Kurkukun Ƙaddara Takun Ƙarshe Page 73 Complete

Kurkukun Ƙaddara Takun Ƙarshe Page 73 Complete

Takun Ƙarshe

Aslm barkanmu da wannan lokaci 

Ina Mai farin cikin sanar daku cewa Zuzeam ventures takawo maku ingantattun magunguna masu inganci cikin Aminci Muna da kaya kamar haka

 Mallaka Maganin sanyi

Maganin cire tumbiMaganin farin jini

Maganin matsiMaganin mata

Maganin sa ni’ima da dandano

Dulka Amare Set na gyran jiki

Set na amarya

Tabaje tsumin Gomba

 Xuma kiba ta hips and Brest

Magungunan gyran Brest

Magungunan Karin hips

Maganin sliming

 Muna da kaya masu inganci cikin sauki da rahusa 

Ina wadda keneman mallaka sahihiya quaranty wlh hajiya kixo ga zuzeam ventures xakiji ddin mallaka duk fadin ran ogah duk fadansa wlh sai yyi sanyi 08144015291

Idan maganin mata kikeso akwai 

Idan gyran jiki kikeso gyran fata gyran Brest magungunan sa kiba da hips 

DOMIN samunta Kai tsaye kira wannan no 08144015291 DOMIN mgn da ita whatapp 08144015291muna tura kayanmu ko ina cikin iKon allah 🥰👌🏻

Bononza Bononza Tsimin kaninfari 1k Tsimin dabino 1k Gumba 700 Gumba aya da nonon rakumi 700 Garin kafi ciccibi 500

Garin bata gaban kishiya 500

Matsin mallaka tada zaune tsaye 2500

Turaren mallaka ba aba mai kishiya 2500 Total kayan 9500

Za a bakisu akan 4k

Kuma mutun goman farko nadakyautar Abun 2k

🗣️🗣️🗣️🗣️🗣️🗣️ ASSALAMU ALAIKUM ALHAMDULILLAH YAN UWA NEW PROMO YA KAMMALA💃🏽💃🏽💃🏽😁😁😁 da 5k dinki ki kwashi kayan 12k hajiyata 💃🏽💃🏽💃🏽😃🙃Kazar gadali ta mallara Rabi 3500 Tsimin gam gam 1500 Ruwan kara zunzurutun dadı😋800 Garin 7in1 1k Gumba 3 balai 500 Gumba kwakwa da dabino 500 maganin Infection 1k Garin zunzurutun dadi 1200 Matsin ba a fira d wando 500 Matsin infection mai matse mace gam 500 12k All at 5k https://wa.link/l1gcz8 kedai dannan link dinnan don samun naki ki maza kiyi bucking koda kudinki saida Rabonki

*Daga Alkalamin Boss Bature💋✍️*

Sallamar Taj ce ta katse tasbihin da ya ke yi, A hankali ya buɗe idanunsa da suka kaɗa sukai ja ya dube shi bayan ya amsa mashi sallamar..

Fuskar Taj da damuwa ya zauna kan sofa yana fuskantar sa..

"Haba Owais, har sai yaushe ne zaka fadamin abunda ke damunka? Ko kafi son in yi ta zama cikin damuwa ne? Unaisah ta ce min ka ce za ta ji a gurina kuma nima din ka ƙi sanar dani ba yadda banyi da kai ba..." ya faɗa yana mai nuna 6acin ransa .

Cikin sanyin murya Chief ya ce, "Am sorry, nasan ban kyauta ba, amma ka ƙara hakuri zuwa gobe idan muka shiga meeting zaka ji komai..." 

Gyaɗa kan shi ya yi, "Allah ya kaimu da rai da lafiya" ya amsa da ameen

Shiru suka ɗanyi Jimm kowa da abun da yake saƙawa a ran shi..

"Please Owais, duk da bansan meya faru ba, amma tun ranar daka dawo daga yanayin ka na lura babu kwanciyar hankali atare dakai, da akwai wani mummunan abu daya faru, saboda ba karamin abune zaisa ka ki kulamu ba, kuma ka kulle kanka adaki, sannan baka son cin abinci, ka rame, even the chefs have complained about your lack of appetite, pls ka yi hakuri kada ka bari damuwa ta yi maka illa, nasan kai mutunne mai tawakkali, har burgeni ka ke yi saboda jarumtarka, da wuya mutun ya iya gane kana a halin damuwa, sai in tura ta kai bango ne ake iya gane me kake a ciki..." 

Murmushi ya yi yana sauraron future in-in law ɗinsa, yana ƙara jin ƙaunar sa a zuciyarsa, da duk wani wanda suke rayuwa a gidan saboda yadda suke nuna damuwa akan shi, suna son shi suna son farin cikin shi, ranar da ya kulle kanshi a ɗaki abun da ya karya mashi zuciya yadda suka dinga zarya a ƙofar ɗakin suna masa magiya don ya buɗe masu, ta ya bazai gode da ni'imar da Allah yayi masa ba?

Sosai Taj yake lallashinsa tare da kwantar masa da hankali,

"Ni bansan da wasu kalmomi zan yi amfani gurin yi maka godiya ba, sai dai ince Allah ya faranta maka kamar yadda ka faranta mini, Allah ya ƙara dankon zumunci da kauna atsakaninmu.." Ya amsa masa da Ameen, fira Taj ya fara jan shi da ita duk dan ya kawar mashi da damuwa ya saka shi nishadi..

"Wa zaka fara aura a cikin su? Ina son in san matsayin ƴata," Ƴar dariya chief ya yi tare da kai hannu ya shafa sajen fuskarshi, cike da jin nauyin shi ya ce, "A rana ɗaya zan aure su." Taj ya ce, "Ban yarda ba, wayo zaka yi mini, kawai ka faɗamin wacece amarya wacece kuma uwargida." 

Ƴar dariya Chief yayi, "Nazli ce uwargida saboda ta girmi Unaisah, ina so Unaisah ta ɗauke ta a matsayin yayarta, ta haka ne zasu mutunta juna.."

 Murmushi Taj ya yi. "That's a good idea, amma yakamata ka sanar ma Unaisah ba ita kaɗai zaka aura ba."

"I couldn't tell her I left it until the time comes, In sha Allah..." 

Kafin Taj ya ƙara magana wayar Chief ta fara ruri, idonsa ya kai kan screen din wayar tasa dake saman table, sunan sheikh Imam Malik ne ya bayyana, janyo wayar ya yi tare da yin picking ya kara a kunnansa...

Bayan sun gaisa Sheikh Imam ya ce mashi ya yi haƙuri ya ji shiru bai neme sa ba, yanzu yana son yin magana da shi in yana free,

Cike da ladabi ya ce toh a ina zai same shi? Bayan ya faɗa masa address din suka yi sallama ya mayar da duban sa kan Taj

"Sheikh Imam yana nema na." Taj ya ce, "Ok, ko zamu iya tafiya tare?" Ya amsa. "Eh."

 


Duk da baisan ko shi kaɗai sheikh Imam yake son gani ba amma yasan Taj bazai bada matsala ba..


A motar Taj suka tafi, bayan sun ƙaraso apartment building din da Imam Malik yake a parking space suka aje motar, lokacin da suka fito sai ga sheikh Imam ya fito sanye da Jallabiya, fuskarsa da fara'a ya nufe su, cikin girmamawa suka gaisa da shi. "Bismillah, mu shiga daga ciki..."


A apartment living room dinsa suka tsaya, bayan kowannansu ya zauna kan sofa ya miƙe ya nufi ciki, jim kaɗan ya dawo hannunshi ruƙe da ƙaramin tray mai dauke da drinks ya ajiye masu akan table da fara'arsa ya ce, "Sai fa kun yi hakuri, kun zo gidan gwauro, ni nake komai nawa, don ma bana jin dadi ai da har girki zan yi maku."


 Murmushi suka saki gaba dayan su.


Chief ya ce, "Da nasan baka da iyali tuntuni dana sa an kawo maka house helpers wadanda za su taimaka maka da ayyukan gidan.." 


Ƴar dariya ya yi. "Daka kyauta Owais, amma fa kada ku damu na saba, bana jin wahalar ayyukan gida, tun da safe nake tashi inyi share share da goge goge, idan na gama in kuma girka abun da zan ci.." Waro idanu suka yi Taj ya ce, "Gaskiya ba zamu bari ka ci gaba da zama babu iyali ba, waɗannan ayyukan bana maza bane, a shekarun nan naka hutu kake bukata..."


 Murmushi sheikh ya yi, ya ji dadin yadda suka nuna damuwa akan shi.


"Bismillanku," 


Ya faɗa yana nuna masu drinks din, har zai zuba masu, chief ya yi saurin kai hannu ya ɗauki juice ɗin ya tsiyaya masu a cups, kowannan su ya ɗauka ya sha.


"Na ga ku biyu kuka zo, shima yasan komai ne"? A ruɗe Taj yake kallon sheikh da ya yi tambayar...


Chief ya ce, "A'a na bari sai mun haɗu gurin meeting zan sanar da su komai tun da atare muke gudanar da binciken case din, kuma Taj da iyalinsa sun bamu gudummuwa sosai..." 


murmushi sheikh Imam ya yi. "Ma sha Allah.." 


Shiru suka ɗan yi, da Taj ya lura kamar akwai abun da sheikh ke son ya tattauna da Chief a sirrance sai ya yi dubarar miƙewa tare da curo waya ya ce, "Ina so zan yi waya." amsa mashi suka yi da toh, Ya nufi ƙofa yana ɗangyasa kafa Sheikh ya yi mashi addu'ar ƙara samun lafiya, bayan ya fuce cikin mota ya koma, Benazir ya danna ma kira bayan ta ɗaga suka fara shan soyayya..



"Ya mutanan gidan naku Owais?"


"Suna nan lafiya, Alhamdulillah."


"Baban naku fa?"


"Har yanzu bai buɗe ɗakin ba, Kuma ya ce baya son mu buɗe shi, mu bar shi har zuwa lokacin da muka kama sauran Elders din zai fito da kan shi.."


"Kun yi magana da shi ne?"


 Jinjina mashi kai ya yi, kafin ya labarta masa abun da suka tattauna da shi, ya ƙara da cewa, "Yana cin abinci idan muka kai ma shi..." 


Shiru sheikh imam ya yi a can kasan zuciyarshi wani irin tausayin rayuwar ahalin Obie ne, dama saida ranshi ya bashi Obie bazai iya guduwa yabar ƴa'yanshi ba koda za'a kashe shi ne da azabtarwa, saboda yasan yadda yake tsananin son su, ta wani bangaren hankalinsa ya kwanta saboda baya son baba Obie ya gudu ya fi son ya tsaya ya kar6i hukuncin da za'a yi masa koya samu sassauci agurin hukuma.



"Owais, Ni ba mazaunin Abuja bane, Idan har ka ganni a abuja to gayyatata aka yi wani muhimmin taro ko wani aiki ya kawo ni, a ranar da abun ya faru na 6oye maku gaskiyar abun da yasa na shiga jikinku, saboda na ga hankalinku ba akwance yake ba, kuma nasan muddin na faɗa zaku ƙara shiga damuwa, shiyasa na ce zan neme ka a waya tun da kai ne jagoran binciken case din nasu.."  


Ya ɗan dakata yana duban Owais da ya nutsu yana sauraron shi


"Ban ji daɗi da ya ƙi faɗa maka su wanene sauran ba, amma karka damu in sha Allah zamu dage da addu'a har sai asirinsu ya tonu...."


Numfasawa ya ɗan yi, kafin ya ɗaura da cewa, "Shekara kusan takwas da suka gabata, mun yi babban rashi na abokin mu ɗan kungiyarmu ta malaman ahlussuna, mai suna Malam Jazuli shi da ƴa'yanshi guda biyu. Ya ta6a kira na awaya kafin afkuwar lamarin a lokacin bana a ƙasar, ina a gidan Uncle dina dake a Sudan, a lokacin da ya kira muryarsa babu nutsuwa ya ce shiekh Imam Allah abun tsoro ɗan adam abun tsoro, na ce masa meya faru? Ya amsa min da cewa ya ga abun da ya ɗaga hankalinsa akan hanyar dawowar shi daga Kano, Uziri ya kama shi har ya yi parking motarsa a gefen titi, ya fito daga motar hannunsa ruke da robar ruwa ya ratsa cikin daji don yayi uzirinsa, bayan ya kammala yana kokarin miƙewa ya jiyo kukan jarirai can nesa da inda yake, lamarin ya ɗaure masa kai, ya yi ta mamakin meya kawo kukan jarirai a cikin dajin Allah? 



Har zai tafi sai kuma ya ji bazai iya tafiya batare da ya ga a ina kukan nan ke fitowa ba, saboda zuciyarsa ta shiga raya mashi zai iya yiwuwa yada su aka yi ko kuma mace ce me ciki wata ƙaddarar ta afka mata da har ta haife su a cikin daji. Bai yi ƙasa a gwiwa ba, Ya ratsa cikin dajin yana ta mamakin yadda ya iya jiyo kukan tun daga inda yake bayan akwai tazara mai nisa tsakaninsa da inda yake jiyo kukan jariran, ba ƙaramar wahala ya sha ba har ya fara tunanin kodai kukan jariran bana mutane bane, saidai kuma ya kasa haƙura ya koma, yana cikin tafiyar kwatsam ya ƙaraso wani guri mai manya manyan bishiyoyi, duk da marece ya nutsa duhu ya fara bayyana hakan bai hana shi ganin meke wakana ba da taimakon hasken wutar dake ci jikin firewood...


La6ewa ya yi bayan bishiya yana leƙen su ganin manyan mutane zaune saman buzu, kwata kwata babu sutura a jikinsu sai jan ƙyallen da suka ɗaure ƙugunsu da shi, daga tsakiyar shimfiɗar ta su jarirai ne sabuwar haihuwa su biyu kwance saman jan ƙyalle sai tsanyara kuka suke yi kamar ran su zai fita.


Gaba ɗaya ya ruɗe ya rasa gane meke faruwa? Su wanene waɗannan mutanen masu kama da bokaye? Me zasu yi da jariran nan...


Bai ƙarasa zancen zucin nashi ba maganar wani daga cikinsu ta ratsa kunnanshi.


"Me kake nema? Daukaka ko arziƙi ko wani kake so a yi ma sihiri? 


Muryar dattijo ya jiyo yana faɗin, "Arziƙi ranka shi daɗe, na gaji da talauci, shekara saba'in a duniya har yau ban mallaki gidan kaina ba, ba ci, ba sha, ba suturar sanyawa ta kirki, mutane har tsangwamarmu suke yi suna kiran iyalina da iyalan faƙiri, so nake ku azurtani ta yadda zan zama hamshaƙin mai kuɗi, shiyasa na kawo maku jariran nan ƴan biyu ne, Jikata ce ta haife su bata san na ɗauko su ba"


Mahaukaciyar dariya suka saka gaba dayansu kafin daga bisani suka ce ma shi ya tashi ya tafi daga rana irin ta yau ya gama talauci a rayuwarsa, duk wanda zai rabesa sai ya yi arziƙi, sannan in akwai wanda ke buƙatar taimakon su, ya haɗa shi da wanda ya yi masa hanya har ya samu ganawa da su." yana faman washe baki ya amsa da toh,


Wani daga cikin dattawan ya ce Sadaukarwar da ya yi ta mallaka ce, In har mutun ya mallaka masu ɗa, koda yana a cikin uwarsa ba a kai ga haihuwarsa ba zasu iya biya masa buƙatarsa, amma fa a bisa sharaɗin koda bayan wanda ya yi sadaukar ya mutu ne sai sun kar6i jinjirin in aka haife sa, kuma basu yarda da asara ba, in suka baka bashi sai ka biya su, dattijon ya amsa da toh..


Hankalin malam Jazuli ba ƙaramin tashi ya yi ba ganin abun yake kamar a mafarki, bayan tafiyar dattijon ya ci gaba da yi masu labe, anan ya ji suna maganar zasu kai yaran kurkukunsu don a raine su.


 Ya ce min a lokacin bai ƙarasa jin maganganun nasu ba jikinsa na bari ya baro cikin dajin ya shige motarshi, ya bata wuta...


Abun ya tsaya mashi a rai, sai dai baisan su wanene suke aika aikar nan ba, amma ya ƙudiri aniyar sai ya gano su saboda bazai bari ana aikata fasadi a doron ƙasa ba.


Baisan ya zai yi ba, kullum da tunanin bayin Allahnnan yake kwana.


Bayan wata biyu da dawowarshi Jos, Kwatsam a wata ranar juma'a ya je masallaci yin salla, bayan an kammala yana akan hanyar dawowarsa gida yanata tunani har baisan ya hau titi ba, mota tayi masa horn a ɗan firgice ya ja baya,


Mai motar ya zuge glass ya fara zazzaga mashi masifa yana faɗin bai da hankali ne zai hau kan titi ko shi makaho ne?


A lokacin da ya dubi fuskar mutumin wani irin faɗuwar gaba ya ji ganin tsohon nan fakiri da ya ta6a gani a daji wanda yaje sadaukar da jikokinsa, lamarin ya daure masa kai har ya kasa tanka masa, mamakinsa yadda yayi arziƙi in a short time, saboda motar da yake a cikinta ta kai ta miliyan ɗaya da rabi lokacin.


Haƙuri ya bashi bayan ya tada motar ya tafi, ya ce na yi saurin tsayar da mai abun hawa na ce ya bi mani bayan motar, mai abun hawan ya kawoni unguwar da yake har layin gidan mutumin, nan fa na ga abun da ya kara daure mini kai ganin gidan da motar ta shiga ya haɗu.


Bayan na dawo gida na yi ta tunanin tayaya zan shiga jikin dattijon nan don in gano su wanene waɗannan mutanan?


 Dubara ce ta faɗo min tunawa da maganganun da su ka yi da mutanen, nan na shirya kaina cikin yagaggun kaya da suka jikata, na sanya takalma ware daban daban, na yi shigar talaka futuk.


Na je har gidan dattijon nan faƙiri da ya dawo mai arziƙi, na yi masa sallama bayan ya fito na zuƙunna ƙasa na fashe da kuka na dinga rokonsa akan ya taimaka min da abun da zamu ci, Iyalina bata da lafiya ga ciki a jikinta, tun safe nake bin gidajen masu hali don su taimaka mini amma babu wanda ya kula ni don Allah ya taimake ni kamar yadda Allah ya taimake sa..." 


Daɗin baki na shiga yi masa, da farko ya ɗaure min fuska kamar bazai taimaka min ba, sai kuma ya zaro kudi bendir ɗaya ya bani ya ce ya taimake nine saboda Allah saboda kuma shima ya taba shiga irin halin da nake a ciki.


Ƙin kar6ar kudin na yi nace masa idan ya bani yau wa zai bani gobe? Na nuna masa bawai don na raina abin da ya bani bane sai don bana so zuciyata ta mutu in koma ina bara da maula, nafi son ya taimaka mini da jari mai ƙarfi, ko ya sama mini aikin da zan dinga yi har in samu wadatar da zan iya ɗaukar nauyin iyalina.


Bai kawo komai aransa ba ya ce nayi tunani mai kyau, In bashi number ta zai neme ni idan ya sama min aikin."


 Jikina na kerma na curo ƴar karamar wayata da ta ji jiki na miƙa masa, da ya kar6i wayar har jujjuyata yayi ganin yadda ta rakwarkwa6e, bayan ya saka min number ya ce in tafi, na yi masa godiya na nufi gidana.


Bayan kwanaki uku ina ta jiran kiransa shiru shiru har na fara fidda ran zai neme ni, kwatsam a cikin kwana na huɗu saiga kiran tsohon ya ce min yana taya ni murna ya sama min hanyar da zan samu jari, na ce Alhamdulillah ya tambayi ina da kudin abun hawa ko kuwa ya zo ya ɗauke ni? Na ce mashi zan ranci kudi in zo, ya ce mini a'a yafi so ya zo da kanshi saboda ya ga iyalina" 


Da jin hakan sai gabana ya fadi na fara tunanin tayaya zan samu iyalin ƙarya wadanda suka jigata? A gurguje nabar gidana na nufi bakin titi, da akwai wasu almajirai da suke bara agurin, mata ce mai jiki tare da ƴa'ya guda biyu, da matar na haɗa baki bayan na yi mata alƙawarin zan biya ta kudi masu yawa in har tayi abun da nake so ta ce mini ta amince.


Bayan nayi shigar basajan da nike yi, na kwashe su a abun hawa ita da yaran nata muka nufi wani kango na ginin da na fara yi.


Anan muka zauna ni da su, kafin ƙarasowar shi nabi mutanan dake rayuwa a layin na basu cin hanci saboda koda ya tambaye su dangane damu su faɗa mashi sun san mu da kuma halin talaucin da muke a ciki. Haka kuwa aka yi bayan ya ƙaraso bai kira ni a waya ba saboda wayau sai ya fara tambayar matasan unguwar ina ne gidan Barau matalauci, suka nuna masa kangon suka ce anan muke da zama, kuma kongon ma ba namu bane, wani bawan Allah ne ya bamu shi don mu zauna ganin yadda muke ta garari muna neman matsugunni.


Da jin wannan maganar sai ya ji tausayinmu ya mamaye zuciyarsa, kusan duk wanda ya tambaya amsa ɗaya ya ke bashi hakan yasa ya yarda da ni.


Bayan ya shigo cikin kangon ya taras damu a zaune kan tabarma, yaran matar suna ta kuka suna fadin baba yunwa muke ji, ita kuma almajirar sai faɗa take min tana faɗin, "wai ba zaka tashi ka nema mana abun da zamu ci ba? Jiya haka muka wuni ba ci ba sha, ko so kake mu mutu ne?"


Sallamar mutumin ce ta katse mu, dama mun san da zuwanshi da gangan muka nuna kamar bamu lura da ya shigo ba, jiki na 6ari na miƙe na je gaban shi ina kuka na ruƙe kafafunsa na yi masa magiya akan ya taimake mu ya dubi halin da muke a ciki, tun jiya rabon mu da abinci, na yi fafutuka amma ban samu komai ba.

Cike da tausayawa ya ke duba na, bayan ya gaisa da iyalin nawa yace in same shi a mota.

Yana fita nabi bayan shi, bayan mun zauna ya ce da ni kamar yadda ya faɗamin na samu jari sai dai baisan ko zan iya bin sharuɗdan ba, saboda sai an kauce hanya..." na ce mashi koma wani irin aiki ne zan yi, in dai bai sa6a ma mahaliccina ba,

Ya ce min, "baka ji me na ce bane? Dole sai an kauce hanya, in har kana son ka zama attajirin mai kudi cikin kankanin lokaci.." Na ce masa toh ya faɗamin inji in zan iya.

Yana murmushi ya ce, "Sadaukarwa ce, in har kana so zaka bada ya'yanka ko jaririn dake a cikin matarka, idan har ka yi hakan ta zaka samu abun da kake so." Hankali a tashe na ce Alhaji bangane me kake nufi ba? Ya'yana fa ka ce, wace irin sadaukarwa ce wannan? me kuma za'a yi da ƴa'ya na?"

Kwantar min da hankali yayi tare da cewa ba wani abu za'ayi masu ba, Uban gidansa ne Allah bai basu haihuwa ba, shine yake neman yaran da zai raina a matsayin nasa, In har na bashi ƴa'yana zan samu abunda nake so kuma yaran nawa zasu taso cikin wadatar arziki, amma fa in har na bada su, ya zama dole in manta da su kwata kwata, don ba za su taba dawowa gurina ba.

Nuna mashi na yi ban amince ba, ya dinga tausata yana kokarin shawo kaina har dai na ce mashi na amince zan bada jaririn dake a cikin matana in ta sauka.

Nan ya ce min toh zai haɗani da ubangidansa don mu yi magana, anan ya kira sa har ya bani muka yi magana, tun daga kan muryarsa na shiga ruɗu saboda sai na ji kamar na ta6a jin ta.

Bayan wasu kwanaki ubangidan nasa ya kira ni a waya ya ce in same shi a gidan gonar shi yayi min kwatance.

Kafin in tafi saida na sallami almajiran nan da ƴa'yanta na ce su nisanta kansu da garin saboda bana so in jefa rayuwarsu cikin haɗari, sai da na haɗa musu sha tara na arziƙi kafin tafiyar su.

Bayan dana zo gidan gonar da yayi mini kwatance, cikin shigar basajan da na saba yi, A garden na iske shi zaune kan kujera, ya rufe fuskarsa da takunkumi ya kuma sanya baƙin tabarau a idanunshi.

 Hakan ya hana in gane wanene, bayan mun yi musabaha ya ce in zauna, na samu guri na zauna kan kujerar dake fuskantar shi, wani kallo na ga yana bina da shi tun daga ƙafafuna har izuwa hular dake a kaina, duk saina sha jinin jikina..

Yace min kada in damu da kallon da yake yi min, na ce masa toh.

"Saura wata nawa matar taka ta sauƙa?" ya tambaya, cikin faɗuwar gaba na ce masa biyar.

Ya ce, "Toh yanzu kamar nawa kake buƙata mu fara baka bashi kafin zuwa lokacin da zata sauka.. ?"

Na ce Miliyan ɗaya..

Miƙa hannu ya yi tare da buɗe jakar dake akan table ɗin gabansa ya zaro bandir bandir na ƴan dubu dubu ya ajiye min a gabana, ya ce in ɗauka in tafi zasu neme ni.

Na yi masa godiya da fara'ata ta ƙarfin hali, bayan ya gargaɗeni akan kar in kuskura wani ya ji maganar na ce masa toh kafin na tafi. 

Bayan na koma gida, na fara tunanin komawa gidan gonar saboda in yi masu leƙen asiri tun da na ga hanya..

A cikin kwanakin matata ta rasa gane kaina, hatta ƴa'yana basu samun kulawata, saboda hankalina ba zai kwanta

Post a Comment

Idan kuna da tambaya akan abinda Baku game ba ko kuma kuma Neman littafin da babu a nan kawai ku ajiye tambayarku a ta comment ko wani shawara da Zaku bamu.

Previous Post Next Post

Sponsored Link

Sponsored Post