Kurkukun Ƙaddara Takun Ƙarshe Page 79 Complete

Kurkukun Ƙaddara Takun Ƙarshe Page 79 Complete

Takun Ƙarshe

Tun lokacin daya wurgo Unaisah ta faɗo jikin Batool arude ta shiga tambayarta meke faruwa? Tana lafiya?

 kasa magana ta yi saboda rikicewar da tayi, ɗagowa tayi tare da kallon madubin Motar, hankalinsa a kwance ya ke driving din su, haɗa idanu su ka yi, Ya sakar mata wani shu'umin murmushi, faɗuwar gaba taji kamar ana luguden ta6are a ƙirjin ta, ganin yadda kamannin big guy suka 6ace daga kan fuskarshi, ainihin suffar shi ta bayyana, wani mummuna da shi.

gaba ɗaya tabi ta ruɗe ta rasa gane meke shirin faruwa da su, Batool fa kwata kwata batasan wainar da ake toyawa ba, wayarta take ta dannawa.

da karfin Hali ta furta"Who are you"?

sai lokacin Batool ta dakata da danna wayar ta ɗago tana kallon  Unaisah.

Bai kula ta ba ya cigaba da yin driving dinsa, Rai a6ace tayi kukan kura ta tsallake backseat ta dawo front seat din motar

Ta rurruƙe hannayensa da ya ke yin driving din da su, ta soma kokarin dakatar da shi,  ta ƙwammace su yi accident su mutu akan ta bari ya tafi da su saboda ta ji aranta daga kurkukun ƙaddara aka turo shi ya ɗauke su.

kokoyi su ka kama yi, out of control motar ta dinga girgiza tana kaukacewa hanya akan titi.

Karfin halin ta ya ɗaure mashi kai tamau, kuma still yaki tanka mata.

Batool ta yi matuƙar razana da ganin abun da ke faruwa, sam takasa magana saboda razanar da tayi ganin big guy ya sauya kamannin fuskarsa.

Tuni wayar hannunta ta fadi ƙasa sakamakon girgizar da motar ke yi har saida kanta Ya da ki window glass, kafin tayi wani yunƙuri, Ya Naushi cikin Unaisah da gwiwar hannunsa nan take wani azababben radaɗi  mai kama dana ciwon mara ya ratsa sassan jikin ta


 Cikin ɗimuwa ta shiga furta Inna lillahi wa'inna ilaihirraji'un Batool ki gudu! Saida na fada maki ba ya Omar ba ne wannan, ki gudu Batool, ki buɗe murfin motar ki gudu, kashe mu zai yi.. "


fashewa da kuka Batool tayi, cikin rawar murya take fadin dan Allah kada ka cutar da mu, ka ƙyalemu mu tafi, ka ƙyale mun yar uwata.." 




 ta mirror ya ke kallon fuskar Batool dake ta kuka, ga Unaisah dake a gefensa ta daddafe cikinta dake mata zogin azaba. dakyar take fitar da numfashi mai haɗe da nishi, da hannu ta dinga yima Batool alamar ta buɗe murfin motar ta gudu saboda ita a halin yanzu yayi mata illar da bazata iya ta6uka komai ba..



Sakin sitiyarin motar yayi, Ta cigaba da driving din kanta, ya damaƙar keyar Unaisah ya yi tare da ɗaɗɗago da ita Ya jefar da ita backseat, jikin batool na bari ta janyota tare da rungumeta a kirjin ta"sis ta ki tashi dan Allah ki tashi, na shiga ukuna wayyo Allahna dan Allah  ka maida mu gida, kada ka cutar da mu,  Chief bazai ƙyale ka ba"

cike da izza ya jingina bayansa jikin seat, yayin da yake kallonsu ta mirror din motar har wani lumshe idanun shi ya ke yi kamar mai jin bacci.

 Zura hannunsa ya yi cikin door pocket din motar, ya zaro sirinji biyu masu ɗauke da ruwan allura a cikin su, ya haura backseat, Ya caka ma Batool allurar a cikin jijiyar wuyanta nan da nan ta fara jin wani irin matsanancin bacci yana fusgarta har bata san sa'adda ta 6ingire kanta jikin seat, ya tallabo kan Unaisah da ta fita hayyacinta, ta langwa6e kanta saman laps din Batool, itama yayi mata allurar gaba daya suka fita hayyacin su, basu ƙara sanin meke faruwa ba.

UMMIN AMERICA

Motsin buɗe ƙofar data jiyo ne Yasa tayi wuff ta miƙe tsaye tana kallon room door din, shigowa ciki yayi fuskarsa a murtuƙe ya nufe ta.



"Big boss! Meyasa ka kulle ni adaki? Ina ka tafi ka barni, Ko ka manta dani ne.." 


bai ko ɗaga idanunsa ya kalle ta ba, ya damƙi arm din ta yana ƙoƙarin janta ta turje, tana kallon fuskarsa dake fitar da gumi tace"me zaka min? Ina zaka kaini" A hankali ya ɗago da raunannun idanunsa Ya dube ta da su"ɗazu kin tambayeni ban baki amsa ba, saboda ban samu abun da na ke so ba, amma yanzu inaso ki zo muje zan fayyace maku komai da ki ke son ji"



bai jira amsarta ba, Yaja Hannun ta suka fuce daga dakin kaitsaye Ya nufo falo da ita.



Juyo da ita ya yi Suka fuskanci juna, da ainihin suffarsa ta JAN WUYA, Idanunsu cikin na juna, ba ta  ta6a jin faɗuwar gaba irin na wannan lokaci ba, tsantsar rudani ne akan fuskarta.


"Ummi, Lokaci ya yi da za ki san ko ni wanene! Maganar 6oye 6oye ta ƙare a tsakanin mu, zan faɗa maki komai da ki ke son ji"



kalamansa sun rikirkita tunaninta.




"Dama nasan duk mun daran daɗewa dole gaskiya ta bayyana, kuma naji dadi da Allah ya nuna min wannan ranar, saboda nima jiran zuwan ta na ke yi"



ya ɗan dakata tare da sakin shu'umin murmushin nan nashi Kafin ya ɗaura da cewa"ɗaukar fansa yasa nake atare dake, Ba dan Allah ba, duk wani abu daya faru atsakanin ku Nine nake kulla maku makirci, Ni na raba ki da mahaifin ki, Na shiga tsakanin ki da shureim, Na kuma lalata martabarki, na maida ki karuwa..." 




ta kasa yarda da abunda kunnuwanta ke jiyo mata daga bakin Uncle musa, jin abun take kamar a mafarki saboda ruɗu da tashin hankali.



"bazan ta6a yarda da abun da ka faɗa ba, bazai ta6a yiwuwa ba, Uncle musa kana cikin hayyacin ka kuwa? Kasan me ka ke faɗa? ko dai giyar da ka sha ce bata sake ka ba"?



Tallabo fuskarta yayi da tafukansa"ko kin ƙi ko kin so dole Ki yarda Ummi, Ki buɗe idanunki ki saurareni, Ni ba mutumin kirki ba ne, tantirin shaiɗani ne, bani da mutunci ko miskila zarratin, Mugunta da zalunci kadai nasa gaba..." 


bai ƙare maganar ba ta katse shi cikin rawar murya ta shiga fadin ya daina batason ji, ba yin kansa bane! Giyar daya sha ce.."



"Ummi, Ki daina yaudarar kanki, mutumin kirki bazai ta6a mayar da kamilar mace karuwarsa ba"!



"Komai daya faru mahaifin ki ne Yaja maki, nayi amfani da ke saboda in sanya mashi bakin cikin da har abada bazai ta6a mantawa dani ba, na daɗe ina neman hanyar da zan koya masa hankali ban ta6a cin galaba akansa ba, saboda kariyar dake gare sa, amma Ranar dana fara ɗaura idanuna akan ki sai na ji maitar sha'awarki ta kamani, Musamman da na ji cewa ke din ɗiyar imam malik ce, naji dadi a wannan lokacin saboda na samu hanyar da zan lalata farin cikin rayuwarsa, saboda ni ba'a shiga gona ta a zauna lafiya, bana yafiya, nasan bakisan komai daya faru ba a tsakanina da shi, may be bai fada maki ba a lokacin, shiyasa kika aminta da ni, saboda ke bakisan wanene Musa ba, kafin na bayyana maki soyayyata saida na fara zuwa gurin mahaifinki saboda in nemi auran ki,  duk da nasan mawuyacin abu ne ya bani ke saboda yasan mugayen halaye na ciki da bai... .."



 labari Ya fara mata na abin daya faru tsakaninsa da sheikh Imam.


 wasu zafafan hawaye ne suka fara Dora kan kuncin ta masu ɗumi.



"Ya san ni mugu ne meyasa bai bini ta lamama ba mun rabu lafiya? Sai ya dinga gaggaya min maganganu marasa dadi da suka tsaya min arai na, ya kalli tsabar ido ne yace wai ni ban cancanci in mallake ki ba, saboda yafi  sha'awar Ki auri mutun mai tsantsar ilmin addini, mai jin tsoron Allah, Mai kuma kyawawan halaye, kuma koda zaki ce kina sona ba zai bari ki aure ni ba, ballema yasan jininsa bazai ta6a ƙaunar fasiki irin na ba, ni da ke sai dai hange daga nesa amma aure har abada ba zai yiwu tsakanin mu ba, abun da yafi baƙanta min rai daya ce ya yi fatan ace shureim ne yazo neman auranki, jiki na 6ari zai bashi ke, wallahi Ummi badan ni ke nema awurinsa ba a lokacin da har kashe shi zanyi, Kuma idan na kashe shi na kashe banza amma sai banyi hakan ba saboda ni so nake in mallake ki gaba ɗaya, arayuwata bana wasa da abu mai daraja da mutane suke rububi akan shi, sannan kuma bana neman abu ban samu ba, kuma bana yin alheri sai idan nasan zanci riba, naga nasara atare dake shiyasa na nace akan saina mallake ki, amma daga ke har mahaifinki Kuka ƙi amincewa da bukatana duk irin wahalar da nayi akan ki, ba irin magiyar da banyi maku ba gaba daya kuka ƙi jinina, Ni ban neme ki da fasikanci ba, sunna naso na raya dake amma mahaifinki ya yi min bakin da har yau na gaza cimma burina akan ki ummi, idan ma saboda mugun halina na ne yasa yaƙi ba ni ne in aura, to ai naga ko fir'auna mace ta gari ya aura ko"?




 Cikin fushi da 6acin rai ya ƙare maganar Yana kallon Cikin idanunta da suka kaɗa jawur kamar an watsa barkono a cikin su, she was completely shocked and confused, unable to speak, Gaba d'aya ta gigice ta ruɗe ta kasa magana, ba ta ta6a sanin Musa ya nemi auranta agurin baba Imam ba sai da ya fayyace mata da bakinsa, kuma anan taji irin yadda Aunty laura taci amanarta saboda abun duniya.



Numfasawa yayi kafin Ya ɗaura da cewa"ke da mahaifin ki ne Kuka cusa min tsanar Shureim a cikin Zuciyata, dama na kuɗuri aniyar saina mayar dake karuwa saboda wadannan maganganun daya gaggayamin, Yana wani alfahari yarsa mai tsoron Allah, mai kamun kai, mai ilmin addini wato ni mutumin banza ban dace na mallake ki ba sai shureim! Shiyasa Ni kuma Na mayar dake fasika don in bakanta masa, Kuma nayi amfani da shureim saboda in shiga tsakanin ku, nasan ba zaki manta da ranar da shureim Ya kawar maki da budurcinki ba, bayan na kira ki awaya nayi maki muryar shureim ki ka zo daki har muka samu sabani, Bayan kin fita daga dakin, Na dauki waya nakira shureim Nace yazo ina nemansa, saboda nasan zai haɗu dake, Ciwon cikin da kikayi a wannan lokacin bana al'ada bane nine na assasa maki shi, hatta lokacin da shureim Ya taimaka maki kika mike tsaye duk ina atsaye a bakin kofar dakin ina kallon ku.



Akan idona Ya fito daga gidanku Yaje chemist ya siya maki maganin ciwon ciki...


Ba'agabana komai ya faru ba amma nasan dole Ya faru kamar yadda na tsara, Shureim bai san yayi raping dinki ba, kuskuren da yayi shine kusanta kan shi da ke, anan ne nayi masa sihirin daya tayar masa da matsananciyar sha'awar da in har bai sadu dake ba, zai iya mutuwa, shiyasa ya keta maki haddi Cikin fitar hayyaci...." 


Ya ƙarashe maganar yana sakin wata yar iskar dariya.



Girgiza kai ta shiga yi hawaye wasu nabin wasu kan kuncinta wani kululun bakin cikine ya turnuke zuciyarta, sam takasa furta kalma still idanunta a cikin nashi.


Bai damu da halin da take a ciki ba Ya cigaba da yin maganarsa.


"Komai dake faruwa Ina samun information gurin Yan leken asirina, daga cikinsu hada officers din dake gadin gidan ku..." ya faɗa yana ɗage mata gira.


"Hatta kullan da ki ka yi wa kanki da zuwa asibitin da ku ka yi saida naji komai, naji dadi saboda haka ta ta cimma ruwa, na dasa bakin ciki a zuciyar mahaifinki, na jefa ku a tsaka mai wuya, na sanya maku fargaba da zullumi a zukatanku, amma hakan bai gamsar dani ba, saboda nafison In ga yana kuka da idanunsa, nafison in bar masa tabon da zaiyi silar da zuciyarsa zata buga ya mutu..."


 wani kallo take binshi da shi me wuyar fassaruwa.


"Lokacin da Mahaifinki Ya kira shureim Har ya faɗa masa Ya gaya ma Iyayensa abun daya aikata ma yarsa sannan Su zo neman auranta"


"Bai san cewa Alhaji Ubaid baida Iko da kansa ba, na riga da na asirce shi ni nake juya shi son raina, sai abun da na ke so ya ke yi, ko shawara bai Isa yayi da wani ba in ba dani ba, bayan ya kira ni awaya ya sanar dani komai da ke faruwa, naji daɗin yadda hajiya layla taki amincewa, shi kuma da naga yana goyan bayan ya aure ki, saina tunzura shi akan karya kuskara Ya amince shureim Ya aure ki saboda ba mutuniyar kirki bace ke, kin saba min maza, Kina amfani da fuska biyu, ko da naga zai musa min sai nace mashi ina da hujja akan maganata dama najima ina bin diddiginki saboda ina jin labarin fasikancin da kike aikatawa tare da Abokanaina hamshakan masu kudi, Kina jan hankalinsu da surarki, nace masa abun dayasa ma nake bibiyarki saboda bana so ki bata tarbiyar Benazir"


Kallonsa kawai ta ke yi saboda ya kashe mata bakin magana.



"Bayan mun gama yin waya da shi, Na tura mashi hotunanki da video, nasan za ki yi mamakin a ina na same su ko"? Ya faɗa yana yin wata dariyar izgilanci.



Babu alamun zata firta kalma.



"Lokacin da nake kawo maku ziyara a gidan dana kama maku haya a germany, kin tuna lokacin da nake zuwa duk weekend in kwana? Bai jira amsarta ba ya cigaba da maganarsa"tsakar dare nake farkawa a lokacin da na saisaici kinyi bacci, batare da sanin kowa ba nake shiga dakin ki, in hau har saman gadonki, saina na tabbatar da sihirina yayi tasiri akan ki tukunna nake rabaki da kayan jikin shi, in shafeki tass in kuma dauki videos dinmu da hotunan mu, Ummi ta haka nake kawar da sha'awarki dake addabata, Bani da abin kallo daya wuce wadannan hotanan na surar jikin ki, da su nayi amfani bayan na yi editing na canza wasu abubuwan da zaisa a gane fuskata a ciki, sai na tura ma Alhaji Ubaid da hajiya Layla a woyoyin su na tunzurasu akan cewa in har suka bari shureim Ya aureki zasu rasa  takarar su sannan kuma mutuncin su zai zube a idon duniya...." 


labari Ya shiga bata tun daga lokacin da ta kai ma Shureim babynsa da irin gallaza masun da iyayensa su ka yi.


 jikinta har tsuma ya ke yi saboda baƙin cikin daya tokare Zuciyarta, ta karaya da jin irin Bakar izayar da iyayen shureim su ka yi masa shida babynsu.



"komai da suke aikatawa ni nake basu shawara ta bayan fage, Kuma Ina sane na kashe layin wayata saboda nasan shureim zai kira ya nemi taimakona, bayan haka ni ne nayi masa asirin da yaja har hankalinsa ya gushe ya binne Yarinyar da hannayensa...." 



tiryan tiryan Musa ya zayyana mata komai babu abun daya boye mata na daga makircin daya daɗe yana kulla mata.



Kamar numfashinta zai ɗauke saboda tsantsar 6acin rai da fusata, har batasan sa'adda ta wanka masa zafafan maruka akan kuncinsa na hagu dana dama.

har saida wuyan Shi ya nemi jirkicewa amma ko kadan Biji zafin marinta ba.

Damƙe hannayenta yayi a cikin nashi 

Cikin shaƙaƙƙar murya mai tattare da bakin ciki ta furta"meyasa kayi min haka? Me nayi maka dana cancanci wannan ɗanyan hukuncin daga gareka? Duk irin halaccin da nayi maka ka rasa da me zaka saka min sai da wannan? Tsawon shekara goma sha takwas Ka ra bani da kowa nawa, ka shiga tsakanina da mahaifina, ka kuma raba ni da masoyina sannan Ka ɗauke min ƴata? 

Fusge hannayen ta tayi daga cikin nashi, Ta damƙi Kwalar rigarshi Kamar zata doke shi, Ta jijjigashi da karfi, hawaye na cigaba da wanke fuskarta tace"kai wani irin azzalumin mutunne? Mugu mara tausayi mara Imani! Kai mutunne Ko Aljan? Kana da zuciya a kirjin ka kuwa? Wallahi da bakin cikin da ka ƙunsa min da ka sani tun farko ka kashe ni"

 ta faɗa tana bubbuga kirjin shi da hannayen ta.

Dukkan Ilahirin jikinta kerma ya ke yi "Inna lillahi wa'inna ilaihirraji'un, ka kashe ni musa! Ka gama dani! Na mutu!  ta faɗa tare da dafe Kirjinta da yayi mata zafi.

wani irin jirin tashin hankali ne Ya ɗe6e ta tayi taga taga zata kife ƙasa yai saurin miƙa hannu zai ruƙo ta, ta bangaje shi gefe ɗaya, ta dafe handsofa tana jan numfashi sama sama, duk wata addu'a da tazo bakinta karantata ta ke yi duk don ta samu sassaucin radadin da zuciyarta keyi mata wanda zafinsa yafi na ƙunar wuta.

"Zargin da su ke yi akaina ba karya ba ne, Ni ne Jan wuya na gidan Kurkukun ƙaddara, kuma Ni ne na sadaukar da ƴata Unaiza, da ita da yarinyar gurina Twins ne, ko mahaifiyarsu bata sani ba, a ranar data haifesu aranar na sa likitana Ya dauke Unaizah, na kaima Natasha ita don ta raineta, ban taba bari Unaizah tasan wani abu game da dangina ba, Ko sunana na asali, saboda Ina yi mata kallon sadaukarwar da na riga nayi, ni na hana Natasha ta fada bata ba ita ta haife ta ba, na gargaɗeta akan karta kuskura koda gigin wasa Unaizah ta gane ba ita bace mamanta ba, nayi mata kulle saboda bana son ma tafita harta ga abun da zaisa tasan wani abu game dani, hatta wayarta da laptop dinta sai abun da naso take gani a cikin su"

bai ƙare maganar ba, ta katse shi cikin karyayyar murya mai rauni tace "nayi danasanin sanin ka da nayi arayuwata, ban taba ganin fasikin mutun, mara imani, azzalumi irinka ba, ka cuci rayuwar mu, Ka zalunce mu, yar cikin ka ma baka ƙyaleta ba, wallahi kaji kunya Musa, jahilin addini jahilin rayuwa, dabba ma tafika Hankali, kwata kwata baka tsoron Allah. ...." 

bata kare maganarba Ya daka mata tsawa Ko gizau batay ba saboda zuciyarta awuya take komai zata iya aikatawa.

"Ki iya bakin ki In har ba so kike In kashe ki ba.." murmushin takaici tayi"ay ni ka riga da ka kashe ni, me kuma ya rage? kuma bazan fasa Magana ba, ka bugeni sannan ka hanani kuka? Bazai yiyu ba, Allah Ya isa tsakanina dakai, Na tsane ka fiye da yadda na tsani mutuwa ta, sannan inaso ka sani, ba mu ka cuta ba, kanka ka cuta, ka daina farin ciki, wlh rayuwarka ce take acikin bala'e da musifa, saboda Allah baya yafe hakkin dake a tsakanin bawa da bawa, ka dade kana sa6awa mahaliccinka, ina zaka kai ɗumbin zunubban dake akanka, ko ka yi tunanin wayon ka da dubarar ka ne zaisa ka zauna lafiya ko? Sai gashi Yarinyar daka kafurtar ta mutu a musulma, kuma tayi silar tonuwar asirinka, kuma in sha Allah tun agidan duniya zaka fara gir6ar abun da ka shuka....." 

Ƙyalƙyalewa yayi da wata shu'umar dariyar izgilanci, ko kadan baiji zafin kalamanta ba saboda yasan ya riga daya gama da ita.

Matsowa yayi dab da ita yakai bakinsa saitin Kunnanta"kome zaki faɗa akaina, bazan ji haushi ba, ke baki isa ki 6ata min rai na ba, kuma maganganunki baza su sa in karaya ba, saboda nayi nisan da bana jin kira, kiyi tunanin me zai biyo baya Idan mahaifinki Yaji irin rayuwar sharholiyar da kikayi a america tare dani? A cikin shekaru goma sha takwas sau nawa Ina kwanciya dake, Ina biya bukatata da ke son raina" 

runtse idanunta tayi cikin bakinci da ƙunci kamar ta haɗiyi zuciya ta mutu.

"Na sanya maki jarabar da ba za ki Iya jure sha'awarki ba, shiyasa kowani namiji yazo maki da buƙatarsa, kike bashi haɗin kai, ko ya baba Imam zaiji idan yaji wannan? Ga hotunanki da videos dinki da na ajiye awayata! baki tsoron In tura mashi yaga kayan takaici? Watakil ma zuciyarsa ta buga Ya mutu..."

 fashewa tayi da kuka mai cin rai...

Cikin halin Ko in Kula Yace"ba yadda za ki yi da ni Ummi, Na riga dana gama morarki, duk da haryan zu banji na koshi dake ba, zan hakura da ke amma ba zan haƙura da abu biyu ba! Zan barki da ranki sai dai ba zan taba bari Ki auri wani da namiji ba har ki koma ga mahaliccinki, abu na biyu zan barki da ranki saboda na samu abinda na ke so..." 

wani sabon kukan Ta 6alle da shi tamkar ranta zai fita

"Ya Allah kafi kowa sanin wacece ni, ni baiwarka ce mai tsananin tsoronka, Mai jin tsoron sa6a maka, mai gudun duk wani abu daka haramta, me yi maka biyayya, Ya Allah ban ta6a nufin wani da cutarwa ba, amma ni anyi min cutarwar da bazan iya jure raɗaɗin ta ba, Amma ba zan tambayi meyasa ka jarabce ni da wannan mugun bawan naka ba, saboda nasan duk wata kaddara data same mu arayu mai kyau ko mara kyau, daga gare ka ne, kuma ba dan baka son mu ba ne, face don ka jaraba imanin mu, kuma kai kaɗai kasan hikmar dake a cikin kowace jarabawa da ka yi mana, Ya Allah ina roƙon ka da tsarkakan sunayen ka, Ya Allah ina roƙonka don son da kake ma fiyayyen halitta Annabi muhammad SAW  ka bani hakuri da juriyar cinye jarabawar nan"

yayin da ta ke yin maganganun nan yana atsaye gaban ta, ya goye hannayensa Kan kirjinsa, Ba yabo ba fallasa ya ke dubanta.

"Ka fadamin Ina ƴata take? Ina son ganin ta, ina son in san Tana araye ko ka kashe ta"? 

"Tana a tare da ke, Komai da muka tattauna akan kunnan su, Sun ji komai..."

aruɗe ta soma ƴan waige waige tana bin falon da kallo don ta a ina ta ke.

"Ku shigo da su" kamar daga sama Taji ya Umarta..

Nan take ƙofar Falon ta buɗe, Ta ƙura idanunta akan ƙofar, tana jira taga su wanene za su shigo, bata san ya akai ta tsinci kanta da jin matsananciyar faɗuwar gaba.

Tun daga kasa ta soma kallon kafafuwansu da ke a ɗaɗɗaure da Leg irons, aruɗe ta ɗago da idanunta tana kallon masu shigowa, Giants biyu ne suka taso so agaba, sun rurruke damtsen hannayen su.

Bayin Allah Kwata kwata babu kuzari a jikin su.

Idanun su sai lumshewa su ke yi sun kasa tsayar da su abude, gaba daya sun haɗa gumi akan fuskokin su, ɗoguwar sumar kansu  ta yarfo harta saman fuskar su ta rufe idon su ɗaya.

Ido ta zaro a firgice lokacin da taga fuskokin su, tsantsar al'ajabi da ruɗani ne Ya kamata, abun daya ɗaure mata kai tayaya har suka iya shiga gidan Dj suka sato su? Amma da ta tuna matsafi ne, kuma ya saba zuwa gidan dj, batare da wani ya gan shi ba, ta dade tana mamakin hakan sai yau ta samu amsar tambayarta.

Wurgar da su Giants din suka yi, gaba ɗaya suka tafi zasu kifa kasa, tayi hanzarin bangaje Musa Ta nufe su, sai dai kafin ta karasa tuni sun jima da kifewa saman floor, a galabaice, ba su iya taimakon kan su ba saboda hannayen su ma a ɗaɗɗaure suke da sarƙa.

Durƙushewa tayi kan gwiwowinta agaban su jikinta na 6ari take kallon su.

Fuskokin su tabi da kallo ga dai idanunsu abuɗe sai lumshewa su ke yi, sai dai basu Iya motsa koda yatsan su saboda kasalar data kashe musu jiki.

Labbanta na kerma ta furta"Inna lillahi wa'inna ilaihirraji'un! U.. Unaisah... bab... batool.. Ku nake gani dagaske ko idanuna ne suke nuna min badaidai ba? Ku faɗa min tayaya har suka ɗauko ku daga gida"?

 Adabarbar ce ta dubi musa, da wata irin fusatacciyar murya ta furta"don me zaka sa a dauko maka su? Saboda me? Meye haɗinka da su? Laifin me suka maka?  

shu'umin murmushin nan nashi ya saki, da hannu yai ma giants din Alamar su tafi, a hanzarce suka bar falon.

Zukunnawa yayi daga gaban ta

 "wannan matashiyar balarabiyar,  itace ƴar ku ke da shureim, na faɗa maki ne saboda shine hallacin da zan iya yi maki na ƙarshe kafin rabuwar mu"

wani irin faɗuwar gaba taji kamar saukar aradu a sukwane take duban fuskar Batool da tsantsar al'ajabi tace

"kana nufin itace Ƴata"? Jinjina mata kai yayi"itace..."  

ta rasa farin ciki zatayi ko bakin ciki? 

Yatsun hannayenta na kerma Ta tallabo kan Batool ta daura saman Laps dinta, ashe ba banza ta ke ganin kamannin ta da shureim ba, ashe yar su ce, lallai rashin sani yafi dare duhu, yarinyar data mutu akan sonta, ta kwallafa rai akanta, ashe tana atare da ita batare da ta sani ba.

Cikin raunanniyar murya ta ce

"na kasa yarda cewa kece Ƴata Batool, Jinjirar dana bari a cikin tsumma, jinjirar da aka fadamin ta mutu! Ashe tana araye kuma itace yarinyar da nake atare da ita? na daɗe ina Mamakin kamannin ki da ya shureim, Tun kan nasan wacece ke Allah ya jarabce ni da ƙaunarki, kuma kema haka, ashe ke din gudan jinina ce"!

ta faɗa tana shafa fuskarta,  wata kerma da jikin Batool ke yi kamar wadda sanyi ya kama, siraran hawayen da ta gani suna sintiri kan kuncin ta ne ya tabbatar mata da taji komai da ta ke faɗa.

A hankali ta ɗago da kannata, ta kwantar da shi kan kirjinta, ta rungumeta sosai, wani irin yanayi suka ji a tare da su.

soyayyar da suke ma juna ta ƙara nunkuwa fiye da ta.

Komai dake faruwa akan Idon Musa, Unaisah dai batasan meke mata daɗi ba, ta kasa juyar da kanta balle taga meke faruwa, sai dai komai da suke fadi a cikin kunnanta, idanunta sun cicciko tab da ƙwalla, gata ga mutumin da take nema ruwa ajallo sai dai ba za ta iya ta6uka komai ba.

"Ka faɗamin me ku ka yi masu dayaja har suka rasa ƙarfin jikin su"

 idanunta jawur ta fada tana kallon shi.

"Allurar maye ce nasa akayi ma su.." 

Cike da takaici ta watsa mashi harara, kafin ta mayar da idanunta akan Batool.

"Nasan Kin ji komai daya faru, ba yin kaina bane, Ki yafe min, na tafi na barki ban kula da rayuwarki ba, kiyi hakuri, kada ki tsane ni, wallahi Inasonki fiye da komai na duniyar nan, har raina zan iya sadaukarwa saboda ki rayu"

 Kalamanta sun karya zuciyar Batool da Unaisah.

"Ko ban faɗa ma ki ba, kin san na so ki tun kafin nasan cewa ke jinina ce" 

Batool tana ta Ƙoƙarin ta buɗe baki don tayi mata magana sai dai takasa, kamar za ta yi hauka.

Unexpected Taji Musa Ya damƙi hannun Batool da karfi ya soma ƙoƙarin rabata da ita, a firgice ta ƙanƙameta ajikinta, ji tayi kamar ranta zai zare daga gangar jikin ta.

"Kada ka rabi da ita, Ka barmin diyata, Ni na haifi abuna.." ta fada tana kara matseta a kirjinta.

"Haihuwarta ka ɗai ki ka yi amma ni ne na yi silar samuwar cikin ta, daga ita har yar uwartata, saboda itama saida na amince tukunna kakanta Ya amince uwarta ta auri ubanta har suka same ta, don haka dama can su nawa ne halak malak, ni ne na sadaukar da su kuma Yanzu Ina buƙatar su, don Haka ki cire rai da su, karma Kisa ran zaki sake ganin su..".

maganarsa ta ɗaga hankalinta.

Kokawa suka kama yi, Yana jan Batool tana jan ta kamar zasu rabata biyu, batai aune ba, taji An rurruke hannayenta ta baya da karfi suka janyeta,  a razane ta dubesu tana haki, Giants ne Guda biyu karfafa.

 Numfashinta kamar zai ɗauke, Zuciyarta sai tafarfasa takeyi saboda kunar da take ji..

Ta naji tana gani giant dinnan suka dinga janta, tana ta kokarin ƙwace kan ta amma takasa saboda sun fi ƙarfinta.

Musa da ke kallonta, murmushin mugunta ya ke sakar mata, ya rurruƙe Batool da hannayensa..

Akan Idonta ta motsa dry lips dinta dakyar da wahala ta furta"mom.. Myyyy..." 

Duk da sauti bai fito ba, amma ta fahimci me tace, fashewa tayi da kuka tadinga yakunshin su da kai masu bugu amma duk abanza ahaka har suka fitar da ita daga cikin falin.

Suna jiyo sautin kukan Ummi acikin kunnuwan su.

Jefar Da Batool yayi ta faɗa kan Unaisah.

baisan meyasa ya kasa cire Ummi aran shi ba, Kukanta yana Illata Zuciyarshi sai dai baya jin zai iya hakura da burinsa akan Yaran, dole Ya salwantar da su don Ya Cika burin shi, bama zai ta6a bari Ta rayu da yar shureim ba, tun da har taki ɗaukar cikin sa, dama da haushin zubar da cikinsa da tayi abaya.

Wayarsa Ya zaro Ya kira wani layi, bayan anyi picking ya furta"Mark, Kasa driver Ya kaita Obie Estate, kada ya ƙarasa da ita ciki, ya aje ta akan titin estate din"

"kai kuma ka shigo Ciki, bana so mu 6ata lokaci, zasu iya farmakar mu a kowani lokaci, nafiso mu hanzarta kai su Gidan Kurkukun ƙaddara, kafin su ritsa damu"

"Okay Sir," rejecting call din yayi, tare da mayar da hankalinsa akan Su Unaisah dake a yashe kasa kamar matattu wata mahaukaciya ya saki hahhhahahaha...

babu wani mahalukin daya isa Ya dakatar dani!

 ya faɗa yana yiwa kansa kirari.

Welcome, Littafin kurkukun ƙaddara 500 ne, dukanshi Book One two and 3 Idan kin shirya biya ga Details da zaki tura

3196407426 

First bank 

Bature Hafsat Muhammad,

 *bayan kin tura zaki bada transaction reciept ko screenshot na debit alert a matsayin shaida ta wannan number din 08103884440*

Post a Comment

Idan kuna da tambaya akan abinda Baku game ba ko kuma kuma Neman littafin da babu a nan kawai ku ajiye tambayarku a ta comment ko wani shawara da Zaku bamu.

Previous Post Next Post

Sponsored Link

Sponsored Post