yayansu, kuma ɗan fari a cikin yaran Fulani Amarya matar sarkin Dutse ta biyu. Ganin abin da ya yi zato ne ya tabbata ya sa ya yi azamar kamo Maryam dake shirin bugeshi ta fita daga sashin.
“Ke Maryam! Maryam! Ina za ki je?”
Ya tambaya yana kokuwa da ita dan gaba ɗaya karfinta ta zage take son ƙwacewa daga riƙon da ya mata. Yanda take ƙwala ihu zai sa ka fahimci cewa ba a hayycinta take ba.
“Ku ƙyaleni! Sa’ad ku ƙyaleni! Wurin Abba zan je, ni wurin Abba zan je”
Gaba ɗaya idanuwanta a ƙafe suke, ihu take tana kokuwa da shi, Adda da Muhibba ko sun kasa yin komai, ita Muhibba ma kukan tausayin ‘yar uwarta take. Domin tana fama da wani irin ciwo ne da ba a san kansa ba, dan har ana zargin ko ta haukace ne… kuma wannan ciwon da take fama da shi ya hanata zama a gidan mijinta.
“Waye Abba? Kuma a ina yake?”
Sa’ad ya sake tambayarta.
“Abbana… Abbana”
Ta ƙara ƙaimi wurin kwaɗa ihun da hatta hadimai da bayin dake sashin sai da suka fito dan ganin abin da ke faruwa, duk da hakan ba wani sabon abu ba ne garesu, har cikin dare ma sai ta farka ta dinga iface-iface da buge-buge, abin dai sak ciwon hauka.
“Kin manta da ni ne Abban naki? Rannan ba kin ce ni ne Abba ba?”
Sai a lokacin ta tsaya da ihu tare da kokawar da take da shi.
“Abba?”
“Eh Abba, Ya Sa’ad Abbanki…”
Ta kuma yin shiru tana kallonsa kamar sha-sha-sha. Da ido Sa’ad ya yi wa Muhibba alama da ta kunna karatun al’kur’ani. Aiko da sauri ta kunna a wayarta, take Maryam ta dafe kanta tana faɗin.
“Abba ka ce su kashe”
“kina so su kashe?”
Ta yi saurin gyaɗa kai idonta a rufe.
“To mu je ɗaki… A can babu karatun”
Ta buɗe idonta ta kalle shi. Ya gyaɗa mata kai alamar tabbatarwa, da wayo da komai ya jata zuwa ɗakinta, ya lallaɓata ta kwanta a saman gado.
“Ki yi bacci abinki, Abba ba ya son yana ganinki kina kuka... Kin ji?”
Ta jinjina kai tana sharar hawaye, bai fita daga ɗakin ba sai da ya kunna karatu, idonta a rufe yake, amma faɗi takw ya kashe, ya kashe ita ba ta so, har ta yi bacci bakinta bai yi shiru ba. Ganin ta yi bacci yasa ya fita ya barta kwance, a falo iske Adda zaune ta yi jigum, damuwar duniya duk ta bi ta isheta saboda wannan ciwon na Maryam, a saman carpet ya zauna yana kallonta.
“Adda na lallaɓata ta kwanta, na san zuwa anjima idan ta farka za ta dawo dai-dai kamar ba ita ba, ki kwantar da hankalinki”
Adda ta sauƙe gwauron numfashi tana jinjina kai, domin abin da ya faɗi ɗin haka ne, ciwon nata zuwa-zuwa ne, idan ya tashi sai ta birkice a kasa ganeta, idan kuma ya kauce sai ka ganta cikin nutsuwarta kamar ba ita ba.
“To Sa’ad… Allah ya saka da alkairi”
“Haba Adda! Sai kace bare? Ai ko bare zan yi wa wannan abin ballantana ‘yar uwata”
Adda ta yi murmushi.
“To Allah ya yi albarka”
“Amin… Amma zuwa yaushe za a kaita asibitin nan ne? Ya kamata a san me ke damunta”
“Hmmm Sa’ad ba na jin wannan ciwon na Maryam na asibiti ne, shi yasa ko da mai martaba ya zo min da zancen zuwa asibitin na ce ya bari mu gwada na gargajiya tukkuna, tun da shi ma Sadiq ɗin (Mijin Maryam) ya kaita asibitin nan sau ba adadi, amma an kasa gano inda matsalar take…”
“Tun yaushe ake na gargajiyar? Amma har yanzu babu wani sauyi, tun da dama ta ki ai sai a koma hagu, zan samu Takawa da batun kaita asibti, idan ya amince ni da kaina zan kaita, wannan karon wurin likitan ƙwaƙwalwa za mu je!”
Adda ta yi murmushi, domin duk lalacewar Sa’ad ta wani wurin ya fi ɗanta HAMMAD kyan hali, duk da shi ma Sa’ad ɗin sai a hankali.
“Abar aka sha ne?”
Kansa ya sunkuyar ƙasa yana sinsina jikinsa, dan ya san abin da take nufi, kuma ta canka dai-dai, dan bayan sashinta ya taho domin shan shisha ya jiyo ihun Maryam, dalilin da ya sa ke nan baisha ba, amma sai da Adda ta gane hakan. Wani murmuhin ta kuma, sanna ta miƙe ta bar shi a falon tana cewa.
“Ya kamata ace in an girma a san an girma...”
“Adda shisha fa ba kamar sigari ba ce!”
“Shi dai hayaƙi sunansa hayaƙi, kuma duka illa ɗaya sukewa gangar jiki… Idan mutum bai kiyaye ba dan mutuncinsa ya kiyaye dan lafiyarsa”
Kansa ya kuma sunkuyarwa, har ta ƙarasa fita daga falon bai ɗago ba.
*Unguwar Yalwawa, Dutse, Jigawa state, Nigeria.*
Wata budurwa ce zaune a tsakar gidan dake ɗauke da ɗakuna uku ginin ƙasa, tsakar gidan ta sha shara ƙwal, duk kuwa da ba siminti ko interlocks ne a tsakar gidan ba, wani irin lallausan yashi ne zube a ƙasa, wanda shatin tsintsiyar da aka share gidan da ita tai masa ƙawa cikin yammacin.
Allo ne riƙe a hannun budurwar, yayin da take rubutu bisa allon da alƙalamin dake riƙe a hannunta bayan ta dangwalo tawada dake cikin wani mazubi. Labulen ɗaya daga cikin dakunan gidan aka ɗaga, wata baƙar dattijuwa ta fito daga ɗakin, motsin saka takalmanta ne ya ja hankali budurwar nan dake rubutu a kan allo zuwa kanta.
“ZAHRA! Wai har yanzu Ruwaida bata dawo ba?”
Budurwar da aka ƙira da ZAHRA! Ta girgiza kanta, kafin ta ce.
“Har yanzu bata dawo ba Mama, ke ma kin san halin Ruwaida na shaɗanci, yanzu haka wasa ta tsaya a hanya!”
“Eh ta yanda ni kuma za a ji daɗin zubar mini da kukata a hanya ba! Kai Allah ya shirya mana”
Mama ta ƙarashe tana ɗaukar buta ta shige bayi, yayin da ita kuma Zahra ta ci gaba da rubutunta. Kamar daga sama haka wata yarinya ‘yar kimanin shekaru goma sha biyu ta faɗo gidan da gudu, abin daya sa Zahra ta tsorata ke nan, dan ba ta zayi zaton cewar Ruwaida ce ta faɗo gidan cikin irin wannan yanayin ba, dan haka ta dubeta yayin da take aje allon hannunta a ƙasa tana faɗin.
“Ke lafiya kika shigo a haka? Ko wani ne ya biyoki?”
Ruwaida da tun da ta faɗo gidan take kallon hanyar soro ta dafe ƙirji tana maida numfashi, saboda gudun da ta sha, gumi ta sharce dai-dai lokacin da Zahra ke kuma tambayarta abin da take yiwa gudu.
“Hummm! Su Farida ne fa suka biyo ni da gudu”
“Me kika Musu?” Zahra ta cilla mata tambayar, sai a lokacin Ruwaida ta samu damar aje takalmanta dake riƙe a hannu, wanda aka sha gudun fanfalaƙi dasu.
“A hanyar dawowata daga gidan Inna mai kanwa na gansu a ƙofar gidansu Fati ita da Fatin suna ɗana da keken Khalil yayan Farida, shi ne suka ce na turosu, da ina turasu sai na turasu da ƙarfi, shi ne fa suka faɗa cikin kwata…”
“Suka faɗa kwata? Ko kika jefa su kwata?”
Mama da fitowarta daga bayi ke nan ta faɗa tana aje butar dake hannunta.
“To ba-ba su suka ce na turasu da ƙarfi ba?”
Ta faɗi tana turo baki.
“Wannan kuma keda su ne, dan na san ba haƙura za su yi ba sai sun rama… Ina kukata?”
Mama ta tambaya tana miƙa hannunta alamun a bata kukar miyar da ta aiketa dan ta je ta siyo mata. Ruwaida ta yi narai-narai da ido, sannan ta soma ja da baya tana kallon Mama.
“Kin jefar a hanaya ko?”
Zahra ta tambaya tana dubanta.
“A’a ban jefar ba, da ina turasu a keken ne ledar ta fashe, shi ne-shi-shi ne kukar ta zube a ƙasa!”
“Kai! Wannan yarinya! Wannan yarinya! Allah ya shiryeki! Kuma ke da Adali (Babban yayansu) dan Wallahi ni dai ba ni da ɗari biyun siyan wata kukar, idan ya zo sai ki masa bayanin abin da ya faru, ba ruwana a ciki!”
Jin batun za a haɗata da babban yayansu Adali yasa nan take hawaye suka taru a idonta, dan ta san karonta da shi ba daɗi, da ace Saamari yayansu na biyu ne za ta iya sha a hannunsa, dan shi kam yana sake musu sosai suyi wasa da dariya, ba kamar Adali ba sai su yi wata uku ba su ga dariyarsa ba.
“Dan Allah Mama ki yi haƙuri, Wallahi ba da ganga na zubar miki kukarki a hanya ba”
Mama ta mata banza ta shige ɗakinta. Nan da nan Ruwaida ta rikice ta koma gefe ta fara kuka tun kafin zuwan Adali, dan ta san yau ba makawa sai ta doku a hannunsa. Ita ko Zahra gaba ɗaya yanda ta bi ta birkice ne yake bata dariya, ba ta hana kanta daurewa ba, dariya ta yi mai kyau, wadda ta fitar da kyakkyawar loɓar dake duka kuncinta.
“Anti Dimple dan Allah ki saka baki kar Mama ta faɗawa Zazzabi, dan Wallahi idan ya sani yau ba abinda zai hana ya dakeni”
Zahra ta kuma yin dariya tana rufe robar da take zuba tawada a ciki, sannan tace.
“Laifinki ne ai, ba kya jin Magana Ruwaida, kafin ki fita ma fa sai da Mama ta ja miki kunne a kan kar ki tsaya wasa, ki yi maza ki je ki dawo, amma da yake kunnen ƙashi gareki sai da kika tsaya wasan”
Tana gama faɗin hakan ta miƙe tsaye riƙe da allo da kuma robar tawadar da ta yi amfani dasu ta shiga ɗakin da suke kwana ita da Ruwaidan. Jim kadan ta fito daga ɗakin, hannunta rike da naira ɗari biyar sabon bugu, ta nufi wurin da Ruwaida ke zaune tana kuka ta miƙa mata.
“Ta shi ki je ki siyo wata kukar”
Ai ko da sauri ta miƙe tsaye tana share hawaye.
“To Anti Dimple… Na gode”
Zahra ta yi murmushi tana dubanta.
“A rage ƙin ji dai”
Ba ta tsaya jin abin da Zahran ke faɗi ba ta fita da gudu, Zahra ta girgiza kai tana murmushi.
“Kai Allah ya shirya Auta!”
“Wai Zahra saboda ɗaurewa ƙarya gindi kuɗi kika sake bata ta siyo wata kukar?”
Cewar Mama daga cikin ɗakinta, Zahra dake ɗauraye tukunya domin ɗora sanwa ta amsa da.
“Ya zan yi da auta? Ai ni rashin ƙiwarta yasa bana ƙin yi mata duk abin da ta naima”
“Ni na so ace kin bari Adalin ya zo ya zane mana ita… Tun da ita ba ta san ranar da za ta yi hankali ba”
Ita dai Zahra murmushi ta kuma yi, lokacin da take haɗa ita ce domin hura wuta a murhu.
“Assalamu Alaikum!”
“Wa alaikassalam”
Zahra ta amsa sallamar da aka yi cikin muryar Saamari yayanta da take bi, wanda suke ƙira da Saama, kanta ta juya ta kalli hanyar soro, inda Saaman ya shigo, sanye cikin jersey da wandonta dake nuna cewa daga filin ball yake, sai kuma takalmansa na ball ɗin da suke riƙe a hannunsa. Duk wuyan rigarsa ya jiƙe da gumi, ga kuma kayan jikinsa duk sun yi datti, alamun dai yau ball ɗin tasu ta yi daɗi. Kallon Zahra dake kallonsa ya yi, ya sakar mata murmushi sanda take masa sannu da zuwa.
“Yauwwa Dimple sannu!”
Ya ƙirata da sunan da kowa ya santa da shi a unguwarsu, ba a unguwa kaɗai ba, hatta a makaranta kowa da hakan yake ƙiranta, abu ne mawuyaci ka ji an ƙirata da Zahra ba tare da ka ji an haɗa da Dimple ba, domin ko magana take sai ka ga Dimples ɗinta biyu na loɓawa, ballantana kuma a ce ta yi dariya ko murmushi.
“Ina Mama?”
Ya tambaya yana zama a kan kujerar da ta tashi daga kai ɗazu.
“Tana ɗaki”
Ta ba shi amsa tana kallon ƙofar ɗakin Maman. A lokacin ita ma Maman da ta ji Shigowar Saaman ta ɗaga labulen ɗakinta ta fito tana dubansa.
“Ga ni, me za a bani?”
“Yanzu laifi ne dan na dawo ban ganki ba na tambaya kina ina?”
“Ai fa. Ni ke nan ban isa na je ko ina ba za a zo a fara mini bi ta da ƙulli dukan kabarin kishiya”
Ita dai Zahra murmushi kawai take tana dubansu.
“Mama ke nan… Ina Auta?”
“Yanzun nan ta tafi gidan Inna mai Kanwa siyan kuka”
Zahra amsa shi.
“Awara na gani a hanya, shi ne na tsaya na sai mata”
“Ai ko yanzu za ka ga ta dawo”
In ji Zahra. Ita ko Mama ɗakinta ta koma tana faɗin in dai Ruwaida ce ga su ga ita nan.
*Paris…*
Wata jar mota mota ƙirar Pagani Huayra BC ce ke tsuga gudu a kan titin Autoroute du nord, waƙar Runaway ce ke tashi a cikin motar, baƙin matashin dake tuƙa motar da hannu ɗaya ya kure sautin wakar, yayin da yake kallon hanya yana shafa gefen fuskarsa da hannunsa ɗaya. A gaban wani kyakkywan gini ya faka motar, dai-dai kan alayin da aka zana domin aje motoci a gefen titi. Sai da ya cire shade ɗin da suka saya ƙanun idanuwansa, kafin ya cire safety belt, ya buɗe murfin motar hakan ya bawa sanyi damar sirnanowa zuwa cikin motar. Wata kyakkyawar shopping bag dake aje a front seat ya ɗauka, sannan ya fita daga motar, ya soma ƙarewa wurin kallo sanda yake rufe motar.
Wani shago dake cikin jerin shagunan dake wurin wanda aka rubuta “MALINA BOUTIQEU” a samansa ya nufa yana gyara zaman puffer jacket ɗin dake jikinsa saboda sanyin da ake. Mai gadin ƙofar shiga ya buɗe masa da sauri har da sara masa. Dube-dube ya kama yi sanda ya shiga cikin kyakkyawan boutiqeu ɗin, wanda aka cika shi da kaya kamar kamafanin ƙera kayan sawa.
“Bonne mantinee Monsieur!” (Good morning sir)
Ɗaya daga cikin ma’aikatan wurin dake sanye da kayan da ma’aikatan boutiqeu ɗin ke sawa ta faɗi cikin harshen faransanci fuskarta ɗauke da murmushi.
“Bonne journee Claire” (Good day Claire)
Ya amsa yana dubanta, kafin ya jefa mata tambayar da ta san dole ita ce abu na gaba da zai furta.
“Ou est votre dirigeant?” (Ina Madam ɗinku?)
“Elle est dans son bureau, veuillez prendre un siege, je vais l’apperler pour vous” (Tana office ɗinta, pleace have a seat, yanzu zan ƙira maka ita)
Ya jinjina kansa yana shirin zama suka jiyo muryarta tun daga cikin office ɗinta tana dakawa wata ma’aikaciyarta tsawa.
“… Fi ce daga nan kafin na sauya miki kammani, ni na ce ki kawo min coffee mai zafi?”
Duban juna suka yi shi da Claire, sai ya fasa zama ya nufi office ɗin nata, yana daf da riske office ɗin ma’aikaciyar da ya san ita akewa tsawar ta fito tana sharar hawaye, binta ya yi da kallo, ya ga yanda ruwan coffee ɗin da aka watsa mata ya ɓata mata gaban riga. Duk da halin ƙunci da take ciki ba ta kasa gaishe shi ba, bai kai ga amsa mata ba aka sake buɗe ƙofar office din, wata farar budurwa ta leƙo tana binsu da kallo. Fara ce, kuma sosai, irin farin fararen fata, siririya ce, mai kyakkyawan dirin jiki, ga dogon baƙin gashinta da ya ji gyara yana reto a gadon bayanta, sanye take da peplum top green color, da white slit skirt, dogayen wedge booties dake ƙafafunta ne suka ƙara mata tsayi, fuskarta ta sha kwalliya kamar ‘yar tsana. Da ka ganta ka ga ‘yar kwalliya kuma ‘yar ƙwalisar zamani, kuma ba sai an faɗa ba, kallo ɗaya idan ka mata ya wadatar ka shaida ba musulma ba ce. Manon Durand ke nan, matashiyar model, kuma ‘yar kasuwa. Da harara ta bi bayan ma’aikaciyar da ta bar wurin, kafin ta kalli masoyinta, lokaci guda ta saki murmushi.
“Boobu kai ne?”
Ta ƙarashe tana nufo shi, kana ta rungume shi kaɗan tana murmushi.
“Na yi kewarka Boobu!”
Da ƙyar ya ƙaƙalo murmushi ya jefeta da shi, dan shi sam murmushi ba ya cikin abubuwan da ya saba yinsu.
“Ni ma haka… Ga rigarki nan!”
Cike da farin cikin kyautar Jersey ɗin da ya bata ta buɗe baki, sai kuma ta sa hannu ta karɓi shopping bag ɗin hannunsa, a gabansa ta fito da sabuwar jersey ta PSG (Paris Saint-Germain) Baby pink color da ratsin baki a jiki, bayan rigar ta juya tana ɗagata sama, kafin a fili ta karanta sunan da aka rubuta a bayan rigar.
“WAKILI!…”
Ta kuma kallonsa idanuwanta na ƙyallim murna, side hug ta sake masa tana cewa.
“Thank you HAMMAD!”
“The pleasure is mine Baby…”
“Mene ne wanna a fuskarka?”
Ta ta tambaya tana taba gefen fuskarsa da ta ga ya kumbura alamun an daki wurin, dan shi kam ba fari ba ne ballantana wurin ya yi ja, yanzun ma ba dan ya kumbura ba ba lallai ta gane da ciwo a wurin ba, Hammad ya ɗan shafa wurin yana girgiza mata kai.
“Is not a big deal… A training ɗinmu na yau Nicolas ya bugeni da ball!”
Manon ta haɗe rai tana matse jerseym daken hannunta.
“Ya kamata ka ɗauki mata a kan Nicolas, abin nasa ya fara wuce gona da iri, babu wanda bai san cewa duk abubuwan da yake maka da gangan yake ba”
Ganin ta fara fusata yasa Hammad ya rike hannunta dake riƙe da jersey.
“Ki kyale shi Baby, za mu ɗauki mataki a lokacin da ya dace…”
Hayaniyar da ta soma tashi a kofar shigowa ce ta ja hankulansu zuwa can.
“Anais wai waye yake tada min hayaniya a ƙofar shago ne? Sau Nawa zan ce ku daina barin mabarata na taruwa a ƙofar shagona?”
Cewar Manon a tsawace tana kallon yanda mai gadin kofar shigowa ke kokawa da wani mutum da yake son shigowa shagon, domin kofar ta glass ce, hakan ya basu damar ganin komai.
“Madam ba mabaraci ba ne, Yallaɓai Hammad yake son gani…”
Anais mataimakiyar Manom ta basu amsa, hakan yasa Marie da Hammad suka dubi juna, kafin ta kalli Anais.
“Je ki kore shi, idan ya ƙi tafiya ku ƙira ‘yan sanda!”
“To Madam!”
Anais ta amsa, kafin ta juya Hammad ya dakatar da ita.
“Dakata Anais…”
Anais ta bi umarni ta hanyar dakatawa.
“Zan gan shi”
“Amma Boobu…”
Marie dake shirin masa magana ta dakata saboda kallon da ya mata, ita kanta ta san yana ɗaga mata ƙafa, amma idan ta kai shi bango to ba sa kwashewa da daɗi.
“Ki je office ki jirani ina zuwa”
Rasa damar musa masa yasa ta juya ta nufi offfice ɗin, shi kuma ya nufi kofar dan ganin mutumin da yake son haɗuwa da shi.
__________________
_TO kamar yadda aka saba yanzu ma gani ɗauke da wani sabon labarin, da fatan shi ma za ku karɓe shi kamar sauran…_
_KAWA ZUCI paid book ne, a kan ₦400, free pages ɗina ba su da yawa, dan haka za ku iya fara biya tun daga yanzu, domin morewa karatunku cikin kwanciyar hankali