Kurkukun Ƙaddara Takun Ƙarshe Page 76 Complete

Kurkukun Ƙaddara Takun Ƙarshe Page 76 Complete

Takun Ƙarshe

Aslm barkanmu da wannan lokaci 

Ina Mai farin cikin sanar daku cewa Zuzeam ventures takawo maku ingantattun magunguna masu inganci cikin Aminci Muna da kaya kamar haka

 Mallaka Maganin sanyi

Maganin cire tumbiMaganin farin jini

Maganin matsiMaganin mata

Maganin sa ni’ima da dandano

Dulka Amare Set na gyran jiki

Set na amarya

Tabaje tsumin Gomba

 Xuma kiba ta hips and Brest

Magungunan gyran Brest

Magungunan Karin hips

Maganin sliming

 Muna da kaya masu inganci  cikin sauki da rahusa 

Ina wadda keneman mallaka sahihiya quaranty wlh hajiya kixo ga zuzeam ventures xakiji ddin mallaka duk fadin ran ogah duk fadansa wlh sai yyi sanyi 08144015291

Idan maganin mata kikeso akwai 

Idan gyran jiki kikeso gyran fata gyran Brest magungunan sa kiba da hips 

DOMIN samunta Kai tsaye kira wannan no 08144015291 DOMIN mgn da ita whatapp 08144015291muna tura kayanmu ko ina cikin iKon allah 🥰👌🏻

Bononza Bononza Tsimin kaninfari 1k Tsimin dabino 1k Gumba 700 Gumba aya da nonon rakumi 700 Garin kafi ciccibi 500

Garin bata gaban kishiya 500

Matsin mallaka tada zaune tsaye 2500

Turaren mallaka ba aba mai kishiya 2500 Total kayan 9500

Za a bakisu akan 4k

Kuma mutun goman farko nadakyautar Abun 2k

🗣️🗣️🗣️🗣️🗣️🗣️ ASSALAMU ALAIKUM ALHAMDULILLAH YAN UWA  NEW PROMO YA KAMMALA💃🏽💃🏽💃🏽😁😁😁 da 5k dinki ki kwashi kayan 12k hajiyata 💃🏽💃🏽💃🏽😃🙃Kazar gadali ta mallara Rabi 3500 Tsimin gam gam 1500 Ruwan kara zunzurutun dadı😋800 Garin 7in1 1k Gumba 3 balai 500 Gumba kwakwa da dabino 500 maganin Infection 1k Garin zunzurutun dadi 1200 Matsin ba a fira d wando 500 Matsin infection mai matse mace gam 500 12k All at 5k https://wa.link/l1gcz8 kedai dannan link dinnan don samun naki ki maza kiyi bucking koda kudinki saida Rabonki.



.~________________________________🌹☠️💗🔥~






A bangaren Ummi ta riga ta gama yanke shawarar zata basu haɗin kai, kamar yadda ta kudirta aranta saboda ta wanke big boss daga tuhumar da su ke yi ma shi ba dan ta yarda da tuhumar da suke yi ma shi ba.



 bayan da ta taje ma Owais da maganar, yayi farin ciki sosai, ta kuma fada masa game da zuwan da zatayi gurin Alhaji musa, Hakan yayi masa dadi sosai, cos wannan dama ce babba agurin su, yace mata idan weekend din yazo zai faɗa mata plan din su, sannan Yace yana son ganin kawarta Natasha, in zai yiwu ta kirata awaya ta fada mata tana son ganin ta cikin week din nan, babu musu ta amsa mashi da toh, tun aranar da sukayi maganar ta kira Natasha awaya, ta faɗa mata tana son tazo Nigeria, tayi missing dinta, tana son ganin ta, Natasha taji dadin jin hakan dama neman hanyar da zato nigeri ta ke yi, har tambayarta ta yi dg zai barta tazo gidansa? Ummi ta gano abunda take ma hari, tace mata karta damu zai barta, kawai ta taho, tace mata toh in ta gama shiri zata sanar da ita.


*~_______________________________HAJJATY🌹~*





A firgice ta farka sakamakon knocking din daya katse baccin ta, idanunta biji biji cike da kasalar bacci ta soma kokarin mikewa, shafa gefen ta tayi jin wayam babu pravin yasa tayi tunanin ko shi ne ya fita, tun da babu wanda yasan da wannan gidan nasa..



Saukowa tayi daga kan gadon, tana mika hadi da yin Hamma, Yar rigar bacci ce a jikin ta dai dai gwiwarta, ga dukkan alamu ta dan ji saukin zazza6in jikin ta..

Bude kofar dakin tayi, Ta nufi kofar shigowa falon don anan ne takejiyo sautin kwankwasa kofar da akeyi.


har ta ruƙe handle din Kofar zata buɗe, Unexpected Tasoma jin sautin durowar wani abu mai nauyi abayanta..



Ta jikin bangon da take fuskanta Ta hango Idanuwar su, wani irin faduwar gaba taji, Kirjinta ya fara mata dakan uku uku, Tuni tasha jinin jikin ta, tsoro Ya hana ta juya, jikinta ya soma 6ari, sai faman zare na mujiya takeyi ganin inuwar mutane




Motsin da suka somayi suna tunkararta ne Yasa ta fasa ƙara, tare da juyawa ta manne ma kofar muryar na rawa ta shiga ambaton sunan Pravin Pravin...



Watsawa tayi da gudu  ta fada bedroon dinsu, adai dai lokacin Pravin Ya fito daga wanka waist dinsa daure da towel tana ganinsa ta boye bayansa, Tana nuna masa kofar shigowa dakin da yatsanta dake kerma sam takasa magana sai haki takeyi...


"Mun shiga uku, pravin dodanni ne masu bakaken kaya suna a falo zasu shigo su kashe mu"


 dakyar ta furta, da farko ya razana amma da ya ji hakan sai ya gane ture akayi masa daga gurin Elders, da kafarsa Ya bangaje kofar toilet Ya jefar da hajjaty ciki Yaja kofar ya kulle ta a ciki.


Ya gyara ɗaurin towel dinsa don ya zauna dakyau, da gudun gaske ya fito daga dakin Ya dira atsakiyar su, suna ganin shi suka girgiza jikinsu nan take suka rikiɗa suka koma dodanni, shima Ya rikida ya koma irin siffarsu, faɗane ya kaure atsakanin su, sautin buge bugensu da gurnaninsu ya cike falon, wata irin ƙura ce ta buɗe su..


shi ɗaya su biyar amma saboda yafi su karfin sihiri ko ƙwarzane basu yi mashi ba, sai dai yaji jiki ba kaɗan ba, daya bayan daya saida yayi masu jahilin bugun daya salwantar da rayuwarsu gaba daya ya zubar da gawarwakinsa saman floor, nan take Ya rikiɗa ya dawo suffarsa ta mutane, a zukunne Yana huci tare da haki kamar mayunwacin zaki, ransa yayi mugun baci, bai ta6a zaton Elders zasuyi masa haka ba, dama yasan ba zasu kyaleshi ba saboda sun tsane shi, suna bakin ciki yadda Elder Ya shigar da shi cikinsu ya bashi mukami daidai dana su..



Akan idanun shi gawarwarkin giants din suka 6ace, dama ka'ida ne Idan giant Ya mutu Evils basu barin gawar shi gaba daya suke 6acewa da shi.



Tunawa da Hajjaty yasa yayi saurin mikewa ya gyara falon ta yadda bazata gane komai ba.



Bubbuga Kofar takeyi da karfi cikin gunjin kuka take fadin"Pravin ka bude min kofa! Meyasa ka kulle ni Pravin? Dan Allah kada ka je gurin su, banaso su kashe min kai, zasu iya cutar dakai, dan Allah pravin ka shigo mu boye anan.." ita kadai take ta sambatun ta.



Jin motsin buɗe kofar yasa tay wuff ta fito atsaye ta taras da shi Yana haki, shassshafa jikin shi ta hau yi tana duddubawa don taga ko akwai rauni a jikin shi.


Adabarbar  ce ta furta"pr.. Pra..vin meya faru? Suna ina? Sun tafi? Ba suyi ma ka komai ba"?


 Murmushi ya ɗan saki ganin yadda take zare idanun ta a tsorace..



Hugging dinta yayi a kirjin shi tare da dan bubbuga bayanta Cikin sigar lallashi Yace"ture akayi mana, amma na kona su da ayar Allah, ba ki jiyo sautin karatun qur'anin da nayi ba a falo"? 



"Banji ba" murmushi ya saki

"Ayatul kursiyo tayi aiki dana fara karantota saida suka dinga bani hakuri akan indaina zasu tafi, nace bazan daina ba sai sun fada min waya turo su.." dagowa tayi daga kan kirjin shi ta zuba mashi ido tana kallon shi..


"Pravin sun fada maka wanene ya turo su"?


Yamutsa fuskarsa yayi"hmmm basai dana fada maki mu bar kasar nan ba kika nace akan mu zauna, toh wlh hajiya saratu ce ta turo su don su kashe mu nima daga bakin daya daga cikin aljanun naji..." ya wani sha mur don karta karto shi.



 rudani ne tsantsa kan Fuskarta, aranta ta ayyana hakan na nufin hajiya saratu tana bin bokaye? Dama itace kenan tayi asirin data gano akwai aure tsakaninta da pravin shine ta hada baki da marwa donsu 6ata shi agurin ta watakil ma itace ta daurawa marwa cutar Kuturta.."



gaba daya ta tsorata da al'amarin nan, daya lura ta yarda da shi sai yace"yakamata musan abunyi tun da har ta gano inda muke, in ba haka ba kashe mu zatayi.." zugata ya dinga yi har saida ta dauki zugarsa tace"pravin jiya naga passports dinmu acikin jakarka, pls ka nema mana hanya mubar kasar nan inyaso daga baya in komai ya lafa sai mu dawo saboda ya'yan ka, ko in suka neme mu, saboda ni wlh hankalina ya tashi, Hajiya saratu bata da imani, ashe har rai zata iya kashe wa? Pravin yace"hmm ke kike mata kallon mutuniyar kirki fiye da haka zata iya aikatawa.."



Ruko hannunta yayi suka zauna daga gefen gadon su.


"Dama saboda kin nuna bakiso mu tafi shiyasa na fasa, amma tun shekaran jiya nayi mana booking flight a online, na gama mana komai, ko yau kika amince ko gobe sai mu tafi" 



Cikin sanyin murya tace"na amince pravin, mu tafi kawai, amma ina zamuje? Ko delhi zamu koma"?


"A'a, Idan muka koma delhi wa muke da shi? Ticket din dana siya mana bana india bane, na china ne, kinsan muna zuwa idan aka tura mu daga Companynmu yin semina ko wani abu, har gida ina da shi, zamu fi samun kwanciyar hankali acan"


Ajiyar zuciya ta sauke tare da kwantar da kanta saman kafadar shi"koma ina zamuje mu tafi Pravin, duk inda zakaje zan bika, amma zanyi kewar Ahlin Obie, da Aminiyata.." ta karashe maganar da kuka..


Ajiyar zuciya ya sauke yaji dadin amincewarta, ƙwara ya gudu da ita tun da har an fara kawo mashi hari, Elders suna neman shi ga jami'an isod da ke neman shi ruwa ajallo...💔





*NATASHA'S ARRIVAL🔥*




Tana a cikin Toilet ta jiyo ringing din wayarta daga cikin ɗaki, saboda kira ne mai mahimmanci yasa ta dakata da abun da takeyi, ta fito da sauri, waist dinta daure da towel, bayan ta dauko wayar tayi picking ta kara a kunne..


Muryar Natasha tajiyo a cikin kunnanta


"Hey, guess what?"



"Your location shows you're in Nigeria, at the airport," Ummi ta faɗa da murmushi akan fuskarta


 "Hehehe, you guessed right, Send someone to pick me up, you knw I've never been to Nigeria."


"Okay, wait a bit, I'll arrange for someone to pick you up."


"Okay."



Bayan ta aje wayar kan gado, shaf shaf ta nufi closet dinta, ta shirya kanta cikin abaya, Ta na kokarin fitowa daga bedroom din su ka yi kici6us da Batool wadda ke shiowa hannun ruke da plate mai dauke da coconut buns


"Aunty ummina, have a bite"

Murmushi tayi tana zura hannu cikin plate din ta ɗauki coconut bun ta tura abakin ta, tana tauna hadi da dan jinjina kanta tace"wow ya yi dadi sosai, Ki aje min a cikin ɗaki, yanzu zan dawo.."


 ta faɗa tare da manna mata peck a forehead dinta.



Saukowa down tayi cikin sauri ta nufi part din Chief Owais tana zuwa ta taras bayanan.


down ta dawo ta fito daga main falo, adaidai Lokacin Motar Chief Owais ta kunno kai ta gate.


Akan idonta motar tayi parking, officer ya buɗe mashi motar





Gently ya fito sanye da kakinsa


"Sir, sunnu da dawowa.."


 juyowa yai  tare da kallon ta, murmushi yayi" yawwa Ummi hope kina lafiya"


"Lafiyalou ya gajiyar aiki"


"Alhamdulillah"


"Am Natasha called me, She's in Nigeria, at the airport pickup area, I told her to wait for me to pick her up."



"Bani contact nata, tare da hotonta, zan tura Officer ya ɗauko ta" 


Nan take ta tura mashi, ta juya ta koma ciki.




Bayan Owais ya turama Officer bayanan Natasha, da sauri yabi bayan Ummi, a main falo Ya taras da ita, tana ganin shi ta nufe shi ganin ya nufo ta, a tsakanake ya tsara mata yadda zata tarbeta batare data zargi wani abu ba.


Lokacin da officern daya tafi dauko Natasha ya karaso  Pickup area din tun kan yayi parking din Motar, Idanunsa suka hango mashi ita ta cikin glass din motar, da kallo ɗaya ya gane aka turo sa ya dauko.


Ta fita daban ko acikin mutanan dake a arean gurin, sanye take da button front robe, daga ciki tasaka Cami top.



Sai wani trouser da tasaka kallar robe din hot pink, gefen cikinta da wuyanta har saman kirjinta zanen tattoo ne na tantiran yan iska, hancinta na sanye da nose ring, saman le6enta ma wani hujan ne mai ɗauke da ring, ga wasu zako zakon Nails masu ƙyalli da tasaka.


Hannunta daya ruƙe da wayarta yayin da dayan hannun ke a dafe da hannun suitcase dinta.


Ta rufe idanunta da shades, ga wani hadadden kitso dake akanta wutsiyarsa jan gashin ta ta sauko har tsakiyar bayanta..


Agabanta ya tsayar da motar, ya fito ya nufe ta tare da mika mata hannu"welcome to Nigeria.."


 yamutsa fuska ta yi, tana yatsina baki tace"Who are you? Or Are you the one ummi sent to pick me up"? Ta faɗa tana nunasa da yatsan ta.


Jinjina mata kai yayi"yeah, it's me"


 Ƙin yarda tayi har saida ta kira ummi ta tabbatar mata da shi ne, sannan ta mika masa hannu suka gaisa, Ya kar6i suitcase dinta ya shigar mata da shi cikin boot, Ya buɗe mata front seat ta shiga ciki ta zauna tare da jan belt ta ɗaura.


Motarsu tana karasawo cikin Gidan, Ummi ta fito da sauri ta nufe ta, fuskarta dauke da murmushi.


Tana fitowa suka rungume juna.



"Welcome to Nigeria My gurl, I'm happy to see you, I miss you," ta fada tana sumbatar cheeks din ta


"I miss you too, Ummi, I'm glad to see you.."



dakatawa ta danyi da yin maganar, mood din fuskarta ya sauya..


A rude tace"You changed, Ummi I didn't expect that, Why are you covering your body?"


("ummi, kin canza min! Ba haka na zata ba, meyasa kika lullu6e jikinki")


 

"Natasha, zanyi maki bayani, kinsan a gidan dg ne, dole inbi dokarsa, shiya hana ni yin shigar da zata bayyana tsiraici na" 



ta fada tare da ruko hannunta"mu shiga daga Ciki" 



"Ciki zan shigo maki da akwatin"? 


Drivern ne ya fada cikin hershen turanci


Da hannu tayi mashi alamar A'a..


"Kabarmin shi a boot, ba'a nan zan kwana ba.."


"Why"? Ummi ne ta tambaya, yayin da suka shiga main falo..


"Gidan dg ne fa, i can't stay long, He won't let me hang out or enjoy myself, I'll be confined like a prisoner, Ƙwara in kira big boss ya turo a ɗauke ni" dariya Ummi tayi aranta ta furta"am sorry Natasha, nayi ma ki laifi, nima bada son raina ba..." 



tun da suka shigo take ta zuzuta kyawun Gidan Dj 


A main Falo suka zauna kan sofas suna fuskantar Juna.


"kin gudu kin barni da mutananki, kullum tambayana sukeyi Ina Ummi Ina Ummi? Ina taje ne, Yaushe zata dawo, Sunyi kewarki ummi, nima nayi kewarki, yakamata ki aje aikin nan mu koma america.."


 Murmushi tayi mata"Natasha, zamuyi wannan maganar, amma ba yanzu ba, Kina bukatar ki huta, nasan kin kwaso gajiyar tafiya"...


Girgiza kai tayi"No, babu gajiya a tare dani"


"Zakiyi wanka ko zaki ci abinci"?


"Zan fara da abincin, but You know I'm allergic to meat"


"Karki damu, nasan me zansa akawo maki"  ta fada tare da kiran landline din kitchen, ta sanar da Chefs abun da take buƙata..


"Big boss ya san da zuwanki kuwa?


"Ban faɗa masa ba, kinsan halinsa baya son mu san identity din shi, in har na fada masa zai hanani ne, ni kuma bana so ya sani saboda wannan zuwan da nayi, nayi shi ne saboda kin neme ni, kuma saboda inaso naga baby preety na..." 



yanayin fuskar Ummi ne ya sauya zuwa damuwa da faɗuwar gaba, tunawa da abun da suka tattauna da Chief game da big boss, batasan ya Natasha zata ɗauki abun ba, tasan halinta tana da kafiya da rashin kunya ba kowane zai iya juya ta ba..


"Ummi me kike tunani ne"? Ta tambaya tana kallon fuskarta"kamar akwai abun da ke damunki"


Girgiza kai tayi"ba abun da ke damuna Natasha..." bata kare maganar ba, Chef Ya shigo falon bayan yayi ma Natasha barka da zuwa yace sun kammala shirya masu lunch a dining room


Godiya ummi tayi masa, kafin ta dubi Natasha mu tafi" mikewa tayi suka nufi dining, bayan sun zauna kan kujera suna fuskantar Juna, chef ya yi serving na su..

Suna cin abinci suna firar yaushe rabo.


"Ina taso in tambayeki Ina handsome boy din nan"?


 Shiru ta ɗanyi jimm kafin tace"Yana a isod camp, gurin training" ta faɗi hakanne saboda tasan ko ta fada ma Natasha ya rasu ba yarda zatayi ba.



"Wow, i can't wait to see him in isod uniform, he will look hotter, but ina sauran yaran? Banji motsin kowa ba, ko ke ka ɗai ce a gidan"


"Bani kadai bace, yaran basa nan, suna agidan Kawun dg, Biyu ne suke a tare dani, bari na kira maki su ku gaisa..



Tana niyar ɗaukar waya muryar Unaisah ta katse su"aunty Ummi, baƙuwa mu ka yi ne"? ta fada tana nufo su, sanye take da long gown.


Lokacin da Natasha ta jiyo suka fuskanci juna wani irin faduwar gaba taji, ganin matar da take ha6o, batayi tsammanin ganin ta ba..


miƙewa Natasha tayi ta mika mata hannu"nasan baki sanni ba, amma nasan ummi ta fada maku dangane dani, ina fata na same ku Lafiya..." 


da ido Ummi tayi mata alamar ta saki jikin ta, cos ta lura da yadda ta haɗe rai kamar bata ta6a yin dariya ba


Murmushi tayi tare da nufarta, suka yi hugging din juna, cike da kyankyaminta Unaisah tayi saurin raba jikin su.


Wani irin kallon tsana Unaisah take jifar ta da shi, yayin da Zuciyarta ke tariyo mata fuskar Unaizah, hatta Kitson kan Natasha shigen irin kitson da ke akan Unaizah.


Daƙyar ta haɗiye abun da ke aranta ta ɗan saki fara'a tace


"I welcome you, I'm happy to see you, Natasha."


Washe baki Natasha tayi tana faɗin"I'm glad to meet you too, What's your name?"


"Unaisah," 


"Wow, you impress me"


.ta faɗa tana ƙare mata kallon, haushi duk ya cika Unaisah ganin yadda take kallon hips dinta da kirjinta tana kashe mata ido har wani zuro harshe take yi tana lashe lips din ta kamar karya..


Ummi bata lura ba saboda ta bata baya.


_Heartless monster, kin gama yawo tun da kika kawo kanki Nigeria_


ta faɗa a cikin ranta.


Juyowa ta yi rai a6ace tabar dinning area din tana gab da zata shiga bedroom dinsu tayi kici6us da Batool dake fitowa"Ina zakije"


"Gurin Aunty Ummi"


Wani kallo tayi mata, aranta ta ayyana bazan bari karyar can ta ganki ba sis..


"Aunty Ummi ta yi Bakuwa, kuma bata son kowa Yaje kusa da su, mu koma Ciki, zan kunna mana korean drama mu kalla....." 


ta faɗa tare da jan hannunta suka shige ciki, taja kofa ta kulle duk don kada ta ƙara ganin Natasha.


"Ummi, this girl has grown I know she's mature now, naga hips dinta sun buɗe, ƙirjinta sun ciko, ta tada min jarabata, dana kalli nipples dinta sai da naji..." 


bata ƙare magabar ba, Ummi ta daka mata tsawa a firgice ta zare idanunta tana tambayar meya faru? Bama tasan me tayi ba, saboda jakkanci..


"Am sorry Natasha, nan gidan dg ne, yakamata kisan irin maganganun da zaki faɗa, yaran nan ko kallon banza ki ka yi ma su ba ƙyale ki za'ayi ba.." zare blue eyes din ta tayi"saboda me"? Banza tayi da ita, duk taji komai ya fita ranta saboda kalaman da ta furta akan Unaisah, har ga Allah ta daɗe tana jin tsanar halin Natasha mace ba kamun kai kamar balamar tinkiya.



Bayan sun kammala Cin abincin, Ummi tace ta tashi su tafi akwai dakin hotel da ta kama mata, Natasha tace ita fa taga wurin zama, ta fasa tafiya anan zata kwana.


Tun da taji hakan ta gane me take mawa aikuwa ta dinga lalla6ata don ta tashi su tafi, saboda batason taja mata abun kunya, Natasha ta kafe akan maganarta, har tana fadin ko dai korarta takeyi ne? In ba haka ba why zata gayyace ta kuma ta matsa mata akan ga inda takeson ta kwana"? Badan taso ba ta ƙyaleta..


Around ƙarfe shabiyu na dare,  natasha ta farka daga bacci, ta sauko daga kan gadon, Camisole ce a jikinta shara shara kana iya hangen Inners din ta.


Mika tayi tare da yin hamma, ko da ta hango ummi kwance kan couch tana bacci wani shu'umin murmushi tayi ganin ta samu damar da zata aiwatar da kudurinta.


Cikin sanɗa ta fuce daga ɗakin, ta sauko down, ta fara neman bedroom din su Unaisah, ko tsoro bataji, bedrooms din dake a down stairs taita buɗewa tana leka cikin su


Batasan Cctv tana  tana ɗaukar duk wani motsin ta ba.


Dakyar ta gano kofar dakin, tana shiga ta hangosu kwance kan gadon sunyi nisa a baccin su, kowannansu da inda yake fuskanta, lashe le6enta tayi, kura taga nama, Cikin sanɗa ta nufi gadon ta tsaya tana bin su da mayataccen kallo, kasantuwar bargon da suka lullu6e ya zame daga kan jikin su.


Shantala shantalan cinyoyinsu da dukiyar fulanin su ne suka tsone mata idanun ta.


Tayi zaton irin yaran da ta saba yima wayou ne ta lalata su. 



A hankali ta hau saman gadon, ta fara shafa laps din Unaisah tana lashe harshe, kamar mayya, har wani sautin jaraba take fitarwa, tana kokarin zame mata pant.


Kwatsam batai aune ba taji an duma mata zazzafan dundu a saman bayanta, ji kake durum! 


 A firgice ta furta"what the f...?!"


 bata ƙarasa ba, Ya toshe bakinta da tafinsa, Ya janyota ya sauko da ita daga kan gadon, yajata ta karfin tsiya ya fitar da ita daga dakin, ya nufi can ciki da ita, a wani daki da ke a hanyar backyard din gidan, Ya jefar da ita Ciki ya kulle kofar, ta dinga bubbuga kofar tana zage zage, batasan ɗakin Soudproof bane, in mutun yana a ciki ko zaiyi ihu babu wanda zai jiyo shi daga waje.


Batasan dama dakonta yakeyi ba, lokacin da take neman  bedroom din su Unaisah yana atsaye kan stairs, Yana kallon duk wani motsin ta.


Dama Yaji a labarin Unaizah ta bada gudummuwa gurin lalata yarinyar hakan na nufin yar les ce ita kuma tana bin maza, tayaya zai iya bacci da mugun abu agidansa? 


Komawa yayi bedroom din su Unaisah, don ya gyara masu duvet din su



Yana ruko bargon unexpected ta cafke hannun shi, har saida gabanshi ya faɗi, farkawarta kenan, a hankali ta mike da rudu kan fuskarta take duban shi

Ganin shi a bedroom dinsu, daga shi sai short da shirt..



Cikin sauri Taja rigar baccinta ta lullu6e laps dinta.


Wani kallon tuhuma take jifarsa da shi, kasa magana yayi saboda ya rasa amsar da zai basa, abun da kunya baisan tayaya zai kare kanshi ba, Natasha taja ma shi Ya taka sahun 6arawo, 



Girgiza mata kai yayi cikin nutsatstsiyar muryarsa ya furta" zanyi maki bayani Unaisah, ki saurare ni, kinsan ba hali bane.. "



"Yaya Owais, wani irin bayani zakayi min bayan wanda nagani da idanuna? Me ya kawo ka dakinmu? Me kuma yasa ka ta6a jikina har ka yi yunkurin cire min rigana? ..."


 bata kare maganar ba, yai saurin toshe mata baki da tafinsa, zama yayi daga gefenta" idanunsu cikin na juna.



Kafin ya dan saci kallon Batool dake a kwance tana bacci, fargabansa kada ta tashi abun zaiyi masa yawa..


"Bani bane nayi maki haka ba, Natasha ce kawar Ummi, Na kamata ne tana kokarin... "



kasa karasawa yayi, ta zare idanunta cike da bacin rai, dama saida ranta ya bata bazata ƙyaleta ba, wannan wata irin dakikiya ce"?


"Ki kwantar da hankalin ki, yanzu haka na kulleta a daki, ba zata kara fitowa ba, har sai mun gama bincike akan ta.." 



ajiyar zuciya ta sauke ta re da cire hannunsa daga kan bakinta"am sorry hubby, rashin sani ne, bansan haka abin ya faru ba.."



Murmushi yayi"na fahimce ki, ki koma ki kwanta.." ya fada tare da mikewa Ya juya har ya kusa fucewa daga bedroom din ya dan dakata tare da kallon ta yace


_"kisa ma ranki, Ni chief bazan ta6a gigin ta6a jikinki ba, har sai munyi aure lokacinne nake da damar da zanyi komai nakeso dake.."_


yana karasa fada ya fuce, murmushi tasaki tare da janyo pillow ta rungume shi a kirjinta.



~______________________________~




Motsin bude kofar da taji ne yasa tayi saurin mikewa cikin bacin rai da fusatacciyar murya tace"Who the hell are you? And why did you lock me in this room?" 



Kunna switch din dakin yayi haske ya kawo, tana ganin Chief Owais ta washe baki ta nufe shi da ƙwarƙwasa don taja hankalinsa, batasan kallon ƙato ya ke mata ba.



"Abun daya faru kuskure ne, ni ban shiga don na cutar da su ba.. " 


ta faɗa tana kokarin kai hannu donta shafa kirjinshi aikuwa ya damƙi wuyan hannun Ya murɗe shi kamar zai 6ulle shi.


 fasa ƙara tayi radadin da tajine yasa ta fitar da gumi, saida ta galabaita ta dinga sambatu tukunna Ya wurgar da ita kasa kamar kayan wanki ta kife kan floor


"Ki shiga taitayin ki idan kinason mu rabu lafiya idan ba haka ba, Jikinki ne zai gaya maki.."


 ya fada tare da zama kan kujera Ya daura kafarsa daya kan daya..


Ranta a6ace ta dube shi"bakasan wacece ni ba, sai na rama abun da kayi min.." mikewa tayi ta nufi kofar dakin tana rukewa tajita a kulle..


"Ni kuwa nasan wacece ke, fasikar data lalata rayuwar matashiyar da aka bata rainonta tun tana jaririya, mace mara imani mara tausayi, wadda bata san zafin haihuwa ba"!


 Kalamansa sun daga hankalinta, tayaya akai yasan wannan labarin? A rude ta juyo ta fuskance shi, a ranta ta ayyana badai ummi ce taci amanarta ba? Ko dai dama ta kira ta ne da wata manufa...



"Abun da kike tunani aranki gaskiya ne"


"Ni nasa Ummi ta kira min ke.."

Cikin rudu da fusata tace"saboda me? dama tarko ne ku ka ɗana min kai da Ita ko? Bazan kyaleku ba, zan kira big boss, you'll all pay for it"



"Taya zaki iya kiran shi? Sai lokacin ta tuna bata da waya a hannunta ga kuma kofar a kulle.



"Open this door! Let me out, Ka bude min kofa in fita in har ba kidnapping dina ku ka yi ba.."


 duk tabi ta ruɗe..


"Akwai tambayoyi da nakeso in yi maki, idan kika amsa minsu ta lalama zan barki ki fita . ." 



bai kare magabar ba, ta kwatsa mashi tsawa"I won't answer your questions, ba mu da wata alaka da juna, bakasan ni ba nima bansan ka ba, don haka ka kyaleni in tafi, ita kuma Ummi bazan ƙyaleta ba, tun da har taci amanata saina tona mata asiri agurin Big boss, dakai da ita duka zaku gane kurenku" 



duk yadda yaso ya shawo kanta taki bashi hadin kai, har saida ta fusata shi ya zuciya rai a6ace ya mike daga kan kujerar da ya ke, ya nufeta tana zare idanu ta shiga fadin kar ya taba ta, karya kuskura ya matso kusa da ita.



Ƙokarin kai mashi bugu tayi, yayi saurin kaucewa ya damƙi ƙeyarta ya buga kanta jikin bango ta fasa ƙara.


"Gargadi zanyi maki na karshe, karki kuskura ki kara yi min magana da tsawa ko kice zaki yi min rashin kunya, I'm easy-going, but don't test me.." ya faɗa da kakkausar murya.



sakin ta yayi, ta juya ta fuskance shi, hannun ta dafe da gefen bakin ta daya fashe.


ya zaro bindiga yayi tare da saita ta da ita, gabanta na faduwa ta zazzare idanun ta, duk tabi tasha jinin jikinta...


"Idan na kashe ki na kashe banza, Kinsan da hakan ko" a firgice ta jinjina mashi kai


"Wa kike da shi a Nigeria? Shi kanshi wanda kike taƙama da shi bazai iya ku6utar dake ba, saboda shima mai laifi ne, idan ke yafi karfinki, baifi karfin doka ba, mahaifina shine shugaban kasar nan, ni kuma dg din Isod ne" 

 

 dabarbarcewa tayi muryarta na rawa ta furta"I won't repeat my mistake, Please don't kill me"


"bazan kara maimaita kuskuren da nayi ba, kada ka ka kashe ni..." ta faɗa tana zama kan kujera



"Ka fadamin meyasa kuka kira ni? Wani laifi big boss ya aikata? Meyasa kuma ni zaku sanyani a ciki bayan ban hada alakar komai da shi ba..." murmushin gefen fuska Chief yayi jin ta sauya magana yanzu dataga bata da mafita..


"Naji komai daga bakin Ummi, game da alakar dake a tsakaninki da big boss,  sai dai ina neman karin bayani, ki fada min komai idan ba haka ba kema zaki shiga cikin wadanda muke zargi .." a tsorace ta ɗan zare blue eyes din ta.



Tana faman share zufa tace"bansan komai dangane da shi ba, ka tambayi ummi, ni ban taba zuwa nigeria ba, wannan ne karo na farko, kuma da nasan tarko kuka dana min da banzo ba, big boss baya bari insan identity dinshi, farkon haduwana da shi a beach ne, ni nafara shisshige mashi har saida ya bani hadin kai, ya kuma nuna yana son in zama karuwarsa zai dauki nauyin komai da zan bukata arayuwata, na amince masa saboda a lokacin ya kwanta min a rai, bayan haka ina cikin bukatar kudi.


Silar haɗuwana da shi, Ya mallaka min gida da mota, ya bani black card dinsa, komai da nakeso yi min yakeyi.."


"Bai ta6a nuna yana son ya aureki ba"?


Girgiza kai tayi"ni nake son shi, Inason na aure shi amma bai taba bani dama ba, ya riga daya fadamin ba da aure yake sona ba, bazai aureni ba, but he will keep coming and having sex with me, ba yadda banyi da shi ba, har na hakura nabiye ma shi"


Lokacin da muka shaku sosai shine ya kawomin jinjira a cikin towel yace min ya bani ita dana tambayesa yar wacece sai yace min yar matar yayansa da ya rasu ne, bayan da ta haifeta ta samu matsalar shayarwa shine ya kawomin ita don in raineta, ya fadamin sunanta Unaizah, yarinyar ta kwantamin araina, ni na shayar da ita na raine ta har ta girma.."


"Meyasa bakiyi bincike ba kika kar6i yarinyar da baki taba ganin wani nata ba? Kawai don ya kawo mi ita, yace miki yar yayansa ce sai ki kar6a? Baki yi tunanin meyasa bai ba wani danginsa ya kula da ita ba sai ke? Bayan kinsan cewa tushen shi daga Nigeria ne, bayan haka saboda rashin hankali kika bada gudummuwa gurin gurbata ta ko? Baki dauketa ya ba, baki bata tarbiya ba, dake da shi ku ka hadu kuna amfani da ita saboda rashin hankali"



"Ai ba laifi bane, abun da takeso ne mukeyi mata..." baisan sa'adda ya wanka mata mari ba, har saida fuskarta ta kalli gefe daya, dafe kuncinta tayi, taji zafin marin sosai, cike da bacin rai yace"kinji kunya, banza dakikiya, saboda kinga ya wukalantata shine kema kika bada goyan bayan a wulakantata ko? baki yi tunanin ya mahaifiyarta zataji ba, baki taba tambayarsa ya maida ma uwa yarta ba,  saboda son zuciya ko? Idanunsa sun ciko da kwalla..


Hankalinta ya tashi da ganin bacin ran dake a cikin idanunsa


"You never asked him to return the daughter to her mother because of selfishness."


"Why should I worry about asking him after he never discussed returning her with me? Why do you keep accusing me when I'm not guilty? Everything I did was with his support, I treated her well, with morals, I never hurt her, I took care of her, made her happy"


(Tayaya ni zan damu da tambayarsa bayan shi bai ta6a yi min magana akan zai maida ta ba? Meyasa zaka dinga tuhumata bayan ni bani bace mai laifi ba? komai da nayi shi ya bayani goyan baya, kuma ni haka na taso rayuwata,  azamana da baby pretty ban ta6a cutar da ita ba, na bata kulawa, na bata tarbiya na kuma bata farin ciki, komai takeso inayi mata shi)


"duk da bani na haifeta ba, bata ta6a sanin bani na haifeta ba, saboda ya gargaɗeni akan bayason ta sani kuma nayi hakan saboda yarjejeniyace a tsakanin mu, Kuɗi ya ke biyana.."



 _cike da takaici Chief ya dafe kansa bakin cikine ya cika zuciyar shi, komai daya faru ubanta ne yaja mata, maganar Natasha gaskiya ne, da ace bai kai mata ita ba da duk hakan bai faru ba, kuma da ace ya kwa6e ta akanta da bata 6atata ba, amma dayake dama da biyu ya kai ta saboda ya riga daya sadaukar da ita bata da amfani a gare sa, bayan haka Natasha baturiya ce baturiyarma mai yanci kuma karuwa, dama wasunsu ba hankali gare su ba, gani suke indai jin dadin rayuwane komai da zasuyi don su faranta ransu mai kyau ko mara kyau ba laifi bane, suna da right din da zasuyi amma duk da haka bazai kyaleta ba, yadda Unaizah ta dandani zafin cin amanar da su kayi mata haka ya ke son kowan nan su ya danɗani kwatankwacin raɗadin da taji a cikin zuciyarta_


"Since last year, ya raba ni da ita,  ya maidata gurin mamanta, yanzu haka wannan zuwan da nayi hada don inason naganta, in kuma rokesu su bani ita saboda bazan iya rayuwa batare da ita ba..." bata kare maganarba ya kwatsa mata tsawar da data razana ta


"Su baki ita don kicigaba da biyan bukatarki da ita ko"? Ya fada kamar zai rufeta da bugu.


Girgiza kai tayi"ba saboda haka nakeso  ta dawo gurina ba, inason ta, ina jinta kamar yar dana haifa a ciki na, After that, I had a problem, I'll never give birth"


"Kina daukarta kamar ƴa? Kina nufin har yarki ta cikin ki zaki iya kwanciya da ita.."? Cike da jin shakkar shi ta ɗaga mashi kai alamar eh


A zuciye ya ɗaga hannu zai mareta tayi saurin kare fuskatarta da hannun ta


"Ya isa haka! Nagaji! Ka daina mari na! Ko dan saboda girmana ya kamata ka girmama ni, na fahimci haushina kake ji, ka tsaneni, amma yakamata ka gane ni bani da laifi..."


"Ke kike ganin girma a tare dake, Ni kaskanci da jahilci nake gani a tare dake, baki da mutunci ko kima a idanuna, saboda ke din mara imani ce, dabba mara hankali.." 


taji zafin kalamanshi sai dai kwata kwata bata nuna hakan ba.


"Yau ki ka zo nigeria, Kuma a yau kika shiga dakin yaran da baki hada alakar komai da su ba, ki kai yunkurin taba jikinsu saboda jaraba kuma a haka kike kiran kanki mara laifi? shiru tayi bata musu ma shi ba.



Jinjina kanshi yayi ji yake kamar ya binneta da ranta saboda haushinta da yake ji


"Kin ta6a haihuwa da shi"? 


cikin fushi tace"I don't know, I'm tired of your questions, kamar nayi maka laifi saboda kawai nazo gidanka zaka tsareni da bugu kamar jaka.." 


rufe shi da fada tayi ta inda take shiga bata nan take fita ba.


Sam ta manta da gun din hannunsa sai da taji ya har6i vase tayi kara taja baki tayi shiru a firgice.


"Zaki amsa min tambayata ko kuwa"?


Harara ta watsa mashi tana yatsina fuska tace"Na ta6a sau ɗaya, amma ba araye na haife su ba" a takure ta amsa tambayar..



"Mata ne ko maza"?



"No, they are mixed twins"


jinjina kan shi yayi da alama akwai abun da ya ke tunani aran shi.


Yanzu ya gane itama Ya ci amanarta batare da sanin ta ba, hakan yayi mashi dadi, saboda itama taji abun da uwa take ji idan wani ya cutar mata da, kuma zatayi danasanin komai da tayiwa Unaizah.


"Pls kada ka kara tambayana nagaji.." ta fada tana yatsina masa baki, fuskarta sai naso ta ke yi kamar ɗanyen nama.


Jinjina kan shi yayi"Okay"


"Tunda na amsa maka tambayoyin ka, nima ka amsa mun nawa, wani laifi big boss ya aikata? Me kuma yasa ku ka kira ni? Sannan meyasa kake tambayana akan Unaizah? Kana da alaƙa da ita ne?


"Zaki sani amma ba yanzu ba"  


Juyawa yayi zai tafi tayi saurin bin bayanshi


Juyowa yayi"ina zuwa"?


"Zan koma ciki mana, in ba baka son ganina tafiya zanyi yanzun nan don ko mintuna banso in ƙara a gidan nan"


Murmushi Chief yayi"nan ne masaukinki a gidan nan, babu ke babu fita, za'a dinga kawo maki abinci, da kuma suturar sanyawa, akwai toilet in bukata ta kamaki .."


 arude tace"bangane ba? Me kake nufi? Garkuwa kukayi dani ko kuwa na aikata laifin daya cancanta ku kulle ni ne? ..." 


bai tsaya sauraranta ba, ya fuce tana kokari fita kofar ta datse kanta.


Bugun kofar ta din ga yi da kafarta da hannunta, kamar zata balleta, a karshe data galabaita, agajiye ta sulale kasa ta jingine kanta jikin kofar, zuciyarta a cunkushe take da bakin cikin cin amanarta da ummi tayi, gayanan taja mata bala'e da ta sani da bata zo ba   🔐



(🔥UNEXPECTED CALL OF HAJJATY🔥) 



Around ƙarfe 2 da rabi na dare suna akwance kan gadonsu,  rabin jikinsu lullu6e yake da duvet, babu wadataccen haske a dakin nasu, kasantuwar sun kashe light din before su kwanta sai dai hasken Bedside lap da su ka bari a kunne..


Ringing din waya ne ya takura baccin nasu..


Wayar sai ruri take daga kiran ya katse wani ke shigowa.


Farkawa tayi bakin ta dauke da addu'ar ta shi daga bacci, a hankali ta buɗe idanunta da suka kada ja saboda bacci ta dube shi da su..


Murmushi tayi, ganin ya samu bacci yau.


Tana tsaka da kallon fuskar shi, Ringing din wayar ya katse ta.


Sam ta manta me ya tayar da ita daga bacci sai da taji ringing din


Gabanta ne ya fadi da rudu akan fuskarta ta furta wanene ke kira na da tsakar daren nan?


 Kasa motsawa tayi saboda tsoro ne da ita, tayi lamo a kirjin Mijin nata.


Sai da taji anƙi daina kiran wayar nata ne yasa ta fara tunanin ko dai wani muhimmin abu ne yasa aka kira ta? Wata kil ma na cikin gidan ne ke kira.


A hankali ta raba jikinta da ga nashi, ta sauko daga kan gadon cikin sanda ta ɗau wayar, duk don kada ta tada shi daga bacci.

Juya ta nufi can cikin dakin daga bangaren walk-in closet din su. 

Screen din wayar ta duba, missed calls ta gani daga new number


Hakanan ta dinga jin fargaba, kamar karta daga kiran, amma zuciyarta ta matsa mata akan ta daga taji wanene..


Adaidai lokacin an sake kira, yatsun hannunta na kerma ta yi picking ta kara wayar a kunne unexpected taji yo muryar Hajjaty tana yin magana cikin muryar raɗa


"Kina jina? Taji ta ambata. 


Wata ajiyar zuciya ta sauke dadi ya lullu6eta kamar zata saka kuka tace"hajjaty ina kika shiga? Meyasa zaki gudu batare da kin neme ni ba? Kin kuwa san halin dana shiga? Kullum tunanina wani hali kike ciki..." bata kare maganar ba ta katse ta..


"Pls, bana so wani yasan na kira ki, ke ka ɗai ce ko kina a tare da Oga"


"Ni kadaice hajjaty, babu kowa a kusa dani" tana jiyo ajiyar zuciyarta.


"Ki fada min meyasa kika gudu? Ta tambaya kamar batasan komai ba.


Fashe mata tayi da kuka"kina nufin baki ji komai ba"?


"Banji ba, nadai ji labarin kin gudu"


Saboda ta aminta da ita yasa ta faɗa mata komai da Pravin ya sanar da ita, turai ta ruɗe da jin labarin yasha banban da wanda ita ta sani.


"Ki yi hakuri ban ta6a sanar dake ba, yanzun ma tura ce takai bango, bani da mafita daya wu ce in sanar dake gaskiya, Pravin ya matsa mu bar kasar saboda yana jin tsoron hukuncin da zamu fuskanta agurin Hajiya saratu da yayyanta, ni kuma banaso mu tafi saboda ya'yan shi da matar shi, ni ma kuma na saba da ahlin obie, nayi nayi da Pravin ya bari muzo mu nemi yafiyar su amma yaƙiya, kwat kwata baison wani yasan inda muke, ko fita zaiyi da mask a fuska ya ke fita, na rasa ya zanyi in shawo kanshi, yanzu haka da nake maki magana baisan na saci wayar shi na kira ba, Yana adaki yana bacci.." 


"Hajjaty, ki kwantar da hankalin ki, Naji komai tabbas baku kyauta ba, da kuka zauna tsawon shekaru kuna boye musu alakar dake atsakanin ku, da tun farko kun fada masu komai da duk hakan bata faru ba, amma yanzu abun da nakeso dake, Karki bari Pravin yasan kin dauki wayarsa, ko kinyi waya dani, tun da na fahimci tsoro ya ke ji, kawai idan mun gama magana ki goge number ta, kada ki kara kira kuma kada ki ta6a ta, ni duk zanji da komai, In sha Allah zan yi kokarin sulhunta tsakanin ku da su.."


"Nagode Aminiyana, dama nasan ke kadaice zaki iya share min hawaye na, amma taya zaki tuntu6e mu idan sun yafe mana? gobe fa zamu tafi" 


"Kin san sunan anguwan da kuke ne?


"Bansan komai ba, lokacin daya kawo ni bana a hayyacina" 


"Okay, Kiyi yadda nace maki, ki ajiye wayar" zan sake kira amma ki kwanta kinji"? Amsawa tayi da toh"amma pls kiyi sauri ki kira kafin ya farka, wlh idan yaga na kira ransa zai baci"


"Toh" daga haka su ka yi sallama.


Juyawa tayi cikin sauri ta koma kan gadon su.


"Babe, ka tashi, Hajjaty, ta kira ni, ka tashi pls! Gobe zasu bar kasar" dakyar ta samu ya farka yana yamitsa fuska idanunsa a rufe yace"pls kada ki takura min, Ki kyaleni.." saitin kunnanshi takai bakinta"hajjaty ta kira yanzun nan.." bata kare maganar ba, taga ya ware idanunsa tare da mikewa yana tambayar ta wace hajjatyn?


"Hajjaty dai daka sani, ba ka ce nemanta ku ke yi ba, To ta kirani da bakuwar number yanzun nan"


 Bai  tsaya sauraron karashen zancen ba Yace Ina number din data kira da ita, Wayar ta mika masa yasa hannu ya kar6a, ya na dubawa..


Me kuka tattauna da ita..


Zayyana masa tayi, ta dan marairaice fuska tace"babe, na rasa gane kan zancen, a maganar hajjaty bata nuna tasan wani abu game da ciwon hajiya saratu ba, ku kuma kunce kuna zargin faɗane ya haɗa su! Ban dai tambayeta komai ba ban kuma fada mata meya faru da hajiya saratu ba, gudun kada in daga hankalin ta, amma tayaya akai hajiya saratu tasan da aure atsakanin su? anya Praveen yana da gaskiya kuwa? Na fara zargin shi, meyasa zai matsa akan su bar kasar nan? Bayan ga matar shi nan rai hannun Allah, ga kuma ya'yansa kuma meyasa pravin yakeso su bar kasar akan abunda bai kai ya kawo ba? Tun da ta fara maganar bai kula ta ba, yana ta danna wayarta.


"Dan Allah kayi kokari ka taimaka masu nasan sun tsoratane shiyasa zasu gudu, tun da sun gane kuskurensu a kira su aji meya faru, ni bana zargin su, pls muyi wani abu, kafin gobe"



Wani kallo Sir mubarak yai mata, tuni taja baki tayi shiru


"Kin cikani da surutu kamar aku, zaki kwanta ko saina matseki"


 ya fada da zolaya, dariya tayi tare da kwantar da kanta, yaja mata bargo ya lullu6eta duka har kanta


Daga cikin bargon taci gaba yi masa magiya akan ya taimaka ya dawo mata da yar kawarta gida.. " 


Saukowa yayi daga Kan gadon, daga shi sai dan short, ya nufi walk-in closet nasu jim kadan ya dawo, sanye da jallabiya a jikin shi, har ya fuce daga dakin bata sani ba sai bayan tafiyar shi ta ɗan leko daga cikin bargon tayi mamakin ganin babu shi kuma bai aje mata wayar ba, fatan ta Allah yasa za su je su dawo da su hajjaty ne.


________________________🔥



*ANEELERH🔥*



Around ƙarfe sha biyu na safe ta farka daga guntun baccin daya dauke ta tun bayan da suka kammala breakfast, Miƙa ta yi tare da yin hamma kafin ta sauko daga kan gadon jikinta sanye da jallabiya, ta lullu6e kanta da hula, doguwar sumar kanta ta sauka gefe da gefen kafaɗarta,  bata damu da rashin ganin junaid a bedroom din ba, tasan bazai wuce dakin mami ba ko na zahra, cos yau ba school weekend ne, har ta juya zata fuce daga dakin wayar ta dake ajiye kan bedside drawer ta fara ruri juyawa tayi cikin nutsuwa takai hannu ta ɗauki wayar ganin sunan Benazir ya bayyana akan screen din yasa ta sakin murmushi cike da zumuɗi tayi picking call din tare da kara wayar a kunnanta.


"Amarya kuma uwar gida agurin Taj, ya kike? Ya su mami? fatan kuna lafiya..."


On the other hand sautin dariyar Benazir ya cika kunnanta"har kinsa naji wani sanyi araina da kika ambaci Taj, da ace muna a kusa har tukuici zan baki saboda faranta min rai da ki kayi..."


 murmushi Anila ta saki, bayan sun gama gaisawa Anila tace"yaushe zamu sake komawa gidan Dj ne? Nayi missing din Aisha, Inaso na sake ganinta, kullum da tunanin ta nake wuni, gashi har yanzu bata ɗaga kirana ...." 


Benazir tace"wallahi nima har yanzu bata ɗaga kirana, bansan me mukayi mata ba, shima ya shureim bata ɗaga kiran shi,  saboda yadda na damu da ita har mafarkinta nakeyi..." 


bata ƙare maganar ba Anila ta katse ta da cewa"bakya tunanin akwai wani dalili dayasa take fushi da mu? In ba haka ba me mukayi mata"? Ta faɗa fuskarta a yamutse kamar tana a kusa da Benazir din.


"Anila ni kaina saida nayi wannan tunanin, amma na rasa gane laifin me mukayi mata? In ma saboda abunda ya shureim yayi mata ne yakamata ace komai ya wuce yanzu, bawan Allah nan har hakuri ya bata, mu ma mun bata hakuri, abu fin shekaru tana rukon shi a zuciyarta..." 


Anila tace"har yanzu bana ganin laifinta, kinsan zuciya bata da ƙashi, Aisha tasha wahalar rayuwa, in har zata dinga tuna bakin cikin data kunsa silar abun daya shiga tsakaninta da ya shureim ba lallai ta yafe masa ba, ni wallahi abun daya daga hankalina game da ita, canzawar da tayi, bansan wata irin rayuwa Aisha tayi a america ba, amma kallo daya zaki mata ki gane ba ustatha bace, zato zunubi amma kammanninta kamar irin na tantiran yan barikin nan, idanunta sun buɗe, dai dai da tafiyarta bata uztazai bace..." 


bata kare maganar ba jin shesshekar kukan Benazir


"Koma meya faru da Aisha mune ne sila"


  lallashin ta Anila tayi har saida ta samu tayi shiru na ɗan wani lokaci kafin Anila ta ce"sun ce zasu neme mu, amma naji shiru har yau basu kira mu ba, nifa kawai ina rayuwa a cikin gidan nan ne saboda iyayena suna a cikin sa, amma wallahi kullum cikin fargaba nake saboda Uncle dan iya, ko haɗa hanya da shi bansan yi, mutumin ya fita araina na tsane shi, shiyasa na kosa su gama binciken su akan videon ana, suzo su kama shi kawai kowa ya huta"


Cikin sanyin murya Benazir tace"nima din hankalina ba a kwance ya ke ba, koda yaushe cikin fargaba nake, tun da na fitar da sirrin abun da na sani game da Uncle musa, dama ina zargin shine ke yunkurin kashe ni, shiyasa time da nayi ciwo nai ta pretending kamar bana acikin hayyacinta saboda na fahimci bai hakura ba, har yanzu yana akan bakansa na daukar mataki akai na, Anila bansan ya zanyi ba, banaso wani abu ya samu iyayena da ya shureim, gashi duk muna a karkashin ikon shi, in har ya gane na fitar da sirrin wlh zai iya binne mu da ranmu tun da ba imani ne da shi ba.."


 gaba daya sun shiga damuwa.


"Benazir, mu dai bamu yi dacen kawunnai ba, wallahi ban taba zaton Uncle dan iya zai iya aikata rashin imanin nan ba, mutumin banza me fuska biyu, Allah kadai yasan ina yakai Ana, na rasa gane kashe ta yayi ne ko kuwa wani gurin ya kulleta, daurewa kawai nakeyi amma duk idan na ganshi ji nake kamar in kama gemun shege in tsistsinka shi,...." ƙyalƙyalewa da dariya Benazir tayi jin abun da Anila tace.


"ni wallahi abun dayafi damuna Su zahra, yara masu kirki sai dai kash ba su yi dacen uba ba.."


"Hmm ke dai bari, Idan suka san mugun abun da fasikin ubansu ke aikatawa ay wlh sai sun kusa zaucewa..." Benazir ce ta fada can kuma tace


"Anila, kin tuna abun da Dj ya gargademu akai? Ki daina daga murya kada wani ya ji yo ki, Ina fata ke kaɗaice a dakin nan don na ji kamar motsin wani a cikin kunne na.." 


Zaro idanu Anila tayi cike da fargaba, can kuma ta saki dariya"wlh kin tsoratar dani, har kinsa gabana ya faɗi, idan Uncle dan iya ya kamani ina yin wayar wlh na mutu"


 dariya Benazir tayi"yaya shureim yana kira na sai anjima zamuyi magana.." 


sallama su ka yi, fuskarta ɗauke da murmushi ta ɗaura wayar saman mirror tare da sauke ajiyar zuciya, ta ɗan lumshe idanunta, kwatsam ta tsinkayi motsin mutum adakin ta, tayi azan junaid ne hakan yasa ta furta "my baby boy, ina ka shiga na farka daga bacci bangan ka a kusa ba"? 


Ta faɗa ba tare data buɗe idanunta ba, ga kuma motsin yana cigaba da tunkarota.


"Babyn mommy ka yi min magana mana, nayi missing dinka, zo nan kusa da ni..." 


ta faɗa tana miƙa hannunta.


shiru taji ba'a tanka mata ba, In har junaid ne tasan bazai ta6a share ta ba, tunawa tayi da maganar Benazir 


_ina fata ke kadaice a dakin nan don naji kamar motsin wani_



Cikin sauri ta buɗe idanunta kaitsaye suka sauka acikin na shi ta cikin madubi, wata irin zabura tayi kamar wadda taga dodo, ta zazzare idanun ta cike da tashin hankali, kwata kwata bata tsammaci zata ga mutun adakin ba, me ya kawo shi dakin ta?  abun da take ma fargaba kada ace yaji wayar da tayi da Benazir, kirjinta kamar ana luguden ta6are, da wata irin faduwar gaba ta zabura jikinta na kerma ta miƙe tsaye tana ƙare masa kallo daga ƙasa har sama ta cikin madubin batare data waiwayo ta fuskance shi ba.



Yana a  tsaye ya ruke qugunsa da hannunsa na dama, yar shara da gajeran wando ne a jikin shi, kwata kwata fuskarsa ba walwala ko miskala zarratin, fuskarsa sai naso take ga wani uban shade fari daya ƙwama a idanun shi ya sauko har ta kan karan bajajjen hancin shi, uban goshin nan nashi kamar jirgi yayi asubanci, bakomai ne akan fuskarsa ba face tashin hankali da ruɗanin abun da bai ta6a zata ba... 


Kafin kace me daga shi har Anila tuni wani azababben gumi ya tsatsafo ta saman goshin su.


aranta ta ayyana Na shiga Uku, Wayyo Allahna, La'ila ha illa anta subhanaka inni kuntu munazzalim, wa'inna hu min sulaiman wa innasu bismillah....


duk tabi ta rude ta rikice duk wata addu'a data zo mata arai cikin hanzari take ambaton ta.


Har murza idanunta tayi don taga ko gizau ya ke yi mata amma koda ta gama goge idanun still babu abunda ya canza.


Cikin rawar murya ya furta"babu abun da zaki 6oye min Anila, Naji komai da kika faɗa a cikin wayarki, inaso ki faɗa min wani video ne na ana kuka gani? A ina kuka gansa? Naji kuma kin ambaci kin kosa su gama bincike su zo su kama ni su wanene? Me kuma nayiwa Ana da naji kina fada mata"? Ya jefa mata tambayoyin a jere..


zazzare idanu tayi tare da haɗiyar yawu ba tare data iya furta kalma ba, jin ta share shi yasa shi daka mata tsawar data razanar da ita a ruɗe ta furta"Inna lillahi wa'inna ilaihirraji'un, Uncle wayar da kaji inayi ba dakai nakeyi ba, firar wani drama muke yi watakil kunnuwanka ne suka jiyo maka badaidai ba..." 


bata ƙare maganar ba ya katse ta da cewa"Karya kikeyi Anila, ko dai ki fada min gaskiya ko kuma inyi maki abun da baki ta6a zata ba..." 


afusace ta juyo ta fuskance shi idanunta suka shiga cikin nashi, duk da shakkarshi da takeji hakan bai hana ta furta"ai ba tsoronka nake ji ba, maganar girma ta kare Uncle, mutuncinka ya zube kasa wanwar, wayar da ka ji inayi dagaske ne, nasan komai Uncle, kar nake kallonka, Allah ya tonu asirinka, Naga komai da idanuna balle kace zaka karyata magana ta, wallahi kasan Inda Ana take kawai ka fadamin Ina ka 6oye ta Idan ba haka ba hmmm" 


babu alamun ya fahimci inda zancenta Ya dosa sai ma ruɗu daya mamaye zuciyarshi cike da tashin hankali Yace"wannan wani irin zancen banza ne Anila? Kina hauka ne? Meya haɗina da Ana? Kin bani ajiyarta ne da zaki tuhume ni akan 6atanta, anya kina a cikin hayyacin ki kuwa, Ko kin fara shaye shaye ne"?


"Ɗan Iya ba shaye shaye nayi ba, Ina Cikin hayyacina, Idan ma akwai wanda ya fara shaye shayen to kaine mutumin banza, mai fuska biyu..."waro idanu waje yayi cikin rudu ya ke kallon ta.


Dakyar yayi karfin halin furta"Har ni zakiyiwa kazafi Anila? Saboda tsabar rashin kunya da ta6ara ki kalli tsabar idanuna ki gaggayamin magana batare da jin shakkata ba? Wani video ne kike ikirari akai"? ta fahimci yafi damuwa dayasan videon menene suke magana akai.



Harara ta watsa mashi kafin tace"videon komai daka aikatawa Ana, kawai ka fada min Ina Ana take? Tana araye ne ko ka kashe ta"? 


aruɗe ya daura hannu saman kan shi ya shafo Sanƙon kanshi tare da jan gemun shi yana faman zare idanunshi kamar na kwarton mazuru.


tsantsar al'ajabi ne akan fuskar shi, tayaya akai har Anila ta samu videon abun da yake aikatawa ana? Tayaya? Anya ba burga ta ke yi masa ba? A sanin shi babu cctv a gidansa.



"Ashe tun bayan da muka dawo gidan nan kake lalata da ana aduk lokacin da takeyin jinin Al'ada, kana amfani da sihirinka ka gusar mata da hankalin ta, sa'ilin da ta gane Allah ya fahimtar da ita komai tace zata tona maka asiri shine ka fara neman hanyar da zaka kawar da ita gudun kada ta jaza maka matsala"


bata ƙare maganar ba sakamakon tsawar da Uncle ɗan Iya ya daka mata wadda tayi silar faduwar gaban ta.


Idanunsa sun kaɗa jawur kamar garwashin wuta, Uban goshin nan nashi sai naso yakeyi ya hada gumi kamar ba A.c adakin..


a hankali Ya cire glass din dake akan idanunsa Ya jefar da shi ƙasa, tare da sanya tafin hannunsa ya shafo ƙeyarsa har izuwa rantalin sa, gaba daya kansa ya ruɗe Anila ta rikita ƙwaƙwalwarsa..



Dakyar ya shanye mamakin shi ya furta"Anila zaki tabka babban kuskure na zargina batare da kina da ƙwaƙƙwarar hujja ba, Ni fa Uncle dinki ne kinsan wanene ni kinsan halina bansan wani shaidani bane Ya yi maki hudubar da har kika gasgata maganar shi ba,  Ni bazan iya aikata rashin imanin nan ba, Ƙazafi ne kawai ake nema ay min..." bai ƙare maganar ba Anila tayi wata irin dariyar takaici


 

"Bayan kasancewarka Matsafi, Fasiƙi kai ɗin babban makaryaci ne...." ta faɗa cikin fusatacciyar murya tare da nuna masa kofar dakin da yatsan ta.


"ka fuce min daga ɗakina, Bana son ganin ka.."


"Ba zan fita ba Anila, ki zauna muyi magana ta fahimta, kada ki manta ni Uncle dinki ne, duk inda za'aje adawo, dole ki amsa min amsoshin tambayoyin da nayi maki! Wani video ne Ana tayi? A ina kika same shi, ke kika dauke shi da kanki ko kuwa itace ta bar abunda ta dauki videon, sannan bayan ke su wanene suka ka kalli videon.." bai kare maganar ba, ta zare mashi idanunta da suka kaɗa jawur cike da tsanar shi ta furta"bazan faɗa ba, Ka jira ka gani, wallahi dole ka girbi abunda ka shuka, har kana wani fadin kai uncle dina ne, to ai ko ubanane ya aikata abunda kayi wlh saina damƙa shi ga hukuma ta hukunta shi, balle kai karen kaɗa miya, karere a danginsu Abie, ai nasan komai, baku da wata alaƙa ta jini, tsintarka su kayi, wallahi jinin abie ɗina bazai ta6a aikata fasikanci da ka aikata ba..."


 maganar Anila ta fusata shi, har baisan sa'adda Ya cije gefen tafin hannunsa ba.


"Cikin lalama ka fita kabar dakin nan, Idan ba haka ba zanyi maka ihun da kowa na gidan nan zai ji, Kuma idan suka tambayeni meke faruwa zan fada musu abun da ka aikata ne..." 


harara ya watsa mata, ya juya ransa a 6ace Ya nufi kofar fita daga ɗakin, har ya daga kafa zai fuce sai kuma ya fasa ya tsaya cak, kwakwalwarsa na tariyo masa abun daya faru.


cike da takaici Ya daki jikin ƙofar, evil heart dinsa ta motsa ji yayi bazai iya ƙyale ta ba, tun da har tasan sirrinsa kuma ga dukkan alamu ta kai shi ƙara gurin hukuma, kwara kawai ya aikata abun daya dace.


Anila dake a tsaye tana kallon sa, wani irin faduwar gaba taji, ganin ya datse ƙofar dakinta, murya na rawa ta furta"me.. me.. me zakayi min..? Ba zaka fita ka bar min ɗakina ba? Wallahi zan yi maka ihu.. "


"kada ka kuskura ka tabani, bani kadai na kalli videon ba, zan iya rufa maka asiri amma idan ka cutar dani asirinka zai tonu kowa ya sani..."


 jikinta na karkarwa ta soma laluban makamin da zata kwaɗe shi da shi.


juyowa yayi yana huci kamar mayunwacin zaki ya durfafe ta, har wani gurnani ya ke fitarwa kamar mazuru.


Da kakkausar murya yace"kinjama kanki bala'e da masifa Anila, tun da har kika shiga gona ta, bazan ƙyale ki ba, zanyi maki abun na ke yi wa Ana sannan In kashe ki, In kuma binne gawarki a cikin ɗakin nan! Su kuma wadanda kika turawa videon suka gani zan gano su ne daya bayan daya in kashe su..."


 hankalinta idan yai dubu to ya tashi, duk tabi ta rude ta razana, sai faman girgiza kanta takeyi kamar yar kadangaruwa, sai zagaye dakin sukeyi taki bari ya damke ta, gaban mirror ta nufa takai hanninta da ke kerma ta rarumi kwalaben turarurrukanta ta dinga jifar shi da su ko gizau baiyi ba,..


"Kada ka matso kusa dani, kada ka ta6ani Uncle, zakayi danasani...."


 ta faɗa tana zare mashi idanun ta cikin tsoro


har ta kware baki da niyar ta fasa ihu don mutanan gidan suji, sai dai kash bata kaiga yin hakan ba,  ɗan iya yayi kukan kura Ya damƙi keyarta da hannu ɗaya, yakai ɗayan hannun saman bakinta ya toshe shi, Ƙyanƙyami da ƙyamar shi ne ya kama ta, Idanunta suka kaɗa jawur, tadinga kokarin kwace kanta daga rukan da yayi mata ta kasa, tafin hannunsa daya toshe bakinta da shi ta dinga cizo hadi da yakushin shi da akaifunta, amma yaki ya sake ta, tana jiyo knocking daga wajen dakin kamar tayi hauka saboda ta kasa iya furta kalma..



Luxury-incense By Sapnah Borno.

Ta kawo muku turarukan wutan su Na maiduguri dana chad, turarukanta masu masifar dadi da kama waje harma da daukar hankali, indai kikayi kabbasa da turaren ta har wajen da kika zauna indai kika tashi sai kin bar kamshin ki, sannan Tana saida mayukan gashi irin nasu na shuwa Arab masu tasirin gaske, wajen gyaran Amare kuwa babu magana dan tazo muku da Chadian and Sudanese dilka Wanda zaki gyara jikinki da kanki, oga ya kasa ganeki, haka zalika akwai wata humrar ta mai suna hana bacci da kuma sirrin shuwa Abun ba magana, yar uwata ki jarraba turaren yar mutan borno nasan zata zame miki best turaren wuta plug. Tanada turarukan da zaki turara gida, toilet, bedsheets, curtains, kabbasa and hair incense ku jarraba kada ku bari ayi babu ku.

Wardrobe balls

Kabbasa spray

Chadian khumra

Hawee

Halud 

Gabgab 

Sandal sukkariya

Kajinguru 

Dilka soap

Ready to use dilka

Karkar oil

Turaren tsuguno 

Habil

Dorut 

Dorot after period 

Brown khumra

Dufr khumra

Body milk

Sudanese kuleccam

Chadian dufr kuleccam

Musk khumrah.


Maganin matan mu sunada inganci Wanda muke kawo su daga sudan, sannan munada maganin karin girman nono, Wanda basuda effects, ga masu bukatar maganin Matsi ko maganin mata Masu aiki garanti munada su, sannan muna zuwa gyaran jikin amarya a duk garin da take


Our Chadian aphrodisiacs are.

Beejay fire

Sata jagab honey 

Wetness and sweetness combo

Daka

Great A sabaya 

Breast engagement powder 

Ciccibi 

Gumbar madara 

Gumbar dabino 

Bita Zaizai 


08093772168



*Welcome, Littafin kurkukun ƙaddara 500 ne, dukanshi Book One two and 3 Idan kin shirya biya ga Details da zaki tura*


3196407426 


First bank 


Bature Hafsat Muhammad,


 *bayan kin tura zaki bada transaction reciept ko screenshot na debit alert a matsayin shaida ta wannan number din 08103884440*

Post a Comment

Idan kuna da tambaya akan abinda Baku game ba ko kuma kuma Neman littafin da babu a nan kawai ku ajiye tambayarku a ta comment ko wani shawara da Zaku bamu.

Previous Post Next Post

Sponsored Link

Sponsored Post