Kurkukun Ƙaddara Takun Ƙarshe Page 80 Complete

Kurkukun Ƙaddara Takun Ƙarshe Page 80 Complete

Takun Ƙarshe

DAGA ALKALAMIN BOSS BATURE✍️💋

Around ƙarfe Goma na dare Motar Taj ta ƙaraso layin gidan Alhaji Musa, baka jiyo sautin komai saina dariyar su da firar da su ke yi cikin nishadi.

Officer ne ke yin driving dinsu, yayin da su ke a mazaunin baya na motar, dawowar su kenan daga Sightseen, a hankali officern ya tsayar da motar kusa da gidan.

"Kin faranta min rai, gaskiya dana rasa ki danayi danasani Ummu Unaisah" farfari tayi mashi da idanun ta..

"Ni yakamata nace haka babe, kwanakin nan dakyar nake bacci saboda tunaninka, jurewa kawai na ke yi amma wallahi nakosa ka maidani ɗakina.." ta fada tana zumbura mashi ƙaramin bakin ta.

Har wani lumshe idanun shi ya ke yi idan suna kallon juna, cike da shauki,  da alama Taj ya manta data gida daya baro, ko maganarta bai son yi agaban Benazir, bai ta6a gigin sanar da ita yayi aure ba saboda yasan halin ta da kishin tsiya.

"Ki sauka zamu juya, na bar yara suna jira na, nasan ba lallai suyi bacci ba" ya faɗi hakan ne ba dan ya gaji da ganin ta ba, sai dan saboda yanayin da take jefa shi.

Maƙe kafaɗa tayi da shagwa6a tace"ai wallahi idan kana so in sauka sai ka yi min kiss" yadda tayi maganar kamar karamar yarinya.

ga dukkan alamu sun manta basu kaɗai bane a motar, Officer yayi zuru yana satar kallon su ta mirror gwanin burgewa.

"Pls, dare yana ƙara yi, nasan su mommy suna ta jiran dawowarki"

 rigima tasaka mashi har sai da tasaka shi dariya.

Saida ta bari ya shagala yana ta tikar dariya tay wuff ta manna mashi kiss on his lips, zare idanu yayi kafin ya farfaɗo daga duniyar shaukin da ta jefa shi, tayi saurin buɗe murfin motar ta fuce da dan gudunta ta nufi Gate din gidan tana dariya benazir kenan hali na nan ya fada a xuciyarshi tare da girgiza kai.



Gaba daya takashe mashi jiki, langwa6ar da kansa yayi jikin seat dinsa, tare da lumshe idanun shi, kamshin turarenta ya cika hancin shi, komai daya faru yau a tsakaninsu yake tariyowa, murmushin gefen fuska ya saki a hankali ya furta"I love you my Benazir, my hero wife, mother of my precious daughter..." 



Har Officern ya tada motar yayi reverse taj bai sani ba, gaba daya ya shagala da tunanin Benazir kamar ba yanzu suka rabu ba.




Adaidai Lokacin da motar shi Ta ƙaraso main gate, sai ga Motar Chief Owais ta nufo bayan tashi, A jere suka ƙarasa shiga Gidan at same time su ka yi parking.



Taj ne ya fara fitowa ya na ɗangyasa ƙafar shi, ya nufi Motar Chief Owais tare da buɗe masa Cardoor, fitowa yayi jikin shi sanye da jallabiya Ya mika ma Taj Hannu su ka gaisa.


Har sun juya zasu nufi main falo, muryar Security Officer ta katse su da ɗan saurin shi Ya nufo su tare da sara masu kafin Yace"barka da dawowa Sir, ɗazu bayan sallar magrib, Big guy yazo.." bai kare maganar ba ganin wani kallon kallon da suke jefawa juna shida taj kallo mai cike da tsantsar rudani..


Har suna hada baki gurin furta"Big guy? Wani big guy din.."


 washe baki security Officer din yayi"big guy namu, ddg, Omar, da kanshi yazo a cikin motar shi.."



 aruɗe Taj yace"ban gane me kake nufi ba? Omar wanda yake a kwance gadon asibiti Yana a coma ko kuwa wani Omar din ka ke nufi..." 


da jin wannan maganar yasa Officer din ya ɗan ruɗe.


"sir, kana nufin bakusan komai game da samun lafiyar sa ba? Amma ya fada mana kun sani har yace may be saboda sirrin aikinku yasa baka sanar damu ba.." 


Tsantsar Al'ajabi Ya hana Chief furta kalma..


Adabarbar ce Taj yace"da yazo ya shiga ciki, ko kuwa a bakin gate ya tsaya.." 



arude officer din Yace"sir, ya shiga Ciki..." ba su karasa sauraron shi ba, cikin sauri suka nufi main falo, Taj tuni ya manta da ciwon kafarsa, saboda tashin hankali.



Abun daya daure masu kai, sunsan Omar bai farfado daga Coma ba, don da ace ya samu lafiya sune mutun na biyu da zasu sani bayan docs din dake kula da shi.



Suna shiga falon suka nufi dakin Su Unaisah tsabar sauri da rawar jiki har bangazar juna su ke yi a sukwane suka ci burki lokacin da suka dira kofar su cikin daki basu taras da kowa ba..



Wani irin matsanancin faduwar gaba su ka ji a lokacin daya suka zaro wayoyin su daga cikin aljihu..


Miss calls suka gani na Unaisah 


Sakon data turawa Chief ne ya  bayyana akan screen din wayarsa.




_"Husband to be, yaya omar yazo zai tafi da mu asibitin da aka kwantar da yan uwan mu inmates, don mu duba lafiyar su,  Ni dai hankali na bai kwanta da shi ba, ya matsa mana sai mun bi shi, kuma kamar ba ya omar ba wallahi, Muryarsa ƙatuwa, idanunsa jajaye, kuma ko tabon ciwo babu ajikin shi, kasan da zuwan shi? Mu bi shi ko mu tsaya"?_



A razane suka kalli juna, bayan da suka gama karanta sakon Unaisah.



"Sir, Ko dai Umar din ne? Tun da in bashi bane Security Officer ba zasu taba bari ya shigo ba, sannan kofar falo tana da tsaro dole sai na'ura ta tantance shi zai iya shigowa ciki, in har ba umar bane bazai taba iya shigowa ba.." 


girgiza kai Chief owais yayi"Taj, ba Omar bane, ka yi tunani mana, in omar ne meyasa ba akira an faɗa mana ya farfado ba? Omar koda ace ya farfado daga Coma Ina yaga karfin da zai iya tuƙo mota yazo estate din nan? Motar wacece? Gaba daya motocin Omar suna A parking space, Taj bana fata abun da nake tunani ya tabbata .." 



Yana ƙarashe maganar, ya juya da sauri Taj yabi bayanshi kaitsaye suka nufi security Officers tunkan su karaso Officers din suka nufo su cike da fargaba saboda Officer din daya fara tarar su  da maganar ya sanar da sauran  akwai matsala.



"Sir meke faruwa"? Cikin 6acin rai yace "tayaya akai kuka bari Ya shigo batare da iznina ba huh? Har suna haɗa baki gurin furta"Sir, Omar ne, tayaya zamu hana shi shigowa? Bayan yana da ikon yin komai a cikin gidan ka, kaine kace babu banbanci atsakanin ka da shi..." 



dafe kanshi yayi da hannu ɗaya"baku da hankaline? Ba mun fada maku Omar baya acikin hayyacinsa yana a gadon asibiti har yau bai farfaɗo daga coma ba.." 




faɗa ya balbale su da shi ta inda yake shiga batanan Yake fita ba, Taj sai kokarin Shawo kanshi ya ke yi Yaƙi sauraron shi.


Hankalin su ba karamin tashi ya yi ba, tun da suke da dg basu taba ganin bacin ransa irin na yau ba.


"Wallahi Sir Omar ne, idan har ba Omar bane tayaya zamu barshi Ya shiga ciki, kuma tayama zai iya shiga batare da na'ura ta tantance shi ba? Sir ba yau muka fara maka aiki ba, mu fa amintattunka ne, bamu taba maka karya ba, kuma bamu ta6a cin amanarka ba, muna yin iya kokarin mu don ganin mun ba ku tsaro, tsakani da Allah muke atare dakai da zuciya daya, Omar ko a mafarki muka ganshi zamu gane shi balle kuma a zahiri"_




"In har Omar din ne meyasa ku ka bari Ya tafi da su Unaisah batare da kun kira kun sanar dani ba"?



Zazzare ido su ka yi cikin rudu da tashin hankali kwata kwata basu san ya tafi da yara ba.



"Sir ya tafi da su? Amma tayaya akai ba mu gani ba"?




"Ni kuke tambaya? Saboda ganganci da rashin kula irin na naku Har wani bare Ya shigo min gida, Ya tafi da yara har biyu duk baku sani ba, baku da amfani, Gidan Dg da aka sani da tsaro..."



 Taj sai kokarin lallashin shi ya ke yi Yaki ma Ya dube shi.



Yana magana Huci na fita"tsawon wani lokaci ya dauka kafin tafiyarsa"?



Cike da jin shakkarshi wani Officer Yace"ya yi mintuna shabiyar a ciki, bamu san lokacin daya fito ba, sai dai muka ga babu motarsa a inda ya yi parking ɗin ta, kuma da tafiyarsa yanzu awa ɗaya da rabi"



 Runtse idanunshi yayi tare da ɗaura hannunsa ɗaya saman kan shi..


"Wallahi, Idan har wani abu ya faru da su, ku kuka da kanku.."


 yana faɗa ya juya cikin zafin nama Taj yabi bayan shi..


Cikin rudu da tashin hankali wasu daga Cikin officers din suka shiga motocinsu da wata irin jiniya suka fice don suje neman Omar.



Daga gaban Motar shi ya tsaya tare da kiran layin doc din dake kula da Omar, bayan ya daga cike da fargaba ya tambayi ya jikin Omar"? 


Doc din yace"har yanzu bai farfaɗo ba, amma muna ganin cigaba a lafiyarsa, kuma muna sa ran zai iya farfaɗowa a kowani lokaci..." 



da jin maganar da doc din ya faɗa nan fa hankalinsu Ya ƙara tashi..


Jikin Taj ya hau yin kerma


"in kuwa hakane, Koma wanene ya ɗauke su zai iya yiyu wa daga Elders ne, tun da har ya iya sauya kamannin shi, hakan na nufin matsafi ne, amma tayaya za'ay mu san wanene Ya ɗauke su? chief ne ya jefa ma kanshi tambayar da bashi da amsarta.



Damuwace tsantsa akan fuskar taj "inna lillahi wa'inna ilaihirraji"un bana fata hakan Ya kasance saboda nasan ba zasu masu dakyau ba, da nasani ban tafi nabar su ba, laifina ne, da duk hakan bata faru, rashin sani yasa dukan mu bamu ga 

kiran Unaisah ba, ni nasan tayi iyakar kokarinta donta same mu  awaya,  kuma inaji raina ba hakanan aka tafi da su ba, saboda Unaisah tana wayou dole akwai wani abu da akayi masu..."



zafafan hawaye ne suka wanke Fuskar shi, ga wani zazzabi da ya rufa sa.



Sum ma rasa ta ina zasu fara binciken wannan al'amari? Wanene Ya dauke su? Meyasa aka sace su? Da wata manufa akayi hakan? Me kuma zai biyo baya!.


Babu wani mai kwanciyar hankali a cikin su, sam sun manta da batun Ummi.



Taj Ne ya kawo shawarar Su jaraba Bin diddigin Layin Unaisah, yana tunanin Ta tafi da wayarta tun da basu ganta a dakin su ba.



A hanzar ce Chief Ya fara ƙoƙarin yin tricking din layin ta ta hanyar wayar sa, sai dai bai Iya gano komai ba duk ƙwarewar sa.



Har Number dinta Ya turama wasu Cyber Experts daga Cikin jami'an su, amma daga baya suka kira tare da sanar da shi sunyi iyakar bakin kokarinsu don ganin sunyi hacking layinta, amma sun kasa gano taƙamaimai location din da wayar ta ke, suna tunanin tana a gurin da babu network ko kuma an jefar da wayar wurin da baza a iya tracking ba.



bakin Ciki ne Ya cika Zuciyoyin su.



Daga shi har Taj an rasa me lallashin wani kowa Ya shiga damuwa.



Tunanin komawa Cikin gidan su ka yi don su kara bincikawa su tabbatar babu su din don jin abun su ke kamar ba gaske ba.



Babu inda basu duba ba, suma officers din gidan sun tayasu neman su,  babu su babu alamar su, Kowan nan su sai da ya haɗa gumi akan fuskarsa.



Falo suka koma su biyu shida Taj suka zauna saman Sofas kowan nan su ya zabga Uban tagumi kamar marasa galihu.



Unexpected suka tsinkayi sautin tafiya, kusan atare suka kalli Mai shigowa cike da sa ran su Unaisah ne.



Kamar mahaukaciya ta faɗo Falon, Ko takalma babu a kafafunta, fuskarta jaga jaga da hawaye, idanunta sun kumbura suntum, gyalenta ma A hannu Ta ruke shi, har suna haɗa baki gurin ambaton Sunanta UMMI..



Kusan atare suka mike suna Kallonta ganin Yadda ta sauya lokaci ɗaya kamar wadda tasha bugu.



Kaitsaye Ta nufi Chief Tana karasawa gaban shi, Ta zube kan gwiwowinta, kamar zata haukace masu, Cikin Kuka da wata irin raunanniyar murya ta furta"zai.. Zai kashe su! Shine Ya ɗauke su! Suna a wurin shi, Kashe su zai yi..." gaba daya ta ruɗar da su sun kasa gane kan maganarta.



Faduwar gaba suka ji, daram dararam,  a razane suka kalli juna.



"Ummi ki yi mana bayani meke faruwa? Su wanene zai kashe? Kuma wanane kike magana akai"?



Cikin shasshake murya tace"U..U..Unaisah, da Bab.. Ba tool, Ya faɗa min komai, Ya cuce ni, ya yaudare ni, shiya rabani da mahaifina Ya kuma rabani da kowa nawa, Batool diya ta ce, Ita ce babyn dana bari, bata mutu ba, tana araye, shiya sadaukar da su yanzu kuma Ya kara ɗauke su ....." 



Tsantsar tashin hankali ne ƙarara akan fuskokin su, Sun riga da sun gane wanene Ya ɗauki su Unaisah, dama sunata hasashen zasu kawo masu farmakin bazata, ba zasu ta6a kawo ma ransu ta kansu Unaisah zasu biyo ba, Wlh sun shammace su, ga kuma Mamakin kasantuwar Batool diyarta.


"Ummi Ki natsu ki fada mana komai da kuka tattauna da shi, watakin mu samu ta hanyar da zamu iya ceto rayuwar su, mu kan mu bamusan tayaya akai suka dauke su ba, saboda ba mu a cikin gidan"



Dakyar ta iya fayyace masu komai da Alhaji Musa ya faɗa mata.


Ba su yi mamaki ba saboda sun riga da sun san komai itace bata sani ba, abun da yafi bakanta ransu ta yadda ya bayyana mata komai da yayi mata batare da tunanin wani hali zata shiga ba.



Kwata kwata basu tambayeta meyasa tayi gangancin daya gano ta ba, duba da halin da take a ciki ba.



Haɗuwa sukayi atare suna Lallashinta tare da yi mata alkawarin zasu yi iyakar bakin ƙoƙarin su don ganin sun Ceto rayuwar su.



Dakyar suka shawo kanta, Taj Yace Ta shiga ta kwanta, ta huta.



Tace mashi ita da hutu Har abada, bata tunanin zata iya rayuwa batare da Yar ta ba, don basu san me take ji a cikin zuciyarta ba.



Tsananin tausayinta ne Ya kamasu, kamar zasu zubda mata ƙwalla.



Tace ma Taj ya ara mata wayar shi, Tana son tayi kira.

Ya tambayeta wa zata kira?

Tace Ya shureim tana son Ta fada masa komai.


chief Yace tayi hakuri ka da ta daga mashi hankali, Ta bari su fara samun mafita tukunna


Kuka tasaka masu tare dayi masu magiya tana rokonsu akan su bata ta kira shureim tana son ganin shi tana son ta nemi yafiyar shi, sannan tana so ta faɗa mashi game da babyn su.


Ƙin amincewa su kayi, gaba daya ta rikice masu kamar ta fara fita hayyacinta sai sambatu ta ke yi masu, can Kuma data galabaita wani matsanancin ciwon 6arin kai Ya taso mata, ta fara ganin jiri jiri tun tana karanta addu'o'i harta kasa, ta fada masu kanta ciwo yake mata, kirjinta zafi, numfashinta zai ɗauke.



da sauri chief ya juya yaje medical room din gidansa ya ɗauko mata sedative, ya dawo falon tare da Glass of water a hannunsa ya mika ma Taj ya kar6a tare da miƙa mata maganin hannunta na kerma ta kar6a ta tura abaki, ya kanga mata ruwan ta sha, har saida takusa ƙwarewa kamar za ta yi amai ta kama kakari.



sun bata maganin da nufin ta samu tayi bacci amma sai ya zamana kamar sun ƙara ninka mata azabar radadin da take ji, baiwar Allah kamar ƙaramar yarinya ta dinga rusa masu kuka tana ambaton sunan Baba imam, shureim, Babynta.



Har tambayar ta su ka yi ta fada masu address din Guest house din sa, tace bata sani ba, sau biyu ta ta6a zuwa, kuma duk zuwan da zatayi shi ya ke zuwa ɗaukarta da motar shi, baya bari drivern daya ɗaukota ya karasa da ita, ba zata iya gane komai ba, ko sunan anguwar bata sani ba.



Gudun kada ta hadiyi Zuciya ta mutu Yasa suka yanke shawarar bata wayar donta kira su, bayan Taj Ya nuna mata Contact din su a wayarta yace ta kira su ta ce su zo amma kada ta fada masu meke faruwa ta bari sai sun zo.



 dama Suna da burin Su sasanta tsakaninta da Mahaifinta, kuma a wannan ga6ar tana bukatar su saboda su kadai ne zasu lallasheta taji don wlh gab ta ke da ta zare.




Chief bai ga ta zama ba, yace ma Taj Ya kula da ummi, shi zai tafi tare da jami'ai su nemo su, Taj yace bazai iya zama ba, ƙwara su tafi a tare, saboda Hankalinsa ba akwance yake ba, in har ba dawo da su Unaisah akayi ba.


Chief yace ya kwantar da hankalinsa in sha Allah ba abun da zai faru da su, amma ba yadda za'ay su tafi da shi saboda har yanzu ƙafarsa bata daidaita ba, kuma gurine mai hadari zasu je, Taj yana sharar kwalla yace"bazai gane ba, tayaya ma zai iya kwantar da hankalinsa bayan yaransu suna a hannun fasiƙin mutumin da babu imani a zuciyarsa? Wa yasan me zai yi musu? Dakyar Chief ya lalla6a shi harya amince zai zauna badan yaso ba.




*Dr. Shureim💔*



Bayan ya kammala Yin Nafila Ya buɗe kur'ani yana karantawa, wayarsa ce ta soma yin ringing, saida yakai aya, Ya dubi wall Clock Karfe shabiyu, Aransa ya ayyana wanene ke nemansa a irin wannan Lokacin? Ko dai na cikin gida ne"? Mikewa yayi daga kan prayer mat din, Ya nufi wayar dake aje kan gadon nasa.


Daukar wayar yayi da rudu Yake kallon bakuwar Number din da aka kirasa da ita.


Baisan wanene ba, Kuma ba ya jin zai iya picking call at this time duk da wani sashe na zuciyarsa yana shawartarsa dayabi bayan kiran.


Har zai aje wayar wani Kiran ya kuma shigowa.


Picking Yai tare da kara wayar Yana kokarin Yin sallama, kunnuwansa suka jiyo masa sheshshekar kukan mace ta cikin wayar, gabansa ne ya fadi


Bai gane wacece ba, addu'ar neman tsari Ya karanta a cikin zuciyarsa kafin Ya yi sallama tare da tambayar wacece?


"Ya shureim ni ce, Aishatu bintu imam ce.." 



sa'ilin da muryarta ta ratsa dodon Kunnansa wani sanyi mai haɗe da dadi yaji a cikin Zuciyar shi, kamar wanda akayiwa albishir da gidan Aljanna


Adabarbarce Ya furta"Aisha dagaske kece? Ba mafarki nake ba? Ke da kanki kika kira ni"? 



"Ni ce Ya shureim, Ba mafarki bane..." bai karasa jin zancen nata ba Ya zube kan gwiwowinsa Ya fuskanci alkibla yayi sujudusshukr..


Time din da ya dago Hawaye farin ciki ne a kwance saman fuskarsa ga wani tsantsar annurin farin Ciki daya bayyana a tare da shi.


"Aisha, har yanzu Ina kokwanto.."


"Ya shureim, Inason ganinka! pls ka zo, idan ba kazo ba zan iya rasa raina, kai kawai nake son gani.." 


muryarsa da zumuɗi ya firta"basai kin rokeni ba, Zanzo yanzu, Karki damu, ki kwantar da hankalin ki.." 


Katse kiran yayi, jikinsa na 6ari  Ya dauki Car key nasa, cike da zumuɗi ya fito Jikinsa na bari cikin sauri Ya nufi Hanyar fita daga Main falo..


Kafin Ya ƙarasa Ya tsinkayi Muryar Benazir a cikin kunnansa.


"Ya shureim!..." ba dan Benazir ce ta kirasa ba da ba abun da zai hana Yaki waiwayonta..


Juyowa yayi fuskarsa da fara'a ya ke duban ta, sanye take da kayan bacci riga da wando maroon tayi rolling headscarf, sai da ta matso kusa da shi Ya lura da wayar dake a hannunta, Fuskarta duk a yamutse.


Car key din hannunsa Ta kalla"ya shureim Ina za ka je da daren nan? Ka duba lokaci kuwa? 


Murmushi ya yi"Ki taya ni Murna Ukhtyna, Aisha ta kira ni yanzun nan awaya, tace tana son ganina, Inzo gidan dg"



 aruɗe ta furta"Aisha kuma? Ya shureim yaushe aisha ta sauko daga kan dokin zuciyar da ta hau da har zata kira ka? Ka kuwa duba kaga ita dince ta kira ka dagaske? 



"Bakuwar Number ce amma Tabbas Aisha ne, Ni naji muryarta.."



 "Muga number din" ta fada tare da mika masa hannu bayan Ya bata wayar ta dubi contact din nan take ta gane Number Taj ce.



"Yanzu Can zan tafi, tana jira na"



"Yaya shureim dagaske Aisha ce, number data kiraka da ita, ta Daddyn Unaisah ne amma meyasa take son ganinka a irin wannan lokacin?  Ta faɗa da rudu akan fuskarta.


"Kada ki tsayar Dani Benazir, ki bani kawai in tafi.." ya fada yana mika mata hannu..


Tana kokarin mika masa wayar, suka tsinkayi Muryar Mami a cikin kunnuwan su..


"Su wanene nan"? Ta fada tana nufo su, atare suka dube ta, Damuwace ta bayyana akan fuskar Shureim har saida Ya harari Benazir ganin taja masa har mami tagansu yasan ba lallai tabar shi Ya fita ba.


Ƙarasowa tayi daga gaban su ta tsaya"meya ke faruwane? Ina kuma zuwa? Ta fada tana nuna key din hannun dr shureim..


Kamar marasa gaskiya sukayi shiru suna kallon kallon atsakanin su..


Hakan Yasa ta fahimci da akwai wani abu dake faruwa kuma basa son sanar da ita..


Har ta buɗe baki zata kuma yin magana phone ringing din Dr shureim Ya katse mata hanzarin ta, ganin number da Aisha ta kira ne yasa shi saurin yin picking..


"Ya shureim ka taimaka min ka zo, naji komai daya faru, bayin kanka ba ne, akwai abun da nakeso in fada maka dan Allah kazo, magana ce mai muhimmanci"


Waro idanu waje su ka yi gaba ɗayan su sun ruɗe sosai, daga mamin har Benazir din sunji komai, basu karasa jin ƙarashen zancen ba kiran ya katse..


Arude Mami Ta kar6e wayar shureim tadinga kiran layin ba'a dagawa, kallon su tayi cikin rudani tace"ku fadamin wacece wannan ɗin? Meyasa take neman ka? Akan me take yin magana? nasan kun sani, kada ku 6oye min ku fada mun kawai in ba haka ba zan sa6a maku.."


 Ta karashe maganar kamar zata doke su..


Ran mami Ya 6aci jin sunyi shiru basu Bata amsa yasa ta daka masu tsawa"wai don ubanku ba zaku bani amsar tambayar da nayi maku ba? So kuke ku haukatani ne..." cikin rawar murya Benazir ta ce"aisha ce mami, kiyi hakuri mun boye maki, amma Aisha ce, tana agidan Dg, Kuma Yarinyar nan Azeezaty, bakowa bace face Unaisah ƴata Angel, mahaifinta kuma shine Taj mijina...." 



wani faduwar gaba Mami taji, sai zare idanu takeyi saboda al'ajabi..


Ruƙe Hannunta Benazir tayi"mami zanyi maki bayanin komai, mu ma bada son ranmu muka 6oye maki ba, Dg ne yayi mana warning akan karmu sanar da kowa game da su saboda Rayuwarsu tana acikin hadari, bazai yiwu a yanzu in fayyace maki komai ba, amma dan Allah mami kuzo mu tafi can gidan, zaifi mu hadu mu duka kowa yaji komai dake faruwa, Saboda Inaji araina Akwai wani abu dake faruwa shiyasa Aisha takira shureim ta nemi da ya je, kuma dama suna bincike akan case din daya shafe mu da kuma shi Taj din..."  



Cike da zumuɗi Mami Tace toh, bari in ɗauko hijabi

Cikin sauri Ta nufi daki, tana shiga ta taras da Alhaji Ubaid Yana kokarin fitowa daga toilet, koda ya tambayi daga ina take? Tace mashi Ya biyota kawai su tafi, akwai wani  babban al'amari"


Badajimawa ba, sai gasu sun fito tare da Alhaji Ubaid din, sai tambayarta yake ina za su je cikin daren nan?  tace mashi Yabi su kawai in sunje zai gani, da yaga Benazir da shureim Hankalinsa Sai ya kara tashi, bai dai tambaye su ba, yabi bayan su Suka fito daga Falon, Cikin sauri suka nufi Parking space, gaba dayansu a motar Dr shureim suka zauna, Hajiya Layla da Alhaji Ubaid suna a backseat, Benazir tana a front seats tare da Dr shureim.



Key ya yi ma motar, tare dayin riverse Ya nufi Gate, sam Sun manta da Security Officers, aikuwa suna hango motarsu suka Tunkareta gadan gadan..

Hajiya layla tace karya kuskura ya tsayar da motar zasu 6ata masu lokaci ƙarshe su hanasu fita, tun da gate din a buɗe yake da alama wasu ne suka fita aka bude ba a kaiga rufewa ba ya fuce da su kawai.


Alhaji ubaid yace kada ay haka su bi komai a sannu.


Dr shureim dayafi su zumudi ya kure speed din Motar, Gadan gadan Ya nufi Security Officers din kiris Ya rage Yabi takansu da mota Hakan yasa suka dare tare da bashi hanya, Ya ba motarshi Wuta Ya kara gaba.



Wasu daga Cikin Security Officers din Har bin Motar shi su ka yi sai dai tuni sunyi musu nisa.


Sai da ya tabbatar da sun 6ace masu sannan Ya rage gudun Motar.


Wayar Benazir ce ta soma ruri cikin sauri Ta duba Mai kira ganin Anila yasa ta yi picking tare da kara wayar a kunne


Tana niyar yi mata sallama kukan Anila Ya katse ta, 

Arude Ta furta"Anila? Meya faru? Meyasa kike kuka"? 



Maganar da tayi ne ta karkato da hankulan su Hajiya layla ga kallon su.



da wata irin raunanniyar Murya ta furta"Benazir, Muna cikin tashin hankali, Uncle Ya kashe ta, mun ga gawarta, yanzu haka da na ke yi maki magana gidan mu a kewaye ya ke da sojoji"


Dafe kirji Benazir tayi"Inna Lillahi wa'inna ilaihirraji"un..."


"Menene? Meya faru? Benazir meke damun ta ne? Me ta fada maki"? Su mami ne Suke ta tambayarta Cikin rudu..


"Bani kadai bace Anila, Ina atare da su mami, Yanzu haka Muna akan hanyar zuwa gidan Dg, Aisha ce ta kira ya shureim tana kuka ta bukaci tana son ganin shi ina tunanin wani abu yana faruwa acan, in ba damuwa mu haɗe acan.."



Ta amsa mata da toh

Bayan tayi rejecting Call din ta dubi Dr shureim da ke kallon ta kafin ta mayar da dubanta ga su mami da ke abaya.


"Anila ce, ta fada min wani abu ya faru agidansu, bana iya jin me take cewa kamar kuka takeyi, Amma nace mata mu hadu a gidan Dj nasan zata zo"



Cike da fargaba suka amsa mata da toh kowa da abunda ya ke saƙawa A cikin ran su..


Lokacin da motar su ta haura kan Titin Obie Estate, Cikin sauri Benazir ta kira layin taj, bayan yayi picking ta fada mashi game da zuwan su, tace ya taimaka yayi masu hanyar da zasu shigo cikin sauki, ya ce mata kada su biyo ta gate din gaba, su shigo ta gate din baya na estate din, zai sanar da securies din.


sallama su ka yi da shi, bayan ta fada ma dr shureim abun da ya ce, Ta yi shiru zuciyarta cike fal da fargaba, Muryar Taj da taji ta daga hankalinta kamar baya a cikin nutsuwar shi.


ta gate din baya suka shiga Estate din  basu sha wahala ba, saboda already Taj Ya sanar da securities din game da zuwansu..



A parking Space dr shurem ya yi Parking din Motarsa.


Bayan sun fito, Hajiya layla ta dinga jinjina kanta, ganin haduwar tamfatsetsan Gidan dg, tayi zaton daga gidan Alhaji musa an gama Gini mai kyau  a Abuja sai yau da Allah Ya kawota gidan Chief.



Shi Kanshi Alhaji Ubaid Ya jinjinama haduwar Villa din..

dr shureim ne ya fara yin gaba jikinsa sai tsuma yakeyi saboda zumuɗi, da sauri suka Bi bayan shi.



Basu kaiga ƙarasawa ga Kofar Ba, Horn din mota Ya katse masu hanzarin su, sunyi tunanin su Anila ne Hakan Yasa suka dakata tare da juyawa suna kallon Motar da ke shigowa da matsakaicin gudu ta nufo Entry Hall sai da takusa ƙarasowa inda suke suka ga gudun nata Ya ragu slowly ta yi Parking daga gefen su.



Gaba ɗaya suka kura idanu suna jiran ganin wanene zai fito daga cikin Motar.



Lokacin daya bude cardoor din Ya zuro kofarsa basu gane wanene ba amma daya karasa fitowa gaba daya suka Zare idanun su, Har suna hada baki gurin furta"Sheikh Imam Malik..."



 kwata kwata baisan da zamansu ba, Har saida suka ambaci sunanshi tukunna ya lura da su.



A hankali ya ɗaura idanunshi akan fuskokinsu, Mutanan da har abada bazai ta6a mantawa da irin Butulcin da su ka yi masa ba, Tsantsar mamaki ne akan fuskokin kowan nan su daga shi har su din sun kasa motsawa.




Tun Lokacin da suka samu sa6ani Yau kimanin shekara goma sha takwas da zumuncin su Ya yanke basu kara haduwa ba kuma babu wanda ya nemi wani, sai yau da su ka yi haɗuwar bazata cikin ikon Allah agidan dg.

 


Wani irin nauyin shi da kunyarshi ne Ya lullu6e su,



Hajiya layla ji tayi kamar ta haƙa kasa ta binne kanta saboda kunyar Imam malik, duk tasha jinin jikinta, Saboda Kunya yasa ta dinga kare fuskarta da kasan hijab din ta.



Alhaji Ubaid kuwa Kasa jure hada idanunsa yayi dana sheikh Imam, wani irin kwarjini yayi masu.



A hankali Yake binsu da kallo mai wuyar fassaruwa..



Kamar yadda suke mamakin ganin shi haka shima Yake mamakin ganin su, komai daya faru arayuwar su suka soma tunanowa kamar a yanzu yake faruwa, ba zai ta6a mantawa da rashin mutuncin da sukayi mashi ba, ganin su da ya yi sai ya zamana kamar sun fama raunin dake a acikin zuciyarsa ne.



Kallon kallo su ke jefawa junan su, dr shureim da Benazir sun yi zuru da idanu kamar wadanda suka ma sarki Karya fadawa suka turke su.


Shureim ne yayi karfin halin tunkarar sa duk da shakkarshi da yake ji, zuƙunnawa ya yi daga gabansa cikin sanyin Murya ya gaishe da shi cike da fargaban martanin da zai mayar masa.


Kallonshi yayi kawai tare da juyawa ya haura kafarsa Ya nufi Ciki, Ransa Ya 6aci da ganinsu, Dayasan zai hadu da su da ba abunda zaisa Ya tako kafarsa Yazo gidan.



Kasa mikewa Dr shureim yayi, saboda karayar da zuciyarsa tayi, kwata kwata baiji haushin abun da baba Imam yayi masa ba, duk da baiji dadi ba, amma kome ya faru yafi ganin laifin iyayensa, saboda sune suka dasa masa ƙiyayyarsu a zuciyarshi..



"Ya shureim, ka yi haƙuri, Ka tashi mu shiga ciki" cikin sanyin Murya Benazir ta faɗa, yayin da take tunkararshi, Ta ruko hannunsa acikin nata, lokacin daya ɗago hawaye ne kwance a saman fuskarsa.



"Ba zan Iya shiga ciki ba, har yanzu baba Imam fushi yake damu, Nasan kona shiga bazai bari mu gana da Aisha ba, ku shiga zan jira ku a mota" 


ya ƙarashe maganar kamar zai fashe da kuka.


Tsananin tausayinsa ne Ya kama su, iyayen nasa da yake sa ran zasu lallashe shi su taimaka masa ahalin da yake a ciki sam sun kasa magana saboda su kan su sun muzanta agaban Imam Malik, Gaba ɗaya sun sare har sun fara tunanin komawa Gida.



Basu Gama Yanke shawara ba, sai ga Motar Abie Ta kunno kai, daga Inda su ke suna iya hango  su a cikin motar, mutum biyu ne agaban motar Abie da isod soldier.


Security Officers ne suka tsayar da su, amma daga baya suka ga Motar ta nufo ciki alamar sun samu iznin shigowa..


Yana tsayar da Motar, Anila ta fito daga back seat, fuskarta sharkaf da hawaye, ta goyo junaid abayanta, cikin sauri Ta nufi Benazir suka rungume Juna..


Daga Bisani Abie Da Mami suka fito Daga motar, kwata kwata babu walwala akan fuskokin su daga gani suna a cikin matsanancin Hali na damuwa.



Bayan sun gaggaysa da juna, Kafin daga bisani suka dunguma Izuwa Cikin gidan, Gaban kowan nan su na faduwa rass rass daram dararam saboda zullumin me zai biyo baya, gasu dai dukan su sun haɗu.



Aslm barkanmu da wannan lokaci 

Ina Mai farin cikin sanar daku cewa Zuzeam ventures takawo maku ingantattun magunguna masu inganci cikin Aminci Muna da kaya kamar haka

 Mallaka Maganin sanyi

Maganin cire tumbiMaganin farin jini

Maganin matsiMaganin mata

Maganin sa ni’ima da dandano

Dulka Amare Set na gyran jiki

Set na amarya

Tabaje tsumin Gomba

 Xuma kiba ta hips and Brest

Magungunan gyran Brest

Magungunan Karin hips

Maganin sliming

 Muna da kaya masu inganci  cikin sauki da rahusa 

Ina wadda keneman mallaka sahihiya quaranty wlh hajiya kixo ga zuzeam ventures xakiji ddin mallaka duk fadin ran ogah duk fadansa wlh sai yyi sanyi 08144015291

Idan maganin mata kikeso akwai 

Idan gyran jiki kikeso gyran fata gyran Brest magungunan sa kiba da hips 

DOMIN samunta Kai tsaye kira wannan no 08144015291 DOMIN mgn da ita whatapp 08144015291muna tura kayanmu ko ina cikin iKon allah 🥰👌🏻

Bononza Bononza Tsimin kaninfari 1k Tsimin dabino 1k Gumba 700 Gumba aya da nonon rakumi 700 Garin kafi ciccibi 500

Garin bata gaban kishiya 500

Matsin mallaka tada zaune tsaye 2500

Turaren mallaka ba aba mai kishiya 2500 Total kayan 9500

Za a bakisu akan 4k

Kuma mutun goman farko nadakyautar Abun 2k

🗣️🗣️🗣️🗣️🗣️🗣️ ASSALAMU ALAIKUM ALHAMDULILLAH YAN UWA  NEW PROMO YA KAMMALA💃🏽💃🏽💃🏽😁😁😁 da 5k dinki ki kwashi kayan 12k hajiyata 💃🏽💃🏽💃🏽😃🙃Kazar gadali ta mallara Rabi 3500 Tsimin gam gam 1500 Ruwan kara zunzurutun dadı😋800 Garin 7in1 1k Gumba 3 balai 500 Gumba kwakwa da dabino 500 maganin Infection 1k Garin zunzurutun dadi 1200 Matsin ba a fira d wando 500 Matsin infection mai matse mace gam 500 12k All at 5k https://wa.link/l1gcz8 kedai dannan link dinnan don samun naki ki maza kiyi bucking koda kudinki saida Rabonki.



*Welcome, Littafin kurkukun ƙaddara 500 ne, dukanshi Book One two and 3 Idan kin shirya biya ga Details da zaki tura*


3196407426 


First bank 


Bature Hafsat Muhammad,


 *bayan kin tura zaki bada transaction reciept ko screenshot na debit alert a matsayin shaida ta wannan number din 08103884440*

Post a Comment

Idan kuna da tambaya akan abinda Baku game ba ko kuma kuma Neman littafin da babu a nan kawai ku ajiye tambayarku a ta comment ko wani shawara da Zaku bamu.

Previous Post Next Post

Sponsored Link

Sponsored Post