Aslm barkanmu da wannan lokaci
Ina Mai farin cikin sanar daku cewa Zuzeam ventures takawo maku ingantattun magunguna masu inganci cikin Aminci Muna da kaya kamar haka
Mallaka Maganin sanyi
Maganin cire tumbiMaganin farin jini
Maganin matsiMaganin mata
Maganin sa ni’ima da dandano
Dulka Amare Set na gyran jiki
Set na amarya
Tabaje tsumin Gomba
Xuma kiba ta hips and Brest
Magungunan gyran Brest
Magungunan Karin hips
Maganin sliming
Muna da kaya masu inganci cikin sauki da rahusa
Ina wadda keneman mallaka sahihiya quaranty wlh hajiya kixo ga zuzeam ventures xakiji ddin mallaka duk fadin ran ogah duk fadansa wlh sai yyi sanyi 08144015291
Idan maganin mata kikeso akwai
Idan gyran jiki kikeso gyran fata gyran Brest magungunan sa kiba da hips
DOMIN samunta Kai tsaye kira wannan no 08144015291 DOMIN mgn da ita whatapp 08144015291muna tura kayanmu ko ina cikin iKon allah 🥰👌🏻
Bononza Bononza Tsimin kaninfari 1k Tsimin dabino 1k Gumba 700 Gumba aya da nonon rakumi 700 Garin kafi ciccibi 500
Garin bata gaban kishiya 500
Matsin mallaka tada zaune tsaye 2500
Turaren mallaka ba aba mai kishiya 2500 Total kayan 9500
Za a bakisu akan 4k
Kuma mutun goman farko nadakyautar Abun 2k
🗣️🗣️🗣️🗣️🗣️🗣️ ASSALAMU ALAIKUM ALHAMDULILLAH YAN UWA NEW PROMO YA KAMMALA💃🏽💃🏽💃🏽😁😁😁 da 5k dinki ki kwashi kayan 12k hajiyata 💃🏽💃🏽💃🏽😃🙃Kazar gadali ta mallara Rabi 3500 Tsimin gam gam 1500 Ruwan kara zunzurutun dadı😋800 Garin 7in1 1k Gumba 3 balai 500 Gumba kwakwa da dabino 500 maganin Infection 1k Garin zunzurutun dadi 1200 Matsin ba a fira d wando 500 Matsin infection mai matse mace gam 500 12k All at 5k https://wa.link/l1gcz8 kedai dannan link dinnan don samun naki ki maza kiyi bucking koda kudinki saida Rabonki.
*Daga Alƙalamin Boss Bature💋✍️*
ZEENATU💗
Tana a zaune saman swing chair dake a cikin katafaren garden din gidan, fuskarta sam babu walwala sai tarin damuwar da tayi mata katutu acikin zuciyarta, ta yi zurfi cikin tunaninta idanunta suna akan Peacocks din da ke shawagi cikin garden din..
Da matsakaicin gudu motar Alhaji Musa ta kunno kai ta cikin main gate din gidan ta nufo parking space, yana hakimce a backseat din motar idanunsa suka hango mashi ita ta cikin glass window, umarni ya ba drivernsa ya tsaya kusa da ita.
Horn ɗin motar ne ya razanar da ita, a firgice ta ɗago da idanunta da suka kaɗa sukai ja ta dubi motar da a daidai lokacin tayi parking, fitowa yayi daga cikin motar, like always fuskarsa a murtuke ya ɗauki wankan suit.
Ya saba idan ta ganshi da gudu zata nufe shi tayi hugging dinsa amma yau ya sha bamban, tunda ta kalle shi sau ɗaya ta kawar da idanunta gefe ɗaya, hakan ba ƙaramin ɗaga hankalin sa ya yi ba.
Daga gefenta ya zauna tare da ɗaura tafin hannunsa saman kanta ya janyota a hankali ya kwantar da kanta saman kirjin shi, sai lokacin ta samu damar fitar da abunda ke ranta, fashe mashi tayi da kuka.
A ruɗe ya soma shafa bayanta da tafinsa, tare da tambayar ta meke damunta? Wa ya ta6a mashi babynshi? Ko bata jin dadi ne.
Lokaci ɗaya duk yabi ya rude saboda ko kaɗan baya son damuwar Zeenatu.
Cikin shesshekar kuka ta ce, "Daddy, Yaya Shureim.."
"Meya yi maki?"
"Daddy, he stopped paying attention to me bana jin dadin share ni da ya ke yi, I don't know what I did to him, he's completely changed towards me" tun da ta fara magana ya haɗe rai kamar bai ta6a yin dariya ba
"Aunty Benazir ma ta rage kula ni, ni gaba daya zaman gidan bai yi min daɗi daddy, mommy ma bata da lokaci na, in ta dawo daga office agajiye bata kulani sai ta shige daki ta kama bacci, da anjima kuma in ta farka bata fira da ni, sai dai ta je gurin mommy Layla su yi fira, shima ya Shureim din baya fira da ni da aunty Benazir ya ke yi kullum suna a tare, kaima idan ka tafi sai tsakar dare kake dawowa lokacin na riga da na yi bacci, ni gani nake kamar baku sona, baku damu da ni ba, baku bani kulawa yadda ya kamata..." Ta ƙarashe maganar cikin shesshekar kuka.
Bai ji dadin halin da take a ciki ba, ya fahimci kaɗaici ne ke damun ta, har cikin ranshi bai ji dadi ba.
Shafa sumar kanta yayi cikin sigar lallashi ya ce "Stop thinking that way, my princess, bana so kina sanya damuwa a ranki, you're more important to us than anything, please ki daina fadin ba'a sonki ko ba a damu da ke ba, sanin kan ki ne bani da abu mafi soyuwa da ya wuce ke, ko da kowa zai juya maki baya ki tuna ni ina atare dake, koda bana nan kina a cikin zuciyata..."
kalamai masu tausasa zuciya ya dinga faɗa mata har ya samu ta ɗan lafa da kukan.
Tighting dinta ya yi a kirjinshi ta yi lamo fuskarta sharkaf da hawaye sai faman sauke ajiyar zuciya ta ke yi.
"Daddy yaushe zan cigaba da karatu? Ka ce sai nayi aure zaka barni in cigaba, dan Allah daddy ka yi mini auren, saboda inaso in dinga zuwa makaranta harma in haɗu da ƙawayen da zamu dinga zumunci atsakanin mu, saboda na fahimci babu tsara na agidan nan shiyasa ba'a zama a yi fira dani...."
Murmushin gefen fuska ya ɗan saki, ya lura da akwai abun da ya 6ata mata rai shiyasa take fadin ta cikin ta.
"Kada ki damu, Nayi maki alkawari ƙarshen shekarar nan, zan aurar dake, kuma zaki cigaba da zuwa makaranta"
Murmushi ta saki saboda taji dadin maganar sa, ba karamin ɗebe mata kewa yayi ba, ya bata lokacin shi sosai sun daɗe suna fira kafin suka sauko daga kan kujerar, hannunsu cikin na juna suka nufi falo.
Lokacin da suka shigo falon, A dining Suka hango mutanan gidan sun hallara suna cin lunch din su, ran Alhaji Musa Ya 6aci ganin yadda su ke yin walwala, hakan yasa shi yarda da maganar Zeenatu, wato basu damu da Zeenatu ta ci abinci ko bata ci ba.
Fusgar hannunta ya yi ya ja ta suka nufi dining din, takun tafiyarsa ne ya ja hankulansu ga duban shi, har saida gabansu ya fadi ganin yadda ya murtuke fuska.
Yana ƙarasowa ya sanya hannu ya damƙi table cloth din da aka shimfiɗa kayan lunch din saman shi, ya hankade shi gaba daya kayan abincin suka 6are kan floor, a sukwane suka miƙe suna kallon shi cikin ruɗu.
A tsorace Zeenatu ta la6e bayansa jikinta na kerma..
Hajiya layla da ranta ya 6aci ta watsa mashi harara tare da cewa, "Wannan wani irin wulakanci ne? Ta ya muna cin abinci zaka 6arar da shi kamar wani ƙaramin yaro.."
Bata ƙare maganar ba ya daka matsa tsawa tare da nuna ta da yatsan shi, "Karki kuskura ki sake min magana idan baso kike in 6ata maki rai ba..."
sakin baki ta yi sototo tana kallon sa, hankalin hajiya Sarah ba karamin tashi ya yi ba, sai yarfa hannayenta take yi tare da marairaice masa fuska don yayi haƙuri.
"Haba Musa, wani irin almubazzaranci ne wannan? Yanzu abun da kayi ka kyauta fisabilillah? Laifin me mu ka yi maka? Meya sa zaka zubar mana da abinci?" Alhaji Ubaid ne ya faɗa cikin fushi,
Harara ya watsa mashi rai a 6ace ya ce, "In har Zeenatu ba zata ji dadi a gidan Ubanta ba, to kuwa babu wanda zai zauna lafiya a cikinku! Saboda rashin hankali kuna nan hankalinku kwance, kun bar min yarinya a waje cikin kaɗaici? Wato baku damu da ita ba, babu ruwanku cikinku kaɗai kuka sani ko!"
Da tsawa ya ƙare maganar kamar zai doke su, Benazir da Shureim sun saki baki suna kallon ikon Allah, sam sun kasa magana..
"Babe, wllh ba haka bane, bansan me Zeenatu ta faɗa maka ba, amma wlh bamu manta da ita ba, ka tambaye su ka ji saida na aika Tani bedroom dinta don ta kira ta tazo ta ci abinci, bayan Tani ta dawo ta ce min Zeenatu tace ba zata ci abinci ba, wai bata jin yunwa, dama kwanan nan fama na ke yi da ita, na rasa gane kanta, da kaina na je ɗakin na matsa mata akan ta zo mu ci abinci amma taƙiya shiyasa na ƙyaleta, na jira saika dawo in sanar da kai..." Harara ya watsa musu, tare da jan dogon tsoki, ya juya yana cika yana batsewa ya nufi part dinsa..
Hajiya layla ji take kamar tabi bayan shi ta shaƙe shi, saboda haushinshi da ya cikata,
"Wlh Musa bai da mutunci, ni wlh na gaji da wulaƙancin da ya ke yi mana, don kawai muna zaune agidansa...?
Bata ƙare maganar ba, Hajiya Sara ta juya tabi bayan shi, bayan tafiyar ta Shureim da Benazir suka haɗu suna rarrashin mommynsu, Zeenatu dake kallonsu duk tasha jinin jikinta ganin abun da ta ja musu...
Fashewa ta yi da kuka tare da juyawa jikinta na kerma ta nufi hanyar ɗakin ta, bata kaiga ƙarasawa ba Dr. Shureim ya bi bayan ta da sauri ya taso ƙeyarta ya dawo da ita dining din, zaunar da ita ya yi kan kujera ya tsareta da tambayar me ta faɗa ma uncle Musa, cikin shesshekar kuka ta zayyana musu komai, cike da takaici Benazir ta ce, "Haba Zeenatu, me yasa zaki mana haka? Idan mu muka 6ata maki rai why ba zaki faɗa mana ba uhum? Kinsan halin uban naki, yanzu gashi kin ja ya zubar mana da abinci hankalinki ya kwanta ko? Kin shiga tsakanin mu da shi..."
Fashewa ta kuma yi da kuka, Alhaji Ubaid ya ce, "Ya isa haka pls, ni banga laifin Zeenatu ba, gaskiya bakwa kyautawa, ku yakamata ace kuna jan ta a jiki, tunda ku kaɗaine ƴan uwa dake a kusa da ita, bayan haka yarinya ce sai kuna haƙuri da ita.."
Ta6e baki hajiya Layla ta yi, "Ni Zeenatu bata yi mini komai ba, in ita bata da cikakken hankali ai shi uban nata da hankalinshi ko? In ba rashin wayau ba meye na ɗaukar maganar yaro? Ta ƙare maganar tare da jan tsoki ta juya ta bar dining din, da sauri Alhaji Ubaid yabi bayanta don ya lallashe ta.
Cikin shesshekar kuka ta ce, "Am really sorry, idan na 6ata maku rai, ni ban faɗa masa don yayi maku faɗa ba, Aunty benazir am sorry, yaya Shureim kaima ka yafe min.."
Tausayinta ne ya kama su, har su ka ji basu kyauta mata ba, lallashinta su ka koma yi.
"Nasan nine na 6ata maki rai ko?" Ya tambaya yana kallon ta, yamutsa fuska ta yi tare da sunnar da kanta ƙasa,
Kallon Benazir ya yi suka haɗa ido, tashin hankali! gaba ɗaya sun gane inda Zeenatu ta dosa, gashi a halin yanzu Dr Shureim baya jin sonta, tun ranar da Allah ya haɗa shi da Aisha, ya gane ba son aure yake ma Zeenatu ba, rashin Aisha ne yasa har ya kula ta da sunan soyayya, amma a zahirin gaskiya baya jin zai iya haɗa Aisha da wata mace a duniyar nan, bai ma ta6a lura da Zeenatu tayi masa ƙaranta ba sai ranar da idanunsa suka yi mashi tozali da Juliet ɗinsa.
Ƙumshe dariya Benazir tayi, don ta riga da ta gane me ya Shureim ke tunani aransa, ɗan ja gefe ya yi yadda zai kauce ma Zeenatu kada ta ji mi zai ce don yasan zata iya fahimta, cikin harshen larabci ya ce, "Ya zanyi Benazir? Wlh tun da na ga Ummi na ji kamar ancire mini son Zeenatu, yanzu soyayyar da nake mata ta ƴan'uwantaka ce bata aure ba."
Itama cikin harshen larabci ta ce, "Ya shureim sau nawa ina kokarin ankarar da kai akan Zeenatu uhum? Saida na ce maka tayi maka ƙanƙanta, ba sa'ar auranka bace, duk da ba haramun bane don ka yi soyayya da ita, amma ni dama nasan mace ɗaya ce a cikin zuciyarka, ka so zeenatu saboda rashin Aisha, yanzu kuma Aisha ta bayyana, in ka ji zaka iya haɗawa biyun tau, ka dai san Zeenatu da kishi, kuma tsakani da Allah da raini ka haɗa Aisha da Zeenatu yar cikin ta.."
Ta faɗa tana dariya, gaba ɗaya maganganun da suke yi Zeenatun bata fahimtar abun da suke fadi saboda basu ɗaga murya ta sadda kanta ƙasa.
"Ka daure ya Shureim, kada ka karya mata zuciya, ko da ba za ka aureta ba, ka taimaka ka kwantar mata da hankali, wlh tana sonka, kaga ta fara shiga damuwa, in ya so daga baya zamu san abun yi..."
Jinjina mata kai yayi tare da mayar da hankalinsa kan Zeenatu ya matsa wurinta, cikin sanyayyar muryar nan tashi ya ce, "Am really sorry rabin raina, na gane kuskurena, ke ce baki fahimce ni ba Zeenatu, taya zan daina kula abar kaunata uhum?" Murmushi ta ɗan fara saki..
Ruƙo hannunta Benazir tayi a cikin nata, "Pls Zeenatu, ki daina biyewa zuciyarki, wallahi babu abun da ya canza na daga kaunar da mu ke yi maki, mun damu dake, muna son ki rabin ranmu, daga yanzu komai a tare zamu dinga yi in sha Allah, mu ci abinci atare, muyi fira atare, muyi kallo atare, mu yi gym atare, kai har tilawar alqur'ani zamu dinga yi kullum tare da ya Shureim."
Murmushin farin ciki ta saki ga wani dadi da ta ji.
"Yanzu ma ba zamu barki da yunwa ba.." ta faɗa tare da kwala ma Tani kira, jim kaɗan sai gata ta nufo su, tana ganin kayan abincin da aka 6arar a ƙasa ta daura hannu akai tana tambayar meya faru..
"Pls ki kwashe kayan abincin da ya zube ki canza mana wani, sannan ki turo wata maid din ta goge floor din, muna jiran ki."
Benazir ce ta fada, jikin Tani na 6ari ta amsa da toh ta zuƙunna tana tattara kayan abincin, bayan ta gama jera su a tray ta nufi kitchen....
______________UNCLE MUSA
Bayan ya shiga bedroom dinsa yana ƙoƙarin fara rage kayan jikinsa, wayarsa ta ɗau ruri.
zaro ta yayi daga cikin aljihun wandonsa yayi picking tare da kara wayar a kunnansa...
"Sir, har yanzu bamu gano shi ba, a binciken da mu ka yi, ba shi kaɗai ya gudu daga estate din ba, hada yar uwarsa ba'indiyar nan.."
Tsoki ya ja cike da takaici ya ce, "Na raina kokarin ku, tayaya har sakaran mutumin nan ya gagare ku ganowa um!" Ya fada a fusace..
"Sorry Sir, we'll do our best to locate..."
Bai ƙare maganar ba ya daka mashi tsawa yana faman cije le6e ya ce, "Idan har baku gano inda ya 6uya ba nan da one week, ku kuka da kanku! sannan bana buƙatar shi araye da shi da yar uwar ta shi, just kill them all and bury them where no one can find their bodies!"
"An gama sir," Rejecting call din ya yi, sai faman fitar da numfashi mai ɗumi ya ke yi, ran manya ya 6aci...
Wani layin ya kira tare da kara wayar a kunnansa,
"Mark, how's his condition? Has he recovered from the coma?"
On the other hand Dr. Mark ya ce "He still hasn't regained consciousness, amma ka kwantar da hankalin ka, yana samun kulawar likitoci, nan bada jimawa ba zai farfado, kasan aminin nasa baya wasa da lafiyar sa"
cije le6ensa yayi tare da jan numfashi ya furzar da shi.
"Ko da zai cire ran shi yaba Omar don ya rayu, bazai ta6a burge ni ba, bana son alaƙar su kwata kwata, sai kace shi na haifa ma shi, Omar ya jima yana baƙanta min rai saboda Owais, shi ya raba ni da shi, ya mallake min ɗa, amma nasan maganinsa dole in shiga tsakaninsu wlh..!"
Bai ƙare maganar ba, ya tsinkayi muryar Hajiya Sarah,
"Babe..."
Nan da nan ya haɗe rai, da sauri ya katse kiran tare da jefa wayar saman mattress, afusace ya juyo yana kallonta tana daga tsaye bakin kofar ɗakin,
"Ban hana ki yi min la6e ba idan ina waya?"
Marairaice masa fuska ta yi, "Am sorry, ba la6e nake yi maka ba, dama na biyo kane don inji meyasa ka yi mana haka pls?"
"Oh! kin biyoni ne don kiyi min faɗa kan abunda na yi halan? Ya fada yana ɗage mata gira..
Ƙwarjini yayi mata hakan yasa ta kasa faɗan ta cikinta..
"In har zaku cigaba da 6ata ma zeenatu rai, nima bazan daina 6ata maku rai ba, yarinya da gidan ubanta ace kowa ya juya mata baya babu mai kula da ita!"
"Bai kamata kana ɗaukar maganar Zeenatu ba, har yanzu fa yarinyace, babu abunda aka yi mata fa, ita ce ta ƙuntata kanta.."
Bata ƙare maganar ba ya katse ta, "Pls, fuce ki bani guri, bana son takura.." gyaɗa kai tayi maganarsa ta 6ata mata rai.
Dama da haushinshi aranta, kwanakin nan kwata kwata baya bata hakkinta yadda ya kamata, in ya fita sai cikin dare ya ke dawowa gidan kamar aljani, tayi ta jiranshi baiwar Allah, har sai bacci ya dauke ta, kuma in ta farka ta gansa ta nemi ya kulata sai ya kama yi mata faɗa yana faɗin ya gaji ita bata da hakuri ne, bata ga a gajiye ya dawo ba, kawai ta kyalesa bacci zaiyi, baiwar Allah zaman hakuri kawai ta ke yi da shi.
"Abincin naka fa?"
"Bazanci ba" Cike da 6acin rai ta ce, "Kada Allah yasa ka ci Musa, ka cigaba da yi min abun da kaga dama, ni da kai in har akwai wanda ke cutar wani Allah zai saka masa ne ka jira ka gani, don kawai ina haƙuri da kai sai ka yi ta min abunda kaga dama..."
A ruɗe yake kallonta cike da mamakin ina ta samu kwarin gwiwar gaya masa magana ido cikin ido batare da jin shakkar shi ba..
"Ƙaddara ce tasa na aure ka, amma wlh nafi ƙarfin ka, koda yake ba laifin ka bane, nina ja ma kaina, shiyasa har ka samu damar wulaƙantani son ranka..."
Juyawa ta yi a fusace ta nufi room door din, batai aune ba taji ya damƙi wuyanta, a tsorace ta kware baki zata fasa ƙara, ya yi hanzarin sanya tafin hannunsa ya toshe bakin nata.
Saitin kunnnanta ya kai bakinsa da wata irin murya mai cike da shu'umanci ya furta, "Matsoraciya..." Ajiyar zuciya ta sauke tana faman haɗiyar yawu...
"Faɗa min a ina kika samu kwarin gwiwar nan ne?" Ya faɗa yana leƙen fuskarta..
"Ka 6ata min rai ne, ni kawai bana jin dadin abun da ka ke yi min ne, basai na fito fili na faɗa maka ba ka riga da ka sani .."
"Am sorry my queen, mother of my princess, na kar6i laifina, bazan ƙara ba, nima bada son raina hakan ke faruwa ba, ayyukane su ke yi min yawa amma zan gyara in sha Allah." ta ɗan yi mamakin yadda yayi mata magana cikin tausasa harshe.
"Muje ki taimaka min in yi wanka, mun kwana biyu bamu yi wanka atare ba.." Bai jira amsarta ba, cikin sigar yaudara da jan hankali ya ɗauketa kamar jinjira ya nufi bathroom da ita.
Lokacin da Taj ya je ma Ummi da zancen neman ta da Chief ya ke yi, hankalinta ba ƙaramin tashi yayi ba, zullumi da fargaba suka cika zuciyarta, ta yi ta tunanin meyasa ya ke nemanta?
Kasa fita tayi daga dakinta, har saida Taj ya kirata a waya ya ƙara tunasar da ita game da kiran da Chief ya ke yi mata yace ta same shi yanzun nan a sitting room dinsa tukunna, ta zumbula dogon hijabi ta fito cike da ɗar-ɗar ta nufi sitting room dinsa, saida ta tsaya bakin door din ta daidaita nutsuwarta, kafin tayi sallama cikin nutsastsiyar muryarta.
Daga ciki ya amsa mata sallamar, ya na daga zaune kan sofa ya ɗaura kafarsa ɗaya kan ɗaya yayin da idanunsa ke akan Apple ipad dinsa da ya ke daddanawa, shiga ciki ta yi, tunkan ta ƙaraso ya nuna mata kujerar dake fuskantar sa, table ne ya raba tsakanin su.
Bayan ta zauna ta sunnar da kanta ƙasa cike da jin nauyin sa gaba ɗaya ya yi mata kwarjini.
"Ina fata kin wuni lafiya."
Da ƙyar ta furta, "lafiyalou, ya kake, ya aiki, ya family ɗin ku"
"Alhamdulillah ina lafiya, suma family ɗina suna cikin ƙoshin lafiya,"
Shiru suka ɗan yi na wani lokaci, daga bisani ta tsinkayi muryarsa a cikin kunnanta,
"Na kwaɗaitu da son jin tarihin rayuwarki.."
Zare idanu ta yi, har ta fara tunanin ko dai ya ji komai agurin su Benazir ne.
Bai damu da yanayin ta ba ya ci gaba da maganarsa, still bai ɗago ya kalle ta ba, idanunsa na akan apple ipad dinsa da yake cigaba da dannawa,
"A ranar da ƙawayenki suka zo gidan nan, Taj ya faɗa min halin da kuka shiga lokacin da kuka ga juna, kuma ya ji a bakin Ex-wife din sa cewa ke aminiyarsu ce..."
Har ya ƙarashe maganar bai ɗago ba, yanayin fuskarta ne ya canza zuwa tsantsar 6acin rai da damuwa, kwata-kwata bata son kowa yasan labarinta, saboda tana jin kunyar a sani, bayan haka bata son ta fama tsohon raunin dake a cikin zuciyarta, abun da ya ɗaure mata kai meyasa Chief ya ke son jin labarin ta? Ko Taj da suka fi shaƙuwa da shi bai nemi ya sani ba sai shi da bai ta6a shiga shirgin ta ba hakan yasa ta dan ji shakkun ta faɗa masa..
"Kin yi shiru ba ki ce komai ba,"
Kamar mara gaskiya ta kama yi mashi yan kame kame, muryarta kamar ta mai in'ina ta ce, "Sir, I'm sorry to say why do you want to hear about my life?"
"Saboda ina son in sasanta tsakaninki da ƙawayenki, cos a fahimtana kun samu sa6ani ne, kuma akwai wani abu da ya faru wanda yayi silar raba ku. "
Yamusa fuska tayi kwata kwata babu walwala ta furta, "Ina ganin girmanka yallabai, bana fata Allah ya nuna min ranar da zaka nemi wani abu agurina in kasa yi maka shi, amma ina mai baka haƙuri, ni bazan iya baka labarina ba..."
Gently ya ɗago da reddish eyes dinsa ya ɗaurasu akan fuskarta, tuni ta ji wata nutsuwa ta shige ta, wani irin kwarjini yayi mata wanda hakan yasa ta kasa ƙarasa maganar tata.
"Pls ki faɗamin, In har kin yarda da ni, amma idan kina ganin da takura ki bar shi..."
Yanayin yadda yake yi mata magana cikin kwantar da murya yasa ta dinga jin kamar yaya Shureim ne ke yi mata magana, hatta fuskarsa sai ta dinga koma mata irin ta Shureim, batasan sa'adda ta fara bashi labarin rayuwarta ba, tiryan tiryan ta labarta masa komai daya faru da ita har izuwa lokacin data bar gidan mahaifin ta.
Idanunta cike tab da ƙwalla ta ƙare maganar, lallashin ta ya yi cikin nuna tausayawarshi gareta har ya samu ya shawo kanta.
"Tayaya akai kika bar ƙasar nan? Ki ka koma America da zama, bayan kin canza rayuwarki?"
Sunnar da kanta ƙasa tayi cike da jin nauyin ta fada.
"Zan fahimce ki Ummi, tun kafin ki fara yi mana aiki mun riga da mun san komai game da rayuwarki a America, don haka kada ki ji komai, abun da ya faru da ke jarabta ce daga Allah..."
Kalamai masu dadi ya faɗa mata har sai da ta ji zata iya fada masa komai saboda ta yaba da hankalinsa ta kuma aminta da shi, a tsanake ta fayyace masa komai da ya faru bayan rabuwarta da mahaifin ta.
Daƙyar ta ƙarasa labarin ganin yadda hankalinsa ya tashi matuƙar sosai, jikinshi har kerma ya ke yi saboda tsabar bacin rai da fusata, bai ta6a jin tsanar mutun kamar yadda ya ji ya tsane sa ba, zaluncin sa yayi yawa, bayan ya rabata da kowa nata, ya kuma maida ta karuwa, cikin fushi ya daki gaban table dinsa da hannunsa.
Hankalinta a tashe ta ce, "Sir meke damunka? Ko labarin dana baka ne baiyi maka dadi ba..!"
"Har yanzu kina atare da Uncle din nata?"
girgiza kai ta yi, "Mun rabu da daɗewa,"
Wani kallo yayi mata da ya sa tasha jinin jikin ta, batasan ya san komai ba.
"Ki ji tsoron Allah, Ki faɗa min gaskiya!"
Tamkar zata fashe da kuka ta ce, "Pls kada ka tilasta mini, bazan iya faɗa maka amsar tambayarka ba, ka yi haƙuri kawai.."
Murmushin takaici ya yi tare da cewa, "Okay, Kin taba haihuwa da shi?"
Aruɗe take kallonsa jin wata tambaya mara ma'ana, ba dan tana ganin girmansa ba da ba abun da zai sa ta zauna yana mata tambayoyi kamar ɗan jarida,
"A'a, amma na ta6a samun cikin shi, wanda silar zubar da cikin da na yi yasa muka samu sa6ani da shi, har ya ɗauke ƙafa da kawo min ziyara, abun da yasa nayi hakan saboda bana so in 6ata shape din jikina sannan bani bukatar in ƙara haihuwa, ƴata dana bari ta ishe ni in ƙarasa rayuwata, ashe ma ƴar da nake ta hauka akanta ta mutu batare da na sani ba...."
Fashewa tayi da kuka ya dinga lallashinta har ya samu ta yi shiru..
"Amma meyasa baki taba kar6ar tayinsa na aure ba?"
Tana cikin share ƙwalla ta ce, "Saboda ban ta6a son shi da aure ba, bayan haka a duk lokacin da yayi mini magiya akan in amince in auresa, da zarar na amince muka fara shirye shiryen auranmu toh bazai ƙara lafiya ba, har sai ya fasa zancen auren, wannan dalilinne yasa har ila yau bai aure ni ba."
Duƙar da kanta kasa ta yi jikinta yayi sanyi da ganin yanayinsa, duk sai taji ta muzanta, saboda tayi zaton haushin rayuwarta ya ke ji, tuni idanunta sun cicciko da ƙwalla,
"Kayi hakuri, idan labarin dana baka ya 6ata maka rai, shiyasa tun farko banso ka matsa min akan in fada maka ba.."
A hankali ya buɗe idanunsa da suka kaɗa jawur ya girgiza mata kai, "Ba abunda kike tunani bane Ummi, labarin ki ya karya min zuciyana, na ji tausayin rayuwar ki..." hankalinta ne ya kwanta jin ba abun da ta zata ba ne.
"Nagode da kika aminta da ni har kika faɗa min sirrinki" Ɗan murmushi ta yi.
"Amma kai ma kamar kana da damuwa, kada ka ce na sanya maka ido, wlh ka rame, babu karsashi a jikin ka"
Murmushin yaƙe ya ƙaƙaro akan fuskarsa, "Kada ki damu da ni, zazzabine ke damuna amma na ji sauƙi..." Girgiza kai ta yi, "Yallabai, halin da ka shiga yafi ƙarfin zazzabi, kada ka boye min pls, tun da har na aminta da kai na baka labarina dayake sirrina kaima ya kamata ka sanar dani taka damuwar, ko da bazan iya sama maka mafita ba, zan tayaka da addu'a." marairaice masa fuska ta yi.
Shiru yayi jim yana tunanin ya zata ɗauki abun in ya fada mata,
Cikin sanyin murya ya ce, "Ummi mun fara gano su wanene Elders na gidan Kurkukun ƙaddara! Kuma muna zargin uncle din ƙawarki Benazir yana ɗaya daga cikin su..."
Bai ƙare maganar ba ganin yadda ta zare idanunta, walwalar fuskarta ta ɗauke tamkar bata ta6a yin dariya ba.
A dabarbarce ta ce, "Sir ka san me ka ke faɗa kuwa? Wallahi ba dan ina ganin girmanka ba da ba abun da zai hana..." Kasa ƙarasawa ta yi, can kuma ta ce, "Bazai yiwu ba, big boss baya ɗaya daga cikin su, saboda shi ba matsafi bane kuma ba mugu bane, ni nasan wanene big boss! Nasan halinsa ciki da bai, pls ku sake bincike akan shi zaka tabbatar da abun da nake faɗa maka!" Rai a ɗan 6ace ta faɗa, ta haƙiƙance akan gaskiyarta.
"Ke baki tunanin mutumin nan da wata mummunar manufa yake atare dake Ummi? Ke fa malama ce, kina da tarin ilimi akan ki, kinsan mai kyau da mara kyau, taya zaki yi tarayya da fasiƙi kuma har kina kare sa daga laifin da ake tuhumarsa...?"
"Baki tunanin saboda kin nuna baki son shi dr. Shureim kikeso shiyasa ya ƙulla makircin da ya shiga tsakanin ki da shureim ya kuma raba ki da mahaifinki saboda yasan bazai bari ki aure shi ba tunda baki son shi, sannan bayan kin gudu da tsakar dare tayaya akai har kika haɗu da shi a wannan lokacin? Shi Aljanine baya bacci ne? Ba yadda za'ayi ya fito in the midst of the night batare da wani ƙwaƙƙwaran dalili ba, gaba ɗaya plan dinsa ne Ummi..."
Shiru tayi jim ba tare data furta kalma ba, bata san tayaya zata fahimtar da Chief ba, gani take kamar ya fara zarewa.
"Kiyi amfani da hankalinki Ummi, meyasa ya ɗauki nauyin karatunku a ƙasar germany? ya kuma kama maku hayar gida, bayan haka duk weekend sai ya kawo maku ziyara har ya kwana agidan ku," ya faɗa yana kallon cikin idanunta.
Gaba ɗaya tabi ta ruɗe, sai dai kwata kwata bata gasgata maganarsa ba, saboda ta yarda da Uncle Musa fiye da kowa tun da ita ya yi mata hallacci, ya so ta a lokacin da kowa ke gudunta, ya zama danginta a lokacin data rasa dangin da zata jingina da su.
Murmushin takaici ya dan saki, saboda ya fahimci ta cikin sauƙi bazata yarda da shi ba,
Zura hannunshi ya yi cikin front pocket na jallabiyarsa ya zaro hotuna,
Kamar daga sama ta ji ya ce, "Nasan har yanzu kuna a tare Ummi, saboda akwai ranar da ya kira ki a waya kin shiga toilet, Batool ta gani ta ɗauka batare da sanin ki ba, a yanzu haka ina da hujjojin da za ki gasgata magana ta.."
She was utterly perplexed, but she didn't believe his words at all.
Ya ƙarashe maganar tare da ɗaura mata hotunan akan table dinsa, lokacin da ta daura idanunta akan hotunan wata irin firgita ta yi, gaba daya tabi ta rude, muryarta da mamaki ta ce, "Sas.. Sir ina ka samu waɗannan hotunan?"
Ta tambaya aƙagare da son jin amsar shi, bai tanka mata ba, har saida ya zaro ɗayan hoton ya jera shi da sauran hotunan..
Lokaci ɗaya ta ƙara ruɗewa, labbanta na kerma ta furta, "Baby preety, Sir Ina ka samu hotunan su um??"
Numfasawa yayi kafin ya ce, "zan faɗa maki inda na samu hotunan amma ki fara faɗa mini miye alaƙar dake atsakanin mutanan dake a cikin hotunan nan?" Jinjina mashi kai tayi kafin ta fara kora masa bayani,
"A tare na san shi da Natasha, sun daɗe a tare, karuwarsa ce kuma baturiyar england ce, ita kuma baby preety rainon ta ya kawo mata tun tana jaririya, amma lokacin da ta kai shekara sha shidda ta ce min ya kar6e ta, ya mayar da ita gurin mamanta da ke anan Nigeria.."
Runtse ido chief Owais yayi saboda takaicin da ya turnuke zuciyarsa, aransa ya ayyana hakan na nufin ƴan biyu ne ita da ƴar wurinsa! Kamar yadda su ka yi tsammani, Ya sadaukar da ɗaya, ita kuma ɗayar tana agurin mamanta.
"Sir meya faru um? Dan Allah tun da na amsa maka tambayarka, nima ka fadamin a ina ka samu hotunan su! Na ƙosa na ji."
Miƙa hannu yayi cikin table drawer din gabansa ya curo diary ɗin Unaizah ya ɗaura mata akan table din, "kinga inda na samu hotunan, Kuma diary din nan mallakin ɗaya daga cikin fursinonin kurkukun kaddara ne, nasan ba zaki manta yarinyar da Unaisah ta bada labarin mahaifinta da ya yaudareta ya sadaukar ita gidan kurkukun kaddara a matsayin Korean School...?"
Wani irin faduwar gaba taji daram dararam kamar ana buga gangunan yaƙi a ƙirjin ta.
Yatsun hannunta na kerma ta buɗe diary din ta soma karanta shi,
Wa'iyazubilla! tana karantawa yayin da brain dinta ke tariyo mata fuskar yarinyar, tabbas ta yarda diary din mallakin baby preety ne babu tantama saboda yawanci duk abunda ta rubuta a cikinsa ta ta6a jin labarin a bakin Natasha.
Bata ƙarasa karantawa ba, ta rufe diary din tare da kifa kanta saman shi, wlh bazan iya misalta tashin hankalin da ta shiga ba, She was completely bewildered and shocked, unable to believe it, Aranta tana jin ba zai yiwu uncle Musa ya iya aikata rashin imanin nan ba, mutun mai tsoron Allah da tausayi irin sa would never do such terrible thing, amma kuma ta fara kokwanto saboda in har ba a diary din baby preety ba, to kuwa babu inda za'a samu hotunan Big boss da Natasha da kuma na baby preetyn, sai dai bata so ma zargin su akanshi ya zamana gaskiya.
"Yanzu kin yarda da maganata ko kuwa kina akan bakanki"
Jinjina mashi kai ta yi, "Bani da matsaya, amma na yarda da big boss, kuma na yarda da kai, sai dai bazan iya yarda da abun da ka fada akansa ba, wadannan hotunan na yarda a cikin diary din baby preety aka same su amma bana tunanin itace yarinyar da Unaisah ta bamu labarin ta, please na roƙe ka ku sake bincike akan shi.."
Duk yadda Chief ya so ya kwatanta mata cewa ba mutumin kirki bane taƙi yarda, tana akan bakanta saboda ta aminta da mutuminta, yadda kasan wadda aka asirce, kwata kwata bai ji haushinta ba saima tausayinta da ya mamaye zuciyar shi saboda ya lura ta ruɗe ne sosai kuma bata son zargin da suke yi ya tabbata akan shi saboda halin da zata shiga, shiyasa tun farko baima yi tunanin faɗa mata komai game da babynta ba saboda gudun halin da zata shiga.
"Ummi, Zan baki lokaci kije ki yi tunani akan abun da na faɗa maki, sannan ko da baki yarda ba, Inaso ki bamu hadin kai please..."
Girgiza kai ta yi, "Ka yi haƙuri ba zan iya ba, nayi masa alkawarin bazan ta6a bari wani ya san muna a tare ba, in har ya ji na karya masa alkawari bazai ji dadi ba, zaiga kamar na ci amanarsa ne, ni ko maganarsa bana son yi da wani." Zuciyarsa ta sosu ransa yaso ya 6aci, sai dai bai nuna mata a fuska ba..
"Zaki iya tafiya..." Har zata miƙe ya tsayar da ita, "Zan gargaɗe ki, Kada ki kuskura ki bari mutumin nan ya gane abunda muke zargi akansa! bama shi ba, ko da ƙawar nan taki ce, idan har na ji maganar nan agurin wani, hmm, ba abun da zai hana in garƙame ki a cell kuma kema zaki shiga cikin zargin da muke akan sa, sannan kada ki canza masa ku cigaba kamar yadda kuka sa6a."
Maganarsa ta ɗaga hankalinta, dama da biyu ya yi mata barazana, fuskarta ta jiƙe sharkaf da gumi, kwata kwata babu walwala atare da ita, Ya rudar da ita ba kaɗan ba, Ya kuma tsoratar da ita.
Hanky ya miƙa mata, "Share zufar dake akan fuskarki, don bana so wani ya gane halin da kike a ciki."
Cikin rawar hannu ta kar6i hanky din ta soma share gumin fuskarta, har ce mata yake yi, "Ki share da kyau fa.." tace toh, bayan ta gama ta juya zata tafi da hanky ɗin ya dakatar da ita, "Bani abuna.." miƙa masa hanky din ta yi, ko waiwayensa bata yi ba saboda a ƙagare take da ta bar sitting room din nasa..
Lumshe idanunshi yayi tare da jingina bayan shi jikin kujarar, bawan Allah abun duniya ya ishe shi, saboda gujewa tunanin da zai haifar masa damuwa yasa baya barin zuciyarsa hakanan batare da yayi tasbihi ba 💔
Bayan fitar Ummi daga dakin, jikin bango ta jingina bayanta, yayin da zuciyarta ke tariyo mata wasu abubuwa da suka haifar mata da kokwanto akan mutuminta! bakomai ta fi tunawa ba face ranar data fara ganin Danish babu shirt a jikinsa! zanen tattoo dinsa ya tsaya mata a rai, har yau bata manta ba, saboda sak irin na big boss ne, kamar anyi photo copy dinsa an ɗaura masa abayansa, kuma tun da take mu'amala da americans bata ta6a ganin mai irin tattoo dinshi ba, sai akan Danish shiyasa ranar data ganshi al'ajabi ya kamata, bayan haka maganganun da Chief ya faɗa a game da shi sun tsaya mata a ƙahon zuciya, tabbas diary din baby preety ne, agurin ta kaɗai za'a samu hotunansu, wani abu da ya ƙara ruɗar da ita nickname dinsa da ta gani a rubuce cikin diary din Preety, kuma a labarin da Unaisah ta basu ta fadi sunan mahaifin Unaizah yar gidan daddy, gaba ɗaya dai kanta ya ɗaure tamau, kwakwalwarta ta rikice sai tufka da warwara ta ke yi.🍁
"Ummi, kun gama magana da Chief dinne?" Cikin kunnanta ta tsinkayi muryar Taj, a firgice ta dube shi yana zaune kan wheelchair dinsa, danne damuwarta ta yi ta kakaro murmushi kan fuskarta, "Eh mun gama magana da shi, shine ma ya ce min in tafi.
Sarai ya lura akwai damuwa atattare da ita sai dai kawai ya basar.
"Yakamata ka ajiye wheelchair din nan, tun da ka fara samun sauƙi, idan ba haka ba zaka manta yadda ake yin tafiya da kafafu," Ta faɗa da zolaya.
Murmushi ya sakar mata, "wlh iya yine irin nawa, kinsan ance sabo turken wawa, ɗan hawan ta da nake yi yasa har na saba da ita.." ya faɗa yana ƙoƙarin mikewa, A hankali ya samu ya tsaya kan kafafunsa, murmushi ta yi mashi, "in shigar maka da kujerar ciki?"
"No, bana so Unaisah tasan na samu lafiya, tafi ji da ni Allah, duk in zata ganni ina gungura kujerar jikinta na 6ari take kamamin ta tura ni.."
Duk da halin damuwar da take aciki hakan bai hana tayi dariya ba, maganarsa ta bata nishadi ashe lambon ciwo yake ma Unaisah.
Bayan ya shiga sitting room din Chief, Jiki asanyaye ta wuce bedroom dinta, tana kallon Unaisah da Batool zaune kan rug, sun baza textbooks dinsu da alama karatu take koyawa Batool, bata bi takansu ba, cikin sanɗa ta wuce don kada su ganta saboda a halin yanzu tafi bukatar kadaici..
Luxury-incense By Sapnah Borno.
Ta kawo muku turarukan wutan su Na maiduguri dana chad, turarukanta masu masifar dadi da kama waje harma da daukar hankali, indai kikayi kabbasa da turaren ta har wajen da kika zauna indai kika tashi sai kin bar kamshin ki, sannan Tana saida mayukan gashi irin nasu na shuwa Arab masu tasirin gaske, wajen gyaran Amare kuwa babu magana dan tazo muku da Chadian and Sudanese dilka Wanda zaki gyara jikinki da kanki, oga ya kasa ganeki, haka zalika akwai wata humrar ta mai suna hana bacci da kuma sirrin shuwa Abun ba magana, yar uwata ki jarraba turaren yar mutan borno nasan zata zame miki best turaren wuta plug. Tanada turarukan da zaki turara gida, toilet, bedsheets, curtains, kabbasa and hair incense ku jarraba kada ku bari ayi babu ku.
Wardrobe balls
Kabbasa spray
Chadian khumra
Hawee
Halud
Gabgab
Sandal sukkariya
Kajinguru
Dilka soap
Ready to use dilka
Karkar oil
Turaren tsuguno
Habil
Dorut
Dorot after period
Brown khumra
Dufr khumra
Body milk
Sudanese kuleccam
Chadian dufr kuleccam
Musk khumrah.
Maganin matan mu sunada inganci Wanda muke kawo su daga sudan, sannan munada maganin karin girman nono, Wanda basuda effects, ga masu bukatar maganin Matsi ko maganin mata Masu aiki garanti munada su, sannan muna zuwa gyaran jikin amarya a duk garin da take
Our Chadian aphrodisiacs are.
Beejay fire
Sata jagab honey
Wetness and sweetness combo
Daka
Great A sabaya
Breast engagement powder
Ciccibi
Gumbar madara
Gumbar dabino
Bita Zaizai
08093772168
*Welcome, Littafin kurkukun ƙaddara 500 ne, dukanshi Book One two and 3 Idan kin shirya biya ga Details da zaki tura*
3196407426
First bank
Bature Hafsat Muhammad,
*bayan kin tura zaki bada transaction reciept ko screenshot na debit alert a matsayin shaida ta wannan number din 08103884440*