Aslm barkanmu da wannan lokaci
Ina Mai farin cikin sanar daku cewa Zuzeam ventures takawo maku ingantattun magunguna masu inganci cikin Aminci Muna da kaya kamar haka
Mallaka Maganin sanyi
Maganin cire tumbiMaganin farin jini
Maganin matsiMaganin mata
Maganin sa ni’ima da dandano
Dulka Amare Set na gyran jiki
Set na amarya
Tabaje tsumin Gomba
Xuma kiba ta hips and Brest
Magungunan gyran Brest
Magungunan Karin hips
Maganin sliming
Muna da kaya masu inganci cikin sauki da rahusa
Ina wadda keneman mallaka sahihiya quaranty wlh hajiya kixo ga zuzeam ventures xakiji ddin mallaka duk fadin ran ogah duk fadansa wlh sai yyi sanyi 08144015291
Idan maganin mata kikeso akwai
Idan gyran jiki kikeso gyran fata gyran Brest magungunan sa kiba da hips
DOMIN samunta Kai tsaye kira wannan no 08144015291 DOMIN mgn da ita whatapp 08144015291muna tura kayanmu ko ina cikin iKon allah 🥰👌🏻
Bononza Bononza Tsimin kaninfari 1k Tsimin dabino 1k Gumba 700 Gumba aya da nonon rakumi 700 Garin kafi ciccibi 500
Garin bata gaban kishiya 500
Matsin mallaka tada zaune tsaye 2500
Turaren mallaka ba aba mai kishiya 2500 Total kayan 9500
Za a bakisu akan 4k
Kuma mutun goman farko nadakyautar Abun 2k
🗣️🗣️🗣️🗣️🗣️🗣️ ASSALAMU ALAIKUM ALHAMDULILLAH YAN UWA NEW PROMO YA KAMMALA💃🏽💃🏽💃🏽😁😁😁 da 5k dinki ki kwashi kayan 12k hajiyata 💃🏽💃🏽💃🏽😃🙃Kazar gadali ta mallara Rabi 3500 Tsimin gam gam 1500 Ruwan kara zunzurutun dadı😋800 Garin 7in1 1k Gumba 3 balai 500 Gumba kwakwa da dabino 500 maganin Infection 1k Garin zunzurutun dadi 1200 Matsin ba a fira d wando 500 Matsin infection mai matse mace gam 500 12k All at 5k https://wa.link/l1gcz8 kedai dannan link dinnan don samun naki ki maza kiyi bucking koda kudinki saida Rabonki.
*daga Alkalamin Boss Bature*
ISOD HEAD QUARTER AT MEETING ROOM..🔥
Meeting Room ba lafiya, tun da suka hallara, Chief ya zabga tagumi da tafukansa biyu, hakan ba ƙaramin daure musu kai ya yi ba, kiran gaggawa ya sa aka yi musu don su yi meeting, kuma sun zo ya kasa magana ko kallonsu bai yi ba, cike da ruɗu suke ta kallon fuskar sa, daga yanayinsa suka fahimci baya jin dadi ganin yadda ya faɗa, kuma akwai wani abu dake damunsa, duk da sanyin A.c ɗin ɗakin wani irin gumi ne ke keto mashi....Cikin kunnuwanshi ya tsinkayi muryoyinsu sama sama suna yi mashi magana cikin harshen turanci tamkar raɗa,
"Sir Are you Okay?"
"Sir meke damunka? Baka da lafiya ne"?
"Sir pls, gaba ɗaya mun damu da kai, ka faɗa mana in akwai abun da ke damunka.."
Dafa Kafadarsa Commender James yayi, "Owais, meke faruwa da kai ne uhum?"
Sai lokacin ya ja dogon numfashi tare da sauke ajiyar zuciya, a hankali ya zame tafukansa daga kan kuncinsa, ya zube hannayensa saman laptop keyboard din gabansa, a hankali ya ɗago da raunannun idanunsa da suka kaɗa juwar ya bi su da kallo.
Na hannun damansa ne zazzaune kan kujerun dake a gefensa na hagu, daga bangarensa na dama U.s Armies ne tare da General Noah da Taj, wannan karon hada shi Chief ya yi inviting..
"Owais, mun fahimci akwai damuwa atare da kai, daga yanayin ka muka fahimci baka da kwanciyar hankali, Pls, in ba damuwa ka faɗa mana mu nema mafita a tare, mun riga da mun zama ɗaya..." Cikin kulawa General Noah ya yi maganar yana dubansa.
Bawan Allah, kallonsu kawai ya ke yi shi kaɗai yasan meke damunsa, baisan ma tayaya zai fara yi musu bayani ba! Ya za su ɗauki abun idan suka ji cewa kakansa ne Elder! Ya Ilahi, fargaban da ya ke yi kenan shiyasa yake ta jin zullumin ya faɗa abun da ya tara su, abun da takaici.
Numfasawa yayi a hankali ya soma magana,
"Abun da ya sa na tara mu anan, saboda in taya mu murnar cigaban da muka samu a binciken da mu ke yi akan Elders na gidan kurkukun ƙaddara, ina yi maku albishir na gano wanene shugaban kurkukun ƙaddara..." Zare idanu suka yi cike da tsantsar al'ajabi jin abun da ya ce, ya basu mamaki matuka don basu taba zaton nesa zata so musu kusa ba...
"Chef ta yaya akai ka gano Elder? Abun da muke tunanin ba zai samu cikin sauki ba....?" Commender ne ya faɗa da mamaki akan fuskarsa..
General Noah ya ce, "Amma dai ka shammace mu Chief, ka yi matukar bamu mamaki..." Ya faɗa da murmushi akan fuskar.
kwata kwata basu lura da yanayin sa ba, Taj ne kaɗai ya fahimci babu lafiya, aransa ya ayyana zai yi wuya in ba wani nashi ba ne Elder, duba da yadda ya rame ga damuwa tsantsa akan fuskarsa, hakan yasa bai nuna farin cikin sa ba..
"Sir, ba dan daga bakinka na ji maganar nan ba, da sai na ce ba gaskiya bane, saboda na razana da jin ka gano mana tantirin dan ta'addan nan, amma tayaya ka gano sa? Kaina ya kulle, banyi zaton zamu iya gano sa ta cikin sauki ba.." CI ne ya fada..
COO ya ce, "Allah yasa ba mafarki nake ba, Chief pls ka fada mana wanene ɗan iskan mutumin nan uhum? Wani shegen ne? Wlh na ƙosa na ji harna fara tunanin azabtarwar da zamu yi masa, kai mutumin nan ko kotu ba zamu kai shi ba, saboda bana tunanin zasu iya yanke mishi hukuncin da ya dace, mu zamu haɗa baki mu murkushe ɗan iska a cikin cell, But, sir sauran Elders din fa?"
Wani raunannan kallo ya ke binsu da shi, sai farin ciki suke yi suna ɗurawa Elder ashariya basu san grandpa din sa ba ne, gaba ɗaya sun ƙagara da su ji wanene Elder din sai tambayar shi suke yi yayi shiru yana kallonsu,
Agent Zahra ya ce, "Zan so inga idon azzalumin mutumin nan, ƙarya ta ƙare masa, ko ya zaiji idan muka ɗamke sa, amma kuna tunanin kamasa zaiyi mana sauƙi kuwa? Tun da basa jin makamin mu, zai iya amfani da tsafi ya 6ace..." Ya faɗa da damuwa akan fuskarsa..
A hankali Chief ya dubi Taj dake ta kallonsa, ruwan hawayen da ya gani kwance a cikin idanun Chief ya ɗaga hankalinsa, girgiza mashi kai ya ɗan yi alamar kada ya karaya, cike da damuwa ya yamutsa pink lips dinsa tare da cizon lower lip din da hakoransa.
Cike da rashin kuzari ya miƙe daga kan kujerar da yake ya fuskance su tare da zuba hannayensa cikin aljihun wandonsa, gaba daya suka bi shi da kallo a ƙagare da son jin me zai ce.
Nauyin haɗa idanu da su ya ji, a hankali ya fito daga gaban kujerar ya juya masu baya lamarin ya ɗaure musu kai,
Ya ji zafi aranshi fiye da zafin ƙunar wuta, surutan da suka yi akan kakansa sun ta6a zuciyarsa, ina ga kuma sauran al'umma idan komai ya fallasu, Allah kaɗai yasan cin zarafin da za a yi musu.
Haƙiƙa Baba Obie ya cutar da su, ya ja musu zagi da cin mutunci a idon duniya, sai da ya yi silar ɗaukakar su tukunna ya tarwatsa darajar su..
Gwauran numfashi ya ja, cikin karyayyar murya, mai matukar rauni da ƙarfin hali ya furta, "Ina baku haƙuri da abun da zaku ji daga gare ni, I'm really disappointed, an karya min zuciyata, zallumi da fargaba ne suka hana in sanar da ku tuntuni..."
A ruɗe suke kallon kallon a tsakaninsu, nan take ransu ya fara basu kodai na jininsa ne Elder ɗin? Wataƙil cikin uncles ɗinsa ne, kwata kwata ba su kawo ma ransu zai zama kakansa ko mahaifinsa ba.
"Kada ka ji komai Owais, ka faɗa mana zamu fahimce ka.."
Commender james ne ya faɗa..
Cikin rawar murya ya ce, "Ba mahaifina bane, Ba kuma cikin Uncles ɗina bane, amma wanda ya yi silar zuwan su duniya shine Elder shugaban Kurkukun ƙaddara...."
Tashin hankalin da ba'a saka mashi date, Tunkan ya ƙarasa maganar A kiɗime suka zabura tare da miƙewa tsaye, a lokaci ɗaya suka ɗaura hannayensu saman kawunansu, Idanunsu azazzare cike da tashin hankali haɗi da al'ajabin da ya kamasu! Lamarin ya gigita su.
Duk da sanyin A.c din dake ratsa fatar jikinsu hakan bai hana gumi wanke gaban goshin su ba, wlh sun karaya matuka, Hankalin maza ya tashi.
A sukwane General Noah ya zame hular kakinsa dake a kansa ya kifa ta saman table dinsa..
A dabarbarce Commender James ya furta, "Owais, kana cikin hayyacinka kuwa? Kasan me kake faɗa? Ko ka sha giya ne uhum? Kakanka fa ke nan, Kana nufin Obinna, anya ka yi bincike da kyau? Ta ya ma hakan zai yiwu?"
Girgiza kai CI yayi cike da takaici ya ce, "Sir am sorry to say da wani ne ya faɗamin maganar nan Allah sai ya ci na jaki, Hakan ba zai ta6a yiwuwa ba, ba gaskiya bane, Baba Obie bazai aikata munanan ayyukan nan ba, Owais ka bani mamaki, ban taba zaton zaka iya furta wannan maganar akan kakan ba, kafi mu sanin wanene shi, amma ko mu kanmu da muke abokanka mun yi imanin baba Obie bashi bane Elder, Mutumin mai kyawawan halaye da tausayi irinsa bazai iya aikata abun da Elders suke yi ba...
"Ni dai danasan zaka fada mana wannan almaran da ba abun da zaisa in halarci meeting ɗin nan, sai dai ka yi hakuri Chief amma yau ka 6ata min rai, ka ce Elder ne kakan ka, Wanda ya haifi baba, gaskiya sir kwakwalwarka bata aiki yadda ya dace kana bukatar a duba ka.." Coo ne ya fada tare da zame glass din kan fuskarsa ya zaro hanky yana sharce gumin dake tsastsafo masa.
Kasa juyowa ya yi ya fuskance su, baisan taya zai yi musu bayani ba, baba Obie ya cuci kansa ya yaudari mutanan da suka yarda da shi, gayanan duk wanda aka faɗamawa sai anyi da gaske kafin ya yarda..
Taj Tuni hawaye sun wanke fuskarsa, dama saida ranshi ya bashi hakan, wata irin karaya ya ji, baba Obie ya bashi mamaki, ba tun yanzu ba ya jima yana al'ajabin dukiyarsa da ɗaukakar ahlinsa ashe bana Allah da Annabi bane, haƙiƙa bai kyauta ma rayuwarsu ba, ya zalunce su wata shari'ar sai A lahira...
"Tun da nake daku na taba yi maku ƙarya? Mutumin nan kakana ne nafi ku sanin wanene shi! Miye ribana in na mashi kazafi? Tun da na ce maku shi ne ku yarda kawai, kakana ne Elder!"
Ya faɗa cikin shesshekar murya ba tare da ya juya ya fuskance su ba,
Wannan karon kusan suman tsaye suka yi saboda sun fara karaya da maganarsa jin kamar yana shesshekar kuka...
"Ba shaye shaye na yi ba, da hankalina da tunanina, Ni ba mahaukaci bane, ba kuma kazafi na yi masa ba, zan sake maimaita maku, Kakana Obinna shine Elder, azzalumin da ya ke azabtar da rayuwar yaran da ba su ji ba basu gani ba a gidan kurkukunsa, mutumin da muke nema ruwa a jallo, ashe daga tsatsonsa na fito, ban ga laifinku ba da kuka kasa yarda da maganata saboda muma lokacin da muka ji hauka ne kaɗai bamu yi ba, na yi fatan ace ban kai wannan lokacin a raye ba, gaba ɗaya mun yi danasanin kasantuwar mu jininsa, amma ba yadda zamu yi haka Allah ya ƙaddara mana, Allah yana fitar da rayyayye daga jikin matacce, Ga misali nan akan mu, Kakanmu gurbatacce ne, mai fuska biyu, mu kuma ba haka muke ba, gaba ɗaya uncles dina da mahaifina babu sa hannunsu a ciki, hasalima basu taba jin wani abu mai suna kurkukun kaddara ba, a ranar da asirin ya tonu, abun ya daure mun kaina, sai na ga kamar ban ma taba sanin shi ba saboda na ji abubuwa game da kakana wanda ni ko iyayenmu babu wanda ya taba sani..."
Jikin taƙaura fa ya yi la'asar, tuni annurin fuskokinsu ya ɗauke duff kamar basu taba dariya ba, zuciyarsu ta karaya, ga baƙin cikin da ya mamaye su, hankalinsu ya tashi, har basu san sa'adda suka cire hulunan kakin da ke akansu suka ɗaɗɗaura su gaban table ba, a ɗimauce suka koma kan kujerun suka zauna tare da sadda kansu ƙasa..
Har tsawon mintuna ashirin cuf babu wanda ya furta kalma daga cikin su saboda matsananciyar damuwar da suka shiga, kwata kwata meeting din yau bai yi musu dadi ba, saboda jin abun da basu taba zata ba, basu ji dadin maganganun da suka faɗa akan kakansa ba, wannan ne karo na biyu da suka ga raunin Chief, ranar da Danish ya faɗa rijiya da kuma yau, wlh sun tausaya masa sosai, sun ma ga kokarinsa da ya iya jurewa in wani ne tuni zuciyarsa zata buga ya mutu ko ya halaka kansa saboda baƙin ciki..💔
Miƙewa Commender ya yi ya nufe shi tare da ruƙo hannunsa ya juyo da shi, hankalinsu ya tashi da ganin siraran hawayen dake zarya kan kuncin sa.
_Zaunar da shi kan kujera Commender ya yi, tare da zaro Hanky ya share mashi ƙwallar shi, mikewa sauran suka yi gaba ɗaya suka kewaye sa duk da raunin da suka yi hakan bai hana su ƙarfafa zuciyarsu gurin lallashin shi da bashi baki akan ƙaddarar data same su, babu wanda bai tofa albarkacin bakinsa ba gurin kwantar masa da hankali, su ka ce ya yi hakuri ya jure radaɗin da ya ke ji, sun san abun da ciwo, dole zai shiga mawuyacin hali amma ya yi hakuri, kada ya ji komai su masu fahimtar shi ne, tabbas su kansu sun karaya sun kuma razana da jin cewa kakansa ne, amma ya zasu yi babu wanda ya isa ya canza abun da Allah ya riga ya kaddara faruwarsa, wlh saboda tausayin da ya basu da suna da halin da zasu cire mashi damuwar shi da ba abun da zai hana su yi hakan kodan su sauƙaƙa mashi radadin da yake ji, amma ba zasu bar shi ba, zasu kasance a tare da shi, No matter what, shi Chief dinsu ne na har abada, su sun yarda da shi fiye da yadda suka yarda da kansu, don haka kada ya ji komai, laifin kakansa ba zai taba shafarsa da ahlinsa ba, zasu tsaya masu tsayin daka don ganin basu tozarta a idon duniya ba, bashi kadai zai yi fadan ba, ya sani yana da su zasu taya shi yin fighting ɗin duk wani wanda yayi yunkurin cin zarafin ahlinsa ta hanyar amfani da abun da kakansa ya aikata! Bayan haka basu san rauninsa, yana ɗaga masu hankali, abun da suke so da shi ya yi ƙoƙarin cire damuwar da ke aransa, saboda zata iya haifar masa da rauni wanda kuma hakan faduwa ne a gare su, sun san Chief ɗinsu jarumin namiji ne, mai dakakkar zuciya, kuma mai tawakkali, basu so ya canza daga yadda ya ke a da, ya sawa ransa cewa zai iya, ya manta da cewa kakansa ne Elder, ta haka ne zai kore damuwarsa har su samu su ƙarasa aikin su."_
Maganganu masu daɗi da ƙarfafa gwiwa suka gaggaya masa har saida
ya ji karfi a jikin shi, sun faranta ranshi, kuma dama abun da ya kamata kenan idan mutun ya shiga wani hali a tausaya masa, a ja shi a jiki, bawai a dinga cuzguna masa ba saboda wata ƙaddara ta same shi, wasu har daɗi suke ji su dinga bullying ɗinka don su baƙanta maka rai, su ja depression ya kama mutun daga haka har ya lahanta kan shi, wa'iyazubilla..💔
Tun suna share mashi ƙwallar da ke gangarowa kan kuncinsa har ta kai ga sun fara tsokanar shi, baisan sa'adda ya fara sakin murmushi ba, saboda dadin da ya ji har godiya ya yi musu, su ka ce kada ya damu hakkinsu ne su bashi kulawa, yanzu tunda sun fahimci ba ya jin dadi yana bukatar ya ga likita saboda lafiyarsa, don haka zasu ɗaga meeting din, zuwa lokacin da zai ji sauƙi.
Ya ce masu bai ƙi shawarar su ba, amma bazai yiwu a ɗage meeting ba, akwai muhimman abubuwan da yakamata su tattauna akai idan ba haka ba zasu iya fuskantar matsala, hankalinsu ya tashi da jin hakan, suka ce tun da haka ne, zasu tafi hutun awa uku saboda sun damu da lafiyarsa suna so ya huta...
A cikin yan mintuna suka kira Isod docs suka bincika lafiyarsa anan cikin medical room ɗin su, bayan sun tabbatar da ciwon dake damunsa ya gargaɗe su akan kada su faɗa musu sakamakon saboda baya son kowa ya sani...
Lokacin da suka koma zaman meeting din, ba laifi sun ga ya ɗan saki jikinshi da walwala akan fuskarsa, A tsanake ya fayyace musu komai da ya faru bayan zuwan Khala..
Sun yi matukar mamakin jin cewa kakarsa ce, kuma Obie ne ya yi ƙaryar mutuwarta ya kai ta kurkukun kaddara, duk ba wannan ba, abun da ya basu haushi da takaici abun da Pravin ya aikata, ashe shima Elder ne na gidan kurkukun kaddara, lallai Obie Family sun haɗa giggan ƴan ta'adda acikin su.
Bayan sun taya shi murnar ganin grandma ɗinsa, da jimamin abun da ya faru da familyn sa Commender James ya ce,
"Yanzu ta ya za'ai mu iya gano sauran Elders? Kana ganin grandma ɗinka zata iya samun sauƙi nan kusa!" Girgiza kai ya yi, "Bakowa ta sani a cikin su ba, yanzu haka da ita da aunt ɗin nawa an kwantar da su asibiti basu san inda kansu yake ba, amma suna samun kulawar likita.."
"Me zai hana mu tuntubi shi Elde...Au, afwan sir grandpa nake so na ce,..." murmushi chief ya yi tare da kallon CI da ya yi maganar. "Duk yadda ma ka faɗa daidai ne CI, already na yi masa magana akan ya fada mun sauran Elders din amma ya ƙi sanar da ni...." Nan ya labarta musu abun da suka tattauna tsakaninshi da baba Obie.
Kallon kallo suka jefawa junan su cike da tashin hankali, Agent Jabeer Osman ya ce, "Akwai sauran rina a kaba kenan, In har bamu yi gaggawar kamasu ba zasu iya mayar da hannun agogo baya, nasan iwar haka suna nan suna shirin kawo mana farmaki."
Gaba ɗaya sunyi amanna da maganarsa, Agent Zahra ya ce, "Ni damuwana ina zasu farmaka? ya tambaya yana duban su,
"Hankalina ya fi karkata akan fursinonin da muka baro a Csh."
Taj ya ce,"Asibitin yana da tsaro tunda na sojoji ne, amma fa kada mu dogara da hakan, mun riga da mun san su wanene Evil Giants, in har suka farmake mu da su, toh Allah ne kaɗai zai iya ƙwatar mu, za su iya amfani da sihiri su kashe sojojin dake tsaron su, su kwashe yaran abunda ba a fata, amma menene mafita...?"
gaba ɗaya suka zurfafa tunaninsu kowa na tunanin abun da yakamata a yi.
"Kuskuren da muka yi tun farko shine barin makaman da grandma ta bamu, da mun sani mun taho da su, saboda da su kaɗai ne za'a iya yaƙar su.."
A cewar Captain..
Cike da takaici Canal ya daki gaban table dinsa yama rasa abun cewa..
Jackson ya ce,"Akwai gagarumar matsala, dole fa mu fara kai masu farmaki kafin su kawo mana idan ba haka ba, ba zasu yi mana da dadi ba, bamu san ina zasu farmaka ba!"
Lieutenant Thompson ya ce, "Ni dai a nawa ganin shawara ɗaya ce, Chief grandpa shine mafita, shi kaɗaine makamin da muke da shi a yanzu, tun da ya ce zai mika wuya toh ya taimaka ya faɗa mana komai idan ba haka ba, ba zamu iya cin galaba a kansu ba, a kowani lokaci zasu iya kawo mana farmakin bazata..."
Girgiza kai Chief Owais ya yi, "mu yi hakuri mu nemi wata mafitar, saboda ba irin magiyar da ban yi masa ba amma ya ƙi fada mun, ya ce a dokar aikinsu wani baya tona asirin wani, alkawari ne suka ɗaukarwa junansu, kuma shi ba zai ci amanarsu ba, tun da har ya fadi hakan bai duba ƙaunar da yake yi mini ba, toh wlh ba zai ta6a bamu hadin kai ba, koda zamu azabtar da shi ne, amma a maganarsa ya ce in har aka kawo mana farmaki mu sanar da shi, amma wannan ba mafita bane, tayaya za a yi mu san za'a kawo mana farmakin?"
Da damuwa ya jefa musu tambayar, gaba daya sun shiga tashin hankali..
"Ni a ganina mu fara nemo wadanda grandma ta fadi sunayen su? In ya so sai muci ubansu mu azabtar da su har sai sun faɗa mana su wanene sauran Elders din..." Taj ne ya fada yana huci zuciya ta kai wuya..!
General Noah ya ce, "No ba zamu iya kama su ba, har yanzu bamu da isassun hujjojin yin hakan!"
"Sir, muna da isassun hujjojin da zamu iya kama su..."
Gaba ɗaya suka maida hankali akan Taj da ya yi maganar har suna haɗa baki gurin tambayar wata hujja ce? Bai jira Chief ya bashi umarnin ya faɗa ba, ya fara zayyana musu komai da ya faru tun daga kan labarin Ummi har izuwa labarin da Benazir ta bashi akan Alhaji Musa.
Lamarin ya ɗaure musu kai, basu gama shan mamaki ba, sai da Chief ya samu ƙwarin giwar tunawa da wata hujjar da yake da ita, nan shima ya labarta musu komai da ya gano game da shi tun daga kan hotansa dake a cikin diary din Unaizah, ya ƙara da cewa, "Har yanzu bai rabu da Ummi ba, bayan ya rabata da kowa nata ya maidata karuwarsa, shine ya tafi da ita America..." A rude U.s armies suke jefawa junansu kallo mai cike da tsantsar al'jabi, Ummi dai da suka sani tantiriyar karuwa yau sun ji asalin labarinta da kuma azzulumin da ya yi silar canza rayuwarta, gaba ɗaya basu ji daɗin abun daya faru da ita ba, tausayinta ne tsantsa a kan fuskokinsu, ba su kaɗai ba hatta General Noah dana hannun daman Chief sun nuna tausayawar su a gare ta, labarinta ya taba zukatansu, kuma basu taba ganin mugun mutun irin Musa ba, labarin yarinyar da ya sa su zubda ƙwalla ashe shine Ubanta, sun ma riga da sun yanke ma kansu shine JAN WUYA mutumin da suke nema ruwa a jallo..
Chief Owais bai dakata ba, ya ɗaura da basu labarin da Sheikh Imam ya ba shi ...
Taj ya ce, "dama sai da raina ya bani, sune suka kashe Uzair..." Ya faɗa cikin ƙunci da baƙin ciki.
General Noah ya ce, "Wai ni Musan nan bashi bane former president ba? Mahaifin Ddg? Kuma ƙanwarsa tana auran daddynka ko?" Jinjina mashi kai Taj ya yi.
Cikin fushi Noah ya buga saman table rai a 6ace ya ce, "Babu tantama zai aika, Ni dama bai ta6a burgeni ba, mutun sai girman kai da izza ashe dukiyar tasa ta kungiyar asiri ce, shi dama karen yan siyasar nan na daɗe ina zargin sa saboda mugun munafuki ne.."
CI ya ce, "Zai yi wuya in ba daga tsatson fir'auna ya fito ba, mutun ba imani ba tausayi! Zalunci da mugunta kaɗai yasa gaba, aikuwa dubunsa ta cika, daƙiƙin kwata kwata baya amfani da kwakwalwarsa, gashi nan cikin rashin sani ya tabka kuskuren da ya yi silar tonuwar asirin sa..."
Coo ya ce, "Wlh ikon Allah ne, ka duba yadda ya daɗe yana sheƙe ayarsa tsawon lokaci batare da an iya kamasa ba, wai a haka har matsayin president ya taka, ko da yake ya samu ɗaurin gindi ne..." Bai ƙare maganar ba, Taj ya yi masa gyaran murya tare da furta "Hattara dai.." Cike da jin kunyar Chief CI ya sunnar da kansa, bawan Allah Chief ɗan murmushi ya saki tare da ɗan girgiza kan kanshi.
"Sir, Yanzu meye abun yi tunda muna da isassun hujjojin da zamu iya kama su? Taj ne ya faɗa yana dubansu..
Commender James ya ce, "Babu bukatar 6ata lokaci, mu kama su kawai su fara kar6ar sakamakon zunubin da suka aikata..."
General Noah ya ce, "da shi ɗan iyan, da Musan, da pravin da aminnan grandpa, da likitocin da momma ta faɗa suna da sanya hannu suma a kama su, sannan kada a kuskura abar pravin ya ƙetare kasar nan, nasan iwarhaka yana neman hanyar da zai gudu, watakil ma ya gudun, shiyasa banso kuka ɗauki lokaci baku sanar damu ba, wlh da kun faɗa mana tun ranar da abun ya faru zamu bi diddiginsa mu kama ɗan iskan, amma na yi maka uziri nasan alhinine ya hana ka sanar mana..."
Chief ya ce, "Mun tattauna da Uncles dina, suma zasu bada gudummuwarsu..." Nan ya labarta masu abunda suka tattauna da Uncles ɗinsu, sunji dadi kuma sun ƙara jin kwarin gwiwa a tare da su..
"Bayan haka tun ranar da ya gudu nake ta trying layinsa a kashe yake, har jaraba bin diddiginsa na yi amma ban iya gano komai ba, ina tunanin ya jefar da wayar ne don kada mu bi diddiginsa."
Agent Zahra ya ce, "Zai iya yiwuwa ya canza layi, in kuwa yayi kuskuren zuwa yin register zamu iya samun bayanansa."
"Ita yar'uwar tashi ka kira layinta ne?" James ne ya tambaya..
"A ɗaki tabar wayar, na kar6i number dinta a hannun yan uwanta maids, dana kira sai na gano location din wayar a cikin gidan ya ke, da kaina na shiga na dudduba dakin har na gano wayar nata."
Taj ya ce, "Za mu iya haɗa baki da abokan aikin nata, ita Hajjatyn zata iya yin kuskuren kiran wani daga cikin su tun da ta yarda da su atare suke aiki, ko basu ba mu nemi aminiyarta ta ƙut da ƙut, wadda muke da tabbacin zata iya kiran ta, sannan mu haɗa baki da ita, da zarar ta kira ta tayi hanzarin sanar damu, mu kuma sai muyi kokarin bin diddigin su..." Shawarar da Taj ya kawo ta yi masu daɗi..
Ya kuma cewa, "Amma ni abun da ya ɗaure mun kai, Ita hajjatyn tasan abun da ya aikata kuma ta bi shi suka gudu? Ko dai dama a tare suke aikata 6arna ta bayan fage..."
Amma da kamar wuya saboda Hajjaty mutuniyar kirki ce .." Wani marayan kallo Chief ya yi masa..
"Mugu bashi da kama Taj, abun da ya faru da ni ya isa yasa ka dauki darasi, ba kowani nagari bane mutumin kirki, akwai masu fuska biyu, a fili Musa a zuci fir'auna, ni bana zargin ta, amma ta aikata babban kuskure da ta haura ƙafa ta bi shi suka gudu, in har muka gano da sa hannunta akan abun da ya faru da auntyna, kuma tasan abunda yake aikatawa wlh na lahira sai ya fi ta jin daɗi, dole mu hukuntata daidai da abun da ta aikata, babu wanda zamu ragamawa kamar yadda bazan raga ma kakana ba, dole kowan nan su ya gir6i abun da ya shuka..."
Ya faɗa tare da bugun kan table din gaban su, gaba daya idanunsu akan fuskarsa, maganarsa ta burge su, suna alfahari da shi, ya cancanci su yaba mashi saboda jajircewar shi akan gaskiya, a dai yadda duniyar nan ta baci da rashin son gaskiya, da wani mai son kan ne idan yasan nashi ne yake aikatawa 6oyewa zai yi, ko ya bashi hadin kai ya gudu don kada a kama sa, ko kada su kunyata a idon duniya, gaskiya samun mutun mai irin zuciyar chief zai yi wuya a fadin duniyar nan, he's a true leader, ba karamun mai tsoron Allah bane zai yi hakan💘💋...
Almost one hour suna tattauna yadda zasu kama Elders, kowa yana kawo idea dinsa, a karshe suka yanke shawarar zasu tuntubi Ummi saboda ta hanyar ta ne suke sa ran za su damƙi Musa ta cikin sauƙi. Chief ya ce su bar komai a hannunshi ya riga da ya yi mata magana amincewarta ya ke jira, zai ƙara yin magana da ita duk yadda su kai zai sanar da su..🔥
*PRAVIN❗*
Aje Motarsa yayi a haraban wani gida, fitowa yayi jikinsa sanye da suit ya rufe fuskarsa da mask, hatta hannayensa da ƙafafunsa ya saka musu safa, sai yan waige waige ya ke yi daga gani yana a cikin fargaba, zagayawa yayi ta baya ya buɗe boot din motar, ya janyo ƙaton buhun dake a ciki ya aje ƙasa, kafin ya bude backseat ya sungumo baƙar jakarsa ya rataya ta kan kafaɗarsa, da sauri ya ja buhun ya shige da shi ciki, kulle door din ya yi da code kafin ya nufi Ciki.
Shigarshi falo keda wuya ya soma jiyo kakarin aman da ta ke yi, hankalinsa a tashe ya zame jakar ya jefar kan sofa ya saki buhun cikin sauri ya nufi bedrom din da take.
Yana shiga ciki bai same ta a saman gadon ba, sai dai bargonta dake a yashe ƙasa, cike da fargaba ya bangaje kofar toilet ya shiga yana haki saboda gudun da ya yi, lokacin idanunsa suka sauka akan ta yayin da take a gaban sink tana kwarara amai tamkar yan hanjin cikinta zasu zazzago, ta daddafe bakin sink din da hannayen ta.
Ƙarasawa ya yi da sauri ya dafe kafadarta yana yi mata sannu. Bata ko kula shi ba sai da ta gama amayar da komai da ta ci, ta kunna faucet ruwa ya wanke aman.
Kokarin daukarta ya yi don ya sauwaƙe mata tafiyar, cikin bacin rai ta bangaje shi ya yi taga taga zai faɗi yai saurin tsayar da kansa yana kallon ta.
Tsantsar bacin rai ne akan fuskarta, idanunta sun kumbura sun kaɗa jawur saboda kukan da take sha, gown din dake a jikin ta tayi squeezing kamar an ƙwatoto daga bakin kura, doguwar sumar kanta ta cukuikuye kamar ta mahaukaciya, mace mai tsafta ta zama ƙazamar karfi da yaji saboda rashin lafiya da damuwa..
A hankali zafafan hawaye suka soma zarya kan kuncin ta, labbanta sun bushe ƙamas sun ɗan faffashe ga jikin nata har yanzu ba sauƙi..
Cike da bacin rai ta furta, "Karka kuskura ka ƙara matsowa kusa da ni, i don't want to see you Pravin, ka nisanta kanka dani, idan ba haka ba zan yi ma kaina illa!" Bai ta6a ganin Hajjaty a cikin fushi irin na yau ba..
A hankali ya sanya hannu ya cire mask din dake akan fuskarsa, cikin yan kwanakin nan saboda zullumi da fargaba har rama ya yi, tun ranar da ya gudo da Hajjaty, bai nufi ko'ina ba sai guest house dinsa da ya daɗe da mallakarsa, babu wanda yasan yana da gidan.
"Ba halin ki bane, bansan ki da fushi ba, na rasa gane kanki cikin kwanakin nan, duk abun da kika ga ina yi saboda in kare ki ne, amma kin kasa fahimta na.."
Harara ta watsa mashi, cikin bacin rai ta ce, "Idan ba halina bane to kai ne ka sauyani Pravin, ni bazan cigaba da yarda da munafuki ba, na gaji da sauraran ƙarairayin ka! ka faɗa min gaskiyar abun da ya faru, ka raba ni da mutanan da nake rayuwa da su ka kawo ni wani gida ka boye ni a cikin sa! Kullum na tambaye ka sai ka yi shiru, wai me ka ɗauke ni ne? Don ina da hakuri ba hakan yana nufin bani da hankali ba! Zan iya jure komai amma wallahi bazan jure rainin wayon ka ba...."
Tuni ya sha jinin jikinshi jin yadda Hajjaty ke masa faɗa kamar uwarsa, tana magana tana ciccije le6enta saboda radadin da take ji..
"Tayaya kake tunanin zan cigaba da zama da kai? Bayan baka ɗauki iyalinka da muhimmanci ba sai ni Pravin? Wani laifi ka aikata ne da yasa har ka gudo da ni? A ranar kafin in fita hayyacina na ji muryar Hajiya Saratu a cikin kunnena, ta shigo daki na, duk da ban ji abun da ku ka tattauna ba amma raina ya bani ta gano abun da muke yi shiyasa har ta shigo ɗakina, kuma na ji lokacin da ta bangaje mu muka faɗi daga nan ban ƙara sanin inda kaina yake ba..."
Dakatawa ta dan yi tana jan numfashi idanunta a cikin na shi, ya yi zuru zuru ya rasa ta ya zai shawo kanta, kwanakin nan basu jituwa saboda yaƙi faɗa mata laifin da ya aikata, ta ƙi kwantar da hankalinta balle har ta ji sauƙin abun da ke damunta..
Girgiza kai ta yi idanunta suka cicciko da ƙwalla...
"Ka kasa kare kanka saboda baka da gaskiya shiyasa ka yi shiru ko? Ni ina ji araina wani laifi ka aikata musu shiyasa ka gudu da ni, saboda hujjar daka bani bata gamsar da ni ba.."
Sunnar da kanshi kasa ya yi, jikin shi ya yi sanyi lakwas, baisan ya zai yi ba, ya jefa rayuwarsu a cikin bala'e da masifa, ya yi danasani tafi sau a ƙirga, yana matukar jin kunyar Hajjaty, yana jin nauyin tasan miyagun laifukan da ya aikata wa'iyazubillah!!
Bata ƙara yin magana ba, ta juya ta nufi kofar fita da sauri ya bi bayanta, shigowa cikin dakin ta yi, jikinta na kerma ta nufi bedside drawer ta soma kwashe magungunanta tana jefa su cikin dustbin din dakin, shigowa ya yi da sauri ya damƙi hannayenta, kokoyi suka kama yi..
"Pls ki saurare ni, zanyi maki bayani, ki daina zubar da maganinki, da tsada na siye su saboda lafiyarki..."
Wani kallo ta wurga masa, "Ban damu ba Pravin, bana son lafiyar tawa, nafi son na mutu, saboda wanda na yarda da shi yana neman ya karya min zuciyata..."
Bai san sa'adda hawaye suka wanke fuskar shi ba, duk yadda ya so ya dakatar da ita abun ya ci tura, ƙarfi yasa gurin ɗaukarta ɗungurugum ya kwantar da ita kan gadon, ta dinga kuka tana bubbuga mattress da hannayenta, bin ta ya yi saman gadon ya janyota jikinshi tana turjewa, ya rungume ta kan ƙirjin shi, duk yadda ta kai ga jin haushin shi da ya yi mata hakan sai da ta ji sassaucin damuwarta.
Cikin sanyin murya ta ce, "Pravin dan Allah ka fadamin meyasa ka gudu da ni? Meyasa ka bar Obie estate? Wani laifi ka aikata? Kada ka yi min karya Pravin, babu sirri atsakanin mu, kasan bani da kowa in ba kai ba, kaine majinginata, ƙashin bayana, bana so ka ci amanar yardar da na yi maka Pravin, dan Allah ka faɗamin na yi maka alkawarin zan rufa maka asiri kuma zan taya ka neman mafita.."
wani irin tsantsar sonta da tausayinta ne ya mamaye zuciyar shi, tsoma yatsun hannayensa ya yi a cikin sumar ta yadinga cakuɗa gashinta kamar yana mata susa,
Cikin sanyin murya ya ce, "Ki yi hakuri na boye maki ne saboda bana so na ɗaga maki hankali, amma gaskiyar abun da ya faru, Hajiya Saratu ta gano ina zuwa dakin ki, harma in kwana, bayan mun dawo an fara shirye shiryen family meeting, sai na shiga ɗakinta don in canza kayan dake a jikina, ina kokarin cire riga na jiyo muryarta a cikin toilet tana yin waya ƙasa ƙasa kamar bata so aji, saina lallaba na je bakin ƙofar dakin na yi mata la6e
a nan na ji tana faɗin wallahi bazata sa6u ba, dama ta jima tana zargin kin asirce mata miji saboda yadda kike gayu, wallahi ba zata ƙyale ki ba, sai ta kashe ki da poison..."
Zare ido Hajjaty ta yi,
Pravin ya sha mur ya ci gaba da zabga mata ƙarya, "Da na ji haka gabana na faduwa na fara tunanin me yakamata in yi saboda nasan mugun halinta na kishi wlh tsaf zata kashe ki, ni banma san wani munafukin bane ya kulla maki makirci, na so inji da wa ta ke yin wayar, ina jin alamun ta gama yin wayar na ma fasa canza kayan, jiki na na kerma na baro dakin nata, na nufo ɗakin ki don in faɗa maki abunda ke faruwa, shigowata keda wuya ina kokarin in tashe ki na ganki a kudundune cikin bargo, kwatsam na jiyo muryar hajiya Saratu daga waje tana tambayar maids ina ne ɗakin ki? da sauri na la6e bayan labule ina jira inga me za ta yi maki, tana shigowa ɗakin ta nufi gadonki hannunta ruƙe da poison..."
Dafe kirji Hajjaty ta yi jikinta ya hau 6ari, daɗi ya ji acikin ranshi ganin ta fara yarda da maganarshi..
"Ji nayi bazan iya bari ta cutar dake ba saboda nasan ba imani gare ta ba, saboda tashin hankali banma san lokacin dana yi wuff na fito daga bayan labulen ba tana jin motsi na ta juyo mu ka yi ido biyu, ta ware baki zata fasa ƙara na shaƙeta tana ta sambatu tana faɗin maciya amana, zarginta ya tabbata akanmu, wlh saita kashe mu, da na ga ta turje ta ƙi saurarena kawai saina sumar da ita, na sungumeki na bar estate ɗin da ke, don nasan muddin ta farka kwanan mu ya ƙare..."
Cike da damuwa Hajjaty ta ce, "Banji dadi ba, amma koma wanene ya ƙulla mana makirci Allah ya isa tsakanin mu da shi, mutane basu tsaron Allah. Amma hajiya Saratu bai kamata tana daukar zigar wani ba, ko da ya ke dama ta tsaneni, tasha faɗamin saita raba ni da gidan ubanta, amma bansan tsanar da ta yi mini ta kai har haka ba, kuma dama kwanaki ko hanya bata son haɗawa da ni, abinci ma indai ni na dafa bata cin shi.."
Pravin ya ce, "Hmmm, ɗan adam fa ba abun yarda bane, indai ka biyewa mutane zasu kaika su baro ka, kuma dama bata sonki ta sha saka ki kuka, ta ƙuntata maki saboda tana jin haushin zaman da kike yi agidansu, ni kaina da nake mijinta bata ƙyaleni ba, kullum saita goranta mini saboda ina zaune gidan ubanta. Saratu bata da wayau, sakarya ce, kwata kwata bata da halin kirki, zaman hakuri kawai nake yi da ita, amma ni kaina ba sona ta ke yi ba, wahalar da ni ta ke yi, taita juyani son ranta." Yana magana yana yamutsa fuska,
"Amma pravin meya kamata mu yi yanzu? Ni ina ga kawai mu je mu basu haƙuri mu faɗa masu gaskiya, In ba haka ba za su mana kallon mutanan banza kuma maciya amana.."
Waro idanunsa ya yi, "Ke! Kina hauka? Tab lallai, ay wlh muddin muka koma estate din nan sai sun hukunta mu, sai ka ce kin manta irin yadda baba Obie da yayyanta suke ji da ita?
"Pravin, koma me zai faru mu ne masu laifi, mutanan nan sun yi mana hallaci, sun yarda da mu, tsawon shekara da shekaru muna rayuwa acikin su basu ta6a gudun mu ba, amma mu muka ƙi fada masu alaƙar dake atsakaninmu, bamu kyauta ba, kuma nasan zasu fahimce mu in har mu ka je muka basu haƙuri muka kuma faɗa masu akwai aure a tsakanin mu za su yafe mana, koda hajiya Saratun bata yarda ba nasan za su yi ƙoƙarin sasanta mu da ita, tun da su din mutanan kirki ne suna da hankali da kuma tausayi...."
Bata ƙare maganar ba ya tari numfashinta da cewa, "Hmmm, na lura har yanzu baki san halin hajiya Saratu ba, nasan mutanan kirki ne amma wlh akan Saratu zasu iya komai, kin manta labarin dana baki lokacin da ta zo da ni don inga danginta? Ƙiri ƙiri suka nuna basu sona sun tsaneni saboda ni ba jinsin su bane, kuma bani da asali da arziki irin nasu, a lokacin ba don baba Obie ya goya mini baya ba ai da basu bani auranta ba..."
Dafe kai ta yi da hannu ɗaya, "Me zai hana mu tuntu6i baban toh? nasan zai taimaka."
"Har yanzu kin ƙi fahimtata, nifa bazan ci gaba da zama ƙasar nan ba, saboda hajiya Saratu ba zata raga mana ba, ƙwara mu tattara yanamu yanamu mu tafi, don yanzu haka nemanmu suke yi ruwa ajallo don su hukunta mu.."
Maganarsa ta ɗaga hankalinta, da damuwa ta ce, "Pravin meya kawo maganar barin ƙasa? Ka san me kake faɗa kuwa? Ina zaka kai ƴa'ƴan naka da matarka? kaima kasan wannan bamai yiwu bane, kawai saboda asirinmu ya tonu sai mu gudu kamar waɗanda suka aikata wani mugun laifi...?"
dafe kanshi yayi da hannu ɗaya baisan tayaya zai shawo kanta ba..
"Pravin ka daina wannan maganar, ba zan ta6a baka shawarar ka tafi ka bar iyalinka ba, bamu aikata laifin daya kai har mu gudu ba, kawai kuskuren mu shine ƙarya da muka yi masu tun farko muka boye masu gaskiya, in har muka nemi yafiyarsu bayan mun faɗa musu komai wlh zasu yafe mana Pravin, mun shaƙu da mutanan nan, mun saba da zama cikinsu, sun zama kamar danginmu da muka rasa! Sun ɗauki nauyin komai namu Pravin, wlh idan muka gudu baza su ji dadi ba, zasu ga kamar dama da wata manufa muke atare da su shiyasa bayan mun samu abun da muke so muka tafi, kai baka tunanin halin da ƴa'ƴanka da matarka za su shiga? Wai kuwa Pravin anya kana jin kanka amatsayin ubansu..."
bata ƙare magabar ba ya toshe mata bakinta da yatsan shi..
Ta rasa meyasa take ji aranta kamar pravin ba gaskiya ya fada mata ba! Saboda yanayinsa da kuma maganganunsa abun tuhuma ne! Kawai saboda ƙaramin laifin da bai kai ya kawo ba sai ya gudu ya bar iyalinsa?
Ganin kamar ta fara ɗago shi ya sa shi saurin daidaita nutsuwarshi cikin sanyin murya ya ce, "Na gane kuskurena, kawai bana so ta cutar dake ne shiyasa na yi wannan maganar, amma ba har cikin raina ba, ni ba zan iya tafiya na bar iyalina ba, banma san na fada ba, ki yi haƙuri idan na 6ata maki rai.." Ajiyar zuciya ta sauke, "Yanzu da yaushe zamu je estate din mu nemi yafiyarsu?"
"Me zai hana mu bari sai an kwana biyu, lokacin da suka yi kewarmu, koma suka neme mu da kansu don su ji ba'asi sai mu je mu faɗa masu gaskiya,..."
ta aminta da maganarsa saboda a halin yanzu tasan jiran su suke yi.
"Na yarda, amma tayaya zasu neme mu? Bayan babu waya gaba ɗaya mun barsu agidan.."
Yamutsa fuska ya yi, "Kash, sam na manta, amma akwai waya da na siya, nama yi mana hada siyayyar kayan abinci, da duk wani abu da zamu bukata.."
"Pravin basu da layin da zasu tuntubemu a yanzu."
"Karki damu, ki bari da kaina zan je estate din, in faɗa masu komai in sun hakura suka yafe mana zan sanar da ke komai." Ta ce, "Toh Pravin, yaushe zaka je ne?" A takure ya yamutsa fuska, kwata kwata bai son tana yi masa maganar Obie estate, da tasan masifar da suke a ciki da bata ƙara marmarin ambaton ko da sunan estate din ba.
"Ƙarshen satin nan." Ajiyar zuciya ta sauke, "Toh Allah ya kai mu, amma dan Allah ka kwantar da hankalinka, bana so in gan ka a cikin damuwa, addu'a yakamata mu yi Allah ya sa abun ya zo da sauki su yafe mana." Jinjina mata kai ya yi batare da ya furta kalma ba. Ta yi tunanin hajiya Saratu ce damuwar shi batasan mugun abun da ya aikata ba.
Ruƙo hannunta ya yi, "Mu je in taimaka maki ki yi wanka, yau kwana huɗu jikinki baiga ruwa ba." Bata musa mashi ba ya ɗauke ta kamar jinjira ya nufi toilet da ita, after mins ya futo dauke da ita, ta yi ɗaurin ƙirji da towel, ya kwantar da ita kan gadon shi.
Juyawa ya yi ya nufi closet tabi bayanshi da kallo tana mai ƙara jin kaunarsa saboda kulawar da ya ke bata.
Dawowa ya yi hannunsa ruke da riga da wando na shan iska, tun ranar da ya kawota nan ya siya masu kaya kala uku uku..
"Za ki iya sakawa ko in taimaka maki?"
Murmushi ta sakar mashi, "Bana so kana wahala, na lura hada damuwar ciwona ke damunka, kada ka damu zan ji sauki in sha Allah..." Murmushin yaƙe ya yi mata..
Bayan ta kar6i kayan ya fuce daga ɗakin, shiru bai dawo ba, saukowa ta yi daga kan gadon, bayan ta kammala zura kayan a jikin ta, ta je gaban mirror tana kallon kanta.
Zuciyarta cike fal da kewar Ahlin Obie, ita dai ta kamu da ƙaunarsu tun farko, kuma ba ta jin zata iya rabuwa da su ko da hajiya Saratu zata hukunta su ne, ta ji zata zuƙunna kan gwiwowinta ta roƙeta akan tayi hakuri ta yafe su.
Bakomai tafi ji ba face halin da ƴa'ƴansu za su shiga idan suka rabu.
Can kuma ta canza akalar tunanin nata, ta fi jin kewar aminiyarta akan komai, ta so ace akwai waya a hannunta da ba abun da zai hana ta kira Turai ta faɗa mata halin da suke a ciki tasan zata fahimce su kuma zata taimaka masu..
Body oil ta shafa ma skin dinta ta dauko comb ta sharce gashin kanta dakyar dakyar saboda yawanshi ga tauri da ya yi ga kuma jikinta ba ƙwari..
Jin shiru pravin bai leƙo ba ya sa tayi tunanin ko ya fita daga gidan ne.
Hakan ya sa ta miƙe daga gaban madubin ta fito ta shiga falo, ɗan madaidaici ne ya haɗu sosai, Pravin ya daɗe yana kokarin jan hankalinta da ta dawo gidansa da zama ta ƙiya saboda bata son rabuwa da obie estate...
Idanunta ne suka hango mata bag ɗinsa da ya ajiye kan sofa, sakamakon jefar da ita da ya yi lokacin da ya shigo har ta buɗe abubuwan dake a ciki sun zubo waje..
Buhun ta nufa ta soma buɗe shi, ba komai ne a ciki ba face kayan abinci, komai da zasu buƙata ya siya masu, murmushi ta yi tare da miƙewa har zata juya idanunta suka sauka akan passports dake ajiye kan hannun kujera.
Zuwa ta yi gaban kujerar, ta kai hannu ta curo Passport din da ta gani, shiru ta yi jim tana duddubasu aranta ta ayyana me Pravin zai yi da passports dinsu?
Bata kawo komai ba a ranta ta mayar da su cikin jakar ta yi zipping dinta, ƙamshin suya ta fara juyowa a cikin hancinta, murmushi ne ya bayyana akan fuskarta jin motsin shi
Direction din da take jiyo motsin ta nufa, dadi kamar zai kashe ta ganin pravin yana girka mata abinci, daga shi sai short a jikin shi, ya haɗa gumi sai aikin motsa suya yake yi...
Kamshin naman ne ya daki hancin ta, cikin sanda ta shiga ciki ba tare da sanin shi ba saboda ya bata baya.
Hugging dinsa tayi ta baya, wata firgita da ya yi saida ta yi noticing wani abu,
"Waw.. waye...! " Ya faɗa tare da ɗaga ƙaton spoon din hannunsa da niyyar ya kwaɗe wanda ya ruke sa..
Ajiyar zuciya ya sauke ganin Hajjaty ce,
"meyasa baki yi min sallama ba?"
"Saboda in baka tsoro." Ta faɗa da murmushi..
"Hmm, zan rama ne Allah."
"Ki koma daki pls, har yanzu babu ƙoshin lafiya atare dake, idan na gama zan kawo maki a daki."
Maƙe mashi kafaɗa ta yi, "Kaima kasan bazan bari kana yin aikin da ya kamata ace ni zanyi ba, in har ba zaka bari in taya ka ba, to ka bani in ƙarasa tun da jikin nawa da sauki."
Dakyar ya lallabata har ya samu ta koma falon ta zauna.
Bada jimawa ba ya fito hannunshi ruke da tray, daga saman shi plates ne na chicken pepper soup, da na shinkafa, ga juice a glasses.." Tunkan ya karasa ta fara haɗiyar yawu..
A saman rug ya a je tray ɗin ta sauko ta zauna shima ya zauna suka tasa tray din a tsakiyar su..
A tare suke ciyar da juna, idan ta bashi a baki shima sai ya bata...
Suna ci suna fira, duk ta ishe shi da santi..
"Da ka yi mini girkin nan har ka tuna min lokacin da muke a gida, kafin mu yi aure, ni dai na yi dacen ɗan uwa kuma yayana sannan mijina, tun ina ƙaramata kake kula da ni baka ta6a gajiyawa ba, ci na, suturata, da duk wata ɗawainiyana kaine, baka ta6a bari na da yunwa ba, koda kai zaka rasa toh zaka nema min ni in ci..." Idanunta cike tab da ƙwalla ta yi maganar.
Jikinsa ya yi sanyi lakwas.
_"Dan Allah Pravin no matter what, kada ka canza daga yadda na sanka, ka ji tsoron Allah ka kuma kiyaye sa6a masa, da ka zalunci wani ƙwara kai azalunce ka saboda Allah baya yafe hakkin dake a tsakanin bawa da bawa, ka kau da ido ga abun da ba halal dinka ba, ka yi haƙuri da abun da Allah ya baka. Duk abun da ka samu shine rabonka, ita duniyar nan ba matabbata bace, wata rana zamu mutu mu barta ne, lahira ita ce matabbata kuma dawwamammiya, mu ruƙa tuna mutuwa da kwanciyar ƙabari, daga kai sai halinka za a binne ka, komai da muka tara anan zamu bar shi, kowa zai girbi abun da ya shuka, walau na alkhairi ko na sharri...."_
Tun da ta fara yi masa nasihar jikinsa ya soma 6ari, zuciyarsa ta ƙuntata sosai. Bai ƙarasa sauraronta ba ya miƙe kamar zararre ya nufi daki, yana shiga ya faɗa kan gadonsa ta rubda ciki ya kwanta..
Da gudu ta bi bayan shi, ta hau kan gadon tana tambayar shi me ya faru? Meke damun shi? Ko nasihar da ta yi masa ne bata yi mashi dadi ba...
Cikin karyayyar murya ya ce baya jin daɗin zuciyar shi bacci yake so ya yi, saukkowa ta yi daga kan gadon taje gaban mirror ta dauko tissue box, yago tissue din ta yi, ta koma kan gadon ta soma goge masa hannayensa da bai wanke ba, bayan ta gama ta daura box din saman drawer..
Rungume kanshi a ƙirjinta ta yi, tana jin yadda zuciyarsa ke harbawa fat fat kamar zata tsaga ƙirjinshi. Ta ruɗe da ganin yadda ya razana daga kawai ta yi masa nasiha, sai dai bata kawo komai aranta ba, a haka bacci ya yi awon gaba da su.
Luxury-incense By Sapnah Borno.
Ta kawo muku turarukan wutan su Na maiduguri dana chad, turarukanta masu masifar dadi da kama waje harma da daukar hankali, indai kikayi kabbasa da turaren ta har wajen da kika zauna indai kika tashi sai kin bar kamshin ki, sannan Tana saida mayukan gashi irin nasu na shuwa Arab masu tasirin gaske, wajen gyaran Amare kuwa babu magana dan tazo muku da Chadian and Sudanese dilka Wanda zaki gyara jikinki da kanki, oga ya kasa ganeki, haka zalika akwai wata humrar ta mai suna hana bacci da kuma sirrin shuwa Abun ba magana, yar uwata ki jarraba turaren yar mutan borno nasan zata zame miki best turaren wuta plug. Tanada turarukan da zaki turara gida, toilet, bedsheets, curtains, kabbasa and hair incense ku jarraba kada ku bari ayi babu ku.
Wardrobe balls
Kabbasa spray
Chadian khumra
Hawee
Halud
Gabgab
Sandal sukkariya
Kajinguru
Dilka soap
Ready to use dilka
Karkar oil
Turaren tsuguno
Habil
Dorut
Dorot after period
Brown khumra
Dufr khumra
Body milk
Sudanese kuleccam
Chadian dufr kuleccam
Musk khumrah.
Maganin matan mu sunada inganci Wanda muke kawo su daga sudan, sannan munada maganin karin girman nono, Wanda basuda effects, ga masu bukatar maganin Matsi ko maganin mata Masu aiki garanti munada su, sannan muna zuwa gyaran jikin amarya a duk garin da take
Our Chadian aphrodisiacs are.
Beejay fire
Sata jagab honey
Wetness and sweetness combo
Daka
Great A sabaya
Breast engagement powder
Ciccibi
Gumbar madara
Gumbar dabino
Bita Zaizai
08093772168
*Welcome, Littafin kurkukun ƙaddara 500 ne, dukanshi Book One two and 3 Idan kin shirya biya ga Details da zaki tura*
3196407426
First bank
Bature Hafsat Muhammad,
*bayan kin tura zaki bada transaction reciept ko screenshot na debit alert a matsayin shaida ta wannan number din 08103884440*