Kurkukun Ƙaddara Takun Ƙarshe Page 78 Complete

Kurkukun Ƙaddara Takun Ƙarshe Page 78 Complete

Takun Ƙarshe

UMMIN AMERICA

Motar su tana karya kwana kan titi, wata dankareriyar Mota zungureriya baƙa mai black tunted ta nufo su gadan gadan tasha gaban su, cikin sauri officer din da ke driving din ta Ya taka burki ƙiiii!!!  motar ta bada sauti tare da tsayawa.

Ummi da ke a zaune cikin backseat na motar, kwata kwata babu alamun damuwa akan fuskarta, ta riga da tasan Big boss ne ya turo a ɗauke.

"Kada ka damu, shine ya turo a dauke ni, zan tafi, idan zan dawo zan kira ka, nagode" ta faɗa yayin da ta ke ƙoƙarin Buɗe cardoor din.

Agent din yace"baki da damuwa ma'am, Ki kula da kan ki" 


"Thanks" ta furta.


Ƙarasa fitowa tayi daga cikin motar, ta tsaya tana ƙarewa dankareriyar Motar nan Kallo, babu alamun na cikin ta zai fito, kwata kwata ba'a iya ganin wanda ke a ciki.


A cikin kunnanta tajiyo tashin motar officer din da ya sauke ta, kamar jira suke motar tabar titin Unexpected Cardoor na backseat din Motar ya soma sliding slowly har ya buɗe gaba ɗaya


Da wata irin tafiya ta jan hankali da dattako Ummi ta nufi Motar, tana ƙarasawa gaban cardoor din ta ɗan russina tare da leƙa cikin ta, har saida ta lumshe idanunta saboda yadda shu'umin kamshin turaren sa da Sanyin A.c din motar suka ratsa hancin ta, A hankali ta buɗe idanun ta akan shi, Yana a zaune ya hakimce cikin backseat din motar, sanye da tailored suit, rabin fuskarsa a rufe ya ke da gold mask, sumar kan nan tashi ya yi wani ɗan iskan hair cut irin na tantiran da suka kai matakin masters atashanci.

Ya ɗaura kafarsa ɗaya bisa daya, kamar wani basarake asaman karagarsa haka ya zauna, daga gefensa Console table ne mai dauke da Drinks, tsabar haduwar motar sai ka rantse da Allah dakin wani basaraken ne.

Bai tanka mata ba, kamar baisan da zamanta ba, a hankali ta shiga daga ciki ta zauna, Cardoor din tayi locking, daga inda take ko drivern da ke driving dinsu bata iya gani saboda curtain din daya shiga tsakanin backseat da front seat na motar, kamar yadda ya share ta haka itama ta share shi, jira take ya sauke girman kan shi da izzar tukunnna sai suyi magana..

Kasa jurewa yayi saboda kasalar da kamshin turaren ta ya haifar ma shi, satar kallon ta yayi ta wutsiyar idanun shi, tun daga kan head scarf da tayi rolling har zuwa wuyanta dake sanye da ziririyar sarƙa, mayar da idanun sa yayi kan kirjin ta wani mayataccen kallo yabisu da shi kamar zai kai mata hari, fitted gown din da ta sanya kamar a jikinta aka dinka ta saboda yadda tayi tighting inta ta fito da shape din jikin ta, sauke idanunsa yayi akan dirarran Qugunta daya cika fam kamar zai daɗe.


Ya dan jima yana ƙare mata kallo kafin ya kawar da idanunsa gefe ɗaya, kwata kwata bata nuna tasan yana kallon ta ba, da gangan ta yi banza da shi, wayar ta ta curo daga cikin Purse ta Soma dannata a hankali..


Komai nata da yanga takeyin shi wanda hakan ba karamin jan hankalin shi ya ke yi ba.


Ya daɗe yana tunanin meyasa baya gaji da ita? yana sonta fiye da kowace mace a duniyar nan, baya jin zai iya rabuwa da ita, shiyasa yake takaicin gaza mallakarta da baiyi, duk da a yanzun ma yana samun abunda ya ke so agurinta hakan bai ishe shi ba, yafi so ta zama mallakinsa, matarsa, uwar ya'yansa, sai dai kash ta nan Allah ya rage shi da ita, yasha fada mata in har bai aureta ba, babu wani mahalukin da ya isa ya aure ta, sai dai ta mutu ba aure, bazai ta6a barin wani ya mallake ta ba, in ba shi ba.

A hankali hamshakiyar Motar ta kunno kai Cikin wani katafaren Gate na wani tanƙameman Villa, Aljannar duniya, me karfin imani ne kadai zai iya rayuwa acikin sa batare daya shagala da yin ibada ba, saboda an zuba kayan alatu, an kuma yi almubazzarancin dukiya gurin ƙera ginin,  ga wasu Giant Security Officers dake sintiri sanye cikin kakin su mai kama da na Jami'an Isod.

Har Motar tasu tayi parking daga gefen Entry Hall bata juyo ta dube shi ba, A hankali Cardoors din motar suka zamiye, ta fito daga ciki, ta ɗan tsaya tana gyaggyara veil din ta, gently ya fito daga motar ya zagayo ta bayanta ya dan jingina bayansa jikin motar ya harɗe hannayensa akan kirjinsa..


"Jira kike inyi maki magana"? Sai da ta mula ta sha iska, ta juya ta dube shi tare da ɗage gira tace"gashi kuma kayi min maganar, saboda ka damu dani, ka gaza jure ƙishin dake damun ka"


tana ƙarashe magabar, ta juya ta nufi katafaren main door din falo.


smirking yayi tare da bin bayanta yana kallon yadda take tafiya butt dinta na jujjuyawa aransa ya furta


_"ita kaɗai ce macen da zata iya juya ni son ranta..."_




tana isowa bakin Kofar, ta daura babban yatsanta akan finger print din kofar, bayan computer tayi scanning dinta nan take kofar ta bude, tana shiga ciki, ta tsinkayi Ai assistant's voice a cikin kunnanta 



_"welcome Ummi, the lights, and temperature have been adjusted for your comfort"_


 

Murmushi tayi da alama taji dadin hakan sosai, komai na furniture din falon masu kyau da tsadane, a hankali ta nufi cikin falon tana tafiya sautin takunta Yana fita kwas kwas.


 Tsayawa tayi daga tsaye tana bin ko'ina da kallo da alama Falon Ya burgeta.


batai aune ba taji ya damƙi hips dinta da faffadan tafin hannun sa, sai taji wani iri kamar bataji dadi.



kwanto da kansa yayi saman wuyanta cikin wani irin salo na jan hankali ya dinga goga tsinin hancinsa akan wuyanta tana jin hucin numfashinsa, da sauri da sauri yake fita kamar zai rasa ransa sai faman kara narke mata ya ke yi, ta fahimci jarabarsa ce ta fara motsawa.



tana a tsaye tana jin duk wani  motsinsa a jikinta, bata san ya akai ta daina jin sha'awar son kasancewa da shi ba, gangar jikinta ce kadai a tare da shi amma ruhinta yana atare da ya shureim.


duk ta6awar da big boss zaiyi mata sai ta dinga jin kamar shureim ne, shiyasa har ta ɗan saki jiki tabar shi saboda yanayin shaukin da ta shiga, bakomai take tunanowa ba face lokaci na farko da ta fara kasancewa da ya shureim dinta, duk da radadin da taji hakan bai hanata jin ni'imar dake a tare da shi ba, har yau bata samu namijin da ya yi satisfying din ta kamar yayi ba.


yana kokarin 6alle zip din rigarta, kwatsam brain dinta ta soma tariyo mata maganganun da suka tattauna da Chief Owais, lokaci ɗaya ta yi saurin buge hannayen big boss daga jikin ta, ta ja baya tana haki tare da juyowa ta fuskance shi.


 walwalar fuskarsa ce ta ɗauke ɗuff, rudani ya bayyana akan fuskarsa.


"Meke damunki ne? gaba daya kin canza min Ummi, ba haka kika saba min ba, kina ji ina ta6aki amma baki wani nuna kinji dadin abunda nake maki ba, yanzu kuma kin buge hannayena kamar wani mugun abu ya taba ki why"? Ya faɗa cikin bacin rai.


tunawa da gargadin da Chief yayi mata ne yasa tayi saurin shiga tai tayinta, shafa cikinta tayi da tafin hannunta tare da yamutsa fuska tace"yunwa nake ji, banci komai ba na tafo saboda zumudin naganka, nafi so mu ci atare..." 


ta faɗa tare da matsawa kusa da shi ta ɗaura hannayenta saman shoulders dinsa.


Lumshe idanun shi yayi, hancinsa na shaƙar mashi shu'umin turarenta, gaba dayansa acikin shauƙinta ya ke,


"Get lunch ready for my babe, within minutes" 


ya furta yana kallon ta, daga inda yake bai motsa ba, bai kuma kira kowa ba yayi maganar, da ya ke computer ce ke isar da sakon.



Tallabo waist dinta yayi da tafin hannuna suka nufi Dining, tunkan su karasa ta hango kitchen staff sanye da uniform dinsu sun kewaye katafaren Dining table din da suke jera kayan abinci akan shi, suna ƙarasowa chefs din suka gaishe da ita with respect, kafin suka juya tare da barin gurin.


Har zata zauna sai kuma ta fasa tunawa da ba haka suka saba cin abinci ba, zai iya zargin wani abu idan ta canza mashi.


Zagayawa tayi ta gefen da yake a zaune ta shafo shoulder din shi da ziraran yatsunta kafin slowly ta zauna saman laps dinsa, har wani lumshe idanun shi ya ke yi




kwantar da kanta tayi saman shoulder dinshi  cikin kashe murya ta furta"babe ka bani abaki naci.."


 ta fada tare da tallabo keyarsa ta shafa ta a hankali tana dan liliyata har iyazuwa sumar kan shi, daurewa kawai yakeyi amma gaba daya ummi ta tayar masa da jarabarsa, tasan duk wani salo da zata gigita gogan nata.


Abaki ya fara ciyar da ita, cikin abinci kala shida da aka jera mata abu ɗaya taci ta dan sha juice kadan, ta dauki spoon da niyar ta bashi baki yai sauri damƙar hannun ta duban shi tayi"ba zaka ci ba"?


"Yunwar da nake ji abinci bazai iya gamsar dani ba ummi.. "


 ya faɗa tare da tallabe butt dinta da hannayensa Ya miƙe ɗauke da ita, duk nauyin jikin Ummi baya jin shi, bedroom dinsa ya nufa da ita gabanta sai faɗuwa ya ke yi, batasan ya zatayi ba, wallahi bata so wani abu ya kara shiga tsakaninta da Uncle Musa, saboda tana jin tsoran zargin da su Chief su ke yi akan shi ya zamana gaskiya, da kuwa ya kashe ta da bakin ciki, wannan karon ba zata bari ya kusance ta ba, dole ta nema ma kanta mafita aranta take ta yin tufka da warwara.



Wani katafaren bedroom ya shiga da ita, alkalamina bazai iya misalta haduwar shi ba, agaban hamshakin gadonsa Ya jefar da ummi ta lumbutse cikin lallausar bedmattress din, har saida headscarf din ta ya warware, gyaran gashin kanta ya bayyana.


 numfashi taja tare da dagowa tana kallon shi yayin da yake a tsaye gaban gadon yana tu6e suit jacket dinsa.


Jefar da kayan jikin sa yayi, ya rage saura short, kamar mayunwacin zaki ya fada kan gadon, for the first time da ta fara jin shakkar Uncle Musa, Yana matsowa tana ja da baya, har saida suka ƙurewa gadon yadda kasan muzuru ya kama 6eta, ta zazzare idanunta cikin tsoro.


Muryarsa tamkar ta wanda ya sha giya ya furta"ummi, tsoro na kike ji? Meyasa kike ja da baya kamar kinga dodo..." 


murmushin yaƙe tayi"ba abun da ka ke tunani bane, ka yi hakuri bana son na bata maka rai shiyasa ban faɗa maka ba, amma bazan iya kwanciya dakai ba.." 


ta faɗa idanunta a cikin na shi, still bai cire gold mask din shi ba.


"Meyasa"?



"Sorry, I'm having my cycle" ta fada cike da fargaban kar yaƙi yarda.


6acin rai ne ya bayyana acikin idanunsa, ya tsani yaji tana period saboda baya samun abun da ya ke so a gurin ta.


"Ummi meyasa baki fadamin ba tun kafin kizo? Sai da kika tada min jaraba na sannan zaki fadamin labarin nan mara dadin ji"? In a weak voice ya fada..


"Am sorry big boss, nima bada son raina ba, ban san ya akai date din da yake zuwa min ya sauyawa ba, sai da na shiga toilet zanyi wanka kwatsam naga jinin...." ta fada tana marairai ce masa fuska.


"Kuma kaga yau ne kaɗai na samu damar da zanzo.. "


sanyayyar muryarta nema take ta zautar da kunnuwansa da dadinta..


"Ummi akwai hanyoyi da zaki iya gamsar dani, ba dole saina shige ki ba, bazan iya hakura ba..."


 zare idanunta tayi tana

Ƙyafƙyaftasu akan fuskarsa.


ya kashe mata ido tare da ɗage girarsa daya.


yana kokarin kai hannu don ya damƙe ta ta yi sauri kubce mashi ta sauko daga kan gadon, arude yabita da kallo da alama ya fara ɗago ta..



"Giya nake so na sha" da mamaki yace"yaushe kika fara shan giya" ya fada tare da kishingiɗe kansa saman pillow.




"Yau zan fara, saboda inaso na bugu na manta kaina"


 wata yar iskar dariya ya saki tare da saukowa daga kan gadon ya nufi wine cabinet din dakinsa Ya dauko bottle ɗaya tare da cup daya, ya dawo gaban gadon Ya zauna tare da tsiyaya mata a cup ya miƙa mata yana faɗin "ki komo kan gadon ki zauna kada ki faɗi"


 komawa tayi gefen gadon ta zauna har zata kai baki ta dan dakata tare da kallon shi ya tsareta da idanunshi da suka kada jawur tarasa gane kallon menene ya ke yi mata .


"Kai ba zaka sha ba.." girgiza mata kai yayi"no, ke dai ki sha.." maƙe kafada tayi"in har ba zaka sha ba, nima bazan sha ba"


 smirking yayi tare da kai kwalbar abakinsa Ya soma ɗaɗɗakarta har saida ya shanye giyar duka.


sannan ya janye kwallar daga kan bakinsa ya daura ta kan bedside drawer, girgiza kanshi yayi yana faman jan numfashi, da alama giyar ta fara bugar da shi, idanunsa na kokarin lumshewa ya dube ta"ki sha"


 kaiwa tayi saitin bakin ta, ta kur6a batare data hadiyeta ba, batai aune ba taji ya janyota jikin shi ba arziƙi ta saki cup din hannun ta.


hugging dinta yayi ya soma undressing din ta, tana ta kokarin kubce mashi takasa saboda karfin daya sa mata, sai da rage daga ita sai pant da bra, sannan ya ƙyaleta, ya janyo duvet cikin maye ya rufa musu, ya zuro hannunsa daga cikin dubet din ya danna wani button jikin gadonsa nan take duhu ya mamaye dakin, romancing dinta ya farayi kamar zai haukatar da ita, short dinsa daya cire ya cillo shi wajen bargon.


gurnanin shi da nishin shi ya cika dakin kamar zai fasa dodon kunnanta, kamar zata fasa ihu saboda kyama da kyankyamin daya kamata tarasa ya akai bata jin dadin hada jikinta da nashi ba kamar da ba, komai da yakeyi mata baya mata dadi yanzu, ta bashi giya don ta gusar mashi da hankalin shi, amma kamar giyar bata aiki akan shi, kokari ya ke ya shige ta, data turje ya yi forcing dinta akan tayi ma shi abun dayake so, duk fa yana a cikin mayen na shi, addu'oi ta dinga karantowa acikin zuciyarta tana rokon Allah yasa bacci ya dauke shi, cikin sa'a giyar dayasha ta ƙarasa bugar da shi, ya dinga sambatu na batsa marasa dadin ji har saida bacci yayi awon gaba da shi.


Kasa mikewa tayi saboda ya matseta a kirjin shi, motsi kadan idan tayi zai iya farkawa in har ba baccin nasa yayi nisa ba, hakan yasa ta jinkirta tashin nata, har batasan sa'adda bacci yayi awon gaba da ita ba






~________HeartBeat🫀Destiny💫____~





A hankali ta fito daga toilet jikin ta sanye da bathrobe ga dukkan alamu wanka tayi duba da danshin ruwan dake a jikin ta, unexpected ta tsinkayi shesshekar kukan Unaisah a cikin kunnanta, gabantane Ya faɗi, da sauri ta nufi couch din da take a kwance ta kudundune jikin ta cikin bargo sai kerma ta ke yi..


"Ukhty! sisterna! Meke damunki ne? meyasa kike ku ka um?  Ta faɗa cikin nuna kulawa tare da zama gefen ta..


Shiru tayi bata tanka mata ba, bubbuga kafadarta Batool tayi"kina jina kinyi shiru ba zaki fada min abun da ke damun ki ba"?



Cikin shesshekar Kuka tace"dan Allah ki rabu dani inji da abun da ke damuna"!


"Unaisah, please Ki fadamin zan taimaka maki mu nemi mafita".


Wannan karan da tsawa ta furta"nace ki rabu dani! Ko da na fada maki babu abun da zaki iyayi min"! 


mikewa ta yi sukuku ta juya ta nufi toilet harta kusa isa ta dan dakata"bansan meyasa kike yi min haka ba, kawai daga tambaya sai ki rufeni da faɗa hada tsawa"? Ta faɗa cikin 6acin rai cos taji haushin tsawar da Unaisah ta yi mata.



"Kawai saboda na nuna damuwa akanki? Batun yau kike min haka ba, duk in zanganki awani hali na tambayeki meke damunki baki faɗamin! Na sha farkawa tsakar dare in ganki kan darduma kina kuka, amma baki ta6a fadamin abunda ke damun ki ba why? Me kika ɗauke ni ne?wani sa'in kamar kina min kallon mara wayau, saboda bani da ilmi yasa kika raina ni Unaisah, Nafa girmeki, shekara biyu da watanni na baki! Ni ba tsararki bace! yakamata kina girmamani amma meyasa ki ke min haka"? 



Ta ƙarashe maganar tare da juyowa ta dubeta da idanunta wadanda suka cuko da kwalla..


Unaisah data yaye bargonta fuskarta sha6a sha6a da hawaye, Kasa furta kalma tayi saboda bata tsammaci Batool zata iya mayar mata da martani ba, ashe abun na damunta, amma saboda tana da hakuri yasa ta ke dannewa ayanzu kuma taji bazata iya ba.



"Baki ɗauke ni kamar yadda na dauke ki ba, na tabbata da ace ina da ilmi ba zaki ta6a yi min haka ba, a tunanina damuwarki tawa ce! Babu sirri a tsakanin mu"


jikinta ne yayi sanyi lakwas, duk sai taji ba dadi saboda maganar da Batool ta faɗa gaskiya ne.



"Na tsani in tambaye ki meke damunki ki ce min baki sani ba, ko ki nemi raina min hankali, sometimes kin kwammace kiyi shawara da aunty ummi akan ki yi dani, ni kuma burina kullum in fi kowa kusanci dake, in fada maki damuwata, in nemi shawararki, amma ke ba haka ba.." 



juyawa tayi da gudu ta shige toilet taja kofa ta datse, bata ta6a ganin Batool a hali na 6acin rai irin na yau ba, kamar mai aljanu.



Saukowa tayi daga kan kujerar ta nufi Toilet door tare da yin knocking, tana jiyo shesshekar kukan ta"Batool ki yi hakuri bansan abun yana bata maki rai ba, bansan nayi maki badaidai ba sai da kika fada min, tabbas nayi kuskure amma inaso ki sani wallahi ba abunda kike tunani bane, kada ki bari shaidan da zuciya su shiga tsakanin mu, Batool ban raina ki ba, wallahi bana maki kallon mara ilmi, ni da nake kokarin inga kun samu ilmi kun waye Batool? Ni ce fa Unaisah me son cigaban ku da farin cikin ku.."? 


Dakyar ta ƙare maganar saboda kukan daya su6uce mata, abun ya ta6a ta, abun ka ga mai zuciya.



"Meyasa kike tunanin haka Batool? Kin bata mun raina, meyasa zaki bar abu yana cinki a zuciya baki sanar dani ba? Kin ƙullace ni aranki, ba halinki bane Batool, kamar yadda kike burin ki fi kowa kusanci da ni nima haka nake buri Batool, inasonki fiye da sauran yan uwan mu, saboda halaccin da kikayi min arayuwa bazan ta6a mantawa ba, dan Allah ki buɗe mun kofa, inason yin magana dake, zan fada maki abun da kikeson ji sannan ki daina kuka bana jin dadi." 


ta faɗa cikin shesshekar Kuka, Kamar marasa galihu sun dage sai kuka su ke yi.


"Ba zaki fito ba? Kuma ki daina kuka acikin toilet babu kyau"


"Ki ƙyaleni, bazan fito ba, saboda kona fito babu amfanin da zanyi maki" bubbuga kofar Tayi kamar zata balle ta tace"ki daina wannan maganar Batool bana son ji"!


"Naje nayi ay gaskiya na fada.." ji take kamar ba Batool dinta ba, ta burkice mata lokaci ɗaya..


"Ki yi mun ko wani irin hukunci zakiyi min in har hakan zaisa ki huce, Ko ki fada min me zanyi in gyara kuskure na"? Ta fada tare da jogana kunnanta jikin kofar..


Sai da ta mula ta sha iska tukunna tace"kin makaro Unaisah, sai da na fada sannan zaki gyara? Hmmm, kawai ki rabu da ni, ko ganinki bana son yi"


"Bazan iya rabuwa dake ba,  bana jin dadin maganarki, Batool jinki nake kamar twin sister dina.."


"Daɗin bakin ki bazaisa in hakura ba" murmushi Unaisah tayi still da hawaye akan fuskarta"ba daɗin baki nake maki ba, wallahi dagaske nake maki my heartbeat, Ki fito in nuna maki irin kaunar da nake maki"


 banza tayi da ita, tunani ta shiga yi meya kamata tayi don ta shawo kanta? da sauri ta nufi wadrobe Shelves inda ta ajiye sauran kayan da suka siyo a shopping mall, Batool ta dade tana kwakwar ta bata wayar nan taki bata a lokacin saboda ta raba gaddama tsakaninta da sajeed da shima ya kwallafa rai akan wayar, sai yau da take son faranta mata.


Phone box din ta ruke a hannunta ta dawo bakin toilet door din"Ukhty na, come and see something special"


 banza tayi da ita, magiya ta dinga yi mata amma tayi shiru, still batayi fushi ba, saboda ta fahimci halin da yar uwar tata take a ciki, tasan Batool tana da hakuri baiwar Allah.


a lokacin Batool tana a zukunne gaban kofar toilet din ta ciki ta jingina bayanta, kunnuwanta suka jiyo mata sautin wakar da Unaisah ta ke raira mata daga cikin dakin.


_Ƙawata kina jina? In har kika barni sai na sha wuya_


_Sai na zam tamkar tsokar da babu jijiya_


_In ba dake ba sai dai rijiya_


_Rijiyar ma mai dauke da ƙugiya_


_Wacce zata caki rai na, ban kara kwana_


_Mai zai sa in kwana? Ban gano masoyiya ba_


_Kece aljannata duniya ta_


_Masoyiya ta, aminiya ta_



 yayin da take sauraron wakar batasan sa'adda murmushi ya su6uce mata ba, wani sanyi taji ya ratsa zuciyarta, kamar ana wanke mata damuwarta.



"Please idan kinji dadin wakar da nayi maki, Ki fito mu fuskanci juna, Inason na ganki, wallahi har nayi missing ɗinki Batool dina, pls ki fito zan baki kyauta ta musamman, da zata faranta ranki" 


shiru tayi bata tanka mata ba, kamar zata saka ihu, Bubbuga kafafunta tayi"wai me kikeso nayi maki ne wanda zaisa ki yafe min"


_"Ki ɗauke ni kamar yadda na ɗauke ki, shi kaɗai ne zai sa ni farin ciki"_


 ta fada a cikin ran ta


"Ina ta maki magiya ki fito amma kin ƙiya, ai ko Allah muna masa laifi ya yafe mana balle mu yan adam, Kada Allah yasa ki yafe kinji ko, Ki ta zama a cikin toilet, madaddalar shaiɗanu.."


 still bata tanka mata ba, yamitsa fuska tayi tare da hararar kofar toilet din, dabara ce ta fado mata, da gudu ta fuce daga dakin tana fadin"oyoyo Aunty Ummi, welcome back home, we really missed you, Muna ta jira ki dawo har munyi fushi.." 


A zabure Batool ta mike jikinta na 6ari ta bude toilet door din, ta watso a guje ta nufi kofar tana lekowa taga wayam babu kowa nan take ta gane set up din Unaisah ne don ta fito, nan da nan walwalar fuskarta ta ɗauke duff,  kamar bata taba dariya ba, tana niyar ta fucewa daga dakin harta daga kafa Unexpected taji an damƙi wuyan kafarta, atsorace ta zare idanun ta tare da kallon ta, ajiyar zuciya ta dauke ganin Unaisah..


"Am sorry Aunty Batool, Kaina bisa wuyana, na tuba bazan ƙara ba, bansan ki da fushi ba, pls, ki tausayawa yar kanwarki Unaisah, Zan gyara kuskurena, nasan bana jin magana amma ki min uziri hada yarinta ke damuna.."


 ta karasa maganar tare da kama kunnuwanta.



Batool dake kallon ta, kiris ya rage ta fashe da dariya, saboda ta bata nishadi musamman da ta kama kunnuwanta kamar zomanya, ta wani marairaice mata fuska.


"Bai kamata ki biyemin ba, kiyi fushi dani, kefa babba ce ni kuma ƙanwarki, idan nayi badai dai ba, nasiha yakamata kiyi min sai in gyara bawai kiyi fushi dani ba.." 


idanunta cike tab da kwalla tayi maganar, ita kanta batool din wasu hawayen ne suka cika idanunta, ta rasa gane meyasa take jin Unaisah fiye da sauran yan uwanta da ta fara sani kafin ita.



Bazata iya jure fushi da ita ba, A hankali ta cire hannu ta miƙa mata, Jikin ta har kerma yakeyi gurin Zura hannunta a cikin na Batool, ta janyo ta, ta mike tsaye suka yi hugging din juna.



Lallashin juna sukayi tare da ba juna hakurin sabanin da suka samu.



"Zan fada maki abun ki ke son ji, daga yanzu babu boye boye atsakanina da ke, sirrina naki ne.."



 ta faɗa yayin da suke raba jikinsu daga juna, cheeks dinsu sunyi ja saboda kukan da suka sha.



Ruko hannun Batool tayi suka zauna kan tattausan rug din dakinsu suna fuskantar juna, batasan ya akai ta tsinci kanta da jin kunyar Batool, tayi mata ƙwarjini ko dan yau tayi gaba da gaba da ita.



Lumshe idanunta tayi a hankali


In a cool voice tace"a duk lokacin da kika ganni ina kuka, to na tuna da shi ne, wallahi shine silar halin da nake shiga! nayi iyakar ƙoƙarina dan ganin na daina tunaninsa sai dai nakasa, Ya mutu amma babu abun daya sauya na daga son da nake masa"!



Nan ta ke Batool ta gane wa take nufi.


"akwai wasu kalmomi daya furta min kafin su tafi kai farmaki sun tsaya min araina! da su nake kwana da su nake ta shi araina, nayi nayi in cire gur6ataccen tunaninsa da nake yi amma nakasa, zuciyata takasa mantawa da cewa shi fa yanzu mamaci ne ba rayayye ba, meyasa take tsananta min akan shi.." 



wasu zafafan hawaye ne suka wanke fuskarta..



Ruko hannayenta Batool tayi a cikin nata, wani irin tausayin ta ne ya mamaye zuciyarta, tayi zaton Unaisah ta daina son shi tun da baya araye ashe har yanzu da son shi sosai a cikin zuciyarta.



shiru tayi tana tariyo kalaman daya faɗa mata a cikin brain dinta, a ranar da zasu tafi kai farmaki lokacin daya yi mata raɗa a cikin kunnanta..



_Unaisaah, my desire for you burns fiercely,Taking your virginity has become my utmost dream, For what feels like an eternity, I've been tormented by my longing for you, I've concealed it for your sake, but my craving for you only intensifies_


_I'm patient, Unaisah, not wanting to rush or harm you, I yearn to make love to you with your trust, your consent, I don't mean to pressure you, I simply can't wait to be with you_


_When I return, grant me my heart's desire, Unaisah. Fulfill my wish, And let's create a memory that will last a lifetime_



 kifa kanta tayi saman kafaɗar Batool, cikin karyayyar murya ta furta"a lokacin daya furta mun kalaman nan, duk da bakomai na fahimta ba, amma naji wani bakon abu da ban ta6a jin shi ba a tare da ni..."


 ta fada tana jan numfashi, gaba daya tausayinta ya kama Batool



_"Daga baya, na zauna nayita yin nazari akan kalamansa, na yi bincike ta hanyar wayana akan abun da ban fahimta ba, har saida na gano komai dayake nufi, i was shocked, Danish da baisan komai ba, tayaya ya samu ilmi kan abun da ni bansani ba, ko Aunty ummi bakomai take fayyace mana ba, saboda tana jin kunyar mu.



 shafa bayanta Batool tayi da tafin ta"mutuwa tayi min yankan kauna, naso ace na cika mashi burin shi akaina, sai dai Allah baya barin wani dan wani yaji dadi, ina daurewa ne idan kewarshi ta addabe ni, bana bari kowa ya sani, saboda abu biyu, bana so na fama ciwon Zuciyata saboda inason na rayu ko dan na ga ƙarshen Elders, sannan bana so in ɗaga hankalin ku, gaba daya na hana kaina kallon hotunansa da vidoes din da nayi masa wasu ma batare da sanin shi ba, saboda yanayin da nake shiga idan ina kallon su, da ace idan na bishi zamu rayu a kabari daya ne da ba abun da zai hana in roki Allah ya dauki raina nima, amma bana fatan hakan saboda a duk lokacin da  na farka yin nafilfili nayi masa addu'a inajin wani dadi a cikin zuciyata"_



Lallashinta Batool ta cigaba da yi gwanin ban tausayi, a yanzu ta fahimci wasu abubuwan tanayi ne saboda ta kawar da damuwar rashin Danish.




"Yanzu da na faɗa maki sirrina sai naji kamar an yaye min damuwana, musamman da kika kwantar min da hankali, pls amana ne atsakanin mu, daga ni sai ke, kema idan akwai abunda ke damunki ki fada min.."



 murmushi suka sakar ma Juna.



"Kada ki damu, zan fada maki nima, amma ayanzu bani da wani sirri daya wuce in taimaka maki gurin ganin mun shawo kan matsalar da ke damun ki" ta fada tana shafa sumar kan ta.



sun jima suna tattaunawa, fira tayi dadi, har saida cook yayi knocking Ya sanar da su su fito su ci lunch din su tukunna suka tsagaita.


Phone box din ta dauko ta mika ma Batool, Wani uban tsallan farin ciki ta daka, hada yin sujudusshukr saboda dadin da taji, hakan ba karamin nishadi ya ba Unaisah ba, ganin ta sanyata farin ciki.


"Ki yi hakuri tuntuni Yakamata in baki ita, sai dai banyi hakan ba saboda Sajeed ya nuna yanaso yanzu da baya nan gayanan na baki, kiyi ma daddy magana ya siya maki sim"


 tana faman washe baki tace thank you sis, you're special, kin faranta min rai


 atare suka buɗe kwalin wayar, sabuwa gal da ita ƙirar Samsung galaxy,


"Nasan yau dakyar zaki Iya runtsawa" tana dariya tace "kamar kin sani"


"Kije ki sanya kaya, zan jira ki"


Ta fada tare da ruke mata wayar, da sauri ta nufi closet dinsu, shaf shaf ta zura gown a jikinta, ta dawo.


"muje muyi lunch daga nan sai mu kira yan uwan mu mu gaisa da su ko"



"Yeah" da farin ciki suka fito daga dakin.


A dining room suka taras da Cooks dake jera masu kayan lunch din su, bayan sun zauna kan kujera suna fuskantar Juna, a tsanake suka soma cin abincin su.


"Har yanzu shiru, aunty Ummi bata dawo ba, gidan duk ba dadi, babu Aunty Ummi, Chief tun safe bai dawo ba, daddy ma ya fita anguwa, sai mu kadai, nayi kewar su" Batool ce ta fada yayin da take tura Steak kebab abakinta tana taunawa.


"Idan muka kammala Cin abincin zan sake jaraba kiran su, Inji yaushe zasu dawo gida"


 Unaisah ce ta faɗa tana tsoma hannunta cikin plate din gabanta dake a shake da farfesun ganda mai zafi da tafshi, daukowa tayi tare da turawa abaki tana taunar gandar.


"Kwanakin baya kin yi min alkwarin zaki bani labarin aunty Ummi, har yanzu ban manta ba, Inaso naji..." 



dakatawa tayi da sharbar farfesun ta danyi shiru tana yanke shawara da zuciyarta, Chief ya hana ta fada amma kafin ya gargaɗeta akan kada ta faɗa ta riga tayi wa Batool alƙawarin zata bata labari, kuma tasan in har bata fada mata ba, zataji ba dadi.


Dagowa tayi suka hada ido cikin na juna, ta kura mata idanun ta..


"Ki bari mu gama cin abincin mana"


 Girgiza kai tayi"haka kullin kike kawo uzirin da zaisa ki manta, kawai ki fada min a yanzu.."


Saboda gudun 6acin ranta yasa tace "Okay, zan fada maki amma pls, amana, daga ni sai ke my sis" murmushi Batool ta saki taji dadin maganarta..


"In sha Allah.." a tsanake Unaisah ta fara labarta mata tiryan tiryan kamar yadda ta saurara a audio din da Chief ya kunna mata.


 tunkan takai karashen labarin Idanun Batool suka cicciko tab da ƙwalla cikin sanyin murya tace"sai yanzu na gane meyasa aunty ummi kuka rannan, nayi zaton ni Batool din take fadin ta rasa na mutu ashe bani bace, sunan babynta ce data rasu, na tausayawa aunty Ummi da uncle Shureim, labarinsu ya taba zuciya ta, ashe sheikh Imam ne mahaifinta amma meyasa ya yanke mata hukunci cikin fushi?


 Ta faɗa fuskarta babu walwala..




"ko dai ni da bani da ilmi bazan iya aikata abun daya aikata ba, abun daya faru tsakanin Aunty Ummi da Uncle shureim sharrin shaiɗanne, bayin kansu bane, duk da ba agabana komai ya faru ba, amma ni ina kyautata masu zato, kuma duk wata kaddara da ta faru da bawa, da akwai wata hikma ta ubangiji wanda mu ba zamu iya gani ba, kamar yadda bamu taba sanin ta arayuwar mu ba sai gashi silar taimakon mu da sojojin America su ka yi mun hadu da ita, kuma mune silar da ta dawo Nigeria harta sake haduwa da mahaifinta, da aminnanta, da kuma ya shureim.."



 muryarta na rawa ta karashe maganar, Unaisah tace"kinyi magana mai ma'ana, pls ki share hawayenki, nasan labarin akwai taba zuciya, amma ni ban fada maki donna sanyaki a damuwa ba, tsakanin mu da su aunty Ummi da babynta Addu'a ne da ita kadai zamu iya taimaka masu..." ta fada tana kur6ur juice da ta zuba a cup.



"Chief yayi alkawarin zai sasanta tsakaninta da kawayenta, da kuma Mahaifinta, in sha Allah.."


 ta karashe maganar tare da zaro tissue cikin box ta mika mata, yatsun hannayenta na kerma ta kar6a tana share hawayen ta, Unaisah dake satar kallonta, batai mamakin ganin yadda jikinta ke kerma ba saboda tasan irin kaunar da take ma aunty ummi, dole labarinta ya karya zuciyarta, shiyasa ba komai ta sanar da ita ba, ta boye mata batun Uncle musa da kuma binne jinjirar da Uncle shureim ya yi.


"Inama ace babyn aunty Ummi tana araye, da yanzu muna a tare da ita, Ni dai na kamu da son ta, Inason aunty ummi da ya shareim harma da mommynki da Aunty Anila"



 dariyar farin ciki Unaisah tayi"kuma kinsan wani abu, dana ji labarin nan sai na ji araina kamar ke ce babyn Uncle shureim saboda bala'en kama da ki ke yi da shi, don dai ta rasu ita bata araye.."




 murmushi Batool tasaki aranta tana tariyo farkon haduwarta da Uncle shureim har yau takasa manta lokacin daya cire mata errings dinta daya sargafe veil dinta.




Ganin ta shagala da tunani yasa ta katse ta"mu karasa cin abincin kada ya huce" sai da suka ci suka koshi tukunna suka koma falo a saman sofas suka zauna.


Sai jaraba kiran layin Ummi ta ke yi baya shiga, Har kiran daddyn ta ƙarayi shima baya picking, ta damu sosai, a karshe ta kira layin Danejo kamar dama jiran kiranta su ke yi, suna ɗagawa muryoyinsu suka cika kunnuwansu dayake handsfree ta saka kiran


"Angel, Kun manta damu, almost one month and weeks An kulle mu a part din daddy taj, Pls mun gaji, wallahi, Muna so mu dawo inda kuke..


"Unaisah wai har yanzu su Chief basu dawo daga kai farmakin bane? Muna jira shiru ba labari, Ko mun kira bakya daga kiran mu, Hankalinmu ba akwance ya ke ba ku fada mana in wani abu ya faru pls"


Angel, Ina danish dinmu? Ina yaya Salsabeel da Chief? Ina daddy taj, babu mai leko mu, kowa ya manta damu.


"Ni abinci ma yanzu ya daina min daɗi, ki6ar har tayi min yawa, baku ga yadda na koma ba, pls Unaisah ku fada ma Chief abude mu, kullen Ya isa haka, mun takura sosai, Muna so mu sakata mu wahala.." muryar Parveen ce


 tuntsirewa su ka yi da dariya ita da Batool kamar zasu shake .


"Pls ku kira mu video call mana" maida kiran Unaisah tayi video call, sai gasu reras su goma shabiyar, waro idanu sukayi ganin yadda hutu ya zauna masu, sunyi kiba kamar rainon turai, fatarsu tayi jajir yadda kasan ya'yan larabawa hatta masu duhun fatar cikinsu sun yi fresh fatarsu tayi kyau.



fashe masu da kuka Azeeza da jemimah su ka yi, ji suke kamar su yi tsalle su shige ta cikin screen din wayar.




Haris sai tambayar Danish Ya ke yi, yana ina? Ya yake? Sun dawo daga kai farmaki ko har yanzu basu kaiga zuwa ba, Kasa amsa mashi su ka yi, shiyasa suke fargaban su kirasu saboda tsoron su tambayesu ina Danish gashi kuma duk sun damu da shi sai tambayar shi sukeyi.



"Pls Sis, Ku fada mana gaskiya, ina ji araina kamar wani abu ya faru, sunje kai farmakin ko basu je bane"? Sajeed ne ya tambaya, fuskarsa amarairaice


dakyar Unaisah tayi karfin halin furta"har sun dawo" waro idanu waje suka yi cikin mamaki da rudu, atare suka hada baki gurin firta"suna ina? Sunyi nasara? Meya faru da suka je? Sun kashe su um? Sun taimaki sauran prisoners din um?


 Kamar yan jarida suka tsare su da tambayoyi.


Numfasawa tayi cikin karyayyar murya tace"sunyi nasarar taimakon fursinoni, yanzu haka suna a asibiti karkashin kulawar likitoci.." tunkan ta kare maganar Suka fara shewar Farin ciki..


"Yar uwata fa? Hada ita cikin su?


 Cike da zumudi Sajeed ya tambaya.


Bata san amsar da zata bashi ba, Batool ce tay saurin cewa"hada ita, wata mai bala'en kama da kai, ai munje asibitin mun gansu, tana nan cikin koshin lafiya, sai tambayar dan uwanta Gabriel ta ke yi" 



bai ƙarasa sauraran Batool ba ya shiga furta Alhamdulillah, Alhamdulillah... " 


"Mu damuwar mu,  ina bugun zuciyar mu? 


Murmushin yaƙe Unaisah ta saki"ku kwantar da hankulan ku, Danish, Yana nan Cikin koshin lafiya, ya ɗan samu rauni ne shi da ya Omar da salsabeel, shiyasa aka kwantar da su asibiti amma jikin nasu da sauki, har tambayar ku ya ke yi kuna ina muka ce mashi kuna nan lami lafiya.."


 jikinsu yayi sanyi lakwas, duk basu ji daɗin jin cewa baida lafiya ba, don basu san baya araye ba da ba karamin hauka zasuyi ba


"Ku sanyasu a addu'a pls, ita suka fi bukata" amsa mata sukayi da toh.."


"Amma da su ka je kai farmakin sun kashe Giants da mugayen da suka azabtar da rayuwar mu"?


Mubeen ne ya tambaya


"Sunyi nasarar kashe giant sosai, amma basu kashe elders ba, amma kada hakan ya dame ku, ita nasara ba'a samun ta cikin sauki, sai ansha wahala, cikin ikon Allah yanzu sun fara gano su wanene Elders kuma nan bada jimawa ba, cikin ma kwanakin nan zasu kamosu, gaba daya zamu gansu da idanun mu..." daɗine ya lullu6e su.





"Yanzu mu sai yaushe za'a bude mu daga kurkukun nan? Muna so mu ganku, ko ku dawo nan, sannan dan Allah ki roki Chief yasa akai mu asibitin da aka kwantar da su danish mu ganshi ko hankalinmu ya kwanta"


 acewar haris"Kada ka damu zamuyi masa magana"!


"Nima pls, ku rokarmin Chief, ya taimaka ya hadani da sister dina" 


Batool tace"kada ka damu zaka hadu da ita, yanzu bayanan in ya dawo zamu fada masa"



 Haris bai yarda da maganganun su unaisah ba, yana kokwanton in gaskiya suka fada musu ya dai bar abun aransa, tun da ba yadda zai yi.



"Ina Aunty Danejo na"?


Jemimah tace"tana can dakin ta kan gado ta hangame baki tana bacci, Ni na sato mana wayarta, don mu kiraki, Kuma munata kira ma bata shiga.." ƙyalkyalewa su ka yi da dariya..


"Munyi missing dinku, kuna aran mu, idan akwai abunda ke damunku bayan wanda kuka fada mana ku sanar damu" cikin kulawa batool tayi maganar .


Har suna hada baki gurin furta bamu da damuwar komai, akwai abinci available ga kayan more rayuwa kawai mudai so muke abude mu mu dawo gurinku sannan akaimu mu gano su danish din mu.." murmushi suka sakar masu..


"Okay zamu fada ma Chief idan ya dawo, duk yadda mukayi da shi zakuji daga gare mu"..


"Dan Allah kada ku manta, babu kyau jan rai, kullum haka kuke ce mana kuma sai muji shiru ko mun kira bakwa dagawa akai akai" acewar rubina..


"Wannan karon ba zamu manta ba, in sha Allah" amsawa sukayi da toh. 


"Kunyi kyau, kun ƙara haske, wasu sunyi ƙiba, tubarkalla masha Allah.." dadine ya lulu6e su jin abunda Unaisah tace..


Sarah tace"kuma haka, kun kara kyau,.."


"Mungode, Ku more lokacinku, soon zamu zo maku da abun ban mamakin da zai girgiza ku" 


"We can't wait to see" Cikin nishadi suka cigaba dayin fira da yan uwan su sun debe masu kewa, baka jin sautin komai a falon sai sautin dariyarsu da surutun su, kamar wadanda suka shekara basu gana da  juna ba..






~_____________________________🔥~





Around Ƙarfe karfe shida na marece, ta farka da wata irin kasala a jikinta, tana kokarin motsawa taji ta a jikin mutun, buɗe idanunta tayi a disashe take kallon fuskar shi, tunawa tayi da abun daya kawo ta, a ruɗe tayi dabarar raba jikin ta daga nashi ganin baccin nashi ya yi nisan kiwo farkawarsa ba yanzu ba, ta karance shi tun da jimawa, In ya fara bacci da wuya ya farka ko da za'a buga ganga ne a kusa da kunnansa.


zanan tattoo din bayansa ta ƙura wa idanu ya fito sosai, cikin sauri ta sauko daga kan gadon ta janyo rigarta daya cire mata, ta saka a jikinta, gabanta na faɗuwa ta ɗauko wayar ta daga cikin yar purse dinta data jefar ƙasa, gabanta na faduwa ga tsoro da fargaba da suka mamaye zuciyarta ahaka ta nufe shi, bayan ta kashe camera sound din wayar ta saita bayan shi da camera ta ɗauki hoton tottoo din shi.


Cikin sanɗa ta juya ta nufi toilet dinsa, ta bude ta shiga daga ciki, taja ƙofar tare da yin locking dinta, ajiyar zuciya ta ɗan sauke, Yatsun hannunta na kerma ta tura ma Chief hoton tattoo dinsa ta whatsapp chat dinsa.



Unexpected taji anyi knocking toilet door din, waro idanu waje tayi tare da hadiyar yawu..


Daga waje tajiyo voice dinsa da alamun bacci bai ishe shi ba ya furta"Ummi, na farka ban ganki ba, kina a ciki'? Wani irin faduwar gaba taji, da rudu ta zare idanu aranta ta ayyana tayaya akai ya farka da wuri?

Mutumin dake da nauyin bacci, Dakyar ta furta"yeah am in wanka zan yi"


"Okay, open the door for me, nima zanyi wankan" dafe kirji tayi da hannu ɗaya, ta rasa ina zata saka phone dinta, Idan har yaganta da waya a cikin toilet zai zargi wani abu, kuma idan ta hana shi zai iya zarginta tun da sun saba yin wanka atare wani lokacin.


Jin tayi shiru bata tanka mashi ba, yasa shi furta"Ummi, meyasa ki ka yi shiru uhum"?


 Cikin sauri ta tura wayar cikin bra dinta, ta gyara headscarf din kanta, kafin ta yi unlocking door din.


Har saida gabanta ya fadi ganin yadda ya murtuke fuskarsa kamar bai ta6a dariya ba.


Adabarbarce ta furta"am.. um.. ai na fada maka period nakeyi, bazan iya yin wanka atare dakai ba, bana so kaga abun da zai tada maka zuciya, nasan kana da ƙyanƙyami, ka jira in gama sai ka shigo"


 ta karashe maganar tare da ruko kofar da niyar ta rufe, batai aune ba taji ya bangaje kofar, ya shigo ciki tare da kulle ƙofar, aruɗe tace"big boss why? Na faɗa maka bazan iya wanka tare da kai ba ina period, yakamata ka jira ni awaje.." 


bata ƙare maganar ba, Ya janyota ta faɗo kan kirjinsa, hugging dinta yayi tightly, kirjinshi ya hadu da nata sosai, har saida nunfashin ta ya dinga fita dakyar.


A hankali Ya tallabe ass dinta da palms dinsa..


In a low voice kamar yana mata raɗa ya furta"kada ki damu, ba zanji ƙyanƙyamin ki ba saboda kina jini, inason komai naki ummi, saboda ke din mai tsaftace, duk abun da zai fito daga jikinki tsaftatacce ne, babu kazanta a jiki mai tsarki irin naki.."


 ji take kamar ta fasa ihu, saboda fargaban kada Ya gano wayar data saƙa a cikin bra dinta, gashi sai yawo yake mata da hannayensa a jikin ta 


"Pls big boss, bana jin dadi, cikina ciwo ya ke yi min, wankan ma na fasa, kasa a kawo min magani in sha.."


 ta faɗa tana kokarin raba jikinta daga nashi, sa6arta yayi kamar diyar roba Ya nufi bathtube Yana fadin"ba sai kin sha magani ba ummi, zansa kiji sauƙin radadin ciwon cikin ki.." 


waro idanu ta danyi ganin ya nufo bathtube da ita, tuni tasha jinin jikin ta, abun da take jima tsoro kada ya yi attempting undressing dinta zai iya ganin wayar data 6oye


Bubbuga kafadunsa tayi da tafukanta"pls, ka maidani bedroom, bazan yi wanka ba, na fasa, bana son ruwa ya ta6a jiki na, zazza6i nake ji.."


Wata yar iskar dariya ya saki"da ruwan zafi zamuyi wankan, zaki ji dadin jikin ki" kukan shagwa6a ta sanya ma shi, bai ko kulata ba.


 da iya karfinta na karshe ta fusge hannayensa daya tallabe ta da su, ta bangaje shi da gudu ta nufi toilet door din tana isa ta bude kofar ta fuce.



Tana ƙarasowa gaban gadon tana haki tayi saurin tura hannu cikin bra da niyar ta ɗauko wayar ta maida a purse sai dai me? Tana zura hannu ta laluba bra taji wayam babu wayar a jikin ta, gaba daya tabi ta rude ta zuge zip din rigar, ta 6alle hannun bra din ta cire ta duka ta zazzaga ta kwata kwata babu wayar, ruɗewa tayi gaba daya kanta ya daure ta rasa tayaya akai har wayar tabar jikin ta?


 Tunani tayi ko dai gudun da tayi ne yaja har wayar ta fado daga jikin ta? Girgiza kai tayi kamar ta6a66a, ta furta ba zai yiwu ba, anan na aje wayar, babu space din da wayar zata iya zamewa daga cikin bra dina saboda ta matse ni, ko dai na barta a toilet"? Yanke shawarar komawa toilet din tayi don ta dubo ko a nan wayar ta fadi.


 Juyawar da zatayi keda wuya kwatsam ba zato ba tsammani, Idanunta suka sauka akan wayarta dake a ruƙe a hannunsa.


Yana a tsaye bakin kofar toilet din, yawu ta haɗiya cikin rudu ta furta"a ina ka ganta"? Shu'umin murmushin nan nashi ya sakar mata"a inda kika 6oye ta, Ummi me kike yi da waya a cikin toilet?


 Bayan asanina dake bakya shiga toiler da waya a hannun ki. 


murmushin yaƙe ta sakar mashi tana inda inda tace"am..um..dama Natasha ne ta kira ni, tana kara tuna min akan inyi maka maganar babyn pretty..." 


tsoki yaja"Ummi banason maganar nan, ki fiɗa mata ta fidda rai akan ta, saboda ba yar ta bace, na maida ma mommynta ita"


Ajiyar zuciya ta sauke ganin bai dago ta ba"babe saida na fada mata haka, nace tayi hakuri, amma takasa saboda ta kwallafa rai akanta, shakuwace ke dawainiya da ita, dole tayi kewanta, ta fada tare da matsawa kusa da shi, cikin salon jan hankali take shafa kirjin shi, har takusa zame wayar daga hannun shi, kwatsam sai ga sako ya shigo wayarta akan idanunsa.



_thank amma ba zamu iya bin diddiginsa ba ummi, Ki kula da kanki zamu nemi wata hanyar da zamu kama shi_



Yanayin fuskarsa ne Ya canza zuwa tsantsar al'ajabi da tashin hankali, cikin rudu da faduwar gaba ya dubeta, duk da batasan sakon menene ba sai da taji ƴan hanjin cikinta sun kaɗa ganin yadda walwalar fuskarsa ta dauke Cikin ruɗu ya furta"ummi, diddigin wanene za'abi don a kama shi, Kuma ta hanyar ki" ❓



Waro idanu waje tayi tamkar kwayar zasu faɗo kasa, adabarbarce ta furta"Um..kada ka damu, kasan nasaba irin wannan aikin na taimaka ma jami'ae donsu kama 6ata gari tun a america, yanzun ma wani ɗan ta'addane suke so su kama shine suka nemi in taimaka masu..."


 shiru yayi jim kamar zuciyarshi tana so ta musa mashi akan abun da ta fada.



sai dai me rawar da jikinta keyi kamar mazari yasa shi zargin bata da gaskiya, saboda gaba daya babu nutsuwa a tare da ita.



"Ina kokwanto akanki Ummi, ban yarda da maganarki ba, ki fada min gaskiya, tun kafin in gano da kaina, Idan ba haka ba, wallahi na lahira sai yafi ki jin dadi..." 


yawu ta haɗiya ƙutt tana faman zare idanu tace"meyasa ba zaka yarda dani ba? Na ta6a yi maka karya ne? Shekara nawa ina atare dakai big boss? Ban ta6a hada baki da wani don a cutar dakai ba babu wanda yasan ma muna atare dakai, pls ka yarda dani.." 



wani kallo yayi mata yana sakin wani shu'umin murmushi ya furta"ummi dan adam ba abun yarda bane, mutun ya sa6a wa mahaliccinsa balle ni, kawai idan kinaso In yarda dake ki cire min security din wayarki In bincika ta..."  



 " Na shiga uku..." 


 yarfa hannu tayi kamar zata fasa ihu saboda tashin hankali bawai don tana jin tsoron nuna masa ba sai don tana jin fargaban maganar Chief ya zamana gaskiya in kuwa hakane kashin ta ya bushe.



Mika mata wayar yayi"bude min ummi na" yatsun hannun ta na kar6a ta kar6i wayar idanunsu a cikin na juna, tunawa tayi da maganar Chief, dole kiyi taka tsantsan idan ba haka ba, in har ya tabbata shine Jan wuya na gidan kurkukun kaddara ya kuma gano kin bamu hadin kai, har kashe ki zai yi, kada kiyi tunanin shakuwar dake a tsakaninku zaisa ya raga maki.."


 da gangan ta saki wayar ta kife kasa har wani sauti ta bada saboda tiles din data daka


Pretending tayi a rude ta zukunna tare da daukar wayar tana fadin"Ya salam, screen din wayar ya fashe"


mikewar da zatayi keda wuya, taga yana matsowa kusa da ita, ja da baya tayi a tsoroce ganin yadda Jikinshi ke kerma ..


Yanayinsa kamar na wanda zuciyarsa ke nema ta karye...


Kwatsam Ya shaƙe wuyanta da hannunsa Ya kure ta jikin bango, da wata irin buɗaɗɗiyar murya ya furta"sabo da kaza bai hana In yankata Ummi, muddin ta ci amanata, Ki fada min menene kike boye min? Tun kwanaki kika sauya min, abun da baki taba min ba, yau tun zuwanki ina lura da duk wani motsinki, baki shan giya ummi amma kikasa na kawo mana giya, saboda kina so hankalina Ya gushe donki samu damar aiwatar da abun da kike so, bayan da bacci ya dauke ni, sai kika dauki hoton tattoo dina, Ummi wanene ya saki huh?..."


 Tashin hankalin da ba'a saka mashi date, tuni ido Ya raina fata, wani irin faduwar gaba ta soma ji a kirjinta kamar ana buga war drum, Muryarta ashake ta furta"big boss, bazan iya cin amanarka ba, ka yarda dani..." katse ta yayi"kada ki min karya, ba halin ki bane, Idan kinaso In yarda dake ki fada min komai.. " 



rintse idanunta tayi tare da cizon le6enta muryarta na rawa ta furt"sus.. Sune suka sanyani, saboda suna zarginka, wallahi bada son raina ba, saida nace masu ba zaka taba iya aikata miyagun laifukan da suke zarginka dasu ba, amma suka matsa min akan cewa kana da sa hannu, koda suka rokeni akan in basu hadin kai gurin ka ma ka nace ni bazan yi ba, shine suka matsa min, ni kuma saboda na yarda dakai nasan baka da laifi shiyasa na amince masu saboda nasan ta silar bincike zasu gane sunyi kuskuren zargin ka"



Aruɗe ya furta"wani irin zargi su ke yi akaina um"?


zazzare idanunta tayi, wani kwarjini yayi mata har bata san sa'adda ta furta"dg yana zargin kana ɗaya daga cikin Elders na kurkukun kaddara, wai kaine Jan wuya, mahaifin Unaizah yar gidan daddy, saboda sun ga hotunanka kai da Natasha acikin Diary dinta data bari a hannun yan uwanta prisoners din kurkukun kaddara, Dan Allah ka fada min gaskiya kaina ya kulle, na shiga rudani, zuciyata ta tsorata, naji fargaba da tashin hankalin da ban ta6a ji ba a lokacin da naji labarin kurkukun kaddara, da irin izayar da wasu azzulaman mutane su ke yi wa yaran da basu ji ba basu gani ba, big boss tayaya zan yarda da abunda suka fada akanka"? Ta faɗa tana kallansa..


 "Bayan ni nasan wanene mutumina, saida na fada masa mutun mai zuciyar imani da tausayi, bazai iya aikata abun da suke zarginka da shi ba.."


Bata ƙare maganar ba, sakamakon tsawar daya daka mata wadda tayi silar ruɗewarta, kamar zai fasa dodon kunnanta, Dafe kanshi yayi da tafukansa kamar mai faɗa da ciwon kai, Cike da tsantsar tashin hankali da rudu ya shiga furta"How is that possible? How do they know everything? How did they get Unaizah's diary? Who told them? Who is behind this? This is a lie! It's not true, it will never be true"


 


Yana magana zufa tana wanke fuskarshi, Ummi dake kallon shi gaba daya tabi tasha jinin jikinta ganin yadda lokaci daya big boss ya nemi zaucewa, yama rasa ina zai sa kanshi kamar mahaukacin, kanshi ya daure da Jin abun da bai ta6a zata ba, ko a mafarki, mamakin shi taya akai Unaizah ta tafi da diary din ta batare daya ankara ba? Yana nan sake da baki Yana ganin cewa wayonsa da dubararsa ba zasu taba bari asirin shi ya tonu ba sai gashi ƙaramin kuskure yana nema yaja masa matsala.



 wata irin ƙara ya fasa tare da nufar maidaidaicin glass table din dake a seating area din dakin Ya kinkime shi, da sauri Ummi tabi bayanshi, Kafin Ta karaso Ya buga table din kasa nan take Ya tarwatse, ruko hannayensa tayi a cikin nata, 




cikin shesshekar murya ta furta"big bosa kada ka lahanta kanka, na fada maka ni ban yarda da su ba, dama nasan idan na fada maka zargin da su ke yi maka dole kaji ba dadi, pls kazo muyi magana, nayi maka alkawarin in har baka da laifi zan yi iya ƙoƙarina don wanke ka daga zargin da ake yi maka"




bangajeta yayi da hannun shi tayi taga taga zata fadi, da sauri Ya damki arm dinta yana huci ya furta"har yanzu baki fadamin tayaya akai suka san ina atare da ke ba"?


Tamkar zata fashe mashi da kuka tace"wallahi bani na fada masu ba, ka yarda dani, ban ta6a fitar da sirrinka ba.."


 muryarsa da tsawa yace"karya ki ke yi Ummi, ba zasu taba neman ku hada baki ba gurin kamani batare da sunsan muna a tare ba, saboda ganina ba abune mai sauƙi ba.." 



cike da jin shakkar shi tace"hakane, ay na fada maka, hotonka dana Natasha suka gani a cikin diary din, aranar da mu ka je airport a america tare da Natasha sun ganta, babu wanda baisan ƙawata bace, bayan haka akwai ranar daka kira video call, bana akusa na shiga toilet, ɗaya daga cikin yaran da nake kula da su ta shigo dakina da karanbani ta dauki wayar ta ɗaga kiran anan taga fuskarka, wallahi big boss yarinyar ko waya bata iya ba, babu komai akanta bansan ya akai ta ɗaga kiran ba...."


 bata boye masa komai ba.., Sakin arm dinta yayi tare da dafe kanshi da tafin hannunsa.


Ita kanta ta tsorata da yanayinsa karfin hali tayi gurin firta"tunda na fada maka abun da ka ke son ji, Nima inaso ka amsa min tambayana big boss, tayaya akai Unaizah ta zama daya daga cikin fursinonin kurkukun kaddara? Waya kaita bayan a labarin da naji mahaifinta ne Ya sadaukar da ita,...."


tiryan tiryan ta zayyana mashi labarin Unaizah, ta kara da cewa"Abun ya dameni, tun da naji labarin ta, saboda nasan Unaizah ƴarka ce, kuma kaine mahaifinta, amma na ruɗe da naji yadda suka bada labarin cin amanar da mahaifinta yayi mata, ya yaudare ta ya kai ta kurkukun kaddara da sunan High school na korea, Big boss Ina Unaizah? Kuma wacece Zeenatu diyarka mai bala'en kama da Unaizah...


bata kare maganarba Ya balbaleta da masifa, yana fadin meyasa take yi mashi tambayoyi kamar tana tuhumarsa? Ko itama ta yarda da abunda ake zargi akansa? Bayan bai ma taba sanin ina ne gidan kurkukun da take magana akai ba, balle wasu elders, shi bazai iya aikata munanan laifukan da ake tuhumarsa ba, tafi kowa sanin halin shi don haka ta rabu da shi, Yarinyar da take magana akai ba Yar shi bace, shi ƴa ɗaya gare shi Zeenatu, Kuma itace baby preetyn da take magana akai.."


Yana magana yana huci kamar zai rufe da bugu, baima kare maganar ba Ya fuce daga dakin tabi bayan shi sai dai kafin ta karasa taji ya datse kofar, bubbugawa tayi taji ta a datse.


Wani irin matsanancin ciwon kaine Ya taso mata, a daddafe ta nufi gefen gadonsa ta zauna, Zuciyarta ta karaya, saboda ta ga tsantsar rashin gaskiya atare da big boss din ta, abunda take jiyema fargaban Ya zamana gaskiya, Ya zatayi da rayuwarta? Ina zata sa ranta taji dadi?meyasa big boss Zai daga hankalinsa akan abunda Yake ikirarin bai aikata ba? Meyasa ya canza mata a lokaci? Meyasa ba zai kare kansa ba? Ya salam


 Kifa kanta tayi saman pillow, hawaye suka cika idanun ta, ga wani bugun barazanar da zuciyarta keyi mata, tana jin tsoron abin da zai biyo baya, wayarta ta ɗauko don tayi Kira sai dai koda ta duba screen din wayar ya tsastsage bata iya ganin komai, gashi ya kulle ta adaki no way out..


Bacci ya ƙaurace wa idanunsu ganin shiru Aunty Ummi bata dawo ba, kuma har time din Chief da daddynta basu dawo ba, sun yi jiran har sun gaji


Suna akwance kan gadonsu sanye cikin pyjamas, sun hada kai suna kallon wani korean drama a wayar Unaisah, ba laifi kallon Ya ɗebe masu kewa duk da hankalin su ba akwance ya ke ba.


Kiran wayar Taj ne ya shigo wayar Unaisah, a hanzarce tayi picking ta kara a kunne.



"Unaisah har yanzu bakuyi bacci ba"?


Muryarta da shagwa6a tace"daddy ba zamu iya bacci  in har baku dawo gida ba"


"Kuyi hakuri ku kwanta, Ku huta pls, nan bada jimawa ba zan dawo gidan"


"Toh daddy, Ina mommyna ba zata zo taga babynta ba" yar dariya yayi"gatanan a gefena, tana sauraronki.." bai kare maganar ba, Muryar Benazir ta katse shi"Babe barka da dare Ya kuke Ina fata Kuna lafiya"?


"Lafiyalou mommy, nayi missing naki, inason ganinki, Kin ki zuwa kiga babynki" 


dariya Benazir tayi"Sorry, Kina araina, Gidan naku ne sai da izni ake shigar shi, ni da anila munata jira, sun ce zasu tuntu6emu in sha Allah zamu zo" 

bata kaiga furta kalma ma, Batool ta kwanto da kanta saman wuyan ta,"Mommy, barka da dare, Batool ce, Ina uncle Shureim din mu, munyi missing nashi.."


"My baby Batool, Uncle shureim yana lafiya, shima yayi missing naku, kullum sai ya tambayeni ina babyn nan mai kama da shi"


 dariya batool tayi saboda dadin da taji"please mommy, ki gaishe min da shi, ki fada mashi ina kaunar shi"


"In sha Allah zai ji, don ma baya akusa da mu ai dana bashi kun gaisa, amma zan sa ya kiraku ku gaisa" washe baki tayi"mungode mommy"



"Okay, babes, ku kula mana da kanku, Ku kwanta kuyi bacci, yanzun nan daddynku zai dawo.." 



amsa mata sukayi da toh bayan sun katse kiran, Unaisah ta daura phone dinta akan ta batool dake akan Nightstand, hugging din juna sukayi babu alamun zasu runtsa saboda tunanin Aunty Ummin su da bata dawo ba.




A hankali wata dankareriyar Mota baka, ta shararo izuwa main entrance gate Na villa din owais, ko da ganin baƙuwar Mota, Security Officers suka yi saurin nufo motar, tare da yiwa mata ƙawanya, knocking Glass din motar sukayi tare da bashi Umarnin Ya sauke glass don suga wanene shi, banza akayi da su har saida suka fusata kamar zasu 6a66ake window glass din motar tsabar yadda suke kwankwasa shi.


sai da na cikin motar ya mula yasha iska tukunna ya zuge masu window glass, Tare da sauke Shade din dake akan fuskar shi, Waro idanu waje su ka yi cike da mamaki, a  hanzarce suka buga kafa tare da sir mashi kusan atare suka furta"Sorry Sir.." 


Ƙayataccen murmushin gefen fuska ya dan saki, yayin da yake a zaune saman Driver's seat. 


"Ina fata na same ku lafiya"?


 "Lafiyalou Sir, munyi mamakin ganinka, bamu san ka samu lafiya ba,Ya jikin naka" still da murmushi yace"Alhamdulillah, naji sauƙi, Owais bai fada maku bane? Ya tambaya da mamaki kan fuskarsa su ka ce wallahi bai sanar da su ba, basu san komai ba game da samun lafiyar shi ba, ko sun tambaye shi sai dai yace masu da sauƙi jikin shi.




"Ku yi masa uziri, Kunsan yanayin aikin namu, Yana a ciki"?




"A'a sir, tun safe daya yabar Gidan har yanzu bai dawo ba"




Okay, ya faɗa tare da yiwa motar key, Ya shige cikin gidan.




Fitowa yayi daga Ciki, Jikin shi sanye da Kaftan, ya fito fess abun shi ko tabo babu akan skin insa, kamar bai taba jin rauni ba.




Lokacin daya shiga Falon gidan bai Iska kowa ba, zama yayi a falon tare da daura kafarsa daya kan ɗaya.




Chef ne ya shugo falon daga kitchen, yana hangosa da sarsarfa Ya nufe shi bayan sun gaisa yayi mashi ya jiki.


 daga bisani chef din ya tambaye sa ko yana bukatar abinci ya kawo masa?




Da buɗar bakinsa sai cewa yayi"ina Unaisah da Batool"?




"Suna a cikin dakin su"




"Ka kira mun su, Inason ganin su"




Amsa mashi yayi da toh, kafin ya juya ya nufi ɗakin su Unaisah 




Bayin Allah har sun fara bacci, suka farka jin knocking, Batool ce ta bude kofar tana mika da hamma ta dubi Chef din




"Big guy, yazo, yana a falo yana son ganin ku"




waro idanu waje ta yi cike da mamaki tace"big guy Yaji sauki! Da kanshi yazo, Wayyo Allahna, Alhamdulillah ka faɗa masa, gamu nan zuwa.."




 juyawa tayi ta nufi Unaisah dake ta juyi kan gado, ta bubbuga kafafunta"sis Ki tashi, Big guy ne ya zo, ya samu lafiya yana a falo, yanzu chef ya fadamin yana son ganin mu"


 dakyar ta samu Unaisah ta sauko daga kan gadon tana mika tace"Dagaske Ya omar ne Ya yazo? Shi ka ɗai yazo ko tare da wani"?


"Kinga ki zo mu je mu gaishe shi daganan sai muyi mashi ya jiki"


Mayafi kowaccen su Ta yafa ma kanta, suka fito da sauri suka nufi falo, tunkan su karasa suka hango shi zaune kan sofa mai mazaunin mutun uku ya daura kafarsa daya kan daya, Yayin da yake danna wayarsa a hankali


Jin motsin tafiyar su ne yasa shi ɗagowa da lumsassun idanunsa da suka kada jawur ya dube su.


Cikin girmamawa suka zauna suna fuskantar shi.

"Ya omar dagaske kaine? Munyi kewarka! Ya jikin naka?  Ina ya salsabeel"?


 Yamutsa fuskarsa yayi"fushi nake daku, kun manta dani, kuna nuna kamar kun damu dani bayan tun da na kwanta jinya baku taba zuwa kun dubani ba" 


Ya faɗa yana kare masu wani kallo wanda yasa Unaisah tayi noticing wani abu a tare da shi.



Batool tace"ba haka bane ya Omar, wallahi kana aranmu, chief ne bai sa akawo mu ba amma muna taso muzo mu duba ku.."


Murmushi yasaki"ina Ummi ne?


"Ta tafi anguwa, har yanzu bata dawo ba, daddy da Chief duk sun fita basu dawo ba"


Agogon hannunsa ya duba 


"ku tashi mu tafi in kaiku asibitin da aka kwantar da sauran yan uwanku prisoners ku duba jikin su" cike da zumudi Batool tace"Toh," Unaisah ta maƙe kafaɗa alamar bazata je ba 


"ya omar, dare ne yanzu, bai kamata mu fita ba, why not zuwa gobe da safe sai muje, kaga kafin nan Daddyna da Chief harma da aunty Ummi sun dawo sai muje ba ki daya mu duba jikin nasu.." 


tunkan Ta kare maganar ya katse ta da cewa"kada ku bari damar nan ta wuce ku, Chief bazai bari ku fita ba, Ya cika tsananta maku tsaro, ku tashi kawai mu tafi in kai ku, cikin yan mintina zamu dawo" 


duk yadda Unaisah taso ta ƙi amincewa da fitarsu takasa saboda ya matsa lamba akan su shirya ya kai su.


 har dai tace"shikenan, bari mu shiga ciki mu sauya akaya"


 ta fada tare da jan hannun Batool suka nufi bedroom dinsu, suna shiga ta datse kofar, ta fuskanci Batool da ke fadin"muyi sauri mu shirya, kafin chief ya dawo, in ba haka ba zai hana mu fita ne"


 cikin muryar rada Unaisah tace"batool nifa ban yarda da ya Omar ba, wallahi kamar bashi ba ya sauya min, ke baki lura ba? Idanunsa kamar na mashayin giya, muryarsa katuwa ba irin ta ya omar ba mai sanyi, sannan Ya omar bai kai wannan duhun fata ba, duk da bawani sanin fuskarshi nayi ba saboda yana yawan saka mask amma wallahi akwai banbanci tsakanin Ya omar da wannan Omar din, kuma tayaya mara lafiyan da ya farfaɗo daga coma ya  iya samun ƙarfin da zai yi driving? Shi kaɗai batare da likita ko wani security ba! nidai hankalina bai kwanta da shi ba..." 



Cike da matsuwa Batool ta bubbuga ƙafafunta akan floor.



"haba sis, ki daina wannan tunanin, wallahi ya Omar ne, kodai kin samu matsalar gani ne? Yamutsa fuska tayi"ba zaki gane ba Batool,  kawai daga zuwan shi sai yace mu tafi ya kai mu asibiti? Batare da iznin Chief ba, kawai sai mu kwashi kafa mu bi shi kamar wasu sakarkaru, bayan haka Mutumin da ya ke a coma yaushe ya farfaɗo? Kuma babu tabo ko kadan akan fatarsa.."


 dafa kafarta Batool tayi"ki kwantar da hankalinki, wannan ba wani abu bane may be yaji sauki tuntuni mune bamu sani ba, kuma in ban da abunki gidan nan atsare yake da jami'ai da kuma cctv, In bada iznin su ba tayaya zai iya shigowa?



 Tunzura ta Batool tayi harta shawo kanta ta amince zataje saboda itama tana son taga yan uwansu fursinoni da aka ku6utar da kuma Ya salsabeel.


Shaf shaf suka sanya wide leg jumpsuit ajikin su masu kyan gaske, ta Unaisah Ja ta Batool yellow, daga sama suka daura Wrap coat, sai sukayi rolling veil asaman kansu, Bayan sun saka takalma suka ɗauki phones dinsu.


Kafin su fito daga dakin saida Unaisah Tayi ta kiran Taj baya picking, ta kira chief shima baya picking, ta kira mommynta still itama bata yi picking ba, taso ta same su don ta fada masu batun zuwan big guy da kuma fitar da zaiyi da su amma bata samu halin yin hakan ba, feshe jikinsu sukayi da turare, suna fitowa suka iske big guy atsaye yana jiran su.


"Mu tafi" ya fada tare da nuna masu hanya, ya yi gaba suka bi bayan shi, Har gaban motar shi tun fitowar su Unaisah ta lura da security officers din gidan sun yi tsaye kamar gumaka kwata kwata basu sintiri kamar yadda suka saba, lamarin ya jefata a ruɗani.


Da kan shi ya buɗe masu mazaunin baya na motar, ya  dafe murfin motar da hannunsa.


Batool ce ta fara shiga ciki ta zauna, Unaisah tana niyar kutsa kanta ciki kamar ance ta saci kallon shi karaf idanunta suka sauka akan zanen tattoo din daya dan leko ta kirjin sa sak kalar na Danish, wanda hakan na nufin giant din kurkukun kaddara ne 

 ruɗewa tayi ta shiga zare idanunta a tsananin tsorace.


ganin ta toge taki shiga yasa shi lura da abun da idanunta ke kallo.


"Sis ki shigo mu tafi" Batool ce ta faɗa daga cikin Motar


 batai aune ba taji ya ingizata cikin Motar, Ya datse Murfin, a hanzarce Ya bude front seat ya shiga ciki, da gudu Ya fusgi motar, ya miki hanyar fita daga estate din~


Welcome, Littafin kurkukun ƙaddara 500 ne, dukanshi Book One two and 3 Idan kin shirya biya ga Details da zaki tura

3196407426 

First bank 

Bature Hafsat Muhammad,


 bayan kin tura zaki bada transaction reciept ko screenshot na debit alert a matsayin shaida ta wannan number din 08103884440

Post a Comment

Idan kuna da tambaya akan abinda Baku game ba ko kuma kuma Neman littafin da babu a nan kawai ku ajiye tambayarku a ta comment ko wani shawara da Zaku bamu.

Previous Post Next Post

Sponsored Link

Sponsored Post